Kannywood

Matar Kirki Matar Kirki Allah Ya Jikan Saratu Daso

Matar Kirki Matar Kirki Allah Ya Jikan Saratu Daso

Matar kirki. Matar kirki. Matar kirki. Mai zumunci. Mai aiki tuƙuru wajen neman halaliyar ta. Mai barkwanci. Mai fara’a. Mai tausayi. Mai zummar tallafa wa mabuƙata. 

Abokiya ta ce a tsawon aƙalla shekaru 20. Amma akan daɗe ban gan ta ido da ido ba; rabon da in gan ta tun cikin 2018 – shekaru 6 kenan. Sai dai waya. Sai text.

Mun yi waya ta ƙarshe a ranar 7/2/2024. Ita ta kira ni ta nemi wata alfarma. Muka tattauna. Na ce za a yi. Amma sai na tuntuɓi wasu mutane a Abuja da Legas. Na ce zan kira ta idan na kammala. Na fara tuntuɓar su. Aka fara dacewa.

Amma ban kira ta ba. Hidindimu sun rincaɓe. A duk lokacin da na gan ta a soshiyal midiya, sai na tuno. Sai in ji wani irin ba daɗi. Sai in ce zan kira ta anjima, ko gobe, ko jibi. Yanzu wata ɗaya. Har ma na tura mata wasu saƙwanni na daban, ta ba ni amsa.

Wayyoo, ashe rayuwar ce ke ƙarewa. Ban san cewa waccan wayar ta bankwana ba ce. Sam, ba mu kawo mutuwa kusa ba. Darasi ne!

Ta yi sahur yau. Ta kishingiɗa domin ta huta. Ba ta farka ba. Tafiyar kenan!

Allah ya rahamshe ki, Hajiya Saratu Giɗaɗo.

Leave a Comment

error: Content is protected !!