Hausa Novels

Matar Mahaukaci Complete Hausa Novel

Matar Mahaukaci Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

A guje ya nufi ƙofar gida ya na shirin fita Abbasi ya rufe ƙofar.Tsayawa yayi cak ya na zaro manya fararen idonsa wanda baƙin gawayin da ya shafe fuskarsa da shi ya ƙara fiddo hasken su,cikin murya mai taushi Abbasi yace “ina za ka je kuma Mahomet?”bai bashi amsa ba sai waigawa bayansa yayi ya na kallon Ammi hannunta riƙe da almakashi cike da tsoro ya koma bayan Abbasi ya na mai ɗora hannuwansa masu datti kan farar shaddar Abbasi.

 

“Ammi tunda bai so ki bar shi kawai”cewar Abbasi , Ammi tace “ba ka ganin duguzar ta yi yawa kamar wani mahaukaci ya bari na ɗan rage masa”daga can bisa ne Hajiya Atine ta bushe da dariya tace “yo da can mine ne in ba MAHAUKACIN ba?”kai Abbasi ya ɗaga ya kalli mahaifiyar ta shi ya na mai girgiza kai kafin ya juya ya kamo hannun Mahomet.

Ammi na gaba su na take mata baya har suka isa ƙurya gida inda a can part ɗin ta ya ke,su na shiga falo Mahomet ya ja ya tsaya bakin ƙofa ya na mai sake kallon almakashin hannun Ammi ganin hakan ya sa ta ajiye shi bisa table da gudu Mahomet ya nufi ɗakin sa ya shige yayinda Abbasi ya bi bayan shi.

 

 

 

Tsakiyar gado ya tsinkaye shi a zaune ya jawo bargo ya rufe dukan jikinsa ya bar fuskarsa a buɗe ya na kallon ƙofar shigowa.Ganin Abbasi ne ya sa shi dirowa ya na kallon shi,ajiyar zuciya ya sauke yace “mu je na wanke ma wannan abun da ka shafa a fuska bai yi ma kyau ba” kafaɗa ya maƙe tare da girgiza kai alamun bai so.

Abbasi yace “ba zan yi ma wanka mu je fuska kawai zan wanke ai ba ka yi dauɗa ba”cike da yarda da lafazin ɗan uwan na sa ya nufi toilet.Fuskar sa Abbasi ya wanke masa da soso da sabulu nan fah ainahin fuskar sa ta bayyana wacce ta ke doguwa siririya mai ɗauke dogon hanci har baka.Madubin da ke cikin toilet ɗin Abbasi ya nuna masa,kallon kansa yayi sai ya saki murmurshi dimple ɗin sa suka lotsa jajayen laɓansa sirara suka buɗe fararen haƙoransa suka bayyana.

 

Cike da dubara Abbasi ya raba sa da kayan jikinsa,yayinda Mahomet ya shagala da kallon kansa dan a duniya babu abinda ya ke so sama da madubi.

 

Pampo ya jawo ya fara yi mashi wanka ya na watsa masa ruwa irin yadda ake yiwa yara,Mahomet ya shiga ƙyarƙyata dariya ya na jin sanyin ruwan na shiga ɓargon jikinsa.

Man wanke kai Abbasi ya shafa masa nan fah aka fara daga dan kuwa babu abinda Mahomet ya tsana irin a taɓa gashin kansa,kamar wani ƙaramin yaro haka ya shiga rera kuka tare da ƙoƙarin zillewa Abbasi kuma na ta ƙoƙarin wanke masa kumfa.

 

 

 

Ko da aka gama wanka tuni Mahomet yayi fushi da Abbasi wanda kusan kullum haka su ke da zarar yayi masa wanka mai ya ɗauko zai shafa masa amman ya ƙi bari sai ma gado da ya ɗale ya duƙunƙune.

 

 

 

Ganin haka ya sa Abbasi yin murmushi ya fito,a falo ya tarar da Ammi ta yi tagumi ta na ganinsa ta miƙe tace “duk shaddar ta ka ta ɓace da dauɗa halan wanka kayi mashi?” Abbasi yace “bai komi Ammi ai da na kai ta wajen wanki tsaf za ta dawo,wanka nayi mashi ya ƙi barin ma na shafa masa mai”

Ammi ta goge ƴar ƙwalla tace “Allah biya ka da mafificin alkhairi Abbasi yadda ka kula da ɗan uwanka Allah baka ƴaƴa masu jinƙai”yayi murmurshi yace “amen Ammi na gode zan tafi na canza kaya,a bashi maganin shi”da “Toh”Ammi ta amsa.

 

 

 

Gorar ruwa ta ɗauko cikin frigo ta nufi ɗakin sa,ya nan kwance ya rufe a bargo kamar sabuwar amarya.Ya na jin muryata ya yaye bargon ya zauna tsakiyar gado daga shi sai gajeren wando wanda Abbasi ya saka masa kafin yayi ƙoƙarin shafa masa mai.

Ledar maganin da ke bisa didilin gado ta buɗe tare da ɓallo masa magani ta basa,babu muso ya karɓa ya hanbaɗa baki sai da ya tatamna sannan ya karɓi gorar ruwan ya shanye tass.

“Ammi…”ya furta da muryar sa mai kamar ta ƴan shaye-shaye, kallonsa tayi ba tare da tace komi ya murmusa ya kuma cewa “Ammi ?”tace “umhum Mahomet ya jikin na ka?”sai da ya karye wuya har bada wani ɗan sauti kafin yace “da sauƙi zan yi sallah”cike da murna tace “dagaske Mahomet ?”kai ya ɗaga mata.

“Je kayi alwala to amman ka yi addu’a in za ka shiga toilet”bai ce komi ba ya sauka daga bed ya nufi toilet yayi addu’a ya shiga,bakin ƙofa ta tsaya ta na kallon yadda ya ke alwala daidai bai manta yadda ake yi ba dan rabonsa da yin Sallah an fi wata uku.

Doguwar riga jallabiya ta miƙa masa tare da shimfiɗa masa tapis,iƙama ya fara yi kafin ya ƙabarta ya fara karatu ya na yi ya na tsayawa saboda yadda zuciyar sa ke suya raka’a biyu kawai yayi salamce.

Juyowa yayi ya dubi Ammi wacce ke bakin gado,saitin zuciyar sa ya nuna mata da sauri ta nufo sa ta na tambayar “mi kake ji?”bai iya cewa komi ba sai lumshe ido da yayi….

 

 

 

 

MAI JAN GERO

 

 

Wani yanki ne daga cikin ƙauyen Tchadoua wacce ke garin Maradi jamhuriyar Nijar.

Ginin ciment ne wanda ya sha ya harshe tun daga waje har cikin gida.

Tun kafin ka shiga gidan za ka iya jiyo sautin kukanta tare da suratai na azaba irin na sargantatun yara.

“Alƙur’an tunda na fara sai kin bari na ida,yo ina dalili yarinya kamar jikanyar lasaru kullum kai a tsefe kamar chrétan (chrétienne)”Inna ke faɗa ta na mai sake matse kan Maryam wacce ke kukan kitso.

“Ai dai gashi na ne dan haka ki sake min kai nace ban so ko doli ne?ke da kika damu ba sai kije ayi maki ba”cikin kuka Maryam ke faɗar haka,Inna ta tuntsire da dariya tace “ai fah dai ko mi za ki faɗa sai na idasa” Maryam na kuka na ƙari Inna ta yi mata zane shidda (manyan kitso)ta na gamawa ta tureta daga gabanta tace “sai ki tashi daga gabana ja’ira ke yanzu hakan da na rufa maki asiri ba ki ji daɗi ba?”Maryam na turo baki ta goge ƙwalla ta fita waje.

Bokiti ta cika ta nufi banɗaki,wanka tayi soso da sabulu kafin ta fito.Hannuwa Inna ta shiga taɓawa ta na ce “laha ila…ke yanzu saboda gantali sabon kitson kika wanke?”Maryam ta turo baki tace “to shikenan sai na yi wanka ban wanke kai ba?”Inna tace “eh ta yaya za ki ƙin wanke kai tunda sabuwar amarya kike”ita dai Maryam ba ta kula ta ba ta shige ɗaki babu jimawa ta fito cikin riga da sket na atamfa ta kashe ɗauri.

“Ina zan tafi sayen awara”ta faɗa ta na mai ɗaukar tasa mai murfi,”a dawo lafiya”cewar Inna.”To ki ban kuɗin”ta faɗa cikin marairaicewa “a’a ko sisi ba zan baki ba tunda ga abinci can tukunya na dafa”cikin gunguni tace “Ni ban cin wake kuma ai na faɗa maki”Inna ta miƙe daga zaunen da ta ke a kujera ta ɗauko radiyo da ke kan frigo tace “sai ki yi ai,wai an yi ma Ɗiya shegen miji yaushe kika fara tsanar wake?ina ce dai jiya alala kika yi”kwanon ta saki ƙasa ta koma ɗaki ta na kuka.

 

 

“Dawo ki karɓa ni ban iya jarabar ki ba, wannan masifa ban san inda kika ɗauko ta ba sai dai can dangin ubanki ni Ɗiyata (cewa da mahaifiyar Maryam) ba haka ta ke ba har mu ka rabu da ita lafiya “fitowa tayi ta karɓi kuɗin ta duƙa ta ɗauki tasar sayen awara kafin ta fice.

 

 

Ta na tafe ta na waƙa Habsou Garba “iyee babu kamar Niger dan ku san babu kamar Niger tashin hankali Niger ba ta gada ba kwanciyar hankali ne mu ka gada…”cak ta tsaya jin Rabe na ƙwala mata kira,daidai gabanta ya tsaya ya na gyara tsayuwa yace “sai ina Autar Inna?”sunne kai tayi ta kasa magana, murmurshi yayi ya kuma cewa “wai Mairo sai yaushe za ki barin jin kunyata?koko sona ne ba ki yi shiyasa kike ƙin yi mani magana?”da sauri ta ɗago kanta idonta suka faɗa cikin na shi.

Tatausan murmushi ta sakar ma shi tare da girgiza kai ta kuma sunne kai.Ajiyar zuciya ya sauke yace “to mu je na raka ki inda za ki je”cikin jin kunya tace “a’a na gode je ka gida kawai ka huta”farin ciki fal zuciyar sa yace “to aikin mi nayi da zaki ce naje na huta? wannan ɓotar da kike gani Baba ne yace na kawo mashi ita gida sam ni ban san yadda ake noma ba balle nayi shiyasa ni ke ta fafutukar yin karatun bokona saboda in samu aikin gwamnati inda za mu huta in mun yi aure”Muryar Inna suka ji ta na cewa “keee!Maryamu sayen awarar ne nan?”da sauri tayi gaba shi kuma Rabe ya shiga gidan su ya na tsinewa Inna da ta hana shi isar da saƙon sa gun masoyiyyar shi.

 

 

 

Maryam kuwa banda dariya babu abinda ta ke a fili tace “hege kaji ƙarya wai bai iya noma ba bayan ga ƙafafunsa nan sun yi futu-futu kamar mai sharar kasuwa,za ka ci ƙwal uban ka ne sai na tatse ka sarai ta yadda ko sunana kaji an ambata sai gaban ka ya faɗi” gidan da ake sayar da awarar ta shiga ta sayo ta dawo gida.

Sai da Inna ta yi mata dundu da baya sannan tace “ban hana ki sauraren wancan ɗan iskan ba?duk ƴan matan garin nan na shi ne ko wacce ya gani ya na so kamar kare shine kika wani sadda kai kamar malam da ɗalibi”

Maryam ta turo baki tace “haba Inna shine sai kin dake ni ?ai dai kin san babu abinda zan yi da wannan baƙauyen ni ɗan birni zan aura”Inna ta dafe ƙirji tace “iyeee!Maryama yanzu ke ce ke faɗar kalmar aure?laha ilah ƙarshen zamani ya zo to bari uban ki Salihu ya zo na shaida masa aure kike so ya yi maki kafin ki jawo ma mu abun kunya”

Maryam tayi rau-rau da ido tace “Ni daga ban ce ina son aure ba”Inna tace “a’a ga shi kuwa sai ƙara nanata kalmar kike”

 

 

 

 

 

★★★ *MARADI VILLE*

 

 

 

Tunda Mahomet ya sha ruwan addu’ar da Ammi ta bashi wata irin masasara ta rufe sa,sai karkarwa ya ke ya na rawar sanyi.

Ammi tagumi tayi ta na kallon ikon Allah yadda Mahomet bai son ko kallon kofin da tayi mashi tofi ciki.Ana haka sai ga Abbasi ya dawo cikin shiga ta ƙananun kaya,”subahanallah mi ke damun shi kuma?”Ammi tace “daga na karanta Ayatul Ƙursiyu da amanar Rasulu cikin ruwa na basa”Abbasi yace “sallah yayi ko?”Ammi ta gyaɗa kai shiru yayi ya na kallon Mahomet kafin yace “Ammi sai ni ke ganin ciwon Mahomet kamar ba na asibiti ba ne duba da yadda ya tsani duk wani abu da ya shafi Ayar Allah”Ammi tace “to mu bari har Daddyn ku ya dawo sai mu ji mi zai ce”Abbasi ya zauna kusan Mahomet ya fara yi mashi karatu ai kuwa ya fara zabura.

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!