Matar Makaho Hausa Novel Complete Download
Matar Makaho Hausa Novel Complete Download
Rukayya Ibrahim
Godiya ta tabbata ga Allah da ya nuna mini wannan Rana da Zan fara rubuta lbr na na farko cikin hukuncin ubangiji Allah ka bani ikon gamawa lfy
Tsokaci wannan shine novel Ina na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error amini afuwa
Free page
Matan Kano Whatsapp Group Link
Page 1
Kuka nake baji ba gani bakin ciki ke dankare a cikin zuciya ta Wanda in har banyi kuka ba bazanji saukin suba Wai ni ce amarya amaryan ma na makaho mara ido na daga lulubena kasanciwar dakin akwai wutan nepa glop ya haska Koh ido shiya bani Daman ganin daki dakin da Koh a mafarki van taba tunanin akwai ranan da Zan iyya rayuwa a irin Shiba Wai yau shi ake Kira da dakina na aure ni sumayya bansan lokacin da wani irin kuka ya sarkeni ba cikin takaici Mai tarin yawa ya Allah me naiwa Yan uwan mahaifina da suka sakamin da wannan rayuwa Mai na tsare musu da suke mini irin wannan muguwar tsana da hassada ya Allah duk wannan magana cikin kuka nake yinsu
Tsaye yake yafi minutes 30 Amma ya kasa karasawa cikin kofar wani irin fargaba ne dankare a cikin ransa Wai yau shine da mata sukutum Koh a mafarki Bai taba tunanin aure ba kasan shiwarsa makaho maraya kuma Mara galihu sai abinda ya nemawa kansa Amma yau har Mata aka basa wance Bai taba tunanin samun taba amasayinsa na miskini Anya zata karbesa a matsayin miji zata yarda ta rayu dashi cikin akwai Koh babu wannan sune abinda suka tsaya masa a Rai yayi ta maza ya daga kafarsa hade da Bismillah Yana tafiya da sandar sa Yana ma kansa jagora zuwa filin kewayayeyyen kofar su Dan madaidaici ya juya ya tura kofar ya rufe harda lalubar sakata ya saka a sannu a hankali yake takawa har yaji ya taba Dan tudu kadan hakan ya nuna Masa ya iso dakalin kufar daki haurawa yayi sama Yana lalube tar yaji ya laluba ginin daki Yana bin ginin a hankali har yaji ya shafa window yanabi a hankali har yaji ya Kama labule mai masifan laushi da kamshi Wanda tunda yake a rayuwarsa Bai taba tunanin zai taba irinsaba kasan shewarsa mutunne shi Dan babu ruwana ba ya maula Koh bara baya neman taimakon kowa in dai na abin duniya ne sai dai na lalurarsa Wanda ya zamto Masa dole
Karanta Littafin Rumah Hausa Novel Complete
Da sallama a bakinsa ya daga labulen tare da jingina sandar sa a kofar dakin ta waji ciki ciki na amsa sallamar itama Dan ta zama dole na daga kaina ina kallon wanda Koh ba’a fadaba nasan shi ake nufi da ango makaho cikin wani irin takaici nake kallonsa don matashine Wanda bazai Gaza shikara 28 zuwa 30 ba laifi makanta da wahalan rayuwa su kadai za’a kira cikas a tare dashi don kyekkyewa ne na karshe dogo fari tas wanda wahala ta kodar da fatarsa Amma duk da haka fatar daga Gani zatayi matsifar laushi gemu mayalwaci sosai ga idanu masu girma da haske amma mara amfani a ganina bakinsa madaidaici Mai shegen kyau ga hanci har baka Mai yalwan gera don daga gani yanada yalwan gashi sosai sai gashin kansa Mai yawa amma rashin samun wadasheshen gera sai ya Yi wani iri Amma daga Gani gashine na Fulani asali duk da babu datti don fes Kan take kiransa na zaratan mazane masu Kiran karfin sosai na kurawa kayan jikinsa ido wani kudadden yadine na shadda wando da riga Mai guntun hannu Wanda suka Sha ruwa sosai wai su ya saka kenan ranan aurensa daga Gani sune na gindin akwatin sa Koh Bai fada ba ni Kam na raya a Raina kauda fuska nayi kamar bansan mutun ya shigo ba shi kuma cikin sanyin jiki da lalube yaji ya taka wani cafet Mai shigin laushi a cikin dakin duk da baya gani yasan tabbas Mai tsadane Koh me na dakin Nan don Bai mantaba dazun khadija take Masa gulma wai dakin Aunty’amarya Mai kyau da Kaya irin na gidan murtala Hon na unguwan su harma nata yafi nasu kyau tun daga lokacin jikinsa ya kara sanyi don ya tabbatar ba yar kananun mutane bane aka aura Masa a matsayinsa na makaho da lalube ya iso tsakiyar dakin Wanda yaji abubuwa Kamar filo a xuzxube a kasar cafet in dakin a hankali ya zauna tare da aje ledan dake hannun sa baka cikin zazzakar muryarsa Mai cike da Kamala ya gai Dani Koh juyuwa vanyiba don bana son ganin sama bare na sake Jin ya sake furta Ina wuni nayi wani dogon tsaki Jin haka yasa shi Jin wani mummunan faduwar gaba Amma baice kome ba yayi shuru munkai minti goma babu Mai shiwa kome sai Karan fanka Kiran OX babba wance Taki bawa dakin wani irin iska Mai sanyi sosai cikin rawar murya yace ga kaza nan kici sai muyi nafina mu gode wa Allah cikin zafin nama da takaici na hayyaya Koh Masa cikin fada Wanda duk Wanda ya sanni yasan ba halina bane Kuma Koh kyau Bata mini ba nace baza’a ci matseyacin kazar kaba kuma sallah kayi tayi har alfijir ya ketoh Bai shemin kome ba Amma kallo daya namar nasan maganar ta dake sa sosai a hankali ya laluba yafita waji yayi iyya nemar buta Koh Randa baiji inda aka aje ba saboda duk kayan kofar an sauya Mata zama kasanciwar sabbi aka kakkawo hakan yasa ya koma dakin a hankali da sallama Ina dai zaune Ina kalonsa yazo ya fara lalube a hankali ya daga labulen ya tura kofar ya rufe harda sakata cikin nutsuwa Naga ya fara lalube ban ankaraba naji ya lalubu ni cikin wani irin shock daga ni harshi muka Masa baya shikam harda buge kafar sa da katakun gado cikin i’ina nace meye haka cikin Dan sanyi jiki yace kiye hakuri ina neman gadone Zan kwanta cikin gadara nace wallahih bazan kwanta dakai gado daya ba gadai kujira a Chan jika kwanta a hankali ya fara lalube Ina dai zaune Ina kallonsa haka ya ringa zagaya dakin daker ya gane kujiran a hankali ya zauna ya cire rigansa ya kwanta a hankali cikin lumsheshen kujira na alfarma 3sita Nima kayan na cire tunda dai ba idone dashiba na ragi daga ni sai brz da siket nayi adu’a na kwanta a hankali nake sauke ajiyar zuciya har bacci ya dauke ni shikam ya kasa bacci sai tunane tunane yake yanason yin lafilfilu Amma ba Hali tunda baisa inda zai samu ruwa ba a kofar tasu Kuma baison zuwa rijiya a Darin nan gudun wani a cikin mutanen gidan su gansa su Masa abinda suka Saba rashin mutunci a sannu a sannu wani bacci Mai Dadi ya daukesa don a tsawon rayuwarsa Bai taba bacci ana zafi da fanka ba sai yau lol asuba da gari amarya da ango
Free page ban yarda da a sayarmin da littafi ba pls
Jinjina ga Yan Free books
Mom Abba
Mrs jabeer
Sarah
Zee black
Nafisa voice note
Kawata ta kaina Salma Adam Allah ya bar kyauna
MATAR MAKAHO
~ Na ~
Rukayya Ibrahim
Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa
Free page
Page 2️⃣
Kiran farko akan kunnensa ya farka a hankali tare da addu’an tashi daga bacci kafarsa yazura ya sauke a kasan cafet da Bismillah ya mike saye ya fara laluben rigarsa daya cire jiya da dare da zai kwanta cikin hukuncin Allah ya samu rigan ya saka a hankali ya nufi kofa cikin lalube ya gane kofar ya bude ya fita ya tuna baisan inda buta take ba don baiga tsohon tasaba sake dawowa yayi a hankali yake lalube harya lalubo gado ba tare daya hauba yasa hannu yana laluben ta cikin sanyi Amma baijitaba a cikin ransa ya kitsima lallai wannan gadon babbane sosai Hawa yayi a hankali Yana lalube har yaji hannunsa ya taba wani abu Mai masifan laushi sosai Kamar fatar jinjira da sauri ya zari hannun cikin murya kasa kasa yake. Tattaba filon da yaji kanta akai inda Allah ya Sosa ma Mai nauyin vaccine ita da Allah Bata San ya taba Mata jiki ba cikin bacci take Jin ana bubuga Mata filo ido ta bude a hankali don baccin Bai ishitaba ta sauke idon ta a kansa Yana zaune kusa da ita cikin sauri ta Mike da masifa tace Kai lfy meya kahoka Kan gadona eye ,, cikin sanyi Wanda na Lura halittansane yace Daman buta nake so ki nuna mini na ibo Mana ruwa asuba tayi wani haushine ya kamani wannan miji ne Koh rainon sa zanyi Amma saboda albarkacin sallah yasa nace toh muje na dauki rigana nasa na fita a dakin nayi wajinda aka kewayemin da fallange Dan madaidaici Wai kitchen na shiga kayan kitchen ne na alfarma kome yaji yar an rasa wajin sawa an koma da saura Kamar yanda aka maida kujiruna da wasu Abubuwan kayan dakina masu yawan gaske na shiga na kunce butan a cikin kwalinsa na karfine cikin kayan da aka saimin da na roba na hada biyu na fitoh na samesa a saye yana jirana Mika Masa nayi cikin kaushin murya nace randuna na babu ruwa cikin lalube ya karbi butan hade da furta bara na ibo a rijiya kala bance Masa ba ya fita sai gasa ya dawo da ruwa a buta daya ya shigo ya ajimin ya koma ya dauko dayan ni kuma tuni na idar da alwala harna shiga daki na bude akwatina na dauki hijab da sallaya na shinfida na tada sallah
Alwala yayi ya tafi masallaci da sandar jagoransa Ina idar da sallah nayi lazimi har lokacin Bai dawo ba na daga idanu na na kalli agogon bango Wanda aka likawa bangon dakin karfi Shida saura naja dogon tsaki Dan a lokacin aka dauke nepa ni kuma bana iyya bacci ba AC Koh fanka Sam nasan Koh na kwanta bazan iyya bacci ba Ina zaune har karfi Shida lokacin gari ya waye dakin yayi haske a hankali nake bin dakin da kallo dakine madaidaici sai gadona Wanda yaci Rabin dakin da kujira dogo guda daya don sauran babu wajin zama Mai dasu akayi plasma TV ta gefin gadon aka makala don ba fili da waddrop ta daya gefen sai kafet da su kushin da aka saka a tsakiyar dakin da karamin freezer ata bakin kofa kayan sawana makil a akwati set dake gefen Kan gado sai fankan kasa sune suka samu wajin zama a dakin a hankali nakai hannu na dauki jakana na bude na dau waya ta Ina dannawa tunda babu nepa bare na kunna TV an hadamin kayan kallo harda Star Time Ina da sallama naji ya shigo dakin na amsa ya laluba kujira ya zauna cikin sanyi yace ina kwana kamar bazan amsa ba na amsa da lfy klau cikin sanyi yace me zakici na sai Miki cikin mamaki da al’ajabi Wai sayo abinci Ina amarya akawoni cikin gidansu Amma arasa Mai bani abinci sai ya siyo duk da ban karewa gidan kallo ba nasan babbane tun jiya da dare maganar sa ce ta dawo Tani daga duniyar tunani Dan wake Koh alele Koh kosai za’a karba miki cikin mamaki nake kallonsa sai Kuma naji ya bani tausayi tun jiya yake kokari yaga ya kyautata mini yasa cikin sanyi nace Masa
Matar Makaho Hausa Novel Complete Download
Jinjina ga free books
Gaisuwa ga members in free books
Mom Abba
Zee black
Sarah
Nafisa voice note
MATAR MAKAHO
~ Na ~
Rukayya Ibrahim
Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa
Free pages
Page 3️
“Basai ka saya abinci ba, akwai kayan abinci, ruwa nake so, asaya da bread sai kayan meya” cike da kuzari ganin na masa magana, a taushashe sabanin jiya, ya Mike ya fita, Yana fita, ya laluba aljuhunsa Aiko Allah yasa,Yana da gudan dari biyu da dari, na cinikin mangoron sa na jiya, da safe da Yan change ya hada ya fita tsakar gidan, sai ji yayi an saka ihu da shewa, daga mata har matasan samarin, ana ga ango ga ango, wanda Koh tantama babu,duk wanda yaji yasan na raini wayo ne, da shikiyanci kasanciwar ya Saba da irin wannan tozarci na Yan gidansu, sai abin Bai damunsa Sam, wuce warsa waji yayi, ya fita kofar gida, dayake bakin titi ne gidan nasu, yasa shi sayuwa a bakin kofar gidan, Bai jima ba dayake safiya ne, yaji Mai ruwa na bugawa kiransa yayi duka ya saya, ya hadasa da yaron makwantansu, ya nuna Masa kofar amarya, shi kuma ya shiga shagon haladu, sayan bread na dari Mai kyau ya hada da Lipton na goma, da sugan hamsin, ya karasa table in gwanja yasai kayan meya ya hada ya kamo hanyan gida ,
Mai ruwa ya shigo da yaro “na tashi na fitar da randana, na roba Mai girma sosai irin Mai cin jarka Sha biyar innan, Mai ruwa na Gama juyewa, Yana shigowa ya biya kudin ruwan, ya ajimin laidan cefenen “dauka nayi nawuce kitchen”, shi kuma ya fita, “kitchen na shiga kome an jiramin kuma ba laifi kitchen din ya dauki Rabin kayan da akai mini, gas na kunna na dauko dankalin turawa na fere na daura a tukunya, kwai na fasa na zuba kayan hadi na aji a gefe, kettle na ruwan zafi, naso daurawa Amma ba nepa dole na daura bojuwa, ( tukunya) a dayan Kan gas in na zuba kayan kamshi da Lipton na rufe, naji” buruntun bude kofa lekawa nayi nagansa rike da Ghana must go na kaya madaidaici na kayansa ya shigo da lalube’ ya fada cikin dakin yaje ya aje sai gasa ya fitoh yana lalube cikin Dan tausayin sa, wanda bansan Ina dashi ba, “nace maikake nema ne” ? cikin sanyin halinsa yace bokati, “na mike na dauko masa” sabon boket, da kwandon soso, na kayana da soso sabo da sabulu, na wanka Mai sada na akwatina,” hada a kwandon na Mika Masa” ya karba cikin lalube ya lalubi kwandon yace La!! ai Ina da soso harda sabulu barshi kawai “cikin Jin haushi nace na sani ai na baka kayi dasu” Bai Musa ba ya karba yaje ya zuba ruwa a bokatin ya cika, da lalube ya shiga ban daki, ya ajiye ya dawo ya lalubi inda ya aji butar da yayi alwalan, asuba ya dauka ya cika ruwa ya wuce bayin,
“Cikin kankanin lokaci na hada breakfast, Mai kyau na soyayyen dankali da kwai tie ga bread a gefe naji daki na dauko kazar dana Gama zagi jiya nazo na juye a kwando na makala gudun karya rube, da rana nayi meya dashi’ na fada dakin na kakkabe gado na jira filon Kan kujira, na share dakin na fesa turarukan daki, na fitoh na share baranda na hada da kasar kofar duk da ban taba share kasa ba, sai dai tayis Koh seminti haka na lallaba na share, Ina gamawa” Yana fituwa a wanka daure da zani, tsoho a kwankwaso hannunsa dauke da kayan sa daya cire, a boket Yana lalube ya dibe ruwa ya zuba a boket in, ya jika kayan ya mayar bayan gida ya aje, ya fito Ya shiga dakin, “na ibi ruwa Nima na shiga Wanka da soso da towel na Ina fituwa na fada dakin, ban Damu ba, tunda ba kallo yakeye ba” “Ina shiga na gansa zaune a kasa ya chanja Kaya zuwa jallabiya fari duk da yasha ruwa jallabiyan, Amma a wanke tas, “na shiga na bude akwatina na dauki Kaya, rigane dogo na material Mai kyau da tsantse, NASA na hada da hula fari na fita waji na shanya towel in a igiya da kayan da na cire samun kar suye tsami, na shiga kitchen na dauko abincin na fada daki da plet na zuzzuba karyawan na Mika Masa” “na ibi nawa nayi Bismillah Muka fara ci” babu Mai magana a tsakanin mu tunda yasa abincin nan a bakinsa yake godiya wa Allah a zuciyan sa, daya mallaka Masa sumayya amasayin Mata, tunda zata iyya dafa Abu ta basa yaci Wanda rabon da adafa abasa tun kafun ummarsa tabar duniya shiyake sayawa kansa, abinci she yake nemawa kansa,
“muna tsaka dacin abinci naji an banko kofar shashin mu an shigo, ba sallama aka daga Mana labule dukkan mu dagowa mukayi don ganin wani ishanshen ne, haka sabanin shida Banga mamaki a fuskar Saba sai dai alamu sun nuna baiji Dadin hakan ba, ya kurawa kofar ido Kamar Mai kallo yanda nayi sakake Ina kallon kofa cike da mamaki…….
Yan free books Naga comments naku naji dadin karfafa mini gwuwa
Mom Abba
Umme
Nafisa voice note
Dr humaira
Da sauran su
[…] Karanta Littafin Matar Makaho Hausa Novel […]
[…] Matar Makaho Complete Hausa Novel […]