Matar Malam Hausa Novel Complete
*MATAR MALAM*
*Bismillahi Rahamanin Raheem*
*Written by*
Mrs Fulani🐄
🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }
*…….1*
Hannuna ɗaya rike yake da wayata yayinda ɗaya hannun ke rike da jakar makarantata, cikin kwanciyar hankali nake taku cikin isa da gadara, dai dai majalasin Imam Usman nazo wuccewa, karatu suke shi da ɗalibansa ina wuccewa ne amma har najiyo tambayar da ɓarawon kajin unguwarmu ya jefa masa, na cewa..
“Allah ya gafarta, meye laifin yan matan da suka zaɓi lalacewa akan aure, zaka gansu kullum cikin shigar kayan banza da siffa marasa kyau.” Ɗagowa sauran sukayi suna kallona, abinda ya tabbatar min kenan dani suke,
Shi kuwa Imam Umar zuciyarshi ɗaya ya fara da cewa.
“Manzon Allah (S.A.W) yace akwai wasu mata amma yan uwane, sazu saka kaya amma zai bayanar da suran jikinsu, inda basun tuba ba, toh wuta ya tabbata a garesui, Allah ya kiyayyemu, sannan iyayensu suna da laifi suma, kamata yayi su nime mutumin kirki subada yaransu gudun karsu lalace.” Bayani sosai yayi musu, wanda ban karasa ji banayi wuccewata dan basu gabana,
Da sallama na shiga cikin gidanmu, da matar Babana muka haɗu girgiza kai tayi cike da bakin ciki tace,
“Naiha Allah ya shiryaki, shirin addinin Islama.Kuma wallahi idan baki cire wannan kayan jikinki ba sai na ɓallaki, shasha kawai”
cikin kunkuni na wucce tare da cewa” ba zan cir…” Haɗa ido mukayi da Yaya Ishaq dodon gidanmu kenan, simsim na shige ɗakinmu na yan mata.
Girgiza kai yayi cikin ɓacin rai ya fito gurin Matar babanmu yace.
“Innaji daga yau Naiha baxata kuma zuwa gidan Annah ba, dan duk wani shaiɗanci acan take ɗaukowa, ɗabi’ar yaran gidan duk ta kwashe dubi irin shigar jikinta don Allah, har kunya nake ace kanwatace ita, ko Ramla da Hajra da Zubaida basu wannan haukar kaman ita, kuma banga laifinta ba, tunda Annah ke saya mata kayan ba wata ba, zanyi maganin abun.”
“Yarinya ce sosai aiko su Ramla da kake zancanka akansu sun ɗan girmemata, kaga kenan har yanxun hankali bai gama wadatarta ba, Allah ya shirya mana ita” inji Innaji.
D’aga labulen ɗakin yayi ya banka min harara kafin yace.
“Uban me kike a ɗakin da bazaki islamiya ba.”
Mikewa nayi cikin taurin kai da rashin kunya, irin na tashen balaga, domin jin kaina nake dai-dai dakowa, kayan isalamiyata nasaka sannan fito ɗauke da jakata ina fitowa banganshi ba sai jin sakonshi nayi a tsakiyar kaina, ihu nasaka ins yarfe hannuna, yace.
“Wucce saura naganki a gurinsu Baby kintsaya,”
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
ina zubda kwalla ina kuka rike da kaina, har na kusan isowa majalasin suna nan tare da ɗaliban basu tashi ba, can gefensu kaɗan ɓarawon kajine naji yace.
“Allah kashirye mu, ace mutun ya zaɓi duniya fiye da lahiranshi makarantarma sai an haɗa da duka, kafin aje.”
Raina ne yakara ɓaci cikin hasala nace.
“Dan kutu…Abukazan kazanka bazan je ba inkai kake da wuta da aljanna karka bani da du… jaki ɓarawon kaji kawai yaushe har kasan Allah da zaka min wa’azi na ɗauka waw…”
“Ya isa haka, Allah ya shiryeki shiriyar Addinin musulunci, wucce ki bar nan.” juyawa nayi ahasale naga waye yayi min katsaladan a cikin maganata da ɓarawon kaji. Ina juyawa naga imam Usman, cike da tsiwa nace.
“Toh kaja masa kunne kar yasake shiga shirgina dan zanci ubanshi,”
girgiza kai yayi cike da al’ajabi, yanda nake kallon kwarya idanunshi nake kafta rashin *M* gyaɗa kai yayi cikin sanyin murya yace.
“Shikenan bazai sake ba balle kisamu damar zaginshi amma ki daina zagi babu kyau, yana zubda mutunci.”
Tafiya nayi tare da ɗaga kafaɗata, rakani yayi da idanunshi, sannan ya maidasu kan Nura, komawa yayi gurin zamanshi ya zauna sannan yace.
“Nura babu ruwanka da yarinyar can dan nalura bata shiga shirgin kowa toh don Allah kodan ka tsira da mutuncika ai sai ka, daina tanka maka, tunda kaga yanzun tana matakin jin ita wata ce, toh karka sake,”
Gyada kanshi yayi, nan suka cigaba da karatunsu.
°°••^^ ΔΔΔΔ^^••°°
Ni kuwa dana isa makaranta na makara ina shiga ana Amir ɗin makarantarmu shi ke taran lati, kallonsu nayi na ajiye agefe sannan nasa kaina wucce, finciko hijabina yayi dan dole na dawo, cike da ɓacin rai yace min.
“Miko hannuninki malama.,”
Murmushi nayi sannan namika masa, sai da yagama tsulla min bulala biyar ko ɗigon hawaye babu a cikin idanuna, har zan wucce Malamin Sira yace min.
“Dawo nan ki cire wannan farcen arnan da kikasa, karamar mara kunya.”
Koɗar banji ba na juya nakalleshi sannan nace.
“Hmm malam Yahaya bazan cire ba sai dai nadaina zuwa makarantar,”
Cike da mamaki, malam yahaya kalleni daman duk cikin malamai yafi zafi, toh ido da ido nace bazan cire ba, karɓan bulalar hannun Amir yayi yazo har gabana yace.
“Kika ce bazaki cire ba, ko?”
Sam babu tsoro a tare dani na gyaɗa masa kaina, zuga min bulalan yayi, sai da na botsare, cike da rashin kunya nace.
“Allah zai saka min,”
Bai fasa ba, sai da yayi min mugun duka, dakyar Malamai suka kwace ni, ina mikewa nace.
“Wallahi zaka biya abinda kayi, zaka san kataɓani, sai nanuna maka iyakarka, kazami kawai.”
Ina gama faɗin haka najuya nabar makarantar, ban tsaya ko ina ba, sai gidan Kakanina, tundaga bakin gater nake fasa ihu, hannuwana akaina, ina cewa wayyo Allah zasu kasheni.
kakata Annah tare da Alhaji Ubale yayan Mamata, suka fiti suna tambayar dalilin da nake kuka nan nafaɗa musu abinda ya faru, dani ba tare da ɓata lokaci Alh ubale yasakani a mota sai makarqntar, yana isa ya shige har ofis ɗin Shugaban makarantar, nan yasamu anawa malam yahaya faɗa, akan dukar da yakewa ɗalibai, shugaban makaranta nagamawa kawuna shima ya ɗaura nashi inda yayi masa barazanar matukar baifita har kana ba, zaisa a ɗaureshi. Hakuri sukayi tabadawa, har muka bar ofis ɗin class ɗinmu ya kaini, nan yayi tabani hakuri, sannan ya koma gida, zama nayi cikin gadara kafana ɗaya akan ɗaya, ina kallon kowa cikin isa da jin kai.
Har aka tashi babu wanda ya shiga harkata, Ramla da Zubaida kuwa rankwashina sukayi ransu a ɓace da abinda na aikata wanda nake ji a raina ko kaɗan banyi kuskure ba.
Koda muka isa gida ɗakinmu muka wucce inda ni nacire kayana, na fada ban ɗaki nayi wanka sannan nafito, hmmmmm
Zaku sha mamaki idan kuka ga irin wanka danayi naci uban ado, kaman me zuwa gasar kyau, badan kowa nayi wannan wankan ba sai dan zuwan saurayina, wanda muke haɗuwa dashi a bayan gidan Imam Usman, nan nake zuwa musha hiranmu.
Ina gamawa najera filo kaman kullum nafita daga gidan dukda an shiga masalaci sallar magirb, nan nabita bayan gidanmu na isa gurin bai zo ba, gidansu baby nashiga, ina gidan har akai sallar isha, sai ga wani yaro ya shigo, wannan ana kiran baby ina jin haka nayi waje shine, dake ta gurin babu mutane ina ganinshi na falla da gudu, buɗe hannunwanshi yayi na shiga ciki, shi kuma ya rungume ni, tsam a jikinshi, sunkuyo da fuskarshi yayi sitin kunnena yace.
“Babylove, muje masaukina mana,” a tsorace na ɗago kai nace masa.
” Kayi hakuri idan akaga bana nan, kusan kashe ni, za’ayi”
jan hannuna yayi muka karasa bayan gidan Imam Usman, nan ya zauna akan wani dutse nikuma na zauna akan cinyarshi, muka cigaba da hira, can hiranmu damuke wanda kusan Ashow yafini zakalkalewa, gurin faɗar manyan magana, ashe a dai-dai window imam muku wannan maganar dan har wani magana nayi dan nanunawa Ashow nima yar garice nayi, aikuwa, jin abinda na faɗa Ashow ya shiga kiss ɗina ta ko ina, shi kuma Imam jin abinda muke yasa ya, fito daga gidan yazo koranmu,, da wani katon toucinsa, yana haskamu kuwa, sai akan fuskana,……
*Matar Usman*
[23/07, 2:31 am] +234 803 800 7509: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }
🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳
*Writtern*
By
Mrs Fulani🐄
*:~2*
Mamaki da al’ajabina ya kusan kadashi kasa, sauka nayi akan cinyar Ashow, dan wani irin kunyar Imam Usman ne ya rufeni, daga can yace min.
“Zoki wucce gidan.”
Dukda muryanshi a sanyayye yake bai hanani fahimtar ɓacin ranshi ba, jikina bakwari nawucce, komawa yayi gurin Ashow ya kalleshi cikin ɓacin rai yace.
“Kaman yanda ka lalata Y’ar wani, Uwar wani, kanwar wani,Matar wani haka Allah zai turo wanda zai lalata naka, sai kayi danasani abinda ka aikatawa yaran mutane, dan nasan ba ita kaɗai kalalata ba, kuma kar nakuma ganinka a area ɗin idan ba haka zansa amaka dukar kawo wuka.”
Cikin sauri na iso gida, inda nashiga tabayan ɗakinmu.Har lokacin su Aunty basu shigo ɗakinmu ba, cire kayana nayi inda naraba gashina biyu nakwanta, ina tuna irin abinda Ashow yayi min, tabbas naji daɗi haka, ji nake kaman nafi kowa sa’a a cikin gidanmu.
Naiha Ibrahim daura shine cikaken sunana, mahaifina ɗan katsina ne, amma haifafen daura, Mahaifiyata ce ba yar kasan nan ba, ita yar nijar ce, ina da yayu hudu Ya ishaq shine babba yanzun yake service ɗinshi a zamfara, sai Aunty Zubaida tana karatunta a KSU, Aunty Hajra tana karatunta, A Poly, Ramla kuma tana Ss3 makarantarmu ɗaya ni kuma ina Ss1, Duk hudu Yaran Innaji ce, nikaɗai Mahaifiyata ta haifa sannan tarasu, Kasancewa Iyayen Mamata, suna nan katsina suka karɓeni, har zuwa yanzun da nagirma sai na koma gidanmu, Kakata Annah tana masifar sona haka yayan Mamata duk suna sona, kuma basu ganin laifina duk abinda zanyi dai-daine, duk yayuna mata suna da mutunci da nutsu uwa uba kamun kai, sanin ya kamata idan kacire ni kuwa na cire tuta a kafta rashin mutunci shigan banza kuwa ai ba sauki, ga tarin rashin kunya, a gidanmu, Ya Ishaq nake shakka dan kuwa yayuna mata ba tsoro, zabga musu rashin M nake, Ashow shine saurayina da nake ji dashi kuma shima yake jidani, mun haɗune, a birthday din kawata, tundaga ranar da yasa idanunshi akaina magana ya kare, kusan haɗuwata dashi idanuna suka buɗe, da farko baya taɓa ni, amma daga baya ya fara taɓani, tun ina kin yatabani har nafara jin daɗin abinda yake min, dukda nasan babu kyau toh yana iya, Karkuyi mamaki dan shekaruna sha shidane, amma idan kaganni zaka ɗauka nakai 20 sabida girman jiki, kuma bawani abu bane, Boons ɗina da button ɗina yake sakawa ake ganin na girma,
Lumshe idanuna nayi cikin jin dadin abunda ya faru dana tuna da wacce me tsukeken wandon ya hanamu cigaba da bidirinmu sai naji raina ya ɓaci.
***
Koda ya kori Ashow, gida ya koma daman abinci yake, ya mike fito gurinmu kallon Uwar gidanshi yayi cikin nutsuwa yace.
“Ina Jameesha take?” ya jefa mata tambaya cikin sanyi murya,
“Tana ɗakinta” ta bashi amsa.
“Kira min ita.” yace hankalinshi nakan abinci da ya saka agaba, wanda tunda yakai loma ɗaya ya ajiye cokalin, bai sake bin takan abincin ba, koda ta isa kofar kwankwasa kofar tayi, buɗe kofar tayi, cikin isa da gadara tace.
“Lafiya kike min knock,”
karamin murmushi Zahira tayi sannan tace.
“Zauji yake kiranki bani ba”
tana gama faɗin haka ta juya tabar gurin, Sai da janeesha taɓata lokaci sannan tafito cikin yauki da yanga, ta isa falon, zamata tayi tare da cewa.
“Gani nan Yaya.”
Tun shigowarta ya kalleta bai sake kallonta ba har tace gani nan Yaya bai ɗago ba saima watsa mata tambayar da yayi, cikin sanyin murya yace.
“Mi kike nufi da taliyar da kika dafa, da rana makaroni yanzun kuma taliya dake da Zahira baku da wani baiwar sarrafa abincine, sai taliya nan idan kukayi tuwo mutum sai ya gwamaci kwana da yunwa da yaci abincinku har sai yaushe zaku iya sarrafa abinci.”
Tunda suke dashi bai taɓa musu magana akan abinci ba sai yau, dole sugyara kafin damarsu ta kwace masu, gyaran murya Zahira tayi sannan tace.
“Yaya kayi hakuri Insha Allah zamuyi kokarin mun gyara kurakuranmu, nd idan kabamu dama zamu shiga makarantan koyan girki,”
“Tab wallahi bazan shiga ko ina ba, gwarama ki daina niman suna, babu inda zan shiga.” haka tagama fitsaran sannan tafita dafe goshinsa yayi cikin ɓacin rai. Zahira ma ganin halin da yake ciki tafita tabar falon tunda ba isa bace da girki, duk sai yakoma kalan maraya.
•••°°°^ΔΔΔ^°°°•••
Washi gari da safe cikin sauri na gama karyawa sannan nafito sanye da kayan makaranta, yayinda Ramla tasaka, riga da wando ni kuwa riga da siket nasaka, kafinshi wani bakin skintie ne a jikina baki sannan na ɗaura bakin siket ɗina, akai bayan nasaka riga me dogon hannun, nasaka butirin rigar, sannan na ɗauko hulata bakin nasaka, tufke gashina nayi cikin nutsuwa nafito, da Abbanmu muka, haɗu har kasa na gaisheshi, shafa kaina yayi cikin jin daɗi yace.
“Uwata Allah kin tashi lafiya, Allah yayi miki albarka, ga kuɗin break nan banda wasa.”
Nodding kaina nayi cikin jin daɗi, na ɗauki skullbag ɗina na rataya, itama ramla haka tayi muka fito daga gida muna tafiya cikin sauri, duk inda muka wucce sai anbini da kallo haka ba sabon abu bane, muna isowa majalisin Imam Usman jikina yayi sanyi sakamakon abinda ya faru ya dawo min, wani shashi na zuciya tace _Akan me kike damuwa manta dashi karki ɗaurawa kanki abinda zai dameki_ take duk wani tsoro ya kau daga zuciyata, sai ma ɗauke kaina nayi ina hura hancina,
Kamshin turarena na perfume crown shiya sanar masa na gifta, ɗago kanshi yayi yaga yanda nake taku cikin isa da yanda nake shaky jikina yasa ya sunkuyar da kanshi cikin mamaki yanda na iya sarrafa jikina, cikin sanyi murya yakalle ɗalibanshi yace.
“Ina son sanin wancan yarinyar daga wani gida take,ne.”
Aikuwa Nura yayi tsagal yace.
“Ai yar gidan Alhaji Ibrahim me katako ce, itace karamarsu kuma itace shaiɗaniyarsu,”
gyada kanshi yayi cikin gamsuwa yace.
“Shekarunta nawa”
Wani magidanci wanda yana cikin ɗaliban Imam yace.
“Akarmakalla ai yarinyace karama sosai dan sha shida ce, sa’ar yar wajenace da suna tare amma daga baya narabasu, sabida ita wannan idanunta a buɗe yake, sha’anin yau kar ta lalata min yarinya yasa nayi mata kashedi da barazana, tundaga lokacin ko a hanya suka haɗu basa ga maciji.”
“Gaskiya ka kyauta malam Ali amma me yasa iyayenta basu saka idanun akanta ba yarinya karama haka ai zata lalace fa.” Inji Imam,
Nura da yake can yace.
“Ai malam gwara ta lalacen domin in bahaka ba iyayenta bazasu san abinyi ba kuma dangin Mamarta suka lalatata,dan Me katako yana bakin kokarinshi.”
A cikin wannan hiran Imam Usman ya fahimci yanda yan unguwar suka tsanani asalima babu wanda ya faɗi alkhairina sai mugayen halayata abin ya bashi mamaki toh meye acikin tunda halina suka faɗa banashi ba.
……Karfe biyar da mintuna goma muka taso, Ramla kan tatafi tabarni sakamakon mun tsaya rigima da wasu class mater ɗina, ni ban ɗauki abin damuhimmaci ci ba, domin ina fama da ciwon mara a duk lokacin da zanyi Period ɗina toh ba sauki a daddafe na iso unguwarmu ina rike marana, yayinda nake cizon leɓena na kasar, hannuna yana dafe da kasar cikina a hankali nake tafiya, wani yarone yazo da mugun gudu yabangajeni saura kaɗan na faɗi, na tsaya sosai finciko rigarshi nayi nace.
“Baka ganin gabankane da zaka tureni.”
Buɗar bakin yaron yace.
“An turokin karuwa kawai yar iska.”
Tsabar mamaki bansan lokacin da na ɗaukeshi da mari ba, nace ” me kace.”
Jin muryan Baban Fati nayi yana cewa.
“Eh ya faɗa ɗin yar iska mara kunya.”
Shikan banyi mamaki ba dan dama ya nime naki shine yake jin ba daɗi nima cikin rashin kunya nace.
“Tabbas bani da kunya, abune nawa kuma naki nabawa kazami irinka sai me, inda kai zan baka kaina gwara namutun bansan ɗa namiji ba banza irinka me tare yan mata a lungun yana matsesu ko karya nayi.”
Take ya ɗaga hannun xai mareni babu tsoro a idanun, Imam Usman ne yace.
“Malam Idi ba girmanka bane sa’in’sa da ita ai koba bubu kome ka haifeta, abin kunyane a gareka faɗa da ita.” Juyewa kaina yayi cikin ɓacin rai yace.
” Kekam Ubangiji ya aiko miki da shirya cikin sauki wannan rawan kan naki, yayi yawa.” Juyawa nayi cikin rashin kunya zan maida masa, kallon cikin idanunshi da nayi shi yasa na sunkuyar da kaina nayi magana kasa kasa nace.
” Idan shiryar takace karka bani.”
*Matar Usman ce*
[23/07, 2:31 am] +234 803 800 7509: RILLIANT WRITERS ASSO
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }
*MATAR MALAM*
*Na:Real MaiDambu Ce*
*:~3*
Mamakine ya kamashi ganin yanda nake maida masa magana cikin rashin kunya. Wani daga cikin ɗalibanshine ya mike tsaye zai isa inda nake, ya dakatar shi da cewa.
” Kyaleta yarinya ce, bata gama sanin kanta ba.”
Murguɗa bakina nayi cikin ko ohho nace.
“Kanku ake ji.”
Tafiyata nayi nabarsu da mamakin abinda nayiwa malaminsu ko ajikina fatana na isa gida lafiya.
Koda na isa gida ciwon marana ya ta’zara, amai nayi tayi, ga mugun ciwon mara da baya, har cinyoyina ciwo suke musaman bayana kaman zanyi hauka, ga jinin da yake fita da mugun gudu, daman haka yake min bani taɓa samun saukin abun sai mun dangana da asibiti toh yau ma haka, asibitin akai kaini, dake sunsan matsalata ba,a ɓata lokaci ba aka karɓe ruwa aka karamin,tare da allura wanda zai rage min zafin ciwon da kuma wanda zai rage min karfin zuban jinin….
Kwanana ɗaya da wuni aka sallame ni, inda akayi min kashedi narabu da kayan zaki idan ina son lafiyata.
Dawowana daga asibiti na jiyo mugun labaru masu ɗaga hankali ɗaya Mutuwar Ashow da kuma labarin da ya karaɗe unguwarmu wai ciki nayi aka kaini aka cire min, abinda yajanyo mugun rikici a unguwamu inda Abbanmu ya kusan kaɗuwa dan baya gari aka kaini asibiti, ranar da yadawo daga tafiya aka tareshi akq faɗa masa, duk abinda nake aikatawa.
Yana shigowa gida ya kamani yayi min mugun duka, sannan ya rantse na daina zuwa makaranta daga ranar, sannan zai badani sadaka duk wanda yayi masa.
Kuka nake ina rokon yan uwana, akan su shawo min kan Abba amma fur yaki, karshe wayar Innaji naɗauka na faɗawa Annah ita tazo da Kawu Ubale suka bawa, Abba hakuri ganin gimarmansu yasa ya kyale ni amma da sharaɗi bai amince min na riƙe waya ba, sannan babu ni babu yawo, gidansu Annah kuwa sau ɗayane asati nidai na amince, dan har lokacin mutuwar Ashow yana dake ni,sosai.
^^•••°°ΔΔΔ°°•••^^
Sati biyun da nayi cikin gida ba karamin kewar waje nayi ba da farin ciki nashirya zuwa makaranta koda gama ramla har ta tafi abinta, haushine ya kamani cikin sauri na shirya riga da wandone a jikina, sai karamin hijab, tunda nafito na lura ana nunani da yatsa, duk inda na wucce sai nunani suke abin yayi min zafi amma nayi fuska ban damu ba, Ta kofar gidansu Baby nabi ina son amsar wani text book ɗina da tazo ta amsa, bata dawo min da shi ba,.
Ina tura kaina cikin gidan naji muryan Baby tana cewa.
” Allah Mamanmu, bata da kome sharri nayi mata, kuma nice na haɗata da Babanta asalima nice da kaina nayi masa maganar abinda take aikatawa Mamanmu Naiha tana da farin jini kuma wallahi abinda boka ya faɗa min gaskiya ce, duk wanda zai nimeta babu karamin mutum, nice na rabata da Ashow nacw mata ya mutu, shima nayi sanadin da ya bar kasan baki ɗaya dan kurciya nayi masa Mamanmu na tsani Naiha, nice nayi mata sharrin zubda ciki aka mata kuma wallahi Mamanmu ina kishin samun farin cikin Naiha idan ina raye sai na hanata sukuni.”
Jikina narawa nashiga gidan ina shiga nakifeta da mugun mari nace.
“Kasheni Baby nace ki kashe ni, tunda na hanaki rawan gaban hatsin me natare mikine, me kika nima a guna da banbaki ba, Baby Allah ya isa tsakanina dake, Kije Duniya tafi gabaruwa jimawa.”
Ina faɗin haka nafito ina kuka hannuna ɗaya akaina, haka nazo na wucce majalisin Imam Usman, da yan majalisin suna ganin halin da nake ciki, basu wani damu ba, saima tsabgarsu da suke, shine kaɗai ya gaza hakuri har yace.
“Amma kun ban…”
Bai karasa ba, wata bakar mota tayi sama dani sakamakon tsallaka titin danayi hankalina baya jikina, karan birkin da me motar ya taka shi yadawo da hankalinsi kafin wani a cikinsu ya miqe har shi yarigasu zuwa gurina, shi ya ɗagoni, dan ni banma san me yafaru dani ba, motar mutumin yasakani, sannan ya shiga gaban motar suka kaini wani kuɗi cikin gaggawa aka karɓe ni, nan aka shiga bani taimakon gaggawa, bayan wani lokaci likitan ya fito ya kallesu, sannan yace.
“Kune kuka kawo yarinya nan ko.”
Lokaci guda sukace “Eh mune”
“Toh babu wani damuwa buguwace kawai a cinyarta amma shima ba matsala zai warke.” likitan ya faɗa musu.
Godiya sukayi likitan nabarin gurin sai ga Innaji da Ya ishaq suka iso, godiya sukawa Imam Usman, sannan suka shiga ganina, shima Mutumin da ya bigeni, hakuri ya basu.
Bayan yaga halin da nake ciki yayiwasu Innaji sallama ya dawo gida,
Mutumin da Ya bugeni kuwa, ya zauna har na farka yana ganin farka gurina yazo sannan yace.
“Preety sannun ko ya jikinki Allah yabaki lafiya.”
Sun innaji sannu sukayita min sallama yayi musu akan sai dare zai dawo, kafin ya tafine ya kalle ni yace.
,”Toh bazaki faɗa min sunanki ba nidai sunana Asad,”
dake mutum ne me bakwarce tuni ya samu shiga cikin zuciyan yan gidamu, ni kuwa ko kaɗai bai burgeni ba dan akalla shekarunsa zaikai talatin da bakwai, kusan Imam Usman zai bashi irin shekaru hudu, dan shima bazai wucce, 45 ba, kin kallonshi nayi na kauda kaina, sabida irin kallon da yake min haushi yake bani,
Ina jin lokacin da Ya Ishaq yace masa.
“Sunanta Aisha amma muna kiranta da Naiha,”
murmushi yayi cikin nutsuwa yace.
“Nice name, sunan Mammyna sunan Yar autanmu suna me daɗi da daraja.”
kara jin haushinshi nayi na rufe idanuna, inajin yayi musu sallama ban buɗe idanun ba, balle yasan inajin shi.
Asad Aminu Shema, ɗane ga mataimakin gwanar katsina, yana da kanne, maza da mata, kafin mahaifinshi ya zama maitaimakin gwana tsohun jami’in difulomasiyane, sannan ya zama jakadar naija a Zurich da Canada.
Sannan ya ajiye aikin ya dawo mahaifiyarshi kuwa,lauyace mai zamankanta, kuma malamace a jami’an ɗan fodio,, Amma sun rabu da mahaifinsa. Kusan rayuwarsa a kasan turai yayisu amma mutune mai mutunci dakamun kai, Gashi tuzurune🙊
……Da dare kuwa sai gashi sunzo shida mahaifinshi da kannenshi sun zomin da kayan dubaya, na ban mamaki sosai suke jana a jikina tare da bani wani irin girma na musaman, shi kuwa gogan sai wani lagwaɓar da kai yake, yana kallona, cikin wani irin yanayi sunkuyar da kaina nayi kaman zanyi kuka, dan ban taɓa ganin ana haka ba, sai ma kunya da ya kamani, shigowan Abbanmu da kawu Ubale, yasa na ɗago kaina sannun suka min, sannan suka shiga gaisawa hiran suka koma irin nasu na yan boko da kuma cigaban taɓangaren sha’anin mulkin, sun jima sannan Mataimakin gwana ya mike alamun zasu tafi, fita sukayi aka barni dashi, zuba hannunshi yayi cikin aljuhun rigarshi yana kare min kallo, can yakira sunana kaman me ciwon baki yace.
“Nai,,,,,ha, kin sace min zuciyata..”
Yana faɗin ya tsuguna a gabana yace.
“Kallo ɗaya danayi ya haifar min da soyayyarki don Allah karki k’i amsar soyayyata zan iya shiga gararin rayuwa, Pls kisoni ko ɗan kaɗan ne, inyaso zanyi maneji da wanda nake miki,.”
Miqewa yayi sannan ya sumbaci goshina yace min.
” Akwana lafiya kiyi mafarkina.”
….
Fita yayi cikin kasaita murmushi nayi a raina nace.
“_Nasamu miji irin wanda nake mafarkin samu.”
Lokacin da iyayenmu suka fita Mahaifin Asad Alh Aminu Shema baiyi kasa a gwiwa ba gurin nimawa ɗansa nima ba cikin mutuntaka Abbana da Kawuna suka bada aurena amma an bari sai na gama karatuna…..
*Matar Usman*
[23/07, 2:31 am] +234 803 800 7509: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }
*MATAR MALAM*
*Writtern*
By
Mrs Fulani🐄
_Ina kike Ummul khairi ga shafin nan dake kawai da kuma jin daɗinki_
*:~4*
Kafin asallame ni kuwa kowa yasan irin Son da Asad yake min, basan yanda zan kwatanta ba, dan Mahaifiyarshi sau uku tana zuwa dubani tare da alkhairori na ban mamaki, take wani jin kai da wani ɗagawa ya karu min, makarantar da nake, Asad ya cireni ya maidani makaranta mafi tsada, a garin katsina, waya kuwa Iphone+8 ne a hannuna, Ga Mamy ɗinshi musaman take haɗamin mayukan shafawa,da kaywn cosmetic, dalilina suka fara abota da Imam Usman, wanda ya tayashi murna da jin an bashi aurena,.
Yau juma’a tare muke dashi a gidan Annah sai shagwaɓa naketa lafta masa yayinda shi kuma ya ɗaukw duk abinda nake masa dan bai damu ba sai ma karin farin cikin da yake ciki idan yana tare dani yakan manta da kome da kowa shi burinshi ya mallakeni shi ɗayanshi, ganin haka yasani nima naki bawa kowa damar da zai takura min sai shi, kuma nake cin karena ba bu babbaka a cikin zuciyarshi dan nasan nice kadai babu wata domin ya gina cikinta da kaunata, cikin sakalci nace.
“Mine ina son ice cream, da cake me chocolat, sai shawarma” na tanɗe bakina cike da jin kwaɗayin abinda na lissafo masa.
Girgiza kai yayi cikin rashin amincewa da abinda nake so sannan yace.
“Second love, kiyi hakuri ba zaki samu kayan zaki da sanyi ba, asalima sai da Abba yayi min gargaɗi da bai yarda nasaya miki koda chewgun ba dan hak….”
Bai kai karshe ba na miqe cikin jin haushi da hasala na ɗauki wayata na fita ko sallamar Annah banyi ba, sabida jin haushin abinda Asad yace min.
A hanzarce ya biyoni yana bani hakuri amma fir naki kulashi ran yan mata ya ɓaci, bai fasa bina nima kuma naki sauraranshi, a haka har muka iso, layinmu, ganin zamu ratsa mutane yasa na juya nace.
“Ya isa kawai kaje gida sai ankwana biyo dan zamu fara exam kaga dole na maida hankalina akan karatu,”
Gyaɗa kai yayi cikin rashin kuzari yace.
“Toh amma muje na rakaki har gida kinji ko baby doll” ya karshe maganar cikin zolaya dan yasan na tsani kace min baby doll, kusan haka yan makaraɓtarmu suke ce min, baby doll, wai ina musu yanayi da biebis,
Tura baki nayi kaman na fasa ihu ina tafiya ina kunkuni shima bai fasa biyoni ba, haks muka ratsa mutane suna ganimu sai nunamu suke da yatsa, sabida yanda muka dace, Imam Usman kanshi a sunkuye yana gyara Yaronshi Khalif takalminsa, yaji Nura da Sayyed suna cewa ai hakane sai kaga yarinya tagama watsewa karshe ka ganta ta buge da auren mutumin kirki, kaga yanda ya mutu akanta wallahi da zatace yabata zuciyarsa da zai ciro yabata, sabida son da yake mata,,”
“Manzon Allah s,a,w yace idan baza kufaɗi alkhairi ba kuyi shiru.” Abinda Imam Usman yace musu kenan take suka kame bakinsu.
*Usman Shehu Usman shine cikaken sunan Imam Usman, Yafito daga jahar Yobe, ɗan babban gidane domin gidansu malamaine, ciki da wajensu, shine ɗa na Takwas a cikin gidansu baya ga kane da suke binshi maxa da mata,Zan iyacewa gidansu ilimin addini da zamani ya same mazauni. Acikin gidan, mahaifinsu ya jima da rasuwa, amma kafin nan yana da mata huɗu yara goma sha takwas, maza da mata, Babba yayansu Muh’d suna kiranshi da Yaya Abba lawan, yana aiki a babban asibitin abuja, sai Mai Abubakar, yana aiki a N.N.P.C, suna kiranshi Yaya Sadeeq, sai Aunty Aisha, tans aure a maiduguri,Sai Aliyu malamine a state poly damaturu, sai Xubair, yana kasuwanci a fataskum, Sai Hafsa, tana aure a Benin,sai Khadija ta rasu, sai Masur,sai Imam Usman sai Umma hani, Fatima Hauwa’u, sai Yan biyu Hassan da Usaina, sai karamarsu Balkisu,
Mata biyune a gidan ɗakinsu Imam su tarane, ɗakinsu Abba lawan kuma su biyarne, gidan akwai kyakyawan fahimta a tsakanin matan, sai suka ɗaura yaransu akan tausayi da jin kan juna, haɗi da girmama juna, babu raini a tsakanin junansu.
Imam Usman aiki ya kawoshi garin katsina, Inda shima alkaline, sabida ɗan kimanin Shakaru 46 zuwa da bakwai, ya karanci harkan shari’a a france, inda yayi degree ɗinshi a can, sannan ya koma jami’a madina yayi degree nabiyu an fanni shara’ar muslunci, bayan ya hada sai ya dawo gidan anan Abba lawan ya nima masa auren Zahira, tunda mahaifinsu ya rasu shi ya ɗauki duk wata ɗawainiyar Yan uwanshi, bayan shekara guda Yar kanwar Umminshi Janeesha tatada rigima ita idan bashi ba zata shiga duniya,
Faɗawa Abba lawan akayi take, ya nime masa aurenta akayi bikin. Yanzun haka yaranshi biyu, Zahira har yanxun Allah bai bata ba, sai Janeesha ita kuma bata kula da yaran sai Zahira ubansu.
_Wannan kenan_
Har gida ya rakone sannan ya zuba min ido kafin yace.
“Naiha Am so sorry kinji ba zan sake ba,”
Murmushi nayi sannan na rausayar da kaina nace.
” Ya wucce.”
Pls Share…..
*Matar Usman*