Matar maza uku Hausa Novel

Matar maza uku Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MATAR MAZA UKU

 

JINJINA

Duk kan marubuta waɗan da ke bani shawara akan harkokin rubutu, da masu gyaramin kurakuraina a duk lokacin da nayi wani rubutun da ba daidai ba. Kamar su:

 

 1. Hauwa’u Haupha.
 2. Safna S Jawabi.
 3. Real Nana Aisha
 4. Muntaseer Shehu
 5. Abba Writer
 6. Sauraniya
 7. Pretty Hayrour
 8. Maryam Marsad
 9. Maryam Nasir
 10. Bamai Dabuwa
 11. Ɗan Mallam Koko
 12. Ɗalhat Gwandou

 

 

Da dai sauran waɗan da ban kawo sunayensu ba saboda suna da yawa.

 

 

GODIYA

Godiya ga Allah subhanahu wata’ala maɗaukaki sarki, wanda ya bani basira da ikon kawo muku wannan littafin mai taken Rikici Kan Rikici haƙiƙa babu abin godiya kamarsa nagode Allah

 

GARGAƊI

 

Wannan littafin a bisa ƙa’idojin rubuta littafi a ka yi shi, a saboda haka laifi ne canja masa tsari ko salo domin yin wani abu daban da shi ba tare da sanar da mai littafin ba.

 

SADAUKARWA

 

Sadaukarwa ne gare ki ƴar uwata ƙanwata Pretty Hayrour.

 

 

SHIMFIƊA

 

A kowa ce al’ada, da kuma addini ko a cikin tarihin duniyar masoya ba inda mace ɗaya ta auri maza har uku.

 

Sai dai a cikin addinin musulunci Allah ya amincewa namiji ɗaya ya aure mace daga ɗaya har zuwa huɗu, wasu ma su kan ƙara da ta biyar wacce ake kira da ƴar baraya.

 

 

 

Wannan littafin zai fayyace yadda wata zankaɗeɗiyar yarinya kyakkyawar gaske ta auri maza har uku. Nasan wasu zasu yi tunanin ta auri ukun ne ɗaya bayan ɗaya. To ba haka ba ne kamar yadda kuka zata, wannan kyakkyawar yarinyar ta auri maza har uku ne, kuma ko wane da igiyar aurensa uku akanta.

 

 

Wani rikici a cikin wannan littafin shine; waɗan nan mazajen uku da wannan zankaɗeɗiyar yarinyar ta aura dukan su mahaifiyarsu ɗaya, sai dai ko wane daga ciki da nashi mahaifi.

 

 

Kenan tun asalin farko akwai rikici danƙare a cikin wannan littafin har zuwa ƙarshensa. Kawai dai ku cigaba da bibiyata don sanin yadda zata faru.

 

 

*** *PAGE 1 & 2*

 

_A Garin Abuja._

 

A lokacin da duk wani mahaluki mai rai da lafiya yake neman makwancinsa don bawa kansa salama gami da hutu, a daidai wannan lokacin Alh. Tukur Abubakar Tela yake ƙoƙarin shiga a garin Abuja kamar yadda ya saba duk ranar monday yana zuwa ne don tattaunawa da abokan kasuwancinsa.

 

Yana tsaka da tafiya a cikin motarsa ya saki sautin wata tsohuwar waƙar shata mai taken _Teacher Uban Karatu_ kwatsam fitilar motarsa ta hasko masa wasu mata da ke ƙoƙarin tsallake titi da sauri ganin yadda motaci ke ta yawan wucewa akan titin. Kallo ɗaya yayi musu ya gane akwai abin da waɗan nan matan ke ƙoƙarin aikatawa ganin yadda suke wani waige-waige, kuma ga su mata.

 

 

Nan take ya ja birkin motarsa ya koma gefe ɗaya yayi parking a cikin duhu inda ba wani haske kuma ba wanda zai hasko shi. Yana yin parking kuma sai ya fito ya ci gaba da bibiyan su da kallo.

 

A sanadin abayar sallah

Matan su biyu ne, ko shakka babu abokan juna ne sosai. Ɗaya ta tsaya a bakin titin tana dubawa a ɓangarenta na hagu da dama ta yadda zata lura idan akwai wani wanda zai ga abin da suke aikatawa, a yayin da ɗayar kuma ta tsallake titin zuwa wata gota dake gefen titin.

 

 

 

Kwandon jariri ne dama jaririn a ciki riƙe a hannunta. Bayan ta kai wurin gotar sannu alaikum ta ajiye kwandon a cikin gotar tana share hawayen dake nuna jinƙai ga jaririn da ta ajiye a cikin gotan. Kafin ta dawo inda wannan ƙawarta ta take ta waiwayi wannan jaririn yafi a lissafa.

 

 

A duk lokacin da ta waiwaye shi kuma sai ta ji kamar ta koma ta ɗauko shi, amma kuma idan ta tuna irin ƙalubalen da zata fuskanta idan har ta sake tayi wannan kuskuren sai ta ji ta karaya da fasa abin da ta zo yi.

 

 

Da haka har suka bar wurin suka koma gida. Alh. Tukur Abubakar Tela yana sauri yaje ya ga jariri ne suka ajiye a ciki. Ganin hakan yasa zuciyar harbawa tamkar dai wanda aka faɗawa ranar mutuwa, amma duk da wannan tsoron da yake ji hakan bai hana shi ɗauko wannan jaririn ba.

 

Yana shiga motarsa ya sauke sit ɗin motar ya shimfiɗe jaririn sannan ya bi bayan su ba tare da saninsu ba har suka isa gida. Gidan Safiyya suka fara zuwa sannan daga baya Rukayya ta wuce gida.

 

 

Bayan ya ga gidajensu su duka sannan ya juya komawa gidansa. Murna da farin cikin samun wannan jaririn su suka hana shi zuwa inda zai je. Ga fargabar haɗuwa da ma’aikata kuma ga tsoron yadda zai gamsar da matarsa asalin wannan jaririn.

 

 

 

Cikin nasara ya isa gida ba tare da ya haɗu da kowa akan hanya ba. Yana isa ƙofar gidansa yayi hon mai gadi ya fito yana murza idanuwansa dake runtsewa don har bacci yayi nisa da shi. Leƙawa yayi don sanin wanda yake masa hon, amma bai gane ko waye ba saboda ƙarancin haske dake ƙoafar gidan kuma Alh.

 

 

 

Ya kashe fitilar motarsa don rufawa kansa asiri. Da dai Alh. Ya fahimci mai gadin zai ɓata masa lokaci sai yayi saurin fitowa daga motarsa ya zo da kanshi ya buɗe gambun motar ya wuce da motar. Ganin wucewar Alh.

 

 

Da sauri ko magana bai tsaya ya masa ba yasa shi faɗawa zargin wani abu na faruwa, sai dai ba damar tambaya.

 

 

 

Parking ɗin motarsa yayi inda ba nan yake parking ba. Faruwar hakan ta ƙara saka mai gadin zargi. A gaban idonsa Alh. Ya fito da kwandon jaririn yana shiga cikin ƙofar matarsa. Yawan motsawa da kwandon ke yi yasa jaririn farkawa daga baccin da yake tare da yin kuka. Kukan da yake kuma shi haddasa farkawar Hajiya Habiba daga baccin da ya kwasheta tun lokacin da kammala sallar isha.

 

 

 

Ji take kuwan jaririn na ƙara ratsa dodon kunnuwanta. Ba tare da ta tsaya wata-wata ba ta fito da gudu tamkar wacce aka koro. Tana buɗe ƙofar ɗakin nata ta ci karo da Alh.

 

 

 

Riƙe da kwandon jariri. Nan take kuma nakkasasshen tunani ya shiga ƙwaƙwalwarta wanda yasa ta tare bakin ƙofar tana neman masaniya akan jaririn. “Wallahi ba inda zan je dole sai ka faɗamin inda ka samo wannan jaririn”? Ta faɗa cikin muryar kuka da nuna rashin yardar Allah.

 

 

Matar Maza Uku

Ya ƙirƙiro wani murmushin ƙarya don ɓatar da abin da ƙwaƙwalwarta ke son haddasa mata. Duk da murmushin da yake yi hakan bai hana shi fargaba don dama yasan dole hakan zata kasance.

 

 

 

Bayan murmushin da yake yi sai kuma ya ce, “Dole zaki san da wannan albarkar da Allah ya nufe mu da ita, don haka kada ki damu zan faɗa miki komai akansa kawai dai ki bani hanya na wuce”. “Wallahi ba zan taɓa yarda da wata ƙarya ba. Tayaya zaka ce min zakaje taron tattaunawa a Abuja, sai kawai yanzu in ganka da wani jariri”. Tana gama faɗin haka kuma sai ta ƙara sabon kuka tana ƙara tare hanyar ƙofar.

 

 

Ana zato hausa novel

Ransa a ɓace ya kalleta a fusace ya ce,”Shin zaki bani hanya na wuce ko kuwa sai na bankaɗe ki?”. Ganin dai ba wargi a fuskarsa tasan zai iya aikata abin da ya faɗa yasa ta jayewa tana magana cikin wata shagwaɓaɓɓiyar muryarta.

 

Yana isa daga ciki sai ya wuce ɓangarensa inda komai nasa yake ya ajiye jaririn sannan ya zauna a gefen gado ya ɗaga hannayensa sama ya yi hamdala ga Allah. Har zuwa yanzu bai daina jin farin ciki na ƙara shiga saƙon zuciyarsa ba.

 

 

Bayan ya gama addu’a sai ya miƙe yana shawagi a tsakar ɗakin yana nazarin abinda zai faru zuwa gaba. Tunanin yadda mutane zasu tuhumeshi da wannan jaririn yake yi. Idan yayi wannan tunanin sai kuma wannan ya zo.

 

 

Matar Maza Uku

Yana tsaka da ƙirƙiro irin ƙaryayyakin da zai yi wa mutane ne don su fahimce shi ne sai yaji matarsa na buga masa ƙofa tamkar wacce aka aiko gare shi. Ganin dai tana ƙoƙarin ƙarya masa ƙofa ne yasa shi buɗewa da sauri. Yana buɗewa kuma suka yi ido huɗu yana ƙare mata kallo tare da saurarenta gata tsaye cirko-cirko. Wani walaƙataccen kallo ta bishi da shi kafin yace me tayi wufff ta shige ƙuryar ɗakin. Yana gama rufe ƙofar ɗakin ya waiwayo gareta sai ya ga har ta kai wurin da jaririn yake ta ɗauke shi sama. Hannayensa biyu ya ɗora a kai kamar zai yi ihu yace, “Dan Allah ki dakata mana, wai meyasa kike son saɓamin ne, meyasa ba zaki tsaya ki fahimce ni ba. Wannan jaririn ba kamar yadda kike…”. Bai ƙarasa maganar ba ta dakatar da shi da matsiyacin kukanta tana yi tana ƙara fashewa da kuka tace, “wallahi ba abin da zaka faɗamin, kawai dai kana da budurwa a waje ne shine da kuka samu saɓani ta baka kayanka ka zo min da shi a nan. Kuma ka yi hakan ne don ka tabbatarmin nice da matsalar. To wallahi tallahi ba zan yarda da irin wannan ƙazamta a cikin gidana ba”.

 

Idan ya bi nan sai ta yi nan har ta ƙara harzuƙa shi ya koma gefe a fusace yace, “To kiyi abin da zakiyi tunda haka kika ce, hakan ne, sai me idan nayi? Na rantse miki da Allah ko ƙwaljane ta samu wannan jaririn bakin aurenki kenan, idan kuma kina da tantama akan hakan to dan Allah kiyi abin da zakiyi kada ki fasa”. Jin wannan ƙazamar magana wacce ta tsana sama da komai a rayuwarta ya sa tayi sanyi sai sauke jaririn sannu alaikum tayi akan gado ta samu wuri ta zauna hawayenta na sauka tamkar ana yayyafin ruwan sama. Alh Tukur na matuƙar jin tausayin matarsa kamar yadda yake matuƙar sonta da ƙaunarta. Kusa da ita ya zauna yana bata haƙuri da ta sauraresa. “Kin fi kowa sanin ba zan taɓa iya cutar dake ba Habiba me ya sa kike zaton zan iya yi miki wani abu da bai dace ba. Kada fa ki manta alƙawari nayi miki ba zan taɓa yin abin da zai ƙona miki rai ba.

 

 

 

 

Matar Maza Uku

Da kin tsaya kin nutsu zaki fahimci komai akan wannan jaririn. Wallahi tallahi ba ɗana ba ne hasali ma ni bana da wata budurwa a waje kamar yadda kike zato”. Yana cikin magana ta ɗago kai ta kalle shi cikin muryarta mai kama da kuka ta ce, “To ka faɗa min inda ka samo wannan tsinannen”? Faɗin tsinuwa akan ɗan alhakin da bai san komai ba a duniya face ruwan nono yasa shi girgiza kai yana jinjina irin tsananin zafin kishinta akansa, wanda ba komai hakan ke nuni ba face tsantsar tsananin so da ƙaunarsa da take yi. “Habiba zan so ki bar wannan maganar har gobe da safe idan Allah ya nufe mu da kai zan faɗa miki komai akansa, dan Allah kije kiyi bacci.” Wani sabon kuka ta sake ɓarkewa da shi wanda duk inda kake a cikin gidan nan zaka ji.

 

 

 

 

 

 

Can suka jiyo kukan ƴarta Safina wacce bata wuce shekara guda da wata huɗu ba tana ƙyalla ihu don ta farka daga bacci ba ta ga Mamanta ba. Hajiya Habiba ta miƙe tsaye tare da binsa da walaƙantaccen kallo hawaye na zuba ta fice tabar masa ɗakinsa. Ajiyar zuciya yayi ya sake ɗaga hannayensa sama ya ƙara godiya a wurin Allah ganin ya kusa shawo kanta. A yadda ya santa da fitina bai yi tsammanin ma zata yi sauƙin kai akan wannan al’amari haka ba. Bayan ta shige ɗakinta ta ɗauki ƴarta ta tana rarrashinta har ta samu tayi bacci. Yawan tunanin da take yi yasa har safiya ta waye bata samu ta runtsa ido ba don Alla-Allah take yi garin ya gama wayewa ta ji dalilin shigo da wannan abin da take kira ƙazamta. Shi ma Alh. Tukur ya kosa safiyar ta waye don ya je gidansu Ruƙayya wato ƙawar Safiyya yaji dalilinsu na jefar da wannan alhakin. Duk da yake bai san wace ce mahaifiyar jaririn ba, amma ya yi ƙwaƙƙwaran zaton Safiyya ce mahaifiyarsa ganin yadda take yawan zubar da hawayenta a lokacin da suka jefar da shi.

 

 

 

 

Matar Maza Uku

Tunda sassafe Alh. Tukur ya tashi ya cire kayan jikinsa ya saka wata jallabiya sannan ya ɗauki jaririn ya fita waje. Tun a cikin ɗakinsa yayi sallar subahi saboda haka ba inda ya tsaya sai garin Abuja a gidansu Ruƙayya. Kafin ya isa gidansu ƙarfe takwas da rabi da ƴan mintina. Yana yin parking ya samu dacewa da wani almajiri zai shiga a gidan, ai ko bai tsaya jira ba ya kira almajirin. “Dan Allah idan ka shiga ciki kace ana sallamawa….” Bai ƙarasa maganar ba ya ja linzamin bakinsa yayi shiru yana tunanin me zai ce da almajirin bayan bai san kowa a gidan ba. Almajirin da shegen kauɗi ya ce, “Ko mai gidan za’a kira?” Alh. Tukur ya ce A’a, amma dai kai ɗan unguwar nan ne ba”? Almajirin nan ya ɗaga kansa da nufin “Eh”. Cikin farin ciki Alh. Tukur ya ce, “To ya sunan ƴar budurwar nan? Na manta sunanta ko ka sani?” Ganin ita kaɗai ce budurwa a gidan yasa Almajirin ya ce da shi, “Ko Rukayya.” Da sauri kamar yasan ita ɗin ce ya ce, “Eh ita fa dan Allah kace ana kiranta.” Nan take almajirin ya shiga ciki kafin ya fara bara ya faɗi saƙon da aka bashi sannan ya fito. Yana fitowa kuma Alh Tukur ya ciro kuɗi ƴar ɗari biyar sabuwa ya miƙa masa yana masa godiya. Haka shi ma ya din ga godiya har ya bar wajensa.

 

Ba tare da ɓata lokaci ba Ruƙayya ta fito daga cikin gida ta zo ta sami Alh a bakin ƙofa daidai yana ƙoƙarin komawa cikin motarsa. A iya saninta dai ba wani mai mota wanda ya taɓa takowa ƙofar gidansu nemanta, don haka shi yasa ta tsaya tantama ko ba shi ba ne yazo wajenta tana tambayar kanta.

 

 

 

Matar Maza Uku

Ganinta yayi ta fito har tana ƙoƙarin juyawa ta koma sai ya kirata. Cikin tsoro-tsoro ta ƙaraso inda yake tana cewa, “Lafiya dai mallam wa kake nema?” Alh. Tukur yayi murmushi sannan ya ƙara gyara tsayinsa ya ce, “Sunana Alh Tukur Abubakar Tela ni mutumin Sokoto ne, sai dai na fi yawan zama a wannan garin naku kasantuwar kasuwanci da nake yi. A daren jiya wuraren ƙarfe ɗaya na fito daga Sokoto tahowa nan na hango ku ke da ƙawarki”.

 

 

 

Yana kawowa a nan da maganarsa sai ta ji wani irin yanayi wanda ita kanta bata san wane iri ba ne kawai dai ji take kamar tayi layar zana ta ɓace ɓat. Ganin hankalinta a tashe ya sa shi yin shiru yana murmushi, sannan daga baya ya cigaba da magana. “Ki kwantar da hankalinki ba abin da zai faru da yardar Allah kawai dai ina neman taimakonki ne”.

 

Matar Maza Uku

Bayan ta yi ajiyar zuciya sai ta ce, “Mallam da me kake son na taimaka maka? Bayan asirin da muka daɗe muna binnewa ya tonu, ai kai ne zaka taimaka mana mu bama da abin da zamu taimakeka da shi”. Murmushi yayi ya ce, “Kada ki ce haka, don baki san wane irin taimako zaki yi min ba”. “Toh! Shi kenan tunda ka ce haka ba damuwa Allah yasa zan iya taimaka maka”.

 

 

 

Tun kafin ya faɗa mata buƙatarsa ya ji wani irin farin ciki sannan daga baya ya ce, “Ina son sanin asalin wannan jaririn don Allah ki taimaka ki faɗamin”. A daidai lokacin ne wayarsa dake cikin mota ta yi ƙara, haddasuwar hakan kuma yasa jaririn farkawa daga bacci. Da sauri ya buɗe gambun.

 

6 Comments

5 Trackbacks / Pingbacks

 1. Guntun Goro Hausa Novel | My Novels
 2. Yayanah ko ruhi na Hausa Novel | My Novels
 3. Gwauro Hausa Novel Page 1 to 10 | My Novels
 4. Yarima Ashman Complete Hausa Novel | My Novels
 5. Matana Hausa Novel Complete | My Novels

Leave a Reply

Your email address will not be published.