Matar wani Hausa Novel part 1

Matar wani Hausa Novel part 1

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[09/10, 9:21 am] +234 813 638 8995: 🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢

 

*MATAR WANI!*

 

_STORY AND WRITTEN_

 

*BY*

 

*MOM SULAYM*

 

*Arewa Writter’s Association*💦

 

_All praise be to the Almighty Allah_

 

_Alhamdulillah for another opportunity that Allah has gave me again to write this novel_

 

*MATAR WANI!*

 

*Labari ne da ya tattara manyan darussa na rayuwa da kuma yanda kowanne bawa ba ya wuce ƙaddararsa, hmm wannan labari yazo da tsantsar tausayi , soyayya,jarumta,sadaukarwa da kuma rikitarwa duk a cikin wannan labari*

 

*MATAR WANI Ƙirƙirarran labari ne wanda be shafi rayuwar kowa ba, idan kikaga ko kaga yay daidai da rayuwarki ko taka to labarinne yazo a haka*

 

*This Book is dedicated to My Mom I can’t never ever forget you’re kindness to me I have really appreciate it 👏*

 

*As always special gift to you Aunty Hauwa*

 

*Doctor Maryam Ina godiya sosai👏*

 

*Ummu intee gaisu wa from my side*

 

*Ummu Affan gaisuwa ta musamman agareki*

 

*Dama wanda ban ambata ba ina yinku Arewa writter’s*

 

*My Groups members especially Ummu Nawwara and others I have so much love you💞*

 

*And my Facebook book fan’s we are together forever*

 

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

🅿️🌀1️⃣➡️2️⃣

 

 

“”””””‘”””””””””””””””Ga duk wanda yasan garin Jos ya kwana da sanin cewa gari ne da Allah ya albarkace shi da wata irin ni’ima ta sanyi kusan ko da yaushe ,to yau ma hakanne domin kuwa ana cikin weathern sanyin ne .

 

*M.M.F STREET*

 

Shine sunan dake jikin wani tafkeken gate da nake hangowa ,gate ne Wanda yay kama da irin gate ɗin da ake amfani dashi a manyan kasuwanni sedai ɗan banbamcin da wannan ke da shi,ban kai ga ɗauke idona daga garesa ba naga ana zugesa tamkar wani zip zuwa gefe guda ,titi ne malale wanda daga gani yasha kwalta tamkar wanda ba a bi ta kansa ,wani ƙaton inyamurin soja ne ya buɗe gate ɗin wanda ba tare da yakammala ba motar ta kawo kai kai tsaye domin shirin fitowa.

 

” Ikon God!”

Nafaɗa kawai, ganin irin gudun da yake tamkar ya hau babban titi,tun kan sojan yakai ga garƙame gate ɗin naga mutum yana falfala gudu kamar an korota daidai ze datse gate ɗin ta samu damar ficewa sut ta ƙaramar ƙofar data rage kai tsaye ta nufi motar data fita.

 

Dama yasan za a rina tunda beyi saurin rufe gate ɗin ba yasan ba abinda ze hana bata fito ba ,buɗe murfin motar yay yafito, nabishi da kallon mamaki.

 

Tunda nake karantun Novel ban fiye jin baƙin mutum ba amma yau kam nagani da idona .

 

Kai tsaye gun megadin yanufa kana ganinsa kasan a zafafe yake .”Micheal, how many time should I told about this girl issue,why are you allowing her to work out? assume it’s not me now what’s going to be happen ?”

 

Duk maganganun da yake

yana ƙame yana sauraransa kawai har se da yaji yay shiru a sannan yace.”Sorry Sir, pls sorry, you know the girl sir ,she didn’t give me chance to lock the gate ,the time that I wa…..”

 

“It’s okay! But you’d be careful ok?”

 

Micheal yace.”ok sir ”

 

Juyawa yay yana me riƙe da hannunta wanda a sannan ne nakai dubana gareta da sauri na sake kallonta.”Subhanah! ”

Kawai na iya furtawa ganin wadda ke bayansa .

 

Bazaka kirata da babba kamar yanda bazaka kirata da yarinya ba bakuma zaka kirata da budurwa ba haka zalika ba zaka ce matar aure ba ce,zuba mata idanuwa nai ina kallon ta ganin wani irin dress dake jikinta daga kasa na fara kallonta ganin wani cambus dake sanye a ƙafarta sake kallo nai dariya na taso mun sabida yanda yay mata oversized ɗinnan jinai dariya na neman kufcemin ,gown ke jikinta milk color sedai fa tasha jirwaye kan na kalla na sake kallo “Ya… ilahi !” Abinda nafurta kenan biyu aka raba gashin amma bana fidda tsammanin kannan be shekara ba wanki ba.

 

Zaro masa idanuwa take tana muzurai ,yayinda ya ɗora hannunsa bisa Lips ɗinsa yana mata alamar tai shiru ,hanya ya nuna mata alamar su wuce ciki,turje-turje tafara yi alamun ba zata wuce ba ,kallon wristwatch ɗin hannunsa yay ganin time na ƙure masa .

 

Da sauri ta juya tana kallon direction ɗin da suke jiyo taku na tunkarosu,juyawa tai da gudu tai bayansa ganin wanda ke tunkaro sun ,har ya ƙaraso yana me doka mata harara,ita kuwa se mutsu-mutsu take a bayansa.

 

“Broth why are you still here? I think you said you have an appointment right?”

 

murmushi kawai yay masa ba tare da yace masa komi ba.

 

Juyawa yay ɓangaren da take da nufin fincikota tai saurin sake juyawa .”Why broth ,why? Saboda wannan mahaukaciyar zaka zauna kana ɓata lokacinka? Wai se yaushe ne zaka bar sabgar yarinyar nan ne ko kaima ka huta haba! ”

 

“Mubeen..Mubeen” kallonsa kawai yay batare da yace masa komi ba.”Se yaushe ne wai zaka dena kiran yarinyar nan da haka ne? Sau nawa nake faɗa maka ka dena takurata ne ?” Ya ƙarasa faɗa cikin sanyin murya sabida shi koda faɗa yake bazaka gane ba saboda yanda fuskarsa kullum take cikin sanyi da sakewa.

 

Turo baki Mubeen yay tamkar wani yaro sannan ya kalli yayannasa yana me narkar da fuskar shagwaɓa ,juyawa yay yaga yanda ta takure waje ɗaya duk tsoro yagama kamata dan gaskiya kaf gidan ba wanda take tsoro tamkar Mubeen ,hanya yanuna mata yana me mata alama da ta wuce ciki,itama inda yanuna matan ta kalla sannan ta ƙasa-ƙasa ta kalli gefen Mubeen.

 

Muhammad da ya gane me take tsoro ne hakan yasa ya girgiza mata kai alamar taje kawai ,sosa kai tashiga yi tana zazzaro da manyan idanuwanta wanda ko da bata zaro su ba dama haka suke manya kaman ana zazzagosun sumi-sumi ta shiga wuce wa tana waige- waige da sosa kai.

See also  Duniya Biyu Mabanbanta Complete Hausa Novel

Cikin sauri Moh’d ya juya ya nufi motarsa dan He’s late already.

 

Mubeen ma da sauri ya nufi wata hanya wadda tsit kake ji baka jin motsin komi awajan se ƙarar babban gen ɗin da ya cika gun dan da alama babba ne, interlock ne ko ta ina awajan se flowers dake gefen ko wanne side na wajan luf a cikin tukwanansu kowacce da kalarta,wanda yabi hanyar ne kawai ze iya sanin tsayin wajan amma nasan me karatu ze iya hasko hakan.

 

Shan gabanta yay da sauri ta tsaya tana sake zaro ido tare da sosa kanta,shikam harara ya tsaya yana zabga mata me cike da zallar ƙiyayyarta wanda hakan kesa ta ƙara jin tsoronsa,bata gama dawowa daidai ba yasake jefa mata wata tsawar.”Ke ! Wai ke mayyar ina ce ne? Ba na rabaki da shiga sabgar yayana ba wai? Se anyi magana kidinga ƙifƙifta ido wai ke ga mahaukaciya ko tom bari kiji da ke da kike kiran kanki mahaukaciya da masu ɗaure miki ƙugun cewa ke mahaukaciya ce duk se nayi maganinku” matsowa yay yayinda ta cigaba da zaro idon da kusan shine aikinta kunnanta ya kama yana me toshe hanci da ɗayan hannunsa ya murɗa da ƙarfi wanda ko gezau bata ko motsa ba yasake kama ɗayan ya murɗa wanda da sauri ta matsa tana me kallonsa idanta yay ja alamun dai tana jin zafi,gwabjejen takalmin ƙafarta kan ya ankara ta kwaɗa masa a fuska ta ranta a na kare tai ciki.

 

A kusan haukace ya shiga parlon yana rarraba ido.”where is she? ” Ba Wanda ya tankasa cikin waɗanda suke zaune parlon side ɗin wasu ƴammata ya kalla tare da sake daka masu tsawar yana sake faɗin.” I said where is she?” .

 

Meerah ce kusan cikin in,ina take faɗin.” Yaaa..Mubeen…ta ” tana faɗar maganar tare da nuna masa inda ta shiga.

 

A fusace ya nufi hanyar wani step dake jere wanda basu wuce biyar ba da alama ze sadaka da wani gun ne kai tsaye yabi har ya taka na ukun kenan yajin ance .

 

“Dakata ! Kada ka kuskura kabi yarinyar nan ina me kashedinka da ka fita sabagarta tun wuri!”

 

Ta ƙarasa faɗa batare da ta kalli inda yake ba tacigaba da duba littafin dake hannunta ,juyawa yay a fusace yana faɗin.”ooh Momi why are you doing this please why? Kullum seki dinga biye ma mahaukaciya kina fifitata akaina why?”ya faɗa tare da buga ƙafa a ƙasa tamkar wani yaro ƙarami “wallahi se ta san ni ta taɓa yau kam sedai idan bazata fito ba” ya ƙarasa faɗa tare da yin ball da wani ɗan basket da alama ma fruit ne ciki dan tuni na hango wani apple na tsalle a parlon,shima dai wani ɓangaren ya nufa a parlon wanda kusan step ɗin benen ɗaya ne da wancan ɗin ,a fusace yake tafiyar kamar ze tashi sama.

 

…………………………….Har dare babu wanda yaga Hanan bare yaji ɗuriyarta dama mutum ɗaya ne ke iya sawa ta fito kuma shima yau be dawo ba.

 

Mom kuwa idan da sabo ta saba dan Hanan takanyi kwana uku ma a kulle idan abun ya motsa bata buɗe kanta ba.

 

Kallon tafkeken agogon dake jikin bangon parlon Meerah tai wanda yake nuna ƙarfe 10:30 hamma tai a karo kusan na uku kenan Hibba ta miƙe har ta fara tafiya taji Meerah tace.”Hi bab wait for me oo”

 

Hibba ta juyo tana murmushi tace.”Haba jaruma yau ba kwana da mahaukaciyan ne ? Go and knock ooo she will open bab” ta faɗa tana sake sakin murmushin mugunta tare da yin gaba abinta .

 

Meerah data biyo bayanta itama ta bata amsa da faɗin.”Da ace idan nai knock ɗin zata buɗe da babu abun da ze hana ni kwana da ita ,sabida ni bana gudunta tunda ita larura nakan kowa ai.

 

Hibbah ta taɓe baki tana me nufar ƙofar ɗakin ta shige tana me aje wayarta bisa side drawern gadonta ta nufi wata ƙofa da nake tunanin bathroom ne,Meerah ma shigowa tai ta maida ƙofan tasa key sannan ta zauna bakin gadon tana tunanin matsala irinta Hanan for how long zatai ta zama a cikin wannan halin? Shiru tai tai nisa a cikin tunani se daga baya ta numfasa ta miƙe ta hau rage kayan jikinta ta nufi safe ɗin Hibbah ta buɗe ta hau dube- dube can kuma taja tsaki tana mita.”mutum se son jikin tsiyavbaze gyara kaya ba kamar ba mace ba,wani towel ta janyo babba ta ware shi tana ɗaurawa Hanan ta fito da alama alwala tayo,Hibba ta wuce kai tsaye zuwa bathroom ɗin ba tare da suncewa juna ƙala ba……………………….✍️

 

*Hmmmmm bamu soma ma labarin ba ku dai ku biyo ƴar’mutan kanawa*

[09/10, 9:21 am] +234 813 638 8995: 🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢

 

*MATAR WANI!*

 

*STORY & WRITTEN*

 

_BY_

 

*MOM SULAYM*

 

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*💦

 

*Pls fan’s kuyi min uzuri na rashin ji daga gareni , I’m so sorry pls kuyi hakuri da yanda ze dinga zuwa muku*

 

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

 

🅿️🌀3️⃣➡️➡️4️⃣

 

Ɓacin ran jiya ne ya hanasa ko saukowa yayi , bare ma yay dinner, dan haka yau tun 6:am yafito yasa Mama Karima ta basa ruwan zafi da kayan tea,yana zaune bisa dinning ɗin ne Mama Karima ta kawo masa har ta juya zata koma idonta ya sauka kanta dake ƙarƙashin dinning se mazurai take ,da sauri Mama Karima ta juya gudun kar ta cigaba da kallonta ta tona mata asiri a zuciyarta kuma faɗi take.”wato ko mahaukaci yasan me musguna masa”

 

Mubeen ya kai spoon na uku bakinsa kenan yaji kamar antaɓa masa ƙafarsa se kawai ya basar yacigaba da cin abincinsa ,can kuma se yaji kamar saukar numfashin mutum aikuwa yay saurin leƙa ƙasan dining ɗin take kuwa sukai ido huɗu ta zabura ta miƙe da sauri ta na neman hanyar guduwa shima cikin azama ya cafke hannunta ɗaya be wata- wata ba ya falla mata mari ya sake bata wani marin a ɗayan kuncinta ,idanuwa ta zuba masa dan ko gezau ba tai ba

See also  Rumaisa Hausa Novel

ya ɗaga hannu kenan da nufin mangareta gefe se kuma ya fasa sakamakon takun da yaji yana tunkaro gun ko ba a faɗa ba yasan waye dole ya yarfe hannu yana cizan Lips ɗinsa.

 

Da gudunta ta tafi da niyyar hugging ɗin Ya Moh’d se dai kuma tuni taji tayi baya ta tafi luuuu ji kake yif ta faɗi kan tiles runtse idonta tai ba tare da ko ta motsa ba,Ya Moh’d yabi bayan Mubeen da kallo domin ya tabbatar da shine ya sa mata ƙafa ta faɗin.

 

Ƙarasowa yai kusa da ita , sai kuma yai saurin matsawa ganin abinda take son yi wato hugging ɗinsa,alama yay mata da ta miƙe,ba tai musu ba ta tashi Ya Muhammad yabi hanyar dinning dan haka itama tana biye dashi har ya zauna ya ja mata seat daf dashi ta zauna ,tea yay making a cups guda biyu wato shi da kuma ita ,sannan ya buɗe wani warmer dake gefe wanda soyayyar doya ce a ciki duk da ba ƙwai ajiki amma kuma se tashin ƙamshi take se kuma plantain wani warmer kuma dake gefe shi kuma egg source ne a ciki a plate ɗaya ya zuba musu yasa spoon guda biyu ya ɗauka ɗaya ya ɗebo gami da bissimillah sannan ya miƙa mata tai saurin amsa daidai ta kai baki ƴan’gidan suka fito kamar a tare kowa daga nasa part ɗin ,dukansu sun sha wanka kowa se zuba ƙamshi yake kana ganinsu kasan cewa kowa da idan ze nufa,Hibba kam wata irin shiga ce jikinta na wandon jeans black se whirt shirt da nake hangowa saboda jacket ɗin da ta ɗora irin kimono ɗin nan ba lefi tana da kauri sosai gashi ta kai mata har gwiwa,kunnuwanta sarƙafe da earphones ga wani irin hill shoe da ƙararsa ma kawai kusan ta gama cika parlon ,Meerah kam sanye take da rigar material doguwa se ɗan white baby hijab da Kuma wata farar riga ƙal irinta ma’ aikatan jinya ,da ɗan sassarfa ta ƙara so da alama tana gab da makara ne da sauri ta zauna ta janyo flask ta fara haɗa ma Momi tea sannan itama ta haɗa ma kanta,gefensa ta kalla tace “Yaya Muhammad morning”murmushi yay yace .” Morning my Mee”waiwaya wa tai gefen Hanan dake cin abincin duk tai gutsi- gutsi- dashi ba wani ci take ba se wasa take dashi hannuwanta biyu tahaɗa tana murza mata alamun dai tana mata magana ,shiru tai taƙi ɗagowa murmushi kawai Meerah tayi tasan halin Hanan ɗin, ta aje tea ɗin da take sha kenan ta tashi,Hanan ta kalli cup se kuma ta ɗauka daidai Meerah na saƙala handbag ɗin ta kenan kawai taji zubar abu ajikinta kan kuma taji wani zafi-zafi ko ɗumi me kama da zafi na ratsa ta lokaci guda ta kai dubanta ga rigar hannunta yanda ta gama ɓaci da tea ɗin tuni ranta idan yay dubu yaya mugun ɓaci ta yarfe hannu tare da faɗin.”ashhh!” Da sauri Momi ta ƙara so ta riƙe hannun nata banda sorry ba abinda take faɗa mata .

 

Yaya Muhammad kam tisseu ya ɗauka ya goge bakinsa tare da miƙewa ya kalli Meerah da itama shi ɗin take kallo tana so taga reaction ɗinsa se dai kawai ya sunkuyar da tare da ce mata.”Sorry my Mee you know her condition”Ya juya kai tsaye yana faɗin.” Momi pray for us I’m going now” ya ƙarasa faɗa yana kallon agogon dake sarƙafe hannunsa ,momi ta buɗe baki tace.”Allah ya kiyaye ya bada nasara” kusan a koda yaushe kalar addu’ar da mahaifiyar ta su ke yi musu kenan.

 

Ya Muhammad da “ameen” ya amsa sannan ya kalli inda Hanan take ya juya ya nufi ƙofa yana tunanin yadda zata kaya mata bayan tafiyarsa dan yasan tabbas akwai ƴan’ kan zagin da baza su barta ba.

 

Tsaye yake dama yana jiran fitar boss ɗin ya ƙara so ya zartar da hukunci,momi kam juyawa tai ta nufi hanyar nata parlon wanda dama tuni Meerah ta wuce ciki abinta.

 

Wani ashar da Hibba ta narko ne yasa na gane ta na gun har yanzu ,nufar Hanan ɗin yai kai tsaye ya zuba mata wani irin gigitaccan mari wanda hakan yasa Hanan ɗin sakin wata ƙara ,ƙarar da zasu ce ita ce ƙara ta biyu da ta taɓa yi tunda tazo gidan, tsaki Hibbah taja tare da barin wajan kai tsaye .

 

Cike da ƙasaita ya ƙara so inda take yasa ƙafa ya zungureta yaga ko gezau ba ta motsa ba shi ɗin ma tsakin yaja yana faɗin.”Ga ra ma da serious one ɗin yazo gaba ɗaya”tsallaketa yay ya nufi ƙofan fita har ya riƙe handle ɗin ƙofan se kuma ya juyo ya kalleta na wani sakanni se kuma a hankali ya buɗe ya fice.

 

 

★★…………………..★★

 

Momi ce riƙe da waya tasa Hanan agaba tana kallo na wani lokaci kafin ta ɗauke wayarta tai dialling wata no ta sannan kara a kunne .”Assalamu alaikum “daga can ɗaya ɓangaren aka amsata tare da tambayarta iyalan gidan tana amsa wa da damuwa tashiga fada masa .”Abeey Muhammad damuwar dai ɗaya ce wato matsalar Hanan har yanzu abun ba canji last month ma taƙi yadda sam ai mata amfani da wancan da Dr.Wahab yabada ban san ya zanyi ba dan yanzunma ta sake shiga irin wancan yanayin da ba a so”. Shiru yay yana sauraron matar tasa da yanayin muryarta kadai yasan tana cikin damuwa sosai

See also  Ummu Aymana Complete Hausa Novels Documents

ya rasa se yaushe ne komi ze zo ƙarshe larurar Hanan na damun kowane baligi me kuma hankalin gidan shekaru sun ja da ciwon Hanan sama da shekaru huɗu kenan tana cikin ciwon hauka duk wani magani anyi amma ina abu yaci tura har yanzu basu dace ba.

 

Cigaba yay da kwantar mata da hankali ta hanyar tabbatar mata da insha Allah watarana zasu yi dace hakan nan kuma zata warke da haka sukai sallama bayan ya kwantar mata da hankali.

 

★★★. ★★★

 

Tsit kake ji tamkar ba wata halitta agidan idan ba ciki ka shiga ba,da Ya Moh’d na ci karo kawai a parlon ya kurawa magzine ido amma kana gani kasan idonsa ne kawai akai amma kuma hankalinsa ba ya kai ,ɗakinsu Hibba na leƙa nan ma shiru Meerah na bacci se Hibba da tai nisa cikin tunanin tabbas komi yana da muhallinsa yanzu kam ta sake tabbatarwa kanta da cewa Hanan wata ɓangare ce na rayuwar gidan .

 

Yau tsawon sati kenan da Hanan ke kwance tun daga ranar basu daga wata walwala ko ba komi idan anzo cin abinci ta ta yin abubuwan da zasu yi ta magana kenan musamman ita da Mubeen da basa shiri ita kam yau ta tabbatar da cewa sau da yawa kafi yin missing ɗin wanda bakwa shiri,juyi tai tana mata fatan samun lafiya.

 

Sha biyu da rabi na dare ya tashi zaune yayi zurfi a cikin tunani can kuma ya miƙe zumbur ya fita , parlon ba kowa ba kuma motsin komi se sanyin a.c dake tashi komi na parlon yayi

neavy blue sakamakon hasken wutar da aka mayar da shi neavy blue a hankali yake tafiya zuwa hanyar da zata sada shi da ƙaramin kitchen ɗin gidan har ya kusa shiga se kuma ya juya ya nufi ɗakin Meerah wanda be wani tsaya ba kai tsaye ya tura ya shiga be ga kowa ba a ɗakin da alama Meerah ba ta ciki Meerah kam yarinya ce da za a kira da ƴar’ halak duk runtsi ba ta barin Hanan ita kaɗai tun farkon zuwan ta gidan lokacin da haukan yake ɗanye ma dan wani tabon da Hanan ɗin tai mata dashi zata je lahira.

Kallon ɗakin yake ba kowa se can ya hangota kwance bisa carpet daƙyar ya iya jan ƙafarsa ya ƙarasa inda take kwance ya sunkuya agabanta tare da tsura mata idanuwansa karo na farko da ya taɓa jin nadamar abinda yake aikatawa Hanan ɗin a rayuwarsa kallon ƴar’doguwar fuskarta yay Wanda eyelashes suka kwanta sukai luf ko tsagun idon baka gani ,gata dai mutum har mutum amma ina ta zama mutun mutumi kowa yana gudu da kuma tsoron irin wannan condition ɗin dan ba ƙaramin warning likitanta yay ba kan shigar ta irin wannan condition ɗin dan idan tana faɗuwa haka to tabbas cikin ɗayan biyu ne ko dai ta warke ko kuma sanadin hakan da wuya ta taɓa warkewa,abubuwa da yawa ke yi masa yawo a kwanyar kansa dan matuƙar aka san shine sanadin tashin ciwon nata to kuwa tabbas da wuya indan zaman gidan be gagaresa ba dan tabbas Abbansu baze barsa ba tunda be taɓa sanin irin musgunawar da yake mata ba …….

 

.

“Ya Mubeen!! ” Karo na uku kenan da ta kira sunan nasa idon jawur kamar garwashi yazuba mata ba tare da ya amsa ba ,a hankali ta ƙara so tazauna tana facing ɗin sa cikin sanyin murya ta fara masa magana.” Ya Mubeen kayi haƙuri insha Allah kafin Abba ya dawo zata tashi ta samu lafiya ” ta ƙara sa muryarta cike da rauni,kusan raba dare yay dan har bacci ya kwashe Meerah wadda ke cike da tsananin mamakin Ya Mubeen duk dai tasan tsoron Abbansu ne ke addabarsa,se kusan quarter to 3 ya tashi yaje yakwanta nan ma kasa baccin yay Wanda hakan ya saka shi dole ya je ya ɗauro alwala ya fara salloli yana me nemawa Hanan fatan samun waraka da kuma fatan Ubangiji yasa ta farka a daren yau ɗin haka nan se kusan asbah bacci ya ɗauke sa .

 

 

……………….Ring na

Wayarsa ne yaji ya cika masa kunne a hankali ya fara murtsuka idonsa ganin wani irin haske da ta cika masa ɗakin da alama dai ba yanzu gari ya waye ba,kallon screen ɗin wayar yay kan daga bisa nita miƙe zumbur ganin sunan dake yawo akai

 

_Sweet brosss_

Zumbur ya miƙe da sauri yanufi bathroom.

30, min’s ago yashigo parlorn wanda lokaci guda ƙirjinsa ya bada rasss! A rayuwarsa ya daɗe beji tsoron wata rana ba irinta yau tun yana yaro ya taso shi mutum ne me tsokana da rashin ji amma be taɓa jin dana sani ba irin yau ɗauke idonsa yay daga kan Abban nasu ya mayar kan *sweet broth* ɗinsa shima kasa kallon ƙwayar idonsa yay daidai megadi yau sallama yashigo ya russuna yana gaida Abban tare da sanar masa cewa motar ambulance ɗin tazo.

“Ambulance….” Ya faɗa a fili rungume Momi ta fito da ita da temakon Meerah da Hibbah idan kaganta a hannun Momi se ka rantse kace wata baby ce ,trouser ne jikinta irin pencil ɗin nan se wata irin gown silk golden as usual kanta sanye da wani irin ƙaramin hijab Wanda iya karsa wuyanta ,tun kan su kai ga ƙarasowa tuni su Yaya Muhammad da Abban suka fita .

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
A kan idonsa aka sakata acikin ambulance ɗin ma’aikatan suka rufe da sauri wanda tuni masu gadi suka wangale tangamemen gate ɗin tuni motocin su Abba suka rufawa motar baya wadda ta gama cika snguwan da ƙara wadda take nuna cewa tabbas akwai wani abu da yake accidentally or emergency ciki……………………..✍️

 

 

*Mum SULAYM*

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top