Hausa Novels

Matasan Mu 1 to 55 Hausa Novels

BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM.

        SADAUKARWA

Wannan littafi naku ne MATASA, ina fatan zakuyi amfani da darussan da suke ciki. Wannan labari ba rayuwar wani bane, na kirkireshi ne domin maslahar al-umma gaba daya. Allah yasa abinda zan rubuta ya zama ishara ga sauran mutane.

Page 1 to 5

Wata motace tashigo cikin wani katon gida, maigadin gidan yana biye da ita bayan rufe gate din da yayi. Wani babban mutum ne ya fito daga cikin motar fuskarshi dauke da damuwa.

Tunda yashigo ihun MATASAN da suke cikin gidanshi ya cika masa kunne. Risnawa Maigadin yayi yana fadin barka da dawowa Alhaji. Murmushi yayi yana fadin yauwa sannu da aiki Baba ya gidan? Yace lafiya lau.

Alhaji yace wallahi Baba halin Abdallah yana bata mani rai, shikenan yaro kamar wanda aka haifa agidan ‘yan kwallo, bashida wani aiki sai kallon kwallo. Abinda yake bani haushi yanda yake tara mani abokansa acikin gida ko kula da lokacin sallah basayi.

Badan komai yasa na hada masa kayan kallon kwallo agida ba saboda banaso yarika zuwa gidan kallon kwallo saboda yawan fitinar da akeyi, amma naga abun yanaso yazamar mani damuwa.

Wai tun yaushe  suka shigo gidan nan? Baba yace wajen karfe 5 : 30. Alhaji yace sun fita sallar magriba da Isha’i? Baba yace gaskiya babu wanda naga fitowarsa, kila dai acikin gida sukayi ta. Abdulhakim ne kawai mukayi sallah dashi.

Tsaki Alhaji yayi yana fadin na rasa dalilin da yasa Abdallah yake son kallon kwallo har haka, kana gani da yanda ya kammala karatunsa, badan na dage ba da yanzu yashiga kungiyar ‘yan kwallo ta pillars kano.

Baba yace ai sai hakuri Alhaji, amma turawa sun bata mana MATASANMU, yanzu kwallo ta zama kamar rayuwarsu, MATASA dayawa suna iya rasa jam’i saboda kwallo, kuma babban abun haushin yawancin lokutan da ake sawa na kallon kwallo duk lokacin sallah ne.

Ko dai ana cikin kallo akira sallah, ko kuma kafin afara ashiga sallah, MATASA da yawa basa sallah akan lokaci. Alhaji yace ai ba MATASA kadai ba, wallahi hada wasu MAGIDANTAN zaka gani awajen kallon.

Ai babu abinda zamuce sai addu’a, amma yaranmu suna cikin matsala wallahi, zamanin nan ya bata mana MATASA. Baba yace addu’a ita kadai ce abinda zamu dage da ita, domin matukar MATSANMU suka lalace tamkar duka al-ummace ta lalace.

Domin MATASA sune al-umma. Allah ya kara tsare mana su. Alhaji yace amin. Rufe motar yayi yana fadin bara na shiga ciki na samesu, wallahi dole na dauki mataki akansu, sam bana son abinda zaisa arika wasa da sallah. Baba yace Allah ya bamu alkhairi.

Da sallama yashiga falon dai dai lokacin da ya kara jiyo wani ihun daga dakin Abdallah, da alama sune suka kara cin wasan. Amal da take zaune afalo ita da Mamy ne suka amsa sallamar.

Tashi Amal tayi tana fadin Abbah sannu da zuwa, murmushi yayi yana fadin yauwa Amal sannu da gida, amsar jakarshi tayi ta nufi dakinshi da ita. Mamy tace sannu da zuwa Abban Amal.

Yace yauwa sannu da gida Mamyn Amal, kina zaune a falo amma sam hayaniyar da take fitowa daga dakin Abdallah ba ta damunku. Ya kamata ace kinyi masu magana, yanzu haka ko sallah basuyi ba.

Mamy tace ni wallahi harna gaji da ciwon baki akan maganar kwallon Abdallah, tun farko sai da nace kada ka hada masa kayan kallon kace bakason yana yin dare awaje. Kuma gani nayi yana tare da abokansa babu dadi ayi masa magana agabansu shiyasa na kyalesa.

Tsaki Abba yayi yana fadin Allah yasa tare da surukansa yake, bara naje na samesu. Wucewa yayi yabar Mamy tana dariyar maganarsa. Yana tura kofa suna hayaniyar cin kwallo. Dif sukayi ganin Abba abakin kofa fuska adaure.

Gaba dayansu suka sauko kasa kai akasa suna gaishe dashi. Amurtuke ya amsa masu yana fadin kunyi sallah kuwa? Abdallah yace Abba wace sallar kuma? Abbah yace bama kusan ko wace sallah yakamata ace kunyi ba kenan? Abdallah yace ayi hakuri Abbah.

Abbah yace sallar magriba da Isha’i nake nufi. Dukar da kai suka karayi, Abdallah yana fadin Abba bamusan ankira sallah ba ai. Cike da mamaki yake kallonsu, sosai ransa ya baci ganin har 8 ta wuce amma suna daki basu san anyi magriba ba bare sunyi Isha’i.

Tsawa ya daka masu yana fadin kowa ya tashi ya tafi gidansu, kuma wallahi matukar haka zaku rikayi babu wanda zai kara shigo mani gida kallon kwallo, wannan ai shirmen banza ne.

Manya da ku kuna zaune bakuyi sallah ba, anyi magana zakuce wai bakusan ankira ba, da yake sallar ba’a ranku take ba dole zakuce bakusan ankira ba. Wallahi kuji tsoron Allah, wannan kallon da kukeyi babu inda zai kaiku sai ga halaka matukar baku kiyaye DOKOKIN ALLAH BA.

Bance kada kuyi kallo ba, amma kusan irin lokacin daya kamata kurika zaman kallo. Mikewa sukayi suna sosa kai suna fadin ayi hakuri Abbah bazamu sake ba. Shigowa ciki yayi kowa ya suri takalminsa suka fice.

Kunkunai Abdallah ya farayi ganin yanda Abbah ya disgashi agaban abokansa. Abbah yace wallahi Abdallah kaji kunya, amatsayinka na babba agidan nan kaine ya kamata ace kana yima su Abdulhakim fada.

Sam baka koyi da kaninka, duk da yana karatu amma baya wasa da addininsa, kuma karatun boko bai hanasa neman na addini ba, kana kallo matukar Abdulhakim yayi sallar magriba a unguwarnan baya dawowa gida sai Isha’i.

Haka yake zama cikin sauran mutane a dora masa karatu, yanzu wannan abun ba abun burgewa bane, yau ko Allah ya dauki ransa yana daukar karatu wace irin makoma kake tunanin zai samu? Da ace mutum ya mutu yana zaune ya shagala da abun duniya gara ace yana kan hanyar neman ilimi ne.

Allah yana gani na baka dukkan wani ilimi na rayuwa, ka kammala karatun degree dinka tun shekara 2 kaki maida hankali wajen aikin da nake nema maka, computer center din dana bude maka sam bakason zama aciki saboda wannan kwallon daka sama ranka.

Da asonka ne na barka karika tafiya kasashe kana buga kwallo, shiyasa sam kaki maida hankali akan aikinka, abokanka da yawa da kuka gama karatu dasu sun samu aiki amma kai ka rika shiga internet kana sanin halin da ake ciki ma nasan bakayi.

To bari gaji, idan zaka cire ma ranka son kwallo gara kacire, nide bazan haifi Dan dazan sallama ma duniyashi yarika buga mata kwallo ba, gara ace na sallama ma addinin Allah shi domin al’umma.

Kuma wallahi idan bakayi hankali ba sai na cire kayan kallon dakin ka, kuma karfe takwas na dare ina shigowa gida dole kadawo na rufe gidana koda wasan duniya ake bugawa kuwa.

Saurin zubewa Abdallah yayi yana fadin Abbah dan Allah kayi hakuri, wallahi daga yau zan rika kiyaye lokacin sallah, kuma Abbah kasan bana wasa da sallah ai. Abbah yace idan ba lokacin kallon kwallo bane ba.

Nide na fada maka. Abdallah yace naji wallahi zan gyara. Murmushi Abbah yayi ganin yanda Abdallah yayi zaman dole jin zai hanashi kallon kwallo, shikansa yasan Abdallah yana matukar son kwallo, wannan dalilin ne yasa ya hada mashi kayan kallon saboda bayaso yarika kai dare awaje.

Abbah yace shikenan, tashi kaje kayi sallolin da bakayi ba. Abdallah yace nagode Abbah, da sauri ya mike yashige bandakin cikin dakinsa. Girgiza kai Abbah yayi yana fadin Allah yashirya.

Juyawa yayi ya fita, afalo ya iske Mamy da Amal, Abbah yace ina Abdulhakim fa? Mamy tace yana dakinsa wani aikin yakeyi shiyasa bai fito ba ko. Amal tace Abbah karatu yakeyi wai karatun da Malaminsu yayi masu dazu bai rike ba.

Abbah yace da kyau, haka akeso ai, yafi yayansa maida hankali. Mamy tace muje ka rage kayan jikinka kashigo ko ruwa bakasha ba katsaya magana akan yara. Abbah yace ai dole nayi. Amal tace Allah Abbah dama ka kwashe kayan kallon Yaya.

Mamy tace to sarkin jan fada, kibari ya jiki zakisha duka ne, dama dazu kin yage masa hoton ‘yan kwallonsa yaso yamaki duka kika ruga. Abbah yace kibarni dashi Mamana wata rana zan kwashe ai. Dariya tayi tana fadin yauwa Abbana.

**** *****

Alhaji Bashir Hamza kenan, haifaffan garin Kano ne, yana aiki da fannin lafiya, shine director under WHO gaba daya, sannan yana da manyan malls guda 2, ga gidajen dayake bada haya. Yana zaune a babban gidansa da yake Sharada.

Matarsa daya mai suna Hajiya Bilkisu wacce take itama ‘yar kano ce. Suna da yara 3, babban cikinsu shine Abdallah, wanda ya kammala karatunshi a nan BUK a fannin computer ya kammala service dinsa yanzu haka yana zaman jiran aiki ne.

Abdallah yana matukar son kwallo tun yana yaro, bayan kammala secondary dinsa yaso Abbansu yabarsa yashiga club na ‘yan kwallo amma ya hanasa, haka ya gaji da naci ya hakura, shiyasa sam baya maida hankali akan karatunsa sosai.

Gashi yana da matukar zuciya, abu kadan sai ya kama dambe musamman idan ka tabo masoyansa wato ‘yan kwallo, yana matukar son Real Madrid, duk lokacin da akayi kwallo idan ba ‘yan gidansu bane sukaci ko abinci bayaci saboda haushi.

Lokacin yana secondary ya taba cirema wani hakori saboda yana masa dariya an cisu kwallo. Shiyasa da yawan mutane suke tsoronsa saboda zuciyarsa.

Abdulhakim shine yake bimasa, yaro natsatstse, yana a 3 hundred level anan BUK inda yake karantar mass com, saboda yana matukar son yin bincike arayuwarsa. Wannan dalilin ne yasa yafi zama awajen manyan domin yanaso yarika saurarar labarun mutanan Da.

Hakan yasa bashida aboki agida kamar Baba Maigadi, domin yana bashi labarai masu dadi, haka kuma malami guda garesa wanda yake koya masa Sirah, dan yana son tarihi. Abdulhakim yana da nutsuwa.

Idan kagansa sai kace shine babba, sam Abdallah ya bar masa girman danshi Abdallah gaye ne. Amal itace karama, sunan mahaifiyar Abba aka sa mata wato Aisha shiyasa ake kiranta da Amal.

Yanzu haka tana nursing school inda take a shekarar farko. Gidansu akwai tarbiya, Iyayensu suna kokari wajen tarbiyantar dasu, kuma suna zaune lafiya.

Wannan shine tarihin gidansu Abdallah.

***** *****

Kwance yake adaki wajen karfe 2 na dare yana kallo acikin wayarsa, kamar daga sama yaji motsin bude kofar dakinsa. A firgice ya mike har yana wurgar da wayar saboda tsoro. Dadynsu ne ya gani tsaye abakin kofa yana kallonsa.

Da ka gansa zaka gane rashin gaskiyar da take boye a fuskarsa. Cikin rawar murya yake fadin Dady lafiya baka kwanta ba? Wanda aka kira da Dady yace kai zan yima wannan tambayar ai.

Salman yace Dady ni na kwanta tun dazu ai. Dady yace amma bakayi bacci ba kuma, motsinka naji yasa nashigo dakin ai. Na tabbatar wannan kallon jarabar ne kakeyi. Farkawa nayi na fito nasha ruwa har zan koma naji kamar motsi shiyasa nayo dakinka saboda nasan kaine mayen kallo.

Wai wane irin kallo ne baza’ayisa da rana ba dole sai da dare? Hannu Salman yasa akai yana sosawa. Dady yace kawai kuna batama kanku lokaci, Salman yace Dady bafa kallo nakeyi ba. 

Dady yace charting kakeyi ko? Salman yace shirin kwanciya nakeyi shine kajiyo motsi. Dady yace wallahi kaji tsoron Allah, ni nasan wannan charting din ko kallon da kakeyi shine yake hanaka samun sallar asuba cikin jam’i.

Kuma kasan kana zuwa makaranta, gashi final year kake ya kamata ace karatu nashigo na sameka kanayi amma ka tsaya kana kallo. Salman yace Dady ina karatu fa, shiyasa yanzu bana dawowa gida da wuri.

Dady yace ni dai na fada maka, kuma ka kashe wayar ka kwanta hakanan. Salman yace to Dady, juyawa yayi ya rufe masa kofar. Ajiyar zuciya Salman ya saki yana fadin ya akayi na manta ban rufe kofar ba ma? Dirowa yayi ya sama kofar key ya haye gado yana fadin haba Dady ai sai da rage zafi.

Wannan kallon ai bazai yuwu ayisa da rana ba, irinsu Saddika ‘yan sa ido tsaf wata rana zata iya ganoni, yanda banida matar nan kallon ai shine abokin debe kewata. Juyi yayi ya lalubo wayarsa yashige bargo ya cigaba da kallonsa yana juyi.

**** ****

Alhaji Mannir mai Canji kenan. Asalinsa dan cikin garin Bicci ne, kasuwanci ne ya maidoshi cikin garin Kano da zama, yana sana’ar yin Canji har Allah ya dagasa yayi kudi sosai da harkar Canji.

Matarsa daya mai suna Rahma wacce suke kira da Ummi, suna da yara 2, Salman shine babba wanda yake karatu a BUK yana shekarar karshe, sai Saddika tana a year 2. Salman bayajin magana, bashida aikinyi sai tara ‘yan mata.

Cikin makarantarsu ‘yan matansa sunfi biyar, duk set sai yayi budurwa, wannan dalilin ne yasa lokacin da Saddika ta gama secondary ya dage ya nema mata addimission a wudil yace bayaso suyi makaranta daya.

Duk yanda Umminsu taso ta tafi BUK Salman yaki yarda, haka suka kyalesa ta rika zuwa Wudil kasan cewar tana da mota. Salman su 4 ne a group dinsu, gaba dayansu basa jin magana, sun iya kwallon film din batsa, wannan kallo ya zamar masu jiki.

Ko yau ma abinda yake kallo kenan Dadynsu yazo. Yana iya kashe dare yana kallo, kullum cikin downloading films yake, har gasa sukeyi aga wanda zai kawo film din da yafi dadi.

Wannan shine labarin gidansu Salman.

***** *****

 Page  5 to10

Zaune wasu MATASA suke asaman wani benci wanda ya kasance majalissarsu, matukar akace maka yamma tayi to zaka samesu awajen suna zaman sa ido ga ‘yan matan da suke wucewa.

Wani ne yazo wajen da sauran MATASAN suke zaune, hannu ya basu suka gaisa daya daga cikinsu yana fadin haba Babban Yaro wai ina katsaya haka ne? Wanda aka kira da Babban yaro yace kai dai bari. 

Wallahi wata kazamar yarinya muka hadu da ita ta yarfamu nida Mubarak. Dariya suka sa, Sani yace ai Allah ya kara maka, kaida kake da Zuby baka iya hakura sai kabi duk macen daka gani ta wuce.

Ko DAN GHANA wanda yake SARDAUNAN MATASA bazai nuna maka bin mace ba, saboda sa’arshi bai taba bin mace ta yarfashi ba. Amma kai ko akuya aka shafama hoda sai ka bita. Dariya gaba dayansu suka sa.

Wanda aka kira da Sardauna yace ai kasan Babban Yaro hadamarsa tayi yawa, nifa ba kowace mace nake bi ba, ai daka ga macen daya kamata kabi kaima kasani ba sai an fada maka ba. Mubarak yace ai sai da na fada masa, haka mukayi ta binta muna mata magana ko kallo bamu isheta ba.

Babban Yaro yace ka barta wallahi sai na yar fata. Sardauna yace mai yakawo na yar fawa kuma? Tunda bata baka hadin kai ba kawai ka barta, kasan nifa banaso ana wulakanta Mata domin Iyayenmu ne.

Sani yace wannan haka yake Dan Ghana, shiyasa muke sara maka kana matukar girmama Mata sannan babu wanda ya kaika iya tsarasu. Babban Yaro yace ko saboda kyanshi ai dole mace ta so shi. Saurin mikewa Sardauna yayi yana fadin ga Malan can ya dawo daga kasuwa bara na tarbesa yana iya zuwa ya yar fani anan.

Wucesu yayi suna mashi dariya, yana zuwa ya kai hannu ya karbi ledar da take hannun Malan yana fadin sannu da dawowa Malan. Murmushi yayi yana fadin yauwa Dan Ghana, ko nace Sardaunan MATASA.

Dariya Sardauna yayi yana shafa kai yace kai Malan. Malan yace ai gara nima na Dana, banda sakarci kana da sunanka mai dadi amma mutanan unguwa sun canza maka suna, duk wanda na sani zaka samesa da sunaye biyu ko daya.

Amma saboda kwarewarka kai suna ukku gareka, na tabbata ayanzu idan wani yazo unguwar nan yana tambayar asalin sunanka da wuya asamu mutane biyar wadanda zasu iya gane kai ake nufi.

Sardauna yace nide Malan mukarasa gida kaga ana shirin kiran magriba. Malan yace tunda bakaso afada maka gaskiya ba, ko kuma bakaso wata budurwarka tazo wucewa taji ina maka fada.

Dariya Sardauna yayi yana fadin nide Malan muje kawai. Malan yace muje yana iya da kai tunda kai daya nake dashi, amma nasan abinda zanyi zansa Innarka tayo maka kannai kamar guda 5 nasan zan samu saukin wannan tabarar taka.

Yaro ya girma kimanin shekaru 26 amma kana jin kan ka kamar dan shekara 15, tunda ka kammala diploma dinka da kyar har yanzu kaki wucewa. Kasuwancin ma bakaso, saboda kaga Innarka tana baka kudi.

Dariya Sardauna yayi yana fadin wallahi Malan nasan Inna bazata kara mani kannai ba, kuma kota kara babu wanda zakuso sama dani. Murmushi Malan yayi ya kamo kunnanshi yana fadin tunda ka maidamu kakanninka ba. Wuce muje kada kasa na rasa jam’i.

Umar kenan wanda akafi sani da DAN GHANA KO SARDAUNAN MATASA. Shi daya ne awajen Iyayensa, Malan Adam shine maifinsa, dan asalin garin kano ne, dan kasuwa ne yana da shagon saida kayan gwari.

Yana da rufin asiri dai dai gwargwado, yana zaune a unguwar Sallari, yana daya daga cikin mutanan da suka dade a unguwar, yana zaune agidan kanshi. Matarsa daya mai suna Halima wadda ‘yan unguwar suke kiranta da Inna Uwani.

Macece mai kirkin gaske, sun dade ita da mijinta da yin aure kafin Allah ya basu haihuwa. Tana sana’ar cikin gida inda take saida kayan awo, mutane da yawa awajenta suke awon kayan abinci.

Kasancewar tana da sauki, sam bata ha’inci a wajen awonta, mutane har lakabi sukayi mata da a Kafta masu, ko awon fulawa zatayi maka idan ka hada dana shago sai kaga bambanci. Mijinta shine wanda ya bata jari.

Sannu ahankali har itama ta tsaya da kafafuwanta, sosai take ciniki, duk da arhar da takeyi hakan besa jarinta yayi kasa ba, kuma batajin kyashin baka bashi koda kuwa baka maido mata na baya ba.

Lokacin da Allah ya albarkaceta da samun cikin Umar sosai sukayi farin ciki ita da maigidanta. Ranar da aka haifesa tamkar balarabe saboda tsabar kyau, gaba daya unguwar ta dauka Inna Uwani ta haifo balarabe.

Haka yara da manya suka rika tururuwa zuwa ganin jariri, ganin yanda Umar yake da farin jini yasa Malan ya tashi tsaye wajen nema masa maganin baki, itama Inna kullum cikin tofa masa addu’a takeyi.

Umar yana girma kyansa yana kara fitowa, Inna har bataso taje unguwa dashi, ita da Malan babu wanda yake kiran sunansa sai dai su kirasa da MARUSANDA, domin na fari ne.

Yayi primary da secondary duk private, sosai suke nuna masa so. Umar tunda yashiga secondary ya fara yin budurwa, babu ruwansa da shashanci amma akwaishi da son mata, sam ba ruwansa da abokai ‘yan iska.

Shiyasa matukar yana abota da kai yaga ko goro kakeci to zai raba hanya da kai. ‘Yan mata da yawa suna matukar sonsa, shiyasa sam Umar baya tsayawa akan budurwa daya, idan ka gansa da wata yau gobe zaka gansa da wata.

Sosai wannan hali na Umar yake damun Malan, duk lokacin da yayi magana sai Inna tace su godema Allah da yasa baya shaye shaye, kuma tayi imani da Allah Marusanda baya neman mata, haka Allah yayisa da son mata kawai.

Kuma yarinta ce wata rana bazaiyi ba. Da wannan maganar ne take kwantar ma Malan hankali. Bayan ya kammala secondary ‘yan ajinsu suka danashi SARDAUNAN MATASA.

Kamar wasa sunan yabishi domin ya iya tsara mace. Lokacin daya shiga makarantar gaba da secondary kuma sai son matansa ya karu. Gashi ya iya gayu, duk kayan dayasa sai sun karbesa.

Shigarsa makarantar ne abokansa suka sa masa Dan Ghana. Tun daga lokacin sunansa ya kasu kashi biyu, idan aka hada dana gida kuma 3, sannan ga asalin sunansa 4.

Ganin Sardauna yana tara abokansa cikin gida adakinsa yasa Malan ya maidasa dakin da yake waje dan su samu saukin hayaniyar da suke masu. Malan yaso Sardauna yarika binsa kasuwa idan yadawo daga makaranta amma sam Sardauna bayaso.

Haka nan Malan ya kyaleshi dan bayaso yarika matsa masa. Akwai wata yarinya mai suna Jamila, anan unguwarsu take, tunda ta taso Allah ya jarabceta da son Sardauna. Sai daishi sam baya sonta yana daukarta tamkar kanwarsa.

Duk da son matansa amma Allah baisa yana son Jamila ba, domin suna mutunci da Iyayenta da Innarsa hakan yasa yake mata daukar kanwarsa. Tun tana boye sonshi azuciyarta har yafito fili amma shi yaki ya nuna mata ya gane me take nufi.

Da haka har ya kammala diplomarsa, anan ya kara samun lokacin zama majalissa. Babu yanda Malan beyi ba akan yazo ya bude masa shago amma yace bayaso, idan ya girma nan gaba zai nemi kudi.

Duk lokacin daya fadi haka sai dai suyi dariya dan shagwabar Sardauna tayi yawa, har yanzu gani yake be kirma ba. Ayanzu bashida wani buri wanda ya wuce yaga mace yace yana sonta, tana amincewa dashi suka fara soyayya ta kwana biyu daya sami wata shikenan ya rufe babinta.

Mutanan unguwa sun sha kawo kararsa wajen Malan akan yaudarar da yakema ‘Ya’yansu sai dai Malan ya basu hakuri. Inna kuwa duk wacce takai mata kararsa to bata sauraranta, kullum tana fadin an sama Danta ido, hakan yasa mutane suka gaji suka kyalesu saboda suna ganin mutuncin Inna.

Wannan shine labarin UMAR, MARUSANDA, DAN GHANA KUMA SARDAUNAN MATASA.

***** *****

Da gudu wani yashigo cikin gida yana haki, haka ya tsallake mutanan da suke tsakar gidan yashige dakinsa. Cike da mamaki mutanan suka bishi da kallo. Cikin sauri ya fito hannunsa dauke da wata katuwar takobi yana mazurai.

Saurin mikewa sukayi mahaifinsa yana fadin kai Aminu lafiyarka kuwa? Ina zakaje da wannan takobin haka? Yana zare ido ya karkace baki yana fadin wallahi Baba yau sai naci Uwar Bala.

Kawai mun lika poster din Dan majalissa shine sukaje shida yaransa suka yageta suka lika tasu. Daya keshi Dan akuya ne. Tsaki Babansa yayi yana girgiza kai yace ai dama nasan maganar bazata wuce akan siyasa ba.

Sau nawa zan fada maka ka fita daga harkar ‘yan siyasa? Kalli yanda ka maida kanka, kazama karensu, basa nemanku sai bukatarsu ta taso, haka zasu jefeku da kudi kadan ku kuma kuyi masu abinda suke so.

Haba Aminu, meyasa kakeso dole sai kajawo mana fitina ne? To bari kaji na fada maka, wallahi duk ranar da kaje ka kashe wani ko ka illatashi akan fadan siyasa kaima kama ka za’ayi, idan hukuncin kisa aka yanke maka babu wanda zai kwaceka domin shekarunka sun kai ayanke maka hukunci.

Kuma ina me tabbatar maka acikin mutanan da kake yima hidima babu kafar wanda zaka gani akotu wai yaje belinka, daga ranar da suka dena ganinka bazasu damuba, abinda zasu maida hankali akansa shine neman wanda zasu maye gurbinka dashi.

Idan kuma illataka akayi babu abinda yayi masu zafi, sai ka ci sa’a ne zasu aiko dan aike ya kawo maka kudin magani domin kai din ba jininsu bane. Kuma daga ranar ka gama amfani awajensu.

Kalli yanda ka maida kanka, kalli hanuwanka yanda ka jera wasu zobuna tamkar mai kidin kwarya, kalli wuyanka ka saka wata sarka kai ba mace ba, kai ba dan Daudu ba. Ga wani uban gashi daka tara sai kace mutanan Da.

Kalli shigarka kana fama da wani gajeran wando guiwa ayage. Duk wanda ya ganka bazai maka kallon mutumin kirki ba, ka maida shaye shaye tamkar abinci. Wallahi Aminu kaji tsoron Allah.

Ka duba kaga kannan ka, ko kunya ba kaji, ace duk cikin yarana kaine ka fita zakka. Bazanyi maka baki ba, amma kabi duniya ahankali, wanda ya bita ahankali ma bai tsira ba, bare kai da kayi mata shigar sauri.

Cikin gungunai Aminu yake fadin haba Baba, kai dai kullum kafiso na zauna ina zaman banza, mutanan nan suna matukar sonmu, ka duba kagani, shekarata nawa da gama secondary babu wanda ya taba daukar ko keke ya bani.

Amma ina shiga harkar siyasa gashi yanzu ina da Adedeta tawa ta kaina, idan basa sona taya zasu bani kyautar Adedeta? Ina ci da ita, nayi sutura da ita kuma ina taimakon ‘yan uwana hada ku kanku.

Ko dauke maku nauyin ciyar dani ai abun a gode mani ne. Ai babu abinda zance da siyasa sai godiya domin ta gama biyana, kuma ashirye nake na bada dukkan karfina domin Mai Kano yaci wannan zabe.

Kawai Baba kucigaba dayi mana addu’a, dole sai mun wahala sannan zamu samu, shiyasa Allah beyi mutane dai dai ba, yayi mai kudi yayi talaka domin asamu rayuwar ta tafi dai dai.

Da yaso sai yayi mu duka masu kudi ko talakawa, kaga babu wanda zaiyima wani aiki, amma saboda rayuwar ta tafi dai dai sai ya bambanta. Tunda Allah yasa abincina yana karkashinsu kawai kucigaba da yimani addu’a.

Cikin kuka Mamarsu tace dan Allah Aminu kada ka fita da wannan Takobin, nasha fada maka duk lokacin da wani ya bata maka rai kada ka dauki hukunci alokacin, domin shedan yana tare dame fushi.

Kadubi kannanka basuda wani babba sai kai, idan suka rasamu kaine zaka kula dasu gashi kai kuma ka jefa kanka cikin fitina, banaso kaje kajawo mana abinda zamu shiga ukku.

Murmushi yayi ya daga labule ya wurga takobin cikin daki yana fadin shikenan Mama na mayar, amma wallahi ya sake yage mana poster sai naci Uwarsa. Juyawa yayi ya fita yana tafiyar kauraye.

Ajiyar zuciya Babanshi yasaki yana mai cike da tausayin Dansa. Mama tace kayi hakuri maigida, addu’a zamu cigaba dayi masa wata rana zai gane gaskiya, amma tabbas Aminu ya jefa kansa cikin rayuwa mai wahala.

Domin dabar siyasa ba abun so bace, ‘Ya’yansu suna can kasashen waje suna karatu cikin jin dadi namu Yaran suna nan suna masu bauta, ka duba irin maganganun da Aminu yayi yanzu masu cike da hikima amma ace yakasa tsayawa ya nemi na kansa sai ya dogara da ‘yan siyasa.

Baba yace haka ne, nima ina tausayinsa domin Aminu yaro ne mai hankali, ga ilimi amma tun bayan shigarsa wannan harkar ta siyasa komai nasa ya canza, sun lalata mani yaro, babban abinda yake damuna yanda yake shaye shaye.

Kinsan kuma shaye shaye babu abinda bayasa mutum. Amma bakomai, akwai Allah, zamu cigaba da kai kukanmu wajensa nasan wata rana Aminu da kansa zai gane illar dabar siyasa. Allah ya shiryasa. Tace amin.

 Page  10 to15

Fada sosai akeyi tsakanin su Aminu da abokan fadansu, da kyar wasu magidanta da suka fito daga masallaci suka raba fadan, shima saboda akwai Limamin masallaci aciki kuma Aminu yana jin nauyinsa shiyasa ya kyale wancan.

Liman yace haba Aminullah, taya da girmanka zaka biyema kannanka kuna fada? Da gani babu tambaya duk cikinsu kaine babba. Aminu yace Malan poster din dan jam iyarmu suka cire fa. Bala yace karya yake Malan mune muka fara sa tamu shine abokansa suka cire.

Aminu yace zanci Uwarka wallahi Bala. Liman yace wa iyazubillah, agabana Aminu kake wannan zagin haka? Dukar da kai Aminu yayi yana shafa kai. Liman yace dan Allah duk ku tsaya.

Na dauka ma akan wani abu mai muhimmanci ne kuke fada, ashe akan mutanan da suka maidaku tamkar bayi kukeyi. Bakuda wani muhimmanci awajensu sai lokacin zabe ya gabato, da ace zaku nemesu kafin zabe ko bayan zabe akwai wanda zaice bema sanku ba.

Ayanzu duk lokacin da kukaso ganinsu basa maku wahala, babu wani shamaki atsakaninku dasu, domin sune suke bukatarku yanzu. Da zarar sunci zabe sai kuyi wata kuna faman yanda za’ayi ku gansu amma ya gagara.

Ashe MATASA bazaku farka daga baccin asarar da kukeyi ba? Sai yaushe ne zaku gane matsayinku a wajen ‘yan siyasa? Shikenan kunfi so rayuwarku ta tsaya a haka ba tare da kun nemi na kanku kun tara Iyali ba? Haba MATASANMU.

kune fa al-ummar da muke alfahari da ita ayau ko gobe. Idan kuka lalace bamuda sauran wani sa rai da muke dashi akan ‘Ya’yanmu masu tasowa nan gaba. Ya kamata kuyima kanku fada.

Kusani duniyar tafiya take, wallahi akwai ranar da zakuyi kuka da idanunku matukar baku gyara kuskuren da kuke shirin aikatawa ba. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa acikin arba’una hadith.

Kuci ribar kuruciyar ku tun kafin tsufa yazo maku. Kuci ribar lafiyarku tun kafin mutuwa tazo maku. Ashe wannan hadisin be isheku darasi ba? Mude amatsayin mu na manyan unguwar nan bazamu gaji da fada maku gaskiya ba.

Ko baku dauketa yanzu ba wata rana zaku dauketa a lokacin da kila mu bama raye. Dago kai su Bala sukayi suna wani rangaji, hannu suka buga irin na kauraye suna fadin cau cau Malan, Allah yaja da ranka.

Mungode da wannan wa’azi, Allah yayi maka sakamako da matsayin gwamnan garin nan  ko ba komai munsan MATASA zasuji dadi. Juyawa sukayi suka tafi Bala yana nuna Aminu da yatsa.

Mutuwar tsaye Liman yayi jin shakiyancin dasu Bala sukayi masa. Girgiza kai yayi yana fadin Allah ya shirya. Hannu Aminu ya mika abokinsa ya bashi sandarsa suka wuce suna fadin mungode Malan.

Daya daga cikin mutanan da suke tare da Liman yace lallai wadan nan MATASA sunyi nisa basa jin kira, a tunanina ko kafiri akayima irin wannan nasiha dole jikinsa yayi sanyi, amma kaga ko ajikinsu.

Liman yace ba komai bane yasa bazasu fahimce mu ba sai Kwayar da take fada masu karya. Wannan shine illar shaye shaye. Bazamu gaji da yimasu addu’a ba domin irinsu ba’a masu mugun fata.

Koba komai ‘Ya’yanmu suna cudanya dasu, wata rana dole tare zamu barsu, idan mu kayi masu mugun baki akan ‘Ya’yanmu zai kare. Allah ya shige mana gaba amma MATASANMU suna cikin wani yanayi, ‘Yan siyasa sun riga da sun bata manasu.

Sune suke kashe mana MATASA. Sukace amin Malan, Allah yayi mana jagora. Yace amin.

Su Bala da Aminu kenan MATASAN unguwar Burget, sam basa jituwa saboda siyasa data hadasu kowa da jam iyar da yake bi, dama kuma basa zama waje daya, gaba dayansu suna da ra’ayin siyasa.

Yanda suke son siyasa tamkar rayuwarsu, duk lokacin da akace zabe ya matso basuda sauran zama, da su ake fadi tashin duk wani zabe da za’ayi. Gaba daya unguwar sune manyan kaurayen ‘yan siyasa.

Ko kudi aka kawo sune masu rabama sauran kaurayensu. Iyayen Aminu kullum cikin damuwa suke da halin da Dansu yake ciki, kafin Aminu ya fada harkar siyasa mutum ne mai ilimi da neman na kai.

Shigarsa harkar siyasa yasa zuciyarsa ta mutu akan abashi, cikin lokaci kankani ya fara shaye shaye domin bada kudinsa yake siya ba. Duk lokacin da zabe ya matso duk wasu kayan cakewa ana raba masu.

Sosai suke kokari akan duk wani wanda yafito takara matukar a jam iyarsu yake, suna kasawa su tsare a duk wani zabe da za’ayi. Shiyasa duk wanda yazo wajensu yake sakar masu kudi domin ansan yanda suke jajircewa a rumfarsu.

Wannan shine labarin Aminu da Bala.

***** *****

Zaune su Salman suke asaman wasu kujeru da suke karkashin wata bishiya suna jiran malamin da suke dashi yazo. Kamal ne yace wai Salman jiya ka gama downloading wannan film din kuwa? Tsaki Salman yayi yana fadin ai jiya Dady yaso ya cafkeni.

Dariya sukasa Nura yace garin ya kabar kofar dakin ka abude? Salman yace wallahi kiwuya kawai ta hanani rufewa, sai da na kwanta na fara kallo na tuna ban kulle dakin ba, ganin dare yayi yasa na share ban rufe ba nasan babu wanda zai shigo mani daki.

Dama Saddika ce sarkin sa ido kuma jiya da wuri ta kwanta. Kawai ina kwance na fara shiga yanayi sai jin motsin Dady nayi har ya bude kofa, a sukwane nayi wurgi da wayar. Allah ya soni ba kofa na bama baya ba da sai yaga abinda nake kallo.

Jabir yace lallai zanso na ganka ajiya. Salman yace da ka ga mazurai, lokaci guda rashin gaskiya ya bayyana a fuskata, da kyar na samu na kwaci kaina. Yana tafiya na sama kofar key.

Dariya suka sa Kamal yace aini jiya network ne ya bani matsala, inaji ina gani sai dai na hakura na kwanta, gashi banida sauran films a wayata kunsan dana kalla nake gogewa saboda gudun  bacin rana.

Haka nabar wayar Data a kunne bacci ya daukeni, yau har jam’i sai da nasamu saboda dawuri nayi bacci, bayan na dawo daga masallaci na duba naga yagama, gashi muna da lecture din safe haka na hakura nashiga wanka ban kalla ba.

Nura yace lallai su Kamal yau anyi abun kirki, nasan Abba ma sai yayi mamakin zuwanka sallar asuba. Kamal yace ai dai gara ni, kaida sai rana ta fito kake sallar fa. Salman yace mude kunna mana mufara gani kafin Malan ya karaso.

Jabir yace a’a Salman, kasanfa wannan kallon yana bukatar natsuwa, kada mushiga cikin class muna rangaji. Kamal yace kowa saiya zauna kusa da budurwarsa ai. Dariya suka sa Kamal ya kunna masu film suka fara kallo.

Gaba dayansu suka nutsu suna kallo, sauran ‘yan course dinsu da yawa sun san abinda suke kallo dan tun suna 2 hundred level suka fara wannan harka. Su hudu ne a group dinsu gasu mayun mata ne.

Biyu daga cikinsu a wajen makaranta suka kama haya saboda ba ‘yan Kano bane, Kamal da Salman kuma agidan Iyayensu suke da zama. Duk lokacin da sukaso lalatarsu agidansu Jabir suke kai ‘yan matansu.

Kowannan su baya rasa budurwa 4 ko 5. Salman shine Oga acikinsu, son matanshi yayi yawa be dauki taba mace abakin komai ba, gashi yana da kyau ga mota yana ja shiyasa duk macen daya taya bata wuceshi.

Sosai suka shagala da kallon film acikin wayar Kamal hankalinsu yana kan wayar duk wanda yagansu sai ya dauka wani abu mai muhimmanci suke kallo saboda yanda suka nutsu kamar masu daukar darasi.

Sam basu lura da shigewar sauran dalibai cikin class ba, tsaye Malaminsu yake abayansu yana kallon abinda suke gani, cike da bacin rai ya daka masu tsawa. A firgice suka mike wayar ta fadi kasa.

Gaba dayansu hankalinsu atashe yake ganin yanda fuskar Malamin ta koma saboda bacin rai, a hankali Jabir yasa kafa ya jawo wayar da take kasa ganin idanuwan Malamin suna kanta. Hannu yasa ya dauka yayi saurin kashewa. 

Cikin daurewar fuska Malamin yace idan mungama lecture ku sameni a office dan yanzu na makara. Bai tsaya jin mai zasuce ba ya shige class.

 Tsaki Salman yaja yana fadin Malamin nan fa yanaso ya samana ido, ina tunanin ya manta cewar nan ba Secondary bace. Muje idan ya ga dama yasa akoremu idan zai iya, dadin abun ma beda wata hujja.

 Page  15 to20

Malamin yana fita daga ajinsu kowa ya fito, su Salman suka fito tare da bin bayansa. Salman! Juyowa yayi fuskarshi dauke da murmushi dan yasan muryar wacece. Matsowa tayi fuskarta dauke da damuwa tana fadin yau kuma ko magana bazakayi mani ba? Matsowa yayi kusa da ita yana murmushi.

Harararshi tayi tana fadin ai tun dazu da kuka shigo naga alamar damuwa a fuskarka, shikenan kuma sai ka sauke haushin akaina, tunda nashigo nake nemanka saboda yau na kusa makara.

Murmushi yayi yana fadin kiyi hakuri Salma, wallahi wannan Malamin ne yakeso yashiga gonarmu, yanzu haka office dinsa zamuje shiyasa kika ga ban nemeki ba, kinsan halin lecturer’s din nan.

Babu wuysa sai su jama mutum sharri musamman da suke ganin muna a final year. Shine yace mu samesa a office idan ya gama lecture, idan bamuje da wuri ba sharrin da yakeso yayi mana sai ya samu mafaka.

Salma tace to me kukayi masa? Yatsina fuska Salman yayi yana fadin kawai dan ya iskemu muna kallo sauran studen sun shiga class da suka hango zuwansa mu kuma bamu tashi ba shine yace yana nemanmu.

Salma tace ko dai ba abun arziki kuke kallo ba? Murmushi yayi yana shafa fuska yace kema kin yarda da abinda mutane suke fada akanmu kenan? Girgiza kai tayi tana murmushi tace ni na isa na kasa yarda da abun sona.

Kawai wasa nake maka. Salman yace ai na dauka kema baki yarda dani bane. Salma tace dari bisa dari na yarda da kai, domin ni sheda ce, da ace kana aikata wani abu marar kyau akaina zaka fara gwadawa domin ba yau muke tare da kai ba.

Murmushin gefen baki Salman yayi yana fadin shiyasa nake kara sonki, na kosa mugama makarantar nan asa mana rana dan bazan iya jiran sai kunyi service ba. Kamal ne ya karaso wajen yana fadin to sarakan soyayya, sai kataho mutafi kafin Malan ya gaji da jiranmu.

Salma tace kai Kamal, kai dai kullum burinka ka raba masoya. Dariya Kamal yayi yana fadin yanzu kam zaki fadi haka, ada da bakida dan gaban goshi sai ni ai bazaki fadi haka ba, bayan na gama gyaro maki komai yanzu kuma nine mai raba masoya ko? Salman yace to sarkin tone tone.

Salma bara muje idan kuka fito zan kiraki. Murmushi tayi ta rausayar da kai gefe guda tana kallonshi tace shikenan sai kadawo. Kamal yace muma da ba’ace mana sai mun dawo ba zamu dawo. Dariya Salman yayi yaja hannunsa suka tafi.

Tsaye Salma tayi awajen tana bin bayan Salman da kallo fuskarta dauke da murmushi.

 Salma kenan, course mate din Salman ce. Itama ‘yar Kano ce, a unguwar Tarauni suke da zama ita da Iyayenta.

Ita daya Allah ya basu, mahaifinta shine sakataren gidan gwamna, yana da kudi, suna matukar son Salma, motar da take hawa kadai abun kallo ce, idan ka ganta sai kace itace diyar gwamna yanda take shiga.

Mahaifiyarta ma’aikaciyar asibiti ce babba ce sosai, suna matukar kashe mata kudi. Salma kyakkyawace gashi duk kudin da iyayenta suke sakar mata Allah besa ta lalata rayuwarta ba.

Tana da tarbiya sosai, gata da ilimin addini, sam bata da dagin kai, kuma duk cikin kawayenta tafisu kudi dan ita bata son kawance da ‘ya’yan masu kudi. Babbar kawarta mai suna Zarah ‘yar Katsina ce.

Tunda ta lura bata da wani hali yasa ta kulla kawance da ita, kuma ganin Zarah ta iya rike matsayinta yasa Salma ta kara sonta, shiyasa abubuwa da dama ita take masu, domin Zarah bata taba daga baki ta roki Salma wani abu.

Wannan hali na Zarah ya kara sa Salma ta so ta. Hatta da Momynta tasan da zaman Zarah. Tun lokacin da ta fara makaranta ta dora idonta akan Salman Allah ya dasa mata kaunarsa.

Gashi sunansu yazo kusan daya, tun daga ranar Salma take dakon soyayyar Salman azuciyarta,Zarah kadai tasan irin son da take ma Salman, kullum cikin bata shawara take akan yanda zasu bulloma al’amarin.

Da haka har suka kammala aji daya, shiko Salman bema san wainar da take toyawa ba yana can kan ‘yan matansa. Bayan dawowarsu aji biyu ne Zarah tayi kokarin neman abokin Salman wato Kamal suka fara mutunci.

Da haka Salma ta samu ya hadata da Salman, abu yazo ga ma iya, shima yana ganinta yaji tayi masa, dama dalilin dayasa baya kulata saboda yaga kamar zatayi wulakanci shiyasa koda ya fara ganinta azuciyarsa yaji batayi masa ba.

Wannan dalilin ne yasa duk son matanshi bai kulata ba. Amma yanzu data kawo kanta lokaci guda shima ya kamu da sonta. Duk cikin ‘yan matansa Salma kadai yake jin nauyinta, duk hanyar da zaibi yaga ya boye mata kada ta gano yana neman wata yana bi.

Haka zalika Salma tana matukar masa kwarjini, ko hannunta Salman bai taba rikewa ba sai dai bisa kuskure, har mamakinta yakeyi dan yasan yanda yaran masu kudi suke. Haka zalika duk wani abu da yake aikatawa marar kyau yana kokarin boye mata.

Shiyasa sam baya barin wani film na banza awayarsa. Agidansu Salma kowa yasan da zaman Salman, hatta da masu aikinsu sun sanshi domin yana zuwa fira. Agidansu ma kowa yasan da zaman Salma, kuma kowa yasan itace yariinyar da yakeso ya aura.

Haka suke gudanar da soyayarsu babu wanda besan Salma da Salman ba, sam Salma bata iya boye soyayyar Salman ko agaban waye matukar ta gansa sai taje garesa inde acikin course mate dinsu ne.

Mutane da yawa suna kawo mata gulmarsa amma sam taki basu kofar da zasu samu nasarar rabasu, kullum Zarah ce take fada mata akan kada ta yarda da maganar duk wacce zata kawo mata gulma akan Salman.

Shiyasa Salman ko zaije wajen budurwarsa baya taba zuwa idan Salma tana cikin makaranta, shiyasa kullum sai dare yake komawa gida saboda sai ya tsaya fira da dare bayan sun rabu da Salma.

Ajiyar zuciya Salma ta saki jin an dafata. Juyowa tayi tana murmushi dan tasan baya wuce Zarah. Itace kuwa. Girgiza kai Zarah tayi tana fadin ai sai kizo mutafi tunda ya bacema ganinki. Dariya Salma tayi tace kai Zarah, wayace maki Salman nake kallo? Zarah tace fadama wata bani ba.

Allah dai ya nuna mana ranar aurenku kowa ya huta da wannan rashin kunyar taku. Salma tace amin, abin haushinma first semister muke kuma ko rabi bamuyi ba bare musa ran mun kusa gamawa. Zarah tace awajen Allah babu wuya ai.

Tun muna level 2 kuke tare gashi har munzo karshe gangara kawai ya rage ai kuwa aski yazo gaban goshi. Muje kafin yadawo to. Murmushi Salma tayi tace muje.

Tsaye suke a office din Malan Jamil yana zaune shida abokinsa shima lecturer ne anan. Malan Jamil yace magana nake maku, yanzu kuna ganin wannan abun da kukeyi abun burgewa ne? Abun ma ya wuce kuje cikin dakunanku ku kalla sai kunshigo cikin makaranta kuna kallo.

Wannan wace irin jarabace haka? Idan aure kukeso  meyasa bazaku fadama Iyayenku ba? Wannan abun da kuke ganin kamar wata burgewace ko wayewa  wallahi kuna halakar da kanku ne.

Mezakuji idan kuka kalli film din batsa? Babu inda zai kaiku sai ga halaka, kuma duk wanda ya kasance yana kallon irin wannan film din wallahi aikata Zina bazai mashi wahala ba. Allah yace kada ku kusanci Zina.

Wannan abun da kukeyi shine mataki na farko da zai kaiku ga aikata Zina. Kawai turawa sun lalata ku suna daukar kansu suna dorawa a yanar gizo domin su halakar da al-ummar musulmai. Kullum burinsu taya zasu bullo da wani abu da zai shagaltar da mutane zuwa ga halaka.

Domin sun san sudin halakakku ne, shiyasa suke neman abokan tafiya. Shedan kuma yana nan kullum yana yawo a cikin jininmu domin yasamu wanda zai dulmiyar. Idan baku sani ba wallahi duk wanda ya kasance yana kallon batsa da idanuwansa ko tsufa yayi bazai tsufa da idanuwansa ba.

Haka zalika duk wanda ya maida Qur’ani abokin tarayyarsa ko tsufa yayi idanuwansa suna nan garau. Kada ku dauki abinda nake fada maku da wata manufa. Nasan nan makarantar ‘yanci ce.

Da ace a Secondary ne na kamaku kuna aikata haka sai nayi maku bulala kuma sai naga Iyayen ko wanne daga cikinku. Amma sanin yanzu kun mallaki hankalinku yasa tsakanin mu da ku nasiha ce.

Idan kuka gyara kanku, idan kuka bata shima kanku domin wata rana kune zakuyi kuka da irin rayuwar da kuka zabama kanku. Fuska adaure Salman yace Malan bafa abinda kake tunani bane muke kallo.

Wani American film ne muke kallo lokacin da kazo shine fa aka nuno wannan abun daka gani amma bawai duka film din haka yake ba, kaima kasan yanda American film yake. Kamal yace Malan kilama ka ganshi sunansa Ruler master of the mask.

Murmushi abokin Malan Jamil yayi jin wani rainin hankali wai American film. Malan Jamil yace koma menene nide na fada maku iya gaskiyata. Allah ya kyauta shikenan kuje. Jabir yace mungode.

Suna fita abokin Malan yace sun ma raina mana hankali, koda yake idan mutum beda gaskiya kowace karya tazo masa fadarta yakeyi. Wannan film din da suka fada fa ba American film bane, Korean film ne. Malan Jamil yace wallahi karya suke blue film ne suke kallo na gansu fa. Kai dai Allah ya kyauta. Yace amin.

Dariya sukeyi hada rike ciki. Nura yace wallahi kai Kamal dan rainin wayau ne, dadina da kai ko karyar baka iya ba, da ka barshi kamar yanda Salman ya fada da yafi, shi yace American film, kai kuma ka fado Korean film.

Dafe baki Kamal yayi yana fadin wallahi na manta, gaba daya idea ta daukewa tayi. Salman yace idan ma hausa film ya fada masu ai su suka ja, taya zasu tsaremu kamar wasu ‘Ya’yansu.

Koma mai muke kallo ai munji zamu iya ne, da ace an kama mu muna shaye shaye ko muna fyade ko sata ai gara muzauna mu ragema kanmu zafi. Duk iskancina ai ban taba aikata Zina ba, dan romancinga de da mace munayi agida amma bama aikata babban laifin.

Kawai kuma sai yarika fada mana wata maganar banza. Jabir yace shima karya yake yace baya kallo, dazu idanuwansa kuri akan wayar har wani rike wando yakeyi yana gyara tsayuwa. Maganar ma da kyar tafito muryarsa sai rawa take da alama yashiga yanayi.

Dariya suka kwashe da ita Nura yana fadin baka da kyau Jabir. Wayar Salman ce tayi kara yana dagawa yace Salma ganinan zuwa. Kashe wayar yayi yana fadin ni natafi afaranta mani rai kowa yatafi wajen budurwarsa. Kamal yace sai kadawo.

**** *****

Inna ce tafito daga cikin gida sanye da mayafi. Cak ta tsaya tana kallon ikon Allah, Sardauna ne abakin kofar dakinsa dagashi sai wando da karamar riga ya yafa towel akafadarsa.

Gefensa Jamila ce fuskarta dauke da damuwa. Tafi Inna tayi tana fadin Marusanda mai zan gani haka? Saurin juyowa yayi yana kallon Inna. Juyawa yayi yana fadin kinga abinda nake fada maki ko Jamila.

Kawai saiki kama zomani daki tunda safe, ko baki shiga ba duk wanda ya ganmu zai dauka daga ciki muka fito. Jamila tace ai dole nazo, haba Sardauna, yau kwananka nawa bakazo gidanmu ba? Ko wayarka na kira baka dauka saboda kaga ina sonka shiyasa kake mani haka.

‘Yan mata nawa wadan da nafi komai kake cewa kanaso amma ni mai yasa bazaka soni ba? Hannu yasa ya dafe goshinsa yana fadin dan Allah kije anjima zanzo. Jamila tace sai ka rantse. Dariya ma tabashi yace insha Allah zanzo.

Juyawa tayi ta tafi saboda kunya ko kallon wajen da Inna take batayi ba. Rufe ido daya Sardauna yayi ya juyo yana kallon ko Inna tana nan. Harara ta buga mashi ta koma ciki. Gumtse dariya yayi ya rufo dakinsa yana fadin yau nashiga ukku awajen Inna, dama ya lafiyar giwa takare.

Allah ya soni ba Malan bane ya ganmu ba, da cewa zai yi daga dakin ma ta fito. Yana gama rufe dakin yashige cikin gida.

 Page  20 to25

Magana fa nake maka Marusanda. Dago kai Sardauna yayi yana fadin Inna kema kinsan halin Jamila, wallahi ba dakina tashiga ba, ina shirin shiga wanka kawai naji bugun kofa na dauka ma kece ina fitowa naganta.

Haba Inna taya zata shigar mani daki, ko Malan da yake fadin ina barin ‘yan mata suna shigar mani daki kawai zargine yakeyi, so daya fa da wata mai awara tashiga amsar kudinta ta zo fitowa suka hadu da Malan shikenan yake fadin haka.

Ni ko mace zan kawo daki mezanyi da mai talla ai ajina ya wucesu wallahi. Inna tace koma me akace kayi Dan Ghana ai kai ka jama kanka, yaro kamar wanda shedan yayima fitsari akai. Idonka idon mace.

Dariya Sardauna yayi yana fadin yaude Inna kema kin dana, kuma da kika fada sai naji sunan yafi dadi abakinki. Duka ta kai masa tana fadin tunda ka tara sunaye da yawa ai dole wata rana na manta na kira wani sunan.

Dan Allah Sardauna kayima kanka fada, ni bance kana neman mata ba, amma shekarunka sun wuce karika zaman gida ana baka kudin kashewa, kana fa da karatunka ko ‘yar Primary din nan baza kaje adauke ka aiki ba kafin na gwamnatin yasamu.

Sardauna yace haba dai Teaching Inna? Allah ya kyauta wallahi naje ina rike alli, nifa banida wata matsala arayuwata, matukar ina tare da ku komai yayi dai dai, na tashi na ganku na fita majalissa shikenan yayi mani dai dai.

Inna tace shikenan mu kuma bazamu so ganin Danka ba? Shekarunka fa sun kai 26 amma kake fadin baka da wata damuwa. Sardauna yace idan na kai 30 zan zama babba ai. Murmushi tayi tana girgiza kai tace Allah ya shirya mani kai Marusanda.

Yace Sardauna dai. Dariya tayi tana fadin tashi kaje ga abincinka can adaki kaci a kula ma na samaka kada ya huce. Kwanciya yayi saman kafarta yana fadin Allah Inna kaina ciwo yake mani.

Hannu ta dora saman kansa tana fadin ko wannan uwar sumar da kake bari akanka ai ta isa ta samaka ciwon kai. Dan Allah kaje kayi aski. Turo baki yayi yana fadin Inna kinsan kudin dana kashema wannan gashin kuwa? Ai duk ranar danayi aski bazan kara fita ba har sai ya taru.

Inna tace naji tashi kaci abinci kasha magani tunda kazama mace, mutum kullum yana gida idan anga ka fita to yamma tayi idan katafi kuma sai magriba kana fita kuma sai da safe. Sardauna yace to Inna kin fiso narika barinki ke daya acikin gida? Inna tace nafiso dai karika bin Malan kasuwa.

Saurin mikewa yayi yana fadin ina abincin yake? Dariya tayi tana fadin an fado makiyar ka ko, yana daki jeka dauka tunda baka son maganar kasuwa, nima daga yau bazan kara baka kudina ba. Dariya yayi yana fadin wallahi Innata bazaki iya hanani ba.

Dana sa maki kuka zaki dauko ki bani. Murmushi tayi tana girgiza kai. Tana matukar son Umar, duk da bashida sana’a sam kashe kudi be dameshi ba, matukar zai samu na kati shikenan.

Babban farin cikinta da baya shaye shaye, kuma baya da wasa da sallah, gashi yana matukar sonta, wannan dalilin ne yasa bata iya hanashi kudi matukar ya tambayeta, dan shima kome ya samo awaje sai ya kawo mata.

***** *****

Da gudu Amal ta fado dakin Mamy tana haki, saurin kallonta Mamy da Abdulhakim sukayi dan ta basu tsoro. Bayan Mamy ta boye tana fadin wallahi Yaya ne zai dokeni. Abdulhakim yace ai gara ya dokeki.

Ni nasan banna kikayi masa. Amal tace ba fa da gangan nayi ba, nazo watsar da ruwan datti na watsa masa a takalmin kwallonsa kuma yafito kenan zaisa yatafi kwallo na watsa masa gashi ya ganni shine fa ya biyoni da gudu.

Mamy tace lallai kam da gangan kikayi, keda kike aiki a kitchen meya kai ki zubar da ruwan datti awaje duk fadin kitchen be isheki ki zubar ba? Zatayi magana Abdallah yashigo yana huci.

Tashi tsaye Mamy tayi tana fadin dakata Abdallah. Kallonta yayi da idanuwansa da sukayi ja yana fadin wallahi Mamy saina cima Amal, kallifa yanda ta bata mani takalmana kuma tana sane tayi saboda bata son naje kwallo.

Mamy tace to yanzu Amal din zakayima kuka? Nima fadan da nake mata kenan, haba Abdallah, kaine fa babba meyasa kakeson dukanta ai sai raini yashiga tsakaninku. Ai bejira Mamy ta gama magana ba ya cafko hannun Amal.

Ihu Amal tasa tana fadin dan Allah Yaya kayi hakuri wallahi bazan kara ba, kokarin kwaceta Mamy takeyi Abdulhakim yace dan Allah Mamy kibarsa yadan koya mata hankali gobe idan akace ta kalli kayansa baza tayi ba.

Haka Abdallah yaja ta har waje, belt din daya aje afalo ya dauka yashiga zabga mata, tun tana ihu har bakinta ya mutu, sai da yayi mata duka sannan yabarta awajen. Fitowa Mamy tayi tana fadin gobe ma ki kara taba masa kaya.

Yarinya kamar mai aljannu, ke ko gajiya da dukan Abdallah bakiyi dole sai kin taba masa kaya, idan kina da zuciya ko inda kayansa suke bazaki kara kallo ba. Cikin kuka Amal tace kuma wallahi sai nasa Abbah ya kwashe kayan kallonsa.

Abdulhakim yace ai sai kisa tunda ke kadai kike da Abban, wallahi Amal kishiga hankalinki dani, wai yaushe zakiyi hankali ne? Kodan kinga ana cemaki auta? Shiru tayi batace komai ba dan tana shakkar Abdulhakim duk da yana sakonta.

Tsaki yayi ya wuce yana fadin ba Yaya ba koni na sake ganin kin taba masa kaya wallahi sai kin raina kanki. Bayan ya fita Mamy ta zauna tana fadin haka kikeso ko? Yanzu ke ko sha’awar kawayenki bakiyi yanda sukeyi da ‘yan uwansu? To wallahi idan baki gyara halinki ba ‘yan uwanki zasu tsaneki.

Amal tace Mamy kiyi hakuri bazan sake ba. Mamy tace bani zaki bama hakuri ba su zaki bamawa. Kullum ina fada maki ku hada kanku, idan bakiyima Yayyanki biyayya ba wa zakiyi mawa? Kefe macece, wata rana akaron banza zakije inda zakiyima wadanda basu kai yayunki matsayi ba biyayyar dole.

Domin wata rana gidan mijinki zaki tafi, idan bama raye wadannan da kika raina sune gatanki, dangin miji ba ko wace mace take sa’ar samun masu kirki ba. Amal tace Allah na dai na. Mamy tace da kyau, sai ki tashi ki karasa girkin da kikeyi.

**** *****

Salman yana kwance akan kujera yana kallo kamar daga sama yaji Saddika tana fadin Yaya wane film kake kallo? Saurin tashi yayi ya kashe wayar yana fadin wai ke yaushe zaki girma? Bakisan kizo waje ki fara da sallama ba kawai sai naji muryarki akaina.

Turo baki tayi tana fadin na fayi sallama tunda ka toshe kunnanka ya za’ayi kajini. Murmushi yayi yace ai banji bane, zo ki bani labarin makarantarku. Zama tayi adayar kujerar tana fadin nide ka fara tura mani film din.

Salman yace Horo film ne bazaki iya ganinsa ba. Saddika tace nide inaso idan naga bazan iya kallo ba sai na goge. Dafe kansa yayi aranshi yana fadin ai fa nashiga ukku. Dagowa yayi yace to bazan tura ba shikenan.

Kafafuwanta ta fara dirawa tana fadin kuma sai na fadama Aunty Salma yawan ‘yan matanka. Dariya yayi yace haba ‘yar kanwata wasa fa nake maki ba wani film bane nake kallo wani music ne nake gani.

Saddika tace Allah ban yarda ba dana shigo na gani ba rawa kake gani ba. Salman yace to mekika gani? Saddika tace nide naga mace da namiji asaman kukera suna shirin tashi tsaye kuma kamar turawa ne.

Ido ya runtse yana fatan Allah yasa iyakar abinda ta gani kenan. Saurin bude ido yayi yana fadin sai me kika gani? Tace shikenan sai hannunka ya kare mani. Ajiyar zuciya ya saki yana fadin to ba film bane.

Ko zanyi maki karya ne? Girgiza kai tayi, yace da kyau. Kuma maganar ‘yan matana yanzu banida kowa sai Salma sauran duk gaisawa mukeyi. Saddika tace da gaske Yaya? Yace da gaske mana.

Ai yawan tara ‘yan mata da yawa bashida amfani, tunda na samu mai sona ai naji dadi, shiyasa nake fada maki kada kiyarda ki tara samari da yawa. Saddika tace ai bana tarawa. 

Yace yauwa ‘yar kanwata, anjima kishirya muje gidansu Salma. Tashi tayi tana murna tashige ciki. Wata ajiyar zuciyar ya kara saki yana fadin Allah ya kara mani, gobe ma zan kara kallo afalo.

**** ****

Zaune Bala yake acikin wata katuwar mota glass dinta gaba daya baki ne, da ka ganta kasan an zuba kudi masu yawa kafin asayeta. Wani babban mutum ne zaune agaban motar da ka gansa kasan kusoshin gwamnati ne anci anyi hanikan.

Idonshi sanye da wani bakin glass. Kallon Bala yayi yana fadin Bala ina fatan komai yana tafiya dai dai? Bala yace baka da matsala Yallabai, duk inda ya kamata mu lika poster dinka mun lika.

Sai dai muna samun wasu ‘yan hassada suna cirewa amma nayima tufkar hanci, kasan Aminu yaron Mai Kano shine abokin adawata. Yallabai yace kada kadamu dashi, Malan ya bani abinda za’a binne mu nakasa Mai Kano, kaga ni daya zan rage dan takara, daga lokacin bani da sauran damuwa sai na kwanta najira lokacin zabe.

Ai dashi suke takama, gara tun kafin zaben ya gabato mu gama dashi kada yazo ya bamu matsala dan naga mutane da yawa suna yinsa. Wata leda ya dauko ya bama Bala yana fadin dan akuya ne sabuwar haihuwa, satinsa biyu aduniya, idan dare yayi sosai kaje ka tona rami ka rufesa da ranshi.

Zakaga sakamakon aikinmu. Dariya Bala yayi yana fadin baka da kyau Maigida. Allah ya baka wannan kujera. Murmushi yayi yace amin Bala. Bandir din ‘yan dari biyar ya bashi yana fadin ga wannan karike kafin jibi.

Ka bude boot akwai wani kwali kayanku ne nasa aka siyo maku sai ka rabama yaranka ku cake domin kuji dadin aiki, duk wanda yashige maku gaba ku kawar dashi. Bala yace cau cau Maigida, shiyasa nake sonka wallahi, kasan makamar aiki.

Yallabai yace maza ka dauka kada wani yagammu tare sai nakiraka, kada fa kayi mani kuskure dan aikin bazeyi ba idan ba’ayi dai dai ba. Bala yace baka da matsala yallabai. Fita yayi ya dauki kwalin Yallabai yabar wajen.

Dariya Bala yasa yana fadin ai bazanso ka kawar da Mai kano ba, gara kucigaba da cakusawa nima zanfi samun kudi, idan kaga kai daya ne mai takara muma kyalemu zakayi. A binne dan akuya ko? Zakaga binnewa.

Idan ma bokan zai fada maka ba’ayi yanda yace ba sai dai yafada amma wallahi sai nayi kuskure. Ledar ya bude dan akuyan sai mutsu mutsu yakeyi, babu tausayi Bala ya murde masa kai ya tona rami ya rufe gawarsa yana fadin tun yanzu aiki ya lalace.

 Page  25 to30

Duk abinda Bala yakeyi su Aminu da yaransa suna labe suna kallonsa, tun daga lokacin da yashiga motar Yallabai har ya gama binne akuyar suna labe. Yana tafiya suka fito.

Murmushi Aminu yayi yana fadin mushurikan banza, ai wallahi matukar muna raye bazaku kai labari ba. Wani yace Oga kawai mu tone abinda ya binne. Aminu yace yanzu kuwa.

Suna gama tonewa suka maida kasar kamar yanda take. Aminu yace Alee dauko waccan ledar asakata ciki kaje can kasan kadar Rimin kebe ka jefata ciki. Amsa yayi suka bar wajen cike da farin ciki.

**** ****

Zaune Mamy take dasu Abdulhakim Amal tana gefe, Abbah ne yace wai har yanzu Abdallah bai shigo gida ba? Mamy tace nima nayi mamakin rashin dawowarsa da wuri gashi har 8:30 tayi. Abdulhakim yace kila yana can wajen abokansa.

Sallamar da sukaji ce tasa sukayi shiru, tashi Abdulhakim yayi ya nufi kofa yana amsa sallamar. Abokin Abdallah ya gani, hannu ya mika masa suka gaisa yana fadin Kabir ina Yayan kuma? Wanda aka kira da Kabir yace wallahi wata ‘yar matsala aka samu shine nazo na fadama Abbah.

Abdulhakim yace shigo Abban yana ciki ai. Bayan ya gama gaishesu Abbah yace lafiya dai ina abokin naka? Dukar da kai Kabir yayi yana fadin wallahi Abbah dazu ne bayan mun gama kwallo lokacin an fara kiran magriba ma.

Abdallah yana cire takalman kwallonsa shine wani wanda ba dana gidanmu ba yazo yana mana dariya saboda yau mu akaci. Tun Abdallah bai kulasa ba har sai da ya kaisa bango. Shine fa suka hau fada.

Muna kokarin rabasu tsautsayi yasa Abdallah ya buga masa wani karfe akai shine ya fadi asume shine fa sauran abokansa sukaje suka kira ‘yan sanda shine aka kama Abdallah shi kuma aka nufi asibiti dashi.

Tun dazu ma muna asibitin shiyasa banzo na fada da wuri ba, sai yanzu daya farfado likita yace babu wata damuwa zuwa gobe da safe za’a sallamesa shine nace bara nazo na fada saboda akwai kudaden da za’a biya.

Salati Mamy ta farayi hawaye suna zuba daga idonta. Abbah kuwa shiru yayi saboda tsabar takaici, wannan shine kusan karo na 3 da aka kai Abdallah police station akan rigimar kwallo.

Abdulhakim yace Abbah dan Allah muje a fiddo Yaya kasan ‘yan sandan nan basu da imani wallahi dukansa zasuyi. Amal tace Abbah dan Allah kuje a fiddosa nasan ko abinci bazasu bashi ba.

Tsaki Abbah yayi yana fadin wallahi bazan je cirosa ba, gara ya kwana yaji yanda akeji a police station, dama saboda yaga bai taba kwana ba shiyasa yake jawo mana fitina kala kala.

Ni tunda nake wata rigima ta taba hadani da ‘yansanda bare ace wai an kaini an kulle, kawai saboda na haihu shikenan sai arika jefani cikin fitina. Ai bashi kadai na haifa ba, haka yaga sauran ‘yan uwansa sunayi.

Shine babba agidan nan kuma shine wanda yafi kowa jawo mani fitina. Tun Abdallah yana karami nake fama da wannan bakar zuciyar tasa, yanzu ma ya mallaki hankalinsa bazan huta ba.

To ai shekarunsa sun kai ya dauki kowane hukunci, wallahi idan ya cigaba da kule ni zan barsa duniya ta koya masa hankali. Matsowa Mamy tayi tana kuka ta rike hannunsa tana bashi hakuri.

Sosai take kuka hakan yasa hankalin Abbah yatashi, kamota yayi yana fadin ya isa haka Mamyn Amal, kamar yanda kikeson Abdallah nima haka nake sonsa, amma dole sai mun nuna masa fushinmu wannan shine soyayyar.

Zamuje amma sai gobe, gara yasan cewar munji haushin abinda yayi hakan zaisa ya gyara kuskurensa. Yanzu bara muje can asibitin domin mu bama Iyayen yaron hakuri kuma na biya kudaden.

Jinjina kai tayi tana fadin nagode. Kallon Abdulhakim yayi yace muje asibitin. Suna zuwa asibitin wajen likita sukaje anan yake fada masu babu wata matsala kawai buguwace da yayi sai dan fashewar da gefen goshinsa yayi.

Abbah yace mungode yanzu ina takardar magungunan da za’a siya? Mika masa takardar yayi tare da sauran bill din da zai biya. Bayan sun fito ya bama Abdulhakim yaje yasiyo magungunan shi kuma suka nufi dakin marar lafiyar shida Kabir.

Hakuri sosai ya bama Mahaifin yaron tare da duba marar lafiyar. Mahaifin yaron yace ai bakomai Alhaji, yara ne ka haifesu baka haifi halinsu ba. Wannan kwallon jarabar haka muke fama da ita.

Ni banso ma aka sako ‘yan sanda a maganar ba, inde rigimar kwallo ce duk wanda yake da yaro ya saba jinta. Dan Allah Alhaji muje a karbo yaron. Abbah yace kada kadamu, inaso ya kwana zuwa gobe zan je can.

Gara ya san yayi laifi, amma idan yana ganin duk lokacin daya jawo rigima yana da masu tsaya masa to bazai taba hankali ba. Jinjina kai Mutumin yayi yana fadin haka ne. Allah ya kyauta gaba. Abbah yace amin na gode.

Zamu tafi gobe kafin asallameku zamu dawo. Godiya mutumin yayi masu suka tafi.

Tun Abdallah yana sa ran zuwan su Abbansa har ya fara cire rai, dan ya saba ana kawosa police station ko minti talatin baya yi Abbansa yake zuwa kuma abada belinsa. Ganin shiru babu wanda yazo yasashi lekawa yana fadin Yallabai zanyi sallah. Budeshi wani yayi ya rakashi inda zaiyi alwala.

****** ******

Sardauna ne zaune da abokansa a majalissarsu suna fira. Mubarak ne yace wai Dan Ghana ina Jamila fa? Tsaki Sardauna yayi yace zaka fara ko? Kai kullum idan baka fadi Jamila ba bakajin dadi. To ko dai sonta kakeyi nayi mata magana? Dariya sauran suka sa.

Mubarak yace haba ya za’ayi na so abun da ka so. Kawai naga yanda ta damu da kai ne shiyasa nake yawan maganarta. Sardauna yace Uban waya fada maka ina sonta? Sani yace fada masa dai Sardauna.

Mubarak yace wallahi karya kakeyi kana sonta, kawai dai kaima baka sani bane. Sardauna yace tunda kaine da zuciyata ai dole ka fadi haka, ni Jamila tamkar kanwa take awaje na. Mubarak yace shiyasa rannan da wani ya tsareta da magana kaje kana huci.

Dariya suka kara kawashewa da ita. Tashi Sardauna yayi yana fadin wallahi sa idonka yayi yawa, shikenan mutum bazai sa ido akan Kanwarsa ba. Mubarak yace E gaskiya dole Yaya yasa ido akan kanwarsa. Allah ya taimaka.

Hasken fitilar da suka gani ne yasa Sardauna yace sai da safenku nasan Malan ne dama tunda ban koma naci abinci ba nasan sai ya biyo sahuna, shiyasa na fiso bayan isha’i naje naci abinci kafin nafito wallahi.

Sani yace kaga Dan Autan Malan da Inna, wallahi shiyasa kake shagwabarka son ranka, yanda su Malan suke ji dakai kamar wani dan shekara 5. Sardauna yace ai sai kasa su dai na. Mubarak yace shi ya isa ma.

Wuce katafi idan ka gama zaka fito? Sardauna yace kaima kasan tunda Malan yazo da kansa ya kirani ai sai gobe kuma. Sai da safenku. Wucewa yayi ya karasa wajen Malan. Yana zuwa yace dama yanzu nake shirin shigowa gida.

Murmushi Malan yayi yana fadin naga alama, wuce muje haka kawai ka sani fitowa da dare. Sardauna yace da kayi zamanka ma yanzu zan shigo ai. Malan yace kona zauna Innarka ai bazata zauna ba.

Gida suka wuce, Malan yana fadin ina fatan kayi masu sallama dan bazaka koma ba? Sardauna yace ni na isa banyi fira daku ba na fita, gashi dare yayi ai sai da safe kawai. Da sallama suka shiga ciki. Inna ta amsa tana fadin ai nasan da ba’aje kiranka ba bayanzu zaka shigo ba.

Malan yace nan gaba ai abincin zaki rika kai masa dakinsa mu rufe gidanmu duk lokacin dayaso idan yadawo ba sai ya buga mana gida ba. Inna tace baza’ayi haka ba, nafiso yazo yaci a gabana sannan.

Malan yace naci sa’a ma dana samesa a majalissarsu, na dauka ko yana wajen Jamila. Turo baki Sardauna yayi yana fadin Inna kinga Malan shima yana cewa Jamila budurwata ce. Dariya sukasa Inna tace ko bako ne a unguwarnan matukar yayi kwana biyu ai sai ya san cewa Jamila budurwarka ce.

Sardauna yace nide Allah ba budurwata bace mezanyi da ita. Malan yace dama tunda kana tara ‘yan mata da yawa ai dole kace babu abinda zakayi da ita, kuma duk cikin ‘yan matanka tafisu kyau.

Kuma nasan ita kadai ce zata iya aurenka a yanda kake. Dariya Sardauna yayi yana fadin Malan nima fa nan gaba zanyi kudi, mata 4 ma nakeso na aura. Inna tace wallahi sai dai idan bana raye, haka kawai yanda kake da wannan sanyin halin naka ka auri mata 4 su kashe mani kai.

Dariya sosai Malan yasa ya nufi daki yana fadin Uwani ina ganin duk lokacin da Marusanda zaiyi aure bazaki barshi ya zauna agidansa ba, wannan kishi haka. Inna tace ai gaskiya na fada. Tashi ka dauko abincinka kaci. Tashi Sardauna yayi yana dariya yace aiko ni bazan zauna da kowa agidana ba, nafiso daga ni sai matana.

 Inna tace ai sai mugani, wallahi babu wacce zata maida mani kai bawa. Daki suka shige suna mata dariya jin yanda ta dage tana rantsuwa.

 Page  30 to35

Zaune Abdallah yake afalonsu kansa a kasa kwana daya har yayi zuru-zuru. Tunda Abbah ya daukosa daga police station har suka iso gida bece masa komai ba, tun amota Abdallah yasha jinin jikinsa.

Tunda yake da Abbansa ko yayi laifi baya sharesa haka, ko lokacin daya taba cirema wani dan ajinsu hakori aka kaisa police station Abbah beyi fushi dashi haka ba. Dago idanuwansa yayi wadan da suka fada saboda yunwa da rashin bacci.

Gabanshi ne ya fadi ganin yanda Abbah ya hade fuska kamar be taba dariya ba. Murya akasa yace dan Allah Abbah kayi hakuri Allah bazan kara ba. Abdulhakim ne ya sauko har kasa yana fadin dan Allah Abbah kayi hakuri ka yafema Yaya.

Amal ma saukowa tayi tana bama Abbah hakuri. Ajiyar zuciya Abbah yayi tare da kallon Abdallah, sai a lokacin yaga ramar da yayi duk da fuskarsa data kumbura. Mamy da take gefe tuni fuskarta ta jike da hawaye ganin yanda fuskar Abdallah ta kumbura gashi duk ya fada rana daya.

Gyaran murya Abbah yayi tare da kallon Abdallah yana fadin ni babu abinda zance maka domin kai ba yaro bane, kuma ina mai tabbatar maka wannan shine karo na karshe da za’a kara kama ka naje na zubar da mutuncina nayi bellin dinka.

Komai ka debo kanka, domin shekarunka sun isa ka dauki hukuncin shari’a. Haba Abdallah, kai fa ba karamin yaro bane, da ace ka maida hankali ya kamata ace kamar yanzu kana gidanka kai ma kazama mai gida.

So kake bakin cikinka ya kashe ni? Duk cikin yara na kai kadai kake bani ciwon kai, hakan yayi maka dadi ko? Matsowa Abdallah yayi yana kuka ya dora kansa saman kafar Abbah yana bashi hakuri.

Gaba daya falon sai da suka yimasa kuka, hatta da Abbah sai da idanuwansa suka cika da kwalla. Hannu Abbah yasa ya dafa kan Abdallah yana shafawa. Shiru ne yadan gifta na wani lokacin dan Abbah yanaji idan ya bude baki hawayen da yake boyewa zasu iya zubo mashi.

Abbah yace ya isa haka, na yafe maka. Amma da sharadin bazaka sake ba. Cikin sauri Abdallah yace insha Allah Abba bazan sake ba na maka alkawari. Abbah yace Allah yasa, amma sai ka rage wannan zuciyar taka.

Babban abinda yake cutar ka Abdallah shine kana da bakar zuciya, sam banji dadin yanda kwallo ta shigar maka rai ba, duk masu irin zuciyarka kwallo bata kamace su ba. Domin duk lokacin da bakuyi nasara ba dole wasu surika maku dariya.

Kaga dole zuciya ta debeka ka aikata wani abu marar kyau. Idan ka duba duk lokacin da zakayi fada da wani ba kai daya ake tono ba, duk wadan da kukayi kwallon dasu hadasu ake tono.

Amma saboda kai kana da zuciya shiyasa baka iya boye fushin ka. Kuma idan baka sani ba babu abinda shedan yakeso kamar yaga mutum yana cikin fushi. An tambayi shedan a wane lokaci ne yafi samun nasara akan ‘yan Adam.

Sai yace alokacin da mutum yake cikin fushi. Shiyasa Annabi yace a duk lokacin da kake cikin fushi idan kana tsaye to ka zauna, idan kuma a zaune kake to ka kwanta. Kuma kada kayi saurin yanke hukunci alokacin da kake cikin fushi.

Babban abinda zaisa ka rage wannan bakar zuciyar taka shine ka rungumi Qur’ani ya zama abokinka, duk lokacin da kake cikin fushi matukar ka dauki Qur’ani ka karanta natsuwa zata saukar maka.

Domin Qur’ani waraka ne, babu wanda zai karantashi ba tare da yaji sanyi acikin ransa ba matukar ka karantashi yanda yake to duk wata damuwarsa zata kau. Dole sai ka rage yawan kallace kallacen da kakeyi ka koma ga Allah Abdallah.

Kana ganin dan uwanka duk da yana makaranta karatun addini baya masa wahala, kai ne ya kamata ace kana a matsayin da yake tunda kana da lokaci, amma ka kasa tsayawa kayi abinda ya kamata.

Wajen aikin dana bude maka ma baka da lokacin zama sai dai ka dora wani awajen sai lokacin da kaga dama kake zuwa. Ina rokonka da Allah Abdallah ka gyara halinka, idan yau mutuwa ta daukemu Abdulhakim da Mamana basu da Uban daya wuce masu kai.

Idan baka gyara rayuwarka yanzu ba sai mun mutu zaka gyara? Dago kai Abdallah yayi yana goge idonshi yace insha Allah Abbah zan gyara. Mamy dan Allah ki yafe mani. Murmushi Mamy tayi tana goge idonta tace na yafe maka Abdallah.

Allah ya kara tsare mana kai, Allah ya kareka daga sharrin abokan gaba. Amal tashi ki hado masa tea ya sha. Abdulhakim kuje ya samu yayi wanka. Tashi sukayi suna murmushi.

 Murmushi Mamy tayi tana fadin har naji hankalina ya kwanta. Abbah yace ai tashin hankali beda dadi. Allah ya kara rufa mana asiri. Mamy tace amin.

**** ****

Umman Salman ce ta fito tana fadin Saddika jeki duba naga yau Salman be fito ba ko beda lectures ne. Saddika tace Umma tunda kikaga be fito ba bazai shiga school ba, da zai shiga da wuri zakiga ya shirya kodan yaje ya hadu da Aunty Salma.

Dady da yake zaune yana shan tea yace kaji ‘yar sa ido, wato kina nan kina sa masa ido badan karatu yake shiga school ba sai dan Salma ko? Dariya Umma tayi tana fadin ai idan muna da ran ta kusa zama ‘yar gida.

Wuce ki dubo manishi kilama beda lafiya. Dady yace nima bangansa a masallaci ba duk da dama baya zuwa sosai. Na rasa wannan rashin zuwan masallaci na Salman, mutum ya rika bacci kamar mace.

Kullum idan nace zan tsaya tadashi ni sai na makara, shiyasa dana farka nake kiransa awaya kafin nashiga alwala. Umma tace kila karatu ne yake hanasa kwanciya da wuri kasan shekarar karshe suke.

Dady yace Allah yasa karatun yakeyi dan kwanaki nashiga dakinsa kallo na samesa yanayi ba karatu ba. Umma tace nide nasan Salman yana karatu gaskiya. Dady yace Allah yasa to.

Saddika tana yin sallama akofar dakinsa taji shiru, sau biyu tana sallama, jin shiru yasa ta tura kofar, karar ruwan dataji ne yasa ta gane yana wanka. Har zata fita idonta ya fada akan wayarsa.

Murmushi tayi tana fadin yanzu haka Yaya yana da films baya son bani ne, cikin sanda ta dauki wayarsa tayi waje. A falo ta wuce su Umna tana fadin wanka yakeyi Umma. Dakinta ta shige ta dauki wayarta tana fadin Allah yasa besa ta key ba.

Cikin sa’a ta iske wayar bata shiga key ba dan yana cikin kallo Salma tayi masa waya yazo tana son ganinsa hakan yasa ya shiga wanka yasa pause a kallon. Play Saddika tasa akan film din data iske yana kallo.

Hannu tasa ta rufe baki ganin badalar da take cikin wayar Salman. Kanta taji yayi mata nauyi ganin irin abinda Dan uwanta yake kallo, ta dauka film ne yake kalla nan ne kawai aka nuno wannan badalar, forwarding tayi dan taga abinda yake gaba.

Har ta kai karshe duk abu daya akeyi, fita tayi daga film din tashiga wani data gani na kusa dashi, shima dai abu daya akeyi, sai da tashiga har 3 duk abu daya akeyi. Hawaye ne kawai suke zubo mata.

Wace irin rayuwa Yayanta yakeyi haka? Blue film a wayarsa? Dama wannan dalilin ne yasa baya son bata wayarsa? Haba, shiyasa rannan data kusa kamashi duk ya daburce yana tambayarta dame dame ta gani.

Aiko bazanyi shiru Yaya ya cigaba da aikata wannan barnar ba, dole na fadama su Dady domin su dauki mataki akansa. Turo kofar da akayi ne yasata saurin kallon bakin kofar.

 Salman ta gani atsaye da ka gansa kasan a rude yake. Mutuwar tsaye yayi ganin wayarsa a hannun Saddika gashi fuskarta duk hawaye. Lokaci guda ya ga tana jifarsa da wani irin kallo alamar tuhuma. Jiki a sanyaye ya tako zuwa cikin dakin.

 Page  35 to 40

Salman yafi mintuna 5 beyi magana ba, yama rasa ta inda zai fara, da alama Saddika taga abinda yake kallo. Da kyar ya tattaro sauran karfinsa ya karasa kusa da ita yana fadin Saddika bani waya ta mana.

Idanuwa ta tsura masa ganin yana so ya nade tabarmar kunya. Zama saman gadon yayi yana fadin me akayi maki ke kuma kike kuka keda kuka baya maki wahala? Murmushin takaici tayi tare da sa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata.

Kara daure fuska yayi yana fadin magana fa nake maki, idan banida amsa bani wayata akwai inda zanje, kuma wallahi kada ki kara shigar mani daki ki dauko mani waya. Murmushi tayi mai dan sauti tace tunda akwai abinda baka so nagani ai dole zaka rika mani rowar wayar ka.

A da kome nace zanyi da wayarka ai baka hanani, amma yanzu kasan kana aikata rashin gaskiya dole zaka fadi haka. Saurin kallonta yayi fuska adaure yana zare ido yace bakida hankali Saddika? Ni kike fadama wannan maganar saboda kinga ina wasa dake ko? Saddika tace ai gaskiya na fada Yaya.

Kuma da ido na nagani ba wani ne ya fada mani ba. Hannu yasa ya fizge wayarsa yana fadin me kika gani? Mikewa tayi tana kuka tace koma me nagani idan na fada ma su Dady zakayi bayani ai.

Saurin kamo hannunta yayi tare da sassauta murya yana fadin haba ‘yar kanwata. Yanzu saboda kinga wani abu awayata marar kyau shikenan sai kirika zargin Yayanki? Bazaki sameni koma menene ki fada mani ba? Idan ma halina ne ya kamata ace kin hadani da Iyaye na? Haba Saddika.

Ya kamata kiyi bincike kafin ki yanke hukunci, kin san dai nidake bama boyema kowa sirrin dayanmu, kinsan halina, kinsan abinda zan iya da wanda bazan iya ba. Nasan akan abinda kike magana, kema kinsan bazan iya saka irin wannan abubuwan awayata ba.

Jiya ne wani abokina yake fada mani akwai wasu films masu kyau idan inaso, kinsan ni da son films masu kyau, ban tsaya dubawa ba kawai na basa wayata nace ya tura mani. Koda ya gama ban duba ba na taho gida, ban samu kallo jiya da dare ba sai yau ganin banida lectures.

Na kunna kenan na fara ganin irin batsar datake ciki kawai na aje nashiga wanka saboda banji dadin abinda ya tura mani ba, ina niyar dana fito wanka na goge shine fa kika shigo. Ido ta tsura masa kamar bata yarda da abinda ya fada ba.

Marairaicewa yayi yana fadin shikenan tunda baki yarda dani ba kije ki fadama su Dady nasan su zasu yarda dani. Mikewa yayi kamar zai fita. Hannunsa ta riko tana murmushi tace kayi hakuri Yaya.

Nayi maka mummunar fahimta, nima nasan bazaka iya aikata irin wannan abun ba, shiyasa ma nashiga damuwa, banaso ace Yayana yana aikata sabo. Ajiyar zuciya yayi ya juyo yana murmushi yace nagode kanwata.

Bani wayar yanzu na goge, naji dadi da kika fahimceni. Bara naje Salma ce takeson ganina. Saddika tace ka gaishe mani da ita Yaya. Yace zataji me zan siyo maki? Murmushi tayi tace abun dadi. Dariya yayi yace shikenan sai na dawo. Har ya kai kofa tace Yaya kada kamanta ka goge fa kafin Aunty Salma ta gani. Murmushi yayi yace dana shiga mota kafin na bar gidan ma zan goge.

***** ******

Sardauna ne yake ta faman sauri ganin wata yarinya data sauka daga Adedeta, Mubarak da suke zaune a majalissa sai dariya suke masa ganin yarinyar ta kusa shigewa gidan da tazo. Sardauna yana zuwa kusa da ita ya dai daita kansa yana fadin barka da zuwa sarauniyar mata.

Juyowa tayi jin ana mata magana, kara ware ido tayi ganin hadadden gaye agabanta. Murmushi yayi yana fadin kiyi hakuri fa na tsaidaki da alama kuma ke bakuwace a unguwar nan.

Murmushi tayi tace bakomai. Sardauna yace ziyara kikazo kenan? Tace aikuwa gidan kawata nazo, kai anan unguwar kake? Sardauna yace anan nake, dama muna zaune naga saukarki nace bara nazo mugaisa.

Meye sunanki? Fari tayi da ido tace sunana Ilham. Sardauna yace lallai sunan ya dace dameshi. Yanda kike da kyau haka sunanki yake. Amma anan garin kike kuwa? Murmushi tayi tace anan nake ina Dorayi.

Sardauna zeyi magana sai ganin Jamila yayi akusa dashi sai huci takeyi. Hannu yasa ya dafe goshinsa. Cikin fushi Jamila tace Malama sai ki wuce, kawai da kunga mijin mutum sai kurika wani kwarkwasa saboda kunyi kwantai.

Sakin baki Sardauna yayi yana kallon Jamila Ilham kuwa kallonta tayi tana fadin ai banice na tsidashi ba shine ya tsaidani, saboda haka shi zakiyi ma wannan maganar. Jamila tace wallahi idan baki bar wajen nan ba zansa ayi maki wulakanci.

Sardauna yace Jamila wai meye haka? Ko kallonsa Jamila batayi ba tacigaba da masifa. Su Mubarak ne suka karaso wajen hango Jamila da sukayi. Tun kafin suzo Ilham tayi wuf tashige gidan ta dauka sune wadan da Jamila tace zatasa ayi mata wulakanci.

Daure fuska Sardauna yayi yana fadin wai Jamila me kike nufi ne? Na fada maki bana sonki meyasa zaki rika mani haka? Shikenan saboda kina sona bazan kula kowa ba? Wallahi kinci sa’a ina ganin girmanki da agabanta zan wulakantaki.

Mubarak ne yace a’a Dan Ghana hakan bai dace ba. Sardauna yace haba Mubarak, kana ganinfa abinda tayi mani wai nine mijinta. Banda hauka irin nata waye zai kalleni yace ina auren wannan kucakar.

Kuka Jamila tasa ta bar wajen da gudu. Sani yace gaskiya Dan Ghana baka kyauta ba, ba halinka bane haka, meyasa zaka mata haka? Kada kamanta Jamila tun kuna yara take sonka, bata kulawa kowa saboda son da take maka.

Duk unguwar nan kowa yasan kai take so, yau gashi saboda wata kana fadar baka son Jamila kuma agabanta. Ai ko baka son mutum be kamata ka fada masa agabansa ba. Gaskiya banji dadin abinda kayi ba.

Mubarak yace haka ne Sardauna, nasan kana hakuri da Jamila, yau ma da kayi mata haka nasan ranka ne ya baci, amma duk da haka gaskiya baka kyauta ba. Turo baki Sardauna yayi yana fadin ni gaskiya ta takura mani, dan taga ina lallabata ne.

Amma yanzu da nayi mata haka zata shiga hankalinta. Murmushi Mubarak yayi yace karantse baka sonta. Tsaki Sardauna yayi yace ni bana sonta. Sani yace koma baka sonta dole muje ka bata hakuri.

Sardauna yace nide bazan je ba, sai dai kuje. Mubarak yace wallahi da kai zamuje, ai ba mune muka bata mata rai ba, idan kuma baza kaje ba ina mai tabbatar maka zanje mu dai dai ta da Jamila tunda baka sonta ni zan aureta saboda ina da abinda zan riketa.

Kallon Sani yayi yace muje tunda yace baze jeba. Wuceshi sukayi yana tsaye ya bisu da kallo, kamar wanda aka zabura ya kwala masu kira yabi bayansu. Dariya Mubarak yasa yana fadin ai nasan zaka biyo mu. Sani yace wallahi yana son Jamila kawai be gama yarda da zuciyarsa bane.

 Page  40 to45

Su Sardauna sun dade akofar gidansu Jamila amma bata fito ba, saboda tana jin yaron yace su Sardauna ne ta shige daki tayi kwanciyarta. Mutanan gidan sunyi mamakin yanda akace Sardauna yazo fira wajen Jamila amma taki fita.

Yanda Jamila kullum cikin maganar Sardauna tana fatan Allah yasa yazo mata fira amma yau yazo taki fita. Dama kuma tunda tashigo sukaga tana bakin rai. Tashi Mamarta tayi tashiga dakinta tana fadin wai Jamila ba Umar bane naji ance yazo? Jamila tace ni ina ruwana dashi.

Wallahi babu inda zanje, yace ba……… Shiru tayi batace komai ba dan tasan halin Mamarta matukar taji abinda Sardauna yayi mata sai ta fita daukar zafi, dama tana jin haushin yanda bata kula kowa saboda Sardauna.

Zama Mamar tayi tana fadin me yayi maki? Saurin goge idonta tayi tana fadin babu komai, so nake shima yaji irin abinda nakeji, tun yaushe na keso yazo bega damar zuwa ba sai yau, nima bazanje ba, idan yaga dama kada yakara zuwa ma.

Murmushi Mamar tayi tace haka akeson dan halak yarika zama a duk lokacin da aka bata masa rai, kinga yanzu sai ki maida hankali kirika sauraron masu zuwa wajenki. Juya baya Jamila tayi tana fadin ai babu wani wanda zan saurara daya wuce Sardauna nah.

Mikewa Mamar tayi tana fadin ke dai kika sani, duk ranar da ki kaga Umar yayi aure ai zaki hakura dashi ne. Ni wallahi banga abinda kika gani ajikinsa ba, yaron da ko sana’a beda ita, babu abinda ya sani sai Innarsa ta basa kudi yaci ya sha yayi wanka ya fita yana bin ‘yan mata kamar bunsuru.

Tashi Jamila tayi tana fadin kai Mama, dan Allah ki daina cema Sardauna bunsuru. Tabe baki tayi tace na fada, idan akwai abinda yafi haka ma zan fada masa dan baya da maraba dashi. Wallahi duk Babanki ne yake goya maki baya shiyasa har yanzu kike abinda kika ga dama.

Tashi Jamila tayi tana buga kafa tabar dakin kamar zatayi kuka. Murmushi Mamar tayi tana fadin Allah ya shirya ki, idan Umar alkhairi ne agareki Allah ya tabbatar, idan kuma ba alkhairi bane Allah yayi maki zabi da wanda yafisa alkhairi kuma ya cire maki sonshi.

Sardauna yace Mubarak mutafi tunda tace bazata fito ba, dama kune kuka matsa mani shiyasa nazo. Murmushi Mubarak yayi yace babu wanda ya matsa maka, kaine kaji zaka biyo mu, da ka barni nazo ni daya nasan zata fito ai.

Harara Sardauna ya buga masa yana fadin ai sai kazo tunda budurwar kace, ko kuma kai take so. Wallahi duk ranar da naji kazo wajen kanwata sai ranka ya baci. Dariya Sani yasa yace ai abu mai sauki kenan, a matsayinsa na abokin ka dan ya nemi kanwarka ai bawani abu bane tunda kace baka sonta.

Da wani bare yazo ya aureta ai gara Mubarak, ko ba komai kasan halinsa. A fusa ce Sardauna yabar wajen yana fadin wallahi bazata auresa ba. Dariya sosai sukeyi Mubarak yana fadin to kabari mutafi majalissar mana. 

Ko juyowa beyi ba ya wuce gida. Haka suka bar kofar gidan suna ta masa dariya. Inna tana zaune tsakar gida ta gama abinci tana kwashewa a kula Sardauna yashigo bakinsa dauke da sallama.

Amsawa Inna tayi tana rike baki ganin Sardauna ya dawo gida yamma likis. Wucewa yayi saman tabarma ya kwanta. Saurin karasawa tayi ta dauke ta kai daki tazo ta zauna tana fadin Sardauna lafiyar ka kuwa? Matsawa yayi ya dora kanshi saman kafafuwanta yana turo baki.

Murmushi Inna tayi tana shafa gashinsa tace da alama baka da lafiya ko? Kara turo baki yayi yana fadi kawai Mubarak ne ya bata mani rai. Inna tace lallai yau Mubarak yayi babban laifi, kaine da kanka yau kake fada da abokinka? Sardauna yace ai laifi yayi mani.

Inna tace naji laifi yayi maka, amma wane irin laifi ne? Kauda kai yayi yana fadin wai cewa yayi zeje yace yana son Jamila kuma ma aurenta zaiyi. Dariya Inna tasa tana fadin ya akayi yace yana son Jamilar to? Sardauna yace wai cewa yayi yaga bana sonta.

Inna tace aikam ya kyauta wallahi, dama yarinyar tausayi take bani, duk irin hidimar da takeyi mani saboda kai ne amma kai ba ka gani. Jamila tana sonka sosai, amma bansan abinda yasa baka sonta ba.

Duk da nasan baka isa aure ba amma idan ka rika kulata hakan zaisa kafi maida hankali wajen neman na kanka. Kai de kafi son ka tara ‘yan mata kala kala, saboda kana SARDAUNAN MATASA.

Murmushi Sardauna yayi yace kai Inna, duk da bana sonta kuma sai yaje yace yana sonta. Kuma ai muna mutunci da ita bazanso tarika kula kowa ba. Inna tace wannan son kai naka da yawa yake.

Ai dama tunda naga ka dawo gida da wuri nasan akwai matsala. To nima zanje na samu Mamarta nace su zaba mata miji kawai suyi mata aure saboda kai kanwa ka dauketa. Saurin tashi Sardauna yayi yana fadin haba Inna.

Dan Allah kidena fadar haka. Tashi yayi yana fadin ni natafi ma. Dariya Inna tasa tace yanzu kuwa ina gama sallar magriba zanje gidan. Kamar zai tashi sama haka yabar gidan yana kunkunai. Dariya Inna tasa tace zaka fito fili kace kana sonta ma, Allah ya bamu rai da lafiya.

****** *****

Zaune su Abdallah suke a saman bencin da yake kofar gidansu shida su Kabir suna ta labarin kwallo. Abdallah yace ai wallahi gobe mukaje match sai munyi raga raga da ‘yan club din su Bashir.

Kabir yace yauma saboda kaji wannan ciwon ne yasa suka cimu. Abdallah yace ai beshani a banza ba, wallahi sai na rama, kila ma yaji mani targade wallahi. Kabir yace ai dole muje wajen mai gyara aduba maka kafar.

Abdallah yace banaso Abbah yaga kafata shiyasa fa tun dazu nake zaune anan. Kabir yace daurewa zakayi muje, kuma kasan gobe bazaka buga kwallo ba sai dai mu buga. Abdallah yace idan naji da sauki zan buga mana.

Kabir yace Allah bazaka buga kwallo ba, tashi muje wajen mai gyaran. Abdallah yace kaga anyi magriba bana so muje mu dade Abbah yayi fada, kabari kawai idan mukayi Isha’i zamuje da Abdulhakim.

Kabir yace shikenan, tashi muje gashi can ana kiran sallar isha’i, yau dai mun samu sallah a masallaci saboda antashi da wuri. Abdallah yace yau zakaga fara’a wajen Abbah ai, kasan yana son yaganni a masallaci. Tashi muje.

Mamy da Amal suna zaune afalo Abdallah da Abdulhakim suka shigo tare da sallama. Mamy ce ta amsa masu tana fadin yau Abdallah da wuri aka taso? Abdulhakim yace ai Yaya yau babu kanta.

Amal tace naga yana dan gyashi. Saurin kallon kafar Mamy tayi tana fadin lafiya meya samu kafar? Zama Abdallah yayi yana fadin wallahi wani banza ne ya takani da takalmin kwallonsa saboda yaga zansa kwallo araga.

Mamy tace ai wannan kwallo ta jaraba abinda yafi haka ma zakaji, yanzu shikenan ya gurdeka ya barmu da damuwa. Abbah ne yashigo da sallama. Amsawa sukayi Abdulhakim ya tashi ya karbi jakar daya shigo da ita.

Amal tace Abba sannu da zuwa, yace yauwa Mamana ya gidan? Tace lafiya lau. Mamy tace sannu da zuwa, yace yauwa, Abdallah yace Abbah sannu da zuwa. Murmushi yayi yace yauwa Abdallah.

Da alama yau akwai wani abu naga ka dawo da wuri? Murmushi yayi yana shafa kai. Amal tace Abbah wani ne ya taka masa kafa da takalmin kwallo. Zama Abbah yayi yana fadin ka je an duba kafar ko? Abdulhakim yace yanzu zamuje.

Abbah yace Allah ya kyauta, yau zakaji yanda mutanan da kake jima ciwo sukeji ashe. Abdallah yace kai Abba, haka zakace? Abbah yace to yazance? Ai duk dan kwallon da ba’a gansa da tabo ba to becika dan kwallo ba.

Kuma tun dazu da kaji ciwon da kun wuce wajen mai gyara da yanzu ka huta, amma yanzu nasan kafar tayi tsami dole kasha zafi. Amal tace shida yake dan kwallo ai bazeji zafin komai ba.

Mamy tace insha Allah ma babu zafin da zeji. Abbah yace Allah yasa, kaga dole zaka zauna agida har ka warke kafin ka koma kwallo. Abdallah yace Abbah gobe ma muna da match wallahi.

Mamy tace wallahi babu inda zakaje ka buga kwallo. Abbah yace kwantar da hankalinki, befa san abinda ya sameshi yanzu ba, dole sai yaje an duba za’a gani. Abdallah yace insha Allah targade ne ma.

Abbah yace Allah yasa, barima nayima wani abokina magana ya turo mani Malan Bello yazo gida ya gyara maka. Abdallah yace nide Abbah muje can. Abbah yace babu inda zakaje gara azo nan agyara maka. Abdulhakim kamashi ya canza kaya kafin yazo.

Tashi Abdallah yayi yana kunkunai. Amal kuwa dariya takeyi kasa kasa a hankali tace yau zamuji ihun maza. Mamy tace maza yajiki. Abbah yace tashi Amal ki dora ruwan zafi ki kawo masu abinci suci kafin yazo ya taba kafar ya kasa ci.

 Page  45 to50

Hawaye sharbe sharbe Abdallah yayi, tun su Amal, Abbah da Mamy suna masa dariya har suka fara tausaya masa. Ashe gurdewace yayi, Abdulhakim hada kwalla saboda yana da tausayi.

Bayan Malan Bello ya tafi Abdulhakim ya kamasa suka nufi dakinsa. Abbah yace wai ni Abdallah dama haka ‘yan kwallon suke da ragwanci? Murmushi Abdallah yayi yace Abbah idan akazo maganar lafiya ai ta wuce mutum yayi dauriya.

Mamy tace kyaleshi kuje kada ka fama kafar. Abdulhakim yace ai wallahi yayi dauriya, da ace irin su waccan mai son jikin ce wallahi har makwafta sai sun shigo. Amal tace ai dai shima yayi kuka. Harara Abdallah ya buga mata da sauri ta tashi tashige daki tana dariya.

***** *****

 Zaune Salman yake a motarsa yana waya da wata budurwarsa, dan yashigo makaranta sauran abokansa basu karaso ba kuma malamin da suke dashi bezo ba, dan lecture din yamma ce, haka ya kwantar da kujerar motar yashiga waya da budurwarsa.

Salma da ta shigo yanzu ganin motar Salman yasa ta nufi inda yake. Bayan tayi parking ta fito ta nufi wajensa bakinta dauke da murmushi. Tsaye tayi a jikin tagar motar  ganin yana waya.

Kasancewar tagar  a bude take yasa take jiyo abinda yake cewa. Sam Salman bai kula da ita ba haka ya cigaba da wayarsa wadda yawancinta duk ta batsa ce, sai wani murmushi yakeyi.

Salma da take tsaye a gefensa tuni ta daskare jin irin abubuwan da Salman yake fada ma wata. Tuna wani lokaci tayi data taba ganin wani blue film a wayarsa tayi, data masa magana yashiga rantse mata akan wallahi besan lokacin da aka tura masa ba.

Yasan ya bada wayarsa atura masa film kila alokacin aka tura masa. Ganin yanda yake rantsuwa yasa ta yarda da abinda yace. Saurin kallonsa tayi jin yana fadin gaskiya kwana biyu nayi kewar kwallaye na.

Dole yau muje gidansu Jabir na bama flower ta ruwa nasan suma suna kewata. Kada ki damu yau bazan koma gida dawuri ba, bayan magriba nasan mun rabu da Salma zanzo na daukeki mu wuce.

Wasu zafafan hawaye ne suka zuboma Salma. Da sauri ta juya ta nufi motar ta, tana zuwa ta shige ta saki wani irin kuka. Ashe dama maganganun da mutane suke fada mata gaskiya ne? Dama Salman mazinaci ne bata sani ba? Dole yau ta rabu da Salman koda sonsa zai kasheta.

Kunna motar tayi ta nufi bakin gate din makarantar aguje. Salman da gama wayarsa kenan ya juyo, ganin motar Salma yasa gabansa ya fadi, yana kokarin fita yaga ta fisgi motar aguje. Saurin fitowa yayi jikinsa yana rawa.

Meyasa Salma zatazo wajensa kuma ta fasa kara sowa? Anya batazo taji yana waya ba hakan yasa ta tafi? Hannu yasa ya dafe kansa yana salati. Kamal ne dasu Jabir suka karaso wajensa yana fadin kai kuma lafiya ka dafe kai? Salman yace wallahi babu lafiya.

Duk yanda akayi Salma taji ina waya da Minal, saboda bayan nagama wayar naganta a mota kusa da motata kafin na fito ta fisgi motar tabar wajen. Kamal yace haba kada ka bada gayu mana.

Kai fa babban yaro ne, ya kamata ka iya takun ka, koda ace ta jika zaka iya mazewa ka nuna bakasan anyi ba. Kasan fa mata sai ana masu jan ido. Salman yace gaskiya banda Salma, kai ma kasan yanda Salma take awajena bazanso ta kamani da wani mugun hali ba.

Kawai ina yine saboda na ragema kaina zafi, da ace ta yarda muna ragema juna zafi ai wallahi babu yarinyar da zan rika kulawa, to ita bata cikin layin da nakeso, shiyasa nake rage ma kaina zafi da munyi aure shikenan sai na daina komai tunda dama arashin Uwa ne nake Uwar daki.

Jabir yace haka ne, amma idan baka seta kan ka ba wallahi zaku bata da ita, yanzu mutafi class idan muka fito kada ka kirata ka barta idan taga baka kirata ba zata sauko ta nemeka kaga idan tayi maka magana sai ka tsarata. 

Amma idan kaine ka kirata zata yi yanda taga dama. Salman yace wannan haka yake, muje kawai, dama sonta yafi nawa yawa ai. Dariya sukasa Kamal yana fadin baka da kyau mutumina.

A bakin gate Salma taci karo da Zarah ta dawo daga cikin gari, parking tayi Zarah ta karaso wajenta, bude motar tayi tashiga tana fadin zamuyi lecture ina kuma zakije? Juyar da kai Salma tayi hawaye suna kara zubo mata.

Cike da tashin hankali Zarah tace Salma lafiya wani ne beda lafiya ko mutuwa akayi maki? Rushewa Salma tayi da kuka ta dora kanta saman kafafuwanta. Nan hankalin Zarah ya tashi tace bara ta kira Salman.

Da sauri Salma ta dago ta fisge wayar tana fadin na tsanesa, bana sonsa. Murmushi Zarah tayi tace da sauki tunda ba rashi akayi ba, yanzu ki tuka motar mubar bakin gate sai naji abinda ya hada ku, yau keda Salman ne wai kukayi fada.

Tada motar Salma tayi suka koma wani waje sannan ta kashe motar. Zarah tace ina jinki fada mani kinga lecture zamu shiga. Salma tace kawai kije bazan iya shiga class ahaka ba. Zarah tace nidai ki fada mani.

Duk abinda taji sai da ta fadama Zarah da kuma blue film din data taba gani awayar Salman sai da ta fada mata. Sosai hankalin Zarah ya tashi jin wannan labarin. Duk da tasan Salman yana kula ‘yan mata amma bata dauka yana nemansu ba.

Babban dalilin da yasa bata taba fadama Salma ba saboda tasan kalar son da take masa, matukar ta fada mata zata rika ganin laifinta, shiyasa tayi shiru da bakinta tunda tasan Salman son aure yakema Salma da sunyi aure komai zai wuce.

Salma tace kinsan Allah Zarah na hakura da Salman, da ace ‘yan mata kawai garesa zan iya hakura na cigaba da tarayya dashi saboda namiji ba dan mace daya aka yisa ba, kuma nima mace ce zan iya maido hankalinsa wajena.

Amma sabo fa yake aikatawa da ‘yan matansa, Zarah wayar batasa, films din batsa. Zarah Zina yake aikatawa taya zan cigaba da tarayya dashi? Ko shine autan maza bazan kara kula sa ba.

Ban kasance Mazinaciya ba saboda haka bazan auri mazinaci ya gurbata mani yara ba. Na hakura dashi Zarah. Jinjina kai Zarah tayi tace ki daina fadar haka Salma. Shedar Zina wahala gareta.

Yanzu kin tabbata Salman yana Zina? Saboda kinga films din batsa awayarsa, kinji yana wayar batsa bashine zai baki amsar yana aikata zina ba. Koda kikaji yace zasuje gidansu Jabir bakida tabbacin Zina zasu aikata. Idan har bakiso ki jefa kanki cikin halaka to ki cire wannan zargin na Zina da kike masa.

Cikin kuka Salma tace amma dai Zarah kema kin yarda yana aikata abinda na fada maki ko? Ko zaki ce mani baki san Salman yana da ‘yan mata acikin makarantar nan ba keda kike kwana tare dasu? Zarah tace Salma kinsan bana shiga harkar da batawa ba.

Ko Salman yana kula wasu bazan sani ba tunda ba shiga harkar mutane nakeyi ba. Ke dai abinda nakeso dake ki bari sai kin kama mutum hannu da hannu sannan ki yanke hukunci.

Bana so ki yanke hukunci cikin fushi daga baya kizo abun ya dameki. Salma tace to yanzu ya kike so nayi? Zarah tace ba kince zasuje gidansu Jabir anjima ba? Salma tace E, Zarah tace abinda zamuyi muna gama sallar magriba mujira muga fitarsu.

Idan har muka ga da gaske sun tafi gidan to zamu shiga domin mu tabbatar ma kanmu. Salma tace idan ko har na tabbatar Salman yana aikata Zina wallahi bazan auresa ba. Gara son sa ya kasheni.

 Kuma nasan bazan mutu da sonsa ba insha Allah, zan dage da addu’a Allah ya cire mani son sa. Zarah tace insha Allah ma bazaku rabu ba, domin kuna son junanku. Muje kada mu rasa lecture.

Koda Salma da Zarah suka je har Malan yashiga, damma baya da tsanani yasa be koresu ba. Tunda tashigo idon Salman yana kanta, ko kallon inda yake batayi ba, wanda ada matukar ya rigata shiga class dole sai ta kalli wajen da yake zama.

Jikinsa ne yayi sanyi, gashi taki daga fuskarta bare yaga halin da take ciki. Ganin kada Malan ya ganosa ne yasa ya maida hankalinsa gaban allo. Haka suka gama dagashi har ita babu wanda ya fahimci abinda aka masu.

Suna fita Salma taja Zarah suka nufi hostel damma kada Salman yace ze tsaidata. Wayarta ta ciro takira Momynta ta fada mata zata tsaya suyi Assignment da Zarah a hostel bazata dawo da wuri ba.

Momy tace shikenan amma kada kiyi dare da yawa. Suna gama wayar tayi saurin kashe wayar gaba daya, bata son Salman ya kirata ma. Salman kuwa yana fitowa yashiga neman Salma.

Har wajen motar ta yaje amma be ganta ba. Gaba daya hankalinsa ya tashi. Kamal ne ya dafasa yana fadin haba Salman, meyasa zaka damu kanka haka? Kasan fa Salma tana sonka.

Ko fushi zatayi da kai bazata iya mai tsawo ba. Kawai ka share kaga yau kuna da haduwa da Minal. Murmushi Salman yayi yace Kamal kasan kuwa ya Salma take acikin rai na? Koda nace maka sonta yafi nawa wallahi nima bazan iya rayuwa idan babu ita ba.

Koda zan rayu tabbas zanyi matsananciyar rayuwa. Ni babu wajen wata Minal da zanje. Wayarsa ya ciro yafara kiran Salma amma akashe. Dafe kai yayi kamar zeyi kuka yace Jabir ka gani ko, ta kashe wayar ma gaba daya.

Salma ba haka ta saba mani ba, tabbas Salma taji wayar da nakeyi, wallahi taji. Dan Allah Jabir ya zanyi? Dafasa Jabir yayi yace kayi hakuri Salman, nima zuciyata ta bani Salma taji wayar da kayi.

Abinda zai faru idan muka gama sallah kaje gidansu kome tayi maka ka bata hakuri. Salman yace mezan fada mata Jabir? Bani da wata karya da zan iya fada mata da zata yarda dani. Tariga taji abinda na fada.

Kamal yace kada ka damu, muje muyi sallah ni zan tsara maka abinda zaka fada mata. Jinjina kai Salman yayi suka nufi masallaci dan lecture din yamma sukayi suna fitowa aka fara shirin kiran sallah.

Salma da Zarah suna gama sallah sukayi saurin fitowa don su cima Salman kada ya fice. Cikin sa’a suka hangesa shida Jabir sun shiga mota. Salma tace kila budurwar tana baya. Zarah tace muje koma menene zamu gani ai.

Insha Allah ma babu abinda zamu gani sai alkhairi. Salma tace uhm. Su Salman suna fita daga gate din makarantar su Salma suka take masu baya. Zuciyar Salma bugun ukku ukku kawai takeyi ganin da gaske Salman ya dauki hanyar gidansu Jabir.

 Page  50 to55

Cike da mamaki suke kallon Jabir daya fito daga motar Salman yana daga masa hannu alamar sai anjima. Ganin Salman ya canza hanya ne yasa suka fara bin bayansa a hankali.

Mamaki be gama kama su ba sai da suka ga Salman ya dauki hanyar unguwar su Salma, duk da haka bata yarda ba haka tarika bin bayansa a hankali. Har sai da yayi parking a kofar gidansu ya fito yana latsa waya sannan Salma ta yarda babu kowa acikin motar.

Murmushi Zarah tayi tace Allah sarki, ashe ma wajenki zai zo duk kika tashi hankalinki. Tsaki Salma tayi tace ai be wanke kansa ba, wayar da naji yanayi me zece mani. Kila ma ya gane na jisa shiyasa hankalinsa ya tashi ya fasa daukar budurwar.

Zarah tace yanzu dai tunda baki kamasa ba ki basa dama ya fada maki abinda yazo fada, muje ki maidani makaranta kinga dare yayi. Juya kan motar Salma tayi dama basu shigo sosai ba tana fadin aiko baze ganni a yau ba.

Salman ganin ya kasa samun wayar Salma ne yasa ya shiga gidan kai tsaye, kasancewar ya saba da yazo yake shiga. Bayan sun gaisa da maigadi ne yake tambayarsa ko Salma ta dawo.

Maigadi yace gaskiya bata shigo ba, amma Hajiya tana ciki. Salman yace shikenan bara naje mu gaisa sai na jirata. Wucewa cikin gidan yayi yana kara gwada lambar Salma.

Bayan sun gaisa da Momy ne yake tambayar Salma. Momy tace tayi mani waya wai zata tsaya suyi Assignment ita da Zarah a hostel kilama tana hanya, bakuyi waya bane? Salman yace kila wayarta babu caji na kira akashe.

Momy tace kajirata nasan bazata dade ba. Bara nasa akawo maka abinci. Salman yace nagode Momy. Gyara zama yayi gabansa yana cigaba da faduwa, basu saba fada shida Salma ba shiyasa gaba daya yau yakejinsa wani iri.

Da sallama Salma tashigo cikin falon. Salman ne kadai ya tasa abinci ya kasa ci saboda damuwa, saurin tashi yayi yana amsa mata sallamar, ko kallon inda yake batayi ba ta nufi hanyar dakinta.

Saurin shan gabanta yayi yana fadin haba Salma, tun dazu fa ke nake jira kuma kin ganni amma zaki wuce. Menayi maki ne haka? Harara ta buga masa tana fadin bani hanya na wuce. Salman yace dan girman Allah kizo muyi magana kada wani ya fahimci muna fada.

Salma tace kowa ma ya fahimta mana, ka bani hanya nace. Salman yace haba Salma, da girman Allah fa na hadaki, kada ki manta kece kike mani fada idan naki nayi abu saboda Allah.

Kallonsa Salma tayi na wani lokaci sai kuma ta juya ta koma falo. Salman yace dan Allah muje falon baki banaso wani yazo wucewa yaji abinda muke fada. Juyawa tayi ta nufi hanyar falon baki.

Zaune Salma tayi a saman kujera ta hade girar sama data kasa, dukawa Salman yayi har kasa yana fadin nasan duk abinda zan fada maki bazaki yarda dani ba, amma dan Allah ina rokonki ki bani dama nayi maki bayanin abinda kike zargi.

Wallahi ba abinda kike zargi bane. Haba Salma, taya zanyi tarayya da wata daban, tarayyar ma ta kazanta. Tun lokacin da kika shigo makaranta naga shigowarki har kikayi parking kusa da mota ta.

Haka kawai naji inaso na gwadaki domin naga wane irin so kike mani. Kafin ki fito nayi saurin kwantar da kujerata ta yanda bazakiyi tunanin zan ganki ba idan kikazo, domin nasan matukar kikazo kika iske ina waya dole zaki jira na gama kafin kiyi mani magana.

Wannan dalilin ne yasa na kwantar da kujerar na fara wayar karya. Salma nasan kema kina mani kallon ina tarayya da wasu matan, kuma ina samun labarin wasu suna kawo maki gulmata.

Hakan ne yasa nace bara naga wane irin yanayi ko mataki zaki dauka idan kika kamani da kanki. Shine fa na fara wayar karya, Allah ya sani ina jin kunyarki amma haka na daure na rika fadar wasu abubuwan badan komai ba kawai dan naga yanayin da zaki shiga.

Sanin kinsan hanyar gidansu Jabir yasa nace zan dauki budurwata muje can, domin nasan dole zaki biyoni abaya. Ina ganin lokacin da kika nufi motarki, kafin na taso har kika bar wajen.

Kinji abinda ya faru amma dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba. Kada kimanta kema kin taba mani irin wannan abun, amma lokacin  April fool ne. Nima haka kawai naji inaso na gwadaki.

Hawaye ne suka karasa gangaro masa ya hade hannuwansa biyu waje guda yana bata hakuri. Itama kukan takeyi, sakkowa tayi kasa ganin Salman ya kara rushewa da wani kukan kamar karamin yaro.

Hannu tasa ta goge idonta tace ya isa haka Salman, bana so saboda ni karika asarar kwallanka, meyasa zakayi mani irin wannan wasan? Kaima kasan babu abinda nafi tsana kamar ace kana aikata wani sabo.

Da ace zuciyata ta buga na mutu fa? Saurin dagowa yayi yasa hannunsa ya rufe mata baki yana girgiza kai. Wannan shine karo na farko daya taba kai hannunsa a jikinta ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Kallonta yakeyi idonsa yana cigaba da zubar da hawaye yace bazaki mutu ba Salma, ya kikeso na kasance idan kika tafi kika barni? Kada ki kara yima kanki fatan mutuwa ba tare da mun rayu tare ba.

Hannu tasa ta cire masa hannunsa tana goge idonta tace shikenan bazan kara ba, amma kai ma kada ka sake mani makamancin wannan wasan. Salman yace insha Allah bazan sake ba.

Murmushi ta sakar masa tace shikenan ya wuce. Murmushi yayi yana goge idonsa yace nagode my life. Salma tace yau kuma na samu wani sabon suna haka? Gyara zama Salman yayi yace ai dole na kiraki da wannan sunan.

Domin ayau na tabbatar da cewar kedin rayuwatace. Ban taba shiga tashin hankali irin na yau ba, duk lokacin dana kira wayarki naji akashe zuciyata sai tayi kamar ta fito. Gaskiya Salma bansan son da nake maki zai iya halakar dani idan na rasaki ba sai yau.

Dan Allah kada ki kara fushi dani kinji my life. Ido Salma ta zuba masa tana murmushi jin yanda yake fada mata dadadan kalamai wanda kullum take fatan tarika jinsu daga bakinsa.

Matsowa yayi dai dai fuskarta ya hura mata isa yana fadin wannan kallon fa? Saurin boye fuskarta tayi ta dan ja da baya tana murmushi. Salman yace gaskiya kullum ina kara ma Allah godiya daya bani mace kamila mai sona.

Allah ya nuna mana ranar da zamu zauna a haka tare acikin dakinmu. Salma tace amin. A yanzu kam zance naji dadin wannan wasan da kayi mani, domin yasa nayi fushi da kai har kazo kana abinda baka taba yi akai naba.

Yau kaine durkushe agabana kana kuka kana rokon na yafe maka, har kake ikirarin bazaka iya rayuwa idan babu ni ba. Gaskiya wadannan kalaman naka sunfi komai dadi agareni yau.

Ko banci abinci ba zan iya bacci ahaka, domin kalamanka sunyi mani dadi sosai, nike da godiya agareka Salman, kuma kai ma rayuwta ne, banida wani buri da yawuce mu gama makaranta muyi aure. Tashi muje kaci abinci tunda komai ya wuce.

Dariya Salman yayi tare da mikewa yana fadin yanzu kam zan saki ciki naci abinci tunda rayuwata ta dawo tana tafiya dai dai. Murmushi Salma tayi ta shige gaba tana fadin nima haka. Ajiyar zuciya Salman yayi aransa yana fadin Allah yayi maka albarka Kamal, wannan dabara taka tayi .

***** *****

Tsaye Sardauna yake akofar gidansu Jamila ya aika yaro ya kira masa ita dan koya kira wayarta bata dauka, tunda yayi mata wanann wulakancin har yanzu taki bari su hadu, shi kuma gaba daya yashiga damuwa.

Ko bacci ya kwanta tunaninta yake hanasa baccin, tunda Mubarak yace zeje ya fada mata yana sonta kullum sai yaje kozai iske shi acan. Duk abinda yakeyi su Mubarak suna ganinsa banda dariya babu abinda suke masa.

Inna kanta ta fahimci Sardauna yana cikin damuwa tunda tace zata je tace afitar mata da miji, dan koda yaushe idan yaga ta fita sai ya tambayeta inda taje, ita ko har tsokanarsa takeyi tace daga gidansu Jamila take.

Ai nan zakaga ya kasa zaune yana so ta fada masa abinda tajeyi. Sosai Inna take masa dariya idan taga duk ya daburce, kuma bata fada masa abinda ta jeyi.

Yaron daya aika ne yafito yace tace gata nan zuwa. Ajiyar zuciya yayi yana fadin da bance Mubarak bane bazata fito ba kenan. Kudi ya bama yaron yana fadin nagode. Cikin minti biyar Jamila ta fito.

Har ta fada saboda tunanin Sardauna, kasancewar ya juya baya bataga fuskarsa ba har ta karaso. Sallama tayi tana fadin Mubarak yau kai ne agidanmu? Juyowa Sardauna yayi fuska a daure.

Itama daure fuska tayi tana fadin to meye na karyar zakace wai Mubarak ne? Kara daure fuska yayi yace ke nine nake maki karyar? Murguda baki tayi tace ai karya kayi tunda bashine na iske awajen ba.

Tsaki yayi yace meyasa kika rai nani haka ne? Idan na kira ki baki daukar wayata, so nawa nazo gidanku amma kin ki fitowa, kinsan abinda ya kawoni wajenki ne? Tabe baki tayi tace ni ina ruwana da mutumin da yace baya sona.

Kome zai kawo ka wajena ai nasan ba alkhairi bane tunda kai ba masoyina bane. Dama nice nace ina sonka, kuma tunda ka fito fili kace baka sona ai gara na hakura nima na rungumi masu sona.

Harara ya buga mata yana fadin wai Jamila yaushe kika koyi tsiwa ne? Jamila tace ranar da kace baka sona. Murmushin gefen baki yayi yace wallahi duk ranar da nazo naganki tsaye da wani sai na cimasa.

Dama Inna ce tace nazo na baki hakuri akan abinda nayi maki shiyasa nake ta kiranki baki dauka. Jamila tace tunda Inna ce tasaka kazo ka bani hakuri kace mata saboda ita nayi hakuri, amma maganar soyayya ko yau saina kula wani.

Matsowa Sardauna yayi kamar zai bugeta har sai da tayi saurin matsawa cike da tsoro. Idanu ya kura mata sannan yace wallahi zakisha mamaki matukar kika kula wani, koba komai aini Yayanki ne, dole na sa maki ido bazan bari kowa yarika zuwa wajenki ba saboda baki isa aure ba.

Dariya Jamila tasa hada rike ciki tana kallon Sardauna. Juyawa yayi yana fadin kina ganin wasa ne, kibari na kamaki da wani, kuma kullum saina leko ko zanga wani yazo. Tafiya yayi ko juyowa beyi ba yana murmushi.

A zuciyarsa yana fadin ai dai ta huce tunda tayi dariya, yau zanyi bacci kenan. Jamila kuwa bayansa ta tsurama ido cike da so, ita dai Allah ya jarabceta da son Sardauna. Duk da tasan beda sana’a ita dai tana son sa.

Tasan zaiyi wuya Iyayensa suyi masa aure yanzu, amma tayi alkawarin zata jirasa har lokacin da zai tashi aure. Dadin da takeji daya ne yanzu take a SS 3 tasan Iyayenta bazasu matsa mata akan aure ba tunda bata gama secondary ba. Haka tashige gida cike da farin ciki yau dai sun shirya da Sardaunanta.

***** *****

Zaune su Aminu suke a majalissarsu banda hayaki babu abinda yake tashi awajen, kowa da kalar abinda yake busawa. Aminu ne ya busa hayaki sama yana fadin Iro dazu da Mai kano yazo bana nan me yace maka? Iro yace dama akan maganar poster ce.

Aminu yace be baka kudi ba? Iro yace gaskiya be bada ba. Aminu yace sufa haka suke, haka zamu lika masa poster abanza, ai ko kudin siyen sigari sai ya bada. Amma kabarni dashi bazamu lika ba, idan yaga ba’a lika ba nasan zai dawo.

So nake ma na hadu dashi na fada masa aikin da mukayi masa dan wallahi saiya biya. Iro yace kaima kasan dole ya biya musamman idan yaji aikin asiri ne muka lalata. Aminu yace na kira wayarsa bata shiga zuwa gobe zan kirasa na fada masa.

Iro ne yayi saurin tashi ya wurgar da takardar wiwin da take hannusa ya taketa. Aminu yace kai kuma lafiyarka naga ka tsure kamar wanda yaga surukinsa? Hannu Iro yasa yana nuna masa mahaifinsa. Sauran ma tashi sukayi.

A sukwane Aminu yayi wurgi da karan sigarinsa ya tashi yana goge bakinsa. Karasowa Mahaifin Aminu yayi fuskarsa cike da damuwa. Iro ne yace barka da dawo wa Baba. Kallonsu yayi yace yanzu wannan halin da kuka jefa kanku shine kuke ganin yayi maku ko? Dukar da kai sukayi.

Kallon Aminu yayi yace Aminu so nawa zan fada maka shaye shaye baya da amfani a rayuwar dan adam? Kaine babba kuma kaine ka lalata rayuwarka. Daure fuska Aminu yayi yace haba Baba, me kaga inayi marar kyau? Ba Zina kaga ina aikatawa ba fa.

Baban yace Zina ita kadaice laifi aduniya? Aminu yace to ai itace dai babban laifin da Allah ya haramta. Kuma wannan sigarin ba wani abu bane. Jinjina kai Baban yayi cike da bacin rai yabar wajen ya nufi hanyar gidansa.

Iro yace haba Aminu, taya zaka fadama Baba irin wannan maganar? Kasanfa ba’a raina Iyaye, tunda ya ganmu kuma yazo yana fada mana gaskiya hakuri ya kamata mu basa ai. Hannu Aminu ya daga masa.

Kallonsa yayi yana fadin Ubanka ne ko nawa? Nafika sanin halin Baba idan ba haka nayi masa ba nasan shi da nacin fada kila ya tara mana mutane. Iro yace duk da haka……… Aminu yace kaga Malan babu ruwanka fa, wucewa yayi yabar Iro a wajen.

Tsaye Bala yake ajikin motar Maigidansa yana fada masa tabbas ya binni abinda ya basa. Yallabai yace amma kuma Malan yace anyi kuskure ba’ayi yanda ya fada ba. Bala yace maigida kasan halin malaman nan fa.

Kodan suci maka kudi fa zai iya cewa baka aikata da kyau ba. Yallabai yace gaskiya nasan yanda aikin Malan yake, bai taba yimani aikin da baici ba. Bala yace to nidai nayi yanda kace, kasan wani aikin bada sauri yake aiki ba.

Yallabai yace shikenan, zan koma wajensa idan yaso ya sake bani wani. Murmushi Bala yayi yace shikenan Maigida sai na jika. Yallabai yace yauwa Bala, hannu yasa aljihu ya ciro kudi ya basa yana fadin ga wannan kaima ka kashe.

Bala yace Allah yaja da ranka maigida, nagode sai ka dawo. Shiga mota Yallabai yayi yabar unguwar. Dariya Bala yayi yace kaji dan iskan Boka zai tona mani asiri. Allah yasa ya kara bada wani sai na lalata sa.

Tunda haka kuka zaba, kuyi amfani damu kuci zabe muma zamuyi amfani daku muci kudinku.

Leave a Comment

error: Content is protected !!