Matsalar Bushewar Gaba (Vaginal Dryness)
Wannan shi ne ake kira da ‘Feminine Dryness’: (Bushewar gaba ko daukewar ni’ima) :
Wannan na nufin karancin ni’ima ga mace kamar yadda matan suka fi fada. Amma masana kiwon lafiya kan ce karancin ‘lubrication’ a farjin mace inda hakan ke jawo jin zafi yayin saduwa, rashin dadin jima’i, rashin sha’awar yi da kuma kaikayi cikin farji.
Hakan na faruwa ne a dalilin ko sakamakon karancin sinadarin ‘hormone’ mai suna ‘Estrogen’ a jikin mace, wanda ita take Samar da damshi cikin al’aurar mace dama sauran mahimman abubuwa a jikin mace da kara jin dadin gamsuwa.
Kamar yadda mukace karincin sinadaran hormone mai suna estrogen ke jawo bushewar farji, to me yake kawo karan sinadaran estrogen : gasu kamar haka :
1- Shayarwa
2- Magungunan Cancer.
3- Damuwa (Stress)
4- Tsaikon Al’ada
5- magungunan tazarar haihuwa.
6- matslar garkuwan jiki.
sirrin rike miji
Ga wasu matsaloli da za su yi iya kawo matsalar Bushewar gaba:
1- Tsiron cikin mahaifa wato (fibroid).
2- Matsalar da kan shafi cikin mahaifa wadda ba kari ba.
3- Tiyatar kwayayen haihuwa a mace (obaries) watakil ko a dalilin cyst.
4- Motsa jiki fiye da kima (Intense edercises).
5- Sai kuma amfani da sabulai, omo, mayuka, turare da mata suke amfani.
Matsalolin da Bushewar gaba zai iya kawo wa mata:
1- Yakan iya bada daman shigar kwayoyin cuta.
2- Jin zafi yayin saduwa, musamman idan namijin bai iya foreplay (wasanni) ba.
3- Rashin gamsuwa.
4- kaikayin gaba
5- Jini lokocin saduwa.
Ya za’ayi a magance wannan matsalar:
Magani ya danganta da abinda binkice ya nuna, duk mai fama da wannan matsalar ta daure taje ta sami kwararrun jami’an lafiya musamman wanda suka karanci bangaren mata (Gynaecologist) don su duba ta su ba ta magani.
Ciwon Sanyi Na Mata:
Za mu dan yi karin bayani game da wannar larura ta ‘baginal infection’ wato ciwon sanyin gaban mata kamar yadda galibin Hausawa suke kiranta da shi.
In sha Allah za mu yi bayani gwargwadon abunda Allah yasanar damu lurada yadda galibin mata ke fama da wannan matsala ta ‘baginal infection’ wanda kusan kashi 70% cikin 100% suna fama da wannan larura.
Insha Allah za mu fara bayani akan ta yaya ake kamuwa da wannan cuta ta baginal infection kafin mu je kan hanyoyinda ake bi ara bu dashi da kuma dabi’unda suke hana warkewa daga wannan cuta Ta yaya ake kamuwa da wannan cuta ta baginal area infection?
Ga hanyoyin Kamar haka:
1. Ita dai wannan cuta ta baginal infection ana daukanta ta wurare da dama sannan tana daga cikin rukunin cututtukan da ake wa lakabi da ‘sedual transmitted diseases (STD)’ wato cututtukan da ake daukawa yayin saduwa.
Don haka kun ga lalle kenan ana daukar wannan cuta ta hanyar saduwa da me dauke da ita. Musamman wadanda suke da abokan saduwa da yawa.
Ana iya daukar wannan cuta ta hanyar yin amfani da bandakin da mutane dayawa suke amfani da shi ( public toilet) idan me wannan kwayar cutar a jikinta ta yi amfani da bandaki za ta yi zuba kwayar cutar a wajen, to idan aka yi rashin sa’a kika zo kika yi amfani da bandakin ba tare da an yi feshin magani ba tabbas za ki iya dauka, kin ga she ba sai me aure ko me bin maza ba ne kawai za ta iya kamuwa da wannan cuta, dalilin haka yana da kyau a dinga yawan tsabtace bandaki lokaci lokaci musamman ma da irin su IZAL, DETTOL da sauransu.
Sannan mace takan iya kamuwa da wannan cuta sakamakon wasu dabi’u da suke aikatawa, musamman masu tushe tushe a gabansu da sunan maganin mata, gaskiya da yawa irin wadannan magunguna suna jawo cutar baginal infection, kamar dai yadda manyan likitotinmu suka mana bayani a baya.
Sannan akwai wasu kuma ba tushe tushe sukeyi ba, a’a kawai tsabar son tsabta ne yake kai su ga kamuwa da wannan larura ta infection.
Yauwa mun san wasu za su ce ta yaya tsabta za ta jawo infection?, To za ku ji a ftowa na gaba, in sha Allah.
Leave a Comment