Hausa Novels

Matsan Mu 55 to 70

 

Matasan Mu 55 to 60

 Page  55 to 60

Haba Aminu, yaushe zakayi hankali ne? Kai baka gajiya da jefa mahaifinku cikin tashin hankali? Kamar yanzu ya kamata ace kana gidanka kaima ka tara iyali. Amma har yanzu baka girma da fadama Mahaifinku magana ba.

Babban abun bakin cikinma wai agaban abokan ka. Yanzu kana ganin ka kyauta kenan? Gashi bakin cikin abinda kayima Mahaifinka yasa ko abinci ya kasa ci, tunda yashigo yana kwance adaki haba Aminu.

Karkace baki Aminu yayi yace ni kuma menayi masa Mama? Kawai daga yaganmu muna zaune a majalissa shikenan fa yaje yana mana fada, kinsan halin Baba baya gajiya da disgani cikin abokaina kamar wani karamin yaro.

Tunda nashiga harkar siyasar nan Baba ya tsaneni, sam bayason farin ciki na, nida babu agidan nan duk daya ne, yafi fifita kannaina sama dani, ai babu dadi. Mama tace koma menene ai Mahaifinka ne.

Tashi Aminu yayi yana fadin ina abincina yake? Girgiza kai Mama tayi tace duba kitchen yana nan arufe. Wucewa yayi yana wata irin tafiya. Mama tace Allah ya shirya mani kai.

**** ****

Da dangyashi Abdallah ya karaso cikin falon, bayan ya zauna ya gaishe dasu Abbah. Mamy tace ya kafar taka? Abdallah yace da sauki amma wallahi Mamy da kyar na tashi da asuba.

Abbah yace dama haka ciwo yake idan ya kwana, Allah ya soka ma an gyara maka tun jiya, daya kwana kila sai kayi fitsari a wando. Abdulhakim ne ya fito cikin shirinsa na zuwa makaranta.

Zama yayi yana fadin Yaya ina  kwana ya kafar? Abdallah yace lafiya lau, kafa da sauki. Kallonsa Mamy tayi tace harka karya? Abdulhakim yace yau alhamis ina azumi ai. Mamy tace haka ne na manta.

Abbah yace ina ruwan Ustazin gidanmu. Allah ya amsa ibadarka karika saka dan uwanka a addu’a ko ya rage son kwallo. Murmushi Abdallah yayi yace Abbah ai na rage son kwallo. Mamy tace da ka rage da jiya bakace zaka buga yau ba.

Abdallah yace nima fada nakeyi, taya wannan kafar zata buga kwallo, zanje dai nayi kallo. Mamy tace wallahi da nice kai zama zanyi agida na huta. Abbah yace kibarsa yaje, idan garin ihun kwallon aka sake famo kafar aikinmu kallon kukan gyara ne.

Dariya Abdulhakim yayi yace insha Allah ma baza’a fama masa ba. Mamy tace Allah yasa. Abdulhakim yace amin, ni natafi. Abbah yace sai kadawo, Mamy tace Allah ya bada sa’a ina Amal ita kuma bazata fito ba.

Da sauri Amal ta fito tana fadin Mamy na shirya fa. Yaya ina kwana ya kafar? Murmushi yayi yace lafiya lau sarkin makara, ke dai kullum sai kin makara kuma kinsan makarantarku kamar Secondary take tacika doka.

Amal tace ai babu abinda za’ayi mani. Mamy, Abbah na tafi. Murmushi sukayi suna fadin adawo lafiya Allah ya bada sa’a. Kallon Abdallah Abbah yayi yana fadin jiya munyi magana da abokina yace ya tura sunanka insha Allah list din da zai fito nan da wata biyu zaka samu aiki.

Mamy tace kai Alhamdulillahi, Allah mungode maka. Idan ya samu aikin ai ya rage wannan kwallon. Abdallah yace nagode Abbah, Mamy kwallota ta tsone maki ido wallahi. Mamy tace sosai ma.

Haka kawai kwallo tana sa Dana yana kwanan police station, kullum jiki cikin jin ciwo ba dole na tsani kwallo ba. Abdallah yace idan nazama babba acikin kwallo aikin ma ajesa zanyi sai dai kirika jin yau muna wannan kasa gobe muna waccan.

Wata rana ma kwallon duniya zamu buga. Dariya Abbah yayi yace ahaka zaka buga kwallon duniyar daga jin dan ciwo kana wani raki? Abdallah yace ai zan kara dagewa da training. Allah wata rana sai kun rika tsare Tv, agaba kuna jiran a hasko domin ku ganni ina buga kwallo da turawa.

Mamy tace Allah mun tuba, alamar karfi ai tana ga mai kiba. Nidai wallahi bana son kacigaba da buga kwallo, babu komai acikinta sai bakin rai da takesa mutune, ga wahala, yawancin ‘yan kwallo kowa zaka samesa da tabon kwallo.

Abdallah yace ai kyau kenan Mamy. Abbah yace babu wani kyau, kuma babu wani aikin da zaka aje saboda kwallo. Tashi ki kawo masa abinci yaci yasha magani. Turo baki Abdallah yayi yana fadin dan Allah Abbah. Mamy tace idan zaka hakura ma gara ka hakura, yanzu dai ka buga lokacin ka ne.

**** *****

Dariya sosai su Kamal sukeyi jin labarin da Salman ya basu yanda sukayi da Salma. Jabir yace shege Salman, ashe ka iya kuka. Salman yace ba dole ba, ina ganin zan rasa farin cikina abinda yafi kuka ma zanyi.

Kai wallahi nashiga tashin hankali jiya, da ace Salma batayi hakuri ba na tafi gida kila da ahanya zan buge wani ko kuma ni abugeni. Uhm, bazaku gane kalar son da nakema Salma ba. Yarinya kamila, mai sona saboda Allah.

Gata da hankali, ai duk wanda ya samu Salma amatsayin mata kawai yasamu rabon duniya, game da tarbiyar ‘Ya’yana ma ba’a magana, shiyasa akeson mutum ya auri mace saliha. Ko annabi cewa yayi mafi jin dadin duniya shine mutum yasamu MAR’ATUSSALIHA wato mace ta gari ba.

Kamal yace Allahu akbar, ashe dai mutumin ya iya jawo hadisi. Salman yace kai dai zauna nan kana ganin wasa. Nura yace sai akayi rashin sa’a kuma kai ba Salihi bane. Salman yace nima ai zan zama Salihin ina zama ango.

Ai wallahi Kamal na gode maka da wanann dabarar daka bani, da ace ban fadi haka ba ni nasan Salma bazata taba yarda dani ba, amma ina fada mata gwadata nakeyi lokaci guda ta yarda. Dariya suka kara kwashewa da ita.

Jabir yace to yakamata dai ka yima kanka fada, kaga duk cikinmu babu wanda ya tsaida macen dazai aura, idan ma akwaita ba cikin makarantar nan take ba, kai kuma taka kuna tare. Kada kaga Allah ya rufa maka asiri kace zaka cigaba da abinda kakeyi.

Wallahi da ace nine na samu Salma babu wacce zan kula acikin makarantar nan, ka tsaya ma a kallace kallacenka ya isa, amma maganar kai mata gidanmu kana dan debe kewa gaskiya ka daina.

Duk da ba Zina kake aikatawa dasu ba duk ranar da ka kuskura wata ta jaka har ka aikata Zina da ita ina mai tabbatar maka ko aure kayi bazaka daina bin mata ba.

Domin Zina bala’i ce, shiyasa duk iskancina  nake tsoronta wallahi. Salman yace wannan haka yake, kuma tun jiya nayi alkawarin na gama kai mata gidanku, ni har yawan ‘yan matana ma zanzo na rage kodan saboda Salma.

Kamal yace kaji Jabir da wata magana, ya mutum yanacin lokacinsa zaka hanasa? Salman fa MATASHI NE mai jini ajika, kuma yanzu ne yake cin lokacinsa. Su sauran mutanen da kake gani da Yara kasan irin abinda suka aikata lokacin suna MATASA? Kuma da suka fara tara iyali gashi sun dena ai.

Nura yace a’a Kamal, maganar Jabir fa gaskiya ce, wallahi Zina masifa ce, gasunan muna ganinsu wasu harda furfura amma sun kasa dena aikata ta. Dan  jin dadi dai zamuyi, amma wanann maganar ma a ajeta gefe daya.

Ina bayanka Salman, tunda har kana da wacce zaka aura gara ka dagama ‘yan matanka kafa, kowacce taji da kanta, ai Salma ma tana da hakuri, wallahi da wata ce sai tarika bibiyarka har ta gano boyayyen halinka.

Salman yace insha Allah zan kiyaye, jiya ni kadai naji abinda naji. Dariya suka sa masa.

Zarah da take zaune nesa dasu kadan tana duba littafinta kafin lokacin shiga class yayi, tun zuwansu ta gansu haka kawai batayi masu magana ba, kuma babu wanda ya ganta acikinsu, haka suka zauna suka shiga zuba zance.

Duk abinda suke fada tana jinsu. Tausayin Salma kawai ya kamata, duk da tasan Salman yana sonta amma tasan halin Salma, kullum burinta ta auri kamilin mutum badan komai ba sai dan Yaransu.

Kullum tana fada mata Salman mutumin kirkine, domin ko hannunta baya tunnanin tabawa duk tsawon shekarun da sukayi atare. Shiyasa kulum take yabonsa. Ashe abinda take tunani ba haka bane.

Kuma sosai taji dadin irin tubar da taji Salman yace yayi, sai dai kuma bataji yace ya daina kallon films din batsa ba. Tashi tayi hango motar Salma tana shigowa. Lokacin data fito ta gabansu sai suka dauka alokacin tazo wajen.

Salman ne yace Kawarmu ina kwana? Murmushi Zarah tayi tace Salman sannunku kun tashi lafiya? Kamal yace lafiya lau Hajiya Zarah. Jabir yace kawarki bata shigo ba kenan? Zarah tace bata shigo ba, amma naga kamar motar tace na hango.

Mikewa Salman yayi yana fadin jikina ya bani itace ma. Dariya suka sa, Nura yace lallai yakamata azo ayi aurenku idan yaso sai ku karasa karatun agidanku, wannan rashin kunyar har ina? Salman yace ai wallahi da Dady zai barni da tun muna aji 3 mukayi aure.

Murnushi Zarah tayi tace ai komai yazo karshe, kafin kuje service sai kuyi aurenku. Jabir yace wallahi kuwa. Wucesu Zarah tayi ta nufi wajen Salma. Kallonta Kamal yayi yana shafa fuska yace ni da Zarah zata amince mani ma ai da mun gyarota. 

Salman yace wallahi bazan baka ita ba, ai kyanka su Zee, amma Zarah tafi karfinka wallahi. Kamal yace nima wasa nakeyi, ina zan iya da kayan ustazancinta. Dariya suka sa Jabir yana fadin dade yafi maka.

Murmushi Zarah tayi tana fadin wai ni yau naga har wani haske fuskarki takeyi saboda fara’a. Bacin jiya mun rabu kamar zaki fashe saboda fushi. Dariya Salma tayi tace ai so ba karya bane.

Kinsan wani abu? Wai ashe Salman gwadani yakeyi…………….. Labarin yanda sukayi da Salman ta fadama Zarah, tana fadin bakiga yanda yake kuka ba. Ai har cewa nayi naji dadin wannan wasan da yayi mani.

Kinji yanda Salman yake fada mani kalaman soyayya, ashe dama ya iya fadarsu ban sani ba. Wallahi jiya da kyar nayi bacci saboda tsabar soyayyarsa da take kara ratsani. Gaskiya ina tausaya maku da bakwa soyayya.

Murmushi Zarah tayi cike da tausayin kawarta tace haka ne Salma, Allah dai ya tabbatar da alkhairin da yake cikin tarayyarku, kuma ki dage da addu’ar zabin Allah akan aurenku. Salma tace insha Allah tsakanina da Salman ma alkhairi ne babba. Tunda naji ya kwanta mani na san alkhairi ne. 

Zarah tace zanfi kowa farin ciki idan naganki adakin ki keda Salman kuna zamanku lafiya, amma kada ki ce ya kwanta maki bazaki kara addu’a ba. Salma tace kai Zarah wai meye kika damu da addu’a ayanzu bacin ada ba haka kike ba, kodai akwai wani abu ne? Zarah tace babu komai, kawai kinsan idan kana mugun son abu to ka dage da neman zabin Allah. 

Salma tace ai sai mun kafa tarihi, daga kanmu student zasu rika auren mate. Zarah tace Allah ya tabbatar mana da alkahairi. Dariya Salma tayi tace amin. Muje kada muyi latti.

***** ******

Wai ina Marusanda yake ne? Saurin fitowa Inna tayi tana daura zani tace lafiya Malan naji kana kwala ma Sardauna kira ko laifi yayi? Malan yace Sardaunan wa? Kema bazaki kirasa da sunansa ba.

Murmushi Inna tayi tace ai naga kaima wani lokacin har Dan Ghana duk kana kiransa. Tsaki yayi yace nidai yana ina? Inna tace dan Allah ka fada mani abinda yayi kake nemansa haka? Malan yace ina shawo kwana naga wata yarinya ta fito daga dakinsa shiyasa nake so yazo naji meya kaita dakinsa.

Salati Inna ta farayi tana fadin Marusandan ne yakai mace dakinsa? Gaskiya Malan idonka be gane maka dai dai ba, taya zakace wai Sardauna ya kai mace daki, yaron da babu ruwansa barsa dai da yawan kula mata.

Malan yace zaki fadi haka man, dama ai kece kike goya masa baya shiyasa yake abinda yaga dama. Yanzu kamar Sardauna, au Marusanda 🤣 za’ace kina basa kudin kashewa. Inna tace Sardauna kuma? Murmushi Malan yayi ya samu waje ya zauna yana fadin kibar sani dariya dan Allah.

Zama tayi tana dariya tace ai dole na saka dariya, kawai mutane suna zuwa suna zugo mani kai kashigo kana abinda ba halinka ba. Haka fa rannan kazo ka hausa da fada wai wani mutum yace ya rabu da diyarsa.

Naga kuma ‘yan mata da yawa sune suke binsa ba shine yake binsu ba, amma kai ka hau ka zauna kana ta masa fada. Idan fa da laifin Sardauna su ma yaran da laifinsu. Nifa wallahi banaso arika sama yarona ido haka kawai su cinye manishi aga yana ramewa arasa dalili.

Murmushi Malan yayi yace to me yaro, yau da ke kadai kika haifi Marusanda nashiga ukku agidan nan, koma menene ai yana da laifi, ni wallahi nagaji da wannan jan maganar da yake jawo mani.

Aure zanyi masa kowa ya huta. Dariya sosai Inna tasa tana fadin haba dai aure? Yanzu Marusandan zaka yi ma aure? Haba Malan, duka shekararsa fa 27 zai shiga ta ina ya isa aure? Malan yace koma 20 yake ni aure zanyi masa.

Duk rashin auren da ba’ayima MATASAN yanzu da wuri shine yake jawo barnar da ake samu. Zamanin mu taya za’a samu MATASHI kamar Sardauna wai ace beda mata. Kuma ana samun irin wannan barnar da tayi yawa akasa yanzu? Inna tace ai zamanin mu da nasu ba daya bane.

Komai canzawa yakeyi, muma zamanin Iyayenmu da kakannin mu ai ba kamar yanda ake mana sukayi ba, kaga kenan kowace al-umma da zamaninta. Kuma Allah ma yana rantsuwa da Zamani.

Addu’a itace abinda yafi kamata murika masa, amma batun aurema be taso ba, shida ko sisi baya dashi bare aje ga maganar gida, bayan kafi kowa sanin DARAJAR MUHALLI (tsohon littafi na).

Jinjina kai Malan yayi yace haka ne, tabbas MUHALLI YANA DA DARAJA, amma kuma ai nine zanyi masa komai, gidan ma nine zan saya masa kinga beda wata matsala. Inna tace idan ka saya masa gidan kaine zaka rika ciyar dashi? Malan yace idan yaga yayi aure dole zai nemi sana’a ai.

Inna tace idan ya fara sana’ar bata karbesa ba fa? Gashi ya tara iyali, auren zamanin nan kamar mace jira take akaita gidanta, wata tara nayi ta sullubo Da, shikenan an jefa rayuwar yaro cikin matsala.

Nidai ka barsa ya fara samun na kansa idan yaso ka saya masa gida, nima akwai ‘yan kudin da nake masa tari sai mu hada asaya masa gida me kyau idan lokacin auren yayi sai yayi. Murmushi Malan yayi yace to mai Da, yanda kikace haka za’ayi.

Amma kije ki kira manishi naji dalilin da yasa naga mace ta fito daga dakinsa. Kinsan fa shedan kullum burinsa ya dulmiyar da zuri’ar annabi, duk son da muke ma Sardauna dole sai mun rika sa masa ido gudun kada son ya zamar mana matsala.

Inna tace haka ne kuma, nima kullum fadan da nake masa kenan, amma tabbas nasan Sardauna baya kawo mata adakinsa, kila dai akwai dalilin shigarta, bara na kirasa muji daga bakinsa.

 Page  60 to65

Tambayarka nakeyi fa ka tsaya kana mani dariya? Hannu Sardauna yasa ya rufe baki dan ya tsagaita da dariyar. Inna tace wallahi Marusanda ka mai damu kakannin ka. Sardauna yace Inna maganar ce ta bani dariya wallahi.

Ya za’ayi na kai mace dakina, kullum Malan yana zargin ina kai mace dakina kawai saboda ina da ‘yan mata. Malan yace ba fa wani ne ya fada mani ba, da ido na na ganka taya zakace ba haka bane.

Sardauna yace to nidai babu wacce tashigar mani daki wallahi. Inna tace tunda ya rantse kila ba daga dakinsa ta fito ba. Malan yace tunda kace haka na yarda, amma ka sani duk ranar da gaskiya zatayi halinta to babu ruwana idan ka jawo abinda yafi karfinka.

Nace zanyi maka aure Innarka tace baka isa ba, to wallahi kashiga hankalinka, ka san dai kai ba yaro bane yanzu, ka kai mizanin da shari’a zata hau kanka, ka kiyaye duk wani abu da zaisa ka zubar mana da mutunci domin sunanka yayi kauri a unguwarnan.

Duk abinda akace ka aikata da yawan mutanan unguwar zasuce haka ne domin kowa yasan wannan halin naka na son mata. Turo baki Sardauna yayi kamar zaiyi kuka yace yanzu Malan baka yarda dani ba kenan? Tashi yazoyi yana alamun goge ido.

Jawosa Malan yayi yana fadin na yarda da kai Sardauna, kawai ina fada maka gaskiya ne, duk son da muke maka bazai hana mu fada maka gaskiya ba. Kamo hannunsa Inna tayi tace shikenan ya isa  Auta na.

Tashi ka dauko abincinka kaci kaji. Kara kwabe fuska yayi yace na koshi. Saurin kallonsa Malan yayi yace meyasa bazakaci ba? Sardauna yace kawai na koshi. Inna tace ko baka da lafiya ne? Girgiza kai yayi.

Tashi Inna tayi tana fadin bara na dauko maka taya zakace ka koshi bayan bakaci abinci ba. Bayan ta kawo masa abinci ta bude tana fadin gashi maza kaci. Malan yace haba Autan Inna sa kaci mana, ko auren kakeso ayi maka? Inna tace inajin dai saboda nace be isa aure bane yake fushi.

Dariya Sardauna yasa yace ni wallahi ban isa aure ba. Inna tace kuma kaga Jamila aure za’ayi mata tana gama makaranta. Sardauna yace wallahi sai tayi ko N C E ce, haba Inna meyasa kikeson ayima Jamila aure ne? Malan yace rabu da ita insha Allah Jamila bata da miji sai kai.

Sardauna yace nifa ba budurwata bace. Dariya sukasa Inna tace naga alama, shiyasa ai ka kasa zaune lokacin da kukayi fada. Sardauna yace ai laifi nayi mata, kuma  bana so Allah ya kama ni ne shiyasa naje na bata hakauri. Malan yace rabu da ita maza kaci abincinka.

***** ******

Cike bakin office din student affairs yake da mutane, gaba daya wajen hayaniya ce take tashi kowa da abinda yake fada. Zuwansu Salman kenan makarantar suka hango taro, hakan yasa suka nufi wajen.

Suna zuwa Kamal yace bara naje na jiyo mana abinda yake faruwa. Kutsawa yayi cikin mutane, wani ya tambaya anan yake fada masa abinda ya faru. Fitowa yayi ya iso wajen su Salman yana dariya.

Jabir yace lafiyar ka kuwa? Kamal yace wallahi ‘yan iska basu karewa aduniya, yanda kasan kullum sabon kyankyasa akeyi. Idan yau kaji wani abun na gobe sai yafishi. Salman yace wallahi dadina da kai idan zaka bama mutane labari sai ka gama ja masu aji.

Kamal yace wai wasu ‘yan iska aka samu ‘yan aji daya sun yima wata yarinya fyade jiya da dare bayan ta tashi daga karatu. Kasan halin sababbin zuwa, itama yarinyar sabuwar zuwa ce. Idan suka shigo makaranta yanda kasan da tsiya haka suke dagewa wai su ga sababbin ‘yan boko.

Taya ina mace zan rika kai wannan lokacin a area classes wai ina karatu, to ko karatun final year nake ai bazanyi dare har haka ba bare kuma first semister exam a year 1. Wai fa wajen karfe 12 na dare ta gama karatu zata koma hostel suka tare ta.

Kuma dan rashin hankali harsu biyu sukayi mata fyade. Nura yace dukansu dai sababbin zuwa ne? Kamal yace Emana, mazan wai ‘yan kauyen Katsina ne wani gari ko Tsauni naji ance. Jabir yace haba ko naji.

Kace mani gardawan kauye ne da suka samu sa’ar shiga Jami’a shine sukazo suka sauke maitarsu akan baiwar Allah. Ai tunda ka fara magana jira nake ka gama nace maka ‘yan wane gari ne.

Ashe kuwa hasashena yayi dai dai ‘yan kauye ne. Salman yace yanzu ina yarinyar take? Kamal yace wai tana asibiti bata ma san inda kanta yake ba. Tsaki Jabir yayi yace wannan abun haushi da yawa yake.

Iyaye suna can suna farin cikin diyarsu tazo karatu sai dai suji mugun labari, shikenan sun lalata mata rayuwa, kuma bazata cigaba da karatun ba. Nura yace idan nine mahaifinta wallahi kinbar makarantar kenan.

Kamal yace nikam idan nine mahaifinta wallahi sai kinyi karatu mai zurfi ma, amma bazaki dawo wannan makarantar ba domin labarinta ya baza makaranta bazata ji dadin karatu ba.

Amma dole zan sama maki wata makaranta domin rayuwarta ta gama lalacewa, ko zata samu miji sai wani iko daga Allah dan duk wanda zai dauketa saura zai dauka. Salman yace gaskiya ne, ko nine mahaifinta gara taje tayi karatu.

To yanzu wannan taron na meye? Kamal yace wadan da sukayi fyaden ne aka kama wai lokacin da abun ya faru wani maigadi ya kamasu shine yayi saurin kiran wani maigadin suka ritsasu.

Shinefa mutane suka taru yau da labari ya bazu. Jabir yace ai nasan korarsu za’ayi. Kamal yace yanzu haka jiran zuwan Iyayenta akeyi dan naji ance Babanta mai kudi ne, ‘ yar Zariya ce yarinyar.

Nura yace aiko nasan har kotu sai sunje. Juyawa sukayi jin karar mota. Jabir yace ai ga Yallabai nan yazo. Salman yace da ganin yanayin tukinsa ransa abace yake. Nura yace ai babu dadi ace kana shugaban makaranta kuma ace an samu irin wannan case din a makarantarka.

Yanzu zakaji gidan redio ya dauka kamar suna jira, kafin rana sai kaji Inda ranka sun fada. Matsawa mutane suka farayi ana bama Yallabai hanya ya shige ciki. Yana shiga wasu motoci guda biyu suka karaso.

Dasauri wani yafito ya bude kofar baya, wani babban mutum ne fari ya fito, da ka ga fuskarsa zaka gane yana cikin tashin hankali. Idonsa dauke da glass baki haka mukarrabansa suka take masa baya yashige ciki.

Kafin su gama shiga motar ‘yan sanda ta iso. Nan take sauran student suka matsa baya. Suna shiga babu bata lokaci suka fito da masu laifin sai sunne kai sukeyi. Kowa da abinda yake fada haka aka sakasu mota suka bar makarantar.

Wannan mutumin ne suka fito shida Yallabai, kowa ya nufi motarsa suka bi bayan su. Kamal yace da alama wannan shine mahaifin yarinyar. Jabir yace shine mana, ga motar nan da lambar Zariya.

Salman yace mutafi da alama yau babu malamin da zeyi lecture. Kamal yace naji ana fadin wadan da zasuyi exam yau ‘yan year 1 an daga masu exam din sai Wednesday. Jabir yace muje dai mu tabbatar kada mutafi.

Salman yace kuje nide wajen Salma zanje musha fira tunda babu lectures. Jabir yace malan Bello ne kawai dama zai karasa mana tunda next week mid semister test zamu fara. Bara muje sai munyi waya. Salman yace shikenan sai kun dawo.

****** *****

Kai Aminu! Aminu! Tashi Aminu yayi yana leken wanda yake kwala masa kira kamar wani yaro. Iro ne yace wane dan rainin wayau ne yake maka kiran Almajirai? Aminu yace shine nake leke naga ko waye.

Da gudu wanda yake kwalama Aminu kira ya karaso sai haki yakeyi. Wani dan kusa da gidansu Aminu ne, kusan tare suka taso shida Aminu sai dai tunda Aminu ya fada harkar siyasa suka raba hanya danshi dan kasuwa ne.

Daure fuska Aminu yayi yace kai Usman lafiya kake kwala mani kira kamar naci ban biya ba? Usman yace maida wukar, nima dole ce tasa na taho wajenka badan halinka ba. Aminu yace dalla idan zaka fadi abinda ya kawo ka wajena ka fada mani.

Usman yace ba wani abu bane, Mahaifinka ne ya fadi gashi can an nufi asibiti dashi a sume. A zabure Aminu ya cafko Usman yana fadin wane asibiti aka kaisa? Cire hannun Aminu Usman yayi yana fadin asibitin Kuroda.

Juyawa Usman yayi yabar wajen. Cike da tashin hankali Aminu yace Iro bani wayarka na kira Mai kano banida ko sisi a hannuna nasan kuma dole a nemi kudi a asibiti kuma nasan Mama bata da kudi.

So biyar Aminu yana kiran wayar Mai Kano amma bai dauka ba. Tsaki Aminu yayi yana fadin shima dan iskan yaki daukar wayar. Iro yace kara kira ka gani. Yana kira bugu 3 aka dauka. Aminu yace yallabai Aminu Jungle ne.

Wallahi Babana ne aka kaisa asibiti asume shine nace kozan samu wasu ‘yan kudi awajenka kasan yanda yanayin yake. Shiru yayi yana sauraron abinda Mai Kano yake fada masa. Ya mutsa fuska yayi yace shikenan nagode sai ka aiko muna Kuroda.

Kashe wayar yayi yana tsaki. Iro yace lafiya dai? Aminu yace wallahi wannan mutumin baida mutunci, wai duk wahalar da nake masa amma kasan me yace mani? Dan Ubansa cewa yayi wai jiya ya bayar da kudin hannunsa amma zaiba yaronsa dubu 1 ya kawo mani.

Iro yace to me dubu 1 zatayi maka? Aminu yace ka barsa, idan be bada don Allah ba zai bada dole, wallahi matukar wani abu ya samu mahaifina sai na masa rashin mutunci, kuma sai na fanshe kudina wallahi. Muje naga halin da yake ciki.

 Page  65 to70

Da kaninsa ya fara cin karo ya fito da gudu yana kuka, ko takan mai Adedetar Aminu be tsaya bi ba ya nufi kaninsa jikinsa yana rawa. Iro ne ya sallami mai Adedetar yabi bayan Aminu.

Aminu yana zuwa ya kama Kaninsa yana fadin kai Yusuf lafiyar ka ina Baban? Ture hannun Aminun Yusuf yayi yana fadin ni ka kyaleni, dama haka kakeso yau bakin cikin ka ya kashe Baba sai kaji dadi.

Zaro ido Aminu yayi jikinsa yana rawa yace kana nufin Baba ya rasu? Be tsaya basa amsa ba ya wuce domin nemo motar da zata daukesu. Da gudu Aminu ya karasa cikin asibitin, hanyar da yaga Yusuf ya fito nan yabi.

Tun kafin ya karasa dakin da aka kwantar da Babansu ya hango Mamarsu a duke tana kuka. Besan lokacin da yaji wasu zafafan hawaye suka zubo masa ba. Da kyar yaja kafarsa ya karasa inda take.

Dukawa yayi yana wani irin kuka a kusa da Mamarsu. Dago kai tayi jin alamun mutum a wajenta. Wasu sabbin hawayen ne suka zubo mata ganin Aminu. Sosai yake kuka yana fadin shikenan na shiga ukku Mama.

Nayi silar mutuwar mahaifina, wallahi nine na kashe sa. Dafasa Mama tayi itama tana kuka tace ya isa haka Aminu kada ka tara mana mutane, koma menene Malan lokaci yayi, babu wanda ya isa ya kashe wani sai da izinin Allah.

Kayi hakuri muje a bada gawarsa mutafi dashi gida domin ayi masa sutura, na kira Malan Babba( Yayan Babansu) na fada masa yace zai fadama sauran ‘yan uwa sai su wuce can gida.

Haka Yusuf ya samo wani mai Taxi nan suka samu aka gama komai da taimakon wani dan unguwarsu ma’aikaci ne anan asibitin. Haka suka nufi gida kowa yana kuka. Lokacin da suka isa gida mutane sun cika kofar gidan.

Da kyar Mama ta fito fuskarta a rufe tashige cikin gida, Malan Babba ne da wasu ‘yan uwansu suka dauko gawar suka shiga da ita cikin gida. Kafin wani lokaci aka shirya Baban su Aminu. Haka aka nufi makabarta dashi kowa yana kuka.

Bayan sun dawo haka aka cigaba da karbar gaisuwa. Aminu da abokansa suna gefe guda yasha wata jallabiya, duk wanda yagansu yasan ‘yan chaku ne, kowa da kalar shigarsa. Sosai Aminu yasha kuka, babu abinda yake tunawa sai yanda suka rabu da Mahaifinsa.

Tun da yayi masa magana a majalissarsu be kara sashi a ido ba sai gawarsa. Lokacin da zai fita da safe sai da Mamarsa tace yaje ya duba Maihaifinsu amma yace sauri yake Mai Kano yana kiransa, tunda Baban bacci yakeyi idan ya dawo zai dubasa.

Tunda ya fita bai dawo ba ya wuce wajen abokansa sai gashi ya mutu basu hadu ba. Kifa kansa yayi saman kafafuwansa yana wani irin kuka. Wanda ya tafi domin ya gani har yanzu bezo ta’aziyar Mahaifinsu ba.

Ya kamata ace dashi akayi jana’iza ma, amma Iro yace daya kirasa ma cewa yayi ayi masa ta’aziya zaije meeting ne idan ya dawo zai shigo. Dafasa Bala yayi yana fadin kayi hakuri Aminu duk mai rai mamaci ne.

Aminu yace dole nayi kuka Bala, shikenan na rasa Mahaifina kuma ace mutanan da muke ma wahala bazasu iya barin abinda suke ba suzo mana gaisuwa. Kiransa fa naje har Mahaifina yarasu amma kaga wai meeting yaje.

Bala yace kayi hakuri, dama haka rayuwa ta gada, ya muka iya tunda sune manyan kasa, tunda haka sukace dole muma mu kwatar ma kanmu ‘yanci. Kada kace zaka nuna masa bacin ranka. 

Aminu yace shikenan, nagode Bala, dan Allah kayi hakuri da abubuwan da nayi maka. Bala yace bakomai, nima ka yafe mani. Aminu yace komai ya wuce. Haka suka ci gaba da karbar gaisuwa.

**** ****

Yanzu shikenan Mamy bazan fita ko kallon kwallon nayi ba? Mamy tace haba Abdallah, meyasa baka tausayin kanka ne, kafarka fa bata karasa warkewa ba so kake kaje akara famo maka ita? Kwabe fuska Abdallah yayi yace gaskiya Mamy nayi missing kwallo.

Amal tace to ba kana kalla a Tv ba. Harara ya buga mata yace waya fada maki da kallon Tv da zahiri daya suke? Kina ganin su Kabeer basa zuwa sai babu ball, idan kuma zasu buga wasa sai dai su barni ni daya.

Amal tace to Mamy ki barsa yaje mana idan aka famo masa kafar ai sai akara gyarawa. Pillow ya wurga mata yana fadin kaji muguwa, wato so kike akara kama mani kafa kenan, to ba bakin ki ba.

Dariya Abdulhakim yayi yace wallahi Mamy Amal muguwa ce, yanzu ko Mamy ta barsa ya tafi ai kince kada yaje amma kece kike rokon abarsa. Amal tace ai gani nayi ya dage abarsa shiyasa.

Abdallah yace rabu da ita Abdul, na dade da sanin Amal ‘yar adawata ce, duk lokacin da zamu buga Ball kullum addu’arta Allah yasa aci mu. Yarinya idan na fara maki addu’a sai kinyi kuka.

Dariya Mamy tayi tace wace addu’a zakayi mata? Murmushi Abdallah yayi yace kibarta kawai Mamy, kullum zan rika mata addu’a Allah yasa duk kwalliyar da zatayi kada tayi kyau. Dariya suka kwashe da ita.

Abdulhakim yace gashi kuwa Amal akwai son kwalliya kamar mai aljanar kwalliya, gashi kuma makarantarsu ba’a barinsu yin kwalliyar. Turo baki Amal tayi tana fadin ai dai ko yayi addu’ar bazata karbu ba.

Abdallah yace shikenan Allah ya kaimu gobe wallahi zakice na fada maki. Dariya Mamy tayi tana fadin nide kubar mani Auta ta haka, ai ita ko batayi kwalliya ba Allah ya bata Natural Beauty.

Abdulhakim yace haba Mamy, Amal ce keda Natural Beauty? Yarinyar da kullum godiya take ma kamfanin da sukeyin hoda. Dariya Abdallah yasa hada kifawa yana fadin wallahi Abdul ka iya sharri.

Mikewa Amal tayi tana buga kafa kamar zatayi kuka tabar wajen tana fadin insha Allah daga yau ka gama cin kwallo. Dariya sosai sukeyi mata. Sallamar Kabeer ce ta sa suka tsagaita dariyar.

Shigowa yayi yana fadin lallai mutumina ka warke. Dukawa yayi yana fadin ina wuni Mamy ya mai jikin? Mamy tace lafiya lau, mai jiki gashi nan yana rigimar abarsa yatafi kallon Ball. Kabeer yace ai na dauka an barsa shiyasa yakirani yace na biyo mutafi tare.

Kallonsa Mamy tayi tace ashe har waya kayi azo atafi da kai? To ni dai babu ruwana, dama dokar Abban ka ne, sai kabari idan yadawo ka tambayesa. Kamar Abdallah zaiyi kuka yace nide dan Allah Mamy kibarni na tafi.

Kinsan idan na fada ma Abba bazai barni ba. Kuma yau nefa za’a buga Ball din. Mamy tace haka kawai wani abun ya faru da kai yace laifi nane, ka dauki waya ka kirasa idan yace ka tafi sai kaje.

Waya Abdallah ya dauko yashiga kiran Abbansa. Yana dauka suka gaisa Abdallah yace Abbah dama Kabeer ne nace yazo ya tukani muje kallon Ball shine nace bara nakira na fada maka. Abbah yace na fada maka idan kaga ka fita zuwa Ball sai an kwance wannan daurin.

Kayi hakuri kaje ka kalla a dakin ka. Abdallah yace dan Allah Abbah wallahi bazamu dade ba, kuma bazan ja kowa fada ba. Abbah yace kasan dai bazan hanaka fita saboda jin dadina ba ko? Nasan halinka da zuciya, da a ce buga kwallon zakayi ma da sauki.

Duk wasu abubuwan da masu kallo zasu fada bazaka ji ba kana cikin fili, amma kana zaune a cikinsu wani na iya fadar abinda beyi maka ba ku kama fada, kayi hakuri kawai nace maka, idan kabi maganata zakaga hasken abinda nake nufi.

Kashe wayar yayi. Abdallah da wasu kwallan bakin ciki suka cika masa ido yayi saurin tashi ya nufi daki ko takan Kabeer be bi ba. Murmushi Mamy tayi tace Kabeer tashi kayi tafiyarka da alama be barsa ba.

Tashi Kabeer yayi yace na wuce Mamy, Abdulhakim sai anjima. Mamy tace sai ka dawo, idan ka dawo sai ka biyo ka basa labari. Kabeer yace tunda be je ba gara na kyalesa. Bayan ya fita Mamy tace Abbah ya tabo joni.

Dariya Abdulhakim yayi yace na rasa me Yaya yakeji a kwallo, ni dama Abbah ya barsa wallahi ya bani tausayi. Mamy tace tunda kaga Abbanku ya hanasa fita akwai dalili, kasan yanda wajen kwallonsu yake.

Duk lokacin da za’ayi kwallo da rigima suke rabuwa, kasan Yayanku da zuciya, hanasa zuwa shiyafi alkhairi. Abdulhakim yace haka ne, Allah dai ya fito masa da aikinsa kowa ya huta. Mamy tace amin.

**** ***** 

Haba Sardauna, shikenan kwana biyu ka manta dani, idan nakira wayarka ma baka dauka bansan menayi maka ba shiyasa rannan da Umma ta aiko ni unguwarku naje har kofar dakin ka, harna bude kofar zan shiga na hango Babanka sai nayi saurin rufe maka kofar nayi gaba.

Saurin kallonta Sardauna yayi yana fadin dama kece wacce Malan yake ta mani fada akanta yaga mace tafito daga daki na? Amma wallahi kin raina mani wayau, da ace Malan bezo ba shigowa zakiyi da gaske? Tabe baki tayi tace gashi kuwa har na bude kofa.

Haba Sardauna, saboda kaga ina sonka shine kake mani wulakanci, kuma ai ba nice nace ina sonka ba, kaine ka fara furta mani kalmar so, sai da ka bari na kamu da sonka kuma sai ka guje ni.

Dama an fada mani halinka nice ban yarda ba, zuwanka yasa duk na kori samarina, akwai saurayina da mukayi alkawarin aure kowa agidansu ya sanni yasan nice zai aura amma zuwanka yasa nayi masa wulakanci karshe daya rabu dani kawata yaje ya aura suna can abunsu harta haihu.

Murmushi Sardauna yayi yace da nazo wajenki na taba cewa bana so kirika kula kowa? Lallai Khairat wautarki da yawa take, ni yanzu ko cewa akayi na fito aurenki ai kin mani girma, kawai daga nazo mudan zama Friends shikenan sai ki dauki abun da gaske.

Kuma koda gaske nake sonki idan naga kinzo dakina wallahi bazan aureki ba, taya zan auri macen da take iya shiga dakin namiji, duk da kin girmi Jamila amma ta fiki hankali. Lokacin da taje dakina tsayawa tayi a waje ta kwankwasa na fito.

Amma ke kawai shiga kikayi niyar yi, yanzu da ace Malan irin Iyayen nan ne masu zafin zuciya haka zai mani abinda yaga dama batare da nasan laifin dana aikata ba, kuma da idonsa ya ganki, yanayin yanda kikayi kowa zai dauka daga ciki kika fito.

Gaskiya abunki ya girme mani, dama ganin kwana biyu bamu gaisa ba yasa nace bara nazo yau na dan rage zafi, amma tunda haka kike inaso daga yau ki manta dani, dama karfin haline irin nawa, domin kin girme ni.

Juyawa yayi yana fadin sai anjima. Saurin shan gabansa Khairat tayi tana fadin haba Sardauna dan Allah kada kayi mani haka, wai kai baka gudun alhakin matan da kake yaudara ya tambayeka? Shi NAMIJI AI BAYA KADAN. Ni wallahi na yarda a hakan zan aureka koda nayi kani na biyu da kai.

Murmushi Sardauna yayi yace sai dai nayi maki fatan Allah ya kawo maki mijin aure, amma wallahi yanda nake karamin MATASHI bazan auri babbar budurwa irinki ba. Wuceta yayi ya barta da cizon yatsa.

**** *****

Yauwa Bala anshi wannan layar, zakaje makabarta ka samu tsohon kabari ka binne ta aciki, wannan kuma ka samu yaron da akayima sabuwar kaciya ko anan unguwarku ne ka basa wannan alawar ya shanye, yana shanta aljanu zasu shanye jinjnsa sai dai Iyayensa su haifo wani.

Dan Allah wannan karon Bala kada kayi kuskure, kaga zaben nan saura sati 1 ayi primary election, kuma Malan yace dole kafin sati daya yazo yakeso ya gama komai, idan har satin ya cika ban aikata abinda yace ba bazan sami wannan kujera ba.

Kaga ni Babban mutum ne, kowa yana ganina da mutunci baze yuwu naje ina neman karamin yaron da akayima kaciya ba na basa alawar ya sha ba. Kai ko zaka iya zuwa har asibiti ma ka samo mana yaro.

Kuma duk wanda ya ganni a makabarta da dare zai iya zargin wani abu kasan masu gadin makabarta basu da amana, kona sayesu zasu iya tona mani asiri, shiyasa dana fadama Malan yace na samu makusancina wanda nasan zai iya aikin batare da wani kuskure ba na bashi yayi.

Wannan dalilin ne yasa na zabeka, domin duk cikin yarana nafi yarda da kai, ko wani ya ganka dama ba wani saninka akayi da mutunci ba babu abinda za’ayi maka. Amma dan Allah ka lura da kyau.

Bana so asamu matsala, idan kuma kayi wasa aka kamaka kada ka kira sunana domin laifinka ne. Murmushin gefen baki Bala yayi yace baka da matsala Maigida, amma zaka bada kudin da zan bama Maigadin makabartar.

Sannan akwai wata hidima da nakeso nayi da kudi wannan karon ina son abani da kauri. Dariya Yallabai yayi yace Bala na wajena, ai baka da matsala, kawai kaje ka aikata abinda na saka zan maka sallama mai tsoka. Bala yace idan da hali abani kudin yanzu domin kafin dare za’azo akarba.

Yallabai yace shikenan ai aiki,mai hadari zakayi ko nawa ne zan baka. Ga wannan ka sallami maigadin, wannan kuma gashi naka ne. Washe baki Bala yayi yana fadin Allah ya biyaka Maigida.

Baka da matsala idan ka bani aiki kawai kaje kayi kwanciyarka kasha bacci, nizan iya hana kaina bacci domin na nema maka farin ciki. Murmushi Yallabai yayi ya kara ciro kudi yace ga wannan ka kara. 

Sallama yayi masa yana fadin saifa dare yayi zakaje makabartar, gobe kuma kada ka bari yamna tayi baka bada alawarba. Bala yace baka da matsala. Mota yshiga yabar wajen. Murmushi Bala ya cigaba dayi yana juya abubuwan da aka basa.

Leave a Comment

error: Content is protected !!