
Mayafin Sharri Hausa Novel Complete
MAYAFIN SHARRI
Page 1
©️Hassana Ɗanlarabawa.
EXQUISITE WRITERS FORUM
Rikicin duniya da mai rai ake yi. Na ƙara yarda da wannan karinmaganar ne a sa’ilin da duniyata ta rikice, na buɗi idanuwa na tsinci rayuwata a bigiren da ban taɓa hasashe ko tsammani ba. Rayuwar da na samu kaina a duniyata ta yau ita ke sake alamta mini ruwan tsari na akuya ne, farau-farau na mai gata ne. Kasancewata mai rangwamin gata ya taka muhimmiyar rawa wajen zama na cikin waɗanda rayuwata da tasu ta sha bam-bam. To amma ai ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi, shi ya sa damuwata takan ragu a duk lokacin da na tuna watarana gaskiya za ta yi halinta, kuma komai ya yi farko, yana da ƙarshe!
“Kai ajawo wai me ka yi aka sanƙamo ka zuwa wurin nan ne? Domin tsarin ka sam bai yi kama da na ma su aikata laifi ba.”
Maganar da na ji a kusa da ni kenan wadda ta saka ni ɗago kaina da ke matse a tsakanin guiwoyin ƙafafuwana, na bi gajeren baƙin saurayin da ke tsaye a kaina da kallo, ya zuba mini jajayen idanuwansa yana jiran amsa daga gare ni, amsar da ni kaina ban sani ba. Maƙoshina a bushe yake ta yadda ko yunƙurin magana na yi azaba ce take ratsa maƙwallatona, amma haka na daure na yi yunƙuri har na samu nasarar ba shi amsa da ce wa, “Yadda ka buɗi idanuwa ka gan ni a wurin nan ni ma haka na buɗi idanuwa na tarar ƙaddara ta sauya mini muhallin zama.”
“Ban gane ba.” Ya ambata da wata irin murya da ta sake yamutsa lafaffen cikina da ya kwashi tarin sa’o’i ba tare da ya samu tagomashin abinci ko ruwa ba.
“Kamar dai yadda ka ji tun farko, ban san dalilin kawo ni nan har aka rataye rayuwata ba, kawai tsintar kaina na yi ba tare da sanin dalilin zuwana ba.” Na sake maimaita masa.
Dogon baƙin mutum kakkaura, wanda ke kwance daga gefen mu shi ne ya kwashe da dariyar da sai da na hanzarta kallon shi, ya nuna ni da yatsansa yana kallon wanda ke kusa da ni, ya ce, “Kai Baharu wai mene ne dalilin ka na son sanin abin da ya kawo shi wurin nan, ni fa kallo ɗaya na yi masa na gane dalilin zuwan nasa.”
Sai na tsinci kaina cikin ɗoki da fatan ya faɗi dalilin zuwan nawa, ko zan rabauta da sanin dalilin tunda ni ma lalube nake ta yi cikin duhu.
Kafin ma wanda ya ambata da Baharu ya tofa tasa tuni ya ɗora bayani da ce wa.
“Kai da ganin wannan santalelen saurayin soyayya ce ta kawo shi wurin nan, ma’ana ya shiga cikin wata giya ta soyayya da ta gusar masa da hankali, bai tashi farkowa ba sai a ofishin ‘yansanda.”
“Kambu! Amma idan haka ne kuwa ya tafka ɗingimemiyar asara Rijalu. Duk namijin da ya tsinci kansa a ofishin ‘yansanda dalilin soyayya kawai a nemi zani da fatala a ba shi ya ɗaura, don daga ranar sunan shi Salamatu.” Kalaman da suka fito daga bakin Baharu kenan.
Rijalu ya kwashe da dariyar shakiyanci. Duk muzancin da suke mini bai dame ni ko ya ɗaɗani da ƙasa ba, ambaton kalmar soyayya da Rijalu ya yi shi ne abin da ya ja linzamin tunanina. Bayan mahaifina da yake a ƙoƙon raina babu kamar masoyiyata Zainab da na rayu da soyayyarta tsawon lokaci, a take zuciyata ta shiga canki-cankar yanayin da suka shiga na rashin ganina a halin yanzu ita da mahaifina.
Kwana uku kenan da na rasa murmushi a kan fuskata, sai tarin takaici da ƙuntacewar zuciya a bisa halin da na tsinci kaina, ban san me ya kawo murmushin kan fuskata a wannan gaɓar ba, har ma na dubi Rijalu na ce masa.
“Da sanadin soyayyar Zainab na samu kaina a wurin nan ba zan taɓa damuwa ba, saboda ko babu komai sunan Habibullah zai shiga cikin jerin mazan da suka yi gwagwarmaya a soyayya, sai dai kash! Tunaninka da hasashenka bai zana maka daidai ba. Kuma ni ma a ɗokance nake da son sanin wanda ya shirya mini daudawar burmi!”
Baharu ya ce, “Daudawar burmi? Me hakan ke nufi?”
Na ce “Wanda ya ɗana mini tarkon mugunta na sharri kuma ya ritsa da ni, to amma ku me kuka aikata da ya janyo muku sanadiyyar zuwa wurin nan?”
“Me ya sa kake son ji?” Rijalu ya ambata yana wata irin dariya tamkar zaman shi a wurin bai dame shi ba. Na sauke numfashi ina ci gaba da kalato miyan da zan haɗiya, domin maƙoshina ya samu danshin da zan iya magana ba tare da na wahala sosai ba, da ƙyar hakan ta samu, daga nan na dubi Rijalu na ce.
“Domin na ƙara ilimi.”
Baharu ne ya dube ni ya fara magana kafin Rijalu ya yi, “Tun daga siffarmu idan ka dube mu za ka san babu wani ilimi a tare da mu balle mu ɓarar ka kwasa, ni nan da ka gan ni ɗandaba ne, faɗan siyasa muka yi ni da wani na yanke shi a kumatu shi ne dalilin zuwana wurin nan.”
Na jinjina kai “Ka ɓarar na kwasa!” Ya bi ni da kallo a yayin da na mayar da hankalina kacokan! Kan Rijalu, ina shirin magana ya tari numfashina.
“Ni ɓarawo ne! Sata na yi, shi ne dalilin zuwana wurin nan.”
“Me ka sata? Kuma wa ka yi wa satar” Na tambaye shi cike da ƙarfin hali.
“Kai Lauya ne?” Rijalu ya ambata yana miƙewa tsaye tare da zagaye akurkin ɗakin da muke ciki.
“Ko ɗaya; mai neman ilimi dai.” Na amsa.
Ya juyo ya zuba mini ido har na ji faɗuwar gaba, amma na dake na ci gaba da kallon shi da sauraren abin da zai faɗa.
“Watarana da ta shuɗe ina cikin tafiya kawai na ci karo da wata haɗaɗɗiyar mota a gefen titi, mamallakin motar ya fito daga ciki muƙarrabansa suna take masa baya, karaf! Idanuwana suka kai kan wata jaka da ke gaban motar a yayin da suka manta ba su zuge gilas ba, suna ƙoƙarin shiga wani super market ne a lokacin na mamaye su na zura hannuna cikin motar na ɗauke wannan jakar, ashe ban sani ba ni na yi shuka ne a idon makwarwa, domin ɗaya daga cikin su tuni ya gan ni har ma ya janyo hankalin ragowar muƙarraban zuwa kaina, ban san na iya mugun gudu ba sai a ranar, domin da na zaburi ƙafafuwana duk da wannan ƙibar tawa gudu na yi ba ɗan kaɗan ba.”
“Sun yi nasarar kama ka kenan?” Na yi azarɓaɓin tambayar shi.
Ya tako ya zauna a gabana muka fuskanci juna, ya ɗora da ce wa.
“Sai da muka yi gudu mai yawa na waiwaya bayana na ga kamar sun daina bi na, sai na yi wuf! Na afka zauren wani gida na ɓoye jakar a bayan ƙyauren gidan, sannan na fito na ci gaba da gudu, ashe talala suka yi mini domin kawai ban ankara ba sai ganinsu na yi a gabana sun damƙe ni, wannan dalilin ya sa a ka kawo ni wurin nan domin na fito da jakar, ni kuma na yi alƙawarin ba zan fito da jakar ba har su gaji su sake ni, daga nan ne zan nufi gidan da na ajiye jakar na ɗauki ajiyata. Baharu kuma a nan na tarar da shi, daman tuni na san shi unguwarmu ɗaya da shi.”
Gabana ne ya yanke ya faɗi a take, sakamakon wani tunani da ya ɗarsu a raina wanda na tabbatar ina da alaƙa da wannan jaka da Rijalu ya ba ni labari. Komai ya fara dawowa kaina kamar ƙiftawar ido da bisimillah.
******
Na dawo daga kwaso ladan da ni kaina ban san adadin shi ba, kasancewata malamin makarantar dare mai koyar da ɗalibai karatun da ya shafi addini. Misalin ƙarfe goma saura minti takwas na dare. Na kutsa kaina zauren gidanmu da duhu ya mamaye dunɗum!’ Yar ƙaramar wayata na zaro daga aljihuna na kunna fitilar da ke jiki na haska zauren, anan ne ma na ankara da lokaci bisa la’akari da kallon agogon kan fuskar wayar tawa. Na riƙa haska saƙo da lungu na cikin zauren ko zan yi arangama da ɓerayen da suke takura mana da motsi da kuka tsakar dare, ba iya nan ba har ma da ɓarnar da sukan shiga su yi mana. Ban yi katarin ganin ko guda ba hakan ya sa na mayar da ƙofar ina shirin saka sakata domin na kulle, na je kuma na yada haƙarƙarina domin hutar da jikina gajiyar da ya kwasa a wunin ranar.
Daram! Sautin da ƙirjina ya bayar kenan, na yi baya da sauri ina ƙwalalo idanuwa, na sake ɗaga wayar da ke hannuna na haska bayan ƙofar. Tabbas idanuwana ba gizo suke mini ba, cikin matuƙar mamaki da faɗuwar gaba na yi bisimillah na ƙarasa gaban jakar da ke maƙale a bayan ƙofar, sai da na karanta ayatul kursiyyu da ƙula’uzai kafin na iya ɗora hannuna kan jakar, alfanun hakan ko da jakar ajiyar aljanu ce to komai zai zo mini da sauƙi tunda na ambaci Allah.
Nauyin jakar da yadda ƙirjina ke tsallen bugu ya sabbaba mini tarin fargaba. Na riƙa juya jakar a hannuna zuciyata na ta ƙissime-ƙissimen hasaso dalilin samuwarta a zauren gidanmu. Na karɓi karatun da zuciyar tawa ta biya mini wajen raya mini na buɗe jakar domin na ga abin da ke ciki, ƙila ta haka ne zan samu nasarar cafko dalilin samuwarta a zauren gidanmu.
‘Dimmu ƙwalin ƙwal!’ Sauti ne da yake fita a yayin da a ka buga mandiri, ban sani ba ko ni ma akwai mandirin a zuciyata, ko kuma zuciyar tawa ce ta yi kwaikwayo da irin sautin a yayin da idanuwana suka yi arba da maƙudan ƙuɗaɗen da ban san adadinsu ba. Daɓas! Na zauna saboda tsuguno ya gagari ƙafafuwana da ke mazari, na yi namijin ƙoƙari wajen janyo numfashin da ke neman gagarata, na zuba wa kuɗaɗen da ke gabana idanuwana, suna ta walwali sababbi fil da su. Tunda Allah ya ƙagi halittata a cikin uwata ya ba ta damar haihuwata ta kawo ni gidan duniya. Ta koma ga Ubangiji lokacin da nake da buƙatar ta domin ba ni kulawa kamar sauran yaran da suke da uwa. Ta bar ni da mahaifina da nakasar makanta ta hau kansa bisa ga idanuwansa da suka gamu da ƙaddara dalilin yawaita kukan rashinta da ya yi. Har na yi gararambar ƙuruciyata na girma na zama cikakken mutum. Kawo yanzu ban taɓa ganin kuɗaɗe masu yawa irin haka ba sai a majigin kallo. Na dafe cikina da hannu ɗaya sakamakon karta mini da ya yi a dalilin maƙalalliyar yunwar da ta taso mini, rabona da abinci tun kokon da na samu na kwankwaɗa da safe, kuma na sanya ƙafafu na fice nemo wa mahaifina abin da zai saka a bakin salati idan hantsi ya dubi ludayi. Da ƙyar na dace na farauto wazobiyar da na saya masa ɗanwaken da ya ci ba tare da ya ƙoshi ba. Na riƙa ɗoki dare ya yi domin na karɓi halalina na kuɗin larabar da yara ke bayarwa, ba don zalama ba sai don na sama mana ko tsuran shayi da biredi ne, domin mu kawar da yunwar da ke addabar cikinmu kar mu kwanta da ita ta hana mu bacci tsakar dare, ashe ni duk sakarci nake yi wai jiran jirgi a tashar mota, na saɓa lamba domin ranar Talata ce ba Laraba ba.
‘Tsuntsu daga sama gasasshe!’ Gefen zuciyata ya raya mini hakan, ɗaya gefen kuma na ƙara kwaɗaitar da ni nisantar haram da gujewa cin abin da ba halalina ba. To amma ai ‘Ruwan kashe gobara, ba a zaɓi.’ Na sake ayyana hakan, zuciyar da ke mini gargaɗi ta sake ankarar da ni wajen raya mini ‘ka da tsautsayin tauna ya saka ka cin jariri.’ don haka ‘Maganin ka da a yi, ka da a fara.’
Zaburar da na yi a tsorace ita ta yanke kai kawon da zuciyata take yi domin samun mafita, sakamakon muryar mahaifina da na jiyo da ƙarfi yana faɗin.
“Wai wane ne a zauren nan nake ta jin kusur-kusur? Habibu! Habibu! Ko ba Habibun ba ne?”
Ƙarar sandar da yake dogarawa dif-dif! Ita ta sake ankarar da ni cewar ya nufo zauren ne duk da duhun da ya mamaye shi, sai ɗan hasken fitilar wayata, saboda tsoratar da na yi sai na manta da makantarsa, jiki na rawa na fara laluben mazugin jakar domin na rufe ta kar ya iske ni ya tarar…
Labarin *Mayafin Sharri:* Labari ne da ya bambanta da salon labaran da kuka saba karantawa, saboda yana ɗauke da sarƙaƙiyar da warwarare ta sai ni da zan jagoranci jan ragamar labarin. Akwai tarin muhimman abubuwa da za ku ƙaru da su. Idan kun shirya ni ma na shirya!
Za ku karanta wannan labarin ne akan kuɗi ƙalilan wanda bai wuce Naira ɗari uku kacal ba (300) daga farkon labarinhar zuwa ƙarshe, ga wanda yake da buƙata zai iya tuntuɓata kan lambar wayata kamar haka:
08080049548
Ko kuma kai tsaye a tura kuɗin ta wannan account.
0557998068 Hassana Labaran GT bank. Sai a tura mini shaidar biyan ta lambar wayata, ga waɗanda ba su da account za su iya turo katin waya na 300, amma MTN.
Free pages ba su da yawa, za ku iya fara biyan kuɗinku tun daga yau.
Na gode.
Leave a Reply