Mayya Ce Hausa Novel Complete

Mayya Ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Page 1*

 

 

 

_____________Saurayi da budurwa ne tsaye a ƙofar wani matsakaicin gida, hirar su suke cike da nishaɗi, dan ko wanne da murmushi a fuskarsa..

Saurayin ne ya kalli budurwar tasa cike da kallon soyayya, yace

 

“Wai nikam Ummi! Kinsan wani abu..?”

 

“A’a masoyi sai ka faɗa.!”

Ummi tayi maganar ta, haɗe dayin fari da

idonta..

 

Murmushi yayi sannan yace

 

“Wallahi in nazo gurin ki rasa sukuni na nake, musamman idan kika min fari da wannan manya manyan idanuwa naki da suka sha kwalli..”

Saurayin ya faɗa cike da wawancin soyayya.. lolx

Washe baki Ummi tayi cikin jin daɗi tace

 

“Kai Sule banda kuma zuga fa!.”

 

“Wallahi da gaske nake! Wai kinsan kuwa mai anti Dije tace miki?.”

 

Cikin zaƙuwa Ummi tace

“Mai kuma tace! Nifa na fahimci anti Dijen nan taku bata sona.”

 

“Hmmm!! Kede bari, Wallahi anti Dije bata sonki, kuma ni Wallahi ko waye baya sonki acikin dangina to Nima bazan so shiba.”

 

Harararsa Ummi tayi sannan tace

“kamar gaske.”

 

“Wallahi da gaske nake! Shiyasa da anti Dije tace min wai ke *MAYYA CE* nayi mata kacca-kacca.”

 

Zaro manyan idanuwanta tayi cikin kaɗuwa tace “Ni *MAYYA CE* ! Lalle na yarda anti dije bata sona, shine zata min ƙazafin maita, to Wallahi ƙarya take mini..”

Ta ƙare maganar cikin marereta da kuma salon kissa..

 

“Haba masoyiyata! Ki kwantar da hankalin ki, yoni ke ko *MAYYA CE* ina ruwana, tunda nagani kuma ina sonki, kuma ni babu abinda zai sa na fasa auranki, koda zaki dinga yankar naman jikina kina ci, to ni bazan iya rabuwa dake ba…”

 

Cikin jin daɗin maganar sa Ummi tace

 

“Har naji zuciya ta tayi sanyi! Amma dan Sule nayi maka kama da MAYYA.?”

 

“A’a wallahi! Itama anti Dijen da ta faɗi haka, nasan duk salon ƙiyayane, da kuma son ta hanani auranki, amma ni na faɗa mata babu abinda zai sauya…”

 

Da haka suka cigaba da hirar su ta soyayya gwanin sha’awa, har Sule ya mata sallama ya wuce…

Ita kuwa Ummi gida ta shige tana tinanin wani kalar mataki zata ɗauka akan ƴan uwan Sule, dan bazata ƙyale suba suyi ta shigan mata hanci da ƙudundune………

 

 

 

 

 

*Tofa jama’a ga MAYYA CE, zaku karɓe ta hannu bibbiyu?, Kude ku biyoni acikin wannan littafin mai suna MAYYA CE*

 

 

 

“`sai fa kunyi haƙuri da yanayin typing ɗin, duba da yadda guda biyu nake typing ɗinsu, kuma kowanne da irin salon shi..“`

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Inga comments da sharhi, to kuma kuga Posting kullum*

 

 

 

 

 

 

 

~Matar khamis ce~

 

 

 

 

 

“`Story and writing“`

*By*

*Ummasalama s yahya*

*(MATAR KHAMIS)*

 

_____________________________________

 

 

 

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*

 

 

 

_(Domin Marubuta Mata)_

 

 

 

(W.W.A)

 

 

 

 

 

 

________________________________

 

 

 

*Ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan kowa ba!*

 

 

 

“`Bissimillahir Rahmanir Rahim“`

 

 

 

 

 

*Page 2*

 

 

 

____________Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin gidan, ranta fes ta ƙara sa inda mahaifiyarta take, karɓar tankaɗen garin da take tayi tana cewa

 

“Iyah!! Kinsan mai sule yace min kuwa..”

 

“A’a mai kuma yace Miki a yau ɗin…”

 

“Hmmm! Kede bari iyah, ina wannan yayar tashi da take nan ƙasan layin mu..”

 

Iyah tace “eh nagane ta koba dije mai Saida fulawa ba..?”

 

Cikin rashin kunya ummi tace

See also  Sanadin Besty Hausa Novel Complete

“Ita fa! Wai sule yaje gindanta shine take ce mai waini *MAYYA CE*, kar ya aure ni..”

 

Dafe ƙirji iya tayi tana cewa “na shiga uku! Karde shima sule ya fasa auranki..”

 

“Hmm! Lalle ai wallahi iyah sule bazai iya rabuwa dani ba, Saboda ba ƙaramin so yake min ba, dan ko ita Anty dijen cewa yayi ya daina mata magana..”

Ummi ta ƙare maganar cike da tabbaci..

 

“To ai shikenan! Amma ni ina tsoron wani abu, kar inje ƴan uwansa su hana ki sukuni, tunda basa wani sonki..”

Cewar iyah tana kallon ummi da ko a jikin ta…

 

“Hhhhh! Ahayye! Wallahi iyah kwantar da hankalin ki kamar kin zaune ɗan mutum, ai duk cikin ƴan uwan Sule ba shegiyar da zata takura min, Saida ni in hana su zama kuma in takurawa rayuwar su, hmm! Basun cemin MAYYA ba?, To Wallahi zasu ga aikin maita…”

Ummi ta ƙare maganar tana sakin dariyar mugunta, dan ita kaɗai tasan tuggun da zata shirya musu…

 

Gyaɗa kai kawai iyah tayi, sannan tace “to Allah ya kaimu lokacin bikin lafiya..”

 

Ummi tace “ameen!..”

Da haka ta cigaba da tankaɗenta tana saƙe saƙe cikin ranta…

 

______________________________

 

Ɓangaren sule kuwa! Yana tafiya daga wajen ummi, kai tsaye gidan su ya nufa, yana shiga kuwa ya taradda anty dije tazo, suna zaune tare da mahaifiyar tasu suna hira, haɗe ransa yayi sannan ya ƙara so wajen da suke, tsugunnawa yayi har ƙasa yana gaida mahaifiyar tasu cike da girmamawa, bayan sun gama gaisawar ne, ya tashi zai shige ɗaki ko kallon Anty dije baiyi ba, bare ma har ya mata wata magana ko gaisuwa..

Cikin jin haushi Anty dije ta kalli mama tace

 

“Kin gani ko! Wai dan na faɗa masa gaskiya, shine yake gaba dani, to Wallahi bari kaji na gaya maka, idan ma gani kake nayiwa budurwar ka sharri, to ka tambayi wasu mana, duk anan gangaren namu babu wanda baisan cewa, uwarta Hajiya iyah MAYYA CE ba, dan wallahi idan ta kama mutum har lahira take kaishi, Saida idan kwanan mutum bai ƙare ba..”

 

Ƙara haɗe fuska sule yayi, sannan ya juyo cike da jin haushin Anty dije yace

 

“Ai uwar ta kikace ba ita ba, saboda haka ki daina cewa budurwa ta MAYYA..?”

 

 

Shiru Anty dije tayi bata ƙara cewa ba komai, dan Yadda ta fahimci sule zai iya damba tawa da ita akan wannan shegiyar MAYYAR……….

 

 

 

 

 

*Tofa jama’a ga MAYYA CE, zaku karɓe ta hannu bibbiyu?, Kude ku biyoni acikin wannan littafin mai suna MAYYA CE*

 

 

 

“`sai fa kunyi haƙuri da yanayin typing ɗin, duba da yadda guda biyu nake typing ɗinsu, kuma kowanne da irin salon shi..“`

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Inga comments da sharhi, to kuma kuga Posting kullum*

 

 

 

 

 

 

 

~Matar khamis ce~

[03/08, 10:20 am] *MAYYA CE*

 

 

 

 

 

“`Story and writing“`

*By*

*Ummasalama s yahya*

*(MATAR KHAMIS)✍️*

 

_____________________________________

 

 

 

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*

 

 

 

_(Domin Marubuta Mata)_

 

 

 

(W.W.A)

 

 

 

 

 

 

________________________________

 

 

 

*Ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan kowa ba!*

 

 

 

“`Bissimillahir Rahmanir Rahim“`

 

 

 

 

 

*Page 3*

 

 

 

_____________washe gari kuwa da safe Sule ne sunkuye a gaban mama, da dukan alamun dai nasiha take mai, ƙura mai ido mama tayi tana karantar yanayin sa, Saida ta Ɗauki wasu ƴan lokuta sannan ta numfasa tace

 

“Suleman!!! Meyasa kake da taurin kai ne, ina laifin ƴar uwar ka dan ta guji abinda zai cutar da kai, yarinyar nan da kake neman auranta fa! Mutane da yawa su kawo min sukarta, kawai magana ce ban maka ba, nidai gaskiya idan Zaka ji magana ta ka rabu da yarinyar nan ka nemi wata, akwai mata da yawa a gari sai wadda ka zaɓa…”

See also  Nida Yaya Muhammad Complete Hausa Novel

 

Cikin ƙunar rai da zafin zuciya sule ya ƙara sunne kansa, ko uffan bai ce ba, cikin zuciyar sa kuwa tunanin ko mai ummi ta yiwa dangin sa suka ɗora mata karan tsana, hakan ya nuna ko ya auro ta baza su sota ba..

 

Mama kuwa da take jiran jin ta bakinsa, ganin yayi shiru hakan yasa tayi ɗan gyaran murya, ɗagowa Sule yayi fuskar sa kamar zai yi kuka yace

 

“Haba mama! Yanzu kema har da ke a masu cewa ummi MAYYA CE, lalle na yarda a gidan nan bakwa sona, kowa ya kawo matar da yake so ya aura, babu wanda ya kushe mai, amma ni Saboda an tsaneni gashi ana so a hanani aurenta…”

Ya ƙare maganar zuciyar sa dan zafi kamar ta fashe..

 

Dakatar dashi mama tayi cikin ƙunar rai tace

 

“Dakata suleman! Kaji nace maka yarinyar nan mayya ce, kawai nace makane ka rabu da ita ka nemi wata, idan kuma kaga baza ka iya rabuwa da ita ba, sai kaje can kayi jarabar nacinka, tunda an gaya maka kaƙi ji…”

 

Dafe ƙirji sule yayi yace

 

“Wallahi mama idan ban auri ummi ba mutuwa zanyi..”

Ya faɗi maganar kamar zai yi kuka..

Cikin mamaki mama take kallon shi, zuciyar ta cike da furgici tace

 

“Iye!!! Sule! mutuwa kuma, lalle na yarda cewa ka haɗu da ƙungurumar Mayya, tun yanzu har an fara lashe maka kurwa…”

Mama ta ƙare maganar tana dafe ƙirjinta..

 

“A’a wallahi mama ba haka bane kawai…”

 

“Kaga yimin shiru! Maza tashi ka bani guri, Ni na rabu da ganin kayan takaicin ka.”

 

Tashi sule yayi ya fita daga ɗakin, zuciyar sa cike da jin haushin anty dije, dan duk ita ta jawo masa wannan matsalar, da batazo tace ummi mayya bace, ai da mama bazata ce komai ba, shide wallahi duk abinda za’a yi bai ga mai hana sa auren ummi ba, dan yanzu ma ya fara sonta…

 

 

_______________________________

 

 

Bayan magribah kuwa sule ne tsaye a ƙofar gidan su ummi, ya kai tsawon minti goma Amma shiru har yanzu bata fito ba, gaba ki ɗaya a matse yake da son ganin ta, ji yake kamar ya shige gidan yaje ya ɗaukota ya gudu da ita..

Ƙamshi turarenta shi ya fara kawo ziyara hancinsa, hakan yasa numfashinsa ɗaukewa na wuccin gadi, fitowa tayi sanye da farin hijabi fuskar ta sam ba kwalliya, amma manyan idanuwan nan nata, ta ranbaɗa musu uban kwalli, kasancewar ta fara kuma tana da mayan idanuwa, sai hakan ya matuƙar yi mata kyau sosai..

 

*MATA! MATA!! MATA!!!*

“`Wallahi a juri sa kwalli a ido, kwalli yana da matuƙar tasiri a idon mace kuma yana ƙara mata kwarjini da soyayya a waje ɗa namiji, idan bake sa kwalli a ido dan Allah yanzu ki fara zaki ce na gaya miki, zaki ga yadda mijinki/saurayin ki zaki mai kwarjini sosai, kwalli a ido yana da matukar jan hankali namiji sosai, dan haka a kula mata…“`

 

Iska ta hura mai a fuska, firgigit sule ya dawo hayyacin sa, daga tinanin da ya tafi, kawai kallo yake binta dashi yama rasa mai zai ce mata, dan in yana kusa da ummi ji yake gaba ki ɗaya ya rasa nutsuwar sa..

Ummi kuwa gani yadda sule duk yabi susuce a kanta, yasa ta fuskance shi cikin son ƙara haukatar dashi tace

 

“Masoyi na ka yini lafiya?”

Ta gaishe shi tana juya idanuwanta cikin salo..

Sule kuwa da ya gama haukacewa saura buge buge kawai da zai fara lolx

Cikin zaƙuwa da tsantsan shauƙinta yace

 

“Ina lafiya! bana lafiya.”

 

Zaro ido ummi tayi sannan tace

“meya same to.”

Ta faɗa cike da damuwa..

 

langaɓe kai sule yayi kamar wani ƙaramin yaro sannan yace

 

“Ina cikin damuwa masoyiyata, ko abinci yau ban iya ciba, kuma wallahi yunwa nake ji kamar mai..”

 

Cikin kissa ummi itama ta langaɓe kai kamar zata yi kuka tace

 

“Meye damuwar taka! Ko na kawo maka abinci kaci, idan ka samu nutsuwa sai ka faɗa min damuwar taka..”

See also  Dhiya'ul Noor Complete Hausa Novels

 

Soyayyar ta sule ya ƙara ji tana shiga lungu da saƙo na cikin zuciyar sa, duk lokacin da yake cikin damuwa, da zarar yazo wajen ummi, neman damuwar tasa yake ya rasa…

Shigewa gida ummi tayi, bata jima ba ta fito hannun ta ɗauke da kofin ruwa da kuma ta barma, shimfiɗawa tayi sannan ta ajje ruwan, komawa cikin tayi ta ɗauko kuloli guda biyu, sai ɗan filet guda ɗaya, tuwon biski ne da miyar taushe, sai ƙamshi gyaɗa miyar take gwanin sha’awa…

Sule kuwa da yake shaƙar ƙamshin abincin nan, gaba ki ɗaya ya ƙagara a zuba mai yaci, dan sai yanzu ya tabbatar da yana jin yunwa sosai…

 

Hannu baka hannu ƙwarya yake cin abincin, kamar wanda yayi shekara bai ciba, ita dai ummi kawai dariya take mai a haka har ya gama cin abincin, ruwa yasha sannan yayi hamdala yana murmushi, kallon sa ummi tayi sannan tace

“ko a ƙaro maka ne.?”

Murmushi sule yayi sannan yace

“A’a Alhamdulillah! Dan ƙoshi ji nake kamar ciki na zai fashe, kede Allah ya miki albarka dan kin taimaki ɗan marayan Allah..”

Dariya ummi tayi tace

“Ai haƙƙine a wuyana na kula da masoyina, yanzu faɗa min miye damuwar taka..?”

Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan yace

 

“Ummi kinsan ban ɓoye miki komai da ya shafe ni ko.?”

 

Tace “eh.”

 

“To ɗazu mama na take cemin wai dole sai na rabu dake na nemi wata, ni kuma gaskiya bazan iya rabuwa dake ba, ke kaɗai nake so, idan kuwa aka min dole wallahi saide aga gawata..”

 

Cikin sanyi murya ummi tace

“Me nayi wa mahaifiyarka zata rabani dakai..?”

 

“Hmm! Duk fa akan maganar anty dije ne, da take cewa ke Mayya ce, shine itama mama ta fara yadda..”

 

Cikin salon jan hankali da kukan kissa ummi tace

 

Karin wasu littafai da zaku so

“Gaskiya sule na fahimci ƴan uwanka basa sona, kawai mu haƙura da juna karka ƙara zuwa inda nake, dan anga kana sona sai a riƙamin ƙazafin maita, ina fa musu kawaici ne saboda kai, amma wallahi da sai mun ɗau mataki a kansu, kowa dai yasan yadda shari’ar maita take a ƙasar nan, Amma idan na rabu da kai sai naji wanda zai ƙara cemin mayya..”

Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai..

Sule kuwa da gaba ki ɗaya ya gama kuncewa, ya rasa inda zaisa kansa yaji daɗi, sai yanzu yake nadamar faɗa mata maganar nan da yayi, musamman da yaji tana cewa ya rabu da ita..

Cikin ruɗewa sule yace

 

“Dan Allah ummi kiyi haƙuri! Bansan kukan nan da kike yi..”

 

Ƙara volume ɗin kukanta tayi sannan ta miƙe tsaye, kallon sa tayi cikin fushi tace

“Eh ai dama dole kace baka son kukana, tunda an bugeni ai dole a hanani kuka, dan muna soyayya da kai sai ariƙa cemin mayya, to wallahi karka ƙara zuwa gurina, daga yau na yanke ko wacce alaƙa da kai, bani ba kai suleman..”

Ta ƙare maganar ta tana shigewa cikin gida………

 

 

 

 

 

 

Tofa jama’a ga MAYYA CE, zaku karɓe ta hannu bibbiyu?, Kude ku biyoni acikin wannan littafin mai suna MAYYA CE*

 

 

 

“`sai fa kunyi haƙuri da yanayin typing ɗin, duba da yadda guda biyu nake typing ɗinsu, kuma kowanne da irin salon shi..“`

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Inga comments da sharhi, to kuma kuga Posting kullum*

 

 

 

 

 

 

 

~Matar khamis ce~are maganar ta tana shigewa cikin gida………

 

 

 

 

 

 

Tofa jama’a ga MAYYA CE, zaku karɓe ta hannu bibbiyu?, Kude ku biyoni acikin wannan littafin mai suna MAYYA CE*

 

 

 

“`sai fa kunyi haƙuri da yanayin typing ɗin, duba da yadda guda biyu nake typing ɗinsu, kuma kowanne da irin salon shi..“`

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Inga comments da sharhi, to kuma kuga Posting kullum*

 

 

 

 

 

 

 

~Matar khamis ce~





Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022



Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top