Me ake nufi da Bitcoin, Crypto Currency
Yayin da muka saba da amfani da kuÉ—in intanet wajen kashe su da kuma karÉ“ar su, har yanzu wasu kuÉ—in intanet kamar Bitcoin na da sarÆ™aÆ™iya ga jama’a.
Ta hanyar yin tambaya da bayar da amsa, mun zanta da Dr William John Knottenbelt, Daraktan Cibiyar Bincike Kan Kudin Intanet na Kwalejin Imperial, domin ya taimaka mana wajen fahimtar kuÉ—in intanet na Bitcoin.
Mene ne Bitcoin, sannan ya ake amfani da s
Bitcoin wani nau’i ne na kuÉ—in intanet. Ba shi da siffa ta zahiri. Madadin haka, ana sayar da rukunin kuÉ—in a intanet da sauran shafukan sada zumunta.
Ba shi da wata iyaka, ma’ana iya shafukan da za a iya amfani da su, sannan ba su da banki, kamar kudin zahiri da aka sani.
A maimakon haka, yana aiki ne a hanyoyin intanet da wasu dubban na’urori da ke hadawa da ajiye bayanan yadda ake kasha kuÉ—in.
Dubban na’urorin ke hana samun bayani dangane da yadda kuÉ—in ke shiga da fita – amma akwai wata fasaha da ake kira ‘blockchain’ da ke iya ba da damar gano shiga da fice kuÉ—in.
Blockchain bayanai ne da ake iya aikawa kan yadda aka kashe bitcoin – yana hana wani ‘kashe kuÉ—in bitcoin sau biyu’ kuma zai yi matukar wahala wani ya iya sauya bayanan shige da ficen kuÉ—in. Da wahala, a iya cewa ma ba zai yiwu a sauya shi ko a wawushe shi ba.
Daga ina ya samo asali?
An fara wallafa Bitcoin ne a wani jerin sakonni na intanet ga masana kimiyyar komfuta da ke karantar yadda za a iya aika sako ta intanet cikin tsaro a 2008.
Wanda ya fara wallafa shi na da wani suna na bogi Satoshi Nakamoto amma babu wani mutum ko mutane kawo yanzu da aka tabbatar shi ne Satoshi.
Ana amfani da shi har yanzu kuma a ina ake amfani da shi?
Ana amfani da Bitcoin har yanzu kuma ana sayen shi a matsayin kuÉ—in da ba na zahiri ba, wanda ke ba masu amfani da shi damar sauya kuÉ—in zahiri da aka saba da shi zuwa bitcoins.
Don amfani da Bitcoins, matakin farko shi ne bude abin da ake kira ‘wallet’ ko lalita (wadda ke iya zama a intanet ko a manhajar waya ko a wata na’ura mai tsaro). Wannan na kare duk wani sirri da ake amfani da shi wajen hadahadar bitcoins.
Lalitarka za ta kunshi ‘adireshi’ wanda yake aiki kamar lambar asusun banki sannan ana iya amfani da shi wajen karbar bitcoins. Haka kuma zai kunshi password din da ake bukata wajen aika bitcoins (ana kiran wannan private key).
Idan ka manta da wannan private key din, ko kuma aka sace, kana iya rasa bitcoins dinka, kamar dai yadda idan ka batar da lambar ka ta PIN ta katin ATM.
4. Me zai sa mutum ya fi son Bitcoin maimakon kuÉ—in da aka sani?
KuÉ—in da muke amfani da shi a yau na da tarihi da daban idan aka yi batun kuÉ—i, wato ba abu ne mai wahalar samu ba kamar sulallan zinare
Yanzu idan ka duba abin da aka rubuta a kan £10: “Na yi alÆ™awarin biyanmai wannan kudin fam goma da zarar ya tambaya.”
Wannan ba wani alkawarin a zo a gani ba ne idan ka duba cewa abin kawai da hukumar da ke kula da kuɗin (kamar Babban Bankin Ingila) za ta yi shi ne ta sake buga wani kuɗin don cika wannan alƙawarin.
Yayin da ake sake ƙirƙirar kuɗi, yana rage daraja kuɗin da ake da shi. Ba lallai ne mutane su gane wannan raguwa a darajar kuɗin ba saboda kuɗin na nan yadda suka san shi; amma za su iya lura cefanen da suke yi duk mako da farashin abincin da suke saye na ƙaruwa.
A nan ne Bitcoin ya sha bamban.
Ana samar da bitcoin ne sannu a hankali kuma a ƙayyade, sannan babu wanda zai iya ƙirkirar bitcoin a lokacin da ya so.
Ba a taÉ“a iya samar da bitcoin sama da miliyan 21 ba; kuma ana iya raba ko wane bitcoin zuwa kashi miliyan 100, wanda ake kira Satoshis. Wannan zai hana raguwar darajarsa kamar yadda kudin da muka sani ke yi (lamarin da ‘yan Zimbabwe da Venezuela suka fi kowa sani).
5. Bitcoin na iya mayar da kai miloniya?
Bitcoin kadara ce mai hatsari. Kamar ko wane hannun jari, yana faÉ—uwa da tashi kuma ya danganta da lokacin da ka siye shi. Yana iya mayar da kai miloniya kuma yana iya talauta ka.
A farko farko, an sayar da Bitcoin daya kan $1; farashinsa ya hau kusan $20,000 ko £15,400 a 2017 kafin farashinsa ya faɗi warwas zuwa kusan $3,000 ko £2,300 sannan ya koma $8,000 ko £6,200.
6. Me ake nufi da haƙar bitcoin?
HaÆ™ar bitcoin na nufin samar da sabbin bitcoin ta hanyar amfani da wasu abubuwa da ake kira ‘blocks’.
Ko yaushe a faÉ—in duniya akwai gasa da ake yi wadda ake kira ‘gasar haÆ™a’ don lashe damar Æ™ara ‘block’ ga ‘blockchain’ wato jerin ko tarin ‘blocks’.
Shiga gasar na buÆ™atar masu amfani su sayi wata na’ura da aikinta shi ne kawai ‘hakar’ bitcoin wadda kuma take shan wutar lantarki sosai.
Ana iya cewa ma an fara daina yayin na’urar saboda sabbin Æ™irÆ™ire Æ™irÆ™ire da ake ci gaba da yi don haka hakar bitcoin bai fiye kawo wa mutane riba sosai ba.
Mutanen da ke wannan aikin ana kiransu masu haƙar bitcoin. Suna shiga wannan gasar ne saboda abu biyu:
Don su samu riba (a halin yanzu ribar bitcoin 12.5) da ake bai wa duk wani mai haƙar bitcoin.
Haka kuma, haƙar na ƙara wahala idan mutane da yawa suka sa hannu; ana haka ne don a takaita bayar da sabbin bitcoins cikin gaggawa.
Haka kuma, ribar ko wane ‘block’ na raguwa da rabu duk shekara 4, wannan na sa wa samar da su ya Æ™ara tsada.
7. Muna iya amincewa da kuÉ—in bitcoin?
Kamar ko wace sabuwar ƙirƙira da ke ci gaba, akwai mai inganci akwai masu ƙarancin inganci.
A fagen kasuwanci irin wannan na fasaha, mutane da yawa na shan wahalar fahimtar wane bitcoin ne mai inganci sannan ba kowa ne ya gama fahimtar yadda su ke aiki ba da sahihancinsu.
Wani lokaci, tsare tsare kamar One Coin sun yi iƙirarin kasancewa kuɗaden bitcoin amma daga baya aka gano na bogi ne.
8. KuÉ—in bitcoin na iya shahara fiye da kuÉ—i na zahiri nan gaba?
Ana iya hasahsen haka, amma akwai yiwuwar za a iya kwashe kwanaki tsawon shekaru kuma sai an duba abubuwa sosai da suka shafi tattalin arziÆ™i da shari’a kafin a cimma haka.
Misali, ‘blockchain’ na Bitcoin a yanzu ba sa iya daukar shige da ficen bitcoin da yawa idan aka haÉ—a da yadda ake amfani da kuÉ—i ta hanyar intanet kamar Visa da Mastercard.
Wani É“angare na kuÉ—in intanet da ke shahara kuma ke da yiwuwar shahara fiye da kuÉ—i na zahiri shi ne ‘stable-coins’, wanda ake alakanta darajarsa da kuÉ—in da muka saba amfani da shi kamar dalar Amurka da Euro da Fam, ba kamar bitcoin ba, yadda ba a iya cewa darajarsa É—aya ta kai £26,000 a wannan shekarar sannan bayan shekara biyu a cewa ya faÉ—i ya koma £6,000.