Gyaran Jiki

Me ke sa mata na ganin farin ruwa na fitowa a farjin su lokacin al’ada

 

SHIN HAKAN YANA NUFIN AKWAI MATSALA NE TATTARE DA HAKAN KO BABU
 
Normally mafi yawan mata suna samun fitowar farin ruwa a gabansu throughout menstrual circle dinsu
Ciwon ciki lokacin al’ada
Akalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mara launi yana fito musu a kowace rana, adadin daya kai kimanin cikin shokalin shayi. Launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara, zuwa farin ruwa, ko kuma baki baki (brown).
 
Banbancin launin ruwan ko kaurin sa yana ta allaqa ne da hormonal changes na jikin ta a lokacin da yake fitowa.
 
Wannan fitan farin ruwa da mace take gani ta gaban ta kafin period dinta normal ne, babu matsala tattare da hakan. Process ne da ake kira “Leukorrhea” Wani lokacin yana iya kasance wa yellowish.
Hakan yana faruwa ne sbd yawan hormones “progesterone” dayake taruwa ajikin ta. A wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”
 
Wa’ennan hormones kamar su”progesterone” “oestrogen” “androgen” etc sauyin yanayin sune ajikin ta shike sawa tayi ta ganin “vaginal discharge” yana fito mata.
 
Idan “estrogen” ne sukayi yawa ajikin ta a lokacin, se ruwan ya kasance fari fari, mai yauki
kuma ruwa ruwa.
 
Idan kuma “progesterone” ne sukayi yawa ajikin ta, se ruwan ya kasance farin madara kuma mai kauri kauri.
Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa ruwa ne, madara madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko qarni, gaban mace baya zafi, kaikayi ko radadi, to wannan normal ne.
 
Aikin sa (ruwan) shine yayi flushing duk wani dattin vagina, wasu harmful germs, etc da kuma ya sa vagina ta zama moist all the time. Hakan yana nuna alamar the vagina and the
reproductive system is healthy and functional.
 

Leave a Comment

error: Content is protected !!