Me zan yi da ita Hausa Novel

Me zan yi da ita Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ME ZAN YI DA ITA?

 

 

NAZEEFAH SABO

NASHE

 

FREE📚

08033748387

 

 

Da sanyin safiya ta fito daga rugar fulanin cikin wata bukka dake daga gefen rugar sanye take da kayan fulani irin usul din fulanin nan fuskarta a cunkushe da mabayyanin ‘bacin rai. Tana tafe tana kunkuni alamar ba dan son ranta ya fito ba.

 

Kwarya ce a kanta da nono a ciki a tsakar gidan ta tarar da mahaifiyarta zaune da turtsesten ciki a gabanta ta had’a kai da gwiwa . Har zata wuce sai kuma ta dawo ta tsaya mata’kerere a ka, bakinta a zun’bure tace “innaji zan tafi” innaji ta saki ajiyar zuciya kafin ta furta “idan kinje ki gaida modibbon saura kuma idan kin fita ki tsaya dukan d’iyoyin jama’a ko tumakinsu “ “ aradu duk yaran da ya higa gonata nima sai na higa ta uwarshi “ cikin takaici innaji ya watsa mata harara “ ina magana shatu kina cewa aradu sai kinyi to ai shikkenan kije kiyi Allah ya shiryeki ni dai ina gaya miki ki kula da kanki kina sani ba kowa ne damu a garinnan ba idan mune yau fa anjima gawa muke bana son ace har yanzu kina wannan halinnaki kowa unguwar nan yasan halinki ba mai fad’ar alherinki sai aibunki shatu don Allah ki shiryu kada kizo nan gaba kina wahala a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido “ . Duk da jikinta yayi sanyi bata fasa cewa “yo innaji sai na bari yara suna tsokanata suna ce min mai idon mujiya kamar ubansu ya rad’a min “ innaji ta mi’ke da kyar da alama cikin yayi mata nauyi murya can ‘kasa ya kama hannunta “ suyi ta fad’a miki mana kyau idanun suke musu masha Allah zaki dinga cewa idan suka fad’a miki yi sauri ki tafi kinga hadari na hadowa ki gaidar min da modibbo ki kar’bo min rubutun idan ya rubuta “. Da sauri ta fice kamar zata tashi sama tana ayyana “ wallahi innaji ba zan kyalesu ba jibgar d’iya ni kayi idan ya shiga gonata’yan kwal uba masu kan faranti “.

Da tsallanta take tafe da wa’karta duk da ‘kwaryar nonon da take kanta har da cilla sanda duk yaran da ta wuce’kus suke da bakinsu kada suyi magana suci Na jaki sai dai tana wucewa suke tuntsira dariya murya ‘kasa’kasa suke cewa “mujiya idonki a loko “ sai su taka da gudu. Shatu ‘kwafa take tana haddacesu d’aya bayan d’aya ta kuma tabbatar wallahi sai sunyi bayani.

Salon So Hausa Novel Complete

A saman buzu ta tarar da kakanta Na gurin uba moddibo wanda ya kasance gawurtaccen malami a garin nutsuwa tayi sosai don shi kad’ai take tsoro a garin , ta ra’be gefensa ta tsuguna sai da ya kai aya sannan ya d’ago ya kalleta fuskarsa ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwar da take masa “ Gashi inji innaji tace tana gaidaka “ moddibo ya girgiza kai had’e da jan’kwaryar yana girgiza kai “ ‘yar nema ai Na zata yau ma kinyi halinnaki kin zubar dashi wallahi da yau ma sai na zaneki dan na lura sam ke baki tausayin innarki idonki a tsakar ka yake d’auki ki kaiwa salame Ta adana shi a ciki” mi’kewa tayi zuciyarta a tunzire kamar ta kai masa mari ita fa ta tsaneshi bata ‘ki ya she’ka barzahu ba don ya takura mata baki kamar shantu ta fad’a a zuciyarta zanyi maganinka aradu gobe. A tsakar turken tumaki ta tarar da ita salame ta amsa gaisuwarta tana kar’bar’kwaryar nonon fuska a sake tace “ya jikin innar taki?” “ ba sauki sai na Allah yo wannan uban ciki yayi mata turtsitsi ta ina zata samu sau’ki Idan ba haifeshi tayi ba aradu duk ranar da Ta haife abin da yake cikinta sai na jibgeshi “ salame ta zaro ido tana kallon shatu da take zaro zance “ashe kuwa dai shatu da ake cewa baki da kai zancen ya kusa tabbata jaririn zaki jibga?” Ta ta’be baki “ yo idan ban jibgehi ba ai aradu ban haifu ba a cikin innaji ko sallah fa a zaune take yi gashi tun a ciki shegen karanbani garai yayi ta kwarafniya jiya fa ina kallon cikin yana wutsilniya wallahi tana cin abinci kika ji d’if tun kan yazo duniya ma ya nuna halinsa” salame ta girgiza kai tana katse’kwaryar ta mi’ka mata daidai lokacin da modibbo ya shigo yana dogara sanda “ to uwar shashashanci kina nan kina zuba kamar ‘ya’yan kanya zo ki wuce ki kai mata rubutun Allah ya raba lafiya” “ ameen “ ta furta murya can ‘kasa “ ai kai na gado a kwakwazo duk gari an sani” mai kika ce “? A guje ta arce tana fad’in cewa nayi Allah ya tashe mu lafiya salame kuwa girgiza kai tayi don ita taji abinda tace sarai don dai shi ma kunnensa yana da matsala ne.

 

 

Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi

Matar Makaho Complete Hausa Novel

Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam

Matar Yaro Hausa Novel

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Gyaran Nono a sari data

Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd

 

Tun a hanya take Allah-Allah taga d’aya daga cikin yarannan sai dai bata gansu ba haka ta koma gida ranta a ‘bace da rashin cikar burinta.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Tana shiga innaji ta kar’bi rubutun had’e da nuna mata buta ta san nufin innaji tunda lazimi take ta sunkuci butar ta fara alwalar. A nutse ta tada sallah duk da rashin jinta innaji Ta tsaya sosai wajen bata ilimin addini don masaniyace sosai Na boko ne dai sai taga dama take zuwa ko idan an tura ta ta shige gonakin jama’a tayi’barna.

 

Suna idar da sallah innaji ta ri’ke hannunta murya a raunane tace “ shatu jikina yana bani kamar rayuwata tazo gangara don haka ya zama dole yanzu Na sanar dake labarina ko da nan gaba zaki bu’kaci haka a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido ga mahaifinki tsawon wata biyar da tafiyarsa har yau ba amo ba labari daga tafiya fatauci ina son ganinsa ban san ina ya tafi ba.” Hawayene ya ciko a idanun shatu sam bata son taji innaji tayi mata zancen mutuwa ta lura kuma kwana biyu kullum zancenta kenan. “ innaji don Allah ki daina min zancen mutuwa idan kika mutu an higa uku “ baki shiga uku ba shatu Allah yana tare dake kuma kina da gata tunda moddibo yana raye balle nasan mahaifinki komai dad’ewa Zai dawo ki share hawayenki burina kawai ki nutsu “ fad’awa jikinta tayi “don Allah ki daina cewa zaki mutu ni kece gatana “ innaji murmushi tayi tana kallon zallar yarinta a idon shatu da Ba zata gaza shekara sha daya ba. “ To ki dinga addu’a Allah ya rabamu da cikinnan lafiya naga aurenki shatu “. Da sauri ta furta ameen “

 

 

Har dare tana son jin labarin da innaji zata bata amma kuma tana tsoron zancen mutuwa don haka tayi mu’kus.

 

Cikin dare ta kasa ha’kuri ta mi’ke zaune “Innaji baki bani labarin ba “ murmushi innaji tayi don tasan shatu da son jin zance ta mi’ke zaune da ‘kyar ta jingina da bango.

 

 

*********. **********

Asalina haifaffiyar garin liman katagum agarin bauchin yakubu sai dai mahaifiyata yar asalin mambilace a jihar yola acan mahaifina ya ganota ya aura shi yasa zaki ganmu da asalin kyau na fulanin usuli.

 

Mahaifina d’an bokone mu biyu iyayena suka haifa daga ni sai yaya ta dijama. Kasancewar mahaifina lecturer hakan yasa ya dage akan harkar iliminmu. Muka taso cikin tarbiyya da ‘kaunar juna ni da yayata mai tsananin kama dani ta girme ni da shekara hud’u. Yayata tana gama secondary samari su kayi mata ca hakan yasa babanmu yace dole ta fitar da miji duk da kasancewarsa d’an boko baya take ilimin addini yana bashi ha’kkinsa sosai. A lokacin ina ss 1 yayata ta fitar da miji a kayi mata aure da wani matashin mai kud’i ahmad manga inda suka tare cikin garin bauchi a unguwar gwallaga.

 

 

Lokacin da na shiga ss2 a lokacin muka fara soyayya da wani ma aikacin makarantar atbu inda gidanmu yake kasancwar a staff houses muke shara yake da gyaran compound d’in gidanmu soyayyarsa ta d’ibeni don kyakykyawa ne sosai . Ba wanda ya sani a gidanmu a ‘boye muke komai duk da bama keta iyakar ubangiji amma fa soyayya tayi zurfi a tsakaninmu ta yarda tabbas a lokacin idan aka hanamu aure zamu iya rasa rayuwarmu. Duk da bashi da ilimi haka nake son shi tunda yana da ilimin addini bokon ma a hankali nake koya masa a ba ca da. Ina ss 3 tashin hankalin ya fara zuwa don kuwa wani d’an abokin babanmu yace yana so na babanmu kuma yace ya bashi gashi bababnmu irin masu kafiyar nan ne sam baya juyuwa mai juyashi dama babansa ne kuma ya rasu. Hankalina ya tashi sosai nayi kuka kamar raina zai fita na gaya wa mamanmu bana sonsa ta fad’awa baba yace ban isa ba bai haifi dan da zai ce yes yace no ba. Haka mamanmu tayi ta rarrashina ita da yayata amma zuciyata Ta kasa ha’kura.

See also  Hadin Iyaye Hausa Novel Complete

Hakan ya tunzira zuciyar Baba yace ya fasa barin sai na gama jarrabawar na ‘karasa a gidan mijina aure zai yi min.

 

Aka fara shirin biki hankalinmu a tashe ni da miji wannan yasa ana gobe d’aurin auren muka gudu ni da miji. Da sassafe muka wayi gari a wata ruga ya bani kayan fulani na saka sai da muka zo gidan ya sanar dani gidansu ne nan ya shiryawa mahaifinsa ‘karya akan cewa iyayena sun rasu a hanya kuma fulanin tashi ne hakan yasa suka rungumeni a gidan bayan wata biyu aka d’aura mana aure da miji duk da kullum zuciyata na bani shawarar na koma gida amma ina tsoron mahaifina. Shakararmu goma da aure kafin Allah ya kawo cikinki. Har yau a garin nnan ba wanda yasan ina da ‘yan uwa sai yanzu da nake gaya miki kina zuwa liman katagum kika tambayi gidan sarkin fulani nan ne main house na familyn babanmu koda ta Allah zata kasance. Ya fad’a hawaye na ziraro mata na tuno iyayenta.

 

Shatu ma hawayen take “yanzu innaji da gatanki muke ta yawo bama nan garin bama can mune har nan niger 🇳🇪 ashe asalinmu yan nigeria 🇳🇬 ne “. Innaji ta dafa kanta tace “kaddarar haihuwarki ne shatu da ta wannan cikin fatana idan kin sadu da dangina kice su yafe min na mutu ina tsananin kewarsu “. Share hawayenta tayi tace “insha Allah innaji ba zaki mutu ba da ‘kafarki zaki ga danginki “.

[01/09, 11:09 am] +234 803 192 1625: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍

 

 

 

NAZEEFAH SABO NASHE

 

 

FREE📚

08033748387

2

 

Sumul suka farka innaji ranar ta d’an ji sau’ki, har yamma shatu na tare da ita Ta kasa motsawa ko nan da can ranar kam jikinta a sanyaye yake duk tsiwar da masifat ta zubar tana gefen innaji a zaune kan tabarmar karauni. Innajin Ta tsefe mata kanta Ta wanke tas da kanwa da karkashi sai ‘kyalli gashin yake yasha man kwakwa kasancewar shatu mai gashi na ban mamaki tamkar mutanen ‘kasar hindu don ma bata son gyarashi da ‘kyar take barin innajin ta ta’ba mata kai shima sai tayi mata jan ido.

Har aka gama tana kwance lamo ba mai magana tsakaninsu ita innaji tana karatun suratu maryama ita kuwa shatu ta lula duniyar tunani gaba d’aya ta rasa sukuni.har la’asar tayi kafin ta mi’ke tayi alwala ta kuma zubawa innajin ruwan alwala innaji ta kar’ba tana murmushi “ Allah yayi miki albarka shatu yasa ki cimma duk burin da nake miki fata a rayuwarki “. “Ameen “ shatu ta fad’a murya a sha’ke. Suna idarwa innajin ta aiketa gidan modibbo kar’bo rubutu.

 

Duk tsokanar da yara suke mata a hanya ranar banza tayi dasu burinta taje ta dawo ta iske innaji lafiya sumul, don haka take ta sauri kamar zata tashi sama.

 

Ko mintuna biyu bata yi ba a gidan moddibon ta juyo a sukwane ko saurarar gwaggoji ( salame) da take ‘kwala mata kira ba tayi ba.

 

Kamar an cillota haka ta afka tsakargidan da sauri ta saki ajiyar zuciya had’e da cewa Alhamdulillah Allah innaji na d’auka kafin na dawo kin mutu” murmushi innaji tayi kafin ta furta “mutuwa ai sai lokaci yayi ayshatu” da sauri ta dubeta jin sunan da ta kira ta dashi innaji ta waro ido tace “lafiya “ ta hau girgiza kai “ ji nayi kin kira ni da sunan da baki Ta’ba kira na ba “ dariya kawai tayi tana shan rubutun ta had’e da kallon shatu kallo mai nuna tsananin ‘kaunar da take mata.

 

 

Cikin dare innaji ta fara jin ciwon na’kuda tun tana daurewa har abin yaci ‘karfinta ta mi’ke da ‘kyar ta bud’e wata adaka ta zaro wasu hotuna da biro ta rubuta address din family house d’insu ta nad’e a takarda ko bakomai bata san ya ta Allah zata kasance ba.

 

 

Da ‘karfi ciwon yazo mata har bata san lokacin data fara tashin shatu ba a razane shatu ta tashi saboda wani mummunan mafarki da take a wannan lokacin, ganin innaji cikin wani mawuyacin hali bata san sanda ta zunduma ihu ba tana ru’kun’kumeta “ bana so innaaji bana son mafarkin da nayi ya tabbata “. Da kyar innaji ta’ka’kalo wani murmushi tana mi’ka mata takarda “ ayshatu ban san ya ta Allah zata kasance ba amma koma dai yayane bayan raina ki nemi dangi na idan mahaifana suna raye ki basu wannan takardar da wannan hoton suna gani sun san ke jini nace Ayshatu idan babanki ya dawo kice masa ya yafe ni Allah ya yanke ganawarmu “. Hawaye take yi sosai na tsananin azabar na’kuda. Ayshatu kuwa ta zama kamar mutum mutumi ta rasa ma mai zatayi abinka da’kan’kantar shekaru. Sai jijjiga innaji take ba bakin magana har zuwa sanda taji innajin ta saki kalmar shahada jikinta gaba d’aya ya saki ji kake d’if lamarin Alhakamu ya tabbata. Ita kuwa a nata tunanin barci innaji tayi bata san mutuwa ba bata san ya ake mutuwa ba gashi ana fad’a musu zafin fitar rai a yanda kuwa ake kwatantawa tabbas wannan ba mutuwa bace barcine ta ayyana hakan a ranta, don haka hankalinta kwance ita ma ta kwanta a gefen innajin barci ya kwasheta barcin da shine ya kaita har’karfe goma na safe.

 

Tana farkawa ta tashi a razane tana kallon hasken d’akin tare da tunanin me yasa innaji yau bata tashesu sallahr asuba ba. dubanta ta kai inda innajin take da sauri ta zare ido ganin idonta a kakkafe ya kalli sama ai bata san sanda ta hau jijjigata ba jin bata motsi yasa ta runtuma waje a guje tana Kiran jama’a “kuzo ku duba min innata tayi barcin zomo na tasheta ta’ki tashi “ ma’kota suka shiga gidan sai gani tayi suna fitowa jiki a salu’be ga kallon tausayi suna mata . Kalmar da taji wata ta fad’a ne Allah yaji’kanki maryamu halinki na gari ya biki yasa ta farka daga tunanin da take na cewa innaji barci take.aiko zuba hannu aka ta ‘kwalla’kara sai ganinta a kayi a zube ba numfashi.

Allahu akbar kabeeran Ubangiji kenan mai yin yarda yaso a lokacin da yaga dama Allah yaji’kan iyayenmu.

 

 

A safiyar juma’ar misalin ‘karfe sha d’aya na safe aka sada innaji zuwa gidanta na gaskiya hawaye sai zarya yake a fuskar abokan arziki kowa ya shaida innaji bata da abokin rigima to ita maganar ma bata dameta ba balle har ta samu abokin rigima. Shatu zube a cinyar gwaggoji sai mayar da ajiyar zuciya take da razana har sai da moddibo ya sake mata rubutu aka bata. To haka dama rayuwa take.

 

 

 

A hankali shatu ta fara sabawa da rashin innaji kullum kuwa ma’kale da takarda da hotunannan take kwana tayi al’kawarin sai ta sadu da dangin mahaifinta. Gidansu gwaggoji ta koma ta daina wanka ta daina komai wai ita ta gama jin dad’in duniya tunda innaji ta tafi ta barta. Yaran mutane kuwa a lokacin ta ‘kara takura musu musammam masu uwa raye shatu bata da ‘kiba sam amma sai ‘karfi ta gallabi mutanen garin tun ana d’aga mata’kafa saboda rashin uwa har tausayin ya kau aka fara kawo ‘kararta wajen gwaggoji. Gwaggoji bata da fad’a sam don haka shatu take’kara sangarcewa kullum da rashin jin da zata rakito ta kai yanzu har manya shiga shirginsu take musamman masu gonaki da suke kuka da ita.

 

Makaranta kuwa tuni tayi sallama da ita ta allo kawai take yi itama don moddibo yana cin gidansu ne da batayi ba. Gashi yanzu shi bashi da cikakkiyar lafiya yau fari gobe tsumma.

 

 

 

BAYAN WATA SHIDDA

 

Da rasuwar innaji jikin moddibo ya ‘kara tsananta, hakan yasa shi fara had’a komatsansa baya so ya mutu anan ya fito ya mutu cikin ahalinsa da suke garin yola. Itama gwaggoji hankalinta yafi kwanciya su tafi musamman saboda shatu ko bakomai a can dangi da yawa za’a samu mai tayasu kula da ita.

 

 

Safiyar wata asabar suka fito da ‘yan ‘kullin kayansu suka fara sallama da mutanen garin da suka yi dandazo a ‘kofar gida, duk jikinsu yayi sanyi musamman yara da suke kallon shatu Idanunsu fal ‘kwalla. Shatun ma kuka take ta kalli yaran tana murmushi “kuyi min tsokanar’karshe don Allah ko bakomai zan dinga tuna ku.” Shiru su kayi mata, murya na rawa ta fara binsu d’aya bayan d’aya tana cewa “ku fad’a mujiya mai idonta a loko….” Ai kuwa yara suka fara har ita suna kuka kuka, dariya- dariya a haka suka rakasu har inda mai amalanke yazo ya d’ebesu tana d’aga musu hannu suna bin amalanke , rayuwa kenan ba mamaki shikkenan tayi sallama da garin nijar. Amma ta’kudirce insha Allah zata dawo.

 

 

 

Kwanansu kusan biyu suna tafiya, kafin Allah ya kawo su garin yola nan suka hau motar garinsu demsa, daga demsa suka shiga wata’kur’kura ta isar dasu cikin ‘kauyensu gwamba. Ai kuwa mutanen garin suna ganinsu suka shiga fitowa ana murnar ganinsu.

Bayan sun shiga cikin gidan mai girman gaske ginin’kasa suka fara yiwa juna gaisuwa anan suke jin labarin mutuwar muji mahaifin shatu. Ashe da ya taho hatsari yayi a garin yola hakan yasa ya bada address din family house d’insu na nan kafin a kawo shi kuma rai yayi halinsa. Su kuma basu san inda zasu samesu ba. hankalin shatu ya tashi ta zube wajen har iskokanta suka ziyarceta, kowa a wajen ya tausaya mata musamman da suka ji labarin rasuwar maryamu ma. Moddibo kuwa innalillahi wa inna ilaihir raji’una yake ja kansa yana juyawa sai gani a kayi shima luuuuu ya kifa. Ai ko ana d’ago shi aka ga rai yayi halinsa. Nan kuwa koke- koke ya ‘karu shatu kuwa kuka take aljannun Na sake bugeta. Gwaggoji kuwa kasa magana tayi tana taajjabin lamarin Ubangiji ashe haka mutuwa take lokaci d’aya taji mutuwar d’anta ‘kwaya guda da rage bata dawo daga razanin ba shima mijin ya mutu, ai ji tayi ina ma ita ma ubangiji ya d’au ranta.

See also  Download A'Indo Tantiriyar Yar Aiki Hausa Novel

 

 

Moddibo kam ya dace ya mutu ranar juma’a aka sadashi da gidansa Na gaskiya. Haka rayuwa take Allah yasa mu cika da imani .

 

 

 

 

Gwaggoji daga ranar bata sake samun lafiya ba. sai dai a kwantar a tayar, hankalin shatu ya matu’kar tashi duk ta sake firgai firgai ko wanka batayi, bata so ta rasa gwaggoji a karo na hud’u Ta san idan ta rasa gwaggoji gatanta ya gama zubewa warwas. Mutanen nan taga basu da zumunci ko a yanzu haka ita take yiwa gwaggojin komai hatta da gyara jiki idan ta’bata. Iyakacinsu da su abinci shima ko yaro’karami zai iya cinyeshi.

 

 

 

Ranar wata juma’a da yayi dai-dai da rasuwar malam sati takwas, suna kwance gwaggoji na nishi sans-sama tace “ shatu ko bayan raina kada ki zauna ana tunda kince maryamu ta gaya miki inda magaifiyarki take kiyi tafiyarki can, wadannan mutanen kowa kansa ya sani, ga ‘yan ubanci da suka a kansu ba zasu ri’ke ki da gaskiya ba , ina jin tsoron in mutu in barki anan don haka na dad’e da tanada miki kud’in mota.” Ta fad’a tana lalube a cikin bujenta dubu goma cif ta ciro ta mi’ka mata. “Ki’boye shatu ki adana su Allah yayiwa rayuwarki albarka ya kareki daga sharrin dukkan abin ‘ki, baki da wani gata sai dangin mahaifiyarki saboda haka ki tafi can ni na san lokaci na yayi, mutanennan mugaye ne duk ‘yan uba suke da malam dalilin gallazawar da suke mana da saran ‘boye yasa muka gudu muka barsu yaranmu ta dalilin azabarsu su uku muka rasa don haka kema ba zasu barki ba….” tari ne ya fara sar’keta tuni ta fara aman jini, zuciyar shatu ta bushe Ta riga ta saba da mutuwa ta san ita d’inma mutuwar zata yi.

 

A Jikinta kuwa gwaggoji ta saki kalmat shahada ta mutu, ko alamar hawaye babu a idon shatu sai zuciyarta data ke wani tu’ku’kin ba’kin ciki. Ta ja mayafi ta rufe mata fuska taja gefe tana jan wani numfashi mai huci ta tabbata yanzu bata da wani gata……..

 

 

Sai asuba ta sanar da mutanen gidan mutuwar gwaggoji. Ba tare da wani nuna jimami ba su kayi jana’izarta aka kaita gidanta na gaskiya.

 

 

Bayan kwana bakwai rayuwa ta canjawa shatu zancen gwaggoji ya fara tabbata, ko abinci basa bata sai tayi musu aikatau. Karshe suka ce zata fara fita tallan nono bayan ga ‘ya’yansu mata basu d’ora musu ba.

 

 

Cikin dare taji jatau suna shawara da d’an uwansa wai su had’a ta aure da liti yaron da kowa ya shaida d’an Ta’addane, ai kuwa shatu a daren ta mi’ke Ta hau shiri tabbas lokacin barinta garin yayi a yau zata tafi dangin uwarta.

 

 

Cikin duhun daren ta fito sai dai kafin ta kai ga d’arewa’karamar katangar jatau ya hasketa. Waye nan…….

[01/09, 11:10 am] +234 803 192 1625: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍

 

 

 

NAZEEFAH SABO NASHE

 

 

FREE📚

08033748387

3

 

 

 

“Waye nan” jatau ya sake fad’a da sauri shatu ta juya tayi kamar zata shiga bayan gida, murya can ‘kasa tace “nice zan zaga ne “ tsaki yayi ya shige yana bambamin fad’an “iskancin banza da wofi kawai ki nemi frigita ni cikin tsohon dare zan yi maganinki mai kama da ifritan aljannu” shatu dai bata ce komai ba tabi bayansa da harara tana sakin ‘kananan tsaki “ aradu Allah zai kaimu lokacin da zanyi maganinku “ yana shigewa sad’af- sad’af Ta shige bayan gidan ta kuma haure’karamar katangar ta bar gidan a guje.

 

 

Shatu duk da kasancewarta yarinya da ba zata gaza shekara sha biyu tana da wayo da kaifin basira, hakan yasa bata sha wuyar kai kanta tasha ba, ta hau motar da zata kaita har cikin gari sannan aka saka ta a motar garin bauchi.

 

 

 

*************

 

Tafiyar awowi ce ta kaisu bauchi ko daga nan ta tambayi motar katagum, yaran tasha yasa ta a motar da zata kaita tafawa balewa daga can ne zata samu motar katagum.

 

Suna isa kuwa kasancewar gidan babban gidane bata sha wuyar nemansa ba a kasadata da family house din nasu. Duk inda ta wuce sai an bita da kallo kasancewar tayi kama da mutanennan da ake kira bararoji, jikinta dukun-dukun hakanan kanta she looks very dirty.

Sam bata damu da rufe gashin kanta ba haka take tafe wurjanjan da silifas wari da wari a ‘kafarta.

 

 

Gidane babba irin ginin mutanen da , mai dauke da d’akuna birjik a kowacce shiyya, kasancewar nan ne ainahin gidan sarauta na garin, yasha gyara sosai da paint kana gani dai kasan ba wahala a tattare da ahalin gidan. Fili ne fetal ga manyan bishiyu ko ta ina. Rashin sanin inda zata yasa ta nufar wasu yara da taga suna wasan’kwallo a harabar gidan, ganinta a gurin yasa suka arce da gudu don su tabbas zatonsu aljannahce. Tsaki shatu taja had’e da komawa can gefe da ‘kullin kayanta ta zauna.

 

Iface-Ifacen yaranne ya fito da ahalin gidan a rud’e suna duban yaran da suke fad’in “Aljannah Aljannah “ shatu ta girgiza kai tana juyosu daga waje a zuciyarta tace “ai kuwa sai kunci ‘kwal uwarku akan iyayenku zan huce a aljannar zan zo musu kafin na bayyana kaina “ da sauri ta hargitse sumar kanta tsaf ta mi’ke ta hau zare ido ta shagid’e hannu d’aya, Ta dumfari babbar shiyyar da taga yaran sun nufa.

 

Ba zato ba tsammani suka ganta a tsakiyar filin kan kace meye iyayen yara sunyi hanyar neman tsira sai tsohuwa dada da aka bari jikinta yana’bari tana fad’in innahu min sulaimanu kuyi min aikin gafara wallahi ba laifina “ shatu ta cusgune fuska ta dumfari dada ai kafin kace mai dada ta saki gudawa da fitsari a wando ganin tana shirin fad’uwa shatu ta tintsire da dariya “ ke tsohuwa dakata kada ki sume min ni ba aljannah bace kamar yarda kuka d’auka mutum ce ni d’iyar maryama ‘ya wajen d’anki Lamid’o “. Dada ta zaro ido tana kallonta kafin tace “ki rantse da Allah “ shatu taja tsaki “ kwarankwatsa ni ba aljannah bace ko kinga kofato a ‘kafata “ sai sannan dada taja dogon numfashi tana zamewa a jikin bango zata zauna. Shatu ta kalli gudawar tace tana toshe hanci. Sai sannan dada ta lura ta saka salati da sauri ta rarrafa tashiga bayan gida shatu kuwa sai tuntsira dariya take.

 

 

Sai dada ta kimtsa ta dubeta bayan ta kaita rumfarta taje ta kira matan gidan “ to duk ku fito ku ji min bayani wai wannan d’iyar maryama ce maryaman da tuni lamid’o ya sallamata ga d’iyarta mai kama da jinnu ta bayyana “ shatu ta girgiza kai a hankali ta furta “zaki bayanin wannan ma “.

 

Sai sannan kowa ya fito cikin tsananin ta’ajjibi ana kallon shatu wai wannan jinin lamid’o ce yarinya kamar fulanin daji ita kuwa maryama mai yayi mata zafi ta za’bi rayuwar daji akan rayuwarta cikin gata da mutuncinta “. ‘Daya daga cikin matan ta fad’a shatu ta watsa mata wani kallo had’e da cewa “ yo haka ‘kaddarar Allah ta za’ba mata kuma kada a sake a zagi uwata don kuwa bata raye aradu raine zai ‘baci “ Ta fad’a cikin karyayyiyar hausarta ta fulanin usli. Gaba d’aya suka zaro ido dada ta saka kuka “yanzu’yar nan kika ce maryama ta mutu? Innalillahi yau ya lamid’o da liman zasuji da wannan ba’kin labarin kullum zancen su na maryama ne “

Ta fad’a tana jan majina hawaye sha’be-sha’be, kafin ta share hawayenta tsaf ta mayar da kallonta kan shatu tana mata kallon ‘kurilla “ wace shaida zaki bamu mu yarda ke d’in jininmu ce d’iyar maryama daso?” Shatu ta mata wani kallon she’ke’ke aradun Allah babu shaidar da zan baku sai na cika cikina tunda ku kam baku san zuru ba kun san wahalar da na hya kafin nazo nan amma ba wanda yace min ga ko ruwa Na hya “ dada tace “kwarai da gaskiyarki ke harira kawo mata abinci ke kuma furera ki kira matar lamid’o kice ko mai suke su biyo jirgi daga habuja suzo hukuncin ubangiji ya tabbata.”

 

Ana kawo mata abincin ta fara ci hannu baka hannu kwarya dad’in abincin har tsakar kanta ga nama zu’ku-zuku wanda rabonta da cin nama tun sallahr layya ta bara idan har bata manta ba. Taci tayi nak ta sha zo’bo sai sannan ta fara washe baki tana dariya ta kalli dada “to ko ki yarda ko kada ki yarda ni d’in diyar maryama ce ga hotunan da ta bani kafin rai yayi halinsa” ta fad’a tana zaro hotunan daga bujen da yake jikinta. Wanda suka san maryama da wanda sai a hoto suka santa duk suka zaro ido dada girgiza kai “ ba shakka hukumullahi la ajabun innalillahi wa inna ilaihirrajiuna wato maryama daso sallama tayi damu “ hawaye shabe shabe dada ta saki tana sake rushewa da kuka , sai kuma ta dubi shatu tana fyace majina “ ikon Allah wato shi ubannaki bararo ne?” Shatu ta zaro ido “ kan bala’i inji uban wa?” Ta fad’a tana cizon yatsa

[01/09, 11:10 am] +234 803 192 1625: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍

 

 

 

NAZEEFAH SABO NASHE

 

 

FREE📚

See also  Izzar So 94 Bakori TV

08033748387

-4

ELEGANT ONLINE WRITERS****

 

 

 

Dada ta zuba mata idanun tsofaffinta , cikin gatse tace “inji ubanki muji da ya sace mana’ya ya gudu da ita” shatu ta girgiza kai had’e da mi’kewa a katifa tayi kwanciyarta. Ba a d’au dogon lokaci ba barci yayi awon gaba da ita. Dada ta bita da harara “ wannan yarinyar daga gani ‘yar daru ce bari kakannin naki suzo ni za’a barwa ke sai na koya miki hankali tukun, ke fure kira min su lamid’on kiji sun taho “ furere ta amsa daya bayan d’aya suna ficewa daga d’akin. Koda furere ta kira wayar taji shiru ta tabbatar sun taho kenan tunda ta san ba sajin kud’in jirgi kullum a tafe suke.

 

 

 

Dada tana zaune tana lazimi ita kuwa shatu barci takeyi sosai abinta cikin kwanciyar hankali.

 

Liman na dawowa dada ta sake bashi labari, cikin farin ciki yake kallon shatu da ba abinda ta d’auko na uwarta da alama can dangin ubanta ta d’auko don ban ga kamanni ba “ ya fada yana kallon dada, dada ta ta’be baki “ yo kaima dai ka fad’a yarinya kamar bararo ko fulanin daji anyi magana tace inji ubanwa? Bari su su lamid’on suzo sa tantance idan jininsu ce ko Ba tasu ba sa san yarda zasuyi da ita, ni wallahi tulin sumar kanta ne ma da idanunta suke ban tsoro yarinya kamar d’iyar jinnu don kyau “. Malami dariyar su ta manya kawai yayi gani n shatu ta mi’ke ba tare da sanin dadar ba tana ta harararta “ yo ki fito kice min kawai baki yarda dani ba mana Allah na tuba na me zan zauna ina muku’karya “

 

Sallamar su lamid’o ce yasa dada yin shiru bata tanka ta bata Allah ya sani tsoro yarinyar ke bata “ maraba lale da iyayen maryama kuzo yau dai kuga jikarku d’iyar maryama “ da sauri suka ‘karasa d’akin suna watsa idonsa akanta ta kuwa ‘kuri tana kallonsu.maman maryama tace “dada kada kice min wannan jinin maryama ce?” Dada ta ta’be baki “babu wai itace maryama ta haifo muku bararoji mai kama da ubanta. Ai mama bata’karasa jin abinda zata ceba ta ‘karasa da sauri ta kamata ta rungume “ Alhamdulillah ashe zan sake ganin maryama?” Shatu ta zame jikinta “ ai kuwa ba zaki sake ganin maryama idan dai ba yau kema zaki bita yarda ta tafi ba ashe kuna sonta ku ka kasa bata burin ranta akan haka ta gudu ta bar gida ta bar gatanta ta gwammace rayuwa cikin daji “. Lamid’o zama yayi yana kallon yarinyar mai cike da tsiwa da surutu mama kuwa sake janta jikinta tayi “ mun dade muna neman inda zamu ga maryama sai yau Allah ya nufa “ cewar lamido dada ta girgiza kai “ yau ai kaga dalilin da yasa ba zaku ga maryama ba tana can ‘kungurmin dajin da ba wuta balle a samu tv ta ina zata ji cigiyarta da ake ba’kin cikina d’aya ne Allah ya dauke maryama ba tare da mun sake ganawa ba sai bararon ‘yarta da ta bar mana” dada ta fad’a tana fashewa da kuka, mama ma zama tayi da’bas a kujera tana juya maganar dada lamid’on kuwa salati kawai yake ja , yanzu maryama ta mutu maryaman da ya dad’e yana nema ya nuna mata gata dama tuni ya yafe mata , mama kuka ta saka sosai tana rungume shatu a cinyarta cikin tsananin’kaunarta sam bata damu da daud’ar da take jikinta ba. Shatu taji zuciyarta ta karye da tausayin kakanninta mutuwar innaji ta dawo mata sabuwa kar itama ta rungume mama tana sake sakin kuka mai ratsa zuciya mama ta sake rungumeta tana shafa himilin gashinta.

 

Tsawon lokaci suna cikin jimami kafin lamid’o ya kalli shatu yace ya sunanki?” Murya a dashe tace “ shatu “ lamid’o ya jinjina kai “ to ya akayi kika gane nan kika zo ina so naji labarinki da garin da kuka zauna da labarin rayuwar maryama a garin……. shatu ta gyara zama daidai lokacin da wani daddad’an’kamshi ya ziryaci hancinta tana d’aga ido ta hango mai sallamar da sauri ta mi’ke tana wara ido tana fad’in “innaji “ mama ta kama hannunta “ zauna aysha ba mamanki bace yayarta ce da take bi ana ce mata mammah “ mammah da take tsaye ta waro ido tace “ mama kada kice min y’ar maryama ce ina maryaman ina ‘yar uwata alhamdulillah yau burina ya cika “. Mama hawaye ya ziraro mata don Ta san za’ayi haka Ta sani sarai deejah bata da buri irin taga maryama kullum zancenta kenan. Shigowar samarin yaran deejan yayi daidai da lokacin da mama tace “ Addu’a ‘yar uwarki take bu’kata yanzu Allah yayi mata rasuwa wannan y’arta ce Aysha da ta bari “. Gani su kayi mammah kawai ta zube numfashinta na ‘kokarin d’aukewa da sauri y’ay’anta su kayi kanta suna jijjigata had’e da kiran sunanta amma shiru. Dada ce ta d’ebo ruwa ta watsa mata sai kuwa ta kawo ajiyar zuciya “mama don Allah kice min wasa kike ko mafarki nake ba maryama ta bace ta mutu “ Lamid’o ya mi’kar da ita zaune Kafin yace “ Allahn da ya fi mu son maryama ya amsheta addua tafi bu’kata yanzu sai kuma d’iyarta da ya bar mana mu dinga kallo muna jin dad’i Alhamdulillah da wannan hikima ta ubangjji “. Da sauri mammah taja shatu jikinta ba tare da ‘kyankyaminta ta rungumta tana bata sumba a gefen kumatu cikin nuna mata tsananin ‘kauna take share mata hawaye tana kallonta with so much caring , saurayin d’anta da yake gefe imran ya hau ‘bata fuska cikin tsananin mamakin mammahn da bata’kyankyamin wannan yarinyar da Daud’a ta samu wajen zama a jikinta. Zuciyarsa har tashi ta fara yi saboda mutum ne shi mai tsananin’kyankyami da tsafta har da ta siyarwa. Runtse idonsa yayi kawai ba ya ma son sake kallon wannan kwamacalar. Ya bud’e kujerarsa wata karama da ya shigo da ita daga motarsa ya zauna. Sai a lokacin dada ta kula dashi duk da’kamshinsa ya sanar da duk ahalin gidan zuwansa’kamshin turarensa na amouage interlude 53 ya karad’e gidan sanye yake cikin black jeans da white long sleeve shirt ta Ralph lauren polo ya gyara glass dinsa da yayiwa idonsa kyau ba’a ganin ‘kwayar idonsa gashin kansa a kwance luf, murya a dashe yake gaida lamid’o da dada. Dada cikin mamakin halinsa na ko da yaushe tace” jakadan turawa yaushe ka bayyana a ‘kasar.” Cije lips dinsa yayi bai bata amsa ba sai ammar kaninsa ne yace “ yau kwanansa biyu “ dada ta kyabe fuska “ ai dama shi ba zaka ganshi ba Sai a dangin uwarsa saboda sun fimu farcen susa ammar kaine namu Allah yayi maka albarka yo wannan dama fuska kamar hadarin kaji wake maraba dashi ga shegen tsurfar tsaftar tsiya da ‘kakale aikin banza ko mu har a gaya mana tsafta “ . Ammar dariya kawai yake shi kuwa imran ya’kare tsuke fuska shi yasa sam baya son zuwa gurin tsohuwar nan mai shegiyar maganar tsiya. Lamid’o ya gyara murya kafin ya dubi Aysha “ ina jinki ayshatu bamu labarin “ ai kuwa ta sake gyara zama ta jingina kanta a jikin mommah ganinta take kamar innaji wallahi. Mommahn ta kara janta jikinta duk da warin da bakinta da jikinta yake bata’kayamaceta ba tana sauraran yarda take basu labari tiryan-tiryan.

 

 

Kafin ta gama bada labarin gaba d’aya gurin kowa kuka yake har ammar banda imran da ya d’auke kai gaba d’aya haushin yarinyar yake ji ga shegen surutu kamar kanya ba mamaki ma ‘karya take ba jininsu bace idan banda haka mai ya had’a su da bararoji. Yanzu haka had’a baki a kayi da ita tazo ta cucesu mutanen duniya da basu da gaskiya musamman su d’in da an sansu a gari . “ ya kamata ku bincika kafin ku tabbatar da gaskiyarta “ hakan kawai yace yaja baki yayi shiru kamar bashi yayi magana. Momma ta d’ago a fusace zata yi magana lamid’o ya d’aga mata hannu ita kuwa shatu wata harara ta zuba masa da ya sashi ware ido yana kallonta cikin mamakin rainin da ta nuna masa sai kuma yayi Kwafa. Dada ta gyara zama “ yo saboda Allah ai gaskiya bature ya fad’a nima fa mamaki nakeyi ace wannan bararojin jininmu ce to ka fad’a ace ina ka fito don dai mune masu kalan dangi sai kuma mu had’a jini da bararo “ mommah idan ranta yayi dubu ya ‘baci ta kalli dadan kafin taja’kafar shatu ta nunawa dadar “ duk wanda ya san yar uwata maryama ya san wannan copyn kafarta ne da hannunta dada ki daina daka ta imran da shegen halinsa dinnan na bin kwakwkwafi a ina yasan maryama balle ya tantance jininta maryama da ta bar gida yana shekara guda duk’kaunar da maryama ta nuna maka ban mance da ita ba.” Imran ya ta’be baki kawai ita kuwa shatu zaro hotuna tayi ta mikawa mommah da takardar da innaji ta bata tace ta basu. Mommah na gani ta mikawa lamid’o “ Baba kalla kaga wallahi rubutun maryama ne wannan tabbas “ lamid’o ya kar’ba ya kuma shaida tabbas rubutun d’iyarsa ne.

 

 

Sun ci sun sha akayiwa maryama addua sannan su lamid’o mazauna abuja suka fara haramar tafiya. Mama tace shatu tayi wanka ta canja kaya kafin su wuce shatu ta had’e rai sam bata san zancen wanka. Mommah ce tace” haba mama na zata zaki bar min ita mu koma kano tare musamman ganin bani da y’a mace ashe maryama ce zata haifa min” mama ta girgiza kai imran yana zaune a gefe yana adduar kada Allah yasa mama ta amine banda rigimar mommah ya zata kai musu bararo gida……😂😂😂😂 To fa!

12 thoughts on “Me zan yi da ita Hausa Novel”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top