Hausa Novels

Meenalyn Daddy Hausa Novel Complete

Meenalyn Daddy Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

Meenalyn Daddy Hausa Novel Complete

Fadila Sani Bakori.

 

 

BAN HAK’URI.

Inaba masoyana hak’uri najina shiru da suka yi.

 

 

GARGAD’I.

Meenalyn daddy banyar da wani/wata ba ya yi min amfani da littafi ba ta ko wata sibgaba sai da izinin marubuciyar .

 

 

KADA KU MANTA ,FADILA SANI BAKORI CE, MARUBUCIYAR.

 

IN DA RAI…

 

OGA HABIB

 

RAYUWAR HAIDAR

 

SO NE SILA

 

ABDURRAHIM MATUK’IN JIRGIN RUWA NE

 

DAGA ALLAH KO D’AURA MA KAI

 

AND NOW

 

MEENALYN DADDY.

 

 

SADAUKARWA:

Na sadaukar da page d’in nan baki d’ayan shi gareki shugubar Jarumai writer’s association, Basira Musa,Wato (Mommyn shukura) Ki dad’e ki yi k’arko ki shekaru irin na dabino.

 

 

 

Page 1 & 2

 

 

 

Garin Kaduna Saban kawo layin ‘yan majalissu.Wanda za’a iya cewa duk Wanda ke layin ‘yan majalisu yaci ya tada kai.koda na shiga Unguwar ban tsaya ko Ina ba sai gidan Doctor Alhaji Abba Sani.

Alhaji Abba Sani kwance yake a faffa d’an gadon shi,sai juyi ya ke bisa ga alamu dai kamar da akwai abinda ke damun shi .

Hajiya Mariya matar Doctor Abba, ta yi sallama ta shiga bedroom d’in,hajiya Mariya jin shiru maigidannata bai amsa mata sallamar da tayi ba ne yasa ta shiga kai tsaye. ta dad’e tsaye kan maigidannata tana tunanin, tunanin me ya ke yi haka ,ita dai a iya saninta bata san wata damuwa da ke damun maigidannata ba.

Hajiya Mariya zama tayi gefan gadon,ta na hura ma Alhaji Abba iskar bakinta,sannan cikin dadda d’an lafazi ta ce.

“Daddyn Meenal lafiya kuwa,tun d’azu nake tsaye kanka amma bisaga alamama bakasan da tsayuwata ba”.

 

 

 

 

Wanda aka Kira da Abban Meenal , kallo d’aya za kai Mai kasan tattijon arzik’i ne.Duk da baza akira shi da tsoho ba , ya dai manyanta Masha Allah, k’ila kuma wadata ce da kwanciyar hankali ta hana tsufan bayyana.

D’ago fararan idon shi yayi ya kalli hajiya Mariya batare da ya motsa ba ko alamun zaiyi magana ba.

Hakan da yayi sai ya sa Hajiya Mariya cikin damuwa ,hakan yasa ta sa hannuta d’aya tana tab’a wuyan maigidan nata taji ko zazzab’i ne,amma jin babu alamun zazzab’i yasa cikin alamun damuwa ta ce

“Abban Meenal bakajin dad’i ne?”.

Wanda aka Kira da Abban Meenal tashi yayi ya zauna ,sannan ya kalli matar tashi Mahaifiyar tilan ‘yar shi ya ce,yana mai sakin murmushi afuskar shi ,dan ya kauda da mata tunanin da take na yanada damuwa,ya ce.

“Mommyn Meenal me kika gani ne?”.

“Abban Meenal dan Allah ka fad’imin damuwarka kawai,alamunka sunnuna kanada damuwa,me ke damunka please?”.

Hajiya Mariya tayi maganar cikin nuna sansanin damuwar maigidannata”

 

 

Alhaji Abba tashi yayi Yana rik’o hannun matar tashi,ya ce.

“Tashi muje muyi breakfast babu abinda ke damuna,kawai dai kinsan watarana hakanan mutum sai ya tashi yaji shi baya jin dad’in garin,shine kawai,amma me zai daman, Meenalyn daddy da mommynta na kusa dani”.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Magana hajiya Mariya za ta kuma yi Alhaji Abba yayi saurin ri gata da cewa.

“Mu je inyi breakfast inada pertient a asibiti da zan duba ga lokaci ya ja muje”.

 

 

 

Alhaji Abba na zaune Yana breakfast ya kalli Hajiya Mariya ya ce.

“Ina Meenalyn daddy fa?”.

Murmushi Hajiya Mariya tayi ta ce.

“Meenalyn daddy yau da fushi ta tafi School bataga daddynta ba,dan na san badan suna da Exam ba da cewa za tai ba zata ba”

 

 

Murmushi Alhaji Abba yayi ya ce.

“Bari idan na fita zan biya ta school d’in tasu”.

“Ai wallahi daddyn Meenal duk kai ke k’ara shagwab’a Meenal shi yasa kullum take ganin kanta kamar k’aramar yarinya,ta girma har yanzu kai da ita baku san ta girmaba”.

 

 

Alhaji Abba aje cup d’in d’in hannun shi yayi Yana kallan Uwar gidan shi ,ya ce.

“Wai Meenal d’in ce ta girma ?”

 

 

” 21 years fa,aiko akowace duniya ta girma ,sai dai awajanka ne bata girma ba”.cewar hajiya Mariya.

 

 

Murmushi Alhaji Abba yayi,ya ce.

“Ni dai kallan Baby har yau nakema Meenalyn daddy”.

 

 

Haka Alhaji Abba ya gama breakfast d’in shi ya yi shirinsa ya fita aiki.

kamar yadda Alhaji Abba yace sai da ya biya ta University d’in da Meenal ke karatu.Yana shiga ya Kira number ta,aiko da hanzarinta ta naimi excuse ta fito.

Alhaji Abba na jingine jikin motar shi Yana murmushin shi da ya saba dan shi mutum ne mai fara’a,bakamar da ya hango Meenal ta tahoba cikin na tsuwarta da take bashi mamaki,dan yana yaba natsuwar Meenal sosai awaje,agida ne dai sai addu’a.

 

 

Meenal na zuwa ta rungume daddynta cikin fara’arta tana cewa .

“Oyoyo my sweet Daddy ,yau nayita jiranka baka tashi ba sai dai Bilya driver ya kawoni”.

Meenal ta idasa maganar tana turo baki,kamar wata k’aramar yarinya.

 

 

Bayanta Alhaji Abba ya fara bubbugawa alamun lallashi,ya ce.

“Yi hak’uri Meenaln daddy nima da na tashi banganki ba sai naji duk ba dad’i,shi yasa Breakfast kad’an nayi ,yafi min dad’i idan naci da Meenalyn daddy”.

 

 

 

Meenal tana murmushi irin na daddyn ta, duk da ita nata mai tsada ne kusan daddynta kad’ai takema irin shi,ta ce.

“Sweet daddy nikam yau banci komai ba “.

 

 

 

Cikin hanzari Alhaji Abba ya kamo hannun Meenal Yana k’ok’arin sata amota ya ce.

“Meenalyn daddy muje restaurant kici abinci,bana hanaki tafiya biki breakfast ba?”.

 

 

“A’a Sweet daddy nikam bazan ci ba ,kasan bana son abinci waje”

 

 

 

D’aurewa Alhaji Abba yayi,ya ce.

“Meenalyn daddy Allah indai biki biyoni ba kikaci abincin nan,yau ba zanyi dinner da ke ba”.

 

Meenal jin haka turo baki tayi ta shiga motar tana cewa.

“Amma dai sweet daddy kasan bana cin abinci waje ko?”.

“Eh nasani ,me yasa biki breakfast agida ba?”.

 

 

Turo baki Meenal tayi daga nan bata kuma cewa komai ba taja bakinta tayi shiru.

 

 

Alhaji Abba da kan shi ya bud’e ma Meenal motar ta shiga,Shima ya shiga yaja motar yabar harabar makarantar”

 

 

 

Restaurant tsadadde Alhaji Abba ya kai meenal taci abinci.Sai dai me bayan ankawo mata white rice da soup ,ko kallan abincin k’i tayi ,Alhaji Abba cikin lallama da lallashi ya ce.

“Meenalyn daddy kici Mana ,ko restaurant d’in ne bai miki ba,mu canza wani,koko abincin ne baiyi ba?”.

“Sweet daddy kasan nifa bana iyacin abinci sai da kai”.

Meenal ta idasa maganar tana mai kauda kai ga abincin.

Murmushi Alhaji Abba ya yi,sannan ya d’auki spoon d’in yaci gaba da cin abinci.

Meenal ma ganin haka itama ta d’auka ta faraci.

 

 

 

Alhaji Abba ya k’oshi kasan cewar sai da yayi lafiyayyan breakfast sannan ya fito gida,amma kasan cewar yasan daga ya cire hannun shi meenalynshi ma zata cire yasa ya d’aure yayita tusawa .

Masha Allah,Meenal an samu taci abinci ba laifi,sannan ta aje spoon d’in tana mai tashi tsaye alamun su tafi.

Alhaji Abba ma tsam ya tashi kasan cewar ya biya kud’in yasa ya kama hannun Meenal kamar wata Baby ya sata mota Shima ya shiga.

Sai da Alhaji Abba ya Maida Meenal school sannan ya kama hanyar zuwa wajan aiki”

 

 

 

Kamar yadda Meenal ta saba da wowa daga school yauma haka ta dawo,tana zuwa ta fad’a kan caution d’in falon tana cewa.

“Wayyo Allahna!”.

 

 

 

Hajiya Mariya Mahaifiyar Meenal,kallan Meenal tayi tana mai cewa.

“Meenalyn daddy dan Allah sai yau she zaki koyi yin sallama ne in kika shiga waje?,kefa ba jahila bace,kinada saninki d’ai-d’ai gwargwado ,kuma ke bak’aramar yarinya bace,amma sai ki shiga waje babu sallama.Tom kin san Allah daga yau indai kika kuskura kika k’ara shigo min falo bikimin sallama ba Allah sai ranki ya b’ace!”.

Meenal turo baki tayi kamar za tai kuka dan idan da akwai abinda tak’ijini bai wuce ai mata fad’aba.Hakan yasa ta turo bakin nan,kamar za tai kuka.

Hajiya Mariya tashi tayi taba Meenal waje dama ita da wiya kaji firarta ita da Meenal sai dai da daddynta”.

 

 

Hajiya Mariya tana ciki har ta gama abinda take ta dawo Falon,amma abin mamaki Meenal na nan yadda ta barta,har yanzu kuma fuskarta babu walwala alamun har yanzu bata huce da fad’an da Mommynta tayi mata ba,na rashin sallama da batayi ba.

Hajiya Mariya zama tayi kusa da Meenal ta na mai dafata dan duk sai taji ta shiga damuwa ganin tilo d’in ‘yartata cikin damuw.Hakan yasa ta ce.

“Haba Meenalyn daddy dan namiki fad’ane akan sallama kika yi fushi haka?,amma dai kin san ni Mommyn ki ce da bazan so inga yarinya ta tayi ba dai_dai ba.Sannan duk cikakkan musulmi baya shiga gu sai yayi sallama,dan amusulinci idan mutum yazo waje baiyi sallama ba idan baka tanka Mai ba bakayi laifi ba.Indai dan fad’an da nai miki ne ki saki ranki,bana so ne mutane su zagi tarbiyar daughterna shi yasa”

Haka Hajiya Mariya ta zauna sai nasiha takema Meenal cikin lallab’awa da lalla shi,kamar wata ‘yar 2 years.

 

 

 

Meenal dai bata tankama Hajiya Mariya ba,kuma har yanzu bakinta a ture yake,daga k’arshema cewa tayi.

“Tom mommy ai mantawa fa nayi, ai tunamin ya kamata kiyi bawai kimin fad’a ba”.

 

 

Murmushi Hajiya Mariya tayi ta ce.

“Tom naji Meenalyn daddy amma fa kullum sai na tuna miki”.

“Tom ai ahaka-ahaka watarana zan rik’e”. Cewar Meenal.

Hajiya Mariya dai shiru tayi,sai zuwa can ta kalli Meenal ta ce.

“Abinci fa?”.

Yatsine fuska Meenal tayi sannan ta ce.

“Kema kinsan sai daddyna ya dawo zamuci tare” .

Hajiya Mariya bata Kuna cewa komai ba ta tashi ta shiga ciki,dan yin abinda ba’arasa ba,har zata wuce ta kalli Meenal ta ce.

“Zoki tayani aikin mana?”.

Meenal tab’e baki tayi tana mai cewa cikin sanyin muryarta da alamun rashin sonyi magana.

“Ai wallahi tunda kika hana daddyna kawo mai aiki gidan nan sai dai ke duk ki rik’ayin aikinki”.

 

 

Hajiya Mariya harta zo zata tafi,komai ta tuno ta dawo tana mai kallan Meenal ta ce.

“Bari daddyn naki yadawo ,yau zai Mana shara’a dake agidan nan,wallahi daga yau dole ki fara ko da sharane “.

 

 

Meenal dai bata ce komai ba,ta juya ta tafi abinta”.

 

 

 

Misalin k’arfe takwai na dare(8:00PM) Alhaji Abba ya shigo gida kamar yadda ya saba da wowa kusan kulkum.

Meenal zau ne ta ke kan caution ,ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya ,ta yi kwalliyar tar bar daddynta kamar yadda ta saba kullum,haka zata zo falon ta zauna tana jiran shigowar daddynta.Aiko tana jin sallamar shi ta ta shi da gudu ta rungume daddynnata,tana mai amsar jakar hannun shi,sannan cikin sanyin muryarta ta ce.

“Welcome daddy”.

Alhaji Abba cikin k’aunar ‘yar tashi ya ce.

“Ina ta sauri kar inyi ma Meenalyn daddy laifi”.

“Ai daddy yau da ka k’ara lokaci da bazan kulaka ba”.cewar Meenal tana mai yima daddyn nata jagoranci izuwa bedroom d’in shi.

Mahaifiyar Meenal ko da fitowarta daga kitchen kenan, ta k’araso da fara’arta irin ta tarbar mai gida d’in nan ta ce.

“Oyoyo daddyn Meenal barka da dawowa”

 

 

 

Alhaji Abba Yana mai ci gaba da tafiya ya ce.

“Yauwa Mommyn Meenalyn daddy”.

 

 

Meenal ko na rik’e da jakar daddynta da ta amsa har i’zuwa bedroom d’in shi.Sai da ta aje jakar sannan ta fita tana mai cewa .

“Tom Daddy ka fito yanzu fa kar Ulcer ta kamain kai”.

Murmushi Alhaji Abba yayi ,batare da ya tankaba ya shi ge toilet”

 

 

 

Meenal ko na fita darning space ta nufa ,ta zauna tana danna wayarta tana jiran fitowar daddyn ta.

Meenal na nan zaune Alhaji Abba ya fito shida Mommyn Meenal.

Bayan Alhaji Abba ya zauna ne,Meenal ta ja plate d’in daddyn ta ta mik’a mai itama taci gaba tacin nata.

Hajiya Mariya Mahaifiyar Meenal kallan Meenal tayi ta ce.

“Wato Meenal ke kullum bakimin ta ido ko?,sai ki zuba ma daddynki kema ki zuba ni ina kallanku ni da nai girk…”.

Alhaji Abba wuf yayi ya ce.

“Aikin ai sai yayi mata yawa,ni bari in zuba miki”.

 

 

 

Meenala dai tanaji bata tankaba, Daddynta ya zuba Mommynta abincin.

Bayan Alhaji Abba ya gama cin abincin ne,Mahaifiyar Meenal ta kalle shi ta ce.

“Daddy Meenal na kawoma k’arar Meenal?”.

Alhaji Abba kallan Mahaifiyar Meenal ya yi ya ce.

“To me kuma Meenalyn daddy tayi?”.

 

 

 

Mahaifiyar Meenal d’aure fuska tayi,alamun maganar da za tai babu wasa,dan ta san Daddyn Meenal zai iya d’aukar maganar da wasa.Mahaifiyar Meenal kallan Alhaji Abba ta kuma yi sannan ta ce.

“Daddyn Meenal,dama akan maganar rashin yin aikin Meenal ne,nifa abinda nake nuna maka Meenal macece ba zai yuwu ba,ace kamar Meenal batasan ta d’auki d’auki tsintsiya ba tayi shara,bare kuma ayi maganar mopping, tom gaskiya nikam nagaji daga yau ga Meenal nan a gabanka koda falo ne ta rik’a gyarawa ,ahankali-ahankali watarana zata iya”.

Alhaji Abba tunda Mahaifiyar Meenal ta fara magana yake kallanta,har ta kai k’arshe, ajiyar zuciya ya sauke sannan,ya kalli Meenal da ta turo baki, murmushi Alhaji Abba yayi sannan ya ce.

“Meenalyn daddy kinji abinda mommynki ta ce ko?” .

Meenal turo bakinta ta kuma yi,kamar ba za tai magana ba sannan ta ce.

“Tom Daddy waya ce ta k’i samun mai tayata aiki idan aiki ne yayi mata yawa”.

Meenal ta idasa maganar tana mai ci gaba ga game d’in da take yi a wayarta”

 

 

Alhaji Abba kallan Mommyn Meenal yayi ya ce.

“Tom kinji”.

Mahaifiyar Meenal cikin kwantar da kai dan daddyn Meenal ya fahinceta dan tasan idai tace da tsiya za tai tom ba zai fa yuwu ba,hakan yasa cikin kwantar da kai ta ce.

“Daddyn Meenal kafa duba lamarin nan ina teaching ,kullum sai sha biyu nake da wowa gidan nan,kuma ace kamar Meenal ba zata iya kamamin komai ba,duk bama haka ba,ni aikin gidan nan bawai ya gagaran bane,kawai dai ina duba rashin dacewar ace mukai Meenal gidan miji mata iya komai b….”.

 

 

Kukan da Meenal ta fara ne tana buga k’afa abin gunin mamaki,kamar wata ‘yar 4 years, tana cewa.

“Daddy kaji ko ta fara ko” .

Alhaji Abba tashi yayi Yana kamo hannun Meenal ya ce.

“Tashi mu bar mata wajan dama abinda take so kenan taga tasaki kuka”.

mommyn Meenal kuwa da ranta ya b’aci ,duk da indai rashin isa da Meenal ne dama saba,sai dai aduk lokacin da hakan ta faru ranta kan b’ac.Mommyn Meenal sai dai ta bisu da ido”

 

 

Alhaji Abba ko har bedroom d’in Meenal ya kaita ,ya zaunar da ita bakin gadonta,sannan yasa hannu yana goge mata hawayanta ya ce.

“Meenalyn daddy ki yi shiru kinji ki goge hawayanki,babu bai saki aiki,wa yace ta kori masu ta yata aiki saboda wata hujjatata ta banza da wofi.ki yi shiru kinji meenalyn daddy kar ki yi ciwan kai”.

Meenal da har yanzu kuka ta ke,kallan Alhaji Abba tayi ta ce.

“Daddy nifa badan ta ce inyi aiki bane nake kuka,kanaji cewa tayi wai akaini d’akin miji,bacin nace ta bar cemin haka”.

 

 

“Yi hak’uri Meenalina batzata K’ara ba,d’akin miji kuma naga mai kaiki har sai ranar da kikai ra’ayin kanki sannan ko?”.

Kai Meenal ta d’aga ta ce ,

“Tom ka kirata kace mata karta k’ara cemin haka”

 

 

 

 

Alhaji Abba wayar shi ya ciro ya Kira Mommyn Meenal.Tana d’agawa ya ce.

“Ki sameni a bedroom d’in Meenal”.

Yana kaiwa haka ya kashe wayar”

 

 

 

Mahaifiyar Meenal ko da tana zaune inda sukabarta tashi tayi tana mai addu’ar Allah yasa Meenal ta amince zata rik’a yin aikin ne”.

 

 

Da sallama Mommyn Meenal ta shiga bedroom d’in.

Alhaji Abba ne ya amsa mata Amma Meenal ko kallanta batayi ba dan fushi take da mahaifiyartata.

Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi alamun inajinka.

Alhaji Abba gyara zama yayi yana Kara rik’e hanun Meenal ya ce.

“Mommyn Meenal wai me yasa ne idan muka fara magana d’aya dake mun dinka nanatata kenan bazamu barta ba?,Me yasa bazaki guji duk abinda kika san Meenal bataso ba?,So nawa ina ce miki duk wata magana da ta shafi aure ki bar furtata akan Meenal ?,inda yarinyar nan ta nuna miki bataso,tom wannan shine magana ta k’arshe kar ki Kuma dan ganta min yarinya da duk wani abu da kika san bataso” .

Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba kawai tayi bata iya tankamai ba,dan idan ma tace zata tanka tasan kanta zata jawoma b’acin rai gara tayi shiru”

 

 

Alhaji Abba kuma hannun Meenal dake cikin hannun shi ya murza ya ce.

“Ki yi hak’uri kinji meenalyn daddy kinji na fad’a mata bazata Kuma ba”.

Meenal gurza ido ta fara alamun za tai kuka ta ce.

“Daddy ai banji ta ce bazata Kuma ba”.

 

 

 

Alhaji Abba kallan Hajiya Mariya ya yi ya ce.

“Hajiya Mariya wai me yasa kike haka ne,shikenan ke kinfiso kita ganin yarinyar nan tana zubba hawayanta, dan Allah ki yi mata maganar bazaki k’araba dan hankalinta ya kwanta “.

 

 

 

Mahaifiyar Meenal da ta fara gajiya da lamarin Meenal kallan Alhaji Abba tayi,ta ce.

“Daddy Meenal taya Meenal tana mace baliga ace bazan mata maganar aure b…”.

Tsawar da mahaifin Meenal yayi ma hajiya Mariya ce yasa tayi shiru”.

Meenal ko ci gaba da bubbuga k’afa tayi tana cewa.

“Ka ji ko daddy bazata bari ba ko!”.

Alhaji Abba cikin b’acin rai ya huna ma hajiya mariya hanya alamun ta fita.

Hajiya Mariya tashi tayi itama cikin alamun ranta ya b’ace ta fita,tana mai jan k’ofar d’akin Meenal d’in da k’arfi”

 

 

 

Bayan fitar hajiya Mariya ne,Alhaji Abba cikin lallashi ya ce.

“Ki yi shiru kinji meenalyn daddy,aure ai ba farillah ba ne,bare ace dole sai kinyi shi,idan ma bakisan yi ba bu komai ki yi shiru, da take maganar aure-aure waye mahaifinki?”.

Meenal nuna Alhaji Abba tayi tana goge hawayanta .

Alhaji Abba kuma yaci gaba da cewa.

“Tom kin gani nine me yi miki auran dan haka kima kwantar da hankalinki ,ita kuma kibarni da ita zata san ta sa Meenalyn daddy kuka”.

Haka Alhaji Abba yi ta allashin Meenal yana nan zaune har sai da yaga tayi bacci sannan ya tashi ya fita……….✍️

 

 

 

 

Meenalyn daddy karki gaggawa Sister ki bini ahankali har in kaiki inda nake son kaiki,salon shi da ban ne daga cikin litattafan marubuciyar.

 

idan kin karanta sister ki, daure ki comment dan ki kasance d’aya daga cikin wa’inda zasu samu banus d’in da zan saki a littafin nan,alk’awari ne insha Allah kuma zan cika.

Share & comment pls

 

 



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Meenalyn Daddy Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!