Hausa Novels

Mene ne aibu na Hausa Novel Complete

Mene ne aibu na Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: MENE NE AIBU NA

 

©Jeeddah Tijjani Adam

(Jeeddahtulkhair)

 

Follow me on Wattpad

@jeeddahtou

 

27/6/2020

 

1

 

Drivern yake amma gaba ɗaya hankalinsa ba a jikinsa yake ba, ya rasa ta inda zai fara, tunani ɓacin rai gami da damuwa su suka mamaye zuciyarsa, duhu kawai yake gani, ya rasa duk wani farin cikinsa, bai qi a ce yau mutuwa ta ɗauke shi ba, sabo da tsananin damuwar da yake ciki.

Lumshe idanu ya yi gami da fitar da numfashi mai tsananin zafi, ɗaci kaɗai yake ji na fita daga cikin makoshin sa, bai san wanda zai tunkara da maganar ba, ballantana har ya iya yi masa maganin matsalar sa, Rahma ce kaɗai ita ma kuma a yau ta guje shi ta juya masa baya, bai ankara ba yaji motar na ƙoƙarin kwacewa daga hannun shi, wannan dalilin yasa ya dai-daita tunaninsa ya fara ambaton Allah don shi kaɗai ne abin da xai kawo masa rangwami a halin da yake ciki a yanxu.

Agogon da ke daure a hannunsa ya duba ƙarfe 12:00 dai-dai na rana, juyar da motar ya yi da niyyar ya wuce gida, amma sai wata zuciyar ta bashi shawara da kada ya tafi idan ma ya je gidan ƙarin wata damuwar ce, don haka ya kama hanyar zuwa ƙauyen Gud’e da ke karamar hukumar Gwarzo, zuciyar shi gaba ɗaya a raunane take sabo da bai san ta ina zai fara ba.

A hankali ya ci-gaba da murza sitiyarin motar har ya isa cikin garin, a bakin hanya ya tsaya ya siya kayan marmari ya wuce da su, tun daga farkon garin mutane ke masa barka da xuwa kasancewar Aliyu mutum ne mai kyauta da girmama jama’a, kuma a duk lokacin da ya je sai ya yi musu alkhairi mai yawa, wannan dalilin ya sanya duk wanda ya ganshi sai ya yi masa barka da zuwa.

Karanta Littafin Kuruciya Hausa Novel

A bakin wani gida ya yi parking, gida ne irin na fulani gefe guda kuma ga shanun da suke kiwo, sai kuma rumfar kwano da ke gefe guda, cike da nutsuwa ya buɗe murfin motar sa ya fito, a hankali yake takawa ya nufi inda wasu dattijai guda biyu ke zaune bisa tabarmar kaba kowannen su hannun shi riƙe da mahuci suna fifita kasancewar lokacin ana zafi sosai, tunda suka hango shi suke washe masa baki tare da yi masa sannu da zuwa, kanshi a sunkuye ya ƙarasa inda suke, cike da girmamawa ya risuna ya gaida su, fuskar su ɗauke da murmushi suka amsa tare da kiran sunan shi.

“Aliyu barka da zuwa kaine a garin namu, ka zo tafiya da Rahma kenan, dama kai ba a ganinka sai ka kawo ta ko kuma kazo tafiya da ita” suka fadi maganar cike da zaulaya.

Rausayar da kai ya yi.

“Haba Baffa ba haka bane, ko da Rahma ko babu ita ya zama dole nazo na gan ku” gaba ɗaya suka kwashe da dariya.

Sai da suka ɗan taɓa hira kaɗan sannan ya miƙa musu ledar da yake ɗauke da ita, godiya suka yi masa tare da saka masa albarka. kallon shi Baffa ya yi tare da yi masa magana cike da sakin fuska “ka shiga ciki mana ka gaisa da mutan gidan ita ma Rahman tana ciki, tunda dama don ita kazo” ya ƙarasa maganar tare da taɓa kafadar Aliyu.

 

Da farko sai da ya ji kamar yace masa bazai shiga ba sabo da bai san irin karɓar da Rahman zata yi masa ba, amma sai ya daure ya tashi, cikin ƙasan zuciyar shi cike take da tsoro, sabo da a yanzu babu wani sauran so ko kauna da Rahaman ke masa, illa ma dai kallon shi take a matsayin mutumin da ta fi tsana a rayuwarta, wanda bata so ko hanya ta haɗa su, wanda take addu’ar Allah ya nisanta ta da shi. Cikin ƙarfin hali ya amsa masa da “To” ya tashi ya shiga ciki.

 

Babu abin da zuciyar shi ke yi banda dukan uku-uku, tashin hankali ne sosai ya bayyana a fuskar shi, a hankali ya ja ƙafa ya shiga cikin gidan cikin sassanyar muryar shi ya yi sallama, wata dattijuwa ya tarar a tsakar gida tana tankade, da fara’a ta tarbe shi. “Barka da zuwa Malam Ali jan zaki, dama na san dole zaka biyo Rahma, kai da kace zata yi sati biyu ga shi ko kwana biyar ba a yi ba ka biyo ta, lallai wannan angon nawa ba kada ta ido”

 

Ɗan murmushi ya saki wanda ya tsaya iya saman lebban shi, wato yau dai innah ɗan biki ku ke yi min ke da Baffa, shi ma abin da ya faɗa min kenan yanzu kema kuma ga shi ki maimaita” Gefenta ya samu ya xauna tare da ɗaukan rariyar da take tankade da shi “bari na taya ki aikin innah” murmushi tayi “A’a bar shi Malam Ali, so kake Rahma ta ci tara ta na saka mijinta aiki ko? ka san kishi take da ni” Da sauri yace

“A’a baxa ta faɗa ba innah ai ta san kece ta karfen” gaba ɗaya suka kwashe da dariya.

 

Rahma na cikin daki tana bacci sama-sama take jin sautin murya kamar ta Aliyu, tsaya wa tayi ta saurara sosai don ta tabbatar da cewa shi ɗin ne ko mafarki take yi? jan dogon tsaki tayi tare da faɗin .

“Lallai Aliyu ya cika cikakken mara zuciya kuma mara kunya, ta ɗauka irin cin mutuncin da tayi masa zai sa ya rabu da ita har abada amma sai ga shi ya zo” sake jan tsaki tayi sannan ta juya ta ci-gaba da bacci abin ta, a yanxu bata buƙatar ji ko ganin Aliyu, ta tsane shi har ƴaƴan da suka haifa tare bata san gani, tuni tsanar shi ta gama shigewa xuciyarta, babu abin da tafi buƙata a yanzu sama da tayi rayuwa ita kaɗai ta tsani duniyar da abinda ke cikinta, da zai sauwake mata auren shi da tafi kowa farin ciki, amma ta san hakan ba mai yiwuwa bane, kasancewar su Baffa baxa su taɓa goya mata baya ta cimma burin ta ba.

 

Shimfida innah ta yi masa suka ci-gaba da wasan su na jika da kaka, sai da suka yi hirar su sosai ta dama masa fura ya sha, sannan ya tambayeta ina Rahmarsa take. Cike da tsokana tace

“Dama na san zancen kenan wato dai baxa ka bar min ita ba kenan, sai ka zo ka ɗauke ta dole, ita da tace sati biyu zata yi yau daga kwana biyar har kazo tafiya da ita, har yanzu ban gaji da ita ba fa”

 

Murmushin ƙarfin hali ya yi “kema fa innah idan na bar miki ita da kan ki zaki ce nazo na ɗauki kayata, don ta riga da ta saba da ni baxa ta iya rayuwa idan bana tare da ita ba” murmushi suka yi gaba dayan su.

 

Nuni tayi masa da hannu “Shiga daki tana ciki tana aikin bacci ka san a rayuwar Rahma ba tada aikin da ya wuce bacci kamar wata kasa, murmushi yayi tare da cewa.

“Ai rayuwar ce sai da hutu innah”

“Hutu yana da kyau amma dai nata ya yi yawa, ya kamata ka riƙa yi mata faɗa tana ragewa, ko don sabo da an fara tara iyali”

 

komawa tayi ta ci-gaba da tankadenta shi kuma ya nausa kanshi cikin dakin da Rahma ke kwance.

 

Cikin rawar murya ya yi sallama amma ga mamakinsa sai ya ji shiru ba a amsa masa ba, nan ya shiga laluben inda take kasancewar dakin da duhu ba haske, wayar shi ya dakko ya kunna touch light, hangota ya yi rakabe jikin karfen gado ta lumshe idonta kamar mai bacci, da dukkan alamu tana jin shi ba bacci take yi ba.

 

A hankali ya ƙarasa inda take tare da jan mayafin da ke rufe a jikinta, a fusace ta buɗe idonta wanda suka yi jawur, cike da zafin rai take masa magana.

 

“Kada ka karaso inda nake, kana karaso wa wlh sai na kashe ka, cikin rayuwar murya yace me kike faɗa haka Rahma ko dai aljanu ne suka shiga jikin ki, ni ne mijin ki fa wanda kike tsananin so, kada ki manta da tsananin kaunar da ke tsakanina da ke me nayi miki wanda na can-canci wannan hukuncin daga gare ki? Me yasa har yanzu kika kasa fitowa ki faɗa min laifina, me nayi kika guje ni me nayi miki, me na rage ki da shi, idan kin guje ni ai bai kamata ki guji ya’yan ki ba, ki dawo mu ci-gaba da rayuwar mu, Rahma kece farin cikina ban san kowa ba sai ke, dan Allah kada ki rabu da ni” Ya ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.

 

Bata ko kalli inda yake ba, ballantana ta san abin da yake faɗa, tashi tayi tsam ta koma kan gado ta shige bargo ta rabu da shi, haka ya gama koke-koken sa ya tashi.

Mamakin taurin zuciya irin na Rahma yake yi, gaba ɗaya ta canja daga Rahman da ya santa, taurin kanta da tsaurin ra’ayinta kamar ba mace ba, yana mamakin irin wannan hali nata, duk wata ya mace tana hakuri da mijinta indai ta fara haihuwa da shi amma a bangaren Rahma sam ba haka abin yake ba,

duk irin halin da ya shiga gaba ɗaya bata tausaya masa ba ko ƴaƴanta bata tunawa ita kawai rayuwarta take yi. Haka ya share hawayensa ya dai-daita tunaninsa sannan ya fita, don baya so innah ta gane halin da suke ciki, don da dukkan alamu bata san abinda ke tsakanin su da ita ba, kuma ya san Rahma baxa ta taɓa faɗa musu ba ko don kada su shigo ciki su dai-daita su. Da jan Kafa ya fito tsakar gida.

Har yanzu innah tankadenta take yi tana ganin shi ta hau murmushi sai yanxu aka fito kenan ai na ɗauka yau zaka tafi da abarka, murmushin ƙarfin hali yayi.

“Innah tace ba tada lafiya shi yasa na kyaleta sai ta warke na tafi da ita” kallon shi tayi to ai ko don yaran ya kamata ta shige ta tafi zaman ya isa haka ziyara tazo mun ganta ta gan mu ya kamata ta tafi haka, waye zai ci-gaba da kula da yaran naku?

A sanyaye yace

“Akwai mai kulawa da su yanxu haka nima kuma ina kula da su idan na dawo daga aiki” bai so maganar ta ci-gaba don haka ya katse mata maganar da suke yi.

hannu yasa a aljihu ya dakko rafar Yan 200 ya miƙa mata. “Ga wannan kya ci goro innah”

“Na gode sosai Aliyu Allah ya yi maka Albarka Allah ya raya maka zuri’a amsawa ya yi da Ameen sannan ya fita.

 

Su Baba ma rafar Yan 200 ya Basu sannn ya wuce ya tafi.

Tunda ya kama hanya xuciyar shi take saƙa masa abubuwa da yawa, bai taɓa ganin Rahma a irin wannan yanayin da ya sameta yau ba, gaba ɗaya bata tausayin shi ballantana taji tausayin ya’yansu da ta baro babu wani mai iya kulawa da kansa a cikin su, bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba yau kuka yake yi sosai kamar ba namiji ba, cikin ƙarfin hali ya ci-gaba da drivern har ya isa bakin wata makaranta mai suna Hikma science academy inda a nan yaransa fateemah (Baby) da Ahmad (Abba) suke karatu, a bakin gate ya tarar da su kowa ya watse saura su kaɗai, sun haɗa kai da gwiwa, da dukkan alamu su ma suna cikin irin damuwar da mahaifin su ke ciki, suna jin tsayuwar motarsa suka taho da gudu suka rungume shi suna murna.

Ɗaukan Abba ya yi ita kuma baby ya riƙe mata hannu suka shiga mota.

 

Baby ce ta kalle shi “Daddy me yasa baka zo ka ɗauke mu da wuri ba” kallon ta yayi tare da dafa kanta.

 

“Naje taho da momyn ku ne” dariyar murna suka yi yauwa daddy dan Allah kace ta dawo mun yi missing dinta, me ta baka ka kawo mana, wata alawa ya dakko ya miƙa musu kun ga abinda tace na baku, da murna suka karɓa suna sha, har suka isa gida babu hirar da suke yi banda ta mahaifiyar su, zuciyar su cike take da kewarta da shaukin son ganinta.

 

Suna isa gida ya yi

Horn mai gadi ya bude masa gate tare da yi masa sannu da zuwa ya shiga, kallo ɗaya zaka yi wa gidan ka san ya rasa abubuwa da yawa, komai kaca-kaca babu gyara ballantana kintsi, kofar parlour ya buɗe suka shiga, ba tare da bata lokaci ba ya cire musu uniform ya shigar da su bathroom ya watsa musu ruwa ya shirya su sannan ya shiga kitchen ya haɗa musu abinci sai da suka ci sannan ya kai su islamiyya, shi kuma ya dawo gida.

 

Gaba ɗaya a ‘yan kwanakin nan Aliyu ya zama abin tausayi shi ne uwar kuma shi ne uban, a kan laifin da bai san ya aikata ba uwar yayansa ta guje shi, wanda idan faɗa masa ta yi suka zauna suka fahimci juna za su iya warware komai ba tare da tashin hankali ba.

 

Kan gado ya faɗa ya kwanta rigingine yana tunanin ta inda zai shawo kan wannan matsalar da ta kunno masa kai.

Rungume pillow ya yi tare da runtse idanunsa yana ta sambatu, babu komai a zuciyar sa face shaukin son Rahmar sa.

 

Follow me on Wattpad @jeeddahtou

 

08094136204

Leave a Comment

error: Content is protected !!