Mijin Buzuwa Hausa Novel Complete
MIJIN BUZUWA complete
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM MUNA GODIYA GA ALLAH DA YA BAMU DAMAN RUBUTAWA DA KARANTA WANAN LABARI UBAGIJI YADDA MUKA FARA LAFIYA MUKAI KARSHEN SHI LAFIYA .
KISHI DA BUZUWA SAI KA KWANTAR DA HANKALI KA KAI AIKI DA HIKIMAR KA WAYEWA DA ILIMI BAI FITAR DAKAI A GARESU, , , ,
GODIYA GARE KUMA KARANTA NOVEL DINA DA KUKE KOKARIN DAUREWA DA HAKKURI WURIN KARANTA LABARAINA WANDA ABUBUWAN DAKE YAWAN FARUWA A NAHIYAR MUCE MUKE TABOWA DON HASKA KAN YAN UWA DAMA MU DUKA.
NOVEL DINA NA KAUYAWA NE BABU YAWAN KARAYAN ARZIKI A CIKIN SHI SAI DAI ABINDA LABARIN YAZO DASHI BABU FAYYACE FITSA A FILI YADDA WASU KE SON IN SAUYA ZUWA HADI DA FITSARA NA KASANCEWAN MACE DA NA MIJI A GADO A HAKKAN KUMA NAKE DA DINBIN MASOYA MASU KARANTA SHI A HAKAN, GODIYA GARE KU HAR KULUN MASOYA DA MASU KAUNA NA.
GAMA SU SON NOVEL DIN ZAKU IYA KIRA NA DA WANAN LAYIN DON NEMAN KARIN BAYANI DARI UKU NE GA MAI SON BIYA TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK
09026931792 KO 08036959257
A Rubuce take Hausa Novel Zafafa Biyar
Hadari ne ya hade garin sosai baka ganin komai sai walkiya da kara kainan motoci a lokacin wanda suke haskawa don ganin gaban su.
A daidai wanan lokacin ne motoci guda uku da suka karyo titin a jera wanda ke nuna wani mai akwaine tafe a lokacin yadda mutane suke ta kaucewa a titin suna basu wuri.
Wasu daga bakin titi ke fadin yanzun haka ma ba maigidan bane tafe wanan fitsarariyar matan tashine haka da bata ganin kowa da mutunci a idon ta.
Wani gida motocin suka shiga a lokacin gini ne na zamani motan ne suka dan tsaya da alama magana akeyi da wani a cikin gidan.
Ba a dade ba suka wuce zuwa cikin gidan kai tsaye security ne suka fito don bude motar nan naga wata farar mata buzuwa ta fito tasha ado na fada da gani daga saman ta har kasanta kwaliya ne.
Doguwa ce sosai ga fari sai dai idan ka kura mata ido zaka iya gano farin ne kawai ke aki yake rudin mutane don kyau akwai kyau inda bamu matan mu na Nigeria masu kyan asali da dire bayan farin da gashi da kuma tsayi babu abin da suka dara matan Nigeria dashi na fannin kyauwo.
Tana wani tako ta shige ciki zuwa part din ta ta dan jima ciki ta fito tana kwala ma wata mata mai suna Labara kira da karfi .
Da saurin matar ta iso gareta tana dukawa tare da fadin hajiya barka da zuwa an dawo lafiya yaya han, , , ,
Dakata tace wa matar yaya naga witan part din can a kunne ko mara zuciyar nan ta dawo ne kuma ?
Matar ta dago kai a hankali tace wa hajiya babba kike nufi waye hajiya baba ina nufin fatima matar wancan shiyan ta fada a fusace jin an kira uwar gidan nata da hajiya babba taji haushi.
Eh ta dawo laraba tace ai tun ranan da kuka wuce washe gari ta dawo kutawa tayi tare da juyawa da karfi ta shige part din ta a hasale.
Anan tabar laraba da kallon mamaki ta nisa tana fadin ikon Allah mata da mijin ta kinzo kin hana zaman lafiya a tsakanin su haka ?
Ita kuma a daki sai faman huce takeyi ita daya nan ta dauki waya ta kira mijin nasu da suka rabu yau ya tafi waje yin wani aiki.
Duk da tasan dare ne a duk inda yake amma bai hanata kiran shi ba a wanan lokacin saboda tsananin kishin dake damun ta a lokacin.
Kiran farko ya tsunke bata hakkura ba ta sake kira a karo na biyu bai daga ba sai wayan na gap da katsewa ya dauka da alaman barci yake a lokacin .
Murya irin ta masu barci ya daga wayan tare da fadin Nafisa lafiya kira da dare haka yanzu fa kin san dare ne nan sosai a wanan lokacin.
Bata jira ya gama magana ba tace watau munafuntana zakayi ashe kasan matar ka ta dawo shine baka fada min ba tun muna tare sai kawai in dawo in samu ta dawo gidan.
Ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin tadawo fa ni ban san ta dawo ba don basu fada min da cewa zata dawo ba ma kit ta kashe wayan.
Ta wurga a gefen gadon ta tana fadi a fili duk sai nayi maganin shegun tsofin don sai auren nan ya mutu inga ta bakin naci irin nasu.
A daidai lokacin ne kuma aka turo kofan side din nata wata matace cikin dogon riga ta dora hijjab a saman rigan nata.
Fuska da murmshi tace mutanen Abuja ashe kuna tafe yanzu ne an sauka lafiya yaya hanya fuska a daure ta juyo tana fadin eh muna tafe ko idan zan dawo sai na sanar da wani akace ko ma ?
Ke yanzu don baki da zuciya dawowa kikayi duk da maigidan ya nuna baiyi dake saboda rashin zuciya irin naki sai da kika dawo kamar ana zama dole ne.
Matar tadan sake murmushin dabai kai ciki ba tace nake ganin ke nan haka amma ni nasan yana yi dani har gobe ke ce dai ganin ki ke rudin ki ga hakan don ko na bar gidan shi bamu rabuba don ga diya ga zumunci a tsakanin mu.
Fati ke nan zakiko ga abinda ba daidai ba wallahi in dan kin nace sai kin zauna min da miji don sai na rami ya fiki shan iska a gidan nan tunda haka kika zaba wa kanki sannu sugar mai iyali ko tasbi sarkin zumunci shida bakajan da daya bai biyo ka ba .
Murmshi tayi Allah na tare da mai gaskiya dama jin kin dawo ne yasa nazo taron ki da dawowa ba wani abu ya kawo ni ba a huta lafiya bata tsanmanin ta amsa mata ta fice daga dakin .
Zuciyar ta yana ciki da mamakin fitsara irin na Nafisa wanda sam babu kunya a cikin shi ko kadan sai zallah cin fuska da fitsara filli.
Daki ta nufa a daidai lokacin da ruwa ya gauce sosai a garin na kaduna kamar da bakin kwarya da sauri ta isa ta rufe mirrow da sauran abinda baison walkiya a dakin saboda tsaro wanda ba kowa ke wanan ba a wanan lokacin sai masu sani da hakan a baya suka saura rufe irin wa yan nan abubuwan a daki yayin da ruwan sama ke zubuwa daga samaniya don kariya daga fitinan walkiya.
Falo ta dawo ta zauna tare da yaranta dake cin abinci a wanan lokacin ido ta tsurawa yaran biyu sai da ba wai don tana kallon su hankalin ta yana gare ta ba ne tunane takeyi a zuciyar ta na irin rayuwan da ta tsunci kanta a ciki yanzu.
Tun shigowan Nafisa cikin su komai na rayuwan ta da mijin nata ya sauya sallo a lokaci daya ba yadda suka saba gudanar da rayuwan su ba suda yaran su da sauran yan uwa.
Hatta yaran yanzu a matse suke da zama gidan mahaifin nasu sun fison zama a gidan kakanin su da zaman gidan nasu saboda matsin da suke ciki a yanzu.
Ita dai tasan aure ne a tsakanin ta da mijin ta na soyayya tun tana karama soyayyan su ta samu asali don gidajen su basu da nisa da juna shi din abokin yayan ta ne.
Kuma akwai zumunci na makwabtaka da ya koma kaman na jini daya a tsakanin gidajen su tun kakan su zumunci ya kulu a tsakanin gidajen biyu.
Wanda yakai bako ba zai iya banbanta tsakanin su ba sai wanda yasan tushen abin koda ta girma bai daina kulata ba cikin yan uwa haka ya kai har aure ya kullu a tsakanin su.
Tayi haihuwan farko lafiya ga cikin na biyune ya samu aiki kano suka koma can sun koma bada dadewa ba ya hadu da Nafisa yar mutan Niger da suka shigo Nigeria neman kudi da iyayyenta ta lake mai tun bai kula ta har ya soma kulata don suna sayar masu da abinci a bakin ma,iakatar su ne.
Yaron ta ne dayazo inda take zaune tana tunane ya katse da da fadin mama daddyn mu bai dawo bane naga anty ta dawo.
Shafa kan yaron tayi taja sauke ajiyan zuciya tace bai dawo ba Affan da kaga ya shigo nan ai anty ce ta dawo ita kadai.
Yaushe daddy zai dawo mama yaron ya kara jefa mata tambaya kuma tace Affan ban sani ba idan ya dawo ai zaku ganshi.
Bai barta ta huta ba ya sake jefo mata tambaya again yace mama ai anty ce bata bari mu ganshi ko munje wurin shi sai tace mu fito muna damun shi yana hutawa.
Murmushi tayi tace kai Affan ba yana zuwa nan ida muke kuna ganin shi ba to may kuma kake so shiru yaron yayi kamar yana tunane a zuciyar shi.
Sai kuma yace ni mama ban ma son ya dawo saboda may Affan uwar ta tambaye shi yace saboda idan ya dawo sai ki ta kuka mama su kuma suna dariya da anty kuma su fita tare.
Affan ban son yawan surutu fa ka faye surutu ina jin tsoron wanan bakin naka kullu naji ka kara fadawa wani matsalan mu sai na yanke ma kunne daya.
Shiru yaron yayi yana tunanen kada uwar ta yanke mai kune kamar yadda tace din kayan da sukaci abinci ta kawar ta gyara wurin suka shige dakin kwanan su.
Da safe bata fito ba sai da ta gyara part din nata ta nufi kitchen don dafa ma yara abincin zuwa school sai ta samu kitchen din a rufe.
Dakin kwanan laraba mai aiki ta nufa a nan ta samay ta tace yau laraba lafiya naga kitchen a rufe Labara tace aikin hajiya karama ne hakan.
Nima na fito zan gyara tace na barshi taja kofa ta rufe nayi tunanen zaki fito don saboda abincin yara gashi kuma ta kulle kitchen din.
Dan jimm tayi tana tunane a ranta wai may Nafisa take nufi da ita ne haka abinci dai na kowa ne a gidan amma haka take mata idan ta bushi iska sai tace wai ana barnan abinci da yawa gidan.
Bayan abinci ma da take ita daya sai ta ba wasu balle yanzu da ya samu karin girma sosai a wurin aikin shi basu da talaucin komai a rayuwan su.
Muryan Laraba ne ke fadin sai hakkuri hajiya idan mutum ya ci gaban ka sai dai bi wallahi gama tana ganin ta samu miji a hannu sai abinda tace a gidan.
Ba komai Laraba na gode badin tura su can cikin gida wurin hajiya su karba haka ta juya ta wuce zuwa part din ta tabar Laranba a wurin tana jin tausayin ta.
Daki ta koma ta shirya yaran ta fito dasu da kanta ta mika wa kanin mijin su dake zaune dasu a gidan ya kaisu cikin gida wurin hajiya a basu abinci.
Yace yau kun makara ne tace eh salis koda na tashi har gari ya haska sosai wallahi kaga idan nace zan tsaya dafa masu yanzu sai su makara.
Ta koma ciki ya kwashe yaran zuwa gidan su dasu don duk a unguwa daya suke zaune da iyayyen nasu gida uku ne a haka kuma Nafisa ke tsula tsiyar ta a gidan.
Don tafi son zaman kaduna saboda anan kawayen ta suka fi yawa da yan yaren su na buza da suke kara zugata tana iya shegen.
Salis na shiga gidan kafin ya isa part din mahaifiyar mijin nasu da yaran matan gidan suka fara magana a, a su Affan ne haka yau da safe nan.
Salis yace eh maman su ta makara ne yau bata tashi da wuri tayi masu abin karyawa ba shine zasu zo nan su dauka.
Murmushi hajiya kubura tayi tace Fatice zata makara da safe kawai dai yar bakin halin gidan su ta dawo jiya akwai da wata a kasa.
Ba an mayar da Fati bata san tadawo ba shine ta dawo ta samay su bakin halin nata na banza ya tashi yanzu ta soma ke nan har sai ta kure ta ta tanka mata.
Allah dai ya sauwa dayar matar gidan ta fada daga daki tace shi kuma da yazo sai ya biyewa iya shegen nata ba daga daki suke magana.
Sun shiga gun kakan su tana ganin su tace ai na sani ba yar iskan yarinyar nan ance ta dawo jiya ba nan yanzu tsiya zai tashi a gidan wanan karo ko ba zan saurara mata ba wallahi.
Salis yace cewa tayi makara tayi fa bata samu dafa masu abinci ba yau yaya maganan ku yazo daya da na mommy ne ?
Hajiya bata iyayin magana ba sai jan yaran datayi zuwa cikin part din ta ta zuba masu abincin da tayiwa yan marayun jikokin ta da suke hannun ta.
Bayan ta gama sallaman yaran ne ta dauki waya ta kira Fati din tace wai may ke faruwa ne yau a gidan naku cikin fara a ta fara gaida surukar nata da bata ko tsaya gaisawa da ita ba.
Amsawa tayi sama sama dakyat tare da maimaita tambayan ta a gare ta tace hajiya makara nayi tace jinan fati na san komai walahi nasan abinda yar banzan yarinyarin nan zata iya.
A sanyaye fati tace hajiya ba haka bane makara nayi yau din ban samu dafawa ba kashe wayan hajiya tayi badon ta yarda ba.
Kashe wayan nata yayi daidai da shigowan hajiya kubura wurin ta tace sai gasu Affan na ga sun zo karban abinci kuma ?
Bari hajiya Kubura duk da uwarsu ta boye min na san akwai wata a kasa wallahi bai yuyuwa haka kawai taki tanadarwa yara abin zuwa makaranta.
Nan suka zauna suna maganan hajiya kubura tace idan ita fatin bata iya magana mu ba kyalewa zamuyi ba ai ana horo da yuwa ne kuma ?
Kai hajiya ta dafe tace Allah ya kawo muna karshen wanan yarinyar a gidan nan hajiya kubura tace amin tana mikewa tare da fadin bari mu gani zuwa rana idan har sun dawo nan kin ga hasashen mu ya tabbata ke nan ta rufe kitchen din nasu ke nan.
Ta fice ta bar hajiya a cikin bacin rai tana tausaya ma wanan rayuwa da yayan nasu suka tsunci kan su a ciki na bamin auren buzuwa da ya dorawa rayuwan shi yana zaune kalau da matar shi ya jajibo masu wahala haka.
A gidan Fati kuma bata karya ba tun safe ba tunanen kanta takeyi ba a yanzu sai tunanen idan yaran sun dawo may zata basu idomie ne ya fado mata arai ta sayo ta dafa masu suci.
Damay zaki dafa wani zuciya yace mata tsaki taja tana tausaya masu a ransu take tunanen da can baya lokacin tana ita kaida ya fado mata a rai.
Abinci sai wanda ransu ke so zata dafa da ita da yaranta da maigidan ta har sai taba makwatab wani lokaci yau kuma gashi a sanadiyar kishi da buzuwa har horo yakai ga a rufe store da madafar abincin gidan baki daya.
Babu wanda zata kara kai kara gareshi tunda baji mijin nasu keyi ba ko ta fada karshe ma ya dawo ya hauta da masifa gashi ita ba son masifa take ba a rayuwan ta.
Haka ta taso da tsoro sam bata fada ko kadan saboda ruwan ciki irin na matan hausawa da ta taso a cikin shi wanda a cikin tarbiyan diyan hausa yake.
Kamun kaina a diyan hausawa rasgin hayani da fada da mutane barkatai wanda akasarin matan hausawa hake ne ke cutar su a gidan mazaje su da gun kishiyoyin su yan bana bakwai.
Tana tuna yadda Nafisa tazo gidan daga ita sai ghana most go din yan kayan ta a ciki amma yau ta koma kamar wata hamshikiya a gida.
Auren ta da aka dauro ba tare da sanin iyayyen su ba can bariki suka dauro auren su da ita inda ta tare a gidan da yake a lokacin a kano.
Sannu a hankali har ya samu iyayyen shi suka hakkura ta fara shiga cikin su inda take baiyana harin ta na zahiri a hankali.
Da farko ta yaudari mutane inda taja yan uwan miji a jikinta duk suka yarda da ita ta gama jin sirin su kaf kafin daga baya data bunkasa ta fara fitar da kalan ta ga mutane.
Inda yanzu kowa ya gama gane ta wasu masu zuciyar imani sun gujeta masu kwadai kuma har wanan lokacin suna tare da ita duk da abin hannun ta bai ban baruwa wasan dadi sai kayi mata bauta kafin kaci abu daga gare ta.
Don haka take kallon kowa a wullakance sai uan uwanta dakan zo jefi jefi cin arziki wurin ta wanda ba a wuce wata daya basu zo gidan ba.
Tazo da wata yarinya da take cewa wai kaunar tane sai da tafiya yai tafi aka gane cewa yar tace ta cikin ta yarinyar.
Nafisa zata girmay ma Fati ga shekaru haka yasa tafi fati wayo sosai har take jin tsoron ga fin karfi ga sihiri don bata shigo haka kai tsaye ba sai da ta shirya ta shigo gidan .
Shi kan shi maigidan ba a banza ta barshi ko yanzu kuma bawai ta fasa abinda takeyi din bane sai ma abinda yaci gaba a cikin halayen nata.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Ina isa na fara bude kofana na lokacin yarinyar ta iso da kayan da Yusuf ya bata tana mika min kallon kayan nayi sai na karba ta karasa min da sauran a cikin daki na.
Godiya nayi mata tace babu komai ai ana tare bayan na aje kayan na fada saman katifa na wasu hawaye masu zafi ne suke silalo min a fuska na.
Idan na tunana da maganganun da ya fada min masu zafi duk da nima din nayi karfin halin ramawa a lokacin sai nake ganin ya kwaraini da yawa.
Na dade a wurin ina neman hanyan da zan rama abinda yayi mun din don yaji zafin da naji ban kai ga samun mafita ba wayana yayi kara a lokacin.
Yusuf ne ya kirani sai da ta kusa tsukewa na dauka na kara a kunne na ina sauraron shi yace har yanzu kina fushi ne yar mama.
Daurewa nayi nace ai ban fushi dakai don bakai min komai ba yaya na yace dakyau ina son ki saurare ni dakyau magana nake so muyi dake yanzu.
Ina jinka nace mai.
Khadija don Allah ina son ki bani hankalin ki ki fahinci abinda zan fada maki yanzu naji na kara furtawa.
Don Allah ina son in rokeki wata alfarma wani aiki zaki nake son ki min a kan aboki na amma aikin yana da wahala sosai sai dai indan kin daure ba wani wahala a cikin sa.
To ina jinka Allah yasa zan iya kuma Allah yasa dai aikin bai fi karfina ba, murmushi yayi yana fadin bai fi karfin ki ba ma insha Allahu don zaki iya.
Nace fada min inji aikin idan ba zai shafe karatuna ba da rayuwa na zan iya insha Allahu yace good girl dama na dade ina neman mace irin ki mai gaskiya da zan saka.
Ba wani abu zan saki ba sai taimako rayuwan abakina Samad nake son in danka a hannun ki don kice a yanzu kadai nake da ita da zatayi min wanan kokari.
Nace ni kuma yayana yace kwarai kuwa ke khadija don ko zaki iya idan munyi laakari da irin halin ki na san zaki iya shiyasa na zabo ki.
Tun ranan da muka shiga dakin hajiya mama na fara ganin ki da kuma abinda yafaru dake da Nafisa matar shi kika tsaya min a rai.
Ban kuma gaskanta hakan ba sai da naga kin iya biyu su a motar su zuwa nan Abuja kuma komai bai faru ba yasa na kara yarda da abinda nake shirin yi din .
Sai gashi kuma yanzu abubuwa suna wakana a yadda nake son su tafi a tsakanin ku cikin hukuncin Allah komai yana tafiya daidai.
Khadija ko kin san ba macen da ta isa ta tsaya kusa da Samad tun lokacin da ya auri Nafisa buzuwar matar shi kuwa.
Nasan kin san matar shi Fati da akai masu auren gida har suka haifi yaya biyu shigowan buzuwa gidan ya sa suka rabu da ita badon basu son junan su ba.
Khadija kin san abinda ya daure min kai nace a a yace yadda Yusuf ya aminta dake a lokaci daya duk da nasan ba abu bane mai wuya a wurin Allah idan ya tashi yin ikon sa akan abu.
Don haka nake son ki taimaka muna ki sake jiki da shi tayadda zai aminta dake idan haka ya samu gare mu na tabbatar da sheri buzuwa yana gap da karyewa.
Da sauri nace ba zan iya ba gaskiya ku nemi wata wanan miskilin mara mutunci ai buzuwar ne daidai dashi yace khadija zaki iya zaki iya komai.
Kyau dai Allah ya baki shi ilimin addini da na boko duk kina dasu a wadace to may zai saki ce bazaki iya ba ai ko ba don niba ko don hajiya mama da fati da yaran ta zaki iya.
Nace yanzu may kaka son in yi wai yace shina ke son in fada maki da farko dai idan ki bi labari na zaki gane Samad bai iya ssoyayya ba shine matsalaan farko da aka samu gare shi.
Murmushi nayi nace bai iya soyayya ba ta yaya ya auri matan shi har suka zauna Fati har ta haihu dashi biyu shima din murmushi naji ya dan yi yace.
Bamu tare ke nan kin manta na fada maki ita fadi hadin iyayyene auren su ita kuma buzuwa abu biyu muke zaton shine silar auren su na farko dai ta rude shi da kyaun ta na biyu kuma ta hanyar sihiri da sauri nace sihiri kuma bada ni ba gaskiya.
Yace da zata iya maki komai da tayi tuntuni ai shine ya bani daman sakaki wanan aiki a yanzu.
Nace a takaice dai kana son in bata lokaci na a kan shi abinda ya kawo ni in barshi inje taimakon wani wanin ma wanda bai san darajan mutane ba.
Aikin da zaki muna ke nan dama ki koya mashi zama da mutane da sauran abubuwan da ya watsar a baya ki dawo muna dashi Abdulsamad din shi na baya.
Babban magana ke nan yayana yace ba wani babba bane a matsayin ki na mace zaki amfani da daman ki taimaka muna ki tai maki hajiya dake cikin halin bakin ciki a kashi.
Shiru nayi ina tunane ko badon Yusuf ba ko don hajiya da yaran Fati zan iya kasadan yin wanan gwajin da suke sona dashi yanzu.
Nace to shike nan naji zan yi matukar hakan ba zai shafi mutunci na ba dai yayi saurin cewa idan nasan zai zubar maki da kiman ki ba zan saka ki ba ai.
Nace amma fa in ya nemi keta min mutunci ba zan kyale shi ba zan dauki mataki da kaina yace wanan ba halin shi bane don nasan halin shi tare muka taso tun muna yara dashi.
Nace Allah bamu sa,a yace amin na godd da kika fahince ni yanzu zan samu lokaci in shigo inji mai kike bukata don kin san dole sai kin koma ke ma babban yarinya sosai.
Kada ka damu zanyi amfani da wanda nake dashi yace kin wuce wanan yanzu khadija zaki zama budurwan mayan garin abuja ne fa.
Yace ina son ki fara daga yau nace yau din nan ina zanganshi yace zai bugo maki waya ba yana da layin ki ba nace eh zaki kaga ya kiraki kan abinda yayi maki.
Amma sai dai please ki bishi a hankali yana da izza da saurin fushi da zuciya bai son yawan magana idan ba yaso ba amma banda wanan baida komai da zaki damu.
Ni kuwa nasan haka nida ya fada ma magana yau sun ranshi sai dai zan jure kamar yadda kuke so inyi din.
Ajiyan zuciya naji ya sauke yace ban san irun godiyan da zanma maki ba ga wanan haracin da kikai muna wanda nasan insha Allahu zai zamo maki alheri ke ma nan gaba.
To Allah yasa hakan alheri ne a gare ni dai fatana in ga ya koma da iyalin shi normal sai naji ya sauke ajiyan zuciya yace final shine dama bukatan mu .
Mukai sallama ya barni ina tunanen yadda abin namu zai kaya tsakanina da miskilin mijin buzuwa ta ina zamu fara nace anya ban daukar wa kaina abinda ba zan iya ba kuwa.
Gashi kuma Yusuf yace sirine ne tsakani na dashi sai Allah sai ko nan gaba da zai fada ma hajiya mama shirin shi.
A raina nace zan iya insha Allahu indai iyalin shi zasu dawo gare shi sai dai ban taba zaton abin zai zo a kaina haka ba amma ba komai wahala bata kissa ai.
Nan dai nayi ta tunanen ta yadda zan fara deal din akan shi amma dai Yusuf yace shi zai fara aiwatar da komai kamar yadda yake yi da farko.
Safiyan lahadi wanki nayi sai wanan bakuwar yarinyar da ta shigo min da kaya don dai han san ta a gidan ba tazo min hira dakina ina gugan kayan da suka bushe min.
Nan take fada min ai ita yar jos ne amma tana zaune ne da yayanta a nan cikin gari ta dawo hostel ne don ta samu yin karatu da kyau naji dasin haduwa na da ita ko banza zan rage zaman kadaici ni kadai da nakeyi ni kadai.
Waya na yai kara na daga Yusuf ne bayan mun gaisa yace fito gamu kofan hostel din ku dam naji gaba ya bada na kalli maryam dake gefe na nace ina zuwa ta mike ita tace zata je ta gyara daki don gobe akwai classes.
Ba wani dogon kwalliya nayi na dan yafa gyale na na fito tun fitowa idon su yana kaina har na iso inda suke a cikin motar su.
Na gaida Yusuf din yace ga abokina ogana baki gaida shi ba na dan juya wurin shi a yatsune nace oh ashe tare kuke ina wuni.
Haushi da takaici ya kama shi ya rasa ma zai yi sai da Yusuf yace khadija na gaishe ka fa cikin yanayi da alama na ko in kula yace lafiya kawai ya kawar da kanshi gefe.
A ranshi yace i hate dis girl wallahi Yusuf ya katse shi da cewa oga gata nan ta fito fa ya fada cikin tsigar tsokana ya juyo da sauri yace wa wurin na tazo dama.
Yace bakai kace muzo kabata hakkuri ba abinda kai mata jiya kasa ta kuka ya damay ka da sauri na tare Yusuf da cewa ai nice zan bashi hakuri nida na bata mashi rai jiya.
Don fadin gaskiya ni kuma nasan gaskiya na fada duk cikkaken namiji da yasan ciwon kanshi ba zai tsaya mace na juya shi macen ma kuma buzuwa wai.
Yusuf dama ka kawo ni nan ne don ta kara ci min mutunci ko may haushi ya ishe shi yarasa may zai ce min wallahi na tsani wanan yarinyar ya fada a hasale .
Cikin ko in kula nace i hate you too dama abinda yasa kuka zo ke nan daga ganin ka nasan ba yin kanka bane buzuwa ta hasala ka ka koma ma matar ka kawai ta asali ko mutuncin ka zai dawo ga idon jamma, a.
Yusuf yace kai oga fitina khadija ko rigima nace bai son gaskiya ne gadai mutum har mutum amma bai kai ga cikan kamala ba har yanzu ga idon jamma a.
Oh stop it gara ku fito fili kununa ma duniya soyayyan ku da wanan sallon soyayyan naku da kuke yi kullun u don’t need to pretend garama ku fara tun yau.
Wai Yusuf may kake nufi dani akan wanan yarinyar ne da kullun kake kawo ni wurin ta taci min mutunci hakane.
Ni dramar kuce take burgeni wallahi don naga idan na kawo ka wurin khadija tana saka magana kana rage damuwa ko yaushe kuma tana ma tuni da abinda ka manta.
Gyara zama yayi a motar ya kwantar da kai tare da harde hanaye shi wuri daya yana kallon bakin hostel din mu yadda mutane ke ta shiga da fita ciki.
Nima kallon Yusuf nayi nace yayana wani wuri zaku ne yace muna dan yawata wane muka zo duba ki kin san ke amanan hajiyan mu ce gare mu yajuya wurin shi yana fadin ko ba haka ba aboki na ?
Tsaki yaja ya kara kawar da kanshi gefe nace sai dai tsiyan abin indan yayi fushi fushin bai mashi kyau sai ma ya kara mai muni sosai.
Murmushin dole ya sake yace kai Yusuf muje don Allah wanan na gane zata iya haukatani in banyi da gaske ba.
Kaiko daukanta zamuyi mutafi da ita adan sawo mata wani abin mana kaga sai ta kara hucewa ko tunda gashi har ta baka hakkuri yanzu ai komai ya wuce kenan.
Kinga ba sai kin fada ma hajiya mama dukan bakin ki da yayi ba jiya ai yanzu kun zama friends kuma ko fada ya kare ke khadija ba yayaki hakkuri don Allah.
Da sauri ya juyo inda nake sai na dan durkusa nace ya Samad kayi hakkuri don Allah idan na maka laifi.
Oh baki san ma kin min laifi ba ke nan Yusuf yace shigo mota sai mu karasa magana a hanya yamma nayi kwarai.
Banki ba tunda nasan plain ne na shiga motar a hankali ya harba titi ina harara dan iska a inda nake zaune Yusuf ne ya shiga aiwatar da nashi shirin a lokacin cikin motar yana dan muna nasiha.
Yace kar kuji komai indan nine take a deep breath and confess your love to each other wani irin dogon nunfashi yaja tare da lumshe idanuwan shi.
Da sauri nace yayana love kuma a ina kataba jin anyiwa mutum dole haka akan abinda yaki jini yace don’t say dat again just say yes to each other don kuna bukatan hakan.
Khadija ina son ki rike min oga na tsakani da Allah ko babu soyayya ku zama aminan juna muna son ki gyara tsakanin shi da hajiyan mu ta fahince shi ta bar hushi dashi.
Sai lokacin ya kallo Yusuf ya sauke wani ajiyan zuciya don ya zaci Yusuf yana son hakane don gyara tsakanin shi da mahaifiyar shi.
Nace yaya zanyi in gyara mashi laifin dashi yayi da kan shi har kake tunanen nice zan gyara hakan yace yes idan hajiya taji kuna tare nasan zata ji dadin yin hakan da kuka kin ga zata fitar ma abokina da zargin da suke mashi na buzuwa bata bari ya rabi wata mace sai ita.
Sai yanzu na gane nufin ka abokina ya danyi gyaran murya sai kuma yayi shiru can yace da farko dai na gane manufan ka yanzu Yusuf .
Yace zamu shirya dake idan har zakiyi min wanan taimakon iyayyena su fahince ni a hankali nace idan ka shirya yin hakan a shirye nake in taimaka ma in har zaka koma masu da zuciya daya.
Maganan ta dan soshi ranshi amma haka ya dake yace na gode a hankali ai lokacin gode min baiyi ba nace mashi.
Tsayar da motar yayi a bakin wani babban sai da kayan sawa irin na mata da maza ga motoci birjit a wurin an paka su a haraban wurin.
Bissimilah yace muna kallon shi yayi yace wa wai ni kake nufi kowa yace daku duka nake magana ai yace may zanyi a wanan gurin yace kaunar mu zamu ma sayayya mana.
No kuje kawai yace yana gyara zaman shi a yadda yake nace da ka barshi ma ban bukatan komai a yanzu yace tunda nayi niyar yin haka barin in fita induba zaku iya jira a mota yana bude motar zai fita yake wannan magana.
Da sauri nace dashi barin fito mu shiga tare yace No ki zauna abinki yanzu zan fito ba dadewa zanyi a ciki ba.
Yana wuce na koma na zauna bayan na bishi da kallo wayana na dauko ina dubawa shiru motar babu mai maga a cikin mu sai can naji yaja guntun tsuki wai da bai harka da kananan mata sai manya masu aji ko su sai a waje idan yafita duk da ba wai yana yawan hurda dasu bane yanzun ga Yusuf yana son ya dauko mashi wani aiki ga wanan yar karamar yarinyar dako sa,an kannen shi batakai ba sosai.
Nima tsakin naja ina gyara zama cikin tunanen da nakeyi nashi.
Ga dai mutum har mutum kudi kwaliya kwarjini duk Allah ya bashi sai dai yawan miskilanci da girman kai da jan aji din yayi yawa kamar ba mace ce ke juta shi ba a gida.
Ke ni kike wa tsuki ko kowa ya juyo tare da zuba min kyawawan idanuwan shi a kaina na ma mance kana cikin motar nan murmushi mai kama da takaici yayi yaci gaba da zuba min kyawawan idanuwan shi can ya koma ya lumshe su tare da komawa saman kujera ya zauna.
Ya sake cewa kina aji nawa ne yanzu ba tare da ya juyo ya kalle ni ba shiru nayi ina game da wayana batare da na nuna mai dani yake magana ba.
Dake nake magana ko bakiji bane nace wa ni ai na dauka da kurma nake a motar a hankali ya kada kanshi ta dan sake murmushi yace ke dai ba zaki bar wanan halin naki ba ke nan.
Nace ba halina bane hakan a ra nayi don in kare kai na daga masu raina ma tallaka hankali ya fido ido waje yace haka kika dauke ni ke nan .
Hakan na gani kamar kana tsoron talaka a kusa da kai sai dai ba abun mamaki bane don ko a gida haka naga kanayi masu wanan daure fuskan.
Kin san nayi ma aboki na alkawarin ban kara fada dake yanzu don haka ki kama min bakin ki tunkan in hasala da wa yan nan maganganun naki.
Kai ashe kasan girman alkawari haka ne nakoji dadin jin hakan saidai kamar yadda kai mashi alkawari ka cika nima ada hakana naiwa kaina alkawarin ba zan tsaya da wani namiji ba sai gashi a sanidin taimako ina son karya alkawarin da na dauka ma kaina.
Yaja numfashi tare da cewa wanan deal ne a tsakanin na dan wani lokaci banga abinda zai sa ki dauke shi kamar serious ba.
Nayi dariya tare da cewa wasa mai kamar wahala ba indan buzuwa ta sanda hakan akwai matsala babba ashe sai na kwashe da wanni irin dariya mai ban haushi dake wa yayi bai ce komai ba cikin kuluwa.
Yusuf ya fito da manyan jakkuna a hannun shi yana kokarin bude motar ta kofar baya ya saka jin dariya yasa shi cewa abin ya fara tafiya ke nan dai.
Ya dai kusa na bashi amsa a takaice kai a fasa wanan deal din nace a fasa gaskiya zai fi don wanan ba zai kai ko ina ba.
Zai kai mana yace yana rufe kofan motan ya zagaya ya shiga kallon Samad dake dafe da kan shi yayi muka kama hanya a lokacin hadari ya hadu sosai a garin ruwa na iya zuba a ko wani lokaci.
Mun iso Yusuf ya tsayar da motar yace khadija mun gode sai mun kara haduwa yanzun ba time hadari ya hade gari ta ko ina nace nagode kwarai.
Ka kula min da mijin buzuwa don Allah na bude motar zan fita yace ga kayan ki nan ki kwasa duka naki ne godiya na sake mai karo na biyu na fice daga motar.
[…] Mijin Buzuwa Hausa Novel Complete […]
[…] Mijin Buzuwa Hausa Novel Complete […]