Mijin ki a tafin hannun ki

Mijinki A Tafin Hannunki.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Da sunan allah mai rahma mai jinkai, tsira da aminci su kara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW), cikin farin ciki nake gabatarwa al’umma wannan littafin wanda kamar yanda kowanne littafina yake shima wannan akan zaman aure yake Magana yanda ma’aurata zasu shawo kan matsalarsu don su zauna lafiya,

Akwai wasu ginshikai guda uku Wanda sune suke bawa mace damar tuka rayuwarta izuwa cimma kowanne burinta, hallau wadannan ginshikai uku suke bawa mace nasarar dauko mijinta ta Dora akan tafin hannunta ta yanda kowa zaice mata MIJINKI A TAFIN HANNUNKI,

1 SOYAYYAR MIJI,,,farkon burin kowacce mace kenan ta samu soyayyar mijinta sannan ta samu yardarsa, babu wani farin ciki da mace zatayi matukar ta rasa soyayyar mijinta, zaman lafiyarta ita da mijinta shine babbar nasara a rayuwarta.

 

 

 

 

Akwai wasu ginshikai guda uku
Akwai wasu ginshikai guda uku Wanda sune suke bawa mace damar tuka rayuwarta izuwa cimma kowanne burinta, hallau wadannan ginshikai uku suke bawa mace nasarar dauko mijinta ta Dora akan tafin hannunta ta yanda kowa zaice mata MIJINKI A TAFIN HANNUNKI,

1 SOYAYYAR MIJI,,,farkon burin kowacce mace kenan ta samu soyayyar mijinta sannan ta samu yardarsa, babu wani farin ciki da mace zatayi matukar ta rasa soyayyar mijinta, zaman lafiyarta ita da mijinta shine babbar nasara a rayuwarta.

2 IYAYE NA GARI,,, koda ace mata mace iyayenta baa raye tana bukatar masu tsaya mata wadanda sune zasu bata kimah da daraja awajen duk wani wanda zai zauna da ita,
haka zalika wadannan sune masu fada mata daidai ko akasin haka.

3 TSAYUWA DA KAFAFUNTA,,, abun nufi mace ta zama me tsayuwa da kafafunta bawai mai dogara da wani ba, komai gatan mace yanada kyau ta samu wani abunyi wanda koda ta shiga wani hali zai zama abun dogaronta.

to nidai kaddarata duka wadannan bana dasu domin tun ina karama na rasa iyayena A gaban mijin yayata na girma shine ya aurar dani daga bisani shima suka rabu da yayar tawa, ya zama bana da kowa sai mijina shine uwa shine uba haka zalika shine ‘yan uwana.

Soyayyar mijina kadai itace gareni wanda da ita na dogara amma daga lokacinda ya kara aure sai itama ta kubuce na rasa wannan soyayyar baya bukatar ya sakani a idonsa,
ya tsani ganina wanda azahirin gaskiya nasan matarshi ce ta rabamu, amma madadin na zauna na zama abun tausayi sai nayi tunanin me yakamata nayi don nazama abun koyi?
anan fa na fara bincike sai naci karo da rubuce rubucenka sai kuma naga kamar baka tabo bangare naba wato mallaka don ayanzu inaso mijina ya dawo hannuna ba tareda nabi bokaye ko maluman tsubbu ba, inaso nayi aiki da hikima tareda magani.

 

 

 

kamar dai yanda jama’a suka sani akwai hanyoyi da muke temakawa ma’aurata matukar munada yanda zamuyi idan babu yanda zamuyi kuma bana batawa kaina lokaci wajen yaudarar mutum.

 

 

 

 

daga lokacinda kika samu sabani da mijinki har aka kai matsayinda baya kallonki agansa ballantana ya saurari damuwarki to saiki bincika kiga meye matsalar?
bangaren saduwa ana samun matsaloli da dama wanda ba kowanne miji ne zai tsaya yanafadawa mace matsalar ba, kamar ciwon sanyi yana iya daukewa mace ni,ima mijinta ya dena jin dadinta kwata kwata tofa da zaran ya kara aure ya samu abunda yakeso dole kisamu matsala dashi.

rashin gyaran jiki da iya kwanciya wadannan sunada muhimmanci wajen mace idan har baki kware sosai ba da zaran ya kara aure ya samu abinda yakeso dole kefa uwargida kiga canji kinga yanada kyau kilura sosai.

rashin iya girki da tsafta da iya kula da miji wannan shima ginshiki ne na musamman da mata yakamata su kula dashi don idan fa kika rasa su da zaran ya samu wanda ta iya dole abarki abaya.

to idan kin tabbatar bakida wata matsala ajikinki to akwai hanyoyin aiki da magunguna wanda aikinsu hada dankon soyayya mace da namiji wasu ta hanyar saduwa wasu kuma hanyar wanka da gyaran jiki ahaka muna iya temakawa ma’aurata don asamu daidaito.

SIRRIN MALLAKAR MIJI
koda yake namiji ana mallakar zuciyarsa ne ta hanyar yi masa abinda yakeso ako yaushe amma kuma bangaren saduwa shine hanya ta farko da mace ke samun zuciyar mijinta.

dalili kuwa shine anan raunin kowanne namiji yake, kowanne irin mutum mace tana iya sarrafashi yanda takeso matukar yana bukatuwa daga gareta a kowanne lokaci,

tabbas akwai mallaka wajen saduwa saidai idan mace bata saniba ko kuma rashin nutsuwa wajen hadawa ko kuma dama mijinta ba mai bukatar mace bane,
shine yasa na duba wasu hanyoyin da mace zatabi don karawa kanta dandano sosai awajen mijinta kuma awannan karon itatuwa ne guda uku wadanda dukkansu tsarki akeyi dasu bawai matsiba, saidai kafin aiki da wadannan yanada kyau mace ta kula sosai don idan kinada ciwon sanyi bazaiyi ba,

 

TABA

akwai taba wanda matan fulane ke amfanida furensa zaki iya samun jijiyarsa wato na cikin kasar saiki hada da ‘yayan dan kadafi saiki tafasa ki tace ruwan saiki samu buta wanda dama ajiyeta zakiyi don hakan saiki zuba aciki ki ajiye kiyi tsarki dashi sau biyu kafin saduwa da miji.

RUMBUN KAYA

wata irin kaya kenan wanda zaki ganta bata rabuwa da ‘yar uwarta don idan zaki dauka saidai da wani abun don hanu baya iya rikeshi zai kama hannunki kamar kurar karfe haka take zaki hadata da ganyen taba da saiki tafasa ki tace shima dai ki zuba a butar amma wannan ana saka masa man damo kadan aciki sai arinka tsarki da ruwan sau biyu kafin saduwa.

 

 

 

 

AURE DAYA

wannan yana aiki 100% amma yanada matsala kamar warin gaba, wato na kashin rakumi da kashin tantabaru,
ganyen da ake hadawa dashi sunansa aure daya
wannan wani itacene wanda ake samu a inda yakeda tsauni kamar taraba da jos zan kawo sirrinsa alittafi na gaba asalin mallaka ne, akwai baiwa ta musamman a tattare dashi,
idan aka hadasu shima za atafasa sai atace ana tsarki da ruwan domin maganin wari zaki iya zuba miski a ruwa don kauda warin. saidai kamar mace wanda mijinta yake kawo bakinsa gabanta babu dama tayi amfani dashi.

KINASO KISAN WANI ABU AKAN TURAREN MALLAKA?

mashahurin hadin turaren mata wanda yakeda matukar tasiri musamman matan aure, Turare lamba daya kenan a duk wani hadin turaren mata wanda ayanzu yakai matakin da wasu ke ganin akwai siddabaru ko sihiri acikinsa amma kasancewar aiki dashi be saba shari’a ba shiyasa a wannan makala din nakeda darasi akansa,

abu na farko da mace zata fara sani kafin aiki da wannan turaren dole saiya zama mijinta yanason kamshin turare wannan shine ka,ida ta farko idan kuma bayaso tofa saiki duba wanda yafiso idan kuma shi kwata kwata bayaso tofa wannan hadin ba naki bane don maimakon kisamu muhibba da kimah wajensa saiya zama kin samu akasin haka.

abu na biyu da yakeda muhimmanci shine kayan hadin wanda sunada yawa don nima nasan sunkai kala 15 wanda kowanne daga ciki zaiyi idan aka hada,

gadalin mata idon zakara
farin goro sauyar jinin mutum
bita zaizai kafi malam
mallaka dan kadafi
hana kishiya biyarana
manta uwa farar mace(marmartau)
farin gamo furen taba
turare

 

kalubalen hada wannan maganin shine samun asalin gadalin don shine ganeshi yakeda wahala amma ana ganinsa dan karami wanda cikinsa keda yauki yana kaikayi wani kuma yana zubarda ruwa me kamshi.

abunda zai baki mamaki a wannan turaren shine yayinda kika hado kayansa misali dagali da farin goro da idon zakara da manta uwa da mallaka idan kika cakuda akwalba daya zakiji kamshin ya canja,

idan aka hada wannan turaren ana shafawa ne lokacinda mace tayi wanka kamar da yamma ko kuma lokacin kwanciya kuma a goshi a keshafawa,

akwai kuma bayani dayakeda muhimmanci wajen aiki dashi shine bayan mijinki yanason turare ya zama yanada lokacinki komai kankanta bawai mijinki baya zaune a gari amma kiyita shafa turare wannan bashida amfani kiyi aiki dashi,

MEYE TABBAS DIN
MALLAKA DA GAMA DIDI

Shidai wannan halitta koda yake yanada
yawan sunaye amma amfi saninsa da
gamadidi anan kasar hausa,
kwarone wanda yakeda suffa irinta
kyankyaso saidai shi kara mine sosai sannan
kuma anfi samunsa ayankin arewa masu
gabas na wannan kasar,
yanada wata baiwa wanda babu wata halitta
da me wannan baiwar,

 

su biyu suke rayuwa
mace da namiji babu inda zakaga daya
bakaga dayaba kullum a manne suke da juna
kuma ta jela da zaran kaga jikinsu ya rabu
tofa daya ya mutu nan take dayanma zai
mutu daya baya rayuwa.

 

 

 

 

 

to akwai abu uku wanda yakeda
muhimmanci mata su sani kafin fara aiki da
kowanne magani
1 abu na farko yanada kyau kifara duba
magnin addininki ya baki damar kiyi?

2 abu na biyu ki duba kiga zai iya cutar dake
ko kuma bashi da matsala?

 

3 saina uku kuma ingancinsa

kowanne magani idan ya tsallake wadannan
matakan hankalinki kwance zakiyi kuma
kiga biyan bukata.

wannan halitta gama didi a kwai wani
mallaka da aka samu ajikinsa wanda nidai
banfi shekara biyu da sanin saba yanda ake
masa kuwa shine da an samesa sai arabasu
nan take zasu mutu daga nan sai akaisu
inuwa su bushe sai ayi garinsu akwaba da
zuma da furen taba danye wanda aka
kirbashi ya bushe a inuwa tofa sai ayi matsi
dashi yanda kuwa ake matsin sama sama
ake shafawa,

 

 

 

 

wannan mace zatayi idan mijinta baya
saduwa da ita, shima na miji zai shafa
agabansa idan mace bata yarda dashi.

wannan yana kawo jaraba sosai wanda zaisa
miji ya dena jin dadin kowacce mace sai
wannan wanda ta shafa agabanta harma na
miji yakan daina saduwa da kowacce mace
sai ita, to amma akwai abu biyu da nagano ajikinsa
shiyasa banma taba ko jarrabashi ba
ballanata nayi darasi akanshi,

1 akwai kaikayin gaba don wannan halitta
zata iya jawo kaikayin gaba ko kuma ta
dawoda infection koda ya tafi don jikinta
ruwane ba kashi bane kamar fara ruwan
kuma yanada dan kaikayi da wari,

2 na biyu kuma ana shiga hakkin wasu
matan dan kowanne abu da mace zatayi
matukar zaisa ya dena saduwa da kowa sai
ita an shiga hakkin wata idan yanada wata
matar ya zama sabon allah.

wallahu a’alamu.

YANDA MATA KE HADA KWALLI

hazikin tozali lamba daya a kwallin gargajiya wanda shine mashahurin daya shahara akasar hausa wajen gyarawa mace idonta musamman mata aure wanda babu abinda ake bukata mace tayi da wannan kwalli sai sakawa lokacinda tayi kwalliya,

shine kwallinda sakashi ke gyarawa mace idonta yayi haske daga nesa kullum tana kara zama amarya wajen mijinta, hallau kallonta ya zama masa abun farin ciki,

domin hada wannan kwallin saikin samu asalin kwalli da abunda ake sashi wato kura tandu ko (mazubi) wanda anan zaki zuba bayan kin hada,

akwai wata kaya me kamada kayar bushiya sunanta bakin suda fara ce sosai za ahadata da marmartau wato (farar mace) da sauyar jinin mutum da kwallin ayi garinsu sannan ya zama itacen yin kwallin sauyar birana ce wannan shine kwallin kiyishi don farin cikin mai gida.
sannan maganin ya zama kadan kwallin anaso yafi yawa.

 

 

GUMBAR KANKANA

hada tsumin kankana sauki gareshi domin koda markadata kikayi da dabino da kwakwa kika zuba madara ta ruwa da ruwan kwakwa ya wadatar kina iya wuni kinasha,

yana aiki shima domin zaki gamsarda mijinki, to amma yin gumbar kankana tana bukatar nutsuwa sosai kafin kiyi nasarar hadata yanda zata bawa mace ni,ima da sha’awa yanda yakamata,

 

 

 

 

Da akwai wata gumbar kankana wanda matan garin maradi dake niger suka fara kawota kafin bin cikenmu ya taddota inda muka sauya maka suffa daga bisani ta zama gumbar kankana wanda mata keshanta da madara ta ruwa peak domin samun ni,ima kuma tana kawowa mace sha’awa ku jarrabata koda sau daya.

anaso kisamu asalin kankana ko kuma me yashi wanda sune kankana da aka sani masu kara ni,ima kafin kisamu kankanar saikin soya ridi sama sama saiki hada da kanunfari da aya itama wanda aka soya sai ahada waje daya ayi garinsu,

to tayaya kankana zata zama gari?
idana kika yanyan kata saiki hada da wannan garin saiki kirba amma kankanar ki lura kada tayi yawa don zai zama ruwa gaba daya idan kika kirba saiki shanyasu arana har sai sun bushe saiki dawo dasu turmi kiyita dakawa anan zai zama gumbar.

SIRRIN TSUGUNO

Abu uku kada kiyi wasa dasu wajen tsuguno na farko miski na biyu man damo na uku totuwar rake,

 

 

 

ki samu miski na ruwa sai man damo original sai totuwar rake me zaki wanda dama sai kinsha raken ki busar da ita saiki samu farar bi rana ganyen ki busar dashi wadannan ake hadawa shi kuma man damo kadan ake zubawa sai mace tayi turaren tsuguno dashi sa’a daya kafin saduwa,
dan danon jima,i gamsarwa cikin nishadi kedai kawai jarraba.

KINASON SANI AKAN GYARAN NONO KO HIP (KUGU)?

Yawan matsaloli da mata ke fuskanta a sanadin rashin nono yasa na bincika wadansu hanyoyi tareda shawarwari.

 

 

 

 

 

mace tana fara fitar da nono daidai lokacin fara jinin al’ada yayinda allah ya banbanta halittar sa jinsi daban daban ta yanda jinsin al’ummar africa bakaken fata ya banbanta dana wasu kasashen don haka abu na farko daya kamata jama’a su fara sani akwai banbanci tsakanin nonon baturiya dana bakar fata dan haka maganin gyaransu da namu ya banbanta dan haka idan gyara nono kikeso girmansu ko tsayuwarsu tareda kyawunsu ba tareda yayi miki illah ba dole saidai kiyi amfanida na gargajiya.

akwai banbanci tsakanin tsayar da nono da girmansa to amma saidai abu daya baya samuwa dole sai an hada da wani ma’ana bazaiyu nono ya tsaya kadai ba har sai girmansa ya karu haka zalika bazaiyu ace nono ya girma ace bai tsayaba kuma wadanda sukafi matsala a gyara nono sune wadanda ya kwanta shiyasa duk maganinda zai kara girman nono kuma ya tsayar dashi zai zama na musamman sannan za’a dauki lokaci ana shansa sabanin wanda kawai cikowa take bukata.

nonon mace yanada suffa kala kala nayi kokarin binciko bayanai akayi dareda bin diddigin magunguna daya dace masu suffar nonon suyi kai harma wanda zaiyi da kowanne

?na farko AKwai nono mai (mango Shape) wato Shine wanda bakinsa (nipples) yaKe Kallon sama irin wannan nonon baya zubewa da wuri irn wannan batashan wahalar gyara dan haka
zaki iya wannan yanda zakiyi ki samu ayaba (plantain) ki yanyankata ta bushe sannan ki daka garin to saiki samu aya ki wanketa kisaka gyada kisaka amarkada miki
saiki tace ruwan kina diban wannan garin plantain din kina zuba madara peak kinasha kamar sau biyu arana kafin sati daya zakiga canji sosai nononki zasu tashi su ciko.

? sai kuma me bi masa wato (Pointed breast) shine zakuga yana kallon gaba (straight) gasKiya irin wannan nonon yana saurin faduwa domin riga kafin faduwarsa arinka kunun alkama wato idan aka nika alkamar sai ayi kununta asaka nono da zuma anasha, idan kuma zubewa yayi.

 

zaki hada farar shinkafa da alkama da garin habatussauda da aya da gyada ki nikasu suyi laushi ki tankade sai ki ajiye wannan garin kina hadashi da nono kinasha kullum wannan shine hadinda zaisa nono ya ciko ya kara girma kuma ko budurwa zata iyayi..

?Akwai nono mai Kallon gefe (left and right) zakuga aKwai nisa sosai a tsaKanin nonuwa biyun zai iya kallon hagu ko dama wadannan sune sukafi matsala domin sa’ar mace wannan nono su zama kanana amma da zaran sun dan fara tashi to tabbas ta rasa nono domin gyaransu su dawo dole sai kinyi amfanida maganin nonon na musamman wato gari da akesha na kwana 30 ko 25 wannan kowanne irin nono mace take dashi zai temaka mata

Domin anyi amfanida ingantattun magunguna kuma na gargajiya, gadalin nono da nonon kurciya da ‘ya’yan baure kumbura fage zakiyi garinsu
idan suka bushe a inuwa saiki samu hulba me kyau ki hada sai kuma kisamu aya da alkama da ridi da gyada da fafar shinkafa da waken suya

dukkansu ki gyarasu kamar gyada da ridi da waken suya saiki soya su sai kiyi garinsu adakasu ko nikawa saiki samu ruwan zafi kamar rabin kofi ki zuba garin cokali daya ki gauraya ki zuba zuma ko zugar da nono ko madara ta ruwa peak kinasha kullum kafin wani lokaci zasu tashi koda kanana ne
sai kuma abinda ya shafi gyaran hip wato yanda mace zata ciko da kugunta yayi kyau bayanta ya ciko tayanda kallo daya mijinta zai mata ta dauke hankalinsa,

Masara da jar dawa zaki fara jikawa su dade kamar sa´┐Żo,I 24 saiki tsame ki shanya sannan kisamu macca da kumbura fage da sassaken kuka da ganyen argun wadannan sune zaki busar dasu kiyi garinsu ki hada da wannan garin masara da dawa saiki soya waken soya da gyada sama sama shkenan saiki hadasu waje daya kiyi garinsu,

Bayan wannan garin ya kamala sai kuma bayani akan yanda zakisha, anaso kisha da nono me kyau idan besamuba kuma madara peak ta ruwa kullum zaki zuba garin cokali daya babba bayan kinci abinci, idan da hali kina damashi kamar kunu wato idan kika zuba garin acikin ruwan zafi saiki gauraya ki zuba madarar ko nono din saiki zuba zuma ki gauraya kisha kullum kisha sau daya akalla kisha na kwana 15 idan beyiba saikisha na wata daya.

Abu biyu sunada matukar muhimmanci ajikin dan adam wajen sha’awa wato zuciya da kwakwalwa wadannan sune farkon kuma ginshikin duk wata sha’awa ajikin mutum,
kowacce akwai halitta na sha’awa tattare da ita kuma kowacce akwai matakin sha’awarta wanda ake cewa matakin karshe itace harija wanda itace karshe wajen sha’awa.
hallau koda yake babu wani sahihin bincike daya tabbatar da yanayinta amma masu hasashe suna iya bayyana yanda surarta yake

zuciya itace mafi tasiri wajen sha’awa kafin ta aikewa kwakwalwa wanda ita kuma kwakwalwa itace ke sarrafa jijiyoyin sha’awa ajikin mace wanda hakan ke kashe mata jiki wannan kuma yana faruwa ne sakamakon taruwan maniyi da yakeyi izuwa kasan maman ta wanda idan har be fitoba zai iya haddasa mata ciwon mara a wannan lokacin ko kuma lokacin al’ada, wannan shine ya bayyana a ilimin kimiyya.
sannan mafi yawa mace tana fara jin sha’awar namiji lokacinda ta fara al’ada ko makamancin haka,

MEKE KASHEWA MACE SHA’AWA?
abu uku sune kan gaba wato ciwon sanyi da matsalar aljanu sai kuma istimna,i,

CIWON SANYI
Yana shiga jikin mace ya hana ni,imarta zuwa daga karshe ya dakatarda sha’awarta, bayaga haka ciwon zai hana miji yaji dadin mace yayinda gabanta zai bushe a koda yaushe irin wannan akwai aiki soaai wajen dagewa dashan maganin sanyi,

ALJANU
akwai Abinda ake cewa namijin dare Wanda yake aurar mace cikin mafarki zataga tana saduwa da namiji tanajin shaukin saduwar amma azahiri batajin dadin mijinta wannan yana kawo yawan fada tsakanin ma’aurata
domin kwata kwata mace bazataji dadin namiji ba wata ko sha’awar bataji to hakan ba karamar illah yake a zaman takewar aure ba.

ISTMNA,I
yawan wasa da gaba ko kuma madugo itama hanyace dake daukewa mace sha’awa shikuma mace tana iyajin sha’awa amma ba bangaren saduwa ba zatafi so ayi wasa da ita sama da saduwa da namiji wannan shima babbar matsalace da zata kawo sabani tsakanin miji da mata,

MEKE HANA MACE INZALI
Kamar yanda yazo a rubutuna na baya akwai banbanci tsakanin inzali na mace Dana namiji domin yanzu matsalarda wasu mata ke ciki
shine basajin lokacinda suke inzali kamar yanda namiji ke sani kuma bisa binciken masana Abu ukune kan gaba wajen faruwan wannan matsalar,

1 akwai infection Wanda yake hana mace sanin lokacinda take inzali domin maniyinta zai tsinke ya zama kamar ruwa zai rinka fitowa kadan kadan wata tanajin dadi lokacin fitarsa.
wata kuma kwata kwata babu abinda takeji na dadi amma mijinta zai iyajin dadin shima kafin ciwon yayi yawa saboda irin masu wannan matsalar koda maganin ni ima sukayi babu wani canji to a hankali sai shima mijin yadena jin dadinta kuma sauda dama abinda ke kawo wannan matsalar shine wasa da farji lokacin mace tana budurwa istim Na.i (mastrabution),
A irin wannan halin abinda zakiyi shine kirinka tsarkida ruwan dumi da magarya aciki kuma kisamu garin hulba da gishiri kadan ki zuba a ruwan dumi kina zama
shima lalle zaki iya dafa ganyen danyensa kina zuba Zuma kinasha
sannan me irin wannan matsalar zata iya amfanida miski na matsi wato miskul dahara tana matsi dashi,

2 na biyu akwai rashin gamsuwa da miji shima yana hana mace inzali domin wasu matan ana dadewa kafin suyi rilessing to idan ya zama mijin bashida juriyar dadewa mace sai taji kamar zaizo amma ba dama ko kuma kankantar gaban namjji baya shiga gaban mace yanda ya kamata to babu damar tayi inzali to wannan matsalar daga wajen mijinne suna iya wasanni sosai har saita kusa yin inzalin kafin afara saduwa

3 akwai rashin sha awa mace Wanda batajin sha awar namiji komai dadewa ana saduwa da ita bazatayi inzaliba irin wannan gaskiya ta dage dashan magungunan kara sha awa tareda ni ima,

to kodai yaya nene mace wanda bata inzali bazata taba jin dadin saduwaba koda kuwa tanajin sha’awa,

 

MAGUGUNAN KARAWA MACE SHA’AWA
garin albanunaj
garin habbatussauda
ganyen dan fadama

wadannan ana hadasu waje daya ana hayakin jiki don kore namijin dare ajikin mace sannan akiyaye lokacin kwanciya arinka addu’a abinda yashafi addu o,i kuma sai atuntubi malaman rukiya,

maganin kara sha’awa kina bukatar kayayyaki kamar haka
1/argaf
2/sassaken baure
3/ruma fada
4/ganyen zogale
5/ganyen idon zakara
wadannan garinsu zakiyi kinasha da nono me kyau,

Bayan haka kina bukatar ingantaccen daka me kyau Wanda ake hadawa da
1/asuwakin mata
2/gyadar mata
3/dabino
5/mazar kwaila
6/minanas
7/zuma
Zaki iya saka kayan kamshi aciki to Wannan dakasu zakiyi suyi laushi sosai ki busar dashi ya zama gari shikuma da shayi da madara zakinasha

domin hada gumbar sha’awa kina bukatar wadannan

1/ridi
2/gyada
3/aya
4/dabino
5/kwakawa
6/mazarkwaila
7/asuwakin mata

To bayan kin soya gyada da ridi sama sama saiki hadosu waje daya kiyita dakawa har saiya hade ya zama gumba ita Kuma zakisha da nono ko madara,

wannan kuma kisamu aya danya sai dabino ki cire kwallon da danyen zogale da kwakwa da kankana da cukuw sai mazar kwaila ki markadasu
sannan ki tace ruwan sannan kidauko nonon rakumi ki zuba ki gauraya kisha
wannan shine ruwan jaraba.

Alhamdu lillah nan ne karshen littafin fatan alheri ga masoya musamman masu fatan alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published.