Mijin Kwaila Hausa Novel Complete

*MIJIN ‘KWAILA* ����♀
“-chapter one-”
Ahankali yake tafiya da motar sakamakon yanda ya iske saitin bakin makarantar yaran yacika yakuma batse da dandazon yaran da’aka riga aka taso daga makaranta,ya d’anja gajeren tsoki lokaci guda yana kallon tsadadden agogon dake hannunshi ya taka burki kamar yanda sauran masu ababen hawa y’an uwanshi sukaja nasu burkin sakamakon dakatar dasu da yellow piper yayi.
Ranshi ‘kwarai yana a dagulene koda yake ba abin mamaki bane ganin fuskar tashi babu walwala kusan dukkan na tare dashi sunsan dahakan duk da yake mutum mayen barkwanci lokaci kankane yakoma kamar wani horror abin tsoro ga kowa saboda yanda yakecin magani kullum idanunshi suna manne da farin gilashi saboda yanda ya matsama idanun nashi da kuka wanda har yazuwa yau d’innan yakasa dena kukan,
Baya zato ko tunanin zaidena kukan rasa jigon rayuwarshi dayayi a cikin watanni shidda dasuka gabata.
Yazuwa wannan lokacin yazama abin tausayi ga kowa to ai dolene dukkan mai imani ya tausayama d’an sangirin saurayin maicike fal da ‘kuruciya akan fuskarshi da dukkan sassa na jikinshi,
Rashi yayi babba rashin dayake ganin bazai ta’ba samun tamka ko madadin taba.ZAHRA ADAM ISHAQ cikakkiyar budurwar dasuka sha’ku tun yarinta shine yaci kashinta da fitsarinta ya goyata a gadon bayanshi yamata soyayya dabai ta’ba yima wani mahalu’ki a duniya irintaba rana guda ciwon mara yayi fatali da rayuwar zahara yazuwa barzahu,
Adai dai lokacin da yarage saura kwana uku rak!
Daurin aurensu,
Yashiga rud’u mara misaltuwa dayawa yawa anzata ya haukace,amma dayake allah gafurune kuma rahimu saiya tashi kafad’unshi yakuma saka mashi dangana duk da ikirarinshi na dena kallon kowacce y’a mace da gashi tunda yarasa zahra.
Y’amma dayawa sunsha kawo kansu gareshi wasu iyayensu zasu kawo talla wasu text zasumai amma haryau baiga mai maye gurbin zahra ba,
Yashafi gefen fuskarshi daya tuna aneesa wacce tanace mashi kamar chewing gum saboda so,
D’iyar ‘kawar mummy ce,
Ya girgiza kai batare daya ankare ba.
Kamar ance dashi ya kalli gefen damarshi ya hangota cikin dandazon yara sa’anninta kamar sauran yara akwai uniform bulu da farin hijabi jikinta sai y’ar jakar makaranta saqale a hammatarta,
Wata mummunar fad’uwar gaba ta riskeshi lokaci guda ya cire gilashin fuskarshi yasake murza idanu gabanshi na bugun goma goma,
Dai dai lokacin data tsallako gefen dayake yara sun ragu sosai,
Tana tafe tana tsokanr yaran dake gefe da ita.
Caraf idanunta suka sar’ke cikin na ishaq wanda tuni anbasu hannu amma tsabar kallonta baimasan anbasu hannunba.
Tarin ababen hawa dasuke bayanshi suka addabeshi da horn hakan yasakashi waigawa da sauri, lokacin wani har yayi mashi overtaken yana fad’in “amma kai wawane,idan kallon mata kazoyi toka bamu hanya mu wucewa zamuyi ”
Ishaq bai tankaba yagyara parking mota zuciyarshi kamar zata tsage saboda tashin hankali.
Ganin ita yaketa kallo yasata cewa da ‘kawayenta”ummilolo kukalli d’an ‘kauye yanata kallona kutsaya kuga yanda zanmashi gobe bazai sake kallonaba,ummana tace mai kallon mutane mayene.”
Saita lalla’ba kamar zata wuceshi sai dai tana zuwa saitinshi inda ya sauke glassa d’in motar ta tofa yawu, cikin sa’a kuwa ya sauka akan fuskarshi.
Sauran students y’an uwanta suka saki baki suna kallonta duk sun kasa tafiya,
Yayinda su ummilolo suka hau tsalke suna kyalkyala dariya.
Itama dariyar take don asukwane tabar wajen da gudu,
Tana zuwa tami’kama su ummilolo hannu suka tafa, kafin tacigaba dayima ishaq gwalo tanasaka hannayenta saitin kunnuwanta almar eho…ya numshe idanu yana tunano zahranshi a irin wannan lokacin tayi makamancin hakan gareshi, lallai batada maraba da zahra, hannu yasaka ya lakace miyon,ya sumbata zahra daban take, komai nata so yakeyi.
Bai ankareba ya hango zahra can kusa dawani matashi irin masu tallar agwaluma d’innan,
Ta mararaice fuska tace dame agwaluma “kai don Allah bani d’aya?
Me agwaluma cikin mamaki ya kalleta yace”kibada kud’i sai abaki agwaluma yammata.”
Sudai su ummilolo sun ‘kunshe baki sunason dariya suna tsoron bala’in zahra don sunsan akwai daru.
Ta murgud’a wa mai agwaluma baki,”nace kabani d’aya kawai.”
Me agwaluma ya fusata yace”tunda ubanki yabani jari meze hana inbaki d’aya.”
Tazaro idanu”la la la..kazagi ubana?
Me agwaluma yayi tsaki,
Aikafin ya ankare tuni ta duma wawa uku ta sura ta fece aguje da fad’in “pdp!!!”
Sauran yara dasuke tsaye sukace “wawaaaa!!!”
Tuni sun duma hannaye suna dumbuzar agwaluma,
Ganin yara sun kwashe agwaluma yasaka me agwaluma binta aguje bayan ya jefar da tiren dayazama empty.
Shegen gudu gareta ko barewa ta shafa mata lafiya,
Sauran yara sukad’au ihu “sai zahra !!sai zahra!!!!
Gaban ishaq dake kallon duk abinda yafaru yabuga da karfi.
Ya maimaita sunan ZAHRA???
��������
Aunty y’ar charas��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN KWAILA* ����♀
chapter 2.
Gudu take kamar wacce zata tashi sama,
Ahaka tasha kwanar layinsu da yawa y’an unguwar sunsan halinta don haka suna ganinta suka fara dariya,
Wasu nafad’in “mai hali baya fasa halinsa zahra.”
Saida ta kutsa d’an sirdad’en lungunsu kana ta dakata da gudun tana luliya agwalumar abango dafad’in”luliya-luliya danya awakin baba da dad’i.”
Sai dai batayi auneba ta hango mai agwaluma a three thirty ya kutso lungun,
Hakan yasakata idasa fad’awa gidan kamar wacce aka cilla da kibiya .
Umma dake tsaye bakin band’aki da buta a hannu, zahra batamasan ta angije ummanba,ta danna d’akinta gami da gar’kama sakata.
Umma tabita da idanu,
Yayinda anty hafsat dake tsaye gefe tabita da tambayar lafiya zah….
Bata ‘karasaba sukaga me agwaluma ya fad’o gidan,
Baikobi takansuba yarufama zahra baya zuwa d’akin datake ciki.
Anty hafsa cikin mamaki ta tareshi dafad’in”lafiya malam bakada hankali zaka fad’o cikin gidan matan aure bako sallama.?”
Yayimata kallon banza ranshi yana zafi kafin yace”aiba sallama ta kawoniba,wlh sai anbiyani kud’ina kokuma in karya yarinyarcen,
Yanuna d’akin da zahra take ciki.
Yayinda take lekowa ta window tana mashi gwalo,
Yakuma ‘kufula,
Anty hafsat itama hararshi takeyi tana nuna mashi kofa”get out”
Ya kalleta da jan idanunshi”bansan wannan yaren ba.”
Anty hafsa itama akwai masifa don haka tamike dafad’a,
“nizakama rashin kunya,wato kashigo gari ka waye haryanzu jahilcin kauye bai sakekaba,idan laifi akamaka kai ataka basirar da wannan cin maganin dakakeyi zaka kwatarma kanka y’ancine,?
Tajuya a fusace ganin yanda yake harararta,yana mata qunquni.
“bari inkira police idan yaso idan kaje bayan kanta zakayi bayanin abinda yashigo dakai gidan matan aure.”
Umma tariketa tana fad’in”me yayi zafi hafsat,bansanki da hakaba,
Kifara tambayar abinda zahra tayimashi don bana raba d’aya biyu itace ta tsokanoshi..”
Umma tasake kwantar da murya tana tambayar me agwaluma abinda yafaru,
Idanunshi taf da hawaye, yake bama umma ba’asin yanda komai ya farun.
Umma tagyad’a kai tana fad’in”nasan za’a rina ai,
Nidai zahra bazan maki bakiba sai dai ince allah ya shiryeki,abinda kikeyi amma nagaji nagaji da halinki bari babanki yadawo a tattara amaidake can kauye inyaso kici gaba da halinki a can am.a nikam nagaji.”
Tajuya afusace tanufi d’akin da zahra tuni ta danna mashi sakata.
Anty hafsa tazuge jakarta tafiddo da dubu d’aya tamikama mai agwalumar tana hararashi dafad’in”next time kasan yanda zakayi magana da nasama dakai “.
Shima hararta yayi,
Sai dai bai tankaba.
Anty hafsa tadafa kafad’ar umma wadda tazauna zugwui da damuwar da zahra ke sakata akoda yaushe,
Tace”umma pls banason ganin damuwarnan taki,kina sane da lalular dakike fama da ita,
Umma kamata yayi kinama zahra addu’a bawai yawan damuwaba.”
Umma tasauke numfashi”toyaya zanyi kinasaje da halin yarinyar nan,khatta da sunan da yaran unguwa suke kiranta dashi wai *zahra’u mala’ikar yara inkin mutu ba ruwan Allah walakiri ya jibgi kayanshi*.”
Umma taci gaba”sam idan kinga nasamu naji sa’ida to kuwa zahra tatafi makaranta toyanzu hatta da makarantar abin yaci tura iya shege kullum sabon salo take fiddowa,jiya Monday tafara zuwa makaranta js 1,take amma wai baifi wata biyu da shigartaba yara bakwai ta fasama kai da dutse,dacirema wata yarinya ha’kori,
Principal ta bugeta shine tatara yara bayan antashi makaranta sukayima motar principal ature,da ‘kasa har suka fasamata glass din mota.shine fa akazo hargida dakorarta sukayi dakyar babanku yasamu ya mayar da ita suka amsheta ,amna saida yabiya kudin duka asarar dasukayimata kinga ayau har ta dakko wata maganar.
[9/20, 1:16 PM] mum meenat: Anty hafsa ta sauke ajiyar zuciya,
“nidai umma sainake ganin kamar lamarin zahra fa akwai sa hannu wannan abin datakeyi bafa normal abu bane,gaskiya is abnormal ne umma yakamata mutashi tsaye,yarinya saikace ana kad’ata da ruwan hanji sam zahra bata d’auko halayyarmuba.”
Umma tace “kema kya fad’a ai,nida ace ba’a gida na haifi zahraba tozan iya rantsewa da Allah anyiman musayar tane batawa bace ba.gata sam bata d’auko kamanni dakuba,hakanan bata dauko halayyarkuba.
Ku shidda na gaifa allah ya dauki ran maza biyun dasuke cikinku sai kumata guda hud’u da allah yabarmun,duk na aurar daku ku ukku akan matakin karatun zamani dana addini dai dai gwargwado bamu tauyekuba,gakunan duka cikin rufin asiri amma zahra sam tazamo zakka acikinku,itabaga karatuba baga natsuwar ba,itakenan kamar tunkiya duk inda ta gifta sai ance kayya.”
Umma ta’kare maganarta kamar zata fashe da kuka.
Da’kyar anty hafsa ta shawo kan umma,ta lalla’bi zahra ta bud’e dakin tanufi kitchen tadauko abincinta wanda tuni ya sandare saboda hucewa,
Tazauna kamar wata saliha tanacin abincin anty hafsa namata fad’a akan rashin jinta.
Itadai bata tankaba,
Har lokacin sallar la’asar yayi tatashi tayi wanka akaja wata kwasheshiyar jagira wadda tasamu matsugunni a gefen kunne,
Tad’auko janbaki jajawur ta dafsa bayan ta zagaye bakin nata da tarin ba’kin kwalli.
Tajuya da fuska tanama madubi murmushi tana tsuke d’an matsakaicin bakinta aganinta ba nabiyunta wajen kyau.
Duk da tana cikin ‘kunci baihanata ganin kyawon nata ba
Sai dai aranta kullum tanajin haushin meyasa anty hafsa da anty salma kai harma da anty lubna duka suke farare tas,
Amma ita saitayo duhun fata,
Taja tsoki ita d’aya dafad’in”nadaisan dama ummanmu ba sona takeyiba shiyasa ta haifoni ba’ka.
Tasaka uniform na islamiyya check blue dasuka d’au guga sukayi luf dasu,
Tafito har lokacin umma bata dena fushi da itaba,
Takalli umman cikin kukawa tace”umma natafi,”
Umma tace”adawo lafiya sauran yauma akawomun ‘kararki kinyi fad’a dawani mutum zaki bani labari.”
Ta turo baki gaba,batare da tatankaba,
Umma tayi tsaki dafadin”shashasha kawai shekaru shabiyu amma fitinarki tafi ta masu shekaru ashirin.”
Itadai gaba tayi abinta kamar yanda tasaba,
Tafito lungunsu tana gunaguni,charaf idanunta suka sauka akan na ishaq wanda ya sar’ke hannayenshi a kan kirjinshi yakafe kofar lungun nasu da idanu,
Duk da rashin tsoro irinna zahra saida gabanta yafad’i,amma dayake tsiwa gareta saita murgud’a mashi baki dafad’in”kurwa
ta kur namana d’aci,me d’a yaci d’anshi mara d’a yaci ‘ko’kon tsuliyarshi.”
Ishaq duk da baya jiyo abinda take fad’i shidai komai takecewa ahakan burgeshi tayi,
Yanason d’an murgudennan nata,
Ya numshe idanu daya tuno da zahra gaf da bikinsu yakafeta da idanu tayimashi murgud’e dafad’in “kallonfa,
Alokacin murmushi yasaki yanace da ita”nanda wata biyu saina tsotse bakin murgud’enanna naki.”
Alokacin dariya tasaki dacewa”kai yaya ishaq,bakajin kunyata nifa kanwarkace”.
Ya runtse idanu,kamar zai fashe da kuka afili yafurta “i really luv yhu zahra,inason koda mace mai sunankine bare kuma mai kammani dake.”
Post everyday nsha Allah
September 20, 2017 at 7:31pm ·
��������
by
Anty yar charas ����
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN ‘KWAILA*����♀
*to you maman Aliyu this page is for you*��
Chapter 3.
‘karfe hudu na yamma dai dai lokacin da matashin ya cinna hancin motar tashi yazuwa cikin tanqamemen get d’in gidan,tare da matsa horn wanda yasaka megadin tashi da sassarfa yaxuwa bud’e katon get din.
Kamar almara ko mafarki haka baba yusha’u yake kallon fuskar ubangidan nashi dake cike da zallah nishad’i,
Yasake murza idanuwa aranshi yana ayyana’shin anma oga kyautar d’an mutum ne da kayanshi kome,?
Ganin yakasa aiwatar da aikinshi yasaka ishaq sake matsa horn da ‘karfin gaske wanda yasaka baba yusha’u tale get din yana washe hakora dafad’in”barka ubangidana barka dazuwa isyaku na zahra baban zahra kaga angon zahra’u…
Isha’q ya numshe sexy idanunshi lokaci guda yanajin wani yanayi yana tsalga ainahin ‘kasan zuciyarshi,
Ya’isada shigoda hancin motar lokacin daya saka hannu a aljihun jeans dinshi ya dumbuzo kud’in da bazai tantance adadinsuba ya dam’kasu ga baba yusha’u wanda tuni ya warcesu yana sake jinjinama isha’q d’in.
Yafito daga motar bayan ajiyeta a mahalinta,yana cilla key’s din motarshi sama yana cafewa a tattare dashi akwai zallah nishad’in daya kwashe watanni shidda gam batare dayayi makamancin hakan ba.
Yakutsa kai acikin ‘katon falon dayakai ma’kura wajen tsaruwa,dagani babu tambaya yasamu tagomashin dukiyarda tsayawa ‘kididdigeta ‘bata likacine.
Da sallama yashiga cikin falon idanunshi suka sauka akan ‘katon kyakyawan hoton zahra wanda tayishi alokacin datake saukowa daga cikin jirgi,ajikinta akwai ba’kar suit saitayi roling white gyale akan wuyanta harzuwa kanta.
Fuskarta akwai full make’up don ita gwanar kwalliyace abinda yake karama isha’q kaunarta don yanason mace y’ar gayu.
Tasaki silent smile dake ‘kayata fuskarta mai matsakaicin kyau.
Duk da ganin doctor ruqayya (wato mahaifiyarshi)
Baihanashi ‘karasawa ga hotonba yasaka yatsanshi guda ya xagaye gefen kumatunta dake murmushin,lokaci guda idanunshi suka canja kala,
Yajuya kamar zaifashe da kuka,muddin zaidinga kallon hoton zahra bazai ta’ba kallon wata d’iya mace da gashiba,
Face zahra mai kamanni da zahransa.
Yadad’e tsaye jikin hoton yanason tabbatarma kanshi banbancin dake tsakanin waccen zahra ‘karamar dakuma real zahramshi,amma yakasa gane koda abu d’aya dazai iya tabbatar mashi cewa bafa zahranshi ce takoma ‘kan’kanuwaba.
Doctor ruqayya tatako a hankali zuwa kusa da d’an nata tadafa bayanshi cikin sanyin jiki da’alamar tausayawa kamar yanda tasaba.
Sa’banin da ayau fuskarshi fayau take babu tarin damuwarnan dake ‘boye kyawon fuskar tashi.
Kama hannayenta yayi duka guda biyun idanunshi cikinnata duk da nata idanun suna manne da siririn farin glass din (medical).
Saida ya ‘kawata fuskarshi da murmushi sannan yace”mummyna nasamu zahra..zahra tadawo gareni mummy awannan karon bazatayi nesa daniba,d’iyarki tadawo gareki mum….!
da hannu ta dakatar dashi”isha’q wai sai yaushene zakasan wanda yamutu baya dawowane,ayaushene zakasan cewar allah daya d’auki zahra yafimu ‘kaunarta.saiyaushene zaka dena takura tunaninka da lafiyarka akan wadda babu ita a doron duniyane?
Zahra ta mutu, a gaban idanuna aka wanke gawar zahra.zahra d’iyar ‘kanwatace nice na reneta tundaga ranar da mahaifiyarta ta haifeta batakoga fuskartaba takwanta tamutu,naso zahra na tausayama zahra nasani bayagani kaine mutum na biyu dayasha d’awainiya da zahra amma kasani zahra ba rayayya baceba.
Mutayata da addu’ar gafara dabeman dacewa don zahra mutumce guda harda ‘kari
Ama yamuka iya’allah yafimu ‘kaunar zahra ya amsheta a daidai lokacin damukafi bu’katarta,saimu bita da add’ua kaikuma kasaka dangana wa ranka ka rungumi ‘kaddara matsayinka na musulmi nagari.”
Bai katsetaba har saida ya tabbatar da takai aya,sannan yaaja hannayenta yaxuwa d’aya daga cikin kujerun falon yazauna yana fuskantarta,bayan yagama saita dukkan natsuwarshi gareta don ta yarda dashi takuma gane baizo da wasaba a wannan karon.”mum wlh kiyarda dazancena mum,naga zahra ganin idanuna,zahra dai mum tana cikin students mum, a tattare da ita akwai yarinta nasani bawai ainahin zahrata baceba.amma inada tabbacin wannan itace zahran da zahrana take gayamun akoda yaushe,itace wacce zahra kefad’amun cewar _isha’q zaka samu zahra madadina koda bayan raina,zakasamu xahran da zata d’auke maka kewata.naro’keka da kobayan babu raina kajirayi xahra,kasota kamar yanda kake sona koma fiye da hakan._ _inamai tabbatarmaka itace alkairi a gareka._
Yaci gaba dafad’in”mum dani dake daduk wani ahali na gidannan yasan dahakan,mum kinatsu kituna maganganun zahra don allah kada kice wai bana cikin hayyacina.”
Doctor ru’kayya tami’ke cike da tsantsar tashin hankali,tana zagaye katon falon hannunta goye a bayanta akan fuskarta akwai zallah damuwa dakuma rud’ani.
Sai dai kuma batasan tayaya zata’iya ‘karyata isha’q a ‘irina wannan lokacin dayazo mata da magana sahihiyaba.
A dukkan nazarinta dakuma hasashe irinnata tanada tabbacin isha’q yana cikin natsuwarshi ne.
Tasauke numfashi,itakam a dukkan tarihi ko’a mafarki kai a film’s ko fili bata ta’ba ganin soyayya zahirinta irinta isha’q da zahraba,
Idan zahra tayi ciwo isha’q ko baya ‘kasar shima saiyace bayada lafiya,
Kuma dsame inda zahra tafad’a yana mata ciwo.
Kai tasha jaraba soyayyar tasu tana ganin ko plane ne suka had’a mata amma inaaa,saitaga zahirin ‘kaunane kawai dakuma had’uwar jini.
Sam bazata iya wancakali da bu’katar isha’q a wannan lokacin dayake neman taimako daga garetaba.
Tataka a sannu ta’isa gareshi tadafa kafad’arshi”bazan kiraka da wanda baya cikin hayyacinshi ba isha’q,nasani soyayya ba ‘karya bace ba.
Koma dai menene kaci gaba da bibiyar yarinyar,nikuma zansamu lokaci kakaini har gidansu inganta da idanuwa don tabbatar da gaskiyar zancenka,kafinnan kasamama zuciyarka salama.zahra adam ta isha’q ce.”
Yawani d’ane bayanta yana fad’in”tnx so much my luvly mother.”
Ta murmusa kawai,gami da kama hannayenshi yazuwa dining don bin abinci.
**************
Zugar su zahra da’aka taso makaranta,kai dagani babu tambaya kasan yau akwai masifa,itada ‘kawayenta duka zasu tseremata a shekaru amma tafisu yanayin girma,saboda jikinta irin ga’ba-ga’ba dinnan yake.
Su shidda reras duka suna fadanci wa zahra wadda keta ruwan bala’i ta d’aura kallabi saman hijabi taci d’ammara da dardumar dasuke xaunawa kanta a makaranta.
Bakinta har kumfa yake tana bamasu ummilolo labarin yanda zasuci uwar dije ali,wacce tasaka malam yayimata bulala biyu d’azu a aji.
Taraba yaran gida uku tace”ke ummilolo kune da hinda zaku shiga gidan saikuce a sammaku ruwa zakusha,daganan saikuce ina dije ‘kawarmu tazo ta rakamu tana zuwa mukuma zamu la’be zaure mu’kunshe mata baki,mujawota aje lungun bata kashi.
Wlh saita gane batada wayo.”
Sauran yaran sukace”eeeefaa haka za’ayi kuwa.”
Sukatafi d’uuuu kamar garken tumakai,
Kafin sukai gidansu dije yamma tayi sosai,
Can wani kango suka hango almajiri yana kashi,
Zahrace tafara hangoshi taja dabaya da sauri,tace da sauran ‘kawayennata”kutsaya kai ga al’majiri yana kashi,asamu d’an dutse a jefe takashin kashin.”
Suka la’be suna lekenshi,can ummilolo ta dau dutse sauko a qeyyar almajiri,suna fad’in amma ka’iya kanannad’a maciji.”
Kowando baigama sakawaba yabiyosu a guje,dayake ko barewa nan tagansu ta barsu almajiri ko ‘kurarsu baiganiba.
Basuyi burkiba saizauren su dije,
Saida suka huta sannan suka gyara kamar natsattsu,ummilolo ce tashiga da sallama,innar dije na alwalar mangarib ta’amsa da kallon rashin sani akan fuskarta.
Ummilolo ta gaisheta ta amsa,sanna tace”don allah a sammun ruwa zansha”.
Matar mai fara’a ta debomata ruwa a randa mai sanyi,ummilolo baki kawai ta d’ofana, ta mikamata kwanan dafadin “angode”
Matar tace”yauwa”.
Tana juya baya ummilolo tayimata gwalo,
Sannan tace”ina dije yau banganta a makarantaba.”
Matar tajuyo da fara’a tace”aiko na aiketa siyen manja aitadad’e da dawowa.kema naga kinmakara ko aikenki mamanki tayine.?”
Ummilolo tayimata gatsine dafad’in “uhm”.
Matar tace “to ayimaza akai lada gida ko.?”
Ummilolo tajuya dasauri,tafita donyima ogarsu zahra albishir amma saita hango zahra ta nad’e ‘kafar wando tacire hijab ta’ajiye gefe guda.
Tana turza ‘kafafu a’kasa
Sauran yaran sunja masu layi ‘atsakaninta da dije,
Dagudu ummilolo ta ‘karaso ta bugi ‘kirjin dije,sannan ta bugi na zahra tace”wanda yaji zafi ya rama.”
Aikafin kace miye,zahra ta kaima dije duka”ninaji zafi.”
Dije da tuni jikinta yad’au rawa tace”nidai bafad’a nazoyiba uwata ta aikeni,kuma inajin maganar uwata.”
Zahra ta fidda manyan idanunta dafad’in”lalalala towaye bejin maganar tasa uwar?”
Dije da ido yacika da hawaye tace”kigane”.
Zahra takaimata duka,
Nanfa fad’a yasar’ke,zahra ‘karfi kamar doki nan danan tadunga sunkuta dije da ‘kasa,
Yara sunamasu wa’kar “bamu rabawa sai dai mu’kara zugawa bugi cikin.”
Zahra ko harwani ‘kara za’kewa takeyi tana nusar ruwan cikin dije.
Isha’q daya dawo daga gidan abokinshi sadiq suna takowa a’kafa saboda hanyar batada kyau yayi parking motarshi acan farkon unguwar.
Yaci gaba dabama sadi’q labarin “abokina kai idan kaganta sam batada maraba da zahrata,”
Sadi’q yace”gaskiya abokina kakamu sosai wlh.”
Isha’q yasaki dariyar ‘kasaita dacewa”kawai kamanninta da zahrane yasaka naji wani mayen sonta,kai bayaga zahra banta’ba ‘kaunar wata d’iya mace kanartaba.”
Sadiq ya kwashe da dariya”gaskiya abokina koda banga girl dinnanba nasan mai zafice,don nasan bakayi da ‘kwaila.”
Isha’q ya murmusa…
Maganarshi ta ma’kale cik,
Sakamakon hango zahra dayayi da bataliyar yara suna dambe,zahra har ‘kara over acting takeyi.
Sadi’q dake duban yaran yace”kai yarinyarcan badai masifa ba,allah tsine ranar da zata fito takoma ga allah batare da anrabata fad’a da yaraba.
Yarinya saikace shed’aniya,
Wannan zanga wandanzai kwasheta yakwashi bala’i.
Isha’q yaji ‘kirjinshi yabuga dam.
muje zuwa guy’s
September 21, 2017 at 12:05pm ·
������������
*Anty ‘yar charas*��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN KWAILA* ����♀
Chapter 4.
Isha’q yaji ‘kirjinshi yabada dam,
Amma dayake jarumine saiya fuske gami da janye hannun sadi’q dafad’in “kayi abinda yadameka malam”,
Sadi’q yasake kyal’kyalewa da dariya yana fad’in”allah yarinyar ce so funny”
Isha’q yaja tsoki bai tankashi ba,
Sai gab da isha’i zahra tanufo gida,’kirjinta yana bugun uku-uku aranta tana addu’ar “Allah yasaka umma bata tsakar gida,
Talala’bo tana sand’a lokacin datashigo gidan takalma a hannu bayan tafara zuro kanta taga gidan babu kowa.
Tafara tafiya sad’af-sad’af danufin fad’awa d’akinta sai dai batayi auneba taji umma tacafketa caraf ,
Ta waigo fuskarta da alamun tsoro,
Kafin tayi wata magana umma takifa mata mari.
Da tambayar “daga gidan ubanwa kike?”
Zahra idanu suka raina fata,
Tafara ro’kon umma”wayyo ummana kiyi ha’kuri bazan sakeba.”
Umma tace”rufemun baki shashashar banza,bazan ‘kara d’inkiba datana tasiri dayanzu namance dawata aba wai ita damuwa.meyasa kikeson sakamun hawan jinine zahra,abinda duka y’an uwanki basuyiba.”
Umma ta’kare maganar kamar zatayi hawaye.
Zahra dai kuka take tana”allah umma nadena.”
Umma bata bartaba saida tayimata ligi-ligi tasaketa,tafara haramar alwalar isha’i.
Zahra ta ‘kyalla idanu taga umma tashige d’aki,
Hakan yabata damar sake ficewa gidan da saurin gaske,
Bazata mance kirarin dasukeyima kansuba wai *abuga asaki bata maganin d’an iska sai dai ta’kara taurin fata*.
Azauren su ummilolo tala’be,tana ‘kwalama ummilolon kiran,
Hajara kishiyar innar ummilolo tafito tana masifa don tasan zahrace”kewai wacce irin ballagazar yarinyace,halan kekam uwarki bata kwa’ba maki.duka yaushe kuka shigo gidan amma dayake bakida tarbiyya harkin sake fitowa,to oya maza fice anan ummi babu inda zataje.”
Shegiyar yarinyar yarinya mai kama da d’inya,ke ba’ka halinki ba’ki.
Zahra ta murgud’a baki dacewa “badai niba.”
Inna hajara tace”sai ubanwa”
Zahra cikin rashin tsoro tace “ubanki”
Aiko inna hajara tayo kanta zahra tajuya da niyyar rugawa amma tuni inna hajara ta cafketa.
Mari biyu ‘kwarara tayi mata, taci gaba dafad’in”duka iskancin dakikeyi ‘kyaleki akayi.wlh kinshigo gonata ubanki zakici.”
Zahra dayake ruwa ruwace tuni ta ‘barke da kuka tayi waje aguje,
Takuwa koma ‘kofar gida ta tara duwatsu tadinga yima gidansu ummilolo ruwan duwatsu,
Duk da haka bakinta bai sassauta da zagin datake d’urama hajaraba.
A tsotsayi d’an hajara yafito zashi kicin d’aukar abinci dutsen ya sauka akanshi jini sosai ya tsinke ganin hakan yasaka hajara kama hannunshi suka nufi gidansu zahra tanata masifa.
Zahra daganan zugar yaranta sukaja,suka la’be lungu ilai kuwa saiga inna hajara tadawo da abbalo ansaka mashi bandage,
Zahra da sauran ‘kawayenta sukayi masu ature da ‘kasa har cikin bakin hajara da idanuwanta.
Zahra data du’ka tana ‘kyalkyala dariya tace”kuma wlh kisake dukana saina kama wannan d’an naki a islamiyya saina fasamai baki.”
Inna hajara tace”tsinanniya kije zaki samu dai daike.”
Zahra dake wani gantsarewa tace”tsinanniya tana bayan uwarta tanashan nono,”
Sauran yaran suka kwashe da dariya.
‘karshe dai inna hajara ganin zasu kunyatata gaban mutane yasakata sulalewa tayi gida,acan tad’ora sabon bala’i tana sauke kwandon zagi akan zahra da iyayenta.
A filin gad’a ma zahra saida suka dambace da yara kusan uku,
Daganan tace ayi zuga atafi jan fad’a.
Suna tafe duk wanda suka gani saisun tsokana,wani ya ‘kyalesu wani yabisu a guje amma baya iya kamosu.
Dai dai wani lungu suka hango saurayi da budurwa na tad’i,
Zahra tace “yauwa alhmdlh dama waccen habibar dake fira prefect d’in makarantar muce gata muguwa tayita dukanmu,
Kuzo muje”
Yara suka bita d’uuuu,tana gaba.
Dayake garin akwai hasken nepa dakuma na farin wata,
Habiba na tsaye gefen saurayin nata can gefe wasu samarine data gama yima wula’kanci taga mai mota yazo.
Bata saka hijabiba sai d’an gyale daya tsaya iyakar kafad’unta.
Gefe dasu teburin masu shayine damasu tsire antara majalisa ana cafta.
Zahra tana isa kusa da habiba batayi wata wataba tasaka iyakar ‘karfinta ta fincike zanin habiba,
Habiba gashi sam bata saka undey ba.
Saiga ‘kafafun habiba tsaye zalo .
Zahra kuwa tace ‘kafa menaci ban bakiba.
Takwasa aguje,yayinda saurayin habiban ya rufa masu baya
Tsabar kunya habiba saita du’ke inda take.
Sauran samarin data yan’kwana kuwa har fad’uwa sukeyi suna burgima saboda dariya .
Majalisar masu tea ma dariya suke suna ‘karawa.
‘karshe habiba d’an gyalen dake kafad’arta ta yafa a kafafunta.
Da rarrafe ta shige gida .
Su zahra sunyi gudun da yakai nisan inaa.sannan suka yarda zanen saurayin ya tsintoshi bayan ya du’ka yanata hakin wahala
Dafad’in “shegun yara saigudu kamar zomaye.”
Daga tonon wannan fad’an kowa ya ware gida,
Kanshi tsaye banda zahra dake faman ra’be ra’be.
Tamakure a lungu,
Abba yadawo daga nemanta har yagaji yanufo gida yaci karo da mutum…
Matsalar nepa.
Ayi ha’kuri da wannan
September 22, 2017 at 7:44pm ·
��������
by yar charas��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN ‘KWAILA*����♀
Chapter 5.
Da touch light ya haske mata fuska ta d’ago fuskarta da alamar tsorata don sarai tasan abba bayada wasa.
Da ‘karfi yakira sunanta”zahra,mekikeyi anan daga ina kije.?”
Kanta tsaye tace”wasa naje yi”,
Abba ya gyad’a kai,”dakyau”.
Kawai yafad’a yayi cikin gida abinshi,yayinda zahra ta rufa mashi baya.
Umma tana tsakar gida hankali a tashe abba yashigo zahra nabin bayanshi,
Umma tana ganin sundawo tawuce d’aki abinta ranta a dagule yake.
Bai tanka zahranba ya kutsa dakin da umma take,tahad’a kai da gwuiwa idanunta daf da hawaye.
Abba yadafa kafad’arta dakiran sunanta”amina,kiyi hakuri kifidda damuwar zahra acikin ranki,kisani kowacce rayuwa akwai jarabta mu tamu jarabtar kenan,don haka kima dena zancen wai kiyita dukanta.kitattara kici gaba da addu’a amma ni sam lamarin zahra yadena bani mamaki yakoma bani tsoro.”
Umma tasauke numfashi,”to yaya zan’iya cire damuwa abban zahra,damuwa ai ita keyin kanta.ace babu rana ta ubangiji dazata fito takoma ga allah ba’azo ancedani zahra ta’aikata wani abuba.saikace tafi sauran y’ay’ane.”
Abba yace”kul dakiyima yarinyar nan baki,mudaici gaba da addu’a,jiyama liman yazo hargida yanamun kashedi wai tajefashi kwata zashi sallar isha’i.”
Umma tazaro idanu dafad’in “liman d’in dakanshi,,?
Abba ya gyad’akai”‘kwarai kuwa,waisuna wasa anrufe idanunta toyazo ‘ketare kwata tazata yarinyace shinefa ta cakumeshi,shikuma wai yana addu’ar zuwa masallaci bazaiyi maganaba.
Nana kokuwa ta sar’ke tajefashi kwata.”
Umma duk da ‘bacin ran datake ciki saida ta dara,
Data tuna yanda liman yake saka malummalum idan zashi masallaci.
Ta girgiza kai,”Allah ya shirya,”
Abba yace “ameen.”
Zahra kam tuni ta kwanta abinta, bata tsaya neman abincin dareba don dama ba ma’abociyar cin abinci dayawa bace.
Barta dai ga ‘kwalama wannan fa ogace.
**********
Bayan kwana biyu….
Zaune yake a tsakiyar grass carpet d’in daya gewaye tsakiyar ‘katon falon,
Gabanshi laptop ce yana ‘kara nazarin banbancin dake tsakanin zahransi da little zahra kamar yanda yasaka mata suna,
Gefe guda ‘kanwarshice hanan wacce bazata shige tsaran zahraba,
Doctor ru’kayya ta tako ahankali daga stairs cikin dakakken leshinta mai tsadar gaske,jikinta akoda yaushe yana fitar da siririn kamshin turarenta mai tsada.
‘yar kyakyawar fuskarta dabata tsufa tana manne da glass din daje kuma kayatata.
Isha’q da hanan atare suka mi’ke dukansu suna sakarmata murmushi
Tazare wayar dake kunnenta tana sakarma kyawawan yayan nata murmushi,
Ta kalli isha’q dafad’in”yayankane muke maganar yarinyar dakake bani labari,yace kamata yayi mushirya muje muganta ayi komai da lissafi,sannan yakira wayarka tana a kashe.”
Isha’q yasaki dariya yace”nakashetane nasaka charge mum”.
Yami’ke da sauri yana fad’in”mum kice kawai inshirya yau saigidansu pretty,yawani dun’kule hannuwa da naushin iska,wlh mum saikin ganta she’s very beautiful nd younger.”
Mum tace “kome kakeso isha’q aibaka ganin muninshi,haka kake tun kana yaro.sa’banin yayanka dayakeda a’kida dakuma ra’ayinshi na santseni.”
Ya shafi gefen fuskarshi yana murmushi,”Allah mum tanada kyau,iluv zahra very much mum.”
Zaunawa tayi tana canja channel”idan kagama surutunka inajiranka,haka zakaje kana rawar jiki ai yarinyar saita raina class dinka,ya murmusa yana tafiyarshi ta ‘kasaita yace”haba mum kada kisa wannan ta’kwalar ta rainani mana.”
[9/23, 10:00 PM] mum meenat: Yanuna hanan wadda ta zubama yayan nata idanu tana kallonshi,
Dasauri ta tashi ta la’be bayan mum dafad’in “mum zakije dani”.
Doctor ru’kayya tamurmusa tace”kibari dai watarana saikije lokacin kinsamu hutun makaranta,yanzu kam ai zaki takuratane.”
(tazata zahra babbace )
Isha’q kam fakaitarta yayi yasaki dariya dafad’in”sai mumcy”,
Tana zaune tana kallon wani series yafito cikin hadadd’en yadinshi filtex mai yal’ki ruwan madara,
Kanshi yasha hular zanna bukar baqa,
Kafarshi cikin bakin takalmin daya matu’kar dacewa da shigar tashi.
Handsome and giant,
(abinda na raya kenan.)
Hadadd’en ‘kamshin turaren American crew yakasa barin jikinshi,
Still akwai farin glass a idanunshi,
Ita kanta doctor ru’kayya tana alfahari da isha’q matsayin d’anta very handsome guy.
Yanada dukan qualities daya kamata mace taso a tattare dashi,
Dogone irin tsayin hadaddun maza d’innan,yanada fasalin ‘karfi da jarumta a tattare dashi don ‘kwarae mayen exercise ne.
Yana rud’a makwad’aitan mata da kamfacecen ‘kirjinshi dakuma murdadden jikinshi.
Wankan tarwad’ane wato ya d’auko kalar doctor ru’kayya ne,
Sa’banin yayanshi aliyu dayake fari tar yad’auko kalar mahaifinsu.
Isha’q gogaggen matashine wayayye daya samu shedar kammala karatunshi na degree mataki na biyu akan mass communication ma’aikacine da gidan talabijin ta ‘kasa wato NTA sosai yake samun sa’konnin yammatan dasuke mutuwar ‘kaunarshi musamman don fara’arshi,
Dakuma iya zama da mutane don isha’q bdai iya kyautatawa ba.
‘karasowa yayi jikinta ya tallafi fuskarta da hannayenta”am readay my mum”
Yafad’a da shagwa’barshi,memasa kyau.
Tace “i see”
Tami’ke tana gyara zama mayafinta dasaka glass d’inta,
Isha’q ya tsuramata idanu”am proud of you be my mother mumma.”
Tashafi fuskarshi itama da murmushi,aranta tana jin zallah farin ciki saboda dawowar walwalar d’anta daya rasa tsawon lokaci.
Tare suka jera gwanin sha’awa suka shige cikin d’aya daga cikin motocin gidan,
Tazauna a mazaunin kusa da driver yayinda isha’q yake driving suka lula gidansu zahra.
Umma tagama gyara d’an matsakaicin gidansu,tana saka turaren wuta tajiyo sallamar doctor ru’kayya,
Taleko da fara’arta tana fad’in “lale marhaba da ba’kin yamma.”
Doctor ru’kayya ta murmusa aranta tana yaba wayewar umma.
Ruwan randa mai sanyi umma ta’ajiye gaban doctor ru’kayya,bayan ta shimfid’a mata tabarma.
Dr.rukayya tazauna tana cire gilashin idanunta,likaci guda tana kai ruwan da umma ta’ajiye mata a baki.
Takur’ba kana tace da umma”nasan baki sanniba ko?.”
Umma ta gyad’a kai”kwarai kuwa.”
Dr. Ru’kayya tasake murmusawa tace a ta’kaice”sunana ru’kayya anas kado malumfashi,ni haifaffiyar malumfashi ce,iyaye da dangi mahaifina y’an canne,sai dai dangin mamana sune mutanen funtu’a, nayi karatun likitana anan Nigeria sai dai nasamu sakamakon zama babbar medical doctor ne a India,inda acanne na’karasa karatun nawa.
Nayi aure anan kaduna da mijina babban d’an kasuwane anan abubakar gumi,awancen lokacin ayanzu yanada manyan kamfanoni a ciki da wajen ‘kasar nan.
Inada y’ay’a uku maza biyu sai autata hanan,
Babban sunanshi aliyu yayinda mai binsa shine isha’q,
Daganan haihuwa ta d’aukemun sai daga baya Allah yabani hanan,Aliyu yanzu haka yana ‘kasar turkey yana kula da kamfanin mahaifinshi dake jigilar rid’i.”
Muje zuwa
September 23, 2017at 10:27pm ·
*by anty y’ar charas*����♀
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
NEW WORLD NOVELS
BY MAMAN MEENAT
EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR)
Wannan shafin naku ne yn (Madarasatul Tahafeezul Qur’ an Funtua, Allah ka qaramana fahimta a
iliminmu)
Chapter 6.
Doctor ru’kayya tad’an tsagaita jin ana kwad’a sallama,duka itada umma sukakai dubansu ga hanyar shigowar,abbane yashigo da ledar yalo a hannunshi,umma tami’ke da sauri tana mashi sannu dazuwa ta’amshi ledar dake hannunshi tawuce d’aki da’ita.
Abba yadubi hajiya ru’kayya kallon rashin sani,
Itakuwa ‘kasa tayi dakai tace”malam ina wuni ya hidindimu.”
Abba ya’amsa da “Alhmdlh”yawuce ciki bakinshi fal da tambayoyi.
Daki yasamu umma tsaye da alama zaman jiranshi takeyi,yamata kallon tsaf kafin yace”wace hajiyace nagani anan tsakar gida,kuma hada wani d’an saurayi nagani a ‘kofar gida dawata kwatsetsiyar mota,wasuke nema kuma?.”
Umma tad’anyi jim kafin tace”to malam nikam bazan iyacewa komai ba,nadaiga tazo batace ga abinda yakawota ba,amma naji tad’auko tarihin yaruwarta tana bani,bansan da wacce tazo ba.”
Abba yace “shige muje,aiyanzu zamani ya canja bana barki ked’ayaba.ina zahra ne,ko bata dawo daga islamiyyar ba.?
Umma tace”kaima kasan nanda isha’i yayima zahra kad’an kaganta anan gidan,watakil sai takwas na dare idan tagama yawon tsokanar jama’a.
Abba yayi ‘kwafa yace”gab nake da kawo ‘karshen iskancin yarinyar nan ai.
Umma tafito har tsakar gidan tana mitar”ai indai zahra ce,bazance bazaka iyaba amma abune mai wahalar gaske.”
Dr.ru’kayya ta kafe umma da idanu tanason nazarin maganar datake jiyowa tana tashi daga bakin umman.
Gefe baba yazauna bisa kujerar roba,yayinda umma tazauna akan y’ar tsugunno.
Abba yasake gyaran murya yace da dr.rukayya”baiwar Allah lafiya dai,bamusanki ba,maid’akina tace kinzo kinata bata tarihinki kodai kinyi ‘batan kaine.?”
Dr.ru’kayya murmushi tasaki dacewa “ko d’aya malam.kamar yanda nabawa matar ka labarina hakane,inada yaro isha’q wata’kila kaganshi anan waje,hakane?”
Tayi tambayar gami da tsatsare abba da fararen idanunta masu cike da zallah wayewa.
Haka kawai abba yaji tayi mashi kwarjini idanu,tanada tarin baiwar cika ido.
Ya’amsa dacewa”kwarai kuwa.”
Tace “gud”
“Yarona isha’q yarone nagari,yanada kyakyawan hali abin ayaba,bawai don yana d’anaba a’a,halin isha’q yasha banban dana sauran maza donshi mutum ne dayasan hakkin wanda yake tare dashi,bayada girman kai bayada miskilanci,yataso tun yana yaro tare da zahra,d’iyar kanwatace wadda Allah yayima rasuwa tun ranar data haifeta batako kalli fuskarta ba.zahra tatashi cikin maraicin uwa hakan yasaka nad’auke duk da mahaifinta baiso hakanba, nareni zahra cikin ‘kauna da aminci.
Zahra tasha’ku da isha’q saboda idan bani ko isha’q ba zahra bata yarda dakowa acikin gidanmu.
Lokacin da isha’q yashiga secondary zahra anyayeta,komai nata isha’q ne yakemata shine ya canja mata sunanta daga zahra adam yamayar mata *zahra adam isha’q*,tunda nake a rayuwa banta’ba ganin soyayya da sha’kuwa irinta zahra da isha’q ba.
Kai intakaice maku labari,lokacin da isha’q zaitafi Germany karatu gaba d’aya dashi da zahra saida suka kwanta asibiti.
Alokacin munzata sha’kuwace,sai dai abin mamaki sam zahra bata kula samari duk da takammala karatunta na secondry ko saurayi zuwa yayi wajenta saitace yaje yatambayi isha’q idan yayimashi to itama yamata.
Isha’q kam kullum cikin kushe samarin zahra yake,kullum cewarshi hadadd’en gaye zahranshi zata aura.”
Doctor ru’kayya ta numfasa tacigaba,
“zahra yarinyace mai tarbiyya da tsoron Allah,tanada matukar natsuwa da kamala,mahaddaciyar Alqur’ani ce.zahra wankan tarwad’ace tanada yanayin girman jiki,don duka sa’anninta zaka zata tagirme masu saboda jikinta mai saurin tofone,
Sam magana bata dami zahra ba,gwanar kwalliya da tsafta,gwanar iya kalailaye mutane da tattausan lafazi ce.
Lokacin dana lura cewar zahra da isha’q sunkamu dason junansu sainafi kowa murna,don inaganin isha’q yayi matarvda har duniya tanad’e bazaiyi kaico da itaba.
Sa’banin yayanshi dabai dace damacen kirkiba.
Isha’q baitafi karatuba saida baikonshi da zahra,
Koda yaushe suna manne a waya suna firar soyayya,
Alokacin itama takoma makaranta tana karantar likita cewarta zata gajenine.
Isha’q yagama karatunshi da sakamako mai kyau yadawo gida,alokacin aka tsaida maganar aurenshi da zahra dangi kowa yayi murna.”
Tashare hawaye taci gaba,
“sai dai kash ana saura kwana uku bikinshi zahra tatashi da matsanancin ciwon mara cikin dare wanda yayi sanadiyyar d’aukewar numfashinta duk da kokarin ceton ranta damukayi Allah ya amshi abarshi.
Alokacin isha’q haukane kawai baiyiba saboda zautuwa saida yakwashe sati guda baisan inda kanshi yakeba,daga baya zama tamkar wanda yarasa memory nashi.dataimakon Allah da addu’u a isha’q yazama normal sai dai duk barkwancin isha’q yatafi yazama tsakaninshi damu gaisuwa kawai,yaci alwashin bazai taba aureba.har yakoma ga mahaliccin shi muddin baisamu kwatankwacin zahra ba,
Tad’ora dafad’in “babu tallar yammatan daba ayiwa isha’q ba amma yace ina.shifa angon xahra ne,tausayinshi yasaka naxura mashi idanuwa,har tsawon watanni shidda.
Dayake Allah gafurune kuma rahimu saiya maido mana abinda muka rasa tsawon lokaci muke kwana muke tashi da kukan rashinta.”
Tadakata tana nazarin fuskokin dattijan biyu,
Sai dai cikinsu babu wanda yasan inda zancenta yadosa,hasalima anasu ganin wannan matsalace data dace tasanarma wad’anda suka santa bawai basuba.
Indai ba’itama tarasa nata hankalinba,su menene nasu illah iyaka suce Allah yajikan rai.
(anasu ganin ba.)
Abba yad’an numfasa yace”to dafarko muna maki ta’aziyya dakuma bakin cikin rasa y’a tamkar zahra.saimuce Allah yajikan rai,abu nabiyu daya tsayamun araina shine mudai bamusan menene ainahin dalilinki na za’barmu a matsayin wadanda zaki sanarma damuwarki ba.
Idan har kina son sanarda wani damuwarkine babu mafi cancanta kamar yan’uwanki da danginki bawai muba,da bamuda maganin dazamu iya baki domin warkewar damuwarku.
Ummata jinjina kai”wannan gaskiyane.”
Murmushi doctor ru’kayya tayi tace”malam aikune maganin matsalata,nazone da ‘kokon barata dakuma nan arziki akan ku taimakeni,kamar yanda Allah ya taimakeku idan baku za’bama d’iyarku zahra mijiba kubama d’ana isha’q aurenta.”
Daga umma har abba had’a idanu sukayi,lokaci guda suka sakarma juna murmushi,abba yace”toga dai dukkan alamu acikin abu biyi dole asamu d’aya,imma dai makuwa kikayi kokuma kema bakida hankalin.idan bayaga haka yaushe zakice inbama d’anki auren zahra.? Tukunnama haka kawai siyaa bagatatan sai ind’auki y’a inbaki saikace banida hankali.”
Dr. Rukayya taji zafin maganar abba,amma dayake ance mai nema baya fushi,saita sake numfasawa tace”kayi ha’kuri abban zahra nafahimci baka gane zancena ba sabo……”
Sauran maganar ta ma’kale a fatar bakinta lokacin da zahra ta kunno kai gidan, tana fad’in”Allah ya isa banyafe ba,muguwa azzaluma kinbugi wuta balbal har kabarinki na balbala da wuta,kuma wlh yaro ya’kara cemun zahra’u mala’ikar yara sainaci kutmar babbar saibitin babakeren buuuuu………”
Bata ‘karasaba umma takaima bakin naushi,tace “to jarababbiya ko’ina saikin nuna halin naki.”
Zahra cikin hawaye tace”to umma sai takamani tayita dukana wai don nabugi d’anta aishi yafara jana.”
Umma ta zuba mata harara”gara dayajaki aike karyace ko.dakowa zaidinga tsokana,kinzama sakarya a layi kowanne datti badole a sauke a kankiba.”
Zahra tace “wlh anjima sainayima gidansu ruwan duwatsu.”
Umma tayi tsoki”aikin da kika iya kenan fitinanniya.”
Dr.ru’kayya datayi mutuwar zaune,tasaki baki aranta tana tasbihi ga Allah wanda ya’kagi kamanni yakuma banbanta halayya.”
Nima sai naga comments xan cigaba don naga kamar buk din beyi muku dadi ba
Kuna tare da maman meenat, Aisha t. Fulani Insha Allah
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
By maman meenat
EDITED BY AISHA ABDULLAHI(UMMUN FAROUQ)
CHAPTER 7.
Umma taja tsoki takoma tazauna abinta,
Yayinda zahra ta cillar da jakar islamiyyar dakuma hijabi tafad’a band’aki.
Dr.ru’kayya tasauke numfashi tana kallon su umma kafin tace”wannan kuma ‘kanuwar Zahran ce kokuwa.?
Umma ta kalleta da mamaki tace”a’a itace zahran ai.”
Wani shegen gumine ya karyoma dr.ru’kayya lokaci guda tafara tsane zufa da handkerchief dake hannunta aranta tana addu’ar tafarka daga rud’adden mafarkin dayayi hajijiya da tunaninta dama kwakwalwarta.
Tad’an saita kanta kad’an kafin tad’ora dafad’in”to agaskiya dolene ku kalleni a matsayin wacce kanta ya zautu,kokuma ‘batan kai inba hakaba babu mahaluki mai hankalin dazai dubi karancin shekaru irinna zahra a gari ba ‘kauyeba yace ayimata zancen aure.”
Tad’an tsagaita tana sauke numfashi kafin tad’ora dafad’in.”adukkan zatona dakuma tunanina nayi zaton zahran babbar budurwa ce,amma don kamanni da tawa zahran tabbas suna kamanni nagasken gaske,sai dai kash wannan zahran tayi kankantar dabe kamata ace anyimata aure yanzuba.”
Sai lokacin su abba suka fahimci inda tasa gaba,
Abba yami’ke yana cewa”inace dai yaron dakeson zahran shine awaje tsaye ko.?”
Doctor ru’kayya ta’amsa dacewar”shine malam”,
Abba yafita kofar gidan,isha’q har lokacin yakafe kofar gidannasu zahra da manyan idanunshi yanason ganin ta’inda kyakyawar fuskar zahra mai kama data black Americans zata ‘bullo,sai dai sa’banin zahra saiyaga abba yafito yana sa’ba babbar riga.
Isha’q yayi saurin du’kawa yana gaida abba,
Abba ya’amsa kanshi tsaye yace”kaine isiyaku.”?
Isha’q yawaro idanuwansa masu kwarjini da haiba,yace”abba isha’q nake.”
Abba yace “afto ai duka dai d’ayane,to inason magana dakai ga mahaifiyarka can cikin gida don haka kashigo ayita a gabanka ta ‘kare.”
Gaban isha’q yabuga da ‘karfi,idanunshi tuni sun canja launi daga farare zuwa green tsigar jikinshi tabada yarrrr,aranshi yana addu’ar kada Allah yasaka yasake rasa zahra akaro na biyu bayan tadawo gareshi.
Kai yama rantse komai rintsi bazaifa rabu da sanyin idaniyarshi ba,aidukkan mai imanin dayasan tarayyarshi da zahra abaya bazaiga laifinshi don lokaci guda ya mayincema little zahra ba.
Abune mafi tsanani agareshi yakice soyayyar da’aka dasa tun zamanin ‘kuruciya yanason zahra yana ‘kaunarta yanamata *so d’aya tak*son daya rantse babu mi’ki ko algussu acikinshi.
Jikinshi babu ‘karfi yabi bayan abba wanda tuni yakai zaure,
Inbayanga addu’ar samun nasara babu abinda isha’q yakeyi acikin zuciyarshi.
Da sallama ya kunna kai cikin gidan,lokacin yayi dai-dai da fitowar zahra daga band’aki,
Idanunta suka sar’ke dana juna lokaci guda duk rashin kunya da fitsarar zahra taji isha’q yamata wani kwarjini wanda ita atata haukar jitayi ya burgeta don zahra akwaita dason y’an gayu,uwa uba tanadason kwalliya duk da cewarta ita ba’kace amma saitafi su anty hafsa zama y’ar gaye.
Tasauke idanunta cikin na isha’q wanda yamace atsaye yana kallon baiwar gashin dake kan zahra,yatunano tashi zahran batada irin wannan gashin,
Ya runtse idanuwa,yana tasbihi ga Allah wanda ya’kagi kamanni tsakanin zahra dakuma little zahra.
Itama dr.ru’kayya mamakin irin gashin zahra takeyi,lokaci guda taji yarinyar tazaunan daram acikin zuciyarta tabbas soyayyar datake yima marigayiya zahra ce zata koma akan wannan zahran,
Kai itama tana ganin kobada aureba yakamata zahra tazama wani ‘bangare daga jikinta,she luv xahra moree.
Isha’q yatako kamar wanda kwai ya fashemawa aciki yazauna kusa da mahaifiyarshi yana gaida umma wadda takafe kyakyawan saurayin da idanu tana dad’a tasbihi ga Allah daya tsara halitta mai tattare da baiwar natsuwa irinta isha’q.
Zahra kam bata saurare suba taja jakarta da hijab tajefa d’aki,
Tadawo kitchen tana neman abincinta hankalinta kwance dukkuwa da sarai tagane isha’q,shine mayen kallonta d’innan idanunshi basamata kyan kallo,saitaji gabanta yana fad’uwa idan tana kallonshi.
Dr, ru’kayya ta kalleta a tausashe tace”zonan d’iyata zahra,
Kamar baki,saiga zahra tataka sif-sif zataje inda dr.rukayya take,
Idanunta suka sar’ke dana isha’q akaro na biyu,
Ta murgud’a mashi baki had’i da jefa mashi harara.
Yasakar mata murmushi,
Abinda ya ‘kufulata yasaka tacije baki had’i da girgiza kai.
Saida taje kamar zata wuceshi taje wajen doctor ru’kayya tasaka ‘kafarta ta take hannun isha’q wanda yadafa ‘kasa dashi.
Yajanye hannun da sauri,yana yarfawa.
Ta kwashe da dariya lokacin data ra’ba jikinta dana dr.ru’kayya tace”yaro kaci gaba da kallona kamanta ranar dana ‘kala maka sheri sojoji suka kamaka ko.?”
Tafad’a tana cije le’be da fiddo sexy eyes dinta waje.
Isha’q ya girgiza mata kai alamar kada ta fad’a,
Amma saicewa tayi”tomiye kuma naga kanata girgiza kai,hhhh katuna marin da wannan mai ‘katon cikin yayi maka ne.?”
Abba ya daka mata tsawa yace “rufe mana baki,waya tambayeki.”
Umma ai kunya bata barta zama wajenba,saita tsiri fura wutar dole.
Dr. Ru’kayya tayi tsam tanason tunano ranar da isha’q yadawo yacemata bashida lafiya dataga fuskarshi da kumburi ta tambayeshi yace mata yafad’ine wajen training.
Ta girgiza kai kawai.
Abba yafara magana”to masha allah isha’q kaine ka aiko mahaifiyarka akan kanason inbaka auren zahra.”?
Isha’q ya gyad’a kai kanshi yana ‘kasa yana wasa da yatsun hannunshi.
Abba yasaki murmushi nasu na manya yace”to isha’q bazan ‘boyemaka ba,bakuma don kunada arzi’ki yasaka zan fad’i ra’ayina akanka ba,wlh kallo d’aya namaka naji nasamu natsuwa dakai.sannan akwai alamar kwarjini da wata baiwa da Allah yamaka wadda dukkan mahalukin daya mallaki hankalin kanshi ya kalleka zaigane kai kamilin mutim ne,”
“Hakane”?
Yajuya yana tambayar umma,wadda ta tsugunna bakin adarkin kitchen,
Umma tace”hakane malam”.
Dr. Ru’kayya sai murmushi take anyaba mata d’an lelenta.
Abba yad’orabdafad’in”kaikuwa wacce ‘jarabta ce takaika za’kulo zahra amatsayin matar dakakeson aure,nafarko zahra dai yarinya ce ‘karama nabiyu zahra bawani kwayon da zaya rud’i mutum gareta ba,illa tulin sumar kai wadda harmun gaji da askewa mun barta taji da abarta.sannan bazan ‘boyemaku gaskiya ba,zahra batada kunya ka ganta nan,”
Ya nunata da yatsanshi,
Takuwa zumbure baki tana ‘kunkuni.
Dr. Rukayya tace”a’ah zahra d’iyata meyasa kike hakane,abban kikema gunaguni.”
Zahra tace”nifa badashi nake ba,”
Umma ta ‘amshe to anan ciki waye tsarar wasanki dawa kike”
Ta nuna isha’q da yatsa,tana sake turo baki”bashine yaketa kallonaba,kuma wai har yana runtse idonshi d’aya,(kashe ido)
Kunya kamar ta kashe isha’q haka yaji.
Dr.ru’kayya maka mashi mafecin dake hannunta tayi dacewa”tashi maza kabar nan,mara ta idanu kawai.”
Yakoyi ‘kememe abinshi baiko motsaba.
Abba yad’ora dafad’in”to agaskiyar zance nikam bantashi yima zahra aureba,donkuwa dukkanin yayunta babu wacce na aurar batare da ta samu sakamakon takardar n.c.e ba,don haka idan nace zanyima zahra aure awannan lokacin na zalunceta nakuma shiga hakkinta duk da bawai musuluncine ya hana aurar da yarinya tana shekaru sha biyu ba,hasalima shekara tara musulunci ya yarda ka aurar da yarinyarka,amma yanzu zamani ya canja akwai cutuka da dama da ada bamudasu sai yanzu,sannan zahra bawai wayone ya iaheta ba,bayaga rashin ha’kurinta tanada mugun surutu dakuma su’butar baki.
Amma nayi maka al’kawarin muddin zahra ta girma tace tana sonka zan aura maka ita,wannan shine kawai maganata.”
Dr. Rukayya ta kalli isha’q wanda idanunshi suka kad’a sulayi jajur,
Tace “tokaji da kunnuwanka abinda abba yace,saikayi hakurin zahra ta girma kusan shelaru goma nan gaba ‘kila.”
Hawayen dayake ‘kokarin ri’kewa tuni sun ‘balle,babu kunya ya ri’ke kafafun abba yana ro’konshi”abba don girman Allah kada ka nisantani da zahra abba,ka tausayamun soyayyata da zahra *had’in Allah*ne,bana nufin cutar da rayuwarta har abada pls abba.”
Duk da taurin zuciyar abba saida yaji tausayin isha’q amma kuma donme ze tauye rayuwar zahra.
Umma jitayi bazata iya kallon hawayen isha’q ba,saita shige d’aki abinta.dama ita nata biyayya duk abinda abba yatsara awajenta yagama tsaruwa.
Dr.ru’kayya ta kalli isha’q daya kasa dena fitar da hawaye tace”kajiramu awaje inazuwa.”
Yatashi ya fita,yana sake waigen zahra wadda dukkan jikinta yayi sanyi ‘kalau tana kallon isha’q badai tagane akan me suke tattaunawa ba.
Dr. Rukayya tasake rusunama abba tace”nagode da kyautar dakayima d’ana amma na ro’keka daka taimaki rayuwarshi,don Allah kada kayi fancakali da lafiyar damuke tarairaya tashi,natabbata isha’q zai rike zahra amana,
Wlh namaka rantsuwa babu wani abu na ga me da auratayya dazai shiga tsakanin isha’q da zahra harsai takai munzalin hakan,
Sannan karatu konan da inane zan tsayama zahra tayishi,inada yarinya bazata shige tsarar zahranba atare zan renesu don dukansu y’ay’a nane.”
Ta tsagaita tanason jin amsar da abba zai bata.
Nima natafi break
September 26, 2016 at 10:43pm · Public
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
BY MAMAN MEENAT
EDITED BY AISHA ABDULLAHI (UMMUN FAROUQ)
Chapter 8.
Tad’anyi jim tanason jin amsar da abba zai Bataan .
Abba yasake gyaran murya gami da tofar da wayu gefe,yana sakace ha’kori da asuwaki yace”nifa hajiya kindai gaza fahimtata ne,amma tayaya zan baku auren yarinya haka kawai nifa bansanku ba,nadai ganku ne kawai gaskiya abune mai wahalar gaske hakan.”
Dr. Ru’kayya taja numfashi”malam mu bawasu ‘boyayyu bane a garinnan,mijina sunanshi alhaji saifullahi mai rid’i yana sana’ar kai rid’i turkey yanada shagon gold anan abubakar gumi.”
Abba ya kafeta da idanuwa kafin yasaki dariya dace”Allahu akbar azzawa jallah gwanin hikima,dama ku iyalan alh saifullahine,mutuminane kai mutum na gari.bazan ta’ba manta alkairinshi gareni ba.”
Yanuna umma data le’ko daga d’aki tana murmushi yace”gata kinganta nan haihuwarta ta farko kamar bazatayi ba,banida sisi a aljihuna banida kadarar sayarwa aka tsawwala mana kudin yimata tiyata dubu tamanin nad’aga gidan danake ciki zan sayar bawan Allah yaganni a asibiti ina kuka yake tambayar meya faru,na sanar mashi wlh hajiya atake ya shiga ofis din likita yarubuta mashi kudin a takaddar banki,yace ayi gaugawar ceto rayuwar saudatu.kuma yace nabishi ofis dinshi,bayan yabani takarda ta address naje shine yabani dubu d’ari nafara sarin bulawus ina kaiwa kasuwa da wannan sana’ar Allah ya d’aukakeni gashi ina cikin rufin asiri har yanzu.”
Dr. Ru’kayya tasaki
lallausan murmushi tasan mijinta yafi dahaka kaf halinshi isha’q ya d’auko.
Abba yadinga mamaki itama umma saida tasake yima Dr Rukayya godiya,
Abba ya ‘kwalama zahra kira yace maza kice ‘bakonnan na waje yazo yanzu yashigo ciki.
Tafita kai bako d’an kwali tahangoshi yajingina bayanshi a mota yayi lamo Allah kadai yasan abinda yake tunawa.
Ta dage iyakar ‘karfinta tace”kai mai motar nan,kai mayen kallon mutane kazo ana kira.”
Isha’q yaji gabanshi yasake bugawa yace “ina zuwa,tajuya zata shige gida,
Yace”jirani mana.”
Tawaigo tana ‘kare mashi kallo saikuma tabuga zani da murgud’a d’uwawu”sumbuqa sagwaigwai takashin mage da barima hada sarqa a gabanta”,
Isha’q yadafe kai “oh Allah zahra kam anya tanada cikakkiyar lafiya kuwa?”
Ita komai nata sai tasaka wauta da shirme.
Ya ta’be baki dacewa “aini nace naji nagani.”
Yashigo da sallama yasamu waje ya zauna,
Abba yasaki murmushi dacewa”taso kadawo kusa dani d’ana isha’q. ”
Isha’q yakoma jikin abba yana du’kar dakai.
Abba yace”isha’q kadaiga wacece zahra,amma ahakan kace kaji kuma ka gani ko.?”
Isha’q yace “hakane abba agaba duka wannan zata dena aikowa da tashi ‘kuruciyar.”
Abba ya gyad’a kai yace”kuzama sheda ni malam adamu jafar nabama isha’q saifullahi auren d’iyata zahra ko bayan babu raina.”
Wata zabura isha’q yayi dacewar “Allah abba gaskene kabani zahra,bakuma mafarkin dana saba yi bane.?”
Abba yace”ba mafarki kakeyiba isha’q idan mahaifinka yadawo daga tafiyar dayayi za’a tsaida lokacin biki,kafinnan zakaji sharad’ina daga bakin mahaifiyarka.”
Dr. Ru’kayya baki har kunne take zuba godiya gasu abba da umma.
Takamo zahra wacce takoma gefe tana y’ar ‘kwado tace”zo d’iyata zahra kina sona,zaki zauna wajena?”.
Zahra tayi jimm kafin tace”indai kinsan gidanku akwai bene tozan zauna indinga shan dad’in bene.”
Dr. Ru’kayya tasaki dariya dacewa “kema d’akinko akan bene yake ma.”
Zahra dad’i yac tace”indai da gaske kike tokice kwarakwatsi”,
Umma tace “au zaki fara shirmen naki kenan,”
Dr. Ru’kayya dari take sosai dacewar “zahra koban rantseba bazan maki ‘karya ai.”
Tazuge jakarta tafiddo rafar y’an hamsin-hamsin tami’kama zahra”karbi kisaya sweet kinji d’iyata zahra,aibanzata ‘karama bace dana siyo maki ice-cream.”
Zahra ta kalli kud’in gami da zaro idanu tace”nidai banaso,ki’aje kud’inki bene kawai nakeso kihau dani,indingayin sululu.”
Mamaki yacika dr.ru’kayya aranta tana riyawa ashe duk wautar zahra tanada tarbiyya?
Lallai zasuji dad’in zama da’ita lokacin da ‘kuruciya ta barta.
Babu yanda batayi da zahraba,amma ‘kememe ta’ki karbar kud’in dole ta mayar a jaka.
Tanamasu umma godiya dacewar zata aikoma zahra da sweet tunda ta’ki karbar kudin.
Har zaure umma tarakata itakuwa tari’ke hannun zahra tace taje taraka mota.
Sunfito bakin lungun isha’q yana bud’e mota,idanun zahra yasauka akan jabiru wanda jiya ya ‘kalamata sheri wai taje kwad’ai gidansu ummilolo,
Bata tsaya tabi takan dr.ru’kayya ba,tafincike taruga da gudu tayi wajen jabiru wanda ya d’auko ni’kan gari akai.
Tana zuwa ta hankad’ashi garin ya zube a kwata,sannan ta cukumi rigar jabiru tafara ‘kuli-‘kulin kubura dashi Dr.ru’kayya tana daga nesa ta hango yara harsun fara zagayesu suna wa’kar”bamu rabawa sai dai mu’kara zigawa bugi cikin.”
Subhanallah cewar dr.rukayya wadda tuni tanufi inda zahra take dambacewa,
Dasauri tarike hannu zahra wadda take yayyafa ruwan bala’i,
Jin anri’ke hannunta yasaka batare data waigo ba tace “wlh kowaye yasakeni inba hakaba najuyo saina yima mutum wanka da ruwan kwatar nan,
Dr. Ru’kayya tace”oh oh zahra haka kike ashe.
Zahra tawaigo suka had’a idanu da Dr Rukayya,
Tace”shinefa jiya wai yace naje gidansu ummilolo naci garin kwaki,alhalin karya yakeyi ni aigidanmu anmafi cin dad’i abbanmu kullum da dare yanama siyomana kifi itakuma umma saitayi wanka taje can d’akin abban mu har…..”
Dr. Ru’kayya tace “ya’isa zahra nasan kunacin dad’i ai,amma kiyi hakuri bakiga kin sakashi kukaba.”?
Tace”aima wlh danban shillirashi nayi mashi fad’an y’an chanis ba,dasaikinga nafasa mashi baki.
Rannan ma damukayi fad’a da hinde saida nakusa ‘kwa’kulo mata kunne,itakuma irin fad’an sharuhkan nayi mata.”
Dr. Ru’kayya ta jinjina kai tana kallon isha’q wanda yayi tsuru,baiso mummy tagane halin zahra yanzu ba.
Yasanta dasakama ranta damuwa dayawa,
Tajuya ga zahra dake cema yaron”yaro zan kamaka,zamuje lungun bata kashi saina gurje maka baki da kashin kaji ha’koranka sun zube,banza latas karas kabeji masu kwana abakin titi d’an kabewa mai…”enough pls.”
Dr. Ru’kayya tafad’a ranta a’bace”kewai waccce irin yarinyace,ahaka kikeson inje dake gidan bene kina dakarmun d’iyan ma’kota.tonikam ba’a haka dani,idan bazaki sake haliba lallai zan ‘bata dake sam banason masifa kin ganni nan.”
Zahra tayi tsit,sannan tace”nadena ai.”
Dr. Ru’kayya tayi murmushi dacewa “gud girl”
Tashafi gashin kanta,
Tayima yara y’an kallo tsawa kowa ya kama gabanshi.
Itama mota tashige tana d’agama zahra hannu,lokacin gaf da magrib.
Motarsu na ‘bacewa zahra ta hango su ummilolo da sauran ‘kawayenta,taje suka kashe “tace yara albishirinku?”
Duka suka kasa kunne dacewa”goro fari ‘kal”
Tarage murya sosai”amanatun amana wa’azabatun azaba,idan kuka tona taciku,kun yarda?”
Duk sukayi tsuru,
Tace “inbaku yardaba shikenan.”
Sukace “munyarda zahra,”
Zahra ta tafa hannaye dacewa”yara kuka gayama wani saina dirji baki ehe.”
“amanatun lauratun ‘kwan kiyashi,yara ankusa yimun aure.
Duk suka zaro idanu waje suna kallonta sun sandai ‘karya ba halin zahra bace,don sam tsage gaskiya take komai d’acinta.
Ummilolo tayi karfin halin cewa”mai ‘karya”
Zahra ta’amsa da “d’an wuta abishi da duka har wuta lantarkin babalo da an kyasta sai wuta.”
Duk suka ce”yeeeee dagaskene.
Nanfa aka zauna ana labarin aure,ummilolo tace “tab ashe zahra ke zaki dinga dafa abinci kiyita ci dayawa cikinko yayi ‘kullumeme saimuga zahra ta haihu.”
Sauran yara suka kwashe da dariya,
Zahra ido ya raina fata tace”ai sai in’ki cin abincin,inyita shan ruwa kawai.”
Uwande tad’an fisu wayewa tace”kai wlh ance bacin abinci kesa mutum ya haihu ba.”
Duk suka zaro idanu sukace “to menene”?
Tace inkun yarda amana,
Sukace sun yarda.
Tace”wlh yara idan kuka yarda namiji ya ri’ke maku hannu ya luliya tafin hannunku saikuga ciki yafito ‘katoto,”
Zahra data gama tsorata tace”lalalala aikuwa Allah yasoni ban wasa da maza.”
Daga nan aka rufe cafta,akace atafi satar kifi,wajen y’an kifi.
Haka kuwa akayi xahrace gaba sungama tsara plane na yanda zasu saci kifi,
Suna zuwa saitin wani mai kifi yakasa a faranti yana tsaye gaban kifinshi,
Zahra nazuwa wajen saitin kifin ta yanke jiki tafad’a akan farantin kifi,
Sauran yaran duk sukayi fuskar tausayi”wayyo zahra sannu,”
Mai kifi ma fad’i yake subhanallahi sannu yarinya.
Zahra ta bala riga akan kifi ta dumbuji uku,
Sannan tari’ke ciki”wayyo cikina ummilolo zoki tadani.
Ummilolo itace mai hijabi,dan haka tana zuwa zahra ta ‘kunsa mata kifin a hannu,
Tasaka ariga,
Suka mi’ke suna kakka’be jiki zahra na d’angyashi.
Kamar ance maikifi ya kalli kashin kifinshi yaga anyimashi rani,
Yabisu aguje yana ‘kwala masu kira,
Sukuwa ‘kafa menaci ban bakiba,
Tuni sun sata.
Maikifi saida yayi Allah ya’isa saboda balagaggun kifayen suka d’auke,gashi ranar ba ciniki.
Awani lungu suka ma’kale zahra ta’amshe kifin ta finfincinar masu,tana la’kume sauran.
Uwande ta kalli d’an nata,taga na ummilolo yaninka nata biyu,tace”gaskiya anyi son kai,na ummilolo dayawa namu kad’an”.
Zahra takaima bakin duka tana harararta”sannu mara gode Allah,da kud’in babanku aka saya kifinne,”?
Uwande tayi gum tana mamular kifin da aka bata kai da bindi.
Nan sukayi gaba,
Dai-dai kwalbatin y’an ganda suka hango wata budurwa da saurayi ana tafe ana rangaji suna gogar kafad’un juna,
Ummilolo ce tafara gani ta lakaci zahra,duk suka ware idanuwa suna mamaki.
Zahra tace”aje ajanye gyalen tsinanniya,”
Nanfa kowa tacire takalmi suka ma’kala a jijiyar hannayensu,suka d’age zani sama.
Saida budurwanan tazo saitin majalisar masu ganda,zahra tayi wuf ta fizge gyalen dake kafad’ar budurwar,
Suka auna aguje,budurwar tarasa yazatayi,ta waiga dacewa”honey dallah kabisu ka’amso man gyalena,kaga kayan jikin rabin ‘kirjina duk awaje yake.”
Saurayin yace”tabd’i,sarai nagane yarannan masu gudu kamar barewa,nida rannan gaban idanuwana suka janyema wata budurwa zani,yaseen da rarrafe tashige gida,camon ki kare wajen kawai mutafi asfa gayu d’innan kingane ai ”
Ran budurwar ya ‘baci kawai saita tsugunna ta fashe da kuka,
Me mutane zasuyi banda dariya da ihu…
*Nima nadara,nabi bayan zahra balbali zahra bala’i ta’ba d’aya kaga goma*
KUNA TARE DA MAMAN MEENAT, INSHA ALLAH
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN ‘KWAILA ����♀
BY MAMAN MEENAT
EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN FAROUQ, HYDR)
Muna miqa saqon ta’ axiyan Hamma umar Allah ya jiqan shi yayi mishi rahma yasa mutuwa ta xama hutu a garesh, muma in tamu taxo Allah kasa muyi mutuwar shahada)
Chapter9.
Daga wajen tonon fad’a su zahra basic zame ko’inaba sai gida,saboda lokacin tuni angama sallar magirb,
Da sand’a tale’ka cikin gidan tace “inshigo'”
Umma dake ninke kayan da abba yacire dazu ta harareta dacewar “dawwama anan,har mahadi ya bayya,”
zahra taahigo kanta tsaye,tad’auki buta tafara alwalar magrib umma bata tankataba.
****************
Hadadd’en saurayin dake sanye cikin ‘kananun kayan riga shirt dakuma wandon jeans kirar kamfanin Gucci,akwai kwatsetsen takalmin kafarshi mai shegiyar tsada gordon rush,
Face dinshi manne da space na Prada,watch na hannunshi dolce jikinshi manne da mayen turaren American crew.
Sumar kannan nashi ka rantse na macene saboda gyara da kula kai infarct isha’q ‘karshene akan tafin hannayenshi kawai yakan kashen kud’i masu yawa,ha’koranshi kuwa akoda yaushe suna walwali da daukar idanu saboda time daya ware musamman domin su yakan je wajen wankin hakora lokaci zuwa lokaci.
Hatta da tafin kafar isha’q baya barinta face ya tsaftaceta da mayukan dake tsaftace ‘kafa dasakata taushi.
Yanda yake wana steering kadai abin kallone,duk inda ya gifta mutane kan bishi da idanu musamman motar dayake tu’kawa new modern ce kirar mazda mx-miat abin saiya bada wani styles na daban.
Adai-dai kofar gidan sadiq ya matsa horn mai. gadin yale’ko dakai lokaci guda ya wangale get din yanama isha’q barka da zuwa,
Yafaka mota inda aka tanada don hakan,lokaci guda yazaro wallet d’in dake manne abayan aljihun jeans dinshi,yafiddo 2thousand yamikawa mai gadin,baijira sauraren godiyar damai gadin keyiba yayi gaba abinshi yana wana keys na motarshi.
Dai dai shiga harabar gidan yahad’u da hindu matar sadi’q da tsohon cikinta tana ganinshi tasaki murmushi”yau makuwa kayine isha’q yau agidan,”
Yasaki simple smile nashi kafin yace”yakike ya jiki kuma.”
Tayi gaba tashige falo tana fad’in”banacin mi’ke,”
Bayanta yabi ya nitse cikin manyan kujerun dasuka zagaye falon yadauki remote yana canja channel daga Bollywood zuwa dstv yana searching ‘kwallo,
Hindu tuni tacika gabanshi da kayan sanyi tasani yafi shan hollandia ko malt sune best drinks nashi.
Ya fincine hancin malt na gongoni yana zubawa a glass cup yana tambayar”ina mutumina ne.”?
“yana jinka yanzu zaka ganshi yafito wankane yana shiryawa.”
Isha’q yad’an dara,dacewa kice nazo asa’a dama tad’i zai rakani.”
Idanu hindu ta fiddo waje”to gaskiya bari yafita ba,haka kawai wata budurwar ta kwaceman shi.”
Tafad’a tana turo baki da alamar fushi.
Isha’q dariya sosai yakeyi yanacewa”aigara kishirya don mutumina hudu zaiyi,”
Maganar sadiq ta katseshi”a’a banganeba,wato kai ka’ki aure shine zakazo ka ‘killen dannawa auren ko,”
Yafad’a yana dariya lokaci guda yana zaunawa kan hannun kujerar da isha’q yake kai.
Yami’kama isha’q hannu suka tafa duk suna dariya
Isha’q yace albishir fa nazo inyi maka,
Duk suka bishi da idanu sunason jin abinda zai fada masu,
Yasake kora maltina yana kallon sadiq wanda ya tsareshi da idanu,
“anbani zahra abokina,daga yau nakoma angon zahra ”
Wata zabura hindu tayi”nice to hear isha’q seriously pls dagaske kasamu zahra?”
Isha’q ya saki dariya lokacin da sadiq yakai mashi duka yana fad’in abokina bakada mutunci wlh,wato saida ka rikita masu yarinya da salon wankanka ko?”
Amma duka sati biyu da had’uwa ace har anbaka saikace kaza,koda yake nasanka gwanin iya sarrafa soyayya but natayaka murna sosai abokina aikawai daga wannan wankan muwuce inga amaryar nan.”
Hinduma fad’i take “nayi murna isha’q kaga nasamu ‘kawa,”
Isha’q ya sauke numfashi.
Headache wlh typin din bayamun dad’i kuyi hakuri pls,
Tun d’azu nakeson typing amma kaina yana matsamun dafatan zaku gafarceni.
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Al

See also  Kawa Zuci Hausa Novel Complete

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top