Hausa Novels

Mijin Makociyata Hausa Novel Complete

Mijin Makociyata Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: mijin makociyata
Zaune take a tsakar gidan kan kujera ƴar tsugunne ta zuba uban tagumi da alama tinani take yi. Kamar daga sama taji tsaiwar mota tare da danna horn. Zumbur ta miƙe ta nufi hanyar soron gidan. Ta jikin ɓular dake jikin ƙofar ta leƙa.

Murmushi ne ya suɓuce mata ganin yana ƙoƙarin shiga da motar ciki dan har an buɗe mai get ɗin. A hankali yaja motar ya shige ciki. Gwaram! Aka maida get ɗin aka rufe. Ƙarar rufe ƙofar ne ya maido ta shagalar da tayi da kallon na cikin motar. Jingina tayi jikin ƙofar gami da lumshe idanta tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa da sauri da sauri tini hawaye ya wanke mata fuska.

A hankali taja sanyayayyun ƙafafuwanta ta nufi ciki. Inda ta tashi ta koma ta zauna gami da zuba wani tagumin dan duk da ta ganshi har yanzu bataji abin da take ji a ran nata ya ragu ba. A fili ta furta. “Zuciyata bakiyi min adalci ba da kike ƙoƙarin jefani ga halaka, wayyo ya zanyi ne?.”

 

Mijin Makociyata

Ta faɗa tana dafe kanta da dukkan hannayenta. “ZAHRA“. da sauri ta ɗago jin magana akanta.

“Tinanin me kike yi kika zuba uban tagumi har na shigo inata sallama baki jiba.”

“Bakomai”. Ta faɗa a taƙaice. Ajiye ledar hannunshi yayi ya zauna akan tabarmar dake shimfiɗe a tsakar gidan gami da faɗin. “Kamar ya bakomai?, inba gizo idanuna ke yimin ba kamar hawaye na gani a idonki.”

“Nace maka bakomai amman sai kuma tambayata kake yi, dan Allah ka rabu dani albasa na yanka tin ɗazu shine idona ke ruwa, bakai ka sani yanka albasar da yawa ba wai kai kafi sonta sosai a abinci?”.

 

Mijin Makociyata Hausa Novel Complete

Ajiyar zuciya ya sauke jin abin da tace. Ɗan murmushi ya yi sannan yace. “Zahra kenan, yanzu yankar albasar shi kike yiwa wannan fushin?, Allah ya kyauta ɗauko min abincina inci yunwa nake ji yau ɗin sosai.” ya faɗa yana cire takalmin ƙafarshi.

Ita kuwa baki ta taɓe ta miƙe ta shiga kicin ɗin nasu. Abincin data zuba mai a flast ɗin ta ɗauko gami da ɗaura masa cokali akai tazo ta dangwarar mai a gabanshi. Buɗewa ya yi ya soma ci. Shinkafa ce dafa duka a ciki.

“Ke kinci?”. Ya tambaya.

“Eh”.

 

Mijin Makociyata Hausa Novel Complete

Ta bashi amsa a taƙaice. “Ki ɗauki ledar na ki sha lemon naki ne na siyo miki yau mun ɗsn samu aiki.”

Buɗe ledar tayi gami da taɓe baki ganin lemon ɓawo guda biyar a ciki. “Nina ƙoshi yanzu da safe nasha”.

Shima bai matsa mata ba yaci gaba da cin abincin shi.Haka ya gama cin abincin sannan ya miƙe ya haɗa ruwan wanka da kanshi ya shiga, dan yaga yau ko ruwan ba a kai masa ba. Ko bayan ya fito ma kayanshi ya zira marasa nauyi ya zauna dan suyi fira. Saidai shi kaɗai yake yin firar dan daga e sai a’a take bashi amsa.

Gajiya yayi shima ya yi shiru, ƙarshe ma wayar shi ya ɗauko ya kunna labaran wasanni ya soma ji. Hakan ne ya bata damar cigaba da tinanin daya soma zame mata jiki.

……..
“Salamu alaikum ƙawata nazo muyi fira.” ta faɗa cike da fara’a kan fuskarta. Wata matashiyar macece sanye cikin kyakykyawar shiga. Fitowa Zahra ta yi daga ɗaki tana amsa sallamar. Itama fara’ar tayi da faɗin.

“MUM SUHAIL sannu da zuwa ƙaraso ki zauna mana, yanzu kuwa nake cewa anjima zan shiga gidan naki dan naji DADDYN SUHAIL bai fita ba shiyasa na zauna.”

Ƙarasowa tayi tana faɗin. “Lah! Ai Dad ɗin suhail ya jima da fita yau da wuri ya fita tin asuba, kuma ma shi ai ko yananan zaki iya shiga aikin san bashi da matsala yana nan ma sai musha firar mu.”

Shiru Zahra tayi tana jin ba daɗi a ranta na fitar da yayi ba tare data kuma ganin kyakykyawar fuskar shi ba a cewar ta. Jiki a sanyaye ta zauna tana cigaba da saurara mum suhail dake bata labarin mijin nata.

“Da ace kinsan yadda nake ji a zuciyata in kina min maganar shi da tini kin dena. Nasan bakisan wannan yabo da zuzutashi ɗin da kike kuma yi a gabana ke ƙara jefa zuciyata a cikin halin da take ciki ba.” ta raya a ranta. A fili kuwa cewa tayi. “Ke kam ƙawata ai kinyi dacen miji da ya haɗa komai da mace ke buƙatar mijinta ya kasance yana dashi. Bashi da wata matsala ba kamar mu ba.” ta faɗa tana mele baki.

Girgiza kai Mum suhail tayi a ranta ta raya. “Rashin sani yafi dare duhu, mai ɗaki shiya san inda yake yi masa zuba. A fili kuwa ɗan murmushi tayi sannan tace. “Gaskiya ni kaina ina ƙara godewa Allah a wasu lokutan da irin baiwar da yayi min. Ni kaina nasan na yi dace ta ɓangarori da dama. Amman kema zahra ai kinyi dacen miji na gari, irin mijinki suna wahala sosai a wannan zamanin da muke ciki. Wallahi akwai waɗanda ke jin daman sune k….!”.

“Niɗin?, A hakan?, Wallahi ban yarda ba. Ina cikin wannan ƙuntataccen gidan da wannan wahalalliyar rayuwar kice wai akwai masu neman ya tawa?. Ai ko duk jikina kunnuwa ne bazan yarda da wannan maganar ba.”

Zahra ta yi saurin katse ta da wannan maganar. Ita kuwa cije leɓe tayi sannan tace. “Ai nasan bazaki yarda ba daman, ai yanzu kwanciyar Hankali a aure ita aka fi buƙata bawai ƙaleƙalen duniya ba. Amman yanzu abin da yafi wuya kenan a wannan zamanin. Kedai ki kuma damƙe mijinki dakyau.”

Baki Zahra ta taɓe tace. “Ke daman ai haka zaki ce tinda kinyi dacen miji, amman mu kawai kice muci gaba da maleji. Yanzu ki duba fa ki gani wai yau tuwon shinkafa yake son inyi masa, bayan yasan bamu da shinkafar tuwo, shine wai in ɗebi shinkafar daya siyo gwangwani huɗu inyi mana har safe mu karya dashi. Kuma shinkafar fa rabi ce ya auno shekaran jiya dazai dawo. Amman dan ya wahalar dani wai inyi tuwo da ita to ta yaya ma zan yi? Ga kuɗin cefanen wai ɗari biyu ya za a yi su ishe ni?”.

Ta ƙarasa faɗa tana yarfa hannu cike da takaici. Dafa ta Mum suhail tayi da faɗin. “Kinga ni banga abin tada jijiyar wuya ba akan wannan. Ai anayi har waina ma anayi da ita. Amman ki bari inada shinkafar tuwo muje yanzu in aunar muku sai kiyi masa tuwon.

Fara’a Zahra tayi cike da jin daɗi tace. “Aikuwa nagode sosai Allah yabar zumunci.”

“Bakomai bari inje in ɗebo miki sai ki jiƙata tafi yin kyau.” ta faɗa tana miƙewa. Itama Zahra tashi tayi ta ɗauko hijab ta jira suka fice. Makulli tasa ta kulle ƙofar sannan suka doshi tanƙamemen gidan dake kallon wanda suka fito…………….✍🏻

 

 

 

Name: [MIJIN MAKOCIYATA HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


Leave a Comment

error: Content is protected !!