Littafan Hausa Novels

Mijin Mu Daya Hausa Novel Complete

Mijin Mu Daya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

MIJINMU ‘DAYA

 

*Writing by*

*Zainab Muhammad (Indian Girl)*

 

 

*Wannan labari akwai rikici da ban dariya faɗakarwa nishaɗantarwa*

 

 

BOOK ONE

 

*Page 1-2*

 

“Hafeez ina magana ka mai dani sha-sha-sha”

 

Ko kallonta bai yiba yaci gaba da shirinsa na fita office.

 

Gabansa taje ta shiga tare da kwace cum ɗin dake hannunsa zai taje kan sa.

 

“Wallahi Hafeez baka isa ka wulakantani ba,me kake da shi da har zan dinga magana kana jina ka mai dani mahaukaciya kenan”

 

Tsaki Hafeez ya yi tare da sa hularsa kafin ya dubeta,Yace”Waike Salma dan Allah yau she zaki samu nutsuwane eyye? koda yau she ke ba za’a taɓa zama lafiya dake ba”

 

“Ni kake cewa haka? Shikenan idan ka manta wace Salma zan tuna maka”

Dua The Hated Girl Hausa Novel

Tana gama faɗar haka ta jefa masa cum ɗin ta fice daga ɗakin.

 

Shima bayan ya gama shiryawa ya ɗauki key ɗin motarsa ya fice daga gidan gaba ɗaya cikin motar.

 

*————————*

“Mijina kullum kyau kake ƙarawa”

 

Murmushi ya yi sannan Yace”Kema haka matata”

 

Tace”Amma ai kai ka fini kyau,am wai me yasa ka shirya baka bari na zo na shiryaka ba?”

 

Hannuwanta ya riƙo suka zauna a bakin gado,”Sajida bana so ki wahala ne shi yasa”

 

Sajida ta kalle shi”Amma dai ka san ba wahala a harkar kula da mijina ko”

 

Yace”Hakane”

 

Sajida ta miƙe zata fita.

 

Ya riƙo hannunta,”Ina kuma zaki?”

 

Ta juyo ta kalle shi kafin,Tace”Break fast zan haɗa maka”

 

Zaunar da ita ya yi yana mai kallon fuakarta,”A’a Sajida ki bar shi kinga yan zu ma na kusa makara a wajan aiki”

 

“To kenan wajan aikinka ya fini?”

 

Zaro ido ya yi,”Wane ya faɗa miki haka?”

 

“Ba ga shinan ka faɗa ba”

 

Ta faɗa tana zumɓura baki.

 

“A’a ni ban ce ba amma ki haɗamin sai na tafi da shi idan naje nayi a can”

 

Murmushi tayi ta miƙe ta nufi kitchen,bayan ta haɗa masa har wajan mota ta raka shi tai masa adawo lafiya sannan ta koma shi kuma yaja motarsa ya tafi.

 

 

 

 

*——————–* Tsaye Meena ke gabansa ta cuno baki irin ran nan nata ya ɓaci.

 

“Gaskiya Baby wannan wajan aikin naka suna tauyeni Allah ma ya sani”

 

Ya ɗaga gira,”Amma Meena kin san cewa…”

 

“Mena sani? Ni ba abinda na sani”

 

Meena ta faɗa cikin ɓacin rai.

 

“Haba matata kiyi uzuci mana gobe insha Allah a gida zan kwana”

 

Ya faɗa yana kallon fuskarta.

 

Meena ta ɗan saki fuskarta,sannan Tace”Amma ai da damuwa ace bani da lokaci ni da mijina sai lokaci zuwa lokaci”

 

Nan dai ya shiga rarrashinta har ya samu ta sauko daga dokin fushin data hau,nan suka ɗan taɓa soyayyarsu kafin ya wuce wajan aiki.

 

 

*——————————–*

 

Zaune yake a office ɗin sa,turo ƙofar akai aka shigo wani ɗan matashin saurayine mai kimanin shekaru 35 ya shigo,Hafeez ya ɗaga kai ya kalle shi ya saki murmushi.

 

Waje ya samu ya zauna sannan suka tafa hannu.

 

“Abokina ka ɓuya kwana biyu?”

 

Hafeez Yace”Hmmm! Kabir kenan ba dole na ɓuya ba saboda wallahi matsaloli sun fara yi min yawa”

 

Kabir ya tuntsure da dariya,kafin Yace”Ba dole matsaloli su yi maka yawa ba abokina”

 

“Saboda me ka faɗi haka?”

 

Hafeez ya tambayi Kabir.

 

Kabir ya sake yin dariya sannan,Yace”Saboda ka haɗawa kan ka boom mana”

 

Hafeez ya harari Kabir,”Ban gane na haɗawa kaina boom ba kafa san dalilin komai”

 

Kabir ya gyara zaman sa,”Na sani mana tunda dani akai,amma kasan Allah wallahi idan da nine kai haɗe matsololin zan yi duk abinda zai faru ya faru”

 

Hafeez ya nisa kafin,Yace”Nima da nayi tunanin hakan amma ban aiwatar ba,amma tunda kaima ka tuna min hakan zan yi”

 

Kabir Yace”To yaushe kenan?”

 

Hafeez Yace”Sai an kwana biyu gaskiya sannan na samu mafita”

 

“Shikenan hakan ya yi”

 

Kabir ya faɗa sannan suka ci gaba da hirar su.

 

*——————————————-* Wayarta ta ɗauka ta danna wata number ta tafi kira,rings 2 aka ɗaga.

 

“Hello Anty Sa’a kina gidane?”

 

Daga can ɓangaran Anty Sa’a,Tace”Eh ina nan zuwa zaki?”

 

“Eh Anty gani nan”

 

Salma ta faɗa tare da kashe wayar.

 

Wanka ta shiga toilet tayi sannan ta fito ta shirya ta ɗauki mukullin motarta ta fice.

 

Tana isa gidan Anty Sa’a ta faka motarta a paking space ta shiga,a falo ta sameta tana zaune tana kallo.

 

Waje ta samu ta zauna,ba tare data gaishe da Antyn ba ta fara magana.

 

“Anty wallahi na gaji da auran nan na Hafeez dama kece kan gaba wajan auran”

 

Anty Tace”Kin gaji da zaman aure kamar ya? Wai Salma dama ban sani ba a she ke raguwace?”

 

Salma da idanunta suka fara kawo hawaye,Tace”Anty mene yake sawa ayi aure? Ba soyayya bace?”

 

Anty Tace”Hakane”

 

“To Anty ni ba auran soyayya mukai ba amma duk da haka nai haƙuri na zauna,sannan kuma ace babu farin cikin aure da zan samu”

 

Salma ta sake faɗar haka.

 

“Ke nifa ban gane abinda kike nufi ba? Kiyi min magana yadda zan gane”

 

Salma ta gyaɗa kai sannan tai ƙasa da kanta,”Anty Hafeez baya da lokacin da zai tsaya ya bani wanda zan ce munyi na auratayya,kullum cikin cewa aiki aiki,Anty ko bana da abinda namiji zai sone a tare dani?!

 

Sai kuma ta fashe da kuka.

 

Ta sowa Anty tayi daga kujerar da take ta dawo wadda Salma take.

 

Dafa bayanta Anty tayi kafin cikin rarrashi,Tace”Ƙanwata kiyi haƙuri kinji amma dama duk wani farin ciki da mace take samu a gidan auranta bayan auratayyar shimfiɗa yake bi”

 

“To Anty dan namiji ya baka abinci suttura da wajan kwana ai bashine ba,kana son ka samu ƙarshen farin ciki”

 

Salma ta faɗa lokacin da kanta yake jikin kafaɗar Anty.

 

Anty Tace”Hakane”

 

Nan ta shiga kwantar mata da hankali da kuma bata shawarwari daya kamata tabi.

 

 

*WACECE SALMA DA HAFEEZ?*

 

Salma ƴace a wajan Alhji Usman da Hajiya Hawwa’u,asalinsu ƴan asalin garin maidugurine fulanine kyawawa.

 

Salma da Hafeez ƴan uwane da mahaifin Salma da mahaifin Hafeez uwa ɗaya uba ɗaya suke hakama ta wajan iyayen su mata.

 

Allah ya yiwa wannan ahali ƙarfin arziƙi domin suna da kuɗi sosai.

 

Alhaji Usman da Hajiya Hawwa’u sun haifi ƴaƴa 4 Anty Sa’a itace babbar ƴar su sannan Yaya Munsur da Yaya Jabir sannan Fauza sai Salma itace ƙarama,sun taso cikin so da ƙauna ga gata.

 

Shi kuma Hafeez ɗane a wajan Alhaji Sulaiman da Hajiya Saude su kuma Allah bai basu haihuwa sosai ba ƴaƴa 2 kawai suka haifa Hafeez shima sai da suka daɗe shekara da shekaru sannan suka haife shi,sai da Hafeez ya kusa gama university sannan aka haifi Shukra wato ƙanwarsa daga kanta kuma basu sake haihuwa ba.

 

Hafeez da ƙanwarsa sun taso cikin gata da sabgarta.

 

Ɓangaran Salma kuwa bayan ta gama secondry school ɗinta ne Anty Sa’a ta fara ƙoƙarin gaɗa auran su da Hafeez,kuma dama shi Hafeez ɗin yana tsokanar Salma tun tana yarinya yana matata.

 

Anty Sa’a sai da ta haɗa auran Salma da Hafeez duk da ita Salman ba son sa take ba,amma tasan ba macen da zata sami Hafeez tace bata so a matsayin miji domin Hafeez namijin gaskene jarumi kuma mai tattare da baiwa irin ta gwarazan jarumai.

 

Lokacin da akai auran Hafeez yana bawa Salma kulawa amma daga ƙarshe sai ya canza bai ma cika zama a gidan ba wataran ma baya kwana,gashi Salma bata haihuwa ba ko ɓari bata taɓa yi ba.

 

 

*Cigaban labari*

 

 

Anty Sa’a ta dubi Salma Tace”Yanzu ki tashi ki tafi sannan kuma karki bari su Mama su san wani abu kinji,domin na sanki da faɗa”

 

Salma ta amsa mata da “To”

 

Anty ta haɗa mata kayan mata iri-iri masu kyau ta bata.

 

Salma tana komawa gida ta fara amfami da magungunan da Anty ta bata.

 

 

 

 

*———————————————*

 

“Farhan kiyi kizo ki fita da kayan nan domin idan baki fita ba ba zanu sami abincin da zamu ci ba,kuma gashinan naga ma hadarine a garin”

 

Ummi dake zaune akan tabarma a tsakar gida tana yanka awara ta faɗa.

 

Wow na faɗa lokacin da naga wata kyakykyawar yarinya ta fito daga wani ɗaki,daka ganta kasan shuwace usul kyawawa duk da hijab ne a jikinta hakan bai hana gashinta bayyana ba ta baya.

 

Inda Ummi take a zaune ta iso ta tsugguna sannan cikin sassanyar murya nai daɗi,Tace”Ummi shiryawa nayi”

 

Ummi Tace”To ai saiki fita da kayan ko,gama shinan har an fara zuwa nema”

 

Farhan ta amsa da “To” sannan ta fara fitar da kayan suyar,bayan ta gama fitarwa ta ɗauki awarar da doya ta fita tare da neman albarkar kasuwa.

[17/02, 11:32 am] +234 903 522 9088: *MIJIN MU ƊAYA*

 

*Daga writer*

*Zainab Muhammad*

*Indian Girl*

 

 

*Wannan labari akwai rikici da ban dariya faɗakarwa nishaɗantarwa*

 

 

BOOK ONE

 

*3-4*

 

Bata daɗe da fita ba ta fara ciniki kan kace me har ta siyar ta kwashe kayanta ta shiga gida da farin ciki.

zaro ido da,Cewa”Kifi Farhan muda muke neman na abinci ina mu ina cin kifi”

 

Farhan ta langwaɓar da kai,”Amma Ummi ai mun fi wata nawa bamu ci ba”

 

Ummi ta gyaɗa kai,”Hakane amma kuma ai ki bari mu fara gamawa da wannan rayuwar idan aka samu mai yawa ba sai a ci ba”

 

Farhan ta nike rai ɓace ta ɗauki buta ta shiga banɗaki.

 

Ummi tai murmushi.

 

Kafin Farhan ta fito daga banɗakin Ummi har ta bayar a siyo masu abin da za su dafa,shinkafa ce da mai da barkono.

 

Farhan bayan ta fito daga banɗakin ko kula Ummi ba taiba ta shige ɗaki tai kwanciyarta.

 

Bayan an kawo Ummi ta tashi ta shiga kici niyar dafawa,bayan ta gama ta zubawa kowa.

 

“Farhan! Farhan!! Farhan!!!”

 

Ummi ta shiga kwala mata kira,Farhan ta fito daga ɗaki tana amsawa rai a haɗe.

 

Tana zuwa Tace”Gani”

 

Ummi ta nuna mata kwanan abinci rufe da murfi,Farhan ta sun kuya ta ɗauka tare da buɗewa washe baki tayi.

 

“Kai amna wallahi Ummi kin min ba zata a she kin siyu?”

 

Ummi tai murmushi da,Cewa”Ke kaɗai na siyawa saboda Farhan ai ba zan iya hanaki cin abinda ranki ke so ba,Farhan karfa ki manta dake ake neman kuɗin”

 

Farhan itama tai murmushi,”Amma Ummi nagode sosai ina ƙaunarki”

 

Ummi itama Tace”Nima ina ƙaunarki Farhan ɗina”

 

Farhan ta samu waje ta zauna sannan ta buɗe abincin,kafin Tace”To yanzu Ummi ki raba ki lauki rabi ki ban rabi”

 

“Wallahi Farhan ba zan ci ba saboda ke kaɗai na siyawa”

 

Ummi ta faɗa tare da miƙewa da kwanan abinci a hannunta.

 

Farhan kamar za tai kuka,Tace”Kai Ummi har da rantsuwa? Amma kin san fa ba zan iya ci ba tare da kin ci ba”

 

Ummi Tace”Hakane,amma yau na yafe”

 

Ba yadda Farhan ta iya haka taci abinta.

 

 

*WACECE FARHAN*

 

Malam Salisu da Binta a salin su shuwane kyawawa na ƙarshen-ƙarshe,Malam Salisu yaga Binta ne sakamakon unguwarsu ɗaya hakan yasa suka haɗu har su kai aure.

 

Malam Salisu malamine babba kuma masani a fanni daban-daban ta fannin addini,kuma ba wasu masu arziƙi bane masu rufin asirine.

 

Sun dawo garin kano da zama sakamakon wani hari na boko haram da aka kai garin hakan yasa kowa yai takansa,a sannan Malam Salisu da Binta ba su haihu ba hakan yasa suka tsira.

 

Lokacin da suka zo garin gidan mai unguwa suka sauka a sannan ne ma cikin dake jikin Binta ya bayyana,sun yi farin ciki duk da ba a cikin daɗi suke ba.

 

Wannan yasa gidan mai unguwa da a halinsa suka zaman sune a halinsu Malam Salisu da Binta.

 

Sun daɗe a gidan mai unguwa kafin daga baya mai unguwa ya saka gidauniyar tallafi,bayan an samu aka siya musu gida aka mallaka musu takardun,a sannan kuma Binta ta haifi ɗanta namiji kyakykyawa aka sa masa suna Abubakar.

 

Sun ci gaba da rayuwarsu Malam yana ƴan buga bugarsa har tafiye-tafiye yake yi yana nema suna ci kuma alhmdlh,a haka su kaita haifar ƴaƴa har 5 bayan Abubakar (Faisal),Sadiya, Rabi’a,Fateema (Farhan) sannnan Hafeez da Hafeeza ƴan biyu.

 

Yan anyi bikin Sadiya da Rabi’a shi kuma Abubakar yana dai kan neman kuɗi tukunnan.

 

Farhan tana da shekara 11 Malam ya ɓata sakamakon ya taf wani ƙauye saro kai kaya daga sannan ba su sake ganinsa ba,han kalinsu ya tashi anyi neman har an gaji hakan yasa suka dangana,amma Ummi ita tana jin zafin abin sosai.

 

Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi wataran su ci wataran su haƙura duk da gidan Malam ana taimaka musu sosai dake suna ƙaunar su,Ummi ta fara ƴan buga-buga kuma a haka su Farhan suke zuwa makaranta har ta shiga secondry,bayan kammala secondry ɗin nata sai karatun ya tsaya suka shiga neman abinda asiri zai rufu.

 

Farhan yanzu shekararta 16 Hafeez da Hafeeza 12.

 

Wannan kenan.

 

 

*Cigaban labari*

 

 

Zaune yake a cikin mota ya zabga uban tagumi yana tunani.

 

“To yanzu mene mafitar matsalarsa ga shi dare ya yi?”

 

Ya kewa kan sa tambayar.

 

Wayarsa dake gefe ta shiga ruri,a firgice ya ɗauka tare da duba wanda ya kira,

 

*wife Sajida*

 

Dagawa ya yi kafin yace wani abu,yaji tana magana.

 

“Wai mijina har yanzu baku tashi a office ɗin bane?”

 

Ya sauke ajiyar zuciya,kafin ya samu abin da zai ce.

 

“Hmmm! ke dai bari Sajida wallahi kin ga kwana ma za muyi aiki kuma koda mun kwana ɗin ma sai wajan dare zamu tashi”

 

Sajida dake zaune a falonta kan kujera ta zaro ido,”Cabb gaskiya amma wannan aiki naku da wuya a ce mutum baya da lokacin hutawa”

 

“Wallahi Sajida nima abin yana damuna jiya ba su barmu mun samu hutuwa yauma haka”

 

Ya faɗa yana murmshi.

 

Sajida Tace”Hakane kam gaskiya,Allah ya tashe mu lafiya”

 

Ya amsa da “Ameen” sannan suka kashe waya.

 

*Wacece Sajida*

 

Sajida marainiyace iyayenta sun rasu hakan yasa take zaune hannun kakarta kuma dama su biyu iyayensu suka haifa da ita da yayarta amma ita bama gari ɗaya suke ba ita tana katsina tana aure.

 

*Wannan kenan*

 

*Cigaban labari*

 

*—————-*

 

 

Safa da marwa take tayi mintuna kaɗan ta kalli agogo tai kwafa,gajiya tayi da zagaye falon da take yi ta koma ta zauna a kan kujera tana duba wayarta ko kira zai shigo.

 

Tafi awa ɗaya a haka tun 8:00pm na dare har 11:00 shiru hakan yasa tai fushi sosai,har ta tashi zata shiga ɗaki taji ana knock na ƙofa dake ta kulle da sakata ta ciki.

 

Komawa tayi ta nufi ƙofar bata tambayi cewa wane ba ta buɗe saboda ta san ko wane.

 

Bayan ta buɗe ko ta kansa bata biba ta juya zata shige ɗaki,ya yu saurin riƙota ta faɗa jikinsa nan suka shiga kallon kallo,kafin kuma can Meena ta shiga ƙoƴarin kwace kanta…

 

 

*# Mores Comment*

*#Mores Typing*

Add Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!