9/7/20, 10:36 AM – Messages to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI
Shimfida
Malam Auwalu dan asalin kauyen Badume ne dake jiyar Kano. Manomi ne kuma dan kasuwa a lokaci daya da Allah ya azurta da rufin asiri. Kafin rasuwar su shida matar shi Balaraba da tsiran su duka shekara biyu ne, dan shine ya rigata rasuwa. Allah ya azurta su da yara shidda.
Da yake daga baya sun dawo cikin garin Kano da zama, hakan yasa duka yaran samun wadataccen ilimin addini dana boko. Dukkan su mazan harkar kasuwanci ta kayan abinci sukeyi da mahaifinsu ya rasu yabar su a kai, banda Aminu da son boko ya shiga ranshi sosai, dan bayan ya kammala Degree din shi ta farko a fannin siye da siyarwa, yana gama bautar kasa ya samu aiki a wani kamfani da yake Kaduna, da yayi aure ma can yaci gaba da zama. Duk da aikin shi bai hana shi cigaba da karatu ba da ya nemi izini suka kuma bashi dama da alkawarin cewar zaici gaba da aiki tare dasu dan mutum ne mai hazaka.
Lokacin daya kammala degree din shi ta biyu ya kuma sake cigaba dan yana son karatun shi yakai matakin da zai zama farfesa, ga aure daya kara rungumowa. Sai yayi dabarar bude gidajen gona har guda biyu anan garin Kaduna din. Inda yake kiwon kaji, zabi, talotalo harda kifin tarwada da a turance akafi sani da catfish. Allah ya saka mishi nasibi da yake mutum ne mai wadata iyali. Cikin wasu yan shekaru kusan duk wasu masu gasa kaji a Kaduna a wajen shi suke siye. Gidan shi daya dauki shekaru yana ginawa suka koma da yake a unguwar Barnawa nan wajen station road a garin Kaduna. Shima Allah ya azurta shi da samun yara.
Auwalu Musa – Balaraba Tukur
-Yaran su
•Mannir •Rabi’u •Humaira •Aminu •Khalil •Salim
Aminu Auwal Musa (Baba)
-Matan shi
Rashida AbdulMannir (Mama)
-Yaran ta
•Muhsin •Huzaifa •Salamatu •Halima •Khadija •Junior •Amna
Karima Sani (Anty)
-Yaran ta
•Zaid •Jafar •Hindatu •Khalil •Asma’u
Kawayen Hindatu Al’amin
•Zainab (Biebee) •Aina’u (Dimples) •Yasmin •Hajarah •Hawwa
*
Malam Abbas bafullatani ne daga shiyar jahar Katsina, kauyen Marake. Auren da ake kira na gata shi akayiwa Abba da matar shi Amina, dan lokaci bata shige shekara sha shidda ba, shikuma yana da ashirin da uku. Haka suke rayuwar su babu yabo babu fallasa har suka sami yara biyar inda a haihuwar ta karashen, Allah yaiwa Amina rasuwa. Haka yaran sukaci gaba da tashi cikin maraicin uwa kafin su rasa mahaifi suna yawo tsakanin dangi.
Cikin hakan ne Abubakar ya shiga Kaduna ko zai sami sana’a inda ya fara aikin katakaye har Allah ya hadashi da matar shi da sadakar yalla ce da tayo gudun hijira saboda hatsaniyar da ake a yankinsu na Sudan sukayo najeriya, garin Kaduna, ita tayo Kaduna tana aikatau a wani gida, ko hausar kirki bataji lokacin. Da yake bashi da dangin da suka damu balle suyi magana akan rashin tabbaci na asalin Mariya, basu sami wata matsala ba sukayi aure ya kama haya anan unguwar Tudun Wada, sukayi zaman su yana cigaba da aikin katakayen shi ciki suke duk wata hidimar su.
Mal. Abbas – Mama Amina
-Yaran su
•Abdallah •Ahmad •Abubakar •Maryam •Rabi’atu
Abubakar Abbas (Appa) – Mariya (Anna)
-Yaran su
•Hamza •Abid •Faruk •Jamila (Auta)
Abokan Hamza Abu Abbas
•Usman Ayoob (Fodio) •Muhammad Kamal (Arafat) •AbdulHafiz Ashir •Abdallah Nuhu
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: 1.
Wani irin shiru ne mai cike da firgici da tsakiyar dare kadai kan samar, badan ta duba agogo ba, amman tana da tabbacin karfe biyun dare zata iya yi, wata walkiya akayi da ta sata sake rakubewa jikin bangon wajen saboda akwai hadarin da yake nuna alamar saukar ruwa ko wani lokaci, da babu taimakon hijabi haka zata kasance daga ita sai rigar bacci, kafin wata irin gigitacciyar tsawa ta sata dafe cikinta da yaron da yake kwance a ciki sai da ya motsa mata da alama tsoratar da tayi ta tabashi shima.
Runtsa idanuwanta tayi wasu irin hawaye masu ciwo na tsiyayo mata, batasan inda zata nufa ba a cikin tsohon daren nan. Tsayuwa ta sake gyarawa tana dafe da cikinta har lokacin, hannunta na rike da bakar leda da take a kulle da alamun wani abu a ciki. Tafi mintina talatin a tsaye bakin kofar gidanta, gidan auren ta bayan ta saurari kashedin da Hamza yaima maigadi da fadin
“Wallahi idan ka bude mata kofar gidan nan, ba aikin ka kadai zai zo karshe ba, sai nasa an rufe mun kai, ka fadi dalilin da yasa ka bude ma wata gidana”
Mamaki ne karshen abinda tayi, tasan Hamza kamar yunwar cikinta, sai dai batayi zaton rashin mutuncin shi yayi kamari haka ba, idan bai tausaya mata ba, zai tausaya ma halin da take ciki, ina zata nufa cikin tsohon daren a unguwar su da ko da rana saika yini bakaji motsin mutum ba, motoci ma sai jefi-jefi ta baki da akanyi a gidajen, ko kuma su mazauna unguwar. Dakyar ta iya jan jiki tana takawa ta rakube inda take tsaye a yanzun, ko takalma babu a Kafafuwan ta. Ajiyar zuciya ta sauke na kukan da takeyi har numfashin ta na tsaitsayawa, dai-dai lokacin da ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya. Idan Allah ya taimaka duk gidajen unguwar ana kunna generator, a haske take fayau, ba kasafai suke gane ko akwai wutar lantarki ko babu ba.
Idanuwanta Hindu ta sake runtsewa, wannan karin ajiyar zuciyar da ta sauke tafi alaka da sanyin ruwan da yake ratsa sassan jikinta, musamman da yake hade da iska mai karfin gaske. Takowa tayi ta dawo jikin gate din tana bubbugawa
“Baba Maigadi dan Allah ka taimakamun, ka duba cikin da yake jikina…in samu wajen rakubewa idan asuba tayi ko ruwan ya tsagaita sai in tafi”
Hindu ta karasa maganar cikin matukar galabaita da rauni, tana saka hannunta dake rike da yar bakar ledar ta share hawayen da ruwa yake wankewa, jikinta na amsawa cikin kyarma da iskar da ta sake kadawa, sake bubbuga kofar take da karfi, jin alamar motsi yasata dakatawa, dattijon maigadin ne ya bude kofar yana saurin ziro kai kafin ta samu damar shiga
“Kiyi hakuri, kinsan halin maigidan, wallahi aikin nan shine rufin asiri na…”
Wasu hawaye Hindu taji sun tsiraro mata, aure mai rufin asiri, aure kuma mai tonon asiri, kaddara na zabar inda zata jefaka batare da ta baka wani zabi ba. Yau itace a tsaye tana rokar inda zata rakube, ita Hindatu Al’amin, gaskiyar hausawa, duniya makaranta, duniya kuma juyi-juyi. Yau ta birkice da ita, asalima a shekara daya duniyar ta fara wasan cikar shekara da rayuwar ta.
“Dan Allah ka taimakamun, bansan inda zanyi a daren nan ba, ban sani ba”
Cewar Hindu, numfashi Baba Maigadi ya sauke, tunda ya koma ciki yarinyar tai mishi tsaye a rai, amman yana tsoron abinda zaiyi sanadin aikin shi
“Sai dai ki shigo na minti kadan, in ara miki wayata inda wanda zaki kira”
Cikin rawar murya mai alamar kuka ta amsa da fadin
“Eh ka aramun”
Dan ta manta da wata abu waya, balle tayi tunanin tata da Hamza bai barta da natsuwar dauka ba, mutumin da ko takalma bai bari ta saka ba, ballantana kuma wata waya. Cikin gidan ta shiga da sauri, tana karasawa yar barandar dake gaban dakin baba maigadi ta tsaya tana tsiyayyar ruwa dan tayi sharkaf, kasa tayi dakyar tana dafe cikinta, wani irin sanyi ne yake ratsata har kwanya.
“Ungo…”
Baba Maigadi ya fadi yana mika mata karamar wayar shi da take daure da kyauro, hannunta na kyarma ta karba, tana kallon shi da yar lemar da yake rike da ita. Wayar ta duba, taji duniya, inka ganta batare da ka latsa ba, zaka iya rantsewa da bata aiki, gwangwan ce. Batama gwada lambar Mama ba, dan tasan kashe wayarta take da daddare, Baba ne zata kira idan ya daga, tunda shikuma ba daga bakuwar lamba yake ba, a duniyar ta lambobin mutum hudu ta haddace, ta Baba, ta Mama, tata, sai kuma ta Hamza da a yanzun babu amfanin da hakan zai mata. Lambar baba ta saka ta kira tana karawa a kunnenta, ringing din da wayar tayi alamar ta shiga na saka ajiyar zuciya kwace mata, kafin wasu hawayen su zubo, wannan karin kuka ne mai sautin alamun zafi da qunar zuciya yake zubo mata.
Har wayar ta yanke bai daga ba, sake kira tayi, sai da ta jera kira biyar tana yankewa ba’a daga ba, zuwa lokacin zuciyarta ta kara karaya, amman tasan hakura da kiran wayar na iya ja Baba Maigadi yace ta tashi ta fita tunda ba’a daga ba, kuma ruwan da ake ko alamar tsagaitawa baiyi ba, ballantana tasa ran zai dauke, inda take zaune ma feshin ruwa na samunta, ga sanyin tiles din ya kara mata sanyin da takeji, sai kyarma jikinta yake. Zazzabi ma takeji kamar ya saukar mata. Lambar ta cigaba da kira harta bace lissafi, cike da tausayawa Baba Maigadi yace mata
“Ki shiga daga ciki…”
Ganin yanda take kara takurewa da alamar sanyin da takeji, a ran shi yake tunanin yanda ba zai sake jin haushi idan mata sukai wa jinsin maza kudin goro na cewar basu da mutunci, basu da tausayi ba. Randa yaji wata ta kira abinda da namiji yayi da akuyanci, kalmar ta kwana biyu tsaye a makoshin shi, dan baiga abinda yai zafi da zata danganta jinsin shi da dabba ba, sai yanzun da kalmar ce ta farko da tazo mishi akan fassara abinda Hamza yaiwa Hindu din batare daya duba tsohon cikin da take tare dashi ba, balle yayi tunanin hadarin dake cikin fitar ko da namiji ne a tsohon daren nan, ko babu hadari, balle kuma mace.
Hindu bata jira ya sake mata magana ta biyu ba, ta mike dakyar ta tura kofar dakin tana shiga, da kafet cike da dakin, irin jan nan, sai tarkacen da batabi takan su ba, dan harda katifa irin ta yan makaranta, daga gefe bakin kofa ta zauna tana dan turo kofar, kar Hamza ya fito ya fatattake su daga ita har Baba Maigadi. Dan kadan ne cikin abinda zai iya aikatawa, ita shaida ce. Lambar Baba taci gaba da gwadawa tana karanto duk wata addu’a da tazo ranta, lokaci zuwa lokaci take saka gefen hijabinta da yake a jike tana share hawayenta da sunki daina zuba.
**
Bacci suke su duka biyun mai nauyin gaske, da yake babu wuta, tasowar hadari da iska yasa an dauke, ga wani irin zafi da ya dira. Sun jima suna juyi, suna dan taba hira kafin bacci ya dauke su wajen sha biyu. Cikin bacci Alh. Aminu yakejin ringing din wayar daya lalubo yana dubawa da bugawar zuciya, ganin bakuwar lamba yadan nutsar da zuciyar shi
“Waye wannan…”
Ya fadi, kiran yana yankewa yaga missed calls da lambar har guda ashirin da daya
“Subhanallah”
Ya furta yana mikewa zaune gabaki daya, dan ya tabbatar ba lafiya ba, baccin na barin idanuwan shi, salatin da yayi shiya tashi matar shi Rashida da yaran gidan duka suke kira da Mama daga bacci, duhun dakin na hanata ganin shi sosai, hasken wayar shi ya tabbatar mata da a zaune yake
“Alhaji lafiya dai ko?”
Kai Alh Aminu ya girgiza ma Mama yana fadin
“Wallahi ban sani ba, wata lamba ce an kirani har sau ashirin da daya fa, bansan irin baccin da muke ba haka yau”
Alh Aminu ya karashe yana kokarin sake mayar da kiran da yaki shiga, da alamar matsalar network. Ita kanta Mama tashi tayi zuciyarta na wata irin dokawa.
‘Inalillahi wa ina ilaihi raji’un’
Take fadi tana maimaitawa cikin ranta, bata son furta abinda zuciyarta take saka mata na camfin da hausawa suke cewar idan wani mummunan abu zai sameka sai baccin asara mai nauyi ya danne ka, dan duk yanda kaso casa’in cikin dari yake kasancewa gaskiya, yau zata kasance da kaso goman. Dan haka bayan Inalillahi jaddada ma kanta kalaman kwarin gwiwa takeyi
‘In shaa Allah babu abinda ya faru’
Tana kallon Alh Aminu da shima hankalin shi a tashe yake, sai da gabanta ya sake mummunar faduwa da taji yace
“Hello…. Waye?”
Alamar kiran ya shiga har an daga
“Hello…”
Ya sake fadi dan bayajin abinda ake fadi, network din na rawa, amman da alamar macece, kashewa yayi ya sake kira, zufa na tsatssafo mishi, a duniya Allah ya dora mishi son ‘ya’yan shi, duk albarkar yawan su daya samu, idan yana da iko ba zai bari ko kuda yahau su ba, balle ya taba mishi su, dan sune jigon rayuwar shi, farin cikin ranshi. Akan ce tsakanin da da uwa sai Allah, kaunar su ba abu bace da za’a fassara kan mizanin kalamai, zai karyata hakan, dan kaunar da yake ma yaran shi har iyayen su mata na jinjina mata lokutta da dama.
‘Allah ka tsaremun yarana, Allah karka jarabceni ta hanyar su, Allah ka dubeni’
Alh Aminu yake fadi yana kara maimaitawa, lokacin da yaji an daga kiran, cikin wani irin raunin murya da shessheka aka ce
“Baa… Baba… Baba na”
Kafafuwan shi Alh Aminu ya sauko daga kan gadon a gigice, badan yagane muryarta ba, saboda ta fito daga kasan makoshinta a galabaice, ga network din bashida kyau, sai dan ita kadai take ce mishi ‘Baba na’ duk a cikin yaran kamar ita kadai ya haifa. Har magana sauran sukan yi akan hakan, maganar Hindu a ko da yaushe itace
‘Baba na ne, kaunar da take tsakanin mu daban da irin ta ku, nafi ku kaunar shi’
Yakan murmusa ko tuna hakan yayi, da gaske ne a cikin ‘ya’ya akwai wanda zaka fi jin kaunar shi, Hindu ta kasance itace wannan ‘yar, har kasan zuciyarshi shi yake jinta, ko digon hawaye bayason gani akan fuskarta, ko da na farin cikine
“Hindatu?”
Ya furta da shakku tattare da muryar shi yana sake fadin
“Hindu? Hindun Baban ta…”
Mama kuwa kallon shi takeyi cikin kaguwa dajin me yake faruwa, amman taga hankalin shi ya tattara wajen sauraron Hindun, fatanta dai Allah yasa komai lafiya. A wahalce yaji muryarta ta sake fita
“Baaba ya koreni, Hamza ya kore ni. Yaki hakura gari ya waye…”
Wani abu Alh Aminu yaji ya tsirga mishi daga dan yatsan kafarshi zuwa tsakiyar kan shi, kafin ya dunkule yana dawowa ya tattaru a kirjin shi hadi da danne zuciyar shi ya takurata
“Ya kore ki?”
Ya bukata yanajin dacin da baisan ta inda ya taso mishi ba a makoshi, zai rantse yaga kan da ta daga mishi, gunjin kukan da take na sauka kunnune shi cikin rashin dadin saurare
“Cikin daren nan? Cikin dare zai koreki? Kina ina yanzun?”
Yanda take maida numfashi na sashi hasashen kalar kukan da take da yake tafasa zuciyar shi, dakyar tana numfarfashi ta amsa shi da
“Dakin Ba…Baba Maigadi, shiya aramun waya… Baba kazo karya fito ya koreni…”
Zuwa yanzun Alh Aminu ya mike tsaye
“Ki tsaya nan, kina jina? Gani nan zuwa, ki tsaya nan karki fito ko ina kinji Hindu… Yanzun zan zo in shaa Allah”
Kukan da take yasan ba zata iya magana ba, haka ya jira har sai da yaji tace
“To…”
Can kasa tukunna ya kashe wayar
“Me ya faru Alhaji?”
Mama ta bukata, ko kallonta baiyi ba balle ya amsa, dan ranshi in yai dubu a bace yake, ga hankalin shi da yake a tashe. Wajen durowar kaya ya karasa ya bude, doguwar riga jallabiya ya dauka ya dora kan wandon shaddar da ya kwanta dashi sai singileti, yanayi yana kiran wayar Muhsin da taki shiga, dan haka ya kira ta Huzaifa, bugu na biyu ya daga ko sallama baiyi ba balle tunanin gaisuwa yana fadin
“Baba lafiya?”
Hankalin shi a tashe, kai Alh Aminu ya girgiza, da wani irin zafin zuciya yace
“Ka sameni gidan Hindu, ka gwada kiramun Muhsin shima”
Duk da Huzaifa yaji shi ta dayan bangaren da wani sabon tashin hankali da yake bayyane a muryar shi yace
“Me ya samun Hindun? Baba me ya sameta? Ka fadamun ko zan samu natsuwar tuki”
Numfashi mai nauyi Alh Aminu yaja yana fitarwa
“Mijin ta ya koreta cikin dare nan, cikin daren nan Huzaifa…”
Ya karasa maganar yana kashewa, da fitilar wayar yayi amfani ya lalubi mukullin motar shi, da idanuwa Mama take ta binshi dan ita din bamai yawan magana bace ba, sai da taga zai fice ne tukunna ta bi bayan shi da fadin
“Kayi tuqi a hankali dai, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”
Tasan halin shi, shisa bata damu ba, komawa tayi ta kwanta tana jin yanda ruwan yake kara sauka har lokacin, da tunanin barkatai a ranta, ciki harda yanda batasan gaibuba, amman ta hasoso karewar auren Hindun a haka.
*
Tana sauke wayar daga kunnenta ta mike ta fito daga dakin Baba Maigadi da yana ganin ta ya taso, wayar ta mika mishi
“Baba nagode”
Ta furta cikin rawar murya tana fitowa daga barandar dan ta nufi kofa
“Ina zaki je?”
Sai da ta share hawayenta, tana ta kyarmar sanyi har lokacin ga wani ruwan da ya soma dukanta
“Za’a zo a daukeni yanzun, kar ya fito in maka sanadin aikin ka”
Kai kawai Baba Maigadi ya iya jinjinawa cikin tausaya mata, shiya bude ma Hindu kofar ta fita daga gidan, jikin bango ta samu ta rakube, ruwan na cigaba da dukanta, tanajin Baba Maigadi bai rufe gidan ba har lokacin, da alama yana tsaye bakin kofa, hankalin shi sam yaki kwanciya duk da tace mishi za’a zo daukarta din. Ba zatace ga lokacin da ta dauka a tsaye a wajen ba, amman tabbas bata da lafiya, rashin lafiyar da bata da alaka da Hamza, zazzabine mai zafi yai mata rumfa, har cikin idanuwanta take jin shi da take budewa tana rufewa, ga dan cikinta da yaketa motsi kamar yana son fitowa, wannan karin har bayanta sai da taji ya amsa, tako dafe cikin tana kiran
“Yaa Rabbi…”
Wata irin azaba na ziyartar kwanyarta, kafin hasken mota ya dirkako ta, daga idanuwa tayi tana jin sabon kuka ya kwace mata da taga motar Baba ce, yanayin parking ko kashe motar baiyi ba ya fito daga ciki yana sauke idanuwan shi kan Hindu da take ta takurewa duk idan iska ta kada, tana hango shi ta fara takowa, yana ganin yanda bata da takalmi, gata rungume da tsohon ciki. Wani abu Baba yaji yana karyewa a cikin zuciyar shi, ga dacin da yai mishi tsaye a makoshi, yama kasa takawa ya karasa inda Hindu take, yayi tsaye ne kamar an dasa shi. A wahalce ta karaso wajen shi tana wani irin kuka kamar zata shide
“Baa… Baaba na”
Ta fadi muryarta na sarqewa, hannu Baba ya mika ya kama na Hindu da baya tallafe da cikinta, yanajin sanyin daya dauka kamar kankara, shi kan shi da baifi minti biyu da shiga ruwan ba yayi sharkaf, ledar dake hannun nata yake bi da kallo
“Ham… Hamza ya bani”
Ta fadi dakyar, karbar ledar Baba yayi ya saka cikin aljihun jallabiyar shi yana taimaka ma Hindu da takejin bayanta kamar zai rabe gida biyu, numfashi ma a wahalce take jan shi tana fitarwa, Baba ji yake tamkar zai kama da wuta saboda bacin rai. Mota ya bude yana taimaka ma Hindu ta shiga, dai-dai lokacin da wata motar ta tunkaro wajen, tsaye yayi bayan ya mayar da kofar ya rufe, Muhsin ne da Huzaifa suka fito suna karasowa inda Baba yake
“Ina Hindun?”
Huzaifa ya bukata dan inba ganinta yayi ba hankalin shi ba zai kwanta ba, murfin motar Baba ya bude mishi yaganta a zaune ta jike sharkaf, numfashi Huzaifa ya sauke cike da nutsuwar da ta saukar mishi
“In dai na isa da ku bana so kayanta su kwana a gidan marar mutuncin nan”
Baba ya fada yana saka Huzaifa kallon shi cike da tashin hankali
“Baba kayi hakuri dan Allah, ka isa Wallahi har kayi yawa ma, amman yanzun dare ne, gashi ana ruwa, ba lallai a samu masu motar da zasu fito ba”
Huzaifa ya karasa maganar da sigar lallashi, yana saka Muhsin dorawa da
“Kayi hakuri Baba, gobe tunda sassafe, kaga yanzun ya kamata muje gida ta sake kayan nan kar zazzabi ya kamata”
Kai Baba ya jinjina wani abu ya tokare mishi makoshi, bai ba Hamza auren yar shi dan yagaji da ita ba, duk da burin kowanne iyaye shine suga yaransu a gidajen mazajen su, amman idan babu kwanciyar hankali da nutsuwa gara ya dinga ganin yar shi cikin gida kullum, zai fi mishi wannan bakin ciki. Dakyar ya iya bude motar ya shiga, dan shima duk ya jike, sai da ya zauna tukunna ya kalli su Huzaifa yace
“Ku wuce gida kawai, goben idan an samu motar da zata kwashe kayan ku kirani”
Wannan karin su duka suka jinjina ma Baba kai, suna tsaye har saida sukaga ya bace musu, tukunna suka koma mota, gida Huzaifa ya fara sauke Muhsin, tukunna ya wuce nashi gidan shima.
*
Wani irin sanyi take ji yana ratsata har cikin kwakwalwar ta yana hana mata wani tunanin daya wuce na son rufa da katon bargo ko zataji dumi. Da suka karasa gidama, Baba ne ya bude mata bayan motar, amman tayi galabaitar da ta sakko kafafuwanta wajen motar, amman ta kasa raba jikinta da kujerar.
“Hindu?”
Baba ya kira ganin yanda take fitar da numfashi a wahalce yana dorawa da
“Ko mu wuce asibiti?”
Kai Hindu ta girgiza mishi, kwanciya kawai take so taji tayi, ba zata iya zaman motar ba har su sake nufar asibiti. Dakyar, hannunta daya dafe da cikinta, dayan kuma ta rike kofar motar ta raba jikinta da kujerar tana mikewa tsaye hadi da runtsa idanuwanta kafin ta sake budesu cike da gajiyar da take ji. Baba na tsaye yana kallonta zuciyar shi cike da tausayin yar tashi, a gefe daya kuma fal da bacin rai, ita ta fara yin gaba tana karasawa wajen kofar tasa hannu ta murza tana turawa ta saka kafafuwanta cikin falon. Tana karasawa kan kujera ta zauna, Baba kuma ya wuce cikin daki inda yabar Mama, ba bacci takeyi ba tun fitar shi, tana kwance ne tana tunane-tunane, ta kunna fitilar and wayarta tunda babu wuta dan ana ruwa har lokacin
Tana jin sallamar shi ta mike tana fadin
“Kun dawo? Ina Hindatun?”
Hanyar waje Baba ya nuna mata, babu shiri ta sakko da kafafuwanta. Tana daukar wayar ta wuce falon ya rufa mata baya, kallo daya taiwa Hindu taga yanda take a galabaice, tana karasawa taba fuskarta tayi zuwa wuyanta tana jin yanda zazzabi ya rufeta ruf
“Alhaji da asibiti aka wuce da ita ai, kaji zazzabin da yake jikinta?”
Mama ta fadi kafin ya amsa tana dorawa da
“Tashi muje ki cire wannan jikakkun kayan”
Saida Hindu ta sa bayan hannunta tana goge hawayen da taji ya zubo mata, tukunna ta kama hannun Mama data riko kafadarta dan taimaka mata, ta mike, dakin Mama din suka nufa tana bata kayanta, ta sake a wajen, dan wata kunyar Mama ce karshen abinda takeji. Sake kama hannunta Mama tayi suka fito daga dakin zuwa dakin baki da yake gyare tsaf, har sauri Hindu take karawa dan so kawai takeyi tajita a kwance, har wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke data kwanta, Mama ta rufa warware katon bargon da yake dakin tana rufa mata. Gefen gadon ta zauna tana kallon Baba daya biyosu ya kasa samun nutsuwa shima tace
“Kaje ka sake kayan jikinka kaima ka kwanta, zan zauna da ita zuwa safe in Allah ya kaimu”
Dan jim yayi kamar zai musa, tukunna ya jinjina kai yana wucewa ya fita daga dakin, duk da shine karshen abinda yake so yayi. Yafi so ya samu waje ya zauna sai yaga Hindun ta warware tukunna. Da tunanin ko da Hamza ne namijin daya rage a duniya Hindu tagama auren shi har abada Baba yake sake kaya. Shi da an sami mota ma cikin daren za’a kwashe kayan, tunda shi bashida mutunci.
Mama kuwa da taga ya fita, jikin Hindu ta sake tabawa taji da zazzabi har lokacin, tana kallon duk da idanuwan Hindu din a rufe suke, hawaye ne kawai yake zubar mata yana sauka ta gefen karan hancinta zuwa kan pillow din da take kwance
“Kiyi hakuri ki daina kukan nan Hindu, kinga bake kadai bace, karki jama kanki wani ciwon kinji ko?”
Kai kawai Hindu ta daga mata badan tana da wani iko akan zubar hawayen nata ba, su suke fitowa da kansu saboda kwanciyar da tayi da dumin bargon da ya rufe jikinta ruf yaba kwakwalwar ta damar tunanin asalin halin da take ciki. Ba tayi mamaki dan Hamza ya koreta tsakiyar dare da tsohon ciki, ana kuma ruwan sama ba, tana da tabbacin yana can kwance yana baccin shi a nutse, dan babu wani abu da yake shiga tsakanin shi da baccin shi. Yakan ce
‘Koma meye zai iya jira, bacci na ba zai jirani ba’
Sake runtsa idanuwanta tayi gam, har radadi suke mata da tasan kukan da tasha ne a daren, kukan da ba yanzun ta fara yin shi akan Hamza ba, bata dai san ranar karshe da zata daina ba, da gaske takeyi lokacin da tace mishi
‘Na manta ranar karshe da hawayena suka zuba akan wani abu da ba kai ba’
Sai takejin kamar tun tana yarinya rabon da wani abu ya sakata kuka sai bayan ta hadu da Hamza, daga ranar ta fara kukan da ya kawota inda take yanzun
“Ko dai sai munje asibiti a daren nan?”
Mama ta tambaya cike da damuwa, dan ita kam bataso taga mai ciki a wani hali. Tunda tasan shi kanshi daukar nauyin cikin idan aka barka dashi batare da an kara maka wani ciwon ba ya isheka. Cikin disashiyar murya tace
“A’a Mama, bacci nake so inyi”
Bawai dan tana jin baccin ba, kai Mama ta jinjina
“In kawo miki ruwa”
Kai kawai Hindu ta iya girgiza mata da alamar a’a. Kyaleta Mama tayi a zuciyarta tana mata fatan samun sauki, ta hau kan gadon tana jan mayafi ta rufe kafafuwanta sannan ta kwanta, dan kanta harya fara ciwo, gara ko baccin kasa da awa biyune ta samu kafin asuba, fitilar wayar ta kashe tana lumshe idanuwanta.
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: 7
Shekara daya bayan gama diploma dinta, ta sake samun gurbin karatu na HND ana Polytechnic din ta Kaduna, duk da Baba yaso ta gwada Direct Entry ana KASU, amman sam makarantar ta gama fita daga ranta, haka kawai take son cigaba dayin Poly din saboda tana sakata jin wani kusanci na daban da Hamza. Ita kanta zuwa yanzun tasan inda a kasar wajene idan Hamza zai kai kararta tsaf za’a kamata da laifin bibiya, wato stalking a turance, a shekara daya da wani abu duk wani hoto da Hamza zai saka akan idanuwanta, tana liking ta kuma yi mishi comment a shafin shi na Instagram, dan ta tabbatar Hamza ko dan wasan film ne ko kwallon kafa, yanda take bibiyar shi yaci ace ya kula da ita, ko da sau dayane ya tanka.
Amman ko inda take Hamza bai taba kallo ba, har haushin kanta take ji wasu lokuttan idan ta gama yi mishi dogon sharhi musamman akan gine-ginen da yakan dora. Ranar da taga ya dawo Najeriya ji tayi kamar an mata albishir da kujerar Hajji, kamar Hamzan zai kulata saboda suna jaha daya, kuma taga dan Kaduna ne daga yanayin wajajen cin abincin da suke hotuna a ciki shida abokan shi. Amman ko like bai taba dannawa akan comments dinta ba. Ta kuma kasa daina yi saboda yanda yake bala’in burgeta.
Zuwa yanzun Samari takeyi kala-kala, ta kasa tsayar da hankalinta akan guda daya, dukkan su saita sami abinda ta kushe a jikin su, duk nasiha da Anty take zaunar da ita tana mata, ta kunnen dama take shiga ta fita ta haggu, daman ita kadai ta rage a gidan da take mata magana akan maganar tsayar da Saurayi daya, Baba kam da Anty ta gwada yi mishi zancen, ca yayi
‘Ki kyale yarinyar nan dan Allah, duka Hindatun nawa take da kikabi kika dami kanki akan ta? Ba karatu takeyi bane wai? Ko kin manta shi auren nan lokaci yake dashi?’
Daga ranar kuwa Anty bata kara daga mishi zancen ba, amman yana damunta matuka, tana kuma addu’a akai. Ita kanta Hindu abin na damunta, yanda har yanzun ta kasa tsayar da hankalinta akan saurayi daya, ta kasa samun wanda zai kwanta mata. Ba sosai take hawa manhajar WhatsApp ba, balle kuma facebook da take dauka sai gidadawa suke yinshi yanzun. Dimples ta koya mata zaman Twitter ba kadan ba. Da yake ita Dimples can tafi ganewa, ko kace ka mata magana a whatsapp bata amsa ba zata ce maka
‘Baka dubani a Twitter bane ba’
Itama Hindun tunda tagane kan Twitter tasan cewa nan din wata duniya ce ta daban, ta hada duk wasu manyan gayu da kake tunani, babu kuma karya kamar yanda akanyi a Instagram. Akwai manyan yaran da suke burgeta sosai a Twitter, yaran attajirai ne daga yanayin shigarsu da motocin da zaka gansu a ciki, duk da kyawun su bai kai mata inda take so ba. Takan shiga wasu lokuttan a dama da ita, kusan tafi Dimples shige-shige a Twitter, ita Dimples idan ma bata sanka a gaske ba, ba zata taba sakar maka fuska har kuyi wata hira ba, ko kabita ma, ba zata amsa gayyatarka ba.
Kalar hotunan da Hindu take sakawa a Twitter yasa take da tarin Mabiya, duk da shigace ta mutunci a jikinta, duk da abaya, sosai ake mata kallan Babbar yarinya. Watan nan daya kama aure akeyi kaca-kaca a twitter, sai kaga matan sunce daga mazan sun tura musu DM wato sako ta inda su kadai zasu iya gani, su kuma suka amsa shikenan soyayya ta ƙullu tsakanin su, yanzun gashi har dunyi aure. Kuma sai taga mazan sun haɗu, ga kuɗi suna dashi, inta duba shafin su sai ta samu basu da wasu mabiyan kirki kuma basa saka hoto ko ɗaya. Abin na matuƙar burge Hindu, ita duk wanda suke mata DM tarkace ne.
Haka kawai saita fara ji a jikinta kamar itama mijinta zai fito daga Twitter ne,tunda taɗan rage burin nata, tanajin kamar ko gajerene indai yana da kuɗi sosai wataƙila ta haƙura taga abinda Allah zaiyi. Lokaci ɗaya ta fara ganin Musbey da suke following ɗin juna yana kwaso mata shafin wani Jalil idan yayi retweet ɗin posting ɗin Jalil ɗin da yake siyar da kayan sawa na maza wato kaftan. Daga yanayin kayan zaka fahimci irin kuɗin da yake dasu, duba shi tayi taga mabiyan shi kaɗan, ko data duba hotunan shi duk tallar kayane da suka ji sirfanin hannu da alamu suka nuna zaiyi tsada matuƙa. Saita tsinci kanta da following ɗin shi kafin ta sauka daga kan Twitter ɗin.
*
“Usztaz kasan dai ya kamata kayi aure ko?”
Abokin sa Adam yace mishi.
“Wai meyasa kuke ce mishi Usztaz ne? Bafa ustazu bane, rashin kaya ne kawai ke ɗawainiya dashi.”
Aliyu yai maganar yana takaicin Ustaz din da ake kiran Jalil dashi, saboda ko kusa bai hada hanya da Ustazai ba. Jalil wanda aka fi sani da Ustaz baice komai ba, maganar mutane bata damunsa. Ba yau bane rana ta farko da mutane da abokan sa suke mishi maganar aure. Amma ta ina zai iya aure tunda ba shida sana’ar kirki. A shekaru arba’in da biyu sana’ar aikin hannu yakeyi. Yana saƙa design a riguna. Shima shagon ba nashi bane. Na wani wan mahaifinsa ne wanda ya gaji da ganin sa yana zaman banza.
“Haka kurum kuyita ce mishi Ustazu kamar abin arziki, daga namiji yana saka manyan kaya shikenan ya zama na kirki?”
Aliyu ya cigaba da sababi. Da Adam da Aliyu yan biyu ne yan shekaru ashirin da bakwai. Sabbin zuwa ne a shagon kuma jininsu ya haɗu dana Jalil, saidai idan ka fita kace mishi Jalil babu wanda zai sani. Anfi saninsa da Ustaz wanda ba’a san inda ya ɗauko laƙabin ba. Shi Jalil yana san gayu amman bashida hanyar da zaiyi, haka ya haƙura abinshi. Tunda yake jikinsa bai taɓa marhaba da English wears ba, toh saidai na haihuwa. Tun tashin shi ya saba saka kwabɗa kwabɗan yadi ko mai kwabo kwabo. Duka kayansa sunyi mishi girma. Gashi bala’in siriri baida faɗin kirji. Yana yanayi da ɗan shekara talatin da biyu yasa yake yarintar sa babu kama hannun yaro. Dan Jalil irin mutanen nan ne da sun girma basu san sun girma ba. Gashi idan yana tafiya saboda girman kayan shi da rashin kiba sai yayi maka kamada tuta.
Cima zaune ne na bugun jarida. Yan kuɗaɗen sa dayake samu baya komai dasu sai siyan data domin yaga kyawawan mata sannan kuma idan an dace ya samu wanda zata aure shi a yadda yake. Yanada NCE wanda yayi a FCE Zaria inda ya karanta English and Literature. Wannan ɗan turancin ne yake ma yan mata bagu dashi. A manhajan Twitter yaji labarin cewa akwai wasu manyan yaran attajirai, tun lokacin ma ta Web yake shiga, bashi da wayar da take sauke application, sai dai yana cikin mutanen da ake ma laqabi da Low-key a Twitter. Baya shiga duk wani rikici ko drama da za’ayi, kawai dai idan abu yayi mishi, sai yayi liking ko retweet, mabiyan shima basu da yawa, amman akwai wanda ake ganin girman su a Twitter da suke bin shi, sosai Jalil ya iya kama girman shi a Twitter ba kamar a fili ba.
Kasancewar Ustaz Jalil a Twitter yasa shi kara wayewa ta fannin da baka tunani, duk da rashin gayun na nan, kafin Twitter yaji yanda ake fadin fararen kaya girma ne, daga lokacin ko dan yadi zai siya sai ya siyi fari, naya saka wani kaya face fari, kuma idan aka ce farin kaya bawai ana nufin farin da mutane suka sani ba. Duk sun koɗe sunyi dariya ta wajen wuyan. Gashi yanada wani farin half cover wanda ya koma kalar madara. Ya saba idan manyan mutane sun kawo ɗinki saiya ɗauki hoton kayan ya wallafa, sannan yace shagon sa ne yanzu yaran ciki sukayi mishi aikin.
*
Zata ce kusan sati biyu da tayi following ɗin Jalil amman baiyi follow back ba, hakan ya sakata tunani barkatai, sai taita ganin kamar ita ce take bin arziƙi shikuma yana ƙinta. Hindu bata taɓa mashi magana ba, tunda dai duk matan da takeji dun sami mijin aure a Twitter duk mazan ne suke fara musu magana, amma tana kallon duk wani rubutun da zaiyi, ya kuma iya turanci ba kaɗan ba. Yanayin sa yana burgeta. Babu ruwan shi. Saidai ya watsa hotunan da yaran shagon sa suka yi kamar yanda yake cewa ya tafi.
Akwai wani kwarjini dayake mata na rashin dalili, bawai ta taɓa ganinsa bane tunda yana cikin mutanen da ko kadan basa saka hoton su,amma kuma yana bala’in birgeta. Wata Isha datayi aure kwanaki tace mijinta a twitter suka haɗu kuma baida followers sosai. Watau attajiran ba’a sansu ba. Gashi kuma mijin Isha ya haɗu cikakken namiji, Allah bai rage shi da komai ba ta fannin halitta. Hindu ta kasa gane dalilin daya sa take ganin cewa Jalil yana cikin wannan sashen. Kuma idan wannan manyan kayan dayake wallafawa daga shagon sa ne. Toh ai kakanta ya yanke saƙa. Dan kullum da kalar wanda zai saka.
Yau haka kawai ta tsinci kanta da yin liking ɗin hoton kayan da ya saka. Ko wayar bats ajiye ba taga yayi following ɗinta, wani irin murmushi taji ya ƙwace mata.
Shi kuma Jalil ana shi ɓangaren dan ƙarfin hali su Adam suna mashi magana ko jinsu baya yi dan sam sai yau ya kula da Hindu tayi following ɗin shi,satin ba’a sami wani aikin kirki ba, yanata lallaɓa data din shi karta ƙare da wuri,shisa baiyi wasu shige-dhigen rashin dalili ba sai yanzun da yaga tayi liking hotunan daya saka, nan take yai follow back yana shiga profile ɗinta. Bin hotunan Hindu yayi yana kallo, ta bala’in birge shi. Bawai aurenta yakeso yayi ba, kawai dai ko gaisuwa su rinƙa yi ana mutunci. Tunda shi kanshi yasan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane.
Sallama yayi mata, abin kuma yayi mugun bata mamaki. Kamar yasan yanzu tayi tunanin ko ita tayi mishi sallamar, Har ga Allah nan take Hindu ta fara hasaso yanda bikinta da Jalil zai kasan ce, tasan shine zai zamo uban yaranta. Batayi jan aji ba ta amsa.
“Wohoho… Maraba garsarshe!”
Jalil yace da ƙarfin tsiya. Yana saka Aliyu ɗagowa cikin ƙunar rai
“Ya dai Ustaz meye haka muna aiki kana mana ihu, kamar wani ƙaramin yaro”
Dama cikin tagwayen yafi zafin kai. Kuma bayason yanda Ustaz bashida kamun kai
Kallonsa Ustaz yayi yana dariya, saiya kara masa wayan a fuska
“Kalli abinda ya faru, nayi kamu jama’a”
Yace sannan ya miƙe ya soma taka rawa. Irin rawar nan da Ibro keyi da kafa ɗaya bayan yaci ɗammara. Haka yayita ji yana zufa, Aliyu haushi ya gama ƙume shi
“Ai ba nan gizo ke saƙar ba, yanzu me wannan yarinyar zatayi dakai? Jibe ka fa. Rigar ka kwara ɗaya, gashi duk ta koɗe bata kama omo”
Aliyu yai maganar, Adam da sauran yan shagon na bushewa da dariya.
Bai kula suba, ya koma gefe ya soma chatting da Hindu gadan gadan. Sai ya zamana a duka satin babu abinda Jalil yake banda hira da Hindu da ta saki jiki ta biye mishi, duk yanda Dimples tayi mata kashedi tabi a hankali, sai ta bagarar da zancen Dimples din na cewar a low-key Twitter tabbas akwai attajiran masu kudi, akwai kuma attajiran amman tantiran yan duniya masu bin mata, kuma zai iya yiwuwa akwai yan yankar kai ma, tunda yanar gizo yanzun ta zama abinda ta zama. Sai Hindu ta alakanta maganar Dimples da rashin son mutanen ta, in da mutane zasu biye mata sam zata wuce su wuce kamar ba daga jinsi daya suka fito ba.
Ko kadan bata da yarda, zaku shekara tare da ita kafin ta sakar maka fuska, kullum girarta a sama take, bata shiga harkar kowa, ba kuma zataki kowa karya shiga harkarta ba, shisa sai ta daina mata zancen Jalil din, duk da tana so ta tambayi Dimples ko zata iya cema Jalil ya turo mata da hoton shi kar a karayin ta Elias, amman kuma nan ba 2go bane ba, Twitter ne, bata taba ganin wata ta fito tace ta hadu da gurgu ba, kuma tana ganin suna ma juna bangajiyar ziyara da kuma godiya a tsakanin su. Ga ajin Jalil din ya burgeta, har lokacin ko lambar wayarta bai karba ba.
Wata safiyar asabar da ta kasance bata da aikin makaranta sosai, ta kuma tambayi Anty Dimples zata zo suje gidan Maman Amrah Yayar Dimples din batajin dadi zata dubo ta, sanin kusancin da ke tsakanin Hindu da Dimples shisa Anty ta amince da kashedin kar Hindun ta kai dare. Ranar kuma tayi dai-dai da lokacin da Jalil ya bukaci yana son ganinta su gaisa. Nan ta shaida mishi cewa bata gida yau zasu fita ita da Kawarta. Ya tambayi unguwar tace mishi wajen Lagos Street ne, kafin wani lokaci Jalil ya amsata da cewa shima zaiyi ta area din sai su hadu ‘Briefly’ su gaisa, yanda yai amfani da kalmar a gayance ya kara burge Hindu.
Sosai taji daɗin wannan maganar, a cikin rana ɗaya tayi babban kamu. Watau Jalil shiru shirun twitter zai ziyarce ta. Kwalliya ta fesa sosai, data karbi jikin ta, tasan cewa harga Allah tayi azkar da kyau. Kuma dama Allah yana tare da mai hakuri. Wulakanci da Hamza yake ta mata ne, da kuma kalar tarkacen Samarin da tayi yau Allah zai wanke mata duk wani bakin ciki da ta kwasa. Tunani kala kala ya rinƙa rikito mata. Ita bata san gajeren namiji kamar an kifa kwando. Fata takeyi kada Jalil ya zamto gajere. Sai kuma ta tuna cewa yanzu kai ya soma wayewa, tsawonka shine aljihun ka. Idan dai yanada kuɗin sa kawai zata aure shine ne amma bazata taɓa barin ƙawayenta suga mijinta ba.
Zata ce mashi bata san snatching, kafin ayi mata dariya ace taci baya. Haka tayita tunani kala kala tana kokarin ta kawo kamannin Jalil wanda take kyautata zaton shine zai zama mijinta. Da wannan tunanin Dimples ta sameta, suka yi ma Anty sallama suka fice, a hanya ne take ba Dimples labari
“Ba zaki rufama kanki asiri da mazan Twitter ba ko Hindu? Bakiji me nace miki ba”
Kai Hindu take girgiza ma Dimples
“Wallahi ina ji a jikina Dee”
Ta kirata kamar yanda take ce mata tana dorawa da
“Ki yarda dani, zuciyata ba ko yaushe take mun karya ba, ina da good feelings akan Jalil. Ina jin kamar shine zai zama mijin da zan aura”
Wani irin kallo Dimples takeyi mata, su duka sunsan halinta, ba akan komai take magana ba, amman idan taji bata yarda da abuba to karshe sai abin nan ya zamana baizo musu da dadi ba
“Hmmm…”
Kawai ta furta suna cigaba da takawa zuwa titi inda zasu hau adai-daita sahu da zata kaisu gidan Maman Amrah
*
“Nifa inada abin yi, ku ce ma Kawu na fita”
Jalil yace tareda miƙewa. Su Adam kallonsa sukayi sai suka cigaba da hirarrakin su. Gida ya koma yana cire kayan jikinsa, wankewa yayi sosai da omo dan yayi haske clean ya saka. Daman ya siyo bula domin ya ƙara ma dan yadin da yake matukar ji dashi armashi. Dayake yadin mai laushi ne kuma ana iska nanda nan ya bushe. Aikam saiya goge da kyau yana mishi karin guga na mutunci.
Takalmin sa wanda ya ɓare ya soma dariya ya ɗauko, yana saka gam da baya rabuwa dashi dan yan liqe-liqe, nan ya gyara tareda gogewa fes. Yanayin Hindu bai mashi kamar wadda zatayi wulakanci ba. Kuma ai ba santa yace yanayi ba, idan sun haɗu bayan yau zai soma binta da kalamai wanda zai sa ta soshi. Bai taɓa budurwan kirki ba, ya dai saba cema yan talla yana sansu saboda su rinka bar masa kaya kyauta. Musamman masu doughnut ko gyada. Su kuma idan suka gane halinsa su zage shi tas suyi gaba.
Karfe huɗu Hindu ta bashi damar ya ziyarce ta, inda ta faɗi yanada ɗan nisa da inda yake. Maimakon ya hau mashin sai Ustaz yace bari yaje da ƙafa tunda akwai sauran lokaci, yan kudin Machine din yayi amfani dasu ya kara siyan data. Inda yake gani babu nisa saida ya kwashi fiye da awa ɗaya yana takawa. Ga rana ana barbaɗawa ranar kamar zai soye. Duk zufa yakeyi ta ko’ina hammatar rigarshi duk tayi dabbara-dabbara da wajen wuyan sa musamman tunda kayan akwai bula.
Ya isa inda ta faɗa mishi sai nishi yakeyi zufa tana karyo mishi. Sai yayi mata text ta twitter ta fito gashi. Hindu kuwa har nuna ma Dimples tayi tana wani murmushi dan taga kalar ajin da Jalil yake dashi, mikewa Dimples tayi batare da tace komai ba ta dauki mayafinta, daman Kimono ta dora akan riga da wandon da yake jikinta, sukace ma Maman Amrah zasu ga wani a waje, yanzun zasu dawo.
Jalil yana cikin jira ta fito sai gari ya juye hadari ya haɗu, anan iska ta ɗauke mishi hular da ta Kawu ce ta aro ta kuwa cilla cikin unguwa. Haka yayita bi yana
“Wait! Wait!!”
shi kaɗai kamar mahaukaci. Dan ya san halin Kawu tunda ya hana shi taba mishi kaya, Hular bata tsaya ba saida ta shiga cikin wata muguwar kwata. Haka ya saka hannu ya tsamo ta. Nan yayi dama dama da hannunsa. Zare ido yayi ya soma dube-dube. Sam baisan nan ne kofar gidan Maman Amrah ba, dama Dimples ta hana Hindu bashi asalin address din tace mata kada ta bashi asalin address ɗin, koda baiyi masu ba zasu iya yi mishi fuska kamar basu bane.
Nan su Hindu suka fito suka ganshi tsaye kamar mahaukaci sai zufa yakeyi ga kaya duk datti, balle kuma kayan sunyi mugun koɗewa. Bai gane Hindu ba tunda hotuna kan bambamta. Balle ita da tafi kyau a fili fiye da hoto. Saiya ƙarasa wajensu yayinda suka fito domin su taimaka mashi da ruwa ya dauraye hannun shi harma da bakar leda ya samu ya saka hular kar Hindu ta fito tagan shi
Yana isa wajen su, bayan yayi sallama yana ajiyar zuciya saboda gudun dayayi. Dimples na watsa mishi wani irin kallo daya saka shi shan jinin jikin shi, a daburce ya soma magana
“Dan Allah kuyi haƙuri, ruwa zaku taimaka mun dashi in wanke hulata data fada kwata…”
Ran Hindu yayi mugun ɓaci saboda bata ƙaunar rainin wayau, kar mutumin nan ya ja mata bad luck, batason wani akasi da zai faru kafin taga Jalil, Dimples ce ta riƙe mata hannu domin su saurare shi, bata son mutane, amman kuma hakan baisa tana da wulakanci ba, musamman taga zai girmesu nesa ba kusa ba, ganin haka yasa Jalil murmusawa cikin yanayin da duk idan yayi a mudubi yakan ga yayi matukar kyau
“Dan Allah ruwan zaku taimaka mun sai yar bakar leda in saka hulata…”
Yai maganar yana dorawa da
“Nazo wajen wata abin begena ne Hindu shine hulata ta faɗa kwata”
Da yake Allah yayi mishi surutu na rashin dalili
“Me?”
Dimples ta tambaya tana son taji ko kunnuwanta yaji ‘Hindun’ da Jalil ya furta. Yana dan fadada murmushin shi ya sake maimaitawa
“Hindu, ko kinsanta ne?
Wannan karin Hindu da take jin jiri na shirin kwasarta ce tace
“Jalil?”
Muryarta cike da matukar shakku, dago idanuwa Jalil yayi yana karema Hindu kallo, sai yanzun da ta kira sunan shi tukunna ya ganeta, yanda take kallon shi ya tabbatar mishi da kiris take jira ta kwada mishi mari
“Kan uban can”
Cewar Hindu tana dorawa da wata ashariya da bata tabayin irinta ba, kafin ta sake wani motsi Jalil ya ari takalman kare ya yanki Hanya da wani irin gudu cikin yadin shi da yake kwasar iska yana hura shi kamar zai tashi sama. Cikinta Dimples ta rike saboda da dariyar da take tattaruwa kafin ta fito fili da wani irin yanayi da yasa Hindu taji idanuwanta sun cika taf da hawaye.
‘Wannan wacce irin rayuwa ce’
Ta tambayi kanta, me yasa na rana daya abinda yake karbar mutane ita bazai karbeta ba? Me yasa duk wani abin arziqi da idan wasu matan sukayi dangane da samun Mijin aure na gari ita idan ta kwatanta sai yazo mata a baibai? Wacce irin rashin sa’a ce take bibiyar rayuwarta har haka?
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: 4
Zatai karya idan tace gabanta baya faduwa. Asali tunda suka fito daga gida wata zufa take tsatssafo mata a saman goshi har zuwa tafikan hannunta, da sukaje gidan su Ummi sam kasa samun sukuni tayi. Biebee na kula da ita, batai mata magana ba saboda ta fada mata daga farko bataji ba, sau daya take gaya maka gaskiya ta koma gefe ta saka maka ido, yanda zataji dadin cewa ta fada maka baka dauka ba idan komai ya kwabe. Bata sake shiga tashin hankali ba sai da Elias ya kira wayarta, jikinta har bari yake
“Bie muje…Anty ta fara kirana”
Hindu ta furta muryarta na rawa, kai Biebee ta jinjina mata, Ummi ce tace
“Wai tun yanzun zaku tafi? Kai dan Allah…. Hindu ba Anty tasan nan kuka zo ba”
Murmushin karfin hali Hindu tayi
“Zata fitane zan dora girki, yamma nayi shisa”
Kai Ummi ta jinjina tana fadin
“Bari in dauko Hijab dina in rakaku”
Wannan karin Biebee ce ta girgiza mata kai
“Dan wahalar da kai? Mu biyune fa, kiyi zamanki dan Allah”
Duk da haka saida Ummi ta rakasu har bakin kofar gida, sannan sukayi sallama, da sauri Hindu ta daga kiran Elias daya shigo a karo na ukku
“Haba Hinduna, inata kira sai an mun sarautar za’a daga?”
Dan murmushi Hindu tayi
“Kana ta ina?”
Sai da yayi jim tukunna yace
“Bakin wani saloon Umtaz…”
Kai Hindu ta jinjina dan ta gane wajen
“Gani nan karasowa to”
Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta batare data jira amsar shi ba, ta kalli Biebee
“Wai yana wajen Saloon din Umtaz”
Biebee ta jita, bata dai ce komai bane, suka dan kara sauri kowa da abinda yake sakawa cikin zuciyar shi. Suna karasawa kwanar da zata kaisu titin da Elias yace yana tsaye Biebee ta riko hannun Hindu
“Zuwa zakiyi, ki kira shi kice yana cikin wacce motar, ki fara hango shi tukunna”
Shawarar Biebeen ta zauna mata, wayarta ta danna tana kiran Elias da ya daga a bugun farko
“Ban ganka bafa… Kana cikin wacce mota?”
Hindu ta fadi kafin ya numfasa
“Cikin wata jar golf”
Elias ya amsata ta dayan bangaren
“Golf?”
Hindu ta maimaita cike da mamaki, daga ita har Biebee suna zira kansu suka hanga wajen saloon din, akwai motoci jefe a wajen, amman jar golf din da suke hangowa tayi kama da motar da ake dibar jogon kaji ana cin kasuwar kauyuka da ita, ga wata irin kura da ba zasuce ta kasa bace ko qoqewar da fentin motar yayi bane ba, kallon juna sukayi, Biebee na kokarin ganin bata kwashe da dariya ba, a hankali tace
“Kice bari mu duba”
Hakan Hindu tace tana sauke wayar da wani irin yanayi da yake fassara ‘akwai matsala’ bayyane a fuskarta, dariya Biebee takeyi harda rike ciki
“Wanne irin iskanci ne wannan Bie? Ya zanyi ni yanzun… Jar golf yace, ni kuma waccen motar kadai ce ma golf a duk motocin titin nan, anya shine? Ko dai wasa yake mun? Aike kinga motocin gidan su”
Kai Biebee take girgiza mata
“A gidan ubanwa naga motocin gidan nasu?”
Tsaki Hindu taja
“Ban nuna miki hotunan shi ba?”
Wani kallo Biebee tayi mata
“Da kika nuna mun hotunan bance miki ni ban yarda dashi ba?”
Numfashi Hindu taja ranta a bala’in bace
“Ni yanzun ya zanyi? Juyawa zamuyi wallahi…”
Kai Biebee take girgiza mata
“Zai yiwu wasa yake miki, ki sake kiran shi kice ya fito ko shi zai hango mu, kice kin saka hijabi ruwan toka”
Duk da taso su juya din tunda Elias yai mata wannan rainin hankalin, amman kuma ita taga hotunan shi, ta kuma ga kalar motocin da yake hotunan a jikinsu, maganar Biebee zata iya zama gaskiya, kilan shima yaga golf dinne yake so ya gwadata, yaran masu kudi kanyi haka wani lokacin dan suga ko tsakani da Allah kake son su. Shisa ta sake kiran Elias ta fada mishi abinda Biebee din tace su duka biyun suna labe jikin katangar da zata hadasu da titin da Elias din yake. Sai dai ga mamakinta murfin motar aka bude ta mazaunin da bana dire ba bane, kafin taga an ziro kafa daya, ana kama murfin motar, sannan taga ya saka dayan hannun shi kamar zai tattaro wani abu ya fito dashi, a tare suka ware idanuwa ita da Biebee
“Butar shayin buzaye…”
Hindatu ta fadi dan shine karshen zaginta idan abu yakaita makurar mamaki, Biebee na karbe zance da fadin
“Inalillahi… Ke Hindatu mun shiga uku….La haula wala quwwata ila billah…. Kinga me nake ce miki ko?”
Cewar Biebee da take a tsorace ganin shanyayyar kaface Elias din ya tattaro ya fito daga ita daga motar yana jingina jikin shi da murfin motar, sannan yai amfani da dayan hannun shi yana fara kiran wayar Hindu da batasan lokacin ma data sauketa daga kunnenta ba, sai da taji ringing dinta, dagawa tayi batare data kara a kunnenta ba, tana hango Elias daya bude baki yana fadin abinda bataji ba ta cikin wayar. Tana godema Allah da duk yanda Elias yayi naci hotonta daya yagani wanda yake a dp dinta na WhatsApp, ca tayi shida zai ganta wata rana harya gaji.
Wayar ta kashe gabaki dayanta
“Na shiga ukuna ni Hindatu”
Ta fadi tana kallon Biebee da mamaki ya hanata dariya, hannun Hindun taja suna komawa baya
“Mu zagaya ta baya mu wuce gida”
Bata bari Biebee ta sake fada mata ba, da sauri suka nufi inda suka fito dan suyi zagaye zuwa gida. Sauri suke kamar zasu tashi sama, basu fara tsagaita tafiyarsu ba saida suka sha kwanar da zata kaisu gida, sannan Biebee tace
“Elias…”
Tana jan sunan kamar yanda Hindu takan fada kar suyi mata iskanci cewar sunan shi Iliya, kafin ta kwashe da wata irin dariya tana dorawa da
“Yar banza… Daman nabari kin karasa wallahi”
Hade rai Hindu tayi tunda ita bataga abin dariya a cikin wannan al’amarin ba, tana da yakinin ita kam yarda da wani namiji da zasu kara haduwa a 2go zai mata wahala, daman Khadee ta fada mata itace taki ji. Tace mata babu kalar tarkacen da babu a 2go
“Yanzun meye abin dariya?”
Ta bukata tana kallon Biebee din da taci gaba da dariya kamar haduwa da Hindun tayi da gurgu shine abu mafi nishadi da ta taba cin karo dashi a duniya. Dogon tsaki Hindu taja tanayin gaba, Biebeen nabin bayanta da fadin
“Haba Kawata ta Eliass”
Shiru Hindu tayi mata, duk tsokanar da Biebee take mata bata kulata ba, ko sallama batayi mata ba ta shige gida. Kai tsaye dakin su ta wuce ta cire Hijabinta tana ajiyewa akan gado, ta ajiye wayar da takejin duk yanda ta saba da ita zatayi kwana biyuma bata dauka ba, idan Elias ya kirata ya gaji zai hakura. Zatayi amfani da lokacin tayi karatun jarabawar da yake gabanta. Amman duk da haka bayan ta fito dan taya Anty hidimar girkin dare sai da taji zuciyarta na lugude kamar Antyn zata gane abinda ya faru, a tsorace take har suka gama aikin, duk surutunta ko magana bata son yi sosai.
*
Duk da girkin Anty ne, bangaren Mama ta shiga tana idar da sallar Magriba, ta kasa hakuri, tunda Huzaifa ya karbi memory dinta yace zai turo mata fina-finai, tun safen bata kara ganin shi ba har yanzun. Halima tagani, batama san ta dawo ba, dan taje gidan Yayan Mama din da yake Unguwar rimi, akwai yar shi da suke KASU tare, suna karatun shirye-shiryen jarabawar su ta zangon karshe a shekararsu ta uku. Dan abokin Baban ne ya manne ma Halima, da Baba yaso sai ta kammala karatunta, Hindu batasan meya faru ya amince aka saka rana ba, gashi yanzun bikin sai kara matsowa yake, sauran watanni biyu, tana kammala jarabawarta da sati daya.
Sosai Hindu take fatan samun mijin da yafi Yaa Ahmadi kamar yanda suke kiran shi, zatayi karya idan tace sanda yake zuwa gidan baya burgeta, duk da bai karasa irin tsayin Mijin da take so ba, amman ya iya gayu, gashi yana shigowa zaka fara jin kamshin turarukan shi na tashi. Magana daya zuwa biyu Yaa Ahmadi kan jefa turanci cikin kwarewa. Amman taji dadin auren Halimar da zaiyi, ko ba komai basuyi asarar hadadden gaye ba, a nata tunanin ya zama nasu, ta kuma ji dadi ba kadan ba
“Yaa Halima yaushe kika dawo?”
Numfashi Halima ta sauke, cikin sanyin muryarta ta amsa da
“Da yammacin nan, Anty tace kunje duba kawarku ke da Biebee”
Kai Hindu ta daga mata, tana jin yanda zuciyarta tayi tsalle data tuna fitar da ta saka Elias fadowa a ranta, duk saurin karbar memory din ma babu amfanin da zai mata yau, dan ba zata kunna wayar ba.
“Eh kam… Yaa Huzaifa ya shigo?”
Kai Halima ta girgiza mata, sallamar da sukaji na saka su juyawa su duka suna amsawa, Hindu na dorawa da
“Ina wuni”
A dakile ganin Musa ne dan Kanwar Mama, ta dauka tana son farin namiji, sai akan shi ta fara gane kalar namiji itace karshe cikin jerin abinda take so a tattare dashi, gajartar Musa ta sa ko kadan baya burgeta, ba ca yayi yana son ta ba, kwata-kwata a tunaninta data kwatanta idan yace yana sonta dinne baiyi mata ba. Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, babu wani dalili tana jin mutum baiyi mata ba, amman kiyayyar da takewa Musa dabance, kuma sai ya dinga abu kamar baisan gajere bane, yana daddaga kafadun da takeji kamar ta kwantara mishi wani abu akai dan takaici
“Hindun Baba….Ya kike?”
Ya fadi cike da iyayin da ita kadai take gani a tare da Musan, ta tsani yanda ta karfi da yaji yake nuna akwai wani kusanci a tsakanin su, sai yashe mata baki yakeyi. Mama tace Baban shi qwara ne, da Hindu ta dauka a bakaken fata kawai akafi samun guntaye, amman saiga Musa ya fito a qwaran shi sak, amman tana hango tsakiyar kan shi
“Lafiya…”
Ta amsa can kasan makoshi, da Halima bata wajen ko inda yake ba zata kalla ba, amman tasan halin Halima, ta kwada mata mari ba abu bane mai wahala, ko Yayarsu Salma basa tsoro haka kafin tayi aure, Halima bata wasa dasu, a haka sai kaganta kamar tana da sanyi, sai kaji saukar mari akan kuncinta, dan bata son raini, bata kuma so taga kana wulakanta mutum, shisa ba sosai suke shiri da Hindu ba, sau daya ta taba cewa Musa gajere a gaban Halima ta kusan kwada mata mari
‘Ko gawayi ba zaki iya yiba, kina kushe halittar da Ubangiji yayi kamar bakije islamiyya ba, idan gajartar shi batai miki ba, sai a samo tsani kihau sama kiji dalili. Wallahi Hindu ki iya bakin ki, ba tun yau nake jin yanda kike kushe halittar mutane ba, idan baki haifa ba, zaki iya aura’
Shine abinda Halimar ta fada mata, a ranta ta dinga zabga addu’a kar Allah ya amsa, dan taji haushi sosai. Tunda bakin cikine, ita ta sami me kyau tana mata fatan auren gajere. Ko maza sun kare sai ire-iren Musa gara ta hakura da auren, yanzun ma dakinsu Khadija ta wuce dan taga Musa naso ya karayi mata wata magana. Halima ce taje ta kawo mishi ruwa bayan ya zauna tana fadin
“Bari in kira maka Mama”
Kai Musa ya daga mata, ba wani dalili bane ya kawo shi gidan sai Hindu, tun randa ya fara dora idanuwa akan yarinyar ta kwanta mishi, yayiwa Mama magana akanta tace ya dakata ta kammala sakandire, amman sosai yaso ace ko sanar da ita Hindun Mama ta bashi dama yayi kar wani yazo yayi masa shigar sauri. Mace irin Hindu ba’a saka wasa a neman auren su, amman duka kasa da shekara daya ya rage musu. Har kasan ranshi yake jinta, lokutta irin haka yakan kasa hakuri sai yazo gidan yaganta sun gaisa, kullum kyau yake kara ganin tana yi mishi da yan matancinta da yake kara fitowa. Dan haka Mama na fitowa suka gaisa yace zai wuce.
Murmushi Mama tayi, ba tun yau ta kula yakan zo gidan bane da sunan gaisuwa dan kawai yaga Hindu
“Ka gaishe su, dan Allah kace ma Hajiya ta shirya da wuri jibin zuwa sunan yar wajen Jummai… Nima da wuri zan fito in shaa Allah”
Kai Musa ya jinjina mata sukayi sallama ya wuce. Zata so yaron da Hindu saboda hankalin shi, kuma duk a gidansu babu wadda ta shaku da ita sama da Hajiya, mahaifiyar Musa, ga Baban shi ma mutum ne na kirki dayake samun shaidar mutane a duk rana, tace ya bari tagama sakandire ne sanin tsarin Baban su Hindun, kuma yaran yanzun ba’a yanke musu hukunci, gara shi Musan ya fara neman soyayya a wajen Hindu kafin manya suce zasuyi katsalandan su sha kunya.
*
Satin bikin Halima yayi dai-dai da satin da Hindu ta fara kallon film din korean da yayi tashe a shekarar 2010 mai suna Secret Garden da ita sam bata san yanda akayi sai yanzun take kallon shi bayan shekara uku dayin shi ba. Daga farko film din yaso yayi mata wani iri, dan ta saba ganin Lee Min Hoo da ya samu wajen zama a zuciyarta yayi kane-kane yana saka duk wasu sauran jaruman fina-finan korea sai take ganin su daban, tamkar kyawun su da soyayyar su bata kai tashi ba. Sai da ta rasa abin kallo, da yake yanzun a wayarta take yin kallon, sai ta saka earpiece ta dade kunnuwanta yanda babu wanda zai dameta.
Yanzun ma saida ta tabbatar har wanke-wanke tayi, tayi sallar isha’i, bata da wani assignment tukunna ta saka earpiece tana kwanciya kan kujera dan daren jiya har mafarkin film din ta dinga yai saboda yanda ta saka shi a ranta. Soyayya ce irin wadda take so, zuwa yanzun ta daina ganin fuskar jarumar, dan ta jima da daukar tata fuskar ta makala a jikin jarumar, ya zamana tanajin kamar da ita ake zuba madarar soyayyar da take faruwa cikin film din. Daman haka rayuwa take, sai kaga mijinka ya fado ta inda baka tunani. Tasan hakan na faruwa a Najeriya, kawai ba sosai ba. Yanda jarumin duk kudin shi, da ajin shi ya bada kai bori yahau wajen soyayya ya gama tafiya da Hindu.
Haka take so ta kasance da ita, dukkan kudin shi ya zama nasu ne, store dinsu da ya kusan rabin barnawa jarumin ya dauki jarumar dan ta zabi dukkan kayan da take so, amman ta watsa mishi kasa a ido tana nuna bata so, ta juya tana fara tafiya, amman duk irin wulakancin da tayi mishi sai ca yayi
‘Nal tteona jima (Karki barni)’
Cikin yanayin daya burge Hindu, bata san lokacin da ta mike ba, tana tsayar da film din, idanuwanta ta lumshe tana bude su, tana jinta tamkar a kasar Korea lokacin data maimaita kalaman da jarumin ya fada, tana watsa hannayenta, ji tayi kamar ba dai-dai tayi ba, haka ta shiga maimaitawa, sai ta girgiza kanta ta sake maimaitawa, ko kadan bata kula da Zaid daya shigo ba yanata magana dan ta tare mishi hanya, sai da taji ya dala mata wani duka a gadon baya hadi da tureta
“Dalla matsa…wawiya kawai”
Ya furta a kufule yana shigewa ciki, dan zai tambayi Anty aron wayane ya kira Baba, katin shi ya kare, kuma yana bukatar magana dashi kan lemukan daya aike shi siyowa da za’ayi amfani dasu wajen bikin Halima din. Sosai dukan ya shigi Hindu, saida ta cire earpiece din ta samu waje kan kujera ta zauna, tana tuna yanda ko kusa batayi hanyar Korea ba, da Zaid bai dala mata dukan da yayi mata ba yanzun, shisa komai na kasashen ketare yake burgeta, yanayin ‘yancin da suka samu na rashin kwaba kansa ta hasashen itace a wannan matsayin. Ka kwanta sanda kaga dama, ka fita lokacin daka ga dama, amman duk gidan Khadee ta dauka zata fahimci wannan fannin, data gwada mata magana tsaki taja tana fadin
‘Sai a sakeka kamar tunkiya, shisa kike ganin ga rayuwar su nan, babu kan gado, musulunci ma Rahma ne wallahi’
Shiru Hindu tayi ta kyaleta, dan ita ba maganar musulunci takeyi ba, maganar zamantakewar rayuwa takeyi. Wayaki irin wannan ‘yancin, ka kula duk kalar saurayin dakaga dama, kaje party babu wanda zai hanaka, har tsakar dare fita sukeyi. Amman sukam a gidansu, mazan ma akwai shekarun da zaka kai kafin ka fara fita bayan Magriba idan ba masallaci zakaje gabatar da sallar isha’i ba. Balle su kuma da in suka dawo daga islamiyya shikenan sun gama fita sai dai in su duka gidan zasuje wani waje. Ko aiken su ma ba’ayi tunda akwai maza a gidan.
Gajiya tayi da tunani kan abinda ba zata canza ba, hakan yasa ta mike tana nufar daki, da niyyar idan Allah ya bata aron rayuwa, ta sami kalar mijin da take mafarki, zasu gina rayuwar su kamar ba daga yankin Najeriya suka fito ba, har yaransu zasu zamana daban, zasu taso cikin yancin duk da ta rasa a yanzun. Shisa Baba yake da waje daban a zuciyarta, shi kadaine mutum daya a yanzun da yake da cikakken ikon da zai takurata amman baiyi hakan ba. Kwanciya tayi tana fasa yin kallon, gara tayi bacci kawai, dan bama lallai tunani yabarta ta nutsu kan kallon ba.
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: 15
Cikin sati daya, ko idanuwanta ka kalla sai kaga yanda tayi zuru-zuru. Anty da ta tambayeta haka kawai tace mata
“Karatun ne ya kara zafi Anty”
Jinjina kai kawai Anty tayi, da damuwa a cikin idanuwanta
“Ki dinga hutawa dai”
Murmushi ta tsinci kanta da yi, Anty na daya daga cikin iyayen da basu cika bayyana kaunar su a fili ba, amman a cikin duk wani motsi da zatayi sai ka karanci tsantsar kaunar da take yiwa yaranta. Su kansu suna mamakin yanda take gane wani abu yana damun su, ko ya canza a tattare dasu. Hindu ba zata iya gayawa Anty asalin abinda yake damunta ba, batasan ta inda zata fara ba ko da zata iya. Jaruman litattafan hausa kan sha gwagwarmaya a ciki labaran su, kafin su samu cimma burin su, amman sunayin hakanne tare da Samarin, suna nuna musu wata irin zazzafar kauna a duk wani motsi da zasuyi.
Samarin basu taba zama matsalarsu ba, sai dai dangi, ko wani abin daban. Amman cikin sati daya, Hamza ya zame mata matsalar da ki a mafarki bata hango faruwarta ba, ga soyayyar shi da ta samu waje tayi mata zaune. Ta dauka tana da rikici, ta dauka ta iya rigima, ta kuma dauka ta gama gane cewar shi Hamzan yana da rikici, sai a satin nan daya, tunda ya fara kiranta da budurwar shi, ko wayarta ya kira yaji busy saiya tsareta da tambayoyi akan wa take magana da shi, idan wani da ba dan uwanta bane ya fara tashin hankali kenan, wani irin kishi take gani tattare da shi daya fara bata tsoro.
Yanzun kiri-kiri yayi mata blocking din Ahmad daga Instagram har Twitter din ta, harda fadin
“Allah ya isa idan kika kara magana da shi, dan bakya son shi baya nufin shi din baya jin wani abu a kanki, ko da bayaji ni baimun ba, bana son shi, bana so kina magana da shi”
Ahmad din har kiranta yayi, bata daga ba saboda batasan me ma zatace mishi ba, taga text din shi
‘Naga kinyi blocking dina Hindu, bansan ko nayi miki wani abu bane ba, na kira baki daga ba’
Goge text din tayi saboda kunyar Ahmad din da takeji, yana da hankali da matuqar kirki, da ta gwada cewa Hamza
“Ba zai yiwu ka dinga mun blocking din mutane ba, wasu abokan karatuna ne, idan ina bukatar tambayar su wani abu fa?”
Yanda ya fadi
“Ni? Ni kike fadama ba zai yiwu ba?”
Sai da tadan raba wayar da kunnenta, kafin ta mayar tana jin shi yana cigaba da fadin
“Kome zaki tambaye su, ni ki tambayeni, ni kadai na isheki, banda yan uwanki, ni kadai ne namijin da zai kasance a rayuwar ki, gara ki saba tun yanzun”
Kafin ma ta sami fadin wata magana harya kashe wayar shi. A kwanaki bakwai rana daya ce basuyi tashin hankali da shi ba, sai ya hau Instagram dinta, ya zaqulo tsohon chat ya tisa mata rigima a kai, ba karamin tashin hankali tagani wajen shi ba, akan hirar su da ya gani da Jalil, inda yasan yanda zancen ya qare ma da bai tashi jijiyar wuya a kai ba. Ita kam tunda ya bata password din shi ta hau sau daya, bata ma sami nutsuwar da zata koma ba. Sai yanzun da batada abinda zatayi, bata da wani assignment saboda jarabawa data qarato, sai project din zangon kawai, da a hankali take bin zanen.
Da yake asabar ce, a daki ta wuni, Anty ma bata sakata aikin komai ba, dan yanda taga tayi zuru-zuru sai ta kyaleta, taji dadin hakan har ranta. Yanzun ma tunda ta idar da sallar la’asar ta koma kan gado tayi zamanta. Hamza yace mata yana da aiki, idan anyi Magriba zai zo ya ganta, tunda duk satin basu hadu ba, sai dai video call kawai da sukeyi. Yau din ma tun safe, sai text din shi bayan la’asar
“Azkar din yamma”
Ta amsa shi da tayi, ko tana makaranta ne haka yake mata wannan tunin, yanzun da Asuba duk baccin da yake idanuwanta in batayi karatun Qur’ani ba sai yasa ta tashi, wani lokacin video call zai kira yaga ko ta tashin, yakan ce mata
“Ranar ki zata tafi dai-dai idan kika fara ta da sallar Asuba a kan lokaci, kiyi karatunki koya ne, kiyi azkar, sai ki rufe da sallah raka’a biyu idan rana ta fito”
In ta nemi yi mishi musu saiya ja mata ayoyin da zasu kashe mata jiki, sosai da duk rana Hamza yake kara samun waje a zuciyarta, lamurran shi kuma na bata mamaki sosai da sosai. Twitter din ta hau tana cin karo da tarin notifications da ta fara budewa, taga Mansy ce da tayi ma Hamza magana, ba gane me tace tayi ba tunda da fulatanci ne, wani irin tsaki taja, tsanar da tayi mata na dawowa farko
“Tsohuwar banza mai tallar goro”
Ta furta a fili tana kara dorawa da wani tsakin, ta tafi DM din Hamzan ta bude, nan ma na Mansy ne a farko
“Nawan ina kaje ne yau haka?”
Ta karanta sakon da tayi da harshen Hausa, wato munafunci ne yasa take mishi yare a bainar jama’a, anan kuma takeyin magana da wanda kowa zai iya fahimta. Shiga sakon tayi, zuciyarta nayin tsalle ta dawo makoshin ta, kafin ta koma kirjinta inda taci gaba da dokawa da wani irin ciwo da yasata yin tari, idanuwanta har yaji suke da abinda ya wuci hawayen da taji sun taru cikin su, hotunan da Mansy ta turo mishi ne tana dorawa da
“Wanne yafi kyau?”
Rigar mama ce mai hade da wani wando da Hindu takan ga turawa sun saka a bakin ruwa, bata ga dalilin da zaisa Mansy ta turo ma Hamza irin wannan hoton bane ba, ko da soyayya sukeyi abune da bai kamata ba sam-sam. Amman kamar yanda Dimples kan fadane
“Ni banga dalilin da zaisa mata suje suna fada da yan matan mazajen su ba, ko ke budurwa da bakima shiga gidan shi ba ki fara tsanar matan da suke tare da shi ba, saboda koma me yake faruwa a tsakanin su, shi ya bada fuska”
Amman hakan bai hanata jin kamar ta soka ma Mansy mashi ba, sama tayi tana karanta hirarrakin su da ko kadan babu kintsi a ciki, sam batasan hawaye take ba sai da taga digar su saman screen din wayarta, sosai kirjinta yake mata zafi, bata taba jin ciwon zuciya irin wanda takeji ba yanzun. Kwata-kwata tashin hankali bakonta ne, fitowa tayi daga hirar, tana cigaba da bude sakonnin sauran matan, da suke ma Hamza tallar kawunan su, sai dai amsar shi daya ce ga duk wadda ya amsa
“Digits”
Ma’ana lambar wayar kenan, in suka ajiye kuma babu wani abu da yake sake hadasu, amman hirar su da Mansy ta gama tabbatar mata da abinda yake faruwa a tsakanin Hamza da sauran matan.
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”
Ta tsinci kanta da furtawa tana sauke wata ajiyar zuciya saboda kukan da takeyi. Hamza na bin mata, ko baya bin sauran matan yana tare da Mansy. Wannan ba zargi takeyi ba, hirar su ce ta tabbatar mata da hakan. Wayar ta ajiye kan cikinta, tana saka tafukan hannuwanta duka biyun ta rufe fuskarta da su. Kuka takeyi da ba zata tuna ranar da tayi irin shi ba, sosai zuciyarta take ciwo kamar zata fito. Tana nan kwance, tayi kuka har fuskarta ta kumbura, kafin ta iya mikewa tana shiga bandaki, ta wanke fuskarta, tana dauro alwalar Magriba. Tana fitowa ana kiran sallah, lokacin da yayi dai-dai da shigowar Asma dakin da sallamarta da Hindu ta amsa murya a dishe.
Tana kuma yin sauri ta kabbara sallah, tana jin Asma ta shiga bandaki, tana fitowa kuma ta fice daga dakin. Tana idar da sallah, dakyar ta iya yin azkar, da ta daga hannuwanta sai ta rasa addu’ar da zatayi, tana tsaka tsakiya neman wani canjin ba Hamza ba, ko kuma nema mishi shiriya, kafin ta yanke hukuncin tsayawa a nema mishi shiriya, dan zuciyarta ta karyatata wajen tunanin cewa abinda tagani akan Hamzan ya canza abinda take ji, yana nan daram a ranta kamar komai bai faru ba.
Wayarta data fara ruri ta mika hannu ta dauka tana ganin shine, dagawa tayi ta kara a kunnen ta
“Ina cikin gidan ku”
Ko magana batayi ba ta sauke wayar daga kunnenta, tana mikewa. Ko fuskarta bata duba a mudubi ba, hijabin jikinta kawai ta sake, tana daukar ruwan toka, da ta Asma ce ta zira a jikinta. Ba zata tsaya shafa wani abu ba, shiya sakata kuka, ya kamata yaga haka, ba zata boye mishi tana cikin yanayin damuwa ba.
*
Komai sabone a wajen shi, inda wani a cikin abokan shi zaice mishi a shekarar nan zai kira wata yarinya da budurwar shi zai karyata. Ba zaice ga yanda akayi ya ce Hindu ta saka shi a layin samarinta ba, yafi ta’allaqa hakan akan yanda tunaninta da wani saurayin yasa shi ganin wani hadarin kishi na gilma mishi ta cikin idanuwan shi, kirjin shi har zafi yakeyi. Bayason kowanne namiji a kusa da ita banda shi, bayason wani yaji muryarta, balle yaji yana son ya riketa kamar yanda yakan ji duk idan tana magana.
Aikin daya sakko su gaba bai hana shi tunanin halin da take ciki ba, da wa tayi magana a makaranta, wayai mata magana, waya tare ta a hanya. Shi kadai sai ya tsinci kan shi da jan karamin tsaki, yanzun tunda ya shiga Instagram dinta rabon daya shiga nashi, yana kai kullum yana ganin yanda ta sake tana hira da maza da yake bala’in bata mishi rai. Yau ma duk da ya yanke hukunci ajiye komai yaje ya ganta, haka ya shiga Instagram yana dudduba sauran chats dinta, dan duk wanda ya karanta saiya goge gabaki daya, yayi blocking idan namiji ne. Matan baya bi ta kansu sam, tsaki yaja ganin wani yayi mata sallama tafi biyar
“Wawa kawai”
Ya fadi yana saka AbdulHafiz da yake shan shayi yana aiki a system din shi ya dago da ido ya kalle shi
“Me yasa maza basu da aji ne?”
Hamzan ya tsinci kan shi da tambaya, yana saka AbdulHafiz yin murmushi
“Me yasa wasu mazan basu da aji zaka ce. Me ya faru?”
Tsaki Hamza ya sake ja, duk satin nan baya rabuwa da ciwon kai, akan Hindu ne kuma, ita ce sabon ciwon kan da ya shigo rayuwar shi
“In kaga mazan da suke DM dinbHindu suna mata magana zakayi mamaki wallahi, kamar basu da wani aiki banda bin yaran mutane”
Shayin AbdulHafiz ya kurba, sannan ya ajiye kofin a nutse, ba sosai yake saka kananun kaya ba, yanzun ma dan suna gidane, anan suke ta aikinsu tun safe, tracksuit ne a jikin shi, riga da wandonsu, yaja zif din rigar har wuyan shi a rufe yake ruf, dago da idanuwan shi yayi yana saukewa kan Hamza da yake girgiza kan shi cike da dana sanin subutar bakin da yayi akan Hindu din. Banda Fodio babu wanda yasan da maganarta, shima Fodio din ya dauka Hamza ya sami abinda yaje nema ya barta.
“DM? Screenshot ta turo maka?”
AbdulHafiz din ya fara tambaya, Hamza ya riga yasan ba zai iya kaucewa maganar ba, ya riga yayi subul da baki, kuma yanayin fuskar AbdulHafiz din ya nuna mishi ba zai bashi wannan damar ba yau, gashi su kadai ne, Arafat da su Fodio suna kamfanin su. Daga shi sai AbdulHafiz din a gidan, da saiya sake maganar, AbdulHafiz zai dauka bayason yayi a gaban su Arafat a lokacin, zai kyale shi.
Kai ya girgiza ma AbdulHafiz din
“Da kai na nake gani”
Shayin AbdulHafiz ya sake kurba yana ajiye kofin
“Abu biyu zan fada maka, ban san me kakeyi a Instagram ko Twitter din ta ba, amman hakan zai saka rashin yarda a tsakanin ku, idan ka yarda da kanka, ka yarda da soyayyar da take maka, sauran mazan bai kamata su dame ka ba”
AbdulHafiz ya fadi yana dorawa da
“Ka zama Sarki a masarautar yarinyar da kake tare da ita, sauran mazan duk da zasu zo fadawa ne, ba su da wani muhimmanci, da kanta zata baka labari kuyi dariya. Karka fara dora alamar tambaya akan zaman ku, in bata baka dalilin yin hakan ba”
Yana jin kalaman AbdulHafiz dinne, amman bai yarda dasu ba, badan bai yarda Hindu tana son shi ba, kawai dai yana so yaga dawa take magana ne.
“Wacce Hindu din?”
AbdulHafiz ya tambaya, tunda maganganun da yayi basa bukatar amsa, kawai saurare ne, idan Hamza yaga dama ya dauka, idan baigani ba ya rigada yayi nashi bangaren.
“Yarinyar da ka amsa a DM dina”
Kai AbdulHafiz ya jinjina, yagane ta, yana son yaji tabbaci ne daga wajen Hamzan. Sosai ya gyara zaman shi yana tattara duka nutsuwar shi da hankalin shi akan Hamzan, dan maganar da yake son fadi na da matuqar muhimmanci a wajen shi
“Nasan kaddara zata hadaku idan Allah ya rubuta hakan ko da ban amsata ba, kaddarar tazo da ni ne sanadi. Ka jini Hamza, saboda zan fada maka sau dayane, kamar dan uwa kake a wajena, kasan hakan, ba yau ne na farki dana fada maka ba, ina maimaita maka ne….”
Numfashi Hamza yaja yana fitarwa, tun kafin AbdulHafiz din ya karasa maganar ta tsinci kanshi da son tashi ya gudu yabar dakin, dan ya kauce ma jin koma meye zai fada
“Kusancin da yake tsakanin mu ba zai sa ka darsa mun kokwanto a neman lahirata ba Hamza. Kana jina, idan ba da niyyar aure kake tare da yarinyar nan ba, idan babu alkhairi a tare da niyyar ka, ka yanke koma menene a tsakanin ku, bazan zama silar baka ticket din da zaka sakata a layin matan da kabi ba. Baka isa kai mun haka ba, wallahi baka isa ba, kaji na rantse, ban isa in hanaka abinda kakeyi ba, shisa nake binka da addu’a, amman banda ita, banda Hindu….ba rokon ka nakeyi ba, fada maka nayi. Bazan yafe maka ba wallahi…”
AbdulHafiz ya karasa maganar yana so Hamza ya fahimci da gaske yake, idan ya bata musu yarinya zai yanke alaka da shi, maganar farko tayi mishi yanayi da Nabilar shi, batayi kama da matan da Hamza ya saba bi ba sam, ba zai zama sanadin da zata lalace ba. Ba zai yafe ma kan shi ba idan Hamza ya taba ta, kamar yanda ba zai yafe ma Hamzan ba. Kofin shayin shi ya dauka yana tura kujerar da yake kai baya, hadi da mikewa dan yaje ya karo wani shayin da yake kitchen cikin kettle.
Nan yabar Hamza a zaune yanajin kamar an mishi wanka da ruwan kankara. Shi bai shirya yin aure ba, sam babu wannan tsarin a rayuwar shi nan da shekaru biyu ma, ko gidan shi bai gama ba. Bai san yanda AbdulHafiz din yake so yayi ba, yanajin dai yanzun ko Hindu bata isa ta raba shi da kanta ba, balle kuma wani. Har ran shi yanzun ba zaice ga abinda yake da niyya akan ta ba, yana son kasancewa da ita, amman shi bai shirya aure ba sam. Kamar yanda bai shirya yanke alakar da take tsakanin shi da AbdulHafiz ba, zai iya hakura da Hindu ko da aurenta zai idan hakan zai shafi alakar da take tsakanin su da AbdulHafiz, yana jin shi kamar dan uwan shi, sun wuce matakin abokantaka.
Sosai kan shi yake mishi ciwo, AbdulHafiz ne ya dawo
“Kai ba zaka sha shayin ba?”
Ya tambaya kamar bai gama hargitsa mishi dukkan lissafin shi ba, ammam AbdulHafiz ne, ya riga ya gama maganar kenan, ba zai maimaita ba. Yabar komai a hannun Hamzan, zabin nashi ne. Kai kawai ya girgiza mishi da yake jin yana kara ciwo. Su dukan su aikin da sukeyi suka cigaba. Kafin AbdulHafiz din ya fara waya da Nabila, ya saka earpiece a duka kunnuwan shi, hirar tasu na saka Hamza jin kewar Hindu da ta danne shi, tun la’asar rabon daya ji motsinta. Aikin da yakeyi yai saving yana kashe laptop din ya mike, zuwa yai yadan watsa ruwa ya dauro alwalar magriba ya fito, kaya ya sake zuwa manya, wani farin yadi daya karbi jikin shi, bakar hula da takalmi ya saka. Ya dauki mukullin mota yana fita falon
Wayar shi ya dauka da take kan tebirin da suka ajiye daga can gefe inda suke ayyukan su, dining ne ba zama suke suci abinci ba, ya zame musu kamar Office din gida. Harya kai kofa AbdulHafiz yace
“Hamza…”
Juyawa yayi
“Allah yasa alkhairin ka ce”
Dan murmushi Hamza yayi yana ficewa daga gidan,wasu lokuttan AbdulHafiz kanyi mishi kamar babban Yaya, duk da watanni biyar ne tsakanin su, shisa yake kasa zagin shi kamar yanda yake zagin su Fodio. Yanayin kusancin su daban ne, kuma su dukan su yana musu kamar Yaya fiye da yanda yake aboki a wajen su. A hanya ya tsaya nan masallacin da yake station round about, yayi sallar magriba, kafin ya karasa gidan su Hindu, maigadi na bude mishi kofa ya shiga da motar shi, bai fito daga motar ba ya kira wayarta, tana dagawa yace
“Ina cikin gidan ku”
Batace komai ba, shima bai jira amsarta ba, ya kashe wayar daga bangaren shi, yana ajiyeta a cikin motar. Wani irin sama-sama yake jin shi, ga kan shi da yake ciwo har lokacin, duk da wani bangare na zuciyarshi na cike da jin dadin zaiga Hindun, yau maganganun AbdulHafiz da yake ji sun dabai-baye shi sun kashe mishi jiki tsaf, a karo na farko tun daya hadu da Hindu da yazo wajenta batare da yanajin kamar inta fito bai riketa ba zai mutu.
Bai fito daga motar ba, sai da yaga Hindu da ta ajiye musu kujeru bayan motar shi, da murmushi a fuskar shi ya zagayo yana jan kujerar ya zauna. Sai dai tana zama ya sauke idanuwan shi kan fuskarta, murmushin da yakeyi ya dishe
“Hindu…”
Ya kira ganin fuskarta da take a kumbure har cikin idanuwanta, ai kamar hakan take jira taji wasu hawaye da ta kasa tarbewa sun zubo mata, yana fitowa taji kamar ta rufe shi da duka, kallon da yake mata cike da damuwa shiya karya mata zuciya yasa hawayenta zuba
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Me ya faru? Menene?”
Hamza ya fadi yana kai hannu ya riko na Hindu data fisge tana goge hawayen fuskarta
“Dan Allah kiyi mun magana”
Numfashi taja tana sake goge fuskarta, zuciyarta take ji tana ciwo kamar zata fado
“Me yasa kabani Password din ka?”
Ta tambaya tana tsare shi da idanuwanta da suke cike da wani yanayi da yaji bayaso
“Saboda bani da abinda zan boye miki”
Ya fadi da dukkan gaskiyar shi
“Har hirar ku da Mansy?”
Ta bukata tana jin kirjinta na gab da budewa, numfashi Hamza yaja, yana huro iska ta bakin shi, ya dauka wani abinne daban akayi mata, ko shi yayi mata bai sani ba. A hankali ya daga mata kai, tunda ta rigada tagani baiga dalilin da zai mata wani boye-boye ba. Cikin sanyin murya saboda kan shi da yake ciwo yace
“Me kike so ince miki?”
Dariya Hindu tayi da bata da alaka da nishadi
“Kana da karfin halin yimun wannan tambayar Hamza? Bakasan abinda ya kamata ka ce mun ba? Akan abinda kukeyi da Mansy har kana ce mun baka da abinda zakace mun?”
Idanuwan nan nashi ya kafa mata, irin wannan dalilin na daya daga cikin dalilan da zasu saka shi kinyin aure nan kusa, ba zai yiwu ana tsare shi da tambayoyi haka ba
“Karkiyi mun ihu, karki fara cewa zakiyi mun fada. Dana baki password dina nace ki karanta mun chats? Na aikeki karanta hirar mu da Mansy? Da kika fara karantawa kikaga ba zaki iya jurewa ba me yasa kika ci gaba?”
Bakinta a bude yake tunda ya fara magana, dariyar ta sakeyi duk da idanuwanta da suke cike taf da hawaye
“Kana da karfin hali, wallahi kana da karfin hali Hamza”
Daga mata gira yayi cike da masifa, kan shi ciwo yake kamar zai rabe biyu. Tana kuma kara mishi ciwon kai kan abinda ita taga zata iya karantawa, shima haka ya jure bin chats dinta da garadan duk da suke mata magana, harda Jalil, baiyi kuka ba duk yanda zuciyar shi tayi mishi ciwo, sai ita da take da hawaye a kusa zatayi amfani da su ta cuce shi, haka mata sukeyi daman ya sani, abu kadan sai su fara kuka, idan wani yagani zai baka rashin gaskiya kamar kayi musu wani babban abu.
“Na karanta hirar ku da Jalil tun daga farko har karshe, saboda bani da hawaye shine zaki fini fada”
Kai Hindu take girgiza mishi
“Karka hada wannan da Mansy, ni banbi Jalil ba, bakama san ya muka kare da shi ba”
Cikin idanuwa Hamza yake kallonta
“Zunubina ne, me yasa zai dameki?”
Mikewa tayi, ba zata iya ba, zuciyarta fadowa zatai idan taci gaba da sauraren Hamza, taci gaba da ganin yanda yake nuna zina a wajen shi ba wani babban abu bane ba. Hannunta ta kama yana janta ta koma ta zauna babu shiri, hannunta ta fisge
“Karka sake tabani, abinda ya kawoka kenan daman. Wallahi ba zaka taba samu ba, saboda ni ba Mansy bace ba, kasani dai ka cutar dani….Allah kuma ba zai barka ba”
Hindu ta karasa wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, zuciyarta ciwo take har cikin makoshin ta, ga wani tsoro marar misaltuwa daya lullubeta na ma’anar kalamanta, ba ta shirya ba, bata san ya zatayi idan suka rabu ba, amman ba zatayi ma kanta karya ba wannan karin, ba zata iya ba Hamza abinda yazo nema ba.
“Ni zaki hada da Allah Hindatu?”
Hamza ya tambaya yanajin tashi zuciyar na tafasa shima, duk abinda zaiyi a rayuwar shi bayaso yaji an hada shi da Allah, yana kokarin ganin zunuban shi tsakanin shi da Ubangiji ne, bai hada da hakkin mutane ba
“Me ma kike so kice mun? Bari na zakiyi?”
Ya karasa maganar muryar shi na wani irin sauka, kan shi naci gaba da sarawa, a karo na farko a tsayin lokaci a rayuwar shi da yaji tsoro ya dabai-baye shi da tunanin cewa zata bar shi.
“Ya kake so inyi? Ba zan iya ba, wallahi ba zan iya baka abinda ka zo nema ba”
Ta karasa maganar tana rufe fuskarta da hannuwanta saboda kukan da takeyi, baisan lokacin daya kama hannuwan yana rabasu da fuskarta ba, ya dumtse su cikin nata, kai yake girgiza mata
“Baki isa ba, wallahi baki isa ki rabani dake ba, Hindu baki isa kisa in fara sonki ba kibarni, ni ban tsara soyayya a rayuwata ba koda aure zanyi, saboda bana so in wahala, ba zaki barni ba, kina jina”
A hankali ta zame hannuwanta daga rikon da yayi mata, dan ya fara karya mata zuciya fiye da yanda take a karye. Mikewa tayi, ta goge fuskarta sosai tana tashi, dai-dai lokacin da aka kira sallar isha’i, muryarta a dishe tace
“Kaga an kira sallah”
Kai Hamza ya girgiza mata, shima yana mikewa
“Dan Allah ka barni, zuciyata ciwo takeyi, in ba kasheni zakayi ba yau, kabarni haka”
Numfashi ya sauke
“Karki barni to, kice ba zamu rabu ba”
Kai Hindu ta iya daga mishi, gida kawai take so ta shiga, ko zatayi kuka har sai zuciyarta ta rage mata ciwo
“Okay…. Koma menene karki barni, ina son ki”
Ya furta kalaman na sauka kunnuwan shi da tabbaci kan abinda yakeji a kanta. Kafin tayi wani abu taji ya riketa a kirjin shi, sosai wannan karin ta ture shi
“Kagani ko? Abinda kake so kenan bani ba”
Kai Hamza ya girgiza mata, ya riketa ne dan ya rage jin tsoron da yakeji, yau ko abinda take tunanin ma bayaji sam, tashin hankalin da yake ciki ya girmi wannan
“Nasan abinda nake so, kuma duka biyun ne”
Numfashi Hindu ta sauke, ta mika hannu taja kujerar daya tashi daga kai, ta dagota tana hadata da dayar. A wajen tabarsu tana wucewa ta shige gida, tsaye Hamza yayi a wajen, gabaki daya gwiwoyin shi sunyi sanyi. Dakyar ya iya zagayawa da nufin ya bude motar shi ya shiga, yaji an mishi sallama, juyowa yayi yana mika mishi hannu suka gaisa, ya gane hoton shi, Hindu tana yawan saka shi a status dinta, Zaid tace mishi, Yayanta ne, tace likita ne. Kare mishi kallo Zaid yakeyi, akwai inda ya taba ganin Hamzan, ya rasa ko ina ne, amman haka kawai yaji baiyi mishi ba.
“Idan kana son ta da gaske, ka turo ayi magana kafin ka sake zuwa”
Zaid ya fadi, ko bai tuna ina ya taba ganin Hamza ba, bayason irin su a kusa da kanwar shi, sam bayaso. Idan da wata niyya yazo Zaid nada tabbacin daga yau ba zai sake dawowa ba, hakan ma zaifi mishi, dan ko turowa yayi har unguwar su zaije da kan shi yayi bincike a kan shi, ba kullum yake yankewa mutane hukunci batare da yasan labarin su ba, amman kuma zuciyar shi kanyi gaskiya akan mutane da yawa, in har yaji kamar baka da hali me kyau sai hakan ya kasance gaskiya. Wucewa yayi kafin Hamzan yace wani abu, dan karma ya samu fuskar ganin wasa yake da shi.
Motar shi Hamza ya shiga, yau dai kowa so yake ya raba shi da Hindu, harda ita da kanta, kuma zai nuna musu basu isa ba, kamar yanda yace ne, yana son ta, da a rabashi da ita gara yayi abinda bai shirya ba, duk sai su sama mishi lafiya su daina kokarin ganin sun rabasu. Hanyar da zata kai shi Tudun Wada ya nufa, gara yayi magana da Appa.
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: 2
Hamza na daya daga cikin mutanen da ba karamin sha zaiwa giya kafin ta bugar dashi, yasan ba ita bace ta saka shi bacci, duk da ya kwankwada daren jiya saboda yanda ranshi yake a bace, dan haka da wani irin ciwon kai ya tashi, kan na shi ya kara sarawa saboda aman da yayi na giyar. Shisa baya so yasha ta da wannan yawan, ran shi a bala’in bace yake jin shi har lokacin. Dan bayan ciwon kan da yake har wani dumi yaji ya dauka na bacin rai, dan karamin kitchen din da turawa sukafi yiwa lakabi da kitchenette ya shiga, dan wajen girkine da zaka iya dafa abin kari ko wani abu dai marar nauyi.
Jikin shi sanye da gajeran wando, amman ya saka riga mai dogon hannu hadi da hula ya saki hular a bayan shi, ya riga yayi wani irin sabo da riguna masu dogon hannu, komin zafin da akeyi kuwa, sai yaji iska na shigar mishi hannuwa duk idan ya saka riga mai gajeran hannu, ko a gida baya zama da ita, da daddare ma ba kullum yake kwanciya da singlet ba, dan ma zai lullube jikin shi tunda da AC. Coffee ya hada ya zuba a kofin tangaran da yake rubuce da Arc Hamzy a jiki, da yake bayason zaki ko da can, ballantana da yasan illar da yake da ita a jikin dan adam idan yayi yawa, haka ya fito da Mug din a hannun shi.
Kurba yayi yana hadiye shi dakyar saboda zafi
“Oh shit…”
Ya furta yana furzo iska ta bakin shi, babu shiri ya koma kitchenette din ya dauko cokali ya saka a ciki yana jujjuyawa cikin son yadan sha iska ko yayane, kan mudubin dakin baccin ya ajiye kofin yana duba agogon dakin yaga karfe takwas da kusan kwata, yana da dan sauran lokaci, dan karfe tara zai fita, kuma yayi wanka. Wajen drawer din gado ya karasa yana zama tukunna ya janyo, paracetamol ya dauko ya balli guda biyu yana daukar robar ruwa da take ajiye a gefe ya jefa maganin a bakin shi tukunna yabi da ruwa. Ya sake mikewa ya dauko Mug din ya kurba yaji zafin ya mishi dai-dai. Bai dauki wani lokaci ba ya shanye yana zuwa ya wanke kofin tukunna ya mayar da shi inda ya dauka.
Gyara gadon yayi tsaf, dan a rayuwar shi bayason ganin waje a hargitse, bakuma ya son kazanta koya take. Ko wajen ajiye kayan shi ka bude a tsare yake sai abin ya burgeka, kowanne kalar kaya wajen su daban, boxers din shi da singlet kan su a tsari suke. Shisa ya tsani wani ya shigar mishi daki, idan akwai abinda yafi saurin bata mishi rai shine wani ya shigo mishi daki ya taba wani abin, dan koya akai kokarin mayar dashi yanda aka gani yana shigowa saiya gane. Saida ya gama tukunna ya taka wajen wardrobe din da take cike da bango daya na dakin saboda girmanta. Wani farin yadi ya dauko da babu aiki a jiki, sai maballan ne kawai da aka saka mishi blue, links ya dauko kalar maballan, sai agogo, hula da takalmi duka blue.
Lokacin da ya gama shiryawa da wahala ko namiji dan uwan shi yai mishi kallo daya bai sake kallon shi ba, ya hadu kamar ba daga jinsin bil’adama ya fito ba. Saida ya feshe jikin shi da turarukan Oud dan yafi son su, tukunna ya dauki mukullin motar shi yana takawa ya fita daga dakin ya sauko daga bene zuwa kasa. Yana zuwa bakin kofa yaja kyauren yana gyara labulen sosai yanda zai datse, bai damu da yasa mukulli ba tunda yana da maigadi kuma yasan babu wanda zai bari ya shigo mishi gida, zai kara mishi kashedi idan zai fita.
Yana karasawa wajen motar shi kirar Toyota corolla CE 2010 ya saka mukulli a jiki ya murza yana budewa, shiga ciki yayi ya kunna yana fitowa daga ita daga jerin motocin shi hudu in har da wadda yake ciki cikon ta biyar, tukunna yai kwana cikin tanqamemiyar harabar gidan na shi yana shirin fita da motar yaga shigowar wata, hakan yasa shi fasa fitar da tashi yayi zaune a ciki yana son ganin kowaye. Parking akayi daga gefe daya kara bata mishi rai saboda ba wajen da aka ware dan yin hakan bane. Yana kallon Huzaifa ya fito daga cikin 406 din shi da duk taji duniya, Muhsin na bude dayan bangaren ya fito shima. Ganin su biyun a tare yasa Hamza kashe motar shi ya bude ya fito shima.
Ganin su na kara harzuqa shi
“Lafiya?”
Ya tambaya cikin yanayin da yasa Huzaifa kallon shi da mamaki bayyane a fuskar shi, Muhsin ne ya iya cewa
“Kaya zamu kwashe”
Tunda ya kula babu alamar mutunci a fuskar Hamzan
“Zan duba in saka muku rana”
Cewar Hamza din yana shirin juyawa
“Bangane zaka duba kasa mana rana ba”
Huzaifa ya fadi yanayin fuskar Hamzan na saka shi son dauke shi da mari, a duniya baya kaunar wulakanci ko ya yake, bama shida hakuri ne gabaki daya, shisa ba sosai yake shiga mutane ba, ballantana wani ya harzuka shi. Cikin idanuwa Hamza ya kalle shi yana amsa shi da
“Hausa nai maka bawani yare ba, meye baka fahimta daga ciki ba…”
Wata yar dariya Huzaifa yayi yana cewa Muhsin
“Kayi magana da shi”
Ya juya yana takawa wajen motarsu ya jingina bayan shi, dan idan ya tsaya bazai san lokacin da zai kaiwa Hamza naushi ba.
“Mun zo da masu mota da mutanen da zasu kwashi kayan, suna waje suna jira”
Muhsin yayi kokarin yima Hamza bayani dan su fahimci juna, su ba rashin mutunci bane ya kawosu, duk da abinda yaima kanwar tasu, tarbiyar da suka samu wadatacciya ce, kai Hamza yake girgizawa tunda Muhsin din ya fara magana
“Fita zanyi, ba kuma zan barku ku kadai a cikin gidana ba gaskiya, gobe ma ina da abinda zanyi. Idan na saka rana zan fada ma Hindun sai ta sanar muku”
Sosai Muhsin yake kallon shi, akwai dalilin da yasa tun ranar daya fara ganin shi tsaye da Hindatu yaji bai mishi ba, a lokacin ya nema bai samu ba, sai jiya daya kwana yana juyi, yana fada ma kan shi yanda bazai kara bata rai idan yaji wata mace tayi wa maza kudin goron zagi ba. Da matar shi rike a kirjin shi tana bacci, darajarta na karuwa a idanuwan shi, baiga riba a wulakanta mace ba, balle wadda ta kasance a karkashin kulawar ka. Tun jiyan ya rasa kalar zuciyar da take kirjin Hamza da har zai iya korar mace tsakiyar dare batare da tunanin halin da zata shiga ba, macen ma da tsohon ciki.
“Kaga ba tashin hankali ya kawo mu ba, kaya kawai zamu kwashe mu tafi”
Inda Muhsin din yasan yanda Hamza yake kokarin ganin ba suyi tashin hankali ba, daya wuce ya sami Huzaifa sun shiga motar su sun bar mishi gida. Tsayuwar da suke, lokacin shi da suke batawa da maganar kwashe kayan da take dawo da Hindu tunanin shi kara harzuqa shi sukeyi ba kadan ba
“Idan baka da abu mai muhimmanci ni ina da shi”
Ya fadi yana bude motar shi, kafin ya shiga ya juyo ya kalli Muhsin din
“Wallahi kuka shigar mun gida karar ku zan kai wajen yan sanda, saboda ina da dukiya a cikin gidana..”
Tukunna ya shiga motar shi, ya tayar yana fisgarta da akwai tsautsayi saiya takama Muhsin da mamaki yagama cikawa kafa. Jikin shi da wani irin sanyi ya karasa wajen Huzaifa yana fadin
“Wallahi mutumin nan bashida mutunci, ko kadan bashida mutunci bansan ya akayi bamu kula da hakan ba kafin mu bashi Hindu, kaji abinda yake gayamun? Wai zai kira yan sanda idan muka shigar mishi gida”
Jinjina kai Huzaifa yayi cike da bacin rai, yana kasa furta wata kalma
“Muje kawai mu sallami mutanen nan, sai mu biya ta gida, kar muyi wani abu ko da sauran zama a tsakanin su”
Sai lokacin Huzaifa yace
“Da wa? Ai kasan Allah ko zata mutu ba zata dawo gidan wannan mutumin ba, daman shegiyar kafiyarta ce, da Baba daya goya mata baya”
Dan murmushi Muhsin yayi yana bude motar ya shiga ya zauna. Huzaifa ya bude dayan bangaren mazaunin direba yaja suka fice daga gidan, masu manyan motocin har biyu suka sallama tare da karbar lambar wayar su da cewar zasu sake neman su azo a kwashe kayan. Tukunna suka kama hanyar gida, Huzaifa har lokacin zuciyar shi a makoshi yake jinta
“Inda na mari yaron nan da zuciyata tadan yi sanyi”
Dariya Muhsin yayi dan baka raba fuskar shi da fara’a ko da yaushe
“Allah dai ya rufa asiri, idan ka biye halin mutane abinda yafi mari ma sai kayi musu. Ni yanzun Baba ma nake tunani wallahi, ran shi ya baci jiya tunda kaji yace a kwashe kayan a daren. Me zamu ce mishi?”
Dan kallon shi Huzaifa yayi kafin ya mayar da hankalin shi kan tukin da yake
“Me zamu ce mishi daya wuce mu fada mishi gaskiya? Yace ba zamu shigar mishi gida baya nan ba, idan kiran shi Baban zaiyi sai yayi”
Numfashi kawai Muhsin yaja yana fitarwa batare da ya sake cewa komai ba. Duk da shine sama da Huzaifa din, bai ja maganar ba saboda bayason ya kara tunzura shi. Yafi so yaga anbi komai a hankali, duk yanda zasu kai da kin Hamza idan zaman su bai kare da Hindu ba yasan haka zasu hakura suna gani ta koma. Sam ba zai so su biye mishi ya kara zubar da mutuncin shi a idanuwan su ba, ko babu rabon komawa akwai ciki a jikin Hindu. Haka suka karasa gida babu wanda ya sake cewa dan uwan shi komai.
*
Baba da kanshi daya dawo sallar Asuba ya shiga bangaren Anty yana fada mata abinda ya faru. Da yake uwa daban ce tun a daren jiyan taji a jikinta, dan haka kawai bacci ya kaurace ma idanuwanta, sai tunanin Hindun daya cika mata zuciya. Kuma ta kasa tashi tayi sallah ko da raka’a biyu ce, jin Mama na tare da Hindun yasa tayi alkunya tana kasa shiga duk yanda zuciyarta take son ganin halin da take ciki. Da yake ita bafullatana ce, lokaci zuwa lokacin fillon na motsa mata. Tana zaune a daki, ta saka wannan ta kwance har karfe bakwai na safe.
Kafin ta fito daga dakin tana shiga kitchen, kowa girkin shi yakeyi tun suna da kuruciyar su. Sai dai yaran duk abinda sukaji suna marmari da aka dafa a gidan shi suke ci, cikin ikon Allah da yake Baba tsaye yake akan gidan nashi, kishin dake tsakanin matan da ba’a iya kauce mishi baisa kan yaran ya rarrabu ba, duk da zaka gane yan daki daya daga yanayin shakuwar su, amman suna kamanta zaman lafiya dai-dai iyawar su, kuma suna kokarin ganin ko da sun sami sabani basu saka yaran a ciki ba.
Asma’u da suke kira da Asma ta samu harta tashi tana soya dankalin turawa
“Ina kwana Anty”
Ta fadi tana daukar soyayyen dankalin guda biyu ta saka a bakinta
“Lafiya kalau… Harkin tashi”
Kai Asma ta jinjina wa Mama tana dorawa da
“Ina da Test da safen nan”
Ta sake saka hannu cikin dankalin ta dauki guda daya
“To ko kibari in karasa kije ki shirya karki makara”
Murmushin jin dadi Asma tayi dan inta tsaya karasa suyar dankalin zata iya makara, tunda karfe takwas da rabi malamin yace. Bata tsaya jan magana ba ta fice daga kitchen din tana wucewa dakinta. Tsaye Mama tayi a kitchen din komai baya mata dadi, kafin taji sallamar Hindun da ta sakata juyawa cikin hanzari tana fadin
“Hindu…”
Itama da ta samu tayi sallar Asuba, bacci ne ya dauketa sai yanzun nan ta tashi, wanka kawai tayi tana zira doguwar rigar da Mama ta ajiye mata kan gado, son ganin Anty taji tanayi ta kuma son halinta, sam ba zuwa zatayi inda take ba, shisa ita ta lallaba ta taho. Ganin Antyn da yanda ta kira sunanta suka hadu suna kara karya mata zuciya, batasan lokacin da wani irin kuka ya kwace mata ba tana karasawa ta fada jikin Anty da duk damuwar da take ciki bai hanata fadin
“Karki kayar dani Hindu, kinga ga mai a wuta. Kiyi hakuri kinji ko”
Ai kamar hakurin Antyn take jira wani sabon kuka ya sake kwace mata, duk yanda taso ta boye halin da aurenta yake ciki saida Hamza ya kure duk wani zabi da take da shi,a hankali Anty ta dagota daga jikinta tana fadin
“Kinci abinci?”
Kai Hindu ta girgiza, ko kadan ta manta da wani abinci, da gaske yunwa ma sai kana cikin kwanciyar hankali kake jinta. Sai yanzun da Anty tayi mata maganar abincin ne ma taji yaron cikinta ya juya mata da alamun yunwa, shisa dazun data mike taji jiri na shirin dibarta, bayan hannuwanta tayi amfani dasu wajen goge fuskarta
“Kije ki zauna in zubo miki”
Kai Hindu ta iya dagawa Anty, tana wucewa falon ta samu kujera ta zauna, dan inta zauna kasa wajen tashi wahala take sha saboda cikin da yake jikinta. Tana zama Asma na fitowa daga daki ta shirya tsaf cikin kayan da Hindu bata gani saboda Abaya da Asma ta dora a kansu, kanta sanye da bakar hula mai duwatse, tayi kyau cikin kwalliyarta mai sauki, da sauri cike da farin ciki ta karaso inda Hindun take tana fadin
“Yaa Hindu”
Kafin tadan dakuna fuska cike da tunanin da yazo mata na me Hindun takeyi a gida da sanyin safiya haka, tukunna ta kula da idanuwan ta da dukkan fuskarta da suke a kumbure da alamun kuka, walwalar fuskar Asma ce ta dishe, damuwa na maye gurbinta
“Asma…”
Hindu ta kira sunan kanwar tata cike da duk wani karfin gwiwa da zata iya tattarowa wajen ganin bata fashe da kuka ba. Gefenta Asma ta zauna tana jin gabaki daya komai yai mata tsaye, kafin tace wani abu Anty ta fito daga kitchen hannunta rike da faranti da dankali a ciki, dayan hannunta da ruwan shayin da ta hada
“Ke ba makaranta zaki tafi ba kika sami waje kika zauna”
Kallon Anty tayi, da bata furta suna da test ba, ita kam batajin zata tafi tabar Hindun cikin wannan damuwar da take gani shimfide akan fuskarta, turo labbanta tayi tana sa Hindu fadin
“Ki tashi karki makara Asma… Ina nan ai har ki dawo”
Idanuwanta Asma ta dauke daga kan Anty tana dawo dasu kan Hindu cike da alamun tambayar dake fassara ‘Kinyi alkawari?’. Kai Hindu ta daga mata tana dorawa da
“Da gaske”
Tukunna Asma din ta mike, kitchen ta wuce tana dan dibar dankalin ta zuba a murfin kular da yake ciki dan ba zata iya tsayawa daukar wani kwano ba, tea ta hada tana shan shi a tsaye cikin sauri kafin Anty ta shigo taganta ta zageta tana cin abinci a tsaye. Tana gamawa ta mayar da kular ta rufe tana fitowa da gudu-gudu ta shiga dakinta tana dauko mayafin Abayar ta nada a saman kanta sai jakarta ta gefe, ta zira takalma tana fadin
“Saina dawo”
Fatan alkhairi Hindu da Anty sukayi mata, ko amsa basu samu ba saboda saurin da takeyi. Kofin shayin da Anty ta bata ta karba tana fara kurba, hadi da dibar dankalin tana ci, ko rabi batayi ba taji yaron cikinta ya harba tamkar abinda taci din harya isar mishi. Jin da tayi komai ya hargitse mata lokaci daya yasata ajiye kofin hannunta tana kiran sunan Allah kafin ta mike cikin hanzari tana nufar bandakin baki da yake cikin falon hadi da tsugunnawa kan gwiwoyinta tana fara kelaya amai tamkar zata amayar da hanjin cikinta, ko sannun da Anty take mata bayan ta shigo bandakin bata iya amsawa ba. Amai take babu kakkautawa har mamakin ta inda yake fitowa takeyi dan tana da tabbacin iya dan abinda taci yanzun nan ya gama fitowa.
Baba ne ya shigo dan yaje bangaren Mama baiga Hindun ba, hankali a tashe ya tsaya daga kofar bandakin yana fadin
“Subhanallah… Me ya sameta?”
Dan rausayar mishi da kai Anty tayi, mai ciki ai ba’a rabata da laulayi kala-kala, mai dalili da akasin haka. Damuwa ce fal a ran Anty da take kokarin boyewa a fuskarta. Ita ta zubama Hindu ruwa tana kuskure bakinta ta kuma wanke fuskarta. Kafin ta dafa sink din tana mikewa dakyar
“Ki dauko mata hijabi mu tafi asibiti… Harda ruwan jiya daya daketa”
Baba ya fadi yana karasa maganar da wani yanayi a fuskar shi, a kasan ran shi yanajin yanda bazai taba yafewa Hamza wannan rashin arziqin ba, murya cike da rauni Hindu tace
“Baba ba sai munje asibiti ba, tunda daman gobe in shaa Allah zan koma awo…”
Kai Baba yake girgiza mata
“Ki kalli yanda kike magana dakyar Hindatu, kice ba sai anje asibiti ba? Kina wasa da lafiyarki ko?”
Dan murmushi Hindu tayi, a fuskar Baba take ganin shine namiji daya a rayuwarta da ba zai taba karya mata zuciya ba, namijin da bai taba karya alkawurran da bai ma daukar mata ba amman yake cikawa a duk rana. Tana kuma jin yanda shi kadai ne dalilin da zai sa ba zataiwa mazan yanzun jimlar marassa mutunci, marassa adalci, marassa tausayi ba. Wata irin kaunar Baban taji cike fal da zuciyarta da take ciwo
“Baba Allah ba sai munje ba, da nayi bacci shikenan”
Badon ran shi yaso ba, sai don bako yaushe yake iya matsama Hindun ba, ko da kuwa a yanayi ne irin wannan.
“Allah ya kyauta, ya kawo sauki…ki kwanta ki huta kinji ko? In dai kika karayin amai asibiti zamu je”
Murmushin karfin hali Hindu tayi tana dan dagama Baba kai, Anty kuwa kallon su takeyi, kaunar dake tsakanin su ba sabon abu bane a wajen ta, lokutta da dama idanuwa take binsu dashi. Baban da kan shi ya taka ya raka Hindu har dakin Asma tukunna ya fito yana kallon Anty da fadin
“In ta sake yin aman ki kirani mu tafi asibiti…zan karya in kira su Muhsin dan nace su kwaso kayanta”
Kallon shi Anty tayi, cikin taushin murya tana fadin
“Alhaji anyi saurin kwaso kaya? Da an bari an kira shi anji me ya hadasu tukunna”
Wani irin kallo Baba yakewa Anty
“Yazo aji me? Ya korar mun yarinya tsakiyar dare, da tsohon ciki tukunna in kira shi? Yace mun me? Ni ince mishi me? Bafa gajiya nayi da kulawa da ita ba, ba kuma kasa ciyar da ita nayi kafin yazo ya tsugunna ya nemi aurenta in dauka in bashi ba, ya wulakanta mun ita haka kice mun in saurari me ya hada su”
Ganin yanda ran Baban yake a bace yasa Anty fadin
“Kayi hakuri”
Dan tasan halin shi, idan ran shi ya baci babu abinda zai saurara, musamman kuma yanzun an taba yar gaban goshi Hindu. Ai tasan sai abinda Allah yayi, ita bataso a yanke hukunci ba’a duba duka bangare biyu ba, dan hakan ne adalci, dan kyautawa ko kadan Hamza bai kyauta ba, ko ita ranta yana kan sosuwa da abinda yayi din, amman zai iya yiwuwa tayi mishi wani abin ne, batajin namiji zaiyi irin wannan hukunci batare da kwakwwaran dalili ba.
“Kawai dai ina jinjina yanda zaiyi irin wannan hukuncin batare da wani dalili bane, shisa nake so aji nashi bangaren”
Antyn ta sake fadi ganin kamar Baba zai saurare ta, karamin tsaki yaja yana ficewa daga dakin kawai, dan idan ya tsaya fada zasuyi da sanyin safiyar nan. Baisan me yasa Antyn take magana kamar ba mace ba, da ya kamata tayi kishin abinda akaiwa yarta, baice kar a kyautata ma dan adam zato ba, bai kuma ce abinda take so ayi din ba mai kyau bane ba, asalima hakan shine adalci. Amman baiga dalilin da zaisa a kowanne yanayi sai anma jinsin shi na da namiji uzuri ba, ko wanne irin abu namiji zaiyi sai an so juya abin ya koma kamar ita macen ce da laifi. Na rana daya ya kamata a kalli mace cikin kuncin da namiji ya kunsa mata a karbi korafinta batare da kokarin gano me tayi da ya ba namijin dalilin yin abinda yayi.
A ganin shi babu wani uzuri da zai karba akan abinda Hamza yayi, kowanne irine kuwa. Daya rufe idanuwan shi Hindu yake gani tsamo-tsamo cikin tsakiyar ruwa da tsakar dare, inda maigadi bai taimaka ta kira shi ba haka zata kwana cikin ruwa, a kofar gida. Ko da wani bai cutar da ita ba, sanyi kadai ya ishi yai mata illa mai girma, ga cikin da yake jikinta. Kirjin shi ma zafi yakeyi ba kadan ba, idan baiga an kwaso kayan Hindu daga gidan marar mutuncin nan ba hankalin shi bazai kwanta ba, indai harya isa yana kuma da cikakken iko akan yar shi ba zata taba komawa gidan Hamza ba.
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: 17
“Baba ni ina son shi”
Hindu ta furta kalaman da ko a mafarki batayi tunanin zata iya gayawa Abba su ba, duk kuwa kusancin da yake tsakanin su, saboda kunya. Anty ma tun satin daya fita sai ta whataapp ta tura mata sakon cewa tayiwa Abba magana Hamza yace zai turo. Amman yau tura ce ta kai bango. Kiri-kiri take ganin yanda duka yan gidan suka juya mata baya kan maganar Hamza. Kuma Zaid ne, duk shi yaja da zancen binciken shi, batama ga matsalar shi akan maganar aurenta ba, yanzun ma da take tsugunne a gaban Baba idanuwanta cike suke taf da hawaye
“Mahaifiyar shifa ba’a san asalinta ba”
Zaid ya fadi, bayan wannan, har kauyane su Appa saida yasa aka bincika mishi, kuma ya samu tabbacin labarin su, kasancewar mahaifin Hamzan maraya. Amman ita mahaifiyar kanta batasan inda danginta suke ba tunda ta dawo Najeriya. A ganin Zaid ta fannin uwa da uba Hamza bashi da wasu dangi tsayayyu, sai yan uwan shi guda biyu. Duk da kowa a unguwar ya bada shaida me kyau akan mahaifin Hamza, haka shi kanshi Hamzan duk da ance yana da zafin rai, amman abin hannun shi bai rufe mishi ido ba tun bayan samun shi.
Kawai akwai wani abu tattare da Hamzan ne da yaki kwantama Zaid shisa ya labe bayan rashin tsayayyun dangin da Hamza bashi dasu ya cewa Anty ayi mata magana ta hakura. Amman ta kafe, shisa ma yazo da maganar wajen Baba.
“Kai da bakin ka kace kowa ya fada maka iyayen shi mutanen kirki ne”
Hindu tayi maganar tana share hawaye
“Ta shi kije abinki”
Baba ya fadi, ta kuwa mike dan bataga wanda ya isa yasa ta rabu da Hamza akan wannan dalilin ba, balle yanda yake nuna mata kauna a cikin satin. Kusan kullum sai yazo makarantar su, dan ma batada wani lokacin da zasu fita, haka suke takawa cikin makaranta suna hira, tana bala’in jin dadin yanda ake binsu da kallo cike da sha’awa. Tana kuma jin dadin yanda ko abu ya sai musu shi yake rikewa, kuma har kofar aji yake rakata, su gaisa da wasu cikin Malaman da suka san shi, dan ya farfada musu ita ce zai aura. Da yawa a ciki kuma sun nuna jin dadin su da maganar.
Shine Zaid zaiyi mata kafar ungulu a cikin lamarinta. Ita zata zauna da Hamza, idan rashin tsayayyun dangin shi bai dameta ba, bataga dalilin da zaisa ya dami kowa ba.
“Yana da asali me kyau Zaid, tana kuma son shi. Babu wani dalili mai kwari na hana mishi aurenta…”
Baba ya fadi, numfashi Zaid ya sauke
“Wallahi Baba akwai wani abu a tattare dashi da baiyi mun ba, na rasa menene, amman har raina bana son shi da Hindu, in dai za’a bi shawarata a hakura. Allah ya kawo mata wanda yafi shi”
Murmushi Baba yayi, yana da tabbaci duk yanda Zaid yake kaunar Hindu bai kai shi ba
“Babu wani abu a tattare dashi banda kaunar kanwar ka da kakeyi, kuma wannan shine soyayyar da zaka nuna mata, kasan tunda macece dole irin ranar nan zata zo daman….da zaka mikama wani amanarta”
Kai Zaid ya jinjina, Allah ne shaidar shi, yayi duk kokarin da zai iya. A wannan matakin yanajin addu’a ce kawai take rage mishi
“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi”
Ya furta
“Amin. Yawwa, ko kaifa”
Mikewa kawai Zaid yayi ya fice daga dakin Baban yana nufar nasu Hindu, kwankwasawa yayi hadi da sallama, sai da yaji ta amsa mishi tukunna ya tura dakin ya shiga. Tsaye yayi a bakin kofa yana kallonta, yanayin fuskarta ya tabbatar mishi da cewar kuka tayi
“Nasan kina jin haushina, kina ganin kamar na shiga abinda na hurumina ba, ba ko yaushe nake jin abu akan mutum bai zamana gaskiya ba. Ina miki fatan alkhairi a ko da yaushe, Allah ne shaida bayan Anty da Baba, kece ta farko a cikin jerin sunayen da suke fita bakina duk sujjadar da zanyi…”
Haka kawai tunda ya fara magana take jin hawaye na zubar mata, da batama yi kokarin goge su ba, tunda taji suna tukundedeniya da juna wajen fitowa tasan bata isa ta tsayar da su ba
“Yanzun ma bazan daina ba, Allah yasa shine alkhairin ki. Nasan kuna tsorona, kuna ganin kamar ba zaku iya tunkarata da kowacce magana ba, Hindu wayata kawai zaki kira idan kina bukatata, kina jina? Kar halina ya taba nisantaki da neman taimakona idan kina bukatar hakan”
Bai jira amsarta ba ya fice daga dakin, saboda bayason kukan da takeyi. Gabaki daya sai taji maganganun shi sun karya mata zuciya, tana so ya yarda da zabinta, tana so ya yarda tayi hankalin da zata san abinda ya kamace ta da akasin hakan. Ta jima tana kuka kafin taje ta wanko fuskarta. Tana dawowa taga wayarta tayi haske, dauka tayi ta duba, taga Baba ne yai mata text
“Ranar juma’a ko asabar, sai su zabi daya. Ki sanar dani”
Murmushi tayi, zuciyarta na samun natsuwa, itama text din ta tura ma Hamza
“Baba yace ko juma’a ko asabar”
Dan ya matsa mata da maganar har fada sukayi da tace mishi Baba yace a dakata tukunna
“Ki fada musu, Hindu ki fada musu bazan iya rabuwa dake ba gara ma su bani dama in turo”
Shine abinda ya fada mata, yaki kwantar da hankalin shi duk yanda take kokarin ganin ta kwantar mishi da shi
“Yau baccin da zanyi daban ne”
Ya dawo mata da shi yana dorawa da
“Zan kira ki”
Suna Kano tun ranar alhamis, yau litinin, kwanan su hudu, sosai tayi kewar shi, duk video calls din da sukeyi, duk kuma aikin da yakeyi sai ya mata ko da text ne. Haka ta wuni a daki, daman karatun jarabawa takeyi, Hamza yace karta bashi kunya, mutane biyu kenan yanzun a rayuwarta da bataso suga gazawarta ta fannin karatu, shi da Baba. Basu kara waya da shi ko magana ba har dare, tunda ta fita taga irin kallon da Anty take binta da shi ta rufama kanta asiri tayi zamanta a daki. Abincin dare ma Asma ce ta zubo musu, Hindu na ganin ita Anty tabi maganar Zaid batare da ko Hamza tagani ba, balle ta bashi dama ya nuna mata yanda suke kaunar junan su, kuma ba haka bane ba, kamar yanda Zaid yakeji Hamza yaki kwanta mishi haka itama Antyn, sai dai tana addu’a sosai akan maganar.
Gajiya tayi ta yanke hukuncin lekawa whatsapp dinta taga ya ake ciki, ko group din ajine ma ta shiga, ba za’a rasa abinda zai sakata dariya ba, dan shaftar su bata karewa sam. Haka suke fama kullum, status ta shiga, ta ga Hamza ya saka minti daya daya wuce, ba sosai yake saka status ba, yana iya sati daya bai saka ba, idan yasa ma bazai wuce zane ba, ko hoton su shi da su Fodio. Budewa tayi tana cin karo da hoton AbdulHafiz da Nabila, tana sanye da alkyabba, shikuma da manyan kaya, kanshi nade da rawani, sunyi mata kyau na gaske, har ranta tana son ganin fuskar Nabila gabaki daya.
Yanzun ma idanuwanta kawai take iya gani
“Wedding bells”
Hamza ya rubuta, yana saka Hindu tambayar
“Bikin shi ya matso ne?”
Kafin tayi gaba tana sake ganin wani hoton
“Saraki na Fulani. Allah ya kaimu lokacin”
Sai take ji kamar ta janyo juma’a ko asabar, tasan ranar da zata fara duba kasancewar irin hakan a tata rayuwar, sauran hotunan ta gama gani da sukai matukar yi mata kyau, kafin taga Hamza ya amsata
“Eh saura kwana talatin, sun sa ina jin kamar ace namu ne”
Murmushi Hindu tayi, kafin ta amsa shi ya sake fadin
“Nace ma AbdulHafiz sai munfi su yin kyau, yana mun musu”
Sosai ta murmusa yanzun, ya sosa mata inda yake mata kaikayi, tunda suka fara maganar aure tagane Hamza na da burin biki dai-dai da nata.
“Ka kyale shi, zamu bashi mamaki in shaa Allah”
Ta amsa
“Allah yasa alkhairi, kace ina mishi fatan alkhairi”
Ta fara rubutu, kiran shi ya shigo, ta daga ta kara a kunnenta
“Ga AbdulHafiz din ki fada mishi da kan ki”
Hamza ya fadi, kafin ta numfasa taji sallamar shi data amsa a kunyace
“Ina wuni… Ya aiki?”
Ta fadi muryarta can kasa
“Alhamdulillah. Ya makaranta?”
Amsa shi tayi da
“Mungode Allah. Allah yasa alkhairi ya kaimu lokacin lafiya”
Bata taba tunanin murya zatai mata kwarjini haka ba sai yanzun da taji ta AbdulHafiz, kuma a cikinta zaka fahimci natsuwar da take tattare da shi
“Amin thumma amin. Nagode. Allah ya kaimu naku. Ga Hamzan”
Tana jin muryar Hamza tace
“Ban shirya ba kawai ka mika mishi wayar”
Dariya yayi
“Wai me yasa AbdulHafiz yakewa mutane kwarjini haka?”
Wannan karin ita tayi dariyar
“Yaushe zaka dawo?”
Zata iya rantsewa girar shi ya daga mata kafin ya amsa
“Bawani nan, sai yau? Ba kinayi kamar ni kadai nake kewarki ba”
Runtsa idanuwanta tayi tana sake budesu, ta tsokalo ma kanta rikici
“Yi hakuri, ina kewarka Allah. Yaushe zaka dawo?”
Saukar da murya yayi
“Ban sani ba fa, kinga bikin AbdulHafiz ba’a saka da yawa ba, idan mun dawo zamu fara hidimar tafiya Gombe ne, gara mu rage aiki sosai sosai. Gobe dai zanyi magana da Appa, sanda zan dawo in shaa Allah muna kirga kwanakin bikin mu”
Murmushi tayi
“Allah ya kaimu, yanzun zan kara wasu satika ban ganka ba?”
Tayi maganar, kewar shi na danneta, kamar tayi fuka-fuki taje Kano tagan shi ta dawo
“Zaki ganni harki gaji idan na dawo, In shaa Allah. Idan bakiyi bacci ba zamu karayin magana, yanzun zamu fita dasu AbdulHafiz”
Kai ta jinjina mishi tana dan sauke wayar daga kunnenta taga tara da rabi
“A dawo lafiya, ka kula da kan ka, kace Fodio ya kulamun da kai”
Tanajin dariyar shi ta cikin wayar kafin ya kashe, yanzun harta saba da yanayin yanda Hamza ya kare wayoyin shi, baya jiran sallama, daya gama fadar abinda zai fada yake kashewa. Sauke wayar tayi da murmushi a fuskarta, Instagram tahau dan tasan yau zata ga soyayya, tana hawa shafin AbdulHafiz din ta fara zuwa, ta kuwa ci karo da hoton daya dora, na Nabila din, an saka shi a baki da fari, da alkyabba a jikinta, da alamu a zaune take, ta daga hannunta ta kare rabin fuskarta da shi
“Allah ya bani aron rayuwa mai tsayi a tare da ke Fulani, ban tana tunanin kwanaki talatin zasuyi mun yawa har haka ba”
Zuciyarta Hindu taji ta cika fam, kamar ta sace AbdulHafiz din haka take ji, wani irin burgeta kalar soyayyarsu takeyi, amman ko da wasa har yanzun Hamza bai taba saka hotonta ba, kwanaki ya saka na Mansy a avi din shi, tabi ta cire, ta jira yayi mata magana yanda zasuyi tashin hankali, sai baice mata komai ba. Ranta yayi matukar baci, har yanzun idan ta tuna sai taji ran nata ya kara baci. Musamman idan tazo taga AbdulHafiz din yanda duke gurzar soyayyar su shida Nabila, ta tabbata ita take kara musu yawan mabiya a Instagram din. Fita tayi tana komawa shafin Nabila, hotuna biyu ne ma ta saka, wani jiya, wani kuma yau.
Na jiyan ta fara dubawa, AbdulHafiz ne zaune a cikin mota, da murmushin nan har dimple din shi ya fito sosai
“Bacci ya kaurace ma idanuwa na, ina jiran wayewar garin da zata kusanta ni da zama taka”
Bude comment section din tayi, tana lalubo na AbdulHafiz da tasan dole ne sai yayi magana.
“Soyayyar ki alkarya jikar Shehu”
Tashi zaune Hindu tayi, tana tunanin yanda za’ayi su fara wannan soyayyar da Hamza. Hoto na biyu ta shiga, ita da AbdulHafiz dinne,a wani falo, tana zaune akan kujera ya tsaya daga bayanya ya daga yatsun shi guda biyu yana dariya
“Saraki”
Kawai ta rubuta sai hoton zuciya. Shima kuma da hoton zuciyar ya bata amsa, ko da bata saka komai ba, yanayin hoton zai fada maka kalaman da basu rubuta ba. Sai take jin kewar Hamza ta danneta fiye da kullum. Twitter din shi taje tana kai daman, taga Mansy tayi tagging din shi a wani abu da yaren fulatanci, tsaki taja, ta duba DM din shi tana ganin sakon Mansy din
“Na kira ka baka dauka ba. Ina kewar ka sosai”
Wannan karin tsakin da Hindu taja sai da Asma da take kwance, kunnuwanta manne da earpiece ta juyo tana cire guda daya ta kalli Hindun
“Ba dake nake ba”
Hindu ta fadi, Asma ta mayar da earpiece dinta, dan mp ce ma, ta saka karatun Qur’ani tana bi dan yafi mata sauri wajen rikewa, kafin lokacin da zasu bayar da hadda yazo sai taga har taci karfin karatun
“Wawiya kawai, mata sai kace mayya”
Hindu take fadi kasa-kasa kafin ta goge sakon. Yanzun haka takeyi mata, in dai zata ga sakonta sai ta goge, idan tayi unfollowing da blocking da Hamza yahau yake sake following ya budeta, sai ta kyale shi, sakone in ba ya rigata hawa ba sai dai suyi waya. Gabaki daya Mansy ta gama bata mata rai, tana cikin farin cikinta, da ta sani ta tsaya ma taci gaba da kallon soyayyar su AbdulHafiz da yafi mata, addu’a tayi tana juya kwanciya, taja ma Hamza, ba zata jira shi ya dawo ba. Baccinta tayi cike da mafarkin bikin su da Hamzan.
*
Basu dawo Kaduna ba sai satin bikin AbdulHafiz, washegari zasu wuce Gombe, shisa suna isowa ya fara sauka gida dan yaga Anna, ruwa kawai ya watsa, yaci abinci ya bar gidan, sallar Magriba ma a hanya ya tsaya yayi. Hindu kawai yake son gani har wani iri yake ji saboda kewarta. Ranar da yayi wa Anna maganarta, tambayar farko da tayi mishi shine
“Yar gidan wacece ita din?”
Dan bataso ya dauko yarinyar da zata saka mishi ido a abinda yake da shi, yarinyar da kudin shi zai zame mata abin alfahari, tafi son yarinyar duk da zai dauko mata a matsayin suruku, kudi ya zama dalili aqalla na biyu na auren shi, hakan zai rage mata tsoron za’a shiga tsakaninta da danta. Duk bayanin da Hamza yayi mata kasa samun natsuwa tayi, har sai da Appa ya tabbatar mata da cewa yarinyar yar mutunci ce, kuma suna da tasu wadatar dai-dai misali. Auta ce ma ta tsare shi da tambayoyi sai da ya zageta
Yana son su, Allah ne shaida zaiyi komai saboda kannen shi, sune dalilin farko na sakashi jajircewa wajen ganin ya samu kudi, saboda bayaso su sha kalar wahalar dashi ya sha, yana so komai yazo musu da sauki, amman ba zai dauki su saka mishi ido akan abinda na huruminsu bane, ko hotonta da Auta tace ya nuna mata haka yace mata
“Me zakiyi da shi? Saurin me kikeyi?”
Dan murmushi Autar tayi
“Kawai zan ganta ne, ko ta dace da kai”
Girar shi ya daga mata duka biyun yana daure fuska sosai
“Kina so ki bani kunya ne Auta? Kina so ki zama irin kannen mijin da suke kushe zabin Yayyen su ko? Ni ban san abinda ya dace dani ba sai kin tayani? Bana so, kina jina? Zamuyi fada dake sosai idan kika fara wannan halin”
Ko Anna da ta dinga mishi tambayoyi akan Hindu dole ce ta saka shi amsawa, Anna ce, babu yanda zaiyi da ita. Amman ya tsani yanda ake magana akan dangin miji, bayason yanda suke yankewa yaran mutane hukunci batare da sun basu damar nuna asalin halayen su ba, sai kaji daga ganin hoto ana fadin
“Ga idon ta na a tsaye, da ganin wannan yarinyar fitsararriya ce”
Sai anje lahira an saka su a layi su farayi kamar masu ciwon asma, babu wata kwakkwarar shaida sai suyita yanke ma yaran mutane hukunci, ba tun yanzun ya saka a ran shi soyayyar da yake ma su Auta ba zata sa ya basu fuskar da zasu raina mishi yarinyar duk da zai kawo a matsayin mata ba, koya take kuwa, idan harya ce itace zabin shi dole su girmama hakan. Da Appa ya nemi zabin shi akan ko wata nawa ya kamata a saka, haka yace a tambayi Anna daman, ita kuma tace ko wata uku ko biyu, dan ta kaqu taga Hamzan ya nutsuwa waje daya.
Wata ukkun kuwa akasa ana dai-daita shi dana Khadee, sosai Hamza ya natsu akan karasa gidan shi, da suka tafi Kano ma Abdallah yabari kan komai tunda batare dashi akaje ba, kuma ginin yana tafiya kamar yanda ya tsara abin shi, tare kuma da kudaden da suke ajiye a bankin shi. Tunda aka saka ranar kullum cikin maganar yanda bikin zai kasance sukeyi shi da Hindu, dan biki yake so ayi na kece raini, tunda harya yanke hukuncin yin aure, kowa zai shaida yayi aure. Wani numfashi ya sauke da yayi parking din motar shi a cikin gidansu Hindun yana kiran wayarta ya fada mata ya iso.
Kafin ta karaso ya fito daga cikin motar, tana ajiye kujerun da ta dauko musu taji ya rike hannunta, kafin tayi wani yunkuri ya riketa a jikin shi yana sauke numfashi
“Nayi kewarki…”
Kwacewa tayi jikinta na bari, sai ware mishi idanuwa takeyi har yaja kujera ya zauna, sai da ya sake kama hannunta yana zaunar da ita. Gani takeyi kamar wani yagan su, ga wa’azin da Khadee ta turo mata shekaranjiya kan yan mata da samarin da suke wannan ‘yan rungume rungumen zamanin kafin aure. Sai taji kamar dan ita da Hamza akayi wa’azin, ko da hannunta ne sai ya rike duk yanda zata nuna mishi bataso, tun da aka sa ranar kuma tayima kanta alkawari daman ba zai sake tabata ba, balle da taji yanda albarkar auren duk take zirarewa tun kafin ayi shi, ga tarin rashin yardar da yake biyo bayan auren.
Banda zunubin da in ba tuba sukayi ba, sahihin tuba irin wanda ta dingayi kafin ya dawo yanzun nan cikin wasu dakika ya kwance mata hannun agogo yana dawowa da shi baya, tayi niyyar har sai ta zama mallakin shi inda duk wani riko da zaiyi mata zai zamana cike da lada
“Bansan sau nawa kake so ince maka ka daina tabani kafin kaji ba, kana ta zubar mana da albarkar auren”
Numfashi Hamza ya sauke, da tasan yanda yake kokawa da kanshi a duk rana akanta da bata ce mishi haka ba, da tasan irin matan da yabi a Kano dan in yazo karya riketa da bataga gajen hakurin shi ba, itace mace ta farko da yake kasa controlling kan shi a kanta
“Bana so inyi fada dake nikam, nayi kewarki da yawa”
Ya fadi yana gyara zaman shi hadi da zuba mata idanuwan shi, hakan yasa ta danyin murmushi, itama batason yin fadan da shi
“Nima nayi kewarka ai”
Dan tabe mata baki yayi, tana ganin yanda yanayin ya kara mishi kyau
“Bawani, saura kwana 72 a daura mana aure”
Dariya Hindu tayi
“Kai ko?”
Ta fadi, yana dakuna mata fuska
“Ke baki damu ba shisa bakya lissafawa, nikam dana damu kinga ina kirgawa ai”
Ya karasa maganar yana saka hannu a aljihun shi ya cire zoben daya siya. Azurfa yaso siya, Fodio yace ya sai mata gold zaifi duk wani tarkacen tsaraba da zaiyi mata, yaga mata naso, dan kanwar Fodio din suka kira suka shiga kasuwa tare. Dubu dari da goma wanda ya siya, badan bashi da halin siyan wanda yafi shi ba, kawai sauran sun mishi girmane sosai, wannan din dai yafi mishi kyau sosai, in an tashi hada lefe ya saka mata wani a ciki, Anna ma tace mishi za’a saka.
Hannunta ya kamo, kafin tayi magana taga ya kama yatsanta na biyun yana zira mata zobe, kasa mishi magana tayi, ta ware idanuwanta ganin yanda zoben yake daukar ido a cikin hasken lantarkin dayake gauraye da gidan.
“Bansan me zan siyo miki ba”
Ya furta yana dago hannunta ya kalli zoben a jikin yatsanta
“Karki cire, nasan karami ne, zan sai miki wanda ya fishi girma”
Kallon shi tayi, wata irin soyayyar shi na cika mata zuciya fam, kafin a hankali ta zame hannunta daga cikin nashi, tana dago yatsunta, gyara ma zoben zama tayi, tana dan kara matse shi dan mai adjusting ne, ya zauna mata daras kamar dan hannunta akayi
“Ban san me zance ba”
Ta furta, dan godiya tayi kadan
“Kice kina sona”
Ya furta yana sake rike hannunta
“Ina son ka”
Ta fadi, tana saka shi dan dumtsa hannunta da yake rike da shi
“Bai fito daga zuciyarki ba”
Murmushi tayi
“Ni na fada maka haka?”
Kai ya jinjina
“Ni ne naji a muryar ki… Ki sake fadamun, ya fito daga zuciyar ki kamar yanda nake fada mishi”
Numfashi Hindu ta sauke
“Ina son ka”
Murmushi yayi yana sumbatar hannunta hadi da mikewa, ya tabbatar wayar shi daya bari su Fodio sun mishi kira yafi goma, tunda akwai abubuwan da zasuyi kafin goben su wuce Gombe
“Ina zaka je?”
Ta bukata tana shagwabe mishi fuska
“Kin gani ko? In rike ki kice nayi laifi, bayan ke kike karamun son ki”
Hamza ya fadi yana kallonta, murmushin da tayi na saka shi sauke numfashi
“Su Fodio na jirana, zamuyi abubuwa da yawa. Zan kiraki, dan Allah kiyi hakuri, dana dawo zaki samu lokaci na”
Kai kawai Hindu ta iya daga mishi, ya mika mata hannun shi, duk yanda zuciyarta take mata ihu, sai da ta mika mishi nata hannunta ya taimaka mata ta mike
“Ki kulamun da kanki. Ina son ki da yawa, kin san hakan ko?”
Kai ta daga mishi, hannunta ya sumbata kafin ya saki yana zagayawa ya shige motar shi, kujerun ta hade waje daya tana jansu gefe, kafin ta wuce gida. Sai da safe zata nuna ma Anty zoben, dan tasan yanzun tana wajen Baba, zatayi fada tace ita duk irin wannan gara yabari saiya aureta, amman abune da ko an sami matsala za’a iya mayar mishi da abin shi tunda ba siyarwa za’ayi ba, tasan Anty zata bar mata abinta, wayama da Hamzan ya sake mata, Anty ta fara fada, Zaid da kanshi yace ta kyale mata wayar, idan biyane ma Allah ya rufa musu asiri za’a iya biyan shi. Haka tayi zaune tana kallon hannunta, sai da ta hau whatsapp dan ta fada mishi yanda taji dadin kyautar, tana lalubo lambar shi, zuciyarta tai tsalle, ware idanuwa tayi tana bude profile din shi.
Ba gizo idanuwanta sukayi mata ba, hotonta ne a dp din Hamza, a karo na farko daya saka hotonta, da sauri ta wuce Twitter din shi tana ganin ya saka hotonta a header din shi, bai dai saka a avi ba. Kwanciya tayi kafin shauqi yasa ta narke, ita kadai take murmushi, ta kasa daina kallon kanta a header din shi na twitter, ta tabbata Mansy zatayi kwana bakin ciki yau
“Tsohuwar mai tallar goro yau za’a kwana ana juyi”
Ta furta a ranta, tanajin kamar taga Mansy din ta fada mata yanda Hamza yayi mata nisa har abada, yanda Hamza nata ne ita kadai, ba kuma zata rabashi da kowace mace ba, sai dai su kalla daga nesa subar mata abinta.
9/18/20, 9:50 AM – mmn khalid: 12
Bashi ya sami kan shi ba sai wajen karfe goma na daren ranar, wata irin gajiya yakeji har cikin kasusuwan jikin shi. Ko da Fodio yayi mishi tayin zuwa club, kai kawai ya iya girgiza mishi. Yanzun yana shigowa gida, ruwa ya watsa ya sake kaya yana fitowa falon gidan jin cikin shi da ya tattare ya kulle gefe daya saboda yunwar da yakeji. Wata zuciyar na mishi Allah ya kara da bai wuce gidansu ba, da yaci abincin Anna. Tunanin hakan kawai ya kara mishi yunwa. AbdulHafiz kadai ya samu a falon yana zaune kan kujera ya jingina kan shi, idanuwan shi a lumshe da earpiece a kunnuwan shi.
Dan tabashi Hamza yayi dan yasan ko yayi magana ba jin shi zaiyi ba, kunne daya na earpiece din AbdulHafiz ya cire yana kallon Hamza da fadin
“Meye ne?”
Saboda yanda ya takura shi, karatun Qur’ani yake ji cikin muryar Sheikh Abdullahi Abba, da Nabila ce ta koya mishi son qira’ar mutumin, lokutta da dama idan ya zauna shi kadai bayaso tunanin duniya ya dame shi yakan saurara, nutsuwar da take saukar mishi daban take, sam bayason ayi mishi magana a lokaci irin wannan
“Me kaci?”
Hamza ya tambaya, numfashi AbdulHafiz ya sauke, shisa yayo musu take away, wanda zaici yaci, wanda ba zaici ba ya saka a fridge, idan yunwa ta koro wani zai dunduma a microwave din da shi ya siya. Lokutta da yawa yana mamakin yanda zasuyi inda baya nan. Yasan yanzun haka kowa zai dawo da yunwa tunda ya rigasu barin wajen aiki, da tunanin shi din ya nemar musu abinda zasuci
“Ka duba Kitchen”
Ya fadi yana shirin mayar da earpiece din shi
“Me ka siyo? Meye?”
Harara ya watsa ma Hamza
“Karka dameni, kaje ka duba, idan bakaci ka ajiye. Dan Allah ka kyaleni”
Murmushi Hamza yayi, yasan magana ce AbdulHafiz din bayason yi, yana sane shisa yake son saka shi yinta dole
“Uban me kake ji?”
Hamza ya tambaya yana kai hannu ya cire earpiece din da yake hade da wayar AbdulHafiz din, sai dai zarewar da yayi ya saka karatun shiga Pause, numfashi AbdulHafiz ya sake saukewa, ya danna play, karatun na gauraye shirun da dakin yayi, kafin ya kalli Hamza, kallon da yake fassara ‘Sai kuma me?’. ‘Yar dariya Hamzan yayi yana girgiza mishi kai
“Ustaz AbdulHafiz, yau kuma Ash-Shura ake ji kenan. Allah ya bada lada”
Earpiece din AbdulHafiz ya mayar, yakan yi mamakin Hamza, babu inda zaka ja a Qur’ani bai cigaba ba, babu kuma inda yake mishi wuyar fahimta, yanda zai zauna yana ja maka ayoyi yana fassarawa, zakace bashi bane idan kuka hadu a wani club din da mace rungume a jikin shi, shisa duk a cikinsu yafi jin haushin lalacewar Hamza, gashi da sanin da zai amfani al’umma ba kan shi kadai ba, sam yabari shaidan yayi galaba a kan shi. Hamza kuwa kitchen ya wuce yana daukar take-away guda daya cikin wanda suke jere a kitchen din, ya bude fridge ya dauko coke ta gwangwani, ya dawo falon ya zauna kasa kan kafet yana budewa, soyayyen danlalin turawa ne, plantain, kwai sai naman kaza.
Sai da ya fara ci tukunna yai tunanin cire wayar shi daga flight mode din daya sakata dan kar wani ya dame shi da kira yana aiki. Duk yinin ranar tun da suka rabu da Hindu ta kara samun waje ta manne a cikin kan shi, zai rantse da Allah har yanzun yanajin yatsun hannunta a cikin nashi. Sai dai a cikin idanuwanta ya karanci bakuntarta a kalar tashi rayuwar, ta waye ta yanayin hirarta da maganganunta, amman ba kalar wayewar shi ba, idanuwanta ba’a bude suke ba, zai kuma ji dadi ya zama na farko daya bude mata su.
‘Ya gajiyar ki, kin ga ban kira ba ko? Sai yanzun na shigo gida ma, abincin zanci, nagaji har cikin kasusuwan jikina Allah’
Ya tura mata ta text, yana shiga tana biyo shi da amsa
‘Gajiya tana wajen ka ai, sannu. Sai ka kwanta ka huta’
Kai ya jinjina yana kurbar coke din shi
‘Sai naji muryarki tukunna’
Ganin ta dauki mintina bata dawo mishi da amsa ba, ya tabbatar da batasan yanda zata amsa maganar da yayi ba
‘Ke me kike yanzun?’
Ya bukata, ga mamakin shi ta whatsapp ta mayar mishi da amsa
‘Na dan yi karatu, ina da test. Ina zaune kawai’
Amsa ya fara rubuta mata, kafin tunanin kudinta ne zai iya karewa shisa tayi mishi magana ta whatsapp maimakon ta amsa mishi ta text ya fado mishi, sauka yayi daga whatsapp din, AbdulHafiz kance
‘Sai kayita chatting da yarinya, kasa ta turo maka hotuna ko video, ko kai ka tura mata. Na rana daya ba zakayi tunanin data dinta da kake kararwa ka tura mata da kati ba. Saboda rashin sanin ya kamata’
Duk shi ya koya musu wannan dabi’ar, Hamza ma ya rigada ya saba, ko ba budurwa ba, in yana tunanin ba wasu kudin kirki gareka ba, zai tura maka kati yace kayi sub da shi. Shisa yaran da kanyi aiki a karkashin shi suke yabawa da yanda bashi da mugunta, hannun shi kuma yake a bude. Yanzun ma bankin shi ya shiga yana tura ma Hindu katin dubu biyar. Kafin ya fita ma yaga sakonta ya shigo ta saman wayar. Budewa yayi yana ganin emoji din mamaki da ta turo mishi
‘Kai ka turomun da kati ko?’
Kafin ya amsa ta dora da
‘Har dubu biyar, katin dubu biyar. Yayi yawa’
Murmushi yayi, dan shikam bai dauki katin dubu biyar wani abu ba
‘Karkiyi ‘dan karatu’. Kiyi da yawa, ina son inga test score din idan kun gama’
Ya tura maimakon amsa abinda tace, da gaske yake kuma har ran shi, yana son gani, batayi mishi kama da marar kokari ba, tunda take Architecture, amman zaisa ta kara dagewa in har hakan zai yiwu.
‘Kar ka canza maganar nan’
Wannan karin shiya tura mata emoji din harara
‘Kar kiyi kamar baki gane bana son maganar ba, zan sauka idan kika sake mun’
Bayason godiya, shine lokaci daya da yakan tabbatar da yana da kunya. Musamman kan karamin abu kamar katin dubu biyar.
‘Yi hakuri. Nagode sosai sosai’
Haka kawai yaji ba zai iya hakuri ba, muryarta yake son ji har tsikar jikin shi tashi takeyi. Sauka yayi daga whatsapp din yana kiranta, bugun farko ta dauka, muryarta da ta daki kunnen shi na kara mishi yanayin da yake ji
“Da gaske jikina ciwo yake”
Ya sake fadi yana gyara zaman shi, yar dariya taji
“Na cika lalaci ko?”
Ya tambaya, yanaji a jikin shi kai ta girgiza mishi
“Ka gama cin abincin sai ka kwanta”
Dankalin ya diba yana sakawa a bakin shi ya tauna
“Bana son magana ina cin abinci, amman gashi na kira ki”
Yayi maganar da dukkan gaskiyar shi, hakan bai taba faruwa da shi ba, amman yanda yake son jin muryarta, da bai kira ba, abincin ma ba zai ciyu ba. AbdulHafiz da yake zaune ne ya kula da kamar waya Hamzan yake. Hakan yasa karatun da yake ji na karewa, kafin wani ya shigo ya tsayar yana zare earpiece din daga kunnuwan shi hadi da kallon Hamzan da matukar mamaki. Dan yanayin maganganun ya tabbatar mishi da ba Anna bace ba. Kuma yaga abinci yake ci, dan rankwafowa yayi yana kai hannu ya taba fuskar Hamzan daya janye yana fadin
“Zan kira ‘yan Hisba, lafiya? Ya kake taba mun fuska da daren nan?”
Dariya kawai AbdulHafiz yayi dan yaji lafiyar Hamzan kalau, babu zazzabi a jikin shi, coke din da yake ajiye a gaban shi ya dauka yana shinshina wa yaji ko ba zallar coke bace ba, dan sosai yake mamakin yanda akai Hamza yake magana yana cin abinci, bai damu da harar shi da Hamzan yake yi ba, ko yanda ya fisge gwangwanin coke din yana ajiye cokalin da yake hannun shi cikin abincin hadi da mikewa. Rigar shi AbdulHafiz ya janyo ta baya yana nuna mishi kwanon daya bari
“Dan Allah AbdulHafiz ka kyaleni, ban gama ba ai, abu zan dauko in dawo”
Hamzan ya fadi yana dakuna fuska, kitchen ya koma ya bude fridge, akwai section guda daya daga gidan saman, tunda fridge din na tsaye ne da babu mai taba mishi, karamar kwalbar giyar shi ya dauka yana kwancewa, a kitchen din ya tsaya, har lokacin da wayar shi manne a kunnen shi, yanajin Hindu na mishi bayanin tambayar da yayi mata, dan ta gaya mishi akan me test din da za’ayi
“Dubawa kikeyi ko? Bana son cheaters”
Dariyar da tayi na saka tsikar jikin shi ta shi, akwai babbar matsala, yai wannan tunanin yana daga kwalbar shi ya sha kusan rabi tukunna ya ajiye.
“Allah ban duba komai ba, inda ka tambaya tun jiya nake karantawa”
Kai Hamza ya jinjina mata yana sake daga kwalbar ya tuttula ma cikin shi, yanajin yanda jikin shi ya soma daukar dumi na daban, amman yaki dishe wanda muryar Hindu yake haifar mishi. Numfashi ya sauke mai nauyin gaske, yana saka Hindu fadin
“Gajiya ko? Ka kwanta dan Allah”
Kai ya jinjina mata
“Yanzun nan….zamuyi magana da safe?”
Sake ji yayi kamar ta daga mishi kai, kafin tace
“In shaa Allah. Allah ya hutar da gajiya. Nagode sosai”
Wayar ya sauke daga kunnen shi batare da yace komai ba, tukunna ya dauki kwalbar yana karasa shanyewa, ya jefa cikin kwandon shara, falon ya koma, yanajin idanuwan AbdulHafiz na bin shi da kallon tuhuma, a karo na farko da yaji dadi AbdulHafiz ne, ba zai taba tambayar shi ba, duk yanda yake so yaji kuwa, in dai bashi ya bude bakin shi yai mishi wani bayani ba, a cewar shi
‘Idan mutum naso kaji abu, zai fada maka da kan shi, lokacin daya shirya, ba saika matsa mishi da tambayoyi ba. Kuma babu kyau jin kwaf’
Gabaki daya rayuwar AbdulHafiz akan tsarika yake tafiyar da ita. Yau dai Hamza ya godema hakan sosai, saboda baya cikin yanayin da zai iya tsayawa bayani, robar da sauran dankalin yake ciki ya dauka da murfin yana mayarwa kitchen ya rufe ya ajiye. Sannan ya wuce dakin shi. Kayan jikin shi ya canza. Bacci ya kamata ace yayi, kafin ya kira Hindu ya sake rikita kan shi abinda yake da niyyar yi kenan. Amman yanzun kam labari ya sha banban. Akwai yarinyar daya kamata su hadu tun satin daya fita, ya tsaya yana mata yanga. Saboda ba ta wani yi mishi bane ba, balle kuma yanzun da idanuwan shi basa ganin kowa Sai Hindu, baya son kasancewa da kowa sai ita din.
‘Zamu iya haduwa nan da mintina talatin?’
Ya tura mata text din da yana shiga ta dawo mishi da address din inda zai dauketa din. Zai iya karasawa wajen cikin kasa da mintina sha biyar ma, in dai ba ya sami cunkoso a hanya ba. Mukullin mota ya dauka yana fitowa
“Komai zai iya faruwa da kai a hanyar zuwa din kafin ka karasa, ko idan ka karasa koma ina ne kake shirin zuwa. Zaka iya mutuwa a kowanne lokaci wallahi, tun da sallama takeyi ba”
Hanci Hamza yaja da yake jin kamar wani yaji a cikin hancin nashi da maganganun AbdulHafiz suka haifar mishi, kafin ya juyo ran shi a bace
“Me yasa kake son shiga rayuwa ta ne haka AbdulHafiz?”
Cikin takaici AbdulHafiz yake kallon shi, ya tsani kalar rayuwar nan daya zabar ma kan shi, ba kadan ba, har kasan zuciyarshi yake jin dacin hakan
“Na fada maka, mutuwa bata sallama, zata iya daukar ka ko me kakeyi”
Tsaki Hamza ya ja yana sa AbdulHafiz fadin
“Karka sake, bana so, karka sake mun tsaki Hamza, karka sake”
Yana sane yayi, bata mishi rai yake sonyi kamar yanda na shi yake a bace, duk da yasan ko me yasha ba zai sake din ba, baya kure hakurin AbdulHafiz din, ya tabayi sau daya, dakyar suka koma dai-dai. Bai sake ba, baya fata ya sake kuma. Juyawa yayi yana ficewa daga gidan. Yaji dadi da motar AbdulHafiz dince, ya ma manta bai karbi mukullin shi ba. A ciki zai dauki yarinyar, da ita kuma zaije hotel din da yayi niyya. Yasan dai inya dawo sai AbdulHafiz yasa an wanke mishi motar daga cikinta har wajenta, kamar wanda ya kwaso mishi wani mugun abu a jiki.
Baice ba zai daina halayyar da yakeyi ba, amman AbdulHafiz din yakan saka shi jin kamar lokaci zai iya kure mishi a ko da yaushe kafin ya tuba. Bayan shi bama kwana zaiyi ba, yana gama abinda yakeyi zai zare jikin shi, ya fito ya dawo gida, komin dare kuwa, bai taba kwana da wata yarinya a waje daya ba, idan ita bata kama hanya ba, shi zai kama, ko da a cikin hotel dinne, idan bayason komawa gida, zai fita ya sake kama wani dakin daban. Shi bama yason jin mutum a kusa da shi idan har bacci zaiyi, ko da macece kuwa, duk yanda yake son mata, baya iya bacci kusa da daya daga cikin su.
*
Ranta kal take jin shi tana gama waya da Hamza, duk yau taki sakewa ta fita falo ta zauna. Sai take ganin kamar Anty zata gane ta fita da wani, kamar zata gane Hamza ya rike hannun ta, ko da ta shiga alwalar la’asar bayan ta dawo, sai da ta saka sabulu ta wanke hannunta, ta jima a sujjadarta, cikinta ta dinga neman yafiyar Ubangiji, ko sallar isha’i da tayi hakan ya kasance, bata dago goshinta sai taji kafafuwanta sunyi sanyi. Saboda so take zunuban da take jin nauyinsu su kakkabe su fado. Sai dai zuwa yanzun da suka gama waya da Hamza, ba tunanin zunubanta takeyi ba, tunanin shi takeyi.
Muryar shi na amsa kuwwa a zuciyarta, koya ta juya sai taga fuskar shi a zuciyarta, murmushin rashin dalili takan ji ya kwace mata cike da wani irin shauki, sanin babu wani abin da zata iya tabukawa, yasa ta shiga manhajar Instagram dan ta more kallon hotuna, tana kuma son duba shafin teloline, har yanzun bata gama yanke hukuncin telan da zai mata dinkunan bikinta ba, so takeyi ta sami ko guda ukune, in yaso daga baya saita zabi guda daya. Haka kawai take jin kamar bikin nata ya matso kusa duk da ba’ayi maganar shi ba, zuciyarta bata taba gaya mata karya ba. Gara ta zaba da wuri kafin lokacin ya kure mata tazo tana hanzari a al’amarin.
Tana refreshing shafin tana cin karo da Nabila da ta saka hotuna har guda uku, tsayawa tayi na farkon ya bude. Sai taga AbdulHafiz ne, akan wani doki mai fari da ratsin baki, dokin kan shi koshin da yayi abin kallo ne, yana sanye da kayan sarauta a jikin shi, kan shi nade da farin rawani daya rufe rabin fuskar shi, da alamun murmushi cikin idanuwan shi, daga kasa ta saka caption din
‘Tafiya dai kwaro, bajimi sai horo, diyan ka basu ruwa. Jikan Shehu mai hidima, Allah ya kare mun kai Dikko na’
Sauran hotunan biyu takai da sukayi mata kyau matuka. Ita kam ba zasu daina burgeta ba, tana duba comments kuwa sai ga na AbdulHafiz a farko.
‘Gaba ke, baya ke, babu kamar ke Fulani’
Sai taji kamar fitilar Hamza nason dishewa a ranta. Akwai wani abu tattare da Sarauta da yake burgeta har cikin kasusuwan jikin ta, lokutta da dama takan ji daman ace ita din ta fito daga gidan Sarauta ne. Kasa duba shafikan telolin tayi, ta saka wayar a key tana yin addu’ar bacci, tukunna ta juya hannu tana lumshe idanuwan ta, da fatan Allah ya taimaketa ta samu bacci. Aikam baccin tayi cike da mafarkin Hamza ya zama sarki, ita kuma ta zama Sarauniya, tana gefen shi tsaye ana zuba musu kirari.
Ita kanta da safe da ta tashi sai da dariya ta kamata. Yau saboda tana cikin farin ciki kitchen ta wuce ta fara sharewa, babu ma wanke-wanke, da alama Asma tayi da dare. Doya ta fere ta dora, sannan ta fito ta share falon ta gyara ko ina. Ta koma ta tace doyar, lokacin Asma ta fito itama
“Sannu da aiki. Ni me zan tayaki?”
Kai Hindu ta girgiza mata
“Kije kiyi shirin islamiyya abunki, doya kawai zan soya mana”
Dan tsaye Asma tayi
“Ko ki kawo in soya doyar to”
Dan murmushi Hindu tayi, tana da tabbacin Asma ta gyara musu daki kafin ta fito
“Asma ki wuce ki kyaleni, kullum ba ke kikeyin aikin ba?”
Dariya kawai Asma tayi tana wucewa ta koma dakin su. Ita aiki bata dauke shi komai ba. Doyar kuwa Hindu ta fara soyawa, ta kunna karatun Qur’ani da take tabi a hankali, Zaid ya shigo kitchen din
“Me kike soyawa? Ina ci… Yunwa nake ji”
Dan juyowa tayi ta kalle shi
“Yaya… Ina kwana. Doya ce fa, amman ban dafa ruwan zafi ba tukunna, bari in duba maka a flask ko akwai saura”
Kai Zaid ya girgiza mata, tashi yayi cikin shi kamar anyi sata.
“In da miya ki saka mun, idan babu kibani a haka nikam, kyale ruwan zafin nan”
Plate ta dauka ta dibi doyar ta zuba mishi, tana karasawa ta bude tukunyar miya da take ajiye ta zuba mishi a gefe. Sannan ta mika mishi, ya karba da fadin
“Nagode sosai”
Ya fice, duk baudadden halin shi, koya kayi mishi abu sai ya nuna maka yaji dadi. Ko shara ya saka idan kayi, ko da baya kusa ya dawo yagani sai yazo ya sameka yace maka ya gode. Akan ce maza basu cika nuna jin dadin su akan al’amura ba, ita kam ta yarda maza nada banbanci halayya, kowa da yanda na shi yake, dan Zaid kawai yasa ta karyata wannan fadar da mutane kanyi. Ko Anty tana cewa matar shi zata sha wahala da halayen shi da yawa, amman idan ta fahimce su zasu dade basu sami matsala ba, dan shi mutum ne mai saukin kai. Kuma kamar yanda zai nuna maka yaji dadi in kayi mishi abu, haka zai nuna maka baiji dadi ba idan kayi mishi ba dai-dai ba.
Tana karasa soyawa, ta gyara takardar ta rufe kular, dan kar zufa ta koma cikin doyar shisa ta saka takarda a kasa. Tasu ita da Asma ta dauka tana kai musu daki, sannan ta dawo ta duba flask, akwai ruwan zafi, shayinta kawai ta hada, tunda tasan bai dami Asma ba, shisa ma ta saka musu miya a gefe. Tare suka karya yau suna dan taba hira, har suka gama cin doyar. Asma ta dauke plate din da kofin da Hindu tasha shayi ta mayar kitchen, hijabi ta dauka da jakarta tana fadin
“Ni kam na wuce”
Hindu na amsa ta da
“Kina da kudine a hannun ki?”
Dan yini sukeyi ranakun asabar da lahadi
“Ina da Naira dari”
Tsaki Hindu taja a fili, dan tasan Asma ba shiga wajen Baba zatayi ba kafin ta wuce din, tana rasa kalarta wasu lokuttan, ko kudine idan ba’a dauka an bata ba, ba zata taba bude bakinta ta tambaya ba.
“Ki mikomun jakata din can, ke ba zaki taba bude baki ki tambaya a baki kudi ba, banza kawai. Uban me zaki siya da Naira dari? Salon ulcer taje ta kamaki a banza”
Asma dai batace komai ba, murmushi kawai takeyi, ita abubuwa irin haka basa bata mata rai. Jakar ta mika ma Hindu, ta bude tana bata dari biyar. Dan ita ko ranar juma’a sai da Baba ya bata kudi.
“Nagode sosai”
Asma ta fadi, tana saka Hindun sake jan wani tsakin. Dariya kawai tayi ta fice daga dakin. Hindu kuwa wayarta ta dauko ta duba taga ko Hamza yai mata magana, amman shiru. Tana tunanin ko ta tura mishi sako taji ya tashi lafiya. Ko kuma ta kyale shi, duk da Dimples kance mata
‘Matan Hausawa na da matsala, sun ma jan aji mummunar fahimta. Su a ganin su jan aji shine namiji ne kawai zai dinga kiranki, idan shi bai miki magana ba ke ba zaki taba mishi magana ba, idan chatting kuke ki dinga amsa shi dai-dai. Kowa fa nasan kulawa, idan bai kira ki ba, ba wani abu bane dan ke kin kira kin duba shi, aji na cikin kama mutuncin ki, karki taba rokon shi wani abu, kisan me kikeyi. Amman ina amfanin bakiyi mishi magana ba, amman yana kira kina makale murya kina fadin sub dina ma ya kare’
Yar siririyar dariya Hindu tayi yanzun ma, babu yanda za’ayi kai mintina biyar da Dimples bakayi dariya ba. Amman a cikin abinda da yawa kan dauka rashin hankalinta, akwai maganganu masu tarin ma’ana, text tayiwa Hamza
‘Ka tashi lafiya? Ya gajiyar ka?’
Sannan ta ajiye wayar tana shiga tayi wanka ta fito. Duk da babu inda zataje bai hanata yin kwalliya ba, ta feshe jikinta da turaruka masu karfi tunda tana gida. Doguwar riga ta saka ta material ja da baki daya karbi jikinta, ta sami hula kalar kayan ta saka a kanta tana dan turata baya. Tayi kyau dai-dai ita, sannan ta dauki wayarta tana dorawa kan drawing table dinta, ta dibo kayan zanenta, ta saita takarda, sai da ta saka earpiece a kunnuwanta ta hada da wayar tana sauraren wakokin Ed Sheeran, sannan ta fara zanenta. Jin alamar shigowar sako yasa ta mika hannu ta dauki wayar tana dubawa, Hamza ne
‘Alhamdulillah. Ke ya kika tashi? Vid call?’
Tana karanta ta zare earpiece din daga kunnenta da sauri, ta tura kujerar da take zaune kai baya tana mikewa, mayafi ta dauka ta nade kanta dashi tana gyara mishi zama. Tukunna ta tura mishi
‘Sure’
Tana komawa manhajar whatsapp, saiga kiran shi ya shigo, kunne daya na earpiece din ta makala tana daga kiran, kyakkyawar fuskar shi na cika screen din wayarta, tana saka ta tunanin yanda mutum zai kasance da kyau haka. Hannu yadan dago mata yana murmushi, a kunyace tace
“Ina kwana”
Maganar da alama ta dade bata kai mishi ba
“Lafiya lau, kin yi kyau”
Ya furta yana sakata ware idanuwa, dan tasan idan yana waje babu wanda zaice tana da kyau
“Zolaya ko?”
Hakoran shi ta fara gani kafin taji yayi dariya, sai dai kafin tace wani abu taga ya juya yana kokarin ture wani da yake son leqowa, amman sai da ya leqo din
“Hello, Fodio ne”
Tana kallo Hamza ya kauda fuskar wayar dan taga alamun kujeru, batajin me yake cewa dai, yakai mintina biyu sannan ya dago taga fuskar shi
“Kiyi hakuri, zakiyita ganin kalar abubuwan nan, abokai na sai hamdala”
Yar dariya Hindu tayi
“Bakomai. Ka gaishe da Fodio din”
Kai ya jinjina mata
“Zan fita yanzun. Amman zamuyi magana anjima. Ki kula da kanki”
Ta bude baki tace mishi shima ya kula da kan shi ya kashe kiran, kai kawai ta girgiza tana rubuta maganar ta tura mishi, sannan ta ajiye wayar tana cire mayafin ta cilla kan gado. Zanen ta cigaba da wani nishadi na daban wannan karin.