Mijinta Ne Waye Mijina? : Karanta Domin Ki Karu
cikakken namiji shine wanda zai zama tamkar suturarki duk wanda zai kare ki daga tsiraicin, hakika a dalilin namiji da ya San hakkin ki kuma yake da zuciyar kawo miki dauki mai tausayi da rikon amana shine ya kamata ya zama uban a wajen ya’yanki.
mafi yawan jama’a suna cewa ba a gane halin mutum sai an zauna da shi ko kuma kaji mata suna cewa maza batukwane.
wasu matan da zarar sun kalli tsarin namiji kuma suka fahimci yana da abin hannu shi kenan su a ganin su sun samu masoyi, basu damu da tantance halaye da dabi’u wadanda Zaki mika amanar rayuwar ki ba.
yar’uwa me yasa ba Zaki binciki hakikanin waye kike tare da shi ba.
yar’uwa ki auna ki gane cewa ya dace dake?
me yasa soyayya zata rudeki ta Hana ki ganin gaskiya ko kuma sauraronta ?
shin kin gamsu lallai wannan saurayin ya dace dake ?
wadannen hanyoyi ya kamata ki Bi don ki tantance waye mijinki ?
▶ HANYOYIN DA ZAKI GANE MASOYINKI NA GASKIYA ◀
akwai hanyoyin da dama da Zaki iya fahimtar ko mijinki yana kaunar ki, amma Zan kawo kadan daga cikinsu.
♥ idan namiji yana sonki to Zaki ga yana mutunta ki tare da sanin kimar ki.
♥ idan namiji yana sonki, to Zaki iya canza dabi’unsa daga marasa kyau zuwa masu kyau.
♥ idan namiji yana sonki Zaki ga yana son zama tare da ke tare da jin dadin Hira dake.
♥ idan namiji yana sonki zai dinga shaukin ki kuma zai dinga gudun abinda zai bata miki rai.
♥ namijin dake son ki koda yaushe zai dinga ganin kin dace da shi, ba zai dinga ganin yafi ki ba.
♥ namijin idan yana sonki hakika zai kasance mai sakin suka tare da murmushi a Gare ki, zai dunga kallon fuskarki kuma ya dinga baki labari yana nishadantar dake.
♥ idan so ya Kai so a zuciyar namiji da kansa Zaki ji maimaita miki cewa wance ina sonki.
♥ namiji idan yana sonki zai dinga kishinki amma kuma ba wai irin kishin da zai takura ki ba, ko kuma kishi na gadara.
♥ idan soyayyarki ta Kama namiji, Zaki ga yana kaunar irin turaren da kike amfani da shi.
♥ Zaki ga yana kula da yan’uwanki wadannan kadan kenan daga alamomi da Zaki gane namiji yana sonki
amma akwai mazan da zakiga suna sonki amma girman mai ko kunya zata Hana shi nuna miki.
♣ DABI’UN DAKE SA MAZA SU DAINA YABON MACE ♣
akwai wasu daga cikin mata wadanda suke aikata dabi’u da mafi yawan maza ba sa so, kuma duk matar da take irin wadannan dabi’u zata zama mai bakin jini a wajen maza. ga kadan daga cikin dabi’u.
➡ KARANCIN ADDINI : idan kika zama ba ruwanki da addini darajarki da farashinki a matakin farko kin fadi kasa wanwar.
➡ RASHIN KUNYA : a duk lokacin da kika maida kanki Mara kunya, to kin rusa kanki da kanki.
➡ DABI’U IRIN NA MAZA: idan maganarki ko tafiyarki suka zama irin na maza, to shi kenan sun rage wa kanki maki %
➡ SAKIN HARSHE: idan kin zama marar kamun harshenki mai surutu da San Kai zance marar kan gado to ke kika jiyo.
➡ MAI ALMUBAZZARANCI : da saurin lalata kayan amfani, to a nan ma da matsala.
➡ RASHIN TSAFTA : ke ma kin San illarsa.
➡ RASHIN DAMUWA DA NAMIJI : shima wannan yana sa ya daina jinki a ransa.
➡ GIRMAN KAI DA TAURIN KAI: shi ma yana Kara wa mace muni da rashin kwarjini a wajen jama’a.
➡ JAHILCI DA SON KAI: wannan ma dabi’u ne da zasu zubar da kimar mace a wajen masoyi ko kuma mijinta.
➡ YAUDARA , KARYA , ZAMBA , HA’INCI , CIN AMANA :
dabi’u ne masu Kama da juna kuma mafi yawan mata suna dasawa a cikinsu kuma ta sanadin hakan sai soyayyar ta rushe aure kuma ya mutu da fatan yan’uwa Marta zamu kiyaye Allah yasa mu dace:
⬛ SANYI ☁ MAI ZUBAR DA FARIN RUWA ⬛
sai kuma amarya wanda take fama da sanyi me saka zubar ruwa a gabanta ko kuma kaikayin gaba.
matukar mace tayi aure kuma tana fama da ciwon sanyi da kaikaiyin gaba to gaskiya batabdaya daga cikin masu burge mijinta don zata zama batada dandano kamar sauran mata kuma kema baza kiji dadi sauran mata jiba saboda haka ga yanda zakiyi ki maganace matsalar.
♻ hulba
♻ garin tafarnuwa
♻ man zaitun
♻ zuma
♻man hulba
ki rinka tafasa ruwan dumi kina zuba garin hulba kina zama a ciki kina shan hulba da ruwan dumi sannan kisamu garin tafarnuwa kina zubawa a abinci kina ci zakiyi wannan har zuwa mako guda ( sati daya ),sannan zaki iya hada man zaitun da man hulba da zuma kina shafawa a gabanki idan Zaki kwanta barci a dai-dai wajenda yake miki kaikayin insha Allah zakiyi Nasara ki shiga gidan mijinki cikin kwanciya hankalin da farin ciki.
◾ GYARAN TSAFTAR FARJI KASHI ◾
tsaftar farji Ana so mace tun tana karrama iyaye surin Kayi mata tsarki da ruwan dumi domin ruwan dumi yana Hana kwayoyin cuta shiga cikin farjinki har lokacin da Zaki mallaki hankalin ki Dora daga Inda iyayenki tsaya.
⬛ RUWAN MAGARYA
⬛ MISKI
sannan daga lokacin da kika Fara al’ada kuma aikin ya karu saiki rinka amfanida ruwan magarya bayan kin gama al’ada sannan Zaki iya saka miski saboda karni wato Zaki tafasa ruwan tareda ganyen magarya danye ko bushashen ki saka miski sannan kiyi tsarki dashi kamar na kwan 3 zai karshe kwayoyin cutarwa Zaki iya dauka a wannan lokacin kuka zai hanaki warin gaba wannan matar aure ma yana da kyau ta rinka yinsa.
a takaice dai kina budurwa babu ruwanki da saka komai a farji da sunnan matsi kadai ki kiyaye da wannan wato amfani da ruwan magarya da miski lokacin al’ada.
Leave a Comment