Genaral info

Minene Amfanin Hada Lambar NIN Da Layukkan wayar Ka

Minene Amfanin Hada Lambar NIN Da Layukkan wayar Ka

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Haryanzu na kasa fahimtar hakikanin nasarar da aka cimma ta dalilin hada NIN da layukan waya, hasalima ni agani na duk abinda aka sanyo NIN aciki dagula lamari yake.

 

Kana ji kana ganin abu sai acema a NIN dinka akwai matsala kaza sabida haka sai ka gyara kafin kasamu wannan damar, sannan wasu gyararrakin kuma kafin ka samu damar yinsu sai an chajeka wasu kudade wanda a wajen talaka me fama da abincin yau da gobe nemosu akwai wahala, Kana ji kana gani zaka rasa abu mai muhimmanci ta dalilin wannan tsarin.

 

 

 

Wasu abubuwan tun muna gani suna takuramana kuma suna shiga mana hakki amma a haka muke kawar da kai, muna toshe kunnuwa, muna jan bakinmu muna yin shiru sabida wadanda muke ganin girmansu ne a wajen kuma su suka kawo wannan tsarin, yanzu har ta kaiga an tunzura mu mun fara fitowa muna magana akai ya kamata a duba lamarin.

 

 

 

 

A wasu Jihohi yanzu haka an rabasu da Network, kuma fitinar da zata faru dalilin rufe network sai yafi muni fiye da in akwai network din, shin menene amfanin hada NIN da layuka da baza’ayi amfani da wannan damar ba wajen dakile ta’addanci a wadannan yakunan ba?

 

Shin duk batun da akayi tayi za’a kulle layukan da ba’a hadasu da NIN ba ashe duk baraza na ce?

 

An sa andaina rejistan layukan na wasu ‘yan watanni ta hakan an tauye hanyar cin abincin wasu, sunyi hakuri duk sabida suna tunanin hakan hanyace ta gyara, ashe duk abin ba haka bane?

Ta dalilin hakan yanzu ba karamin tashin hankali bane mutum ya rasa wayarsa ko layinsa sabida wannan tsarin yasa abubuwan sunyi tsauri sosai.

 

Karanta Wasu Matan Hausa Novel

Gwamnatin Najeriya haryanzu bata dauko salon kawo karshen ta’addanci yanda ya dace ba, a duk kokarin data keyi na magance matsala 1 sai ta bullar da hanyoyin wasu matsalolin sama da 5. Kuma daga karshe shi wannan 1 dinma yakasa magantuwa.

 

Wasu lokutan ma takurawa da tsadar rayuwar da ake kara jefa mutane aciki shiyake kara haifar da sabbin hanyoyin ta’addanci.

 

Kafin akawo tsari yana da kyau ayi tunani akan abinda zai haifar bayan zamansa da kuma yiwuwan abin.

 

Sai an cire tsoro da kunya wasu lokutan ake iya fadan gaskiya, duk wanda yayi ba daidai ba ko yashiga hakkinmu daga yanzu bazamuyi shiru ba ko waneneshi, idan wannan tsarin NIN din bazai kawo karshen ta’addanci a Najeriya ba gara a sokeshi kawai.

Leave a Comment

error: Content is protected !!