Gyaran Jiki

Minene ciwon basur ya ake rabuwa da shi mi ke haddasa shi

Cutar Basur (Dan kanoma) Me haddasa tada kuma matakan kariya

Basur na nufin ciwon kananun jijiyoyi ko magudanan jini na dubura wato (blood vessels) wanda suke a bango-da-bangon dubura walau jijiyoyin can ciki-ciki (internal) ko kuwa na waje-waje (external) inda wadannan magudanan dake samarwa da dubura (Anus) jini don hanata bushewa ko lalacewa kan kumbura su bude wato kamar anhura balloon saboda matsin da suka samu wanda bayan sun kumburan sai su kama zugi, akejin ciwo.
Sa6anin mutanen mu da dake kiran attini wato kashi me tauri walau da jini ko ba jini, ko in mutum na nishi yayin bahaya da kyar sai arika cewa basir ne. A’ah taurin bayan gida ATINI ake kiransa wato CONSTIPATION ake cemasa ba basir bane saide yana daga abunda ke sawa wadancan jijiyoyin na jini matsi domin yanasa dubura ta tale sosai, wani kashin ma baya fita sai mutum yasa hannu ya jawosa da kansa saboda azaba.
Abubuwan da aka alakanta na taimakawa wajen kawo kumburin jijiyoyin jinin dubura su haifar da basir sun hada da;
 Yawan zama wuri daya na tsawon lokaci. Musamman teloli, direbobin mota, Ma’aikatan office, da yan makaranta
Sai attini (constipation) …. yawan bayan gida mai tauri shi walau da jini ko ba jini, galibi jinin dama fashewar jijiyoyin jinin dubara kona hanji ne kesa agansa ajikin kashin bawai daga can cikin ciki jinin yake ba, wanda inyaci gaba da faruwa ba adau mataki ba na qara azabar basiri din jijiyoyin su kumbura sosai su rika ciwo.
 Sai juna biyu, sakamakon nauyin da ciki yayi, Mace intaje tsuguno hakan na sanyawa jijiyoyin duburarta matsi shyasa galibin mata sai suna da ciki yakan bayyana musu
Sai kuma KIBA, Mutane masu kiba sosai suma saboda nauyin da mararsa ke sauka na jikinsu hakan na sawa dubura matsi, wanda hakan ke jawo basir.
Halayyar sanya gaggawa wajen kashi, ko yin yun’kurin kasaye abunda dake cikin mutum sakamakon kin tafiyarsa da kyau, saboda attini shine curewar kashin, to anan kuma yinkurin da mutum keyi shima na haddasa basir.. domin hakan na takurama jijiyoyin duburar.
Yawan zawo (gudawa) awadanda suke da cuttukan hanji irin IRBS ko masu HIV din da basa shan magani ko suke wasa, ko masu wasu cuttukan de dake sanya yawan tsuguno.
Halayyar kin tashi ayi kashi sanda ake jinsa har kashin ya koma yai concentrating aciki ya zamto mutum yama dena jin alamun zai kashin.
Nan-nauyan kugu wato te6a amma wajen mara ko duwawu abunda Mata ke kira Hips, arika wance tana da hips… kila sauran jikinta zakaga normal shape babu kiba amma mararta dam take da kitse… wannan ma na jawo basir saboda dubura najin nauyin.
Baya ga Juna-biyun dana fada abaya hakama nakuda kan haddasa basir musamman macen data haihu da kanta wato wajen yunkurin fito da jinjiri. Yanasawq dubura matsi, wannan ko abune afili ganin yadda gun kan talle ya denneta, wani bun ko ķari za ai dama tanan akafi karata ta kasa kafin dan ya fita.
Haka ma jima’i ta dubura. Walau masu jima’i da matansu ta dubura, da kuma ‘yan luwadi suma kan fuskanci basir saboda matsi da gugar da sukewa bangon dubura shiyasa ma jijiyoyin kanyi leaking din jini wannan kuma tasa sukafi saurin daukar kwayar HIV in akwai fiye da saduwa ta dubura. Da dai sauran su.
Dukkan wadannan yanayi nasa magudanan jinin dubura su kumbura, suja ruwa, wani lokaci su fashe. Shiyasa mai basir kanji zafi ko zogi a dubura wani lokaci har da zubar jini.
Yana da stages har guda hudu wanda kuma daga stage 1 yake farawa inba ai komi na daukar mataki ba har yakai stage 4;
STAGE 1: Shine basir din da ake jin zafi ta dubura kuma in anyi kashi akanga jini yadan biyo bayan kashin, koda anshafo duburar baza aji komi ba.
STAGE: Shine bayan angama bayan gida akasa hannu za’aji jijiyar ta zazzago ana ta6ata amma bayan mutum ya wanke kashin da kanta mutum zaiji ta koma.
STAGE 3: Idan mutum ya gama tsuguno zaiji ta zazzago, kuma koda ya wanke duburar basir din bazai koma ba sai mutum yasa yatsa ya turasa da kansa. Idan ya mayar zaiji shikenan ya bace.
STAGE 4: Shine mai zazzagowa baya komawa, kuma inkazo maidashi ga zaba, kuma hakanan da kansa zai qara zazzagowa, wato koka mayar sai ya qara saukowa.
Shi basir kowa na iya haduwa dashi a wani lokaci na rayuwa inde angirma, akalla duk mutum 3 cikin 4 sai sun hadu dashi arayuwarsu.
Mahimmin abu shine kiyaye dukkan abunda zaisa kashinka ya rika tauri, wato zamo active, nasha fada yawan motsa jiki abune mahimmi, sannan ka yawaita amfani da ganyayyaki da yayan itatuwa cikin abincinka wadanda kansa bayan gida yai laushi wato su; Lemon 6awo, kankana, lettuce, Apple, Na’a-na’a, lemon grass, kabeji, abarba da sauransu, gami da yawan shan ruwa akallah lita 2 arana.
Akwai magungunan rage zogi da akan sayar a chemist irinsu; Hemorrhoidal cream, topical anesthetic, su ‘anusol’ da sauransu, da ake shafawa adubura in za’a kwanta da dare domin samun saukin zogin.
Sannan duk sanda kaji tsuguno to ka tashi kaje kayi, ba’a rike kashi kuskurene, saboda sanda kaji kashi toh lokacin tafe yake hade da ruwa wanda zai lausasashi ya saukaka maka fitarsa, amma inkaqi tashi kayi toh karshe hanji zai tsotse ruwan wato absorption sai ya bar zallar tuwon kashin kwance cikin hanjinka… duk sanda wani kashin ya qaru ya zamto dole asannan bazaka iya rikewa ba sai kaje ka kasayar tohfa asannan ne zaka sha wahala, kaji kana nishi da kyar, kana strecthing, kila saika sa hannu ko kinsan hannu kin jawosa saboda kayiwa kanka mugunta kaqi yi sanda kajisa da farko… wanda hakan na daga abunda ke haddasa basir.
Sai hadawa da tsarki da ruwan dumi, ko kuwa zama acikin ruwan dumin musamman wanda akansa gishiri kwatankwacin cikin hannu daya wanda hakan ka iya kadhe kwayoyin cuta dake duburar su kuma hana basir din fashewa ya rika jini tare da sa jijiyoyin su motse kuma su rage zogi.
Sannan wasu ma kan amfani da sassaken mangoro atafasa su rika zama ciki wannan ma supplement ne.
AMMA BAYAN NAN
Duk basir din da yaqi jin wannan toh sai anyi ’yar karamar tiyata anyankesa, ko kuma ansa roba an daure tushensa wato an datse masa hanyar samun jininsa tunda jinin ne abincinsa idan akasa roba aka datse hanyar jinin wato litigation… shikenan za’a sallami mara lafiya yai tafiyarsa…bayan kwana biyu yana tsugunawa kashi inyasa pressure saide basir din ya 6ungulo yabi kashi shikenan an rabu tunda jijiyar basir din mutuwa take bayan datse mata hanyar samun jini.
Wannan shine dan bayani game da basir. Don haka wanda yasan nasa yai duk kokari abu yavi tura to ya daure yaje babban asibiti yaga babban likitan Gastroentrologist zai sami mafita insha Allah, cire basir baida wani hatsari yanzu aranar da aka cire kana iya tafiya gida da yamma.
Allah ya karamana lafiya, ya tsaremu, ya kuma biyamana dukkan bukatunmu na alkhairi ameen.
.
Masu copy na post dina ina jan hankali da kudena cire sunana musamman wadanda suka san bani da su na basu damar hakan ba…. kunsan kanku, ina kallonku, kuma ina iya daukar matakin shari’a akai ba abun wasa bane, rayuwar mutane ce nake tattaunawa …! Nafiso kubar sunana bawai don asanni ba, sai don saboda wasu kan biyo sunan sui mun tambayar dani me rubutun ne zan iya warwareta, ku insun muku bakwa iya amsawa.
Banso rubutuna ya zamo abunda zaike bawa wasu lasisin tattaunawa da matan mutane alhalin bakasan komi ba game da abun.
Duniya ta shige tunanin mutum acigaba ina da software da nake tracking rubutuna saboda plagiarism koda private group kakai saina gani ko whatsapp ballantana timeline dinka (har garin da kake idan naso tracking zan iya kamo location dinka da sunan wayar da kake amfani da ita, da daidai lokacin wallahi), so muke appreciating effort din mutane pls… rubutun lafiya ba irin sauran taci barkatan rubutu bane, saboda mistake kadan kana iya saka rayuwar dubban mutane a hatsari.
Saide Kamar yadda nace akwai groups din da izinina suka nema na basu suke kai rubutuna kuma suna kiyaye hakkin malaka suna sanya sunana bani da matsala da wannan, wasu kuma bloggers ne suna sawa a jaridu wannan ma sun nemi izinina bansa matsala dasu.

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!