Hausa Novels

Mr Bello Hausa Novel Complete

Mr Bello Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Mr Bello Hausa Novel Complete
GGUSS KWATAR-KWASHI

A haraban Babbar Makarantar ta GGUSS, Goverment Girls Unity Secondry School Kwatar-kwashi Dake Tsakanin Dajin kwatar-kwashi Zuwa Gusau, Da Misalin ƙarfe 10:30am na Safe.

Daga Cikin Babban Filin Haraban Makarantan Na Hangi ɗalibai Birjit ba Adadi mata ne Zallah Ta Ko”ina Suna Yawo Wasu Suna Tsaye da Tarin Akwatunsu da Jakunkunansu Wasu kuma Suna ta Tururuwan Shiga Doguwar Mota Fara mai Ɗauke da Tambarin GGUSS KWATAR-KWASHI, gefe ɗaya kuma Kowaccensu Tana Sanye da Uniform ne Ajikinta wasu Nasu Wando light green ne Both Riga da Wando da Ɗan kwali sai Farin Hijabi A yayinda Wasu kuma ke Sanye da Dark green d’in Wando sai Both Farin Riga da Da’n kwali da Hijabi.

A yadda Haraban Makarantan ta Rikice da Hayaniya da Murna da Iface ifacen Ɗalibai zaka Fahimci Hutu ne Ɗaliban Suka Samu Tun ma Ba Daga yadda Wasu Iyayen Ɗaliban keta Zuwa Ɗaukan yaransu Wanda basu yi Register da Motar Makaranta ba, Ayayinda Wasu ke Ta Fitowa Bakin Get d’in Mkrantar ga masu Mashi nan suna ta Ɗaukansa Zuwa inda zasu Hau Mota Zuwa Gida.

 

 

Mr Bello Hausa Novel

Daga chan ɓangaren Na Hangi Wasu ‘Yan mata su Uku Tsaye A bakin Wata Bishiyar Dalbejiya Dukkansu Gabansu Akwai Tarin jakunkuna, da Sauran Tarkacensu masu yawa, sakamakon Wannan Hutun Third term ne ƙarshen Zangon karatunsu na Jss 3 sai Shiga SS1 Kenan, Suna Sanye da Uniform ɗinsu na Junior, light green both Riga da Wando da Ɗankwali sai Hijabi Fari, Dukkansu Ukun Tsawonsu Ɗaya Sai dai kuma Biyu Daga Ciki Farare ne Tas.

Sai Ta Ukun Wacce ke Tsakiyansu Ɓaka ce Sulub ammh Bak’inta bamai Duhu bane mai haske ne, Wanda Ke Shining, Doguwa ce Mai K’arancin Girman Jiki, Fuskarta tana da Faɗi Ammh ba Sosai ba, Tana da Manyan Idanuwa Masu Ɗauke da Gashin Ido Zarara sai Ƙaramin bakinta Wanda Yake Baƙi baki, A shekaru Dukkansu bazasu gaza Shekaru goma Sha Shidda ba Daga Kallon Farko Zaka Fahimci Zallar Ƙuruciyarsu A lokacin.

Daga bayansu sukaji Ance ” *ANEESA…*” atare Suka Waiga dukkansu suna Kallon Ɗaya Daga Cikin Senoirs ɗinsu Jidda Madaki Waɗanda Suke Kan Zana Jarabawarsu ta Fita Ma’ana WAEC, Saboda Haka Su Suna Makaranta basu Azuwa Hutu sai Sun kammallah Neco wanda kuma bazai yi ba Sai ya Tattara ya koma gida.

Itama ɗin Sanye Take da Uniform ɗinsu na Senior, Dark green da Farar riga da Hijabi, Kyakkyawar Gaske ce Gata Fara gata Doguwa mai Ɗauke Da Daran Daran Idanuwa masu Haske Cikin Siririyar Muryanta tace “Aneesa Plz D’an zo na ganki…” Ta faɗa Cikin Yanga Wanda ya Zame mata Halitta.

Jin Abunda tace yasa Aneesa Ta ƙara Haɗe Ran Kamar Wacce Aka Aikoma da Saƙon Mutuwa Saɓanin Sauran ƙawayenta da Fuskarsu ke Washe na Farin cikin Zasu koma gida yau, Cikin Sanyi Jiki da Takun Ɓacin Rai Aneesa Ta Nufi Jidda tana Faɗin ”

S. JIBIYA, B. KAITA Ku jirani bari na Dawo..” Jin Haka yasa S. Jibiya tace “Ok

A. BUKAR BULAMA

Ta faɗa Tana bin Aneesan Da Kallo kafin Ta Maida Kallonta kan B. Kaita Suka haɗa ido Suna Ƙunshe Dariya.

 

 

Zaman Hostel

Aneesa kamar bazata Taka ƙasa ba Haka ta Rinƙa jan ƙafa Zuwa Wajen Jidda Dake Tsaye tana Jiranta Tana ƙarisowa ta Riƙo Duka Hannayeta Cikin Salon Muryanta tace “Aneesa Don Allah karki manta da Alƙawarin mu Kinji..” Ta faɗa Tana Sakar mata Fararen Idanuwanta.

Gyara Tsayuwa Aneesa Tayi Tana Jifan Jiddan Da Wani Banza Kallo A fakaice, kafin tace “Wani Alƙawari kenan…?” Ta faɗa Da Sigar Rainin Wayau Lokaci Ɗaya Itama tana Sakar mata Manyan baƙaƙen Idanuwanta masu Ɗauke da Zara zaran Gashinta baƙaƙe masu ƙara Fito da Salon Kamaninta da *KANURI*, Jidda Ta Saki Ajiyar Zuciya kafin Ta ƙara Riƙe Hannun Aneesa Tana bin Haraban Mkrantan da Kallo Yadda Taga Kowa na Haraman Tafiya sai D’ai d’ai Irinsu ne Suke Hidimar gabansu.

 

Mr Bello Hausa Novel

 

 

Name: [MR BELLO HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


Leave a Comment