Mu gani a kasa Hausa Novel Complete
*MU GANI A ƘASA…*
_Hot Love_
©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN
_GAWURTATTU BIYAR._🔥
*Page 1-2*
*Godiya ga Allah (S A T) da ya sake bani dama da iko da sake zaman rubuta muku wannan labarin, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga manzonmu Annabi Muhammad (S A W). Da fatan zaku bini sannu a hankali domin jin inda wannan karon labarina ya nufa.*
_Haƙƙin mallaka na Ummu Affan ne, ban yadda a juya mini labari ta ko wacce siga ba, ko ɗaurawa a wata kafa ba tare da izini na ba, yin hakan kuskure ne. Sannan ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi domin kowa ba idan yazo daidai da rayuwarki/ka a rashi ne._
*_ÆŠungurungun littafin nan sadaukarwa ne ga Auntyna Ƴar’uwata Ta gaban goshina ta Æ™asan zuciyata MARYAM MODIBBO wato ADDA Maman Hamdana da Hamd. Ke É—in ta daban ce Zinariya kike a zuciyar Abbansu Humaid._*🙈💃😍
*Masu san na musu talla a pages na littafina zasu iya magana cikin farashi me sauƙi mai tallah shi ke da riba.*
_Bismillahir rahmanir rahim._
*ABUJA NIGERIA*
Sanyayyiyar iskar damina ce ke kaÉ—awa a daidai lokacin, gari ya yi luf da ni’ima ya yin da sararin samaniya ya yi fayau dashi gwanin burgewa da ban sha’awa. TuÆ™i yake cike da Æ™warewa yana sharara gudu saman lafiyayyar kwaltar da ke birnin tarayya Abuja. Yayi tafiya me nisa kafin ya iso babbar unguwar tasu ta Asokoro. Wani katafaren gate ya dosa inda ya buga hurn, da sauri Maigadi yazo tare da wangale mishi Æ™aton gate É—in ya kutsa hancin motar shi ciki. Sannu da zuwa Officer ke masa hannun shi kawai ya iya É—aga mishi. A cikin babban harabar gidan ne ya samu guri ya yi parking, kusan minti biyu kafin ya iya zuro Æ™afarshi daga motar, Æ™afar tashi mai sanye da Æ™ayatattun baÆ™aÆ™en takalmi sau ciki ce ya zuro a hankali kamar mai tsoran fitowa. A hankali kuma sassan jikin ya fito da shi, “Ma sha Allah” Ƙyaƙƙyawa ne ajin farko. A hankali yake tafiya kamar mai tsoran takawa hannun shi É—auke da Æ™atuwar wayar shi yana duba saÆ™on da yaji shugowar sa tun yana tuÆ™i. Dan tsaki yaja ganin mai saÆ™on kafin ya zura wayar cikin aljihu ya doshi hanyar da zata sada shi da parlourn gidan. Da gudu ta taso tare da nufarshi da niyyar faÉ—awa jikin shi “Oyoyo Yaya Aliyu!” Ta furta da tsantsar farin ciki. Saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar É—aga mata hannu, chak ta tsaya jiki a matuÆ™ar sanyaye. Ƙarasawa Yayi gaban Amminsa dake tsaye tana kallon abin da ke faruwa. Zaunawa yayi saman Cushin yana me duban Ammin tashi. “Barka da hutawa Ammi!” Ya furta cikin sanyi bazaka taÉ“a cewa shine yayi maganar ba, sakamakon laÉ“É“ansa ne kawai suka motsa idan ma ba kusa dashi kake ba, ba lallai ne kaji me ya furta ba. Wani kallo ta ma shi ba tare da ta amsa ba, ta mayar da kallonta ga yarinyar da ya nunawa ko in kula wacce ke tsaye kamar gunki har zuwa lokacin. “Sareenah tsayuwar ta isa haka, ko baki gaji da kallon nashi ba ne?” Cike da kunya tayi wani far! Sai ta juyo a sanyaye tare da zama gefen shi. “Abuturrab har yanzu halinka na nan ko? Ko ka mance wacece Sareenah a gareka ne?” Wuci ya fesar me zafi kafin ya ce”Ammi yunwa nake ji” Ya faÉ—a da nufin É“angarar da wancen zan cen. Kallonsa take ko Æ™ittawa babu, wani murmushi ta saki wanda ita ce kawai tasan ma anarsa kafin ta kalli Sareenah “Ki kai mishi abinci part É—in shi” “No Ammi!” Ya furta kamar zai yi kuka. “Ki kawo mishi anan” Girgiza kai yake amma ya kasa cewa komi sakamakon kallon da Ammi tayi mishi. Tashi tayi a gurin yabi bayanta da kallo har ta Æ™arashe hawa saman benen, sanyayyar ajiyar zuciya ya saki Æ™irjin shi na wani irin bugu. Bai san time ya É—an ja yana gurin zaune ba sai da Sareenah ta Æ™ara so tare da ajiye tray É—in dake hannunta. “Yaya Aliyu ga abincin!” Ta faÉ—a tana Æ™oÆ™arin zama gefensa. Da sauri ya miÆ™e yana jifanta da wani mugun kallo, Æ™ala bai iya ce mata ba ya miÆ™e tare da nufar Æ™ofar parlour. “Abincin fa? Ko na biyoka da shi part É—inka?” Ta jero mishi tambayoyin a lokaci guda, juyowa bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata. Yana fita kai tsaye part É—in sa ya dosa, komi fes-fes kamar yadda ya zata. Kai tsaye bedroom ya wuce yana zuwa komi na jikinsa ya cire tare da faÉ—awa toilet, wanka ya yi ya É—auro alwala sannan ya fito É—aure da towul É—aya a hannunsa yana goge sumar kan shi. Mirror ya nufa inda ya shafa maya-mayansa tare da feshe jikinsa da turaren sa mai daÉ—in Æ™amshi, Ƙananun kaya ya saka dogon wando tare da riga t-shirt sai ya É—ora wata me kauri ta sanyi me haÉ—e da hula, sakamakon yanayin garin na sanyi. Ya so ya huta amma kiran sallar ta Azahar da ake Æ™wala kira a masallacin Æ™ofar gidansu ne ya sashi nufar hanyar fita daga badroom É—in. Yana fita kai tsaye masallaci ya nufa.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
Sareenah bayan fitarsa da gudu ta hau sama bedroom É—in Ammi, tana shiga ta sami Ammin na waya da gudu ta Æ™arasa tare da faÉ—awa jikinta ta saki wani kuka. Ba shiri Ammi tayi sallama da wacce suke wayar tare da sanar da ita anjima zata kirata. “Sareenah lafiya kuwa?” Ammi ta tambayeta bayan ta ajiye wayarta saman Æ™aramar durowar dake kusa da ita. Cikin kuka wanda zallarsa shagwaÉ“a ne da sangarta ta ce “Ammi Yaya Aliyu ne! Mene ne na masa ya tsane ni haka?” Da sauri Ammi ta katseta ta hanyar É—aura É—anuatsanta saman laÉ“É“an Sareenah “Kar in kuma ji” Ammi ta faÉ—a tare da kawar da É—an yatsanta kafin tacigaba da cewa”Shi har ya isa? Bai kai matsayin tsanarki ba Sareenah kicigaba da shige masa kamar yadda na nuna miki a juri zuwa rafi dai, nasan dole wata rana tulu zai fashe.”
“Har zuwa yaushe ne tulun zai fashe Ammi? Kin san dai yarda Yaya Aliyu ke zuciyata!” “Ke dai Sareenah albasa ba ta yi halin ruwa ba, da tayi tabbas ba za ta yi yaji ba tun da har na ce miki haka to ki É—auka mana, kin san bana san É“acin ranki” Ammi ta faÉ—a tana sharewa Sareenah hawayen dake zuba a fuskarta. Numfashi ta sauke tare da lafewa jikin Ammin tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, sannan tasan wacece Ammi bata faÉ—in Æ™arya sai abin da ke Æ™asan zuciyarta.
Fitowarsa daga masallaci ba É“ata lokaci ya É—auke key É—in motarsa, cikin tafiyarsa ta alfarma ya doshi harabar gidan, tun daga nesa ya dannawa motar key ta buÉ—e yana zuwa ya faÉ—a ciki tare da kunnawa. A É—ari ya fita gate É—in gidan daman tuni Maigadi ya buÉ—e masa tun lokacin da yaga ya doshi motar. Wani gidan abinci ya nufa na manya sai wanda ya amsa sunansa ke cin abinci a gurin. “Barka da zuwa Æ´allaÉ“ai” Wata murya siririya ce tayi maganar. Bai É—ago kan shi ba, tun bayan zamansa saman kujerar haka jin maganarta bai sa shi jin zai É—ago ba, duk kuwa da jin bugun zuciyarsa da ya tsananta. “Me kake buÆ™ata?” Maganar É—azu ta Æ™ara ratsa masarrafar sautin sa, bai ce ko ci kanki ba wata farar talarda ya ga an ajiye mishi, sai lokacin ya kai idanuwansa kan takardar, abinci ne da nasha da dangin na Æ™walama kala-kala rubuce a jikin takardar. Pen ya ciro gaban rigar shi tare da making abin da ke buÆ™ata tare da ture takardar da baya jin zai iya magana miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi. Ta É“angarenta kuwa tun bayan parking É—insa Madam (Shugabar gurin abincin) Ta ce”Ke *Tataah* ga kostoma nan jeki gurinsa” Cikin sanyinta ta miÆ™e tana ta fiya sulow kamar yarda take, daidai zamansa ta Æ™arasa tare da tambayarsa abin da yake buÆ™ata. Jin shuru ta É—ago idanuwanta ta dubesa, gabanta taji ya bada dammm! Haka ta daure ta kuma tambayarsa cikin sanyi amma bai bata amsa ba sai ta saka mishi takardar tana mai jin haushi a zuciyarta sakamakon ko in kula da ya nuna mata. Ganin abin da yayi a ranta ta ce”Uhmm! Masu abu da abin su, tabbas a rashin kira karen bebe ya É“ata” Tana duba irin wannan izza da girman kai na wannan mutumin. Lokacin da Madam ta ce taje tsoro ne ya fara É—arsar mata sakamakon yadda Æ™adangarun bariki ke kai mata haushi a gurin, tana tsananin tsoron zuwa tambayar abin da masu sayen abinki ke buÆ™ata saboda wasunsu maganar banza suke mata, a kallon farko ta É—auka shima hakanne musamman da ta ganshi matashi sai ta fuskanci maganar nan ta kowa da halinsa amma wannan kuma girman kai ke damunsa, da wannan tunanin ta É—auki takardar tare da nufar gurin Madam ta miÆ™a mata. Komi da ya buÆ™ata aka haÉ—a masa tare da ba Tataah ta kai mishi, tsaye tayi a gurin tana kallon yarda yake danna wayarsa bai damu da kallon kowa dake gurin ba. Jin tsayuwar mutum kuma ba a ce komi ba ya sashi É—agowa a hankali, idanuwansu ne suka gauraya da na juna, sauran kaÉ—an tiren hannun Tataah ya sun É“ule saboda tsorata da tayi da yarda da tsinci gabanta na dukan tara-tara. Da sauri ya saka hannun ya amshi Tray yana jan dogon tsaki duk da shima yaji shock a haÉ—a idanuwansu amma ba zaka taÉ“a gane hakan ba. Wani banzan kallo ya aika mata da faÉ—in “Noneses baki da hankali ne zaki É“ata ni?” Da sauri ta juya tare da barin gurin. Duk bayan saÆ™on É—aya sai yaja tsaki jin zuciyarsa ya yi sam babu daÉ—i, yunwar da yake ji ne yasa shi buÉ—e abincin ya fara ci, amma da ya tuno fuskarta sai yaja tsaki da haka ya cika cikinsa, Drink ya É—auka yana sha a hankali yana amsa wayar da ake ta kiransa tun É—azu. “Aliyu ka shugo ne?” Abin da aka faÉ—a daga can É“angaren kenan, sai da ya kurÉ“i lemunsa ya haÉ—iye sannan ya furta “I akwai wani abu ne?” “ÆŠan renin wayau, mu muna nan muna jiranka kana shanya mu!” Robar lemun ya ajiye tare da cewa “Faruuk bacci zanyi” Ƙit! Ya katse kiran daidai miÆ™ewarsa. Gurin biyan kuÉ—i ya dosa tare da barin gurin cikin sauri.
Tataah dake leÆ™ensa ganin yarda motarsa ta fita harabar gurin a sittin ta sauke numfashi nan take kuma idanuwanta suka kawo ruwa, kawar da abin da yazo mata tayi tare da dosar gurin zamanta. Ba ita ta bar gurin ba sai gabda magrib lokacin da ma’aikatan dare suka iso, gurin Madam taje inda ta bata sallamarta na ranar. Ƙarasawa tayi gurin kayanta tare da É—aukar babban hijabinta da ke gurin wanda ya tsufa sosai, sakawa tayi ta É—auki Æ™aramar jakarta tare da kularta. Madam ta kai mawa ta zuba mata abincinta na rana da na dare wanda take basu, to ita bataci sai zata tafi take amsa. Kai tsaye bakin babban titin ta nufa domin samun Kekenapep da zai mayar da ita gida, ta tare kusan napep uku amma rashin daidaitawa yasa suke wucewa domin a kullum nera É—ari biyu ta ware domin zuwanta gurin a É—ari ta koma É—ari, idan bata samu wanda zai kaita a hakan ba to tana haÆ™ura har ta samu. Tana tsaye gurin rungume da kularta da jakarta, yadda garin ya kaÉ—a hadari ne ya bata tsoro duk ta cure guri guda, tsoranta É—aya karta Æ™ara hamsim ya zama É—ari da hamsim taci bugu gurin Gwoggonta domin duk wanda ta tsayar haka yake ce mata. Shada tayi akan ta sayar ta hau tasan dai bugu kam sai ta shashi haka ta fara Æ™oÆ™arin tsayarwa amma duk wanda ta tsayar basu tsayawa sakamakon hadarin da ya Æ™ara turniÆ™e garin na Abuja har yayyafi aka fara, duk ta tsure sai kama hijabinta take daidai tsayuwar wata Æ™atuwar mota. “Yan mata ina zaki?” Mai motar ya tambaya bayan yayi parking ya buÉ—e gilas É—in gaban motar. Gabanta ne ya buga amma bata da zaÉ“i dole a wannan lokacin tana amsa mishi saboda tana buÆ™atar temakon nasa tabbas. Cikin rawar murya da sanyi ta ce”Maitama zani” “Hanyar za mubi zo mu rage miki hanya” Ma tuÆ™in motar ya faÉ—a domin sai yanzu na lura ashe su biyu ne cikin motar, matasa ne da baza su wuce 32 ba, ba yadda ta iya dan har ruwa ya fara sakkowa, ganin ya buÉ—e mata back sit da sauri ta shiga tare da furta “Na gode” Tun da suka hau titi ba wanda yayi magana har suka isa Maitama sai lokacin MatuÆ™in motar ya tambayeta inda zai ajiyeta domin an tsuge da ruwa sosai. Da sauri ta ta É—ago fuskarta domin ta cure guri guda sanyin gari da na Ac dake kunne a motar ya Æ™ara mata jin sanyi gashi daman basu shiri da sanyi har wata Æ´ar kyarma take. Kwatanta masa tayi har Æ™ofar gidan da suke zaune ya kaita. Tana niyyar fita ya ce”Sunana Faruuk ke baki faÉ—a mini naki sunan ba” Gabanta ya buga sosai “Faruuk!” Ta nanata cikin sanyi ta ce”Na gode sunana Tataah!” Daga haka ta fita da sauri, da gudu ta shiga cikin madaidaicin gidan. Tana motar Faruuk yayi abokinsa dake gefe mai suna Ma’aruf ya ce”Faruuk ka cika kwashe-kwashe daga temako mene ne kuma na faÉ—a mata sunanka da tambayar nata, bakaji rainin wayaun da ta maka ba wai Tataah wannan suna ne?” Murmushi ne É—auke fuskar Faruuk ya ce”Tun da kaji ta ce haka to sunan nata kenan, ni fa ban faÉ—a mata sunana da wata manufa ba, kamar yarda ban tambayi nata da niyyar komi ba” TaÉ“e baki Ma’aruf yayi tare da lumshe idanuwanshi da haka suka Æ™arasa gida.
Tataah tana shiga kai tsaye É—akin Ummanta ta nufa.
Da sauri ta Æ™arasa gabanta ganinta kwance kamar yarda ta barta tun safe, daman tasan hakan zata kasance, kular hannunta ta ajiye tare da cire hijabin dake jikinta, kama mahaifiyar tata tayi tare da saka fillow ta jinginar da ita jikin bango. “Sannu Umma!” Ta furta cikin tsananin jin tausayin mahaifiyar tata, kallonta kawai Ummar ke yi ko Æ™ittawa babu, tsumma ta É—auko tare da share mata miyun dake zuba a gefen bakinta sannan ta É—ebo ruwa ta kafa mata kai, sosai Ummar tasha ruwan da alamar ba Æ™aramin Æ™ishi take ji ba ‘Dole taji Æ™ishi Tataah tun safe fa’ Wani É“angare na zuciyarta ya sanar da ita. Bata cika mata ciki da ruwa ba da sauri ta É—auko abincin da tazo dashi tare da cokali ta fara ba Umman, ta É—an ci ba laifi sannan ta Æ™ara mata ruwa tasha, duk bayan minti É—aya tana jerowa Ummar sannu. Ganin Ummar ta Æ™oshi sai lokacin hankalinta ya kwanta ta ci ragowar itan ma tun safe sai yanzu take ci, bayan ta gama sake tattare Æ™aramin É—akin nasu tayi tare da É—aurawa Umma alwala jin ana kiran sallar Magriba ita ma fita tayi ta É—auro. Salla ta gabatar ita ma Umma a yadda take zaune take tata a haka. “Tataah! Tataah!! Tataah!!!” Yarda taji muryar mahaifinta na Æ™wala mata kira yasa Æ´an hancin cikinta murÉ—awa. Tana Æ™oÆ™arin miÆ™ewa sai gasu sun shugo É—akin shi da Gwoggonta, jiki na rawa ta duÆ™a Æ™asa “Gwoggo sannu da gida…” Tsawa ta daka mata “BaÆ™ar munafuka algumguma me baÆ™in hali baÆ™ar fuska! Ashe kin dawo hakima mandiya shine kika barni ina ta jiranki” A sanyaye ta ce”Kiyi HaÆ™uri lokacin da na shugo ana ruwa ne shiya…” “Dakata mini haka!!” Ta katseta ta hanyar daka mata tsawa. Baba ya ce”Amma me na ce miki akan idan kin dawo gidan nan?” Tuni idanuwanta suka cika da hawaye “Kace na fara zuwa na gaisheta tare da bata duka kuÉ—in aikin” “To uwar waye ya ce yau ki karya dokar” “Kuyi haÆ™uri wallahi ruwa akeyi lokacin” “Karya ne ai kafin magariba kike dawowa kuma sai da aka kira sallah aka fara ruwa” Da sauri Baban ya kalli Gwoggo da ba hakan bane amma kallon da ta wurga mishi ne yasa yayi saurin cewa”Haka ne” Jawota Gwoggo tayi tare da fara kilarta tana cewa”Saboda kin raina maganar ubanki danni nafi Æ™arfin ki rainani, kin zo gurin nakasasshiyar uwarki da bata da mamora to bani kuÉ—in da uwarki gantalalliya kawai, a haka zaki Æ™are a gantale ke da uwarki!” Jiki na rawa tana kuka ta ta miÆ™a mata kuÉ—in duka, Allah yaso ta cire É—ari biyun motar gobe da kuma É—arin ta ta yau da Allah yasota aka rage mata hanya, dan da tasan tana cirewa bazata bari ba.. Tana amsa ta turata ta faÉ—i tare da tasa Baba gaba suka bar É—akin. Tataah É—agowa tayi tare da sakin Æ™ara ganin hannunta da ta É—ora a goshi da jini, sake kama goshinta tayi tare da sakin kuka…..
*MU GANI A ƘASA…*
_Hot Love_
©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN
_GAWURTATTU BIYAR._🔥
*Page 3-4*
Motsin da taji Ummanta nayi ne yasa ta saurin juyowa, da sauri ta Æ™arasa kusa da ita. Hawayen da taga Umman nayi yasa ta mance da ciwon da ke goshinta, “Umma kuka? Mene ne ya faru? Dan Allah ki dena kuka Ummata!” Ta Æ™arashe maganar ita ma tana hawayen tare da sharewa Umman nata hawayen. ‘Ina ma ina iya magana, ina ma komi nawa yana motsi, ina ma ina da lafiyar da zan iya tsayar da zubar hawayenki, Tataah da bakiyi kuka ba har Æ™arshen rayuwarki’ Abin da Umma ke faÉ—a a zuciyarta kenan sai dai kamar yarda ta faÉ—a tabbas bata da damar hakan a yanzu. Tataah kuwa ganin tana goge mata hawayen amma wasu na zuba sai ita ta dena kukan nata cikin karyewar murya take faÉ—in “Umma na bari kema ki dena, zubar hawayenki tamkar ana É—iga mini dalma ne a cikin jikina na bari” Ta faÉ—a da sakin dariya-dariya wacce take ta zallar yaÆ™e tana dariya amma hawaye na zuba. Jin ana kiran isha’i gabatarwa sukayi sannan Tataah ta jawo wani yaÆ™unannan zani ta shimfiÉ—a a inda zata kwanta ta gyarawa Umma kwanciyarta a saman tabarmar da ta gama fita hayyacinta sai zanin da ta shimfiÉ—a mata, wani tsohon bargo ta É—auko ta lilliÉ“e Umman sakamakon ruwan saman da akayi ya sakar da sanyi me shiga jiki ita kuma ta rufe da hijabinta, haka bacci ya kwashe su daman suna sallahr isha’i take bacci saboda asubar fari take tashi. Ilai kuwa tun huÉ—u na asuba ta tashi alwala ta farayi tazo ta gabatar da nafila da yiwa Ummanta addu’ar samun lafiya kullum sai tayi wannan sallah dan roÆ™awa Ummanta samun sauÆ™i gurin sarki Allah. Bayan idarwarta fita tayi ta fara share tsakar gidan wanda hasken sola ya mamaye ta É—ayan gidan dake jikin nasu ne, mai gidan ya basu wannan Æ™aramin suke zaune to har solar dake gidansa ya jona musu. Bayan kammalawarta ne ta shiga kitchen wanke-wanke tayi tare da gyara kitchen É—in dake kaca-kaca kuma kullum sai ta gyara amma haka zata dawo ta iske shi kamar anyi yaÆ™i da kaya a cikin shi, fitowa tayi daidai kiran sallar asubahi wanka tayi da ruwan sanyi sai kyarma take saboda sanyin da ake sannan ta É—aura alwala ta shiga da ruwa tayiwa Umma wacce ta iske ta tashi alamar gaisheta tayi sannan ta jinginar da ita domin tayi sallah. Ita ma ta gabatar da tata, ko man shafawa bata da zarrar shafa shi domin basu dashi, ta daÉ—e zaune tana lazumi Æ™arfe shidda nayi ta miÆ™e ruwa ta bawa Umma tasha sannan ta gyara mata kwanciya tare da tofa mata addu’o’i cikin sanyinta ta ce”Kiyi haÆ™uri Umma yau ma haka zan fita ba tare da kinci komi ba, anan babu shago balle na sayo miki ko wani abu ne da nera É—arin jiya, amma kiyi haÆ™uri har na dawo” ÆŠan lumshe idanuwanta tayi wanda shine kawai ke aiki a jikinta alama ce ta mata da ba komi, jiki a matukar sanyaye ta fita tare da ja mata Æ™ofa. Kamar yadda Babanta ya sanar da ita Æ™a’ida ne taje gaida Gwoggo kafin ta wuce haka ta shiga amma sai ta iske tana barci kamar kullum Baba ne zaune bakin Æ™ofa yana wankin Gwoggo da yaranta biyu mace da namiji Æ™anne a gurin Tataah. Sudees da Tataah ta girma da shekaru biyu sai Ruhaima wacce ta girmi Tataah da shekara É—aya amma sune BAba ke yiwa wanki, har Æ™asa ta duÆ™a. “Baba ina kwana” Da sauri ya É—ago dan sam bai lura da zuwanta ba sai maganarta yaji, duba gefe da gefensa yayi dan ko gaisuwarta Gwoggo ta hana ya amsa a hankali ya ce”Lafiya Æ™alau Tataah zaki wuce gurin aikin ne?” GyaÉ—a kai tayi alamar “I” Ba tare da ta ce komi ba, shuru ya biyo baya na É—an wani lokaci a hankali ya ce”Ki tashi kije kawai basu tashi bacci ba” MiÆ™ewa tayi tana tafiya a hankali ba tare da ta ce Æ™ala ba, yabi bayanta da kallo yana girgiza kansa. Tayi tafiya mai nisa kafin ta iso bakin titi sannan ta daÉ—e tsaye kafin ta samu abin hawa, lokacin da ta isa gidan abincin bakwai saura minti goma, hamdala tayi domin Æ™a’idar shiga gurin bakwai ne bata san latti kamar yadda aka gargaÉ—e su da hakan shiyasa take fitowa da wuri. “Baki latti har kin iso?” ÆŠan murmushi tayi bata ce mishi komi ba, ciwon da ya gani a goshinta ne yasa shi salati tare da faÉ—in “Ciwo kikaji?” Sai lokacin ta tuna da ciwon ta ce”FaÉ—uwa nayi!’ Tare da wucewa dan bata san wata magana kuma akan ciwon. Lawan abokin aikinta ne a gurin suna É—an gaisawa da shi amma ita ba da kowa take magana ba saboda kamun kai da gudun shiga abin da bai dameta ba. Gurin masu girki ta Æ™arasa tana temaka musu duk da ba aikinta bane amma tana sa hannu don sam bata da Æ™iwwar aiki, suma duk suka tambayeta ciwon abin da ta cewa Lawan shi ta maimaita musu, wajen takwas duk an gama wasu yayin da kuma wasu aka barsu a wuta saboda karsu huce. Mutane ma banbanta ne ke ta shugowa gurin abincin saboda sunan da gurin ya yi ana son abincin gurin sosai ko ba komi akwai tsafta ga daÉ—in abinci.
Tun bayan barin shi gurin abincin yake yawan tuno fuskar yarinyar, yaja tsaki yafi cikon masaki, kai tsaye gida ya wuce daret part É—insa ya shiga saman bed ya faÉ—a nan take kuwa barci me nauyi ya É—auke shi. Ya daÉ—e yana barcin har zuwa lokacin da aka fara ruwan sama, sanyayyen sanyin da ake ne ya Æ™arawa barcin nashi armashi ya shige cikin bargo ya naÉ—e yana kwasar baccinsa. Yaye bargon da akayi ne yasa shi buÉ—e idanuwa a hankali, idanuwansa suka sauka akan Faruuk dake riÆ™e da bargon, guntun tsaki yaja tare da gyara kwanciyarsa ba tare da yayi magana ba. “Aliyu magana fa nake” Ma’aruf da ya Æ™arasa shugowa ne ya ce”Kai sai kace baka san wane ne Aliyu ba, ka barshi fa idan ba haushi ne kake so ya kar ka ba” Zaunawa Faruuk ya yi bakin bed É—in yana faÉ—in “Tun jiya da yake Æ™asar jajayen can nake kiransa yana wulakantani amma ba komi na shi auren zai zo ne?” Jin abin da Faruuk ya faÉ—a ne yasa shi tashi yana É“ata fuska “Auren wa?” Ya tambaya so silent, Ma’aruf ya ce “Aurenka! Ko bazakayi ba ne?” ÆŠan smile ya saki na gefen baki kafin ya ce”Ku dai fitinannu Allah ya baku sa’a, ku dena lissafi da ni” Dariya suka saka su biyun har da tafawa “Ana maganar fitina har kai kayi magana Aliyu, wannan baccin ma da kake daga gani na wahala ne” Cewar Faruuk. Tsaki Abuturrab yaja tare da miÆ™ewa ya nufi bathroom ba tare da ya ce musu komi ba, su kuwa dariyar shaÆ™iyanci sukaci gaba da yi mishi. Bayan ya fito dukansu sukayi alwala sannan suka wuce masallaci jin ana tada salla. Ko da suka dawo cikin gidan suka nufa Ammi tasa house girl É—inta ta shirya musu komi. Aliyu ko kallon abincin bai yi ba, Faruuk daman yasan baci zai yi ba hakan yasa duka suka tashi kai tsaye motar Faruuk suka hau duka suka nufi Husse two gidansu Faruuk. Ammi da ta fito bin gurin tayi da kallo sosai ranta ya É“aci da ganin abin da sukayi “Abuturrab!” Ta furta da huci kafin ta tuno Faruuk “Shege yaro da maÆ™ar fuskarsa irin ta uwarsa wallahi duka sai nayi maganinku mtsuuuw!” Ta Æ™arashe maganarta da jan tsaki. Sareenah wacce ta fito yanzu ita ma bin gurin tayi da kallo kafin ta ce”Ammi ina su Yaya Aliyun?” “Yadda kika ga gurin wayam haka nima na fito na gani, ai kin san wannan Faruuk É—in idan har suna tare komi yayi shi Abuturrab ke yi” Sareenah da idanuwanta yayi ja saboda É“acin rai ta ce”Wallahi ba tun yau ba na tsani Faruuk kina ganin ko gani na yayi sai ya dinga mini wani kallo a raine” “Barni da shi daga shi har uwarsa na tsane su kuma nice maganinsu, kwanaki akan uwar Faruuk sai da mukayi faÉ—a da Alhaji kin san Æ™anwarsa ce kuma su biyu uwarsu ta haifa sonta yake kamar me, ni kuma bazan iya jura ba” Sareenah kasa cewa komi tayi sai numfashi da take saki cike da jin tsanar Faruuk a ranta.
Sosai Mami ta cikawa su Abuturrab gaba da abinci, cikin farin ciki suka fara cin daddaÉ—an abinci Mami da ta kasance gwana gurin iya tsara girki. Faruuk ya kai lomar jellop rice bakin shi da taji haÉ—i na musamman ya ce”Mami gaskiya ko dai anan gidan zamu zauba da Rahina domin ta iya girki kamar naki?” Abuturrab ya É“ata rai kafin ya ce”Sai ana maganar mutane kana sako wannan Æ™wailar yarinyar dan Allah ka din ga magana irin ta mutane” A yadda yayi maganar sai ka rantse da Allah ba shine ya yi ta ba domin laÉ“É“an sa ne kawai ke motsawa Faruuk ne kawai yaji mai ya ce yadda kuma ya mayar da hankalinsa wajen cin abincinsa sai ka rantse da Allah ba shine yayi maganar ba. Mami kam murmushi take ta ce”Wallahi ba dani ba wai gaÉ—a a hurumi, me zai jani zama da ku a gidan nan? To sai dai idan wata laluurar amma kaje da matarka can da rawar kanka” Tana faÉ—a ta miÆ™e ta basu guri, dan tasan halin Faruuk da shegen rawar kai yanzu sai ya ce zaiyi wata maganar. Faruuk ya mai da hankalinsa gurin Abuturrab bayan wucewar Mami “Limamin bayan fage me kake cewa É—azun?” Banza Aliyu yayi masa yana ci gaba da cin abincin. “Da a maimaita mana da anji zazzafar amsa” “Mtsuw!” Abuturrab yaja tsaki ba tare da ya kuma cewa komi ba har suka ida. Ganin lokaci yaja ya ce”Malam zo ka mayar dani gida dare nayi” “Gida kuma? Wallahi baka isa ba zance zaku raka ni gurin Rahina” ÆŠan zaro ido Abuturrab yayi alamar tsoro kafin ya ce”Zance? Mene ne hakan!” “Oho dai idan mun je ka san ko mene ne” TaÉ“e baki yayi tare da É—aga kafaÉ—a cikin cool voice É—in sa ya ce”Allah ya raka taki gona ba da Aliyu za a ganin shirme ba” Wata muguwar dariya Faruuk ya saki Ma’aruf ya ce”Ina rabaka da kiwo kana Æ™yalla ta mutu Aliyu, kar nan gaba kaÉ—an ka afka Æ™aton tafkin so kafi mu zaÆ™ewa” “Allah sitiri buÆ™wi ba da ni ba” “Wai nikam ina kaji hausa ne?” ÆŠan murmushi ya yi tunowa da wani abu kafin ya basar bai ce komi ba. Faruuk shi ya maida Aliyu gida kafin ya sauke Ma’aruf a nasu gidan sannan ya wuce gida dan sanyin da ruwan saman da akayi ya sakar yasa shi jin bazai iya zuwa gurin Rahina a yau ba.
Ammi da ta kasa ta tsare tana jiran dawowar Abuturrab anan bacci ya yi gaba da ita, duk a tunaninta da mota ya fita idan ya dawo dole zataji Æ™arar motarsa, shi kuwa a bakin gate yasa Faruuk ya ajiye shi sannan ya shugo ta Æ™aramar Æ™ofa, daret part É—in sa ya nufa bai ma yi tunanin shiga part É—in Ammin ba. Coppe ya haÉ—a yana sha a hankali daidai ringing É—in wayarsa, jawo wayar yayi ganin mai kiran yaja tsaki kafin ya É—auka. “Lafiya cikin tsohon daren nan?” Sanyayyar ajiyar zuciya ta saki wanda shi kansa da yaji ta, cikin kwantar da murya ta ce”Tun É—azu nake turo maka saÆ™o ba amsa, daman so nake naji ko ka sauka lafiya?” Huci ya fesar me zafi kafin ya ce”Baheerah please ki bar ni, wai ana so dole ne?” Tun kan ya sauke numfashi ya fara jin Æ™arar kukanta Ƙit! ya yanke kiran cike da fusatuwa ji yayi coppe É—in ma ya fita ranshi kitchen ya mayar tare da shigewa bedroom sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kunna na’ura me É—umama É—aki. Sareenah ce ta fito cikin sanÉ—a ta niyyarta na barin gidan domin saurayinta ya kirata yana wuce zasu wuce club, ganin Ammi a parlour taji ranta ya É“aci, gurinta ta Æ™arasa sai ta tarad da bacci take mai nauyi ajiyar zuciya ta saki tare da ficewa daga parlourn cikin sauri. Officer na ganinta ya sara mata “Ranki ya daÉ—e barka da fitowa” Murmushi ta saki tare da zage zagarta ta ciro dubu biyar ta bashi. Godiya ya fara mata da wasata ta ce”Kamar kullum kar wanda yasan da fitar nan, har Ammi” “An gama ranki ya daÉ—e” Har takai gate kuma ta juyo “Officer Yaya Aliyu ya dawo kuwa?” “I Ya shugo tun É—azu kuwa” GyaÉ—a kai tayi tare da fita daga gidan, nesa kaÉ—an da gidan ta hango shi cikin baÆ™ar motarsa da sauri ta Æ™arasa, tun kafin ta iso ya buÉ—e mata gaban motar, murmushi suka sakarwa juna “Ma’aruf!!!” Ta ambaci sunansa cike da Æ™warewa. Tada motar yayi sai da ya hau titi ya ce”Sareenah ta Aliyu” GabaÉ—aya suka saka dariya ta ce”Har kasa naji wani sanyi, amma nazu raina ya É“aci da Faruuk ya jaku wallahi ban taÉ“a tsanar wani irin Faruuk ba” Numfashi ya fesar da cewa”Faruuk bai da matsala jininku ne kawai bai zo daidai ba, shi ya mayar dani gida yana wucewa kuma na samÉ“o nan” Dariya tayi ta ce”Shi ya sa fa nake Æ™aunarka kai ma kasan kan bariki” Ya ce”Hahahaha Sareenah kenan” Da wannan hirar suka Æ™arasa shahararren gidan rawar dake garin na Abuja. Guri suka samu sukayi ciye-ciyensu da shaye-shayensu abin da Aliyu ko Faruuk basu san Ma’aruf nayi ba kenan. Daga Æ™arshe ma É—aki suka kama suka gama sheÉ—ancinsu. Sareenah bata dawo gidan ba sai wajen biyar na asubahi, har lokacin Ammi na gurin tana sharara bacci, kasancewar Sareenah ba cikin hayyacinta ta ke ba yasa bata lura da ita ba bedroom É—inta ta wuce tana zuwa ta faÉ—a saman bed wani fitinannan bacci ya yi awon gaba da ita….
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUÆŠINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
………..🥚👩❤️👨💥🌎….
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUÆŠINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_