Girke-Girke

(Mu Koma Kitchen) Wasu samfurin Girke Girke na Zamani Ku karanta anan

VEGETABL BEEF SAUCE

INGREDIENTS:

1.Nama

2.Tattasai and tarugu 

3.Al’basa and Oil

4.Tafarnuwa and citta thyme, curry 

5.Onga

6.Carrots and green beans

PROCEDURE:

Da farko ki jajjaga dukkan kayan hadi kuma ki yanka vegetables including Albasa  sai ki zuba Oil a wuta, juye albasa idan ya ďan soyu sai ki zuba kayan miya yana fara soyuwa sai ka sa spices ki jujjuya sai sai ki zuba Vegetables tare da yankakken tafasashen nama ki jujjuya, sai ki zuba ruwa kadan wanda zai sanya Vegetables su yi laushi sai ki rufe, kina duba ruwan idan ya tsotse kayan lambun kuma sun yi laushi sai ki sauke……. 

FANKASU

INGREDIENTS

1.Alkama 3 Cup

2.Yeast tea spoon 1

3.Flour 2 Cup

4. Mai

PROCEDURE:

Da farko zaki kai Alkama a nika miki sai ki tankade da rariyan laushi shima Flour zaki tankade shi a cikin Alkama, sai ki zuba ruwa kiyi ta juyawa har sai ya hade sosai, kwabin kamar na fanke zaki yi amma yafi Fanke tauri sosai, sai ki rufe ki barshi ya tashi sosai, idan kinji akwai tsami zaki iya dan zuba ruwan kanwa ki buga sai ki rufe.

sai ki sa mai a wuta idan yayi zafi sai ki rink’a debo kwabin kina yin sa da fadi sannan kina huji a tsakiya sai ki sa cikin mai ya soyu, idan ya soyu sai ki kwashe…..

KOSAI

INGREDIENTS:

 

1.Wake 3Cup

2.Maggi

3.Gishiri

4.Curry

5.Man gyada

6.Attarugu

7.Albasa

8.Tattasai

 

PROCEDURE:

Da farko za ki wanke wake ki cire hancin ya fita tas, sai ki jika shi kamar na 10Minutes idan ya jika sai ki zuba Attarugu and Tattasai, sai ki yanka Albasa sannan ki bayar a kai miki markade, idan ankawo sai ki zuba Maggi Gishiri Curry, sai ki dauko ludayi fara bugawa.

Zaki bari sai ya bugu sosai sai ki dora Oil a wuta idan ya yi zafi sai ki nema karamin ludayi ki na diba ki na sawa a Oil kadan-kadan kina soyawa. Idan ya soyu sai ki kwashe…… 

COLESLAW

INGREDIENTS:

1.Cabbage and Carrots

2.Green pepper and Onion

3.Mayonnaise, Milk

4.Sugar

5.Cucumber

6.Eggs

PROCEDURE:

Da farko zaki samu Cabbage ki wanke shi da kyau, sai ki yanka sirara, idan kin yanka sai ki dauko Carrots ki kankare dattin, sannan ki kurza shi, sannan ki kawu Cucumber shima ki yanka shi kanana, sai ki dauko Green pepper ki yanka kana-kana ita ma Albasa haka haka zaki mata amma ba dayawa zaki yanka ba, dan kadan ma yayi, sannan zaki hada su wuri daya idan kuma duka a wuri daya, sai ki dafa Egg shima zaki yanka shi ne  kana-kana, sai ki dauko Mayonnaise ki dibi dai-dai yanda kike ganin zai isheki, Madarar ruwa ki tsiyaye amma ba da yawa ba sannnan ki zuba Sugar wannan Madarar shi ne zai sa Mayonnaise din ya tsinke yanda zaki ji dadin hada shi da ganyen, idan kinyi haka shi kenan ya hadu……

 *SALMA’S KITCHEN*

DAN WAKE

INGREDIENTS:

1.Shinkafar tuwo

2.Flour

3.Kuka

4.Kanwa

5.Man gyada

6.Maggi

7.Yaji

PROCEDURE:

Da farko zaki nemi shinkafa ta tuwo kiwanke ta fita tas,

sai ki kawo ruwan dumi mai zafi sosai ki zuba akan wankekken shinkafarki ya dan yi kamar 20minutes

bayan ya yi 20minutes sai ki tsiyaye ruwan ki bayar a kai miki inji a markada, kar a sa ruwa da son samu ne ayi shi da kauri,

bayan an markada sai ki kawo Flour ki tankade a kan markadadden shinkafar, sai ki sa kuka da ruwan kanwar da kika jika

sai ki kwaba sai yayi daidai kaurin da ki keso, sannan sai ki fara sakawa a ruwan zafin da kika dora idan ya tafasa, sai ki dinga jefawa idan yayi sai ki sauke ki kwashe ki tsane kisa mai da Maggi and yaji, idan kina bukatar salad zaki iya sa kawa…….

KOSAI AND FISH

INGREDIENTS:

1.Egg

2.Fish

3.Albasa

4.Attarugu

5.Flour

6.Maggi

7.Gishiri

8.Man gyada

 

PROCEDURE:

Da farko ki samu kifi wato (ice fish) ki wanke sai ki zuba a tukunya ki sa Maggi gishiri Albasa ki dora akan wuta, idan ya dahu sai ki sauke ki cire kayar shi sai ki zuba kifin da Attaruhu Albasa a turmi ki daka su, idan kinyi haka sai ki dauko Egg ki fasa ki zuba a ciki, sannan ki dauko Flour ki zuba kadan, sai ki zuba gishiri da Maggi ki juya sannan ki rink’a mulmulawa kina sakawa a cikin man gyada mai zafi kina soyawa idan yayi brown sai ki kwashe……

SPINACH EGG SAUCE

INGREDIENTS:

 

1.Spinach (Alayyaho)

2.Eggs and Oil

3.Tattasai, Tarugu 4.Al’basa and Garlic

 

PROCEDURE:

Da farko zaki wanke Alayyaho ki yayyanka kanana sai ki yayyanka Albasa ki jajjaga kayan miya, sannan zaki samu tukunyar da babu komai sai ki dura a wuta ki juye Alayyahon duka, sai ki tafasa shi, idan kina da steamer zaki iya saka shi a ciki ya turaru sai ki sauke

ki zuba Oil kadan a tukunyar sai ki juye Albasa, idan ya dan soyu sai ki zuba kayan miya, ki zuba Seasonings ans Spices, in ya soyu ki juye alayyahon ki jujjuya su hade, ki kada Eggs ki juye a ciki ki juya su hadu da kyau, in ya gama soyuwa sai ki sauke……

GASHASHEN KIFI

(Grilled Fish)

INGREDIENTS:

1.Fish tilapia

2.Albasa, lemon 

3.Ginger, Kanunfari,

4. Masoro, tafarnuwa, 

5.Garin yaji ko Tarugu

6.Maggin Knorr,

7.Gishiri, Curry Thyme

9.Man gyada

PROCEDURE:

Da farko ki wanke kifin ki ciki da waje, idan kin wanke sai ki tsane ruwan, daga nan sai kiyi Blending kanunfari da masoro, Ginger thyme, da sauran su, idan kuma kina da garin su shikenan sai ki juye a mixing bowl, sannan ki dauko Albasa ki saka, ki zuba tafarnuwa idan Ginger ne dake to a cikin nan ne zaki hada shi, sai ki yi Blending ko ki daka idan Attarugu ne dake ba garin yaji ba a nan zaki saka shi,

daga nan sai ki juye duka hadin a wuri daya, ki zuba Curry kadan ki zuba Knorr da Gishiri, sannan ki matse lemon ki zuba, sai ki zuba Oil yanda hadin zai kama jikin kifin, bayan kin jujjuya sai ki yiwa kifin tsagu tsagu (gashes) a jikin sa kamar guda biyu zuwa uku, gaba da baya yanda ruwan hadin zai shiga ciki, sai ki zuba masa dukkan hadin yaji sosai ya kama, ragowar ma duka ki zuba a kansa, sai ki saka a Fridge yayi kamar 30minutes in a Freezer ne so ake kayan hadin da ke jikinsa su bushe a jikin ba wai yayi k’ank’ara ba, daga nan kuma sai kiyi gashi in baki da Ovn ki tada rushi ki sa abu mai raga raga sai ki daura kifin, kina yi kina jujjuya wa har ya gasu……

SAUCE-SAUCE

NGREDIENTS:*

1.Albasa

2.Tarugu, Tattasai 3.Green pepper

4.Tafarnuwa

5.Gishiri Maggi knorr

PROCEDURE:

Da farko zaki yanka Al’basa Tattasai Green pepper shape da kike so amma dan manya, sai ki daura Oil a tukunya kamar k’aramin ludayi idan yayi zafi sai ki zuba Albasa da Tattasai ki yi ta juyawa, daga nan sai ki zuba nik’akken tarugu biyu ko garin yaji da tafarnuwa sai ki zuba ruwa kadan yanda zasu dahu, zaki ga ya dahu shi bai dahu can ba, shi kuma ba danye ba wato daidai wa daida, daga nan kifin ki ya gasu in kina so sai kawai ki zuba wannan sauce din………

SALAD AND MEAT

INGREDIENTS:

1.Carrot

2.Cucumber

3.Eggs

4.Al’basa

5.Tumatir

5.Nama

7.Sweet pepper

8.Mayanoise 

9.Salad cream

10.Maggi

PROCEDURE:

Da farko dai zaki tsaftace komai kiyayyanka su Salad din manya-manya, ki gurza carrot sannan ki dafa Eggs din , shi Naman zaki dafa shi ne amma kadan zakisa bayan kindafa kiyayyanka a tsai-tsaye kihada komi, duk abubuwan da kika yanka ki hada su guri daya, Mayanoise ko Salad cream ki zuba kisa Maggi ki jujjuya zakiga yatsinke, sai ki kawo hadin Salad ki zuba hadinnan na Mayonaise ko Salad cream, ki jujjuya da kin gama shikenan…….. 

ACI LAFIYA

KOSAN BUREDI AND EGG

INGREDIENTS:

1.Garin biredi

2.Egg

3.Attarugu

4.Maggi

5.Curry

6.Tafarnuwa

PROCEDURE:

Da farko ki samu biredi sannan ki guggutsura shi kanana har sai ya bushe sannan a mutsuttsuka shi, sai ki fasa kwai kamar biyar a ciki sannan ki zuba Maggi, ki jajjaga Attarugu da tafarnuwa ki zuba da Curry. sai ki kwaba Eggs sosai. sannan ki dauko abun soya  ki dora a kan wuta kina zuba Man gyada da Albasa, idan ya yi zafi sai ki sa cokali ki rink’a gutsura kullun kamar yadda ake gutsura kullun kosan wake kina zubawa a cikin man gyadan, idan dayan gefen ya soyu sai ki juya zuwa dayan gefen domin ya soyu  sannan ki   kwashe……

DANBUN NAMA

INGREDIENTS:

1.Nama 

2.Attarugu

3.Maggi

4.Albasa

5.Gishiri

6.Tafarnuwa

7.Citta

8.Man gyada

9.Curry

PROCEDURE:

Da farko zaki wanke Nama ki sa Albasa da Maggi ki dora  wuta ki bari ya tafasa sosai.

Idan yayi sai ki sauke ki kawo turmi mai kyau ki daka Naman, idan ya daku sai ki kwashe, ki jajjaga Attarugu da Albasa da Tafarnuwa Citta ki zuba akan dakekken Naman, sannan ki sa Maggi Curry ki juya sosai komai ya hadu, idan yayi sai ki dora tukunya a wuta kisa Man gyada sai ki  kawo Naman ki zuba sannan ki fara juyawa idan ya fara kamshi alamun yayi yanda akeso zaki iya kwashewa , ki nema plt me kyau ki juye……

FATEN KUSKUS

INGREDIENTS:

1.Couscous

2.Man gyada 

3.Maggi Ko Rayko

4.Gishiri, Curry

5.Alayyahu 

6.Gyadar miya

7.Gwangwanin tumatir

PROCEDURE:

Da farko zaki soya kayan miyan da muka jajjaga a manja ko mangyada sai ki zuba ruwa, sannan ki zuba su Maggi da dakakkiyar gyadar miya, Curry Gishiri, idan ruwan ya tafasa sai ki dauko Couscous ki rinka zubawa ahankali kina juyawa har ki gama, sannan ki rufe amma kina rinka yi kina juyawa don kar ya dunkule, idan ya nuna sai ki kawo yankakken Alayyahun da Albasa ki zuba idan suka nuna sai ki sauke…….

Alhamdullah Alhamdullyah, Alhamdullahi Alah kulli halin.

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!