*MUGUN ABU JAKADA..*
_(Her Rude Boss)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 1 and 3
Free page
*Littafin Mugun Abu Jakada na kudi ne akan naira dari shidda 600, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 07066537181, Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 07066537181*
*A wannan karon ba zanyi maku free pages da yawa ba, iyakar page ukku sune zanyi maku a matsayin free page*
*_(The Bite Of Betrayal)_*
A matuk’ar fusace ya fito daga parlour’n ya nufi daya daga cikin motocin dake a parking space na katon Mansion din, Mami ta biyo bayansa walking briskly tana mashi magana amma ko juyawa baiyi ba ya shige mota ya figeta with speed ya dannata waje kamar zai bi ta kan Mai guard.
Mami ta durkushe tareda fashewa da kuka, “Abbakhar mi yasa zakayi mamu haka? Mi yasa zaka zab’i soyayya akan mu? Mi yasa zaka fifita mace akan mu?” Ta k’arasa maganar muryarta tana rawa.
Asiya dake bayanta ta buga tsaki, she stuttered walking with joy har zuwa gabanta tayi dariya cike da nishadi tana mai jin dadin abun da ya faru, “Kin bani tausayi matuk’a, ko wahalar nakudarsa da kika sha ba ya gani yana maki taurin kai… Koda yake ba ya da tarbiyya ne that’s why yake behaving haka, koda yake dani dake mun san cewa saboda baki iya bada tarbiyya bane shiyasa ba ya da ita, fiye da haka zai aikata, dama waye zai tsammaci tarbiyya daga yaron da ya tashi a hannunki, bunch of useless being.” Ta juya ta shige ciki tana mai shekewa da dariya tana tafiya tana nishadi na abun da ya faru.
Mami taji ciwo kwarai akan maganganu da Asiya ta fad’a mata, wacce a auren wuri ta isa haihuwarta, amma ya ta iya, fad’an da yafi karfinka hakura kake dashi.
******
A fusace yake sarrafa motar with speed kamar wanda zai tashi sama yana huci, ya bugi starry ya danna horn wa motar dake gabanshi, “Damn it, ka bani waje fool with this you damn called car,” he shouted. Ya figi motar ba tareda yabi takan wanda yake tuk’a waccen motar ba, ya bugi starry a karo na biyu, “Damn it, bazan tafi karatun ba, bazan tafi kasar wajen ba, damn you kun janyo wa kanku na fasa karatun baki daya, babu wanda ya isa ya rabani dake Jidderh.”
Da matuk’ar gudu yake jan motar yayinda maganganunsu suke mashi amsa kuwwa a kunne wanda yake ji tamkar saukar aradu akan kunnuwansa, “You must go abroad and study, it’s the only way to secure your future.” Amma ba ya san zuwa kasar waje karatu, yana so ya zauna a kasarshi ta gado ya rayu da masoyiyarsa Jidderh, ya auri Jidderh, su gina rayuwa mai inganci. A shirye yake ya bujurewa iyayensa, ya rabu dasu da dukkanin wani gata da yake samu. Damn them, he thought, his anger boiling over.
Gudu yake sosai da motar ba tareda ya damu ba, ita kadai yake tunawa His Jidderh and rayuwar soyayya da kulawa da zasuyi a tare. Mami ba zasu tab’a fahimta ba, abun da suka damu dashi kawai shine kudi da matsayi, basu damu da farin cikinsa ba, ko mafarkinsa a rayuwa. Ba zasu iya tankwarashi ba, zai bi zuciyarsa ne da farin cikinsa. Ya k’ara gudun motar – 90, 100, 110. He felt alive, free, kamar wanda yake gudu wa kurkukun da Mami suke son saka farin cikinsa a ciki. But deep down yasan cewa yana gudu ne zuwa gareta. His Jidderh. Kuma zai iya sadaukar da komai domin kasancewa tare da ita.
Parking motarsa yayi daidai da fitowarta, tunda ta fito yake kallonta har ta tsaya kusa dashi, the atamfa she wears paired with the veil dake akan kafad’arta, with kallabi wanda ta kashewa dauri samfurin ture kiga tsiya, which adorned her looking gorgeous and attractive. “Koda ka kirani muryarka babu walwala… Waye fad’a min inje inyi fad’a dashi? Waye ya tab’a min yaya Abbakhar inje inji dalili? Yeah zamu dambace ne…” ta ce da murmurshi akan fuskarta wanda ta tabbata yana matuk’ar so a tattare da ita.
Saida yayi dariya yana kallonta imagine tana dambe, dariya yake har da kyakyatawa, well she don’t belong there, she belong to his house by his side as his wife, the love of his life Hauwa kulu, Maijidda, his Jidderh. “Murmushi da kayi yana nuni da nayi nasara… Ya ake ciki?” Abbakhar ya dunkule hannu ya kaiwa iska naushi yana huci kamar bashi bane yake dariya not a while ago, “Gidanmu ne suke son su rabani dake Jidderh…”
“Ban gane ba!…” Ta katseshi.
Under his breath yace, “Damn it, sun ce saidai in tafi abroad karatu, that I can’t marry until nayi PhD, ni kuma aurenki ne burina, aurenki nike son inyi in cigaba da karatuna a nan amma sun kasa fahimta, don haka na hakura da karatun baki daya, secondary da nayi ya isheni tunda karatun ba rayuwata bane ba, na hakura dasu, babu ni babu su, zan aureki, zanyi koda daukar kaya ne a tasha in ciyar dake… Jidderh that’s how I love you.” Jidderh ta zaro idanu jin abun da yake fad’a, “What! Magana fa ake ta iyayenka!”
“Ehhh tunda har basu sona dake nima bana sonsu, na hakura dasu, babu ni babu su na hakura dasu, zan iya rayuwa ba tareda dasu ba, i can survive on my own… Jidderh dukkanin wanda ba ya sona dake nima bana sonshi, kin fiye min komai a rayuwa, that’s how I love you.”
“Magana ake ta iyayenka, wadanda suka haifeka, suka kula da kai, suka baka gata da jin dadi na rayuwa har ka girma ka ganni kaji kana sona.”
“Jidderh na hakura dasu, na rabu dasu tunda basu sona dake.”
Ta fashe da dariya har da kyakyatawa sai kuma ta murtuke fuska kamar ba itace take dariya ba, tace,
“Let be the bitch then it’s worth it, ina ta gocewa amma saida ka kaini bango, well I’m gold digger, yeah, damn yes… Ina k’ok’arin rabuwa da kai lafiya amma kana gocewa, ina son mu rabu lafiya amma ka tursasani bayyana daya fuskata ta mai idon cin naira, not that your innocent Jidderh, your kind Hauwa Kulu… Kana sona, Right? Kuma saboda ni zaka iya rabuwa da iyayenka, Right?”.
“Ehhh… Jidderh, that’s how I love you.”
“Well Ina son kudi fiye da yadda kake sona, kaunata da kudi yafi kaunar da kakeyi min, and iyayenka ne suke da kudi, don haka idan baka tare dasu ka koma talaka, matsiyaci, matalauci, and I don’t date poor people, ni da talauci munyi hannun riga bazan maimaita kuskure da Mamana tayi na auren talaka ba.”
Tayi tab’i akan fuskarsa ganin ya zuba mata idanu fuskarsa dauke da matuk’ar mamaki.
“Are you there, of course you are, yeah bari inyi maka kwari-kwari, ina kulaka ne saboda kudi, saboda kana bani kudi, but kudin ba naka bane, na iyayenka ne, tunda har ka rabu dasu ka koma talaka kenan, and Jidderh bazata iya rayuwar talauci ba…” Ta wurga mashi waya dake hannunta, “Here you go, wayar da ka bani ce, ka siyar ka had’a sai ka nemi sana’a da zakayi a tasha, watakila a can zaka samu wacce zata aureka a haka, sauran kudin da ka kashe min kuma na cinye ka aiko mai karfin gidanku yazo ya amsar maka… Amma idan ka sauya shawara akan barin iyayenka zaka iya dawowa mu dasa daga inda muka tsaya, don’t blame me, you brought it upon yourself, that’s how I love money that I can’t hide, same as the way you love me.”
She walk forward and backward ta juya ta k’ara juyawa kamar model, “Jidderh ba matar talakawa bace ba…” she said.
Ta buga tsaki, he’s totally speechless, his Jidderh the love of his life, he can’t believe it.
Page 2
Tunda ta fara magana yake kallonta cike da mamaki, hawaye suna bin fuskarsa, he feel the betrayal, his Jidderh turn out to be this, his Jidderh the love of his life, wacce ya shirya rabuwa da iyayensa saboda ita, wacce ya shirya rayuwar talauci a saboda da ita, wacce ya shirya ya rabu da dukiya da tarin gata da yake dashi duk saboda ita, ita ce tayi mashi haka, ji yake dama ace mafarki yake, that ba ita ba bace, ya kasa yarda, yana k’aryata abun da yaji da kunnuwansa, that’s how he loves her.
“Do you love me for who I am, or for my family’s wealth? Jidderh ni Abbakar kike so ko kuma dukiyar iyayena?” Ya tambayeta muryarsa tana rawa, watakila ba haka bane, watakila bai ji abun da tace bane ba, his Jidderh ba zatayi mashi haka ba.
Jidderh ta saki wani shegen murmushi, idanunta a bude da mugunta. “Oh, darling, I love you for both, Ina son Abbakhar kuma ina son dukiyar iyayensa” ta karasa maganar kamar wacce take mashi rad’a. “Amma idan zamu fuskanci gaskiya, dukiyar gidanku ta taka muhimmiyar rawa akan wannan alaka, like kaso casa’in da tara. Ina son jin dadin rayuwa, mukami, matsayi, the status, the power, waye bazai so hakan ba, and I’ll do whatever it takes to get it, zan iya aikata komai domin in cimmasu.”
Ji yayi sanyi yana yawo a kasusuwansa a lokacin da ya gane gaskiyar da ya kasa fuskanta, gaskiyar da baya son ta kasance gaskiya, gaskiyar da yake karyatawa despite the fact that itace gaskiya. Jidderh bata tab’a sonshi ba, tana kulashi ne saboda kudi da yake bata. Kudinsa take so bashi ba.
“Jidderh ke azzaluma ce, you’re wicked,” ya fad’a muryarsa tana shaking a yayinda hawaye suke sauka akan fuskarsa. “Jidderh you used me, manipulated me, kinyi amfani dani, har na shirya rabuwa da dangina, na shirya rabuwa da dukiya da gata da nike samu a wajen iyayena domin kasancewa a tare da ke, and now you’re flaunting it in my face? Haba, ki tausaya min mana baki ganin abun yayi min yawa.”
“Ah, Haba,” ta fad’a tana juya idanunta. “Ka daina zagaye-zagaye ka fuskanci gaskiya. Arzikin gidanku kyauta ne wacce ban shirya watsar da ita ba.”
“Kyauta” ya maimaita yana mai d’aga muryarsa da tsawa. “Kina kiran yaudarata saboda dukiyar gidanmu a matsayin gaskiya?”.
“Gaskiya ne shiyasa na kirashi gaskiya.” Tace tana mai d’aga kafad’a alamar bata damu ba.
“Na samu dama ne nayi amfani da ita. And you kaga dama ne na soyayya da Jidderh mai kyau, kana matuk’ar buk’atar soyayya… it’s almost pathetic. Abbakhar dukiyar iyayenka kyauta ne wacce idan ka shirya watsar da ita, Jidderh bata shiryawa wannan ganganci ba ko ince bacewar basira. Ina son kudi kuma zanyi amfani dasu inyi rayuwar da ta dace dani, that’s rayuwar jin dadi. Ka fusata ne kawai saboda baka da kwanya da zaka gane miye yake faruwa.”
“Bani da kwanya?” ya maimaita, yana mai d’aga murya, he can’t believe abun da take fad’a mashi akan fuskarsa.
“You think you’re so much better than me, don’t you? You think you’re so much smarter, so much more clever, ke a ganinki kin fini dubara da wayo?”.
“Ahh, ba na tunanin haka,” ta fad’a da murmushi akan fuskarta. “Gaskiyar itace nice wacce nike juya akalar wannan alaka tun daga farko… You’re just a puppet, darling… Kai kamar dan kukuye ne, shi kuma d’an kukuye abun juyawa ne don haka ka koma ka nemi gafara a gidanku, ka durkusa ka rokesu kayi kuka a gabansu kace masu ka tuba su yafeka that zakaje kayi karatu abroad, cry, beg for mercy, be miserable har su tausaya maka su karbeka ka dawo mu dasa daga inda muka tsaya domin ni bani da damuwa as far as zaka rink’a min aike daga abroad, abun alfahari ne a gareni wanda zan aura ace yana karatu abroad, don’t you think…”
“Ki dakata,” yace muryarsa tana cracking. “Kawai ki dakata, kina juya komai ne, kina mayar dashi kamar ina hauka ne. Ina ji kamar bani da hankali. Ina jin kunci a zuciyata, ina jin radadi a zuciyata. Ina tunanin mu masoya ce wanda suke son junansu da gaskiya. I thought kina matuk’ar sona kamar yadda nike matuk’ar sonki.”
“Son junanmu da gaskiya? That ina matuk’ar sonka…” Jidderh tayi dariya. “You really are naive, aren’t you? Babu wata alaka ta soyayyar gaskiya, idan akwai ban yarda dashi ba. There is nothing like real relationships, there’s only power and control, and I’m the one who’s been controlling this relationship from the beginning.”
“Ke muguwa,” ya fad’a da tsawa. “You’re a heartless, soulless monster. And I hate you. Na tsaneki, bana son ganinki, na tsaneki, ban kaunarki.”
Jidderh was like, “Oh, haba har jikina ya fara rawa, cikina ya dura ruwa,” tana nuna halin ko in kula. “Ka tsaneni? That’s cute, abun yayi kyau, but hate is just a weakness, darling, and I don’t have weaknesses. I only have strengths. That’s who Jidderh is…”
“Bace min daga gani,” ya daka mata tsawa. “Leave me and my family’s wealth behind. I don’t want to see your face again.”
Jidderh was like, “So be it,” ta shige gida ta barshi a tsaye totally speechless.
******
Jidderh tana shiga ciki ta tarar da gidan ya hargitse da kukan k’annanta yayinda Umma take yashe a kasa bata motsi, da gudunta ta k’arasa inda take yashe, ta durkushe tana mai tallafota da hannuwanta tana kuka tana girgizata.
“Umma wake up, wake up… Safiya mi ya faru?”.
Macen cikinsu tace,
“Kira aka yi aka ce babanmu sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Takum kuma ya rasu, shine ta fad’i a kasa bata motsi muna ta magana bata amsawa.”
Jidderh ta d’aura a hannu a kai tareda fasa ihu saying,
“Wayyo mun boni mun lalace, wayyo babanmu, wayyo ummarmu, please yadikko ki tashi, yadikko ki tashi kadda kema ki tafi ki barmu.”
Tana ihu tana girgizata tana kuka wanda shine ya janyo hankalin neighbour dinsu suka shigo domin jin miye yake faruwa.
*****
Jiki a sanyaye ya shiga mota, direct ya wuce gida, ya zube akan kujera saying,
“Mami, Abbi… Ku yafe min akan b’ata maku da nayi, na tub’a na biku, na yarda zan tafi abroad karatu har sai kunce ya isa, zan zauna a can ko hutu bazan dawo ba.”
Mami wacce tayi mamakin sauyawarsa a cikin wannan k’ank’anin lokacin duba da yadda yabar gidan a d’azu.
“Da gaske zaka tafi karatun?” Tace da mamaki kwance akan fuskarta. Ya gyad’a kai, tace, “That’s good, Allah yayi maka albarka…”.
“Amin Mami, ki cigaba da saka min albarka domin inyi albarka kadda in had’u da diyan banza.”
Abbi yace, “That’s good for you that you choose to go it willingly, dama itace take lallab’aka domin ni ina da hanyoyi da yawa da zanyi maganin taurin kanka, saboda na fika taurin kai.”
“Tuba nike, kaina a kasa,” Abbakhar ya fad’a.
Mami ta dubi Abbi tana mashi alama da yayi shiru kadda yayi provocation dinsa tunda har sun ya samu ya yarda zai tafi karatun, Abbi yayi banza da ita saying,
“Kaje ka shirya, yau zaka wuce Abuja, gobe kayi boarding flight to London.”
Yace, “Sure.”
Asiya dake zaune a daya bangaren kuma tana jin komai, ta tab’e baki under her breath tace,
“Damn it, ayi dai mu gani.”
Ta fusata matuk’a domin ba haka taso ba, taso ne Abbi ya koresa that she will be only child and daga baya ta kori Mami, that will make her the only person in his life.
****
Seven Years Later,
A sanyaye ta fito daga kamfanin wanda shine waje na biyar da taje neman aiki amma babu sa’a, tunda sanyin safiya ta baro gida but no luck, rabonta da abinci tun kunu da tasha da safe, ta gaji matuk’ar gajiya har jiri take gani, ta duba poss dake hannunta naira ashirin ne kadai suke rage mata, and she can’t trekk home a yadda take jinta, saidai wacce mafitar take da ita bayan wannan, ta harari tulun takardu dake hannunta, she have to struggle to take herself home with wadannan tulun takardun wanda sai a yanzu take jin nauyinsu.
Email ne ya shigo wayarta, she can’t believe it, jiya k’awarta da suka hadu online ta tura mata link na neman aiki a kamfanin wanda a daren ta cike, she can’t believe har sun kirata interview a yau, a map dake wayarta ta lalubo address dinsu, akwai nisa a tsakani, daga inda take zuwa roadblock tafiya ce sosai wanda daga nan zuwa kamfanin tafiya ce mikakka, amma bata wata mafita da ta wuce trekking there tunda itace take nema, ta sayi pure water tasha kafin ta kama hanyar kamfanin, tun daga round about mai fartanya.
Tayi turus tana kallon kamfanin da mamaki akan fuskarta, bata tab’a tunanin za’a samu gini mai tsayi da kyan wannan ba a garin Jalingo ba, gini kamar abroad, tunda take bata tab’a ganin gini mai kyau da haduwarsa ba, takardar gayyata da suka tura mata ta nunawa security suka barta ta shiga.
Wani kallon saida ta shiga ciki sannan ta tabbata da ginin yafi kama da abroad, ma’aikata ne a receptionist sanye da expensive suit suna kaiwa da komowa, duk wanda ta kalla ba ya tare da wahala, hutu ya zauna masu, tayi mutuwar tsaye tana k’arewa ginin kallo tana mamaki na girma, tsayinsa da k’ayatuwarsa, elevators ne ta kowanne bangare.
Murya taji daya bayanta saying,
“Ma’am how can I help you?”.
Jidderh ta juyo, daya daga cikin employee’n kamfanin ne, ta nuna mata takardar gayyata da suka turo mata, tace,
“Alright, let go.”
Heading to one of the elevator tana biye da ita, tun tana kirga floor da suke wucewa har ta hakura ta shafawa kanta lafiya, a floor na ofishin CEO suka tsaya wanda shine floor na karshe, ta ware idanu tana yaba kyawu, haduwa da girma na ofishin.
Fari ne sosai har yellow skin dinsa yake saboda haske, yana tsaye ya basu baya yana amsa waya, she can’t believe suit da yake sanye dasu which is worth millions of dollars, kudi ne wanda idan aka bata su zasu zame mata yanke talauci, that zasu sauya rayuwarta, she can’t believe it koda yake ba abun mamaki bane ba duba da girma, kyau da k’ayatuwar kamfanin.
Ya juyo tareda d’aga hannu, ta rusuna ta juya heading back, ji tayi yace,
“Come, and have a seat Miss Ahmad.”
Under her breath tace, “O çok tatlı.”
Ta zauna tana tattara nutsuwarta kadda kyawunsa ya saka ta rasa wannan aiki wanda shine last hope dinta.
“My name is Jidderh, kun gayyaceni interview…”.
“I’m Sadeeq.” Ji tayi yace, “Mun daukeki aiki.”
She can’t believe abun da kunnuwanta suka jiyo mata, ita ce aka dauka aiki a wannan kamfanin, ya cigaba da cewa,
“Salary dinki dubu dari ukku, kamfani zai siya maki gida, mota da kaya da zaki rink’a sakawa zuwa aiki.”
Jidderh ba zata iya misalta matuk’ar farin ciki da take a ciki ba, tana zuba mashi godiya kamar zata ari baki, amma a cikin zuciyarta ta fara samun waswasi. Maganarsa ta katse mata tunani, “Amma akwai sharad’i.”
Tace, “Na’am.”
Yace, “Akwai sharad’i, zan baki takarda ki saka hannu akan zakiyi aiki damu na tsayin shekaru biyu idan kika ce zaki ajiye aiki kafin lokacin zaki biyamu linki biyu na kudaden da muka biyaki tun daga daukarki aiki har zuwa wannan lokacin.”
Page 3
“So, Jidderh,” Sadeeq said, his voice smooth as silk. “Na daukeki aiki, ni daya zakiyi wa aiki, zaki dauki order ne kawai daga gareni, is that clear, ni na daukeki aiki, ni daya zakiyi wa aiki a wannan kamfanin.”
Jidderh ta gyad’a kai, tana k’ok’arin b’oye kokonto dake mata yawo a zuciya. “Na gode Sir.”
Sadeeq yayi murmushi mai cike da mugunta. “Excellent,” yace. “Yanzu saura ki saka hannu akan takardar, let’s just sign the contract.” Ya ajiye mata takardar contract ya daura pen a samanta, “Sign this, Miss Ahmad. A standard contract, merely a formality.”
Jidderh ta ware idanu a lokacin da hannunta ya sauka akan takardar, tayi wa rubutun dake a sama kallon kaikaice wanda aka rubuta da turanci.
“I, Jidderh Ahmad, agree to work for him for a period of two years. In the event of breach of contract, I will pay double the amount of any expenses incurred by the company in relation to my employment.”
Ji tayi sanyi ya fara shigarta, a karo na farko taji tsoron saka hannu akan wannan takardar duk da hali da take a ciki na matuk’ar buk’atar aikin. “What expenses?” she asked, stalling for time.
Sadeeq yayi murmushi yana mai lissafa kowanne motsinta. “Salaries, benefits, training… everything. And idan kika ce zaki daina aiki damu kafin shekarar shekaru biyu zaki biyu linki biyu na kudaden da kika samu a tare damu. Double, Miss Ahmad.”
Bugun zuciyarta ya k’aru, tana waswasi akan wannan abun da zata aikata ta sani tana matuk’ar buk’atar aikin amma tana hango kuskuren da saka hannunta a wannan takardar zai iya janyo mata, babu wanda yasan mi gobe zata haifar, saidai bata da wani zab’i da ya wuce saka hannu akan wannan takardar, ta daura pen akan takardar tayi signing tana mai sakin siririn tsaki.
Tana saka hannu murmushi dake a saman fuskarsa ya k’ara fad’ad’a saidai mugunta ce cike dashi.
“Welcome to….. Miss Ahmad,” ya furta. “You won’t regret this.”
Sai kuma ya zaro blank takarda ya ajiye a gabanta, ta dubeshi ta dubi takardar. “Ki saka hannu.” Ta dubeshi da mamaki sannan ta maida dubanta akan farar takardar wacce babu rubutun komai a ciki, tace, “Amma babu rubutu a ciki, kuma already na saka hannu a waccen takardar.” Saida ya k’are mata kallo sannan ya kalli takardar ya d’ago saying, “Yeah I know that, now sign…”
Ganin har lokacin bata saka hannun ba, yace, “Ko baki son aikin ne? Idan aikin ne baki so, bazan maki dole ba, kofa a bude take.” Ya nuna mata kofa, ganin tana b’ata mashi lokaci, yayi kamar zai janye takardar daga gabanta, da sauri ta saka hannu ta riketa like her life depend on it, “Ina so…” Ta janyo pen tayi signing akan takardar, yaja takardar yana wani shegen murmushi, under his breath yace,
“Welcome to the hell, barkanki da zuwa inda zaki wahala, inda zaki girbi abun da kikayi, sai na tabbatar da kin wahala.”
Ta gagara kawar da shakku dake yawo a kanta, that tayi babban kuskure, ta saka hannu akan shekaru biyu na rayuwarta, wanda bata da masaniya akan abun da ta saka hannu a kanshi, bata da masaniua akan abun da ta saka kanta a ciki.
Taji kamar yana magana, tace, “Na’am.” Yace, “No, ba dake nike ba.”
Tunda ta shigo ya lura da yunwa dake addabarta, bazai sakata aiki cikinta babu komai, zai bari ne taci ta koshi yadda zata tantance wahala, ya fi buk’atar taci ta koshi ta yadda zai gana mata azabar aiki hankali kwance, she have to be on full stomach that he will get the hell out of her, taga hell ganin idanunta, ya dauki alwashi akan daukar fansa, sai ya tabbatar da tayi nadamar abun da tayi mashi shekaru shidda da suka wuce, he will make her remember every bit of it, sai ya tabbatar da ta tuna cewa shine Abbakhar wanda ta yaudara.
K’ara cikinta yayi wanda ta tabbatar da ya ji, ta d’ago suka had’a idanu, wannan tonon asiri da mi yayi kama, mi yasa cikinta zaiyi k’arar yunwa that now she can’t denied it, (ni kuwa nace yaga alamar idan aka tambaya zaki mashi k’arya ne, ki cuceshi shiyasa ya tona tun kafin a tambaya that you can’t denied it), kunya taji kamar ta nutse a kasa, yace, “Ohhh abinci.”
Tana ji yayi kira yayi order na abinci, babu jimawa aka jera abinci kala-kala akan table dake a daya daga cikin kusurwowin katon ofishin, yana lura da yadda take kankame hannuwa alamar AC dake a ofishin yayi mata yawa, yayi kamar bai lura ba ya mike walking toward the table ya bude kalolin abinci da aka ajiye ya juyo gareta saying,
“Come and eat kafin ki fara aikinki, Miss Ahmad.”
Ta girgiza kai, “A’a na koshi.” Duk da kuwa yunwa ce sosai take addabarta, wanda yayi daidai da k’arar da cikinta ya k’ara yi a k’aro na biyu wanda ta tabbatar da yaji, kunya ya saka ta kasa d’agowa, shiru taji tana d’agowa taga yana aiki ne akan system dake a gabansa.
Jin yunwa zata illata ta mike heading there, rice, yam, stew wadda taji naman kaji, chicken, pepper chicken, bottle with mineral, anything is to her like he know her favourite, komai dake a wajen yadda take sonshi yake tamkar wanda yasanta ne ya girka mata, rabonta da taci normal abinci har ta manta, jiya wuni sukayi da yunwa saida daddare suka jik’a gari suka kwad’a suka ci, wanda lidde daya kowannensu ya samu.
By the site of the food da aroma dake tashi, yawu ya tarar mata a baki kasancewar an d’ad’e ba’a hadu ba, shekara da shekaru, ta hadiye yawu mukut wanda ya bada sautin da tana da tabbacin cewa yaji.
Ta d’ago suka had’a idanu, ya d’age mata gira tareda mata pointing abincin da idanunsa yana wani shegen murmushi.
“Abinci, Miss Ahmad,” He said.
“Jidderh,” She said.
Murmushi yayi, “Well Jidderh Ahmad, I will be calling you Miss Ahmad.”
Ta gyad’a kai tareda maida dubanta akan abinci ta hadiye yawu wanda ya k’ara bada sauti, ji tayi ta muzanta, tayi kasa da kai ta dauki spoon ta soma ci tana kad’a kai saboda dadi da yayi mata, an d’ad’e ba’a hadu ba saida ta cinye komai sannan ta ankara da ta’asar da tayi, ta ankara da abun kunya da tayi, da wasu idanu zata kalleshi bayan ta tada uban abinci a zama daya.
Da mamaki yake kallonta ganin ta gama da abincin, yace,
“Har kin gama.”
Ta kasa d’agowa ballantana ta bashi amsa har saida ya maimaita.
“Yes sir, thank you sir,” she said ba tareda ta yarda sun had’a idanu ba.
Cikin ransa yace, “That small person eat wannan abincin duka, wonder shall never end, koda yake talauci ne da take gudu.” Amma a zahiri yace, “Tunda kin ci kin koshi sai ko fara aiki.” Ya janyo tulun takardu wadanda shi kanshi bai san adadinsu ba yace, “Here, kiyi stamp akan kowanne sannan kiyi photocopy guda biyar kiyi arranging.” Ta kalli tulun takardun, ta ina zata fara photocopy, stamp da arranging na wadannan tulun takardun, yaushe ta fara yaushe ta gama, ba wannan ba, it that even possible, tace, “Bağışlamak?”.
Bai ji abun da ta ce ba, ya ce, “Kika ce?” Ta amshi tulun takardun tace, “Okay, Sure Sir.”
“Sir Sadeeq that’s how you will be addressing me,” He said.
“Sir Sadeeq,” She said.
Cikin ransa yace, “Hausa suka ce Mugun Abu Jakada, naki yanzu zai dawo ya sanar dake yadda yayi aiki a kaina, sai na tabbatar da kin wahala makurar wahala, sai na nuna maki hell ganin idanuwanki, sai kin wahala that zaki roki gafara, that zaki zab’i barin aikin wanda bazai yiyu ba domin kin saka hannu akan abun da ba zaki iya biya ba. I will get the hell out of you, I will work you black and blue har sai kin tuna abun da kikayi min, I will overwork you that you will be begging for mercy, that you will consider leaving but you can’t because you sign and you can’t abroad paying back double of the money… Jidderh welcome to hell… Kudi ne matsalarki zan zame maki yanke talauci but sai kin gwammace talauci da abun da zaki tarar.”
Wannan shine free page na karshe da zanyi maku, kuyi payment domin cigaba da samunsa kadda ku bari a baku labari
Koda daga jin yadda labarin yake tafiya kun san yaci sunansa MUGUN ABU JAKADA… HER RUDE BOSS… Shin ya zata kaya da Jidderh da Sir Sadeeq, her boss who’s her ex that she betrayed, kun dai ji kudirin da ya dauka a kanta wanda alamu sun nuna bata da hanyar gudu, tunda ta saka hannu a takarda and she can’t abroad paying back.