Mugun Nufi Hausa Novel Complete

Mugun Nufi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MUGUN NUFI*

_(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

 

PAID BOOK

 

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ’ى*  *ASS

_{Onward Together}_

Mugun Nufi

_STORY AND WRITTEN_

_BY_
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )

 

FREE PAGE

 

P1

 

Yanayin fuskokin mutanen da ke cikin falon kawai za ka kalla ka tabbatar da zaman da su ke yi ba na daɗi bane, a hankali shassheƙar kukan matashiyar budurwar da ta kasance ita kaɗai ce mace a cikin su ke tashi, kaf ilahirin jikinta rawa ya ke, kamar me jin tsoron wani abu kar ya kamata haka ta ƙanƙame kujerar da ke kusa da ita.

 

Cikin fusata ɗaya daga cikinsu me suna Baba Musa ya ce, “Ke ki buɗe baki ki yi mana magana mun gaji da salon munafurcin da ki ke yi, a komai sai kin nuna cewar kin sha baƙin nono, wannan shine karo na farko da za ki maishemu ƙananan mutane, tunda har waje ta ƙi ki ai dole ne gida ya karɓe ki, hakanan za mu haɗaki da ɗan uwanki shi sai ya rufa mi ki asiri.”

Ya ƙarasa maganar yana huci.

 

Ɗaya bayan ɗaya na sake kallon fuskokin mutanen da ke wurin, maza ne guda biyar uku daga cikin su magidanta ne, se biyu su ne basu wani zama magidanta ba.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Baba Musa yana gama magana, ƙaninsa ya ɗauka wato Baba Isah, cikin izgili ya ce, “Kana ta maganar gida gida to wa ka ke tunanin ze amsheta ni dai gaskiya ba zan iya aurawa ɗana ba, yana da wacce ya ke so ta ke sonsa.”

 

Murmushin jin daɗi Baba Musa yayi tare da faɗin, “A’a Isah ai hannu baya rubewa a yanke a yar, haka dai ni zan yi wannan sadaukarwar na aurawa Bashir ita.”

 

Cike da jin haushi karamin cikin su ya ce, “Wai me ku ke yi haka saboda Allah Yaya, Meemerh fa ƴarmu ce, ƴar ɗan uwanmu ce, ko da ace duniya kowa zai ƙita ya aibata ta mu ba za mu yi haka ba, kowa ya shaida ya kuma tabbatar ita ɗin jinin DURUMBU ce, kuma babu wanda ya isa ya musa haka. Shin dama auren bare yana zama illah ne, menene laifinta a gare ku? ku sani aure lokaci ne, kuma insha Allah za ku yi mamakin Mijin Meemerh, sai kun yi mamaki.”

Mugun Nufi Hausa Novel Complete

Tsit ka ke ji babu wanda ya sake magana da alama sun ji nauyin maganar kanin nasu garesu, ganin haka ya saka shi kallon inda Meemerh take ya ce, “Kinga Mamana tashi ki tafi, ki kwantar da hankalinki, za mu san abun yi kin ji.”

 

Sai yanzu ne ta samu ƙarfin gwaiwar kallon inda mahaifinta ya ke, dan ta tabbatar cewa zai fita shiga cikin damuwa, ilae kuwa dan tana kallonshi ta ga idon nan nashi ya kaɗa ya yi ja tsabar ɓacin ran abinda ƴan’uwansa su ke yiwa gudan jininsa kuma a gaban idon sa, suna haɗa ido wani kukan ya sake kubce mata da ƙarfi, tashi ta yi da gudu ta fita daga falon.

 

Kai tsaye ɗakinta ta shige ta faɗa kan gado ta sake fashewa da wani kukan me cin rai, bata san tsawon lokacin da ta shafe tana wannan kukan ba, sai da ta ji an fara shafa bayanta alamar rarrashi, hakan ne ya bata tabbacin cewar lallai ɗaya daga cikin mutanen da su ke jiɓantan lamarinta ne wani ya zo, wato Babanta ko kuma Aminiyarta Suhaima, duk da zuciyarta na faɗa mata cewar Suhaima ce, dan ta san shi kansa Baban na ta yana can cikin damuwa.

 

Fara sassauta kukanta ta yi sai ajiyar zuciya ta ke saukewa, tayar da ita Suhaima ta yi ta zaunar ba tare da ta ce mata komai ba ta fita, ita ma bata yi magana ba sai dai binta da ido da ta yi tare da ci gaba da sauke ajiyar zuciya, tana nan zaune sai ga Suhaima ta shigo hannunta riƙe da ruwan gora da kuma cup, buɗe murfin gorar ta yi ta tsiyaya mata ruwan ta miƙa mata, bata Musa ba ta karɓa ta sha, sake zuba mata wasu tayi ta kauda kai alamun sun isheta, marairaice fuska Suhaima ta yi alamar magiya, amsa ta yi ta sha kaɗan ta ajiye kofin tare da jan dogon numfashi, tana hurzar da iska.

 

Ita dai Suhaima da ido ta ke ta binta, bata ce komai ba, tana kallon bakinta da ke motsi tasan tana so ta sanar da ita damuwarta ne, amma zuciya ta hana. Sai da suka ɗauki kusan minti goma a haka, kafin Suhaima ta ce, “Wai se yaushe ne Meemerh zata zama jaruma ne, ta dena kuka akan ƙaramin abu, ta dena kuka domin ta baiwa magauta mamaki, a kullum fa so su ke su ga wannan tsadaddun hawayen na kwarara a kyakkyawar fuskarta, ko da yake na san hakan ma ba zai yiwu ba, domin Meemerh raguwa ce Abie ya rigada ya shagawaɓata da yawa, kinga zo ki faɗa min yanzu kuma me ya faru wa ya taɓa ƴar gaban goshin Abie?

 

See also  Yar Gan Gan Hausa Novel Complete

Cikin muryarta da ta fara dishewa saboda kukan da tayi tace ” Suhaima se yaushe ne ƙaddarar matar da ban ma santa ba zai dena bibiyata? Sai yaushe ne za’a dena jin warin kashin da ta shafa min, me yasa Abie be zaɓamin uwa ta gari kamar kowa ba? Na tsaneta bana son ta bana fatan Allah ya haɗani da ita ina rokon Allah yadda ta hana zuciata salama itama kar ta samu kwanciyar hankali a duk inda take, ina rokon Allah ya sadata da…… ”

 

Toshe mata baki Suhaima ta yi da sauri tana girgiza mata kai cike da ɓacin rai ta ce, “Bansan se yaushe ne Meemerh zata fara amfani da ilimin ta ba, ban san se yaushe ne zata yarda da ƙaddara wacce yarda da ita wajibi ne ga dukkan Musulmin kirki, Meemerh duk lefin uwa, ba zai canja matsayinta a wurin ƴaƴanta ba, wahalar ɗaukar cikin ki na tsawon wata tara kawai da tayi ya isa yasa ki girmamata, bare kuma wahalar naƙuda, Meemerh akwai abinda yake a ɓoye wanda mu bamu sani ba ke dai mu ci gaba da addu’a, Allah yana ji kuma yana gani”

 

Ture mata hannu Meemerh ta yi da karfi, tana so ta yi magana amma numfashinta ya fara barazanar barin jikinta idonta ya fara sauyawa.

 

“Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un! Meemerh kin ga abinda nake gudu ko, ina kika ajiye inhaler ɗinki? Ina Meemerh bata ma san abun da Suhaima ke yi ba, se kiciniyar jan numfashi ta ke yi, da sauri Suhaima ta fara duba side drowers, cikin sa’a kuwa ta ga inhaler ɗin, saurin shaƙa mata ta yi tare da cire mata rigar da ke jikinta, ganin ta fara dawowa hayyacinta ne ya saka ta tashi da sauri ta nemo mafici ta fara yi mata fifita, sai da suka shafe tsawon lokaci kafin ta samu Bacci ya ɗauketa.

Ajiyar zuciya Suhaima ta sauke ta rafka uban tagumi, tausayin ƙawarta ne ke ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciyarta, duk da bata san dalilin shigarta cikin wannan damuwar ba amma ta san dai ba zai wuce dangin Mahaifinta ba da suka ƙi yarda da cewar ƴar su ce har tsawon wannan lokacin, saboda wani banzan dalilinsu da kuma anƙi a sanar dasu ko menene.

 

sai da ta tabbatar da baccin ya yi nisa tukunna ta fita, a falo ta samu wata dattijuwar mata, ta rafka uban tagumi, ƙarasawa ta yi wurinta ta zauna, cikin damuwa tace ” Bahba dan Allah me kika sani dangane da mahaifiyar Meemerh?”

 

Da sauri dattijuwar nan ta dubeta, cikin raunin murya ta ce, “Ban san komai ba Suhaima se bayan fitar ta gidan nan ni kuma na shigo, kamar yadda na sha faɗa miki ni kula da Hajiya ƙarama ne kawai dalilin zuwana gidan nan. Yanzu ya take, ina fatan dai ciwon ta be tashi ba ko?”

 

Cikin ƙunar rai Suhaima ta ce, “Bahba to burinsu kenan ai, sun fi muradin ganinta tsakanin rayuwa ko mutuwa, ban san dalilin shigar ta cikin wannan halin ba.”

 

“Suhaima shinma Mujahid ya janye daga maganar auren ta, iyayen sa basu amince ya aure ta ba?

 

“Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un! Bahba shi kuma wane dalilin ya kawo?”

 

“Ban saniba Suhaima, nima a wurin Hajiya A’isha na tsinci zancen, kinsan bata rabuwa da tsegumi.”

 

“Anya Bahba ba wani ke yi wa rayuwar Meemerh bita da ƙulli ba kuwa, anya wannan matslaar ba daga gida ba ne? Meemerh tana da nagartar da kowa ze so ta, tana da ilimi uwa uba natsuwa, zamanin yanzu ma kusan kaso tamanin 80 na maza auren kyau suke yi ba wani nagarta ba, to Meemerh kyakkyawa ce, meyasa maza ke wasa da hankalin ta me yasa suke shinfida mata inuwa se ta doso kuma su sake mata rana? Ya Ubangiji ka fimu sanin dalilin faruwar hakan, ka kawo farin ciki a rayuwar wannan baiwar ta ka, masu nufarta da sharri ka maida musu kan su.”

Ta ƙarasa addu’ar hawaye na saukowa kan fuskarta.

 

“Ameen Ameen Suhaima, ke dai ku ci gaba da addu’a, nasan Indai za’a juri zuwa rafi to watarana dole tulu zai fashe, Kuma masu iya magana ai sun ce MUGUN NUFI baya kashe ɗan barewa, wannan makircin tun akan mahaifiyarta ya fara, tunda har kika ga Meemerh ta kai yanzu to tabbas rayuwarta zatayi ƙarko.”

 

Wani irin kallo tukuna Suhaima ta fara jifan Bahba da shi. “Bahba kika ce sai bayan mahaifiyar Meemerh ta fita daga gidan nan sannan aka ɗauko ki, shin me ki ke ɓoye mana dan Allah?”

 

Da sauri ta mike tsaye, “Kinga Suhaima ni babu abinda nake ɓoye miki, Kinga bara na koma kar Hajiya ta nemeni.”

 

Ganin haka yasa Suhaima ta fahimci cewar tabbas Bahba ta san wani abu dangane da barin Mahaifiyar Meemerh gidan sai dai ba zata faɗa bane, bata san dalilin da yasa kuma take ɓoye mata ba.

 

 

 

_To fa

Bazamfariarku ta dawo, da wani salon ta zo muku, but ƙwarin gwaiwarku ne ze kaimu inda muke so muje domin jin surƙullen ƙulallen ƙullin wannan labarin.

 

_Kafin nan kun sani labarin na kuɗi ne farashi ne me_ sauki _babu yawa, ku biya kuɗi ku sha romon_ _labarin_

_300 ne kacal_

 

RealBazamfaria

*MUGUN NUFI*

_(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

 

PAID BOOK

 

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ’ى*  *ASSɷ* 📚✍*

_{Onward Together}_

 

_STORY AND WRITTEN_

_BY_

////////////////////////////////////////////////////

*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )

//////////////////////////////////////////////////

 

FREE PAGE

 

🅿️2️⃣

 

 

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*

*Fiddausi sani*

*Stanbic bank*

*And send ur evidence* *Via my* *Watsap number 08039228702*

*Is 300 only*

 

 

Haka Suhaima ta kasance zaune ita kaɗai a falon, sai da lokacin sallah ya yi tukunna ta koma bedroom ɗin, ganin numfashin Meemerh ya koma normal sai ta gyara mata kwanciya ita kuma ta shiga toilet dan ta yi alwala.

 

Tana cikin sallah ne ta ji motsin Meemerh alamar ta tashi kenan, toilet ɗin ta shiga ta yi wanka kafin ta yi alwala ta fito ita ma. Lokacin Suhaima har ta idar da Sallah tana bakin gado zaune tana danna wayarta da alama chat ta ke yi, haɗa ido suka yi se suka sakarwa juna murmushi “Ya jikin naki?”

See also  Muradin Rai Littafin Hausa Novel

Suhaima ta tambaya tana ajiye wayarta kan bed side drower, kai Meemerh ta ɗaga mata alamun da sauƙi, bata damu ba, saboda ta saba dama can Meemerh ba me yawan surutu bace, idan ka ga ta yi doguwar magana to da Abie ne ko kuma ita Suhaiman. Ta shi ta yi ta shimfiɗa mata pray mat, tana kallon ta sai da ta gama shirinta tsaf kamar babu abinda ya faru kafin ta kabbarta sallah.

 

Tana cikin sallah ne Abie ya shigo ɗakin.

 

Ajiyar zuciya ya sauke ganinta cikin ƙoshin lafiya, maida hankali sa ya yi wurin Suhaima da ke masa sannu da shigowa, cikin sakin fuska ya ce “Sannu da ƙoƙari Suhaima na ji daɗin ganin Meemerh cikin natsuwarta, ban yi tunanin zan sameta a haka ba.”

 

Dariya ta yi, ta ce, “Abie yanzu fa ƴar budurwarka ta fara zama jaruma, ai ta girma.” Meemerh da idar da Sallahn ta kenan ta juyo tana watsa mata hararar wasa.”

 

“Dama jaruma ce ni Malama ko Abie?”

 

“Ƙwarai kuwa.” Ya faɗa cikin farin ciki, “Ina fatan dai babu abinda ya ke damun ki a yanzu?”

 

“Babu komai Abie ina lafiya, na ji daɗin ganin ka haka kaima, ka yi haƙuri Abie ina jin tsanar kaina, kasantuwa ta ƴa ɗaya tilo da Ubangiji ya baka, kuma na kasa sama maka farin ciki, a kaina kullum ake faɗa maka baƙaƙen magana, na yi maka alƙawari insha Allah wannan shi ne karo na ƙarshe da hakan zai sake faruwa, ba zan sake kula ko wanne namiji ba bare har daga ƙarshe akai sukana akan abinda wata bare ta aikata tun ban san menene duniya ba. Abie ka yi min komai na rayuwa, abu ɗaya da ka kasa yi wa rayuwa shi ne auren macen da bata da ce ba me yasa na fito ta tsatson ta, kullum se na yi wa kaina wannan tambayar, bana sonta kamar yadda na san cewar ita ma bata sona, na tsaneta, ko a lahira ina rokon Allah kar ya nunamin azzalumar fuskar ta!”

 

Share hawayen da suka zubo masa ya yi, ya tsuguna tare da kama hannun Meemerh. “Mahaifiyarki bata cancanci wannan kalaman naki ba Meemerh, tana sonki, ni na san cewar tana sonki kuma har abada ba za ta dena son ki ba, daga yanzu idan ba Alkhairi za ki faɗa akan matata ba kar ki sake aibata ta a gabana, kina da damar faɗar abunda ki ka faɗa saboda hakan aka dasa a zuciyarki, sai dai yau ina so na faɗa miki cewar idan cuta ne ni ne na cuceta ba ita ta cuceni ba kamar yadda su ke faɗa, mu ci gaba da addu’a insha Allah wata rana komai ze zama labari”

 

“Abie kullum fa haka ka ke faɗar komai ze zama labari shin se yaushe ne zan bayar da wannan labarin, se yaushe ne ƙaddarar matarka zai dena bibiyana, wani lokacin laifin ka nake gani, ina ganin kamar da gangan ne ka ƙi zaɓa min uwar da ta dace, duk da ina kwaɓar zuciyata duba da halaccin ka a gareni, ka maye min gurbin uwa da uba ina ma a ce kai ne uwata kuma kai ne uban, kana da nagartar da babu wanda ya isa ya aibata ka, da yanzu ina cikin farin ciki babu wani tabo a rayuwata, amma babu komai akwai Allah shi zai saka min.” Kife kanta ta yi a jikin Abie tana sakin wani marayan kuka wanda ke bayyana ainahin ciwon da ke damun zuciyarta, Abie be sake magana ba se shafar bayanta da ya ke yi alamar rarrashi, ita kanta Suhaima kukan ta ke yi.

Ta rasa wane irin sirri ne wannan wanda ba za’a faɗa ba, duk da a zuciyarta tana zargin koma menene silar barin Mahaifiyar Meemerh a gidan Abie to ba zai wuce kitimurmurar ƴan’uwansa da matan sa ba ne.

 

Tsawon lokaci suka share a haka, kamar ma sun manta da junan su. Sallallamin da suka ji ana yi ne tare da tafa hannu ya sa dukan su dawo wa hayyacin su, da ido kawai su ke raka jarababbiyar tsohuwar “Yanzu kai saboda Allah Amadu abinda ka ke yi kana ganin shine dai-dai? yarinya tana abun da ta ga dama, ta mayar da kai ƙaramin mutum jama’ar gari se zunɗe suke yi, a maimakon na sameta ka yi mata dukan mutuwa amma shine ka sakata a gaba kana shafa? Gandamemiyar yarinya ga ƙanwarta can ƴar gidan Isah har ta haihu amma ita shekara Ashirin da huɗu tana nan tana gantalewa ko waye ya zo da ya ji tushen ta se ya gudu, shiyasa tun farko na so ka bar su su tafi da ƴarsu amma ka kafe akan cewa kai ka yi cikin ta wannan sam na kasa yarda ba jinina bace ita, domin duka jikokina farin jini ne da su, ko da yake uwarta ma a danginsu babu wanda ya kwasa se ni da ƙaddara ta cim ma nawa ɗan shine ya kwaso mana jan gwamgwama, ka ci amana ta Amadu” Se kuma ta fashe da kuka, har tana fyatar da majina.

 

 

Wani irin ciccira jikin Meemerh ya fara se mika ta ke yi tana kakari kamar numfashin ta ze fita, idon ta duk y ƙaƙƙafe, gata a jikin abie ya ma kasa motsawa, cike da tsana Suhaima ta ce, “Haka ki ke son gani ko Dada hankalin ki ya kwanta za ki kashe baiwar Allah da bata ji ba bata gani ba, wallahi ki bar ganin ke kakarta ce matuƙar wani abu ya sameta kotu zan kai ki.” Yanayin maganar Suhaima kawai zai tabbatar maka da ita ma ba’a hayyacin ta ta ke ba.

 

“Ke kar ki sake ki yi min ɗibar albarka, ni da jika ta har ke da ki ke bare ne za ki gaya min maganar banza, kai kuma Amadu kana jin ta amma ba ka wanke min fuskar shegiya da mari ba.”

 

Fita Suhaima ta yi da gudu ganin Abie ko motsawa be yi ba.

 

Bayan kamar minti biyar sai gata sun shigo da gudu ita da Bahba, haka suka cicciɓi Meemerh daga jikin Abie suka fita da ita, shi dai ya dafe kai kawai amma ko motsi be yi ba.

See also  Kawar 'Ya ta ce complete

 

A babban falo suka haɗu da Hajiya A’isha (Matar Abie ta biyu) ta na ganin su ta fashe da dariya, a haka za’a ƙare ai, ba’a mutu ba kuma ba’a yi rai ba, a hana mutanen gida kwanciyar hankali, ko da yake da alama shima wanda ke taɓukawar ya fara sanin ciwon kan sa shiyasa be fito ba” cicciran da Meemerh ke yi ne ya hana ko wanne daga cikin su bi ta kanta, haka suka fice ba tare da sun tanka mata ba, ko da yake ita Bahba dama bata da wannan damar sai dai Suhaima, ta zame musu kashin wuya sam sun kasa hanata zuwa gidan kuma idan ta zo bata ɗaukar iskancin su, idan suka ce kule, sai ta ce cass, sam ba ta da tsoro.

 

A ƙofar falon Suhaima ta tsaya rungume da Meemerh ita kuma Bahba ta tafi neman driver, sai dai babu shi ba alamun shi kuma Me gadi ya tabbatar mata da be fita ba, ga kuma mota a ajiye saboda haka kawai tace wa Mai gadi ya buɗe musu ƙaramar ƙofa su fita.

 

“Suhaima mu kamata kawai mu fita ko Allah ze sa mu samu Napep dan na duba driver ba ya nan.” Suhaima bata ce komai ba ta tashi suka kamata suka fita. Sun daɗe a bakin titin kafin Allah ya kawo musu me Napep kasancewar irin unguwar nan ce da ba’a cika samun abun hawa ba tun mafi yawan masu zama a cikin ta sun mallaki abun hawan su, sunan asibitin da zai kaisu Suhaima faɗa masa, suka shiga. Suna cikin Napep ɗin ne Suhaima ta tuna cewar basu fito da kuɗi ba, ga wayarta na can bata ɗauko ba, dan haka ta roƙi me Napep ɗin ya bata aron waya, babu musu kuwa ya bata, numbern Mamanta ta kira bugu biyu kuwa ta ɗaga, anan ta sheda mata cewar Meemerh ce babu lafiya suna hanyar asibiti kuma babu kuɗi a hannunta nan take Mahaifiyar ta ta ce ga ƙanwarta nan zuwa a asibitin se ta kawo musu kuɗin.

 

Kusan a tare motar gidan su da Napep ɗin suka shiga asibitin, da sauri ta fita ta taro ƙanwarta.

 

“Aunty me ya sameta ne haka?. Ƙanwarta me suna Aminatu ta tambaya.

 

“Kinga Meena je ki biya me Napep kuɗin sa mu zamu shiga da ita ciki sai ki biyo mu.” haka suka kamata suka shiga da ita cikin asibitin, da sauri Nurses ɗin suka amsheta,

nan take likitan na zuwa ya rubuta Omalizumab injection, ya miƙawa Suhaima tare da faɗin “Hurry get this injection.”

Da sauri ta fita a waje ta haɗu da Aminatu karɓar jakan da ke hannun ta ta yi ta tafi pharmacy bata wani ɓata lokaci ba ta siyo allurar ta dawo.

 

Nan ta ke ya yi mata allurar cikin ikon Allah kuwa within 5 minutes sai gata ta koma breath a hankali, numfashin yana daidaita cikin abun da be wuce daƙiƙa 20 ba bacci ya yi nasarar ɗauke ta.

 

Sai a lokacin hankalin su Suhaima ya kwanta, mayar da hankali ta ta yi wurin Aminatu da ke tambayar ta “Me ya tayar da ciwon kuma Aunty?

Mere baki ta yi ta ce, “Abun da ya saba tayar da shi Meena, Meemerh na cikin jarabawa sai dai kawai mu tayata da addu’a, amma rayuwar ta juye take a cikin murɗaɗden sirri wanda babu wanda ze fasa mata wannan sirrin sai dai Allah, shi ne ya san gaskiyar abinda su ke ɓoye wa.

 

Haka dai su ka yi ta jimamin abun har tsawon lokaci kowa zuciayar shi babu daɗi, ganin har an fara kiran sallar La’asar kuma bata falka ba, sai Suhaima ta ciro 500 ta ce, “Bahba ina ga kawai ki karɓi kuɗin nan se ki koma gida, mu daga nan gidan mu za mu wuce da Meemerh har ta gama jin sauƙi, kin san mutanen gidanku ba wani kitsen ido ne da su ba, ba za su damu da cewar bata da lafiya ba tsaf zasu sake maimaita iskancin su, ciwon ya sake tashi.”

Cike da tausayawa Bahba ta karɓi kuɗin, addu’ar samun lafiya ta yi wa Meemerh, ta tafi.

 

Meemerh bata falka ba se around 5 of clock, ta tashi lafiya lau sai kanta da ya ke ɗan sara mata a hankali, Suhaima ta taimaka mata ta zauna tare da jingina jikinta a bango.

 

“Sannu Meemerh.”

 

Da kai ta iya amsata.

 

“Sannu Aunty Meemerh ya jikin?.

 

Buɗe lumsassun idanun ta ta yi jin muryar Meena, murmushi ta sakar mata a saman laɓɓanta ta furta “Ke kuma yaushe kika zo nan?”

 

Itama murmushin ta yi, ta ce,

“Tare da ku na zo ai.”

 

Ba ta sake magana ba sai kanta da ta jinjina mata, taɓe baki Meena ta yi dan ta san halin Meemerh ko da lafiyar ma wani lokaci haka take da shariya bare yanzu ana halin ciwo. Fita Suhaima ta yi ta kira Doctor, sai da ya yi mata ƴan tambayoyi, ta bashi amsa prescription ya yi mata na tablet, kafin ya ce Suhaima ta tafi ta biya kuɗi za su iya tafiya gida.

 

Suna nan zaune Suhaima ta tafi ta siyo har maganin kafin ta dawo, suka taimaka mata ita da Meena suka fito a tare, suna tafe suna hira ita da Meena dan Meemerh bata cewa komai zuciyarta babu daɗi, a daidai coridon da zai fito da su asibitin ne Meemerh ta dafe ƙirjinta tana furta

” Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un!”

Duk firgicewa suka yi suna tambayarta lafiya tare da waige don ganin abun da ya bata tsoro, babu kowa sai wani mutum da suka gani duƙe hannun sa riƙe da wata mata itama kamar ta yi tuntuɓe ne, dan a duƙe take kamar yadda Meemerh ta zube a ƙasa.

 

Jin bugun zuciyarta na ƙara gudu ne ya saka ta harhaɗa kalmomin fadin,

“Suhaima mu bar wurin nan dan Allah, kamar wani abun na kusanto ni.”

 

Da sauri kuwa suka tayar da ita, dama drivern da ya kawo Meena yana jiransu da sauri suka buɗe motar suka shiga.

 

 

_Wai me ku ke tunanin ya haddasa wannan faɗuwar gaban?_

 

_Hehehehe na saba zuwa muku da ƙullallen sirri amma wannan ya zarta na kullum ku dai ku biya ku sha labari_

 

 

 

#Real@Bazamfaria

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top