Muradin Rai Littafin Hausa Novel
Muradin Rai Littafin Hausa Novel
Page: 1
____A Shekarar 2019 wanda yay daidai da 28/12/ na wannan shekarar, Gudu yake rungume da qaramin yaro wanda baze wuce shekaru bakwai zuwa takwas ba, gudu yake bilhaqqi da gaskiya wanda daga kallon farko zaka fahimci cewar gudun ceton ransa dana ɗan dake hannunsa yakeyi, ko ina ya samu jefa qafarsa kawai yakeyi a cikin qungurmin dajin wanda ke cikeda tarin bishiyu, bakajin sautin komai iface na nishin sa gamida qarar busassun ganyayyakin dayake takawa sabida yanayin bazarar da ake ciki a wannan lokacin
Can daga bayansa haniniyar dowakai ce ke tashi gamida ihun mahaya kan dokin wanda suka nufoshi a sukwane kuma sukeda muradin kama wannan matashi wanda baze wuce shekaru 35 ba.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels PdfÂ
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
Ganin da sukai wankin hula na shirin kaisu ga dare ne yasa É—aya daga cikin mahaya kan dokin ya zaro Bindigar dake saqale a bayan wandonsa ya saita wannan matashin dake gudun tsira da rayuwarsa cikin baqin zafin nama ya sakar masa harbi a gefan hannunsa na dama, take matashin ya kurma wani uban ihu wanda yasa sumammen yaron dake hannunsa ya farka tareda kafe matashin dake riqe dashi da manyan fararen idanunsa waÉ—anda suke farare dasu tas tamkar bana namiji ba.
Azabar harbince tasa matashin ya fara qoqarin sakin yaron amma kuma se yaron ya qanqame wuyan rigarsa qyam tareda runtse idanunsa a lokacin daya saddaqar da cewar tabbas rabuwarsu tazo koda kuwa basu shiryawa hakan ba.
Burki yaja a lokacin da suka iso gabar wani babban dutse wanda ke fitar da ruwa daga tsakiyarsa, daqyar yake iya É—aga qafafunsa wanda ke cikin wata farar safa wadda sabida wahala ta koma nau’in wata kalar daban, gabaÉ—aya qarfinsa ya gama qarewa amma sabida baqin naci gamida wutar Muradin dake cin zuciyarsa yasa har wannan lokacin be yanke qauna ba akan cewar zasu iya cigaba da rayuwa ba.
A haka ya samu wani guri daga jikin dutsen ya kwantar da yaron tareda bubbuga kumatunsa Alamar ya buÉ—e idanunsa, a hankali yaron ke buÉ—e idanunsa harya gama buÉ—esu tas akan hannun matashin wanda keta zubarda jini tamkar an buÉ—e bakin fanfo, lokaci guda kuma ya zabura ya qanqame matashin tareda fashewa da wani irin kuka yace “Banaso wani Abu ya sameka Dady idan har wani abu ya faruda kai a sanadina har abada zanyi dana sani!!!
Zareshi daga cikinsa yayi lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka keto masa sannan ya dubi É—an nasa cikeda soyayya irinta É—a da kuma mahaifi yace ” lokaci yayi HATEEM dole ne mu rabu a wannan ranar muddin kanaso ka sake ganina da raina a tareda gangar jikina, don haka ka saurareni dakyau Hateem nasan shekarunka sunyi qaranci su fahimci abinda nakeson sanar dakai, duk rintsi duk wuya kada kayi wasa da shan maganin ka!!!!   Matashin ya faÉ—a a lokacin da yake miqa masa wata qaramar jaka dake rataye a bayansa.
hawayene suka sake zubowa Hateem a karona biyu sannan ya buÉ—e baki dayar yace ” idan ka tafi kabarni a nan Dady waze dinga kula dani idan ciwona ya tashi?
Haniniyar dawakai sukaji a dabda su alamar mahaya kan dawakan na dabda riskar inda suke lokaci guda kuma suka juya a tare suna masu kafe Æ™ofar kogon dutsen da idnu cikeda tsoro………….. Cikin sauri matashin ya janye yaron daga gabansa zuwa bayansa lokaci guda kuma ya fuskanci yaron yace “ka saurareni da kyau Hateem a kwai wata qaramar waya a cikin jakar nan lallai karkayi wasa da ita idan har Allah ya nufa na tsira da rayuwata to da ita zanyi amfani wajen gano inda kake…
kuka sosai Hateem yakeyi tareda qara qanqame rigar mahaifin nasa dake hannunsa yace “kayi min alqwari cewar zaka dawo gareni a raye ba tareda wani abu mara kyau ya faru dakai ba!!!
Idanunsa a kafe bisa fuskar kakkyawan yaron yace “I promise you zan dawo gareka no matter what if am survive insha Allah!
Daga haka be sake kallin yaron ba ya miqe da hanzari yabar gurin yana me qara hanzarinsa akan na farko, a haka yayta ratsawa ta cikin lingu da saqon duhuwar djin yana gudu jirin jini na ɗibarsa, a haka ya yanke jiki ya faɗi a dedai gaɓar wani babban ruwa me tafiya cikin qanqanin lokaci igiyar ruwan ta samu nasarar jansa tai gaba dashi wanda hakan yay dedai da rufewar idanunsa.
Wannan kenan
__________________
KADUNA STATE (unguwar Malali Gambia Road)
babban gida ne na Alfarma wanda aka qawatashi da tsarin gini na farin dutse, gida ne wanda ya amsa sunansa gida irin na manyan masu hannu da shuni wanda hannunsu ke cutar gadon bayansu, komai na cikin gidan qirace ta musamman wanda akayo odar sa daga qasashen qetare wanda ya kasance mallakar babban É—an kasuwar nan wanda duniya keji dashi a fanin kasuwanci, a zahiri cikakken É—an kasuwa yake inda a baÉ—ili kuma ya kasance cikakken tantirin É—an fasaqaurin safarar miyagun qwayoyin da suke É—auke da wani sinadari me É—auke da wata É“oyayyiyar cuta.
Alhaji Qasim Banazir kenan mamallakin Companyn sarrafa magungunan ciwon zuciya dana qoda, wanda ya kasance kaf qasar nan babu kamarsa a wannan fagen.
Duk irin tarin dukiyar da Alhaji Qasim Banazir kedashi Æ´a É—aya tilo Allah ya bashi wadda yake matiqarso kamar ransa, Suna kiranta Nooreyn.
Ko kaɗan bayason abinda ze taɓa masa lfyarta koda kuwa meyeshi, idan nooreyn bata da lfy kokuma tana cikin yanayi na rashin walwala ko ɓacin rai gabaki ɗaya yanayinsa shima sauyawa yakeyi, shiyasa yake matiqar kiyaye dukkan abinda ze taɓaasa ita.
a hankali take sakkowa daga sters cikin takunta na isa da qasaita, sanye take cikin wani pink ɗin wando wanda yay masifar matse ta kamar ze yage, inda rigar jikinta ta kasance very short ta tsaya mata dedai tsukakken cikkinta wanda hakan ya bawa fatar cikinta damar fitowa kaɗan, gashin kanta a baje yake bisa doron dogon wuyanta wanda ya sauka bisa cikakken qirjinta, fuskarta a zagaye take wadda ke ɗauke da dogon hancinta gamida manyan fararen idanunta, bakinta yanada ɗan tudu kaɗan wanda hakan ya qara baiyan zallar kyan da take dashi.
Tana gama sakkowa daga sters ɗin ta wani tsaya tanabin daining ɗin da aka cika da abinci iri-iri, tsaki taɗanja kaɗan sannan Ta nufi side ɗin dadyn ta wato Alhaji Qasim Banazir.
Tun kafin ta shiga wayarta dake hannunta ta É—auki ruri don haka ta wani yatsina fuska tareda jan siririn tsaki ta É—aga ba tareda tayi magana ba.
Katse wayar tayi sannan ta saki murmushin daya qara fallasa madarar kyan datake tashi ta juya da sauri zuwa side ɗinta, a gaggauce ta buɗe drower ɗinta wadda ta kasance zallar p-caps ɗinta ne a ciki ta ɗauki wata me launin kalar light pink tasaka akan bajajjen gashin kanta ba tareda ta ɗora wata riga akai ba ko mayafi ta nufi sheo Rak ɗin ta ta ɗakko wani haɗaɗɗen takaimi irin me kaiwa har wuyan qafa ta saka Wanda ya kasance same colour with p-cap Din dake kanta sanan ta fita da sauri har tana haɗa steps ɗin wajen sauka.
Koda wasa batabi takan mom É—inta dake part É—inta ba ta nufi jibgegiyar motar ta qirar ford ta buÉ—e ta shiga tareda murza mata key. Tana qoqarin barin gurin taji Ance “Nooreyn!!!!!!
Ɗagowa tayi da fararen idanunta tana kallon back sit ɗin motar ta cikin mirrorn dake manne a jikin glass ɗin motar ta gaba ba tareda taja motar ba,  Ajiyar zuciya ta sauke me qarfin gaske wadda ke baiyana irin yanayin tsoron datashiga.
Tsaki taÉ—anja kaÉ—an tareda watsa masa harara tace ” what are you doing in my car without my parmisson Saleym?
Matashin data kira da Saleym wanda ke kwance bisa back sit na motar yay murmushi yace ” I just want to see you Nooreyn thats why I’m here, I’m definitely sure zaki fito at this time shiyasa na shigo gidan ba tareda kowa ya sani ba.
har lokacin daya kai qarshe a maganarsa she’s still staring at him, rintse idanunta tayi daqarfi sannan ta sake buÉ—esu akan Saleym tana wani male baki kamar wadda ke shirin sakin kuka, siririn tsaki ta saki sannan ta murzawa motar key ta nufi get da gudun gaske kamar zata tashi sama.
Sabida sanin halinta da Masu tsaron gidan sukai ba shiri kowa ya tsaya a inda yake inda shi kuma get ɗin Aka wangale matashi ta fice. Tana fita titin daze kaita Governor Road ta jefar kan motar cikin mintuna kaɗan ta isa inda takeso taje shidai Saleym yana maqale a bayan motar yana faman dannar waya.
burki ta matsa me qarfin gaske wanda yasa wayar dake hannun Saleym ta suɓuce inda shi kuma kansa ya faɗo kn kafaɗunta. Dariya ta qyalqyale masa da ita har tana tafa hannu inda shi kuma Saleym ya kafe dogayen fararen haqoranta da kallo batareda qiftaa ba.
Kunnensa tasa hannu ta kama tareda murdawa da qarfi tace ” wannan shine hukuncinka na shigar min mota ba tareda izini na ba.
“Eyyah Nooreyn nimafa kina min hka jiyama fa haka kika min don na rama shine zakimin mugunta ko?  Zatayi magana kenan ya bige hannunta tareda É—aukar wayarsa ya É“alle murfin motar ya fito yana É—ariya.
itama fitowa tayi tana murmushi sannan tasaa motar lock tareda sunkuyawa tana gyara zaman igiyar takalminta
kafeta da ido Saleym yayi a ransa yana jinjina kyawu gamida tsarin kyan surar da Nooreyn take dashi, babu abinda yafi komai ɗaukar hankalinsa a tareda ita kamar hips ɗinta daya fito ya buɗe a jikin wandon dake jikinta, a hankali idanunsa suka sauka bisa wuyan cikinta wanda yake a kwance flat dashi ya wani irin tsuke tamkar babu wani abincinci dake samun gurbin zama a cikinkata sabida yanda yake a lafe, kasancewar rigar dake jikinta qaramace sosai ne ya bawa cibiyarta damar fitowa tunda dama rigar bata Arziqi bace.
Tana É—agowa ta wani baza gashin kanta wanda ya qara bajewa bisa doron wuyanta har zuwa kan cikakken qirjinta sannan ta sake gyara zaman p-cap É—in dake kanta ta kalli Saleym tace ” heeeyyy yadai ?
Murmushi ya fuzgo daqyar yace “you look so pretty Nooreyn!
Dariya tayi tareda cuno masa pink lips É—inta tace “oya muje ko.
suna shirin shiga makeken gidan dake gabansu wata marashiyar yarinya ta fito a cikin wata zabgegiyar benz baqa wadda bazata wuce sa’ar nooryan din ba, qasa tayi da glass É—in motar tace “Nooreyn long time no see?
murmushin gefan baki noor tayi tace “wllh kuwa bt ya naga kin fito kuma?
Ae wllh aiba a nan zamuyi ba a can River kaduna ne.
zaro ido Noor tayi tace “kina nufin duk faÉ—in garin kaduna babu inda yayi muku se bakin wannan ruwan me tafiya a lokacin kuna da ake yawan yin ruwan sama?
matashiyar yarinyar tace ” Ae mana kedai kawai muje karmu É“ata lokaci duk su Aventika suna can nasan an fara shagali. Noor tace “Amma Ekram why se’a nan za’ayi?
Zata sake magana kenan Saleym ya dafa kafaÉ—unta yace “kinga noor muje kawai karmu É“ata lokaci insha Allah babu abinda ze faru mara daÉ—i se alkhairi.
Kama hannunta yayi suka koma mota ita kuma Ekram tayi gaba Sukuma suna binta wanda saleym ne a yanzu yake jan motar har suka isa inda ake gabatar da shagalin nishaÉ—in nasu duk qarshen wata
Tunda sukaje gurin Saleym ke gaisawa da mutane inda itakuma noor take riqe da hannunsa, duk wanda kagani a gurin taron to ubansa yaci kuma ya tara shiyasa duk wadda na kalli fatarta senaga kamar mudubi sabida sheqin jin daɗi, amma sedai abin takaicin kaf matan dake gurin babu wadda tayi shigar arziqi dukkansu shigar baiyana tsaraici sukai, a hakan ma wai gara noor tunda wandonta dogone rigarta kuma ta ɗan sauka dedai saman cibiyarta.
Ana kan ganiyar tiqar rawa ne wayar dake hannun noor ta É—auki ruri tana neman agaji, yatsina fuka tayi tana kallon screen É—in
Sunan Popsy ta gani yana yawo a saman screen na wayan, fita tayi daga gurin tana takawa a hankali harta ɗanyi nisa da gurin da kiɗan ke tashi sannan ta amsa wayar cikeda qaunar mahaifin nata.
Hira suka dan tattauna har suka kammala ta kashe wayar tana murmushi, har a zuciyarta takejin son mahaifin nata yana ratsa ta, a hankali takejin qarar tafiyar ruwan dake É—an nesa da ita
A nitse take É—aga sawun qafarta cikin nutsuwa gamida salonta wanda idan har baka santa ba seka rantse cewar yanga takeyi harta kai bakin ruwan tana kallo, wata irin iskace me sanyi gamida wata sihirtacciyar ni’ima me daÉ—in gaske suka shiga ratsa duk wata gaba dake jikinta, a hankali ta zauna bisa wani qaramin dutse wanda seda ta tabbatar da kafuwarsa a gurin sannan ta zauna tareda zare dogon takalmin fatar dake ɗaure a qafarta, a É—an tsorace ta zura duka qafafuwanta a ciki tana wasa kaÉ—a ruwan a hankali nan take murmushi ya baiyana a saman fuskata.
ta jima tana hakan kamar daga sama taji wani Abu ya daki qafarta, a matiqar firgice ta janye qafarta na dama kafin tajanye na hagun taji kamar abu ya sarqe qafar…… Ihu ta qwallah lokaci guda kuma tayi baya Zata faÉ—i cikeda kiÉ—ima gamida firgici ta fara qoqarin janye qafarta.
Duk wani qoqarin ta a wannan lokacin be wuce na tazaro qafarta daga cikin ruwan ba, amma kuma fir se hakan taqi yuwuwa mata sabida yanda belt É—in É—ake É—aure bisa gefan qirjinsa na dama ta naÉ—e mata qafa, wani irin qarfi ne yazo mata lokaci guda wanda yake ta’allaqe dason ganin ta raba qafarta na haqun da belt É—in ya É—aure
Tana jawo qafar waje taga mutum yana bin qafar kamar takarda sabida yanda mutum ke rage nauyi a cikin ruwa, zaro idanu Nooreyn  tayi sabida tsafar tashin hankalin datake ciki. Gabaɗaya se tsoron nata ya ninka na farko sabida arbar datayi da mutum a irin wannan yanayin da bata taɓa zato ko tsammani ba!
A zahiri ihu takeson yi amma kuma ta kasayin hakan sabida tsabar kaÉ—uwar datayi, gabaÉ—aya ilahirin jikinta Rawa yakeyi wanda hakan ke faruwa duk a sanadin yanayin data samu kanta a ciki.
Kasancewar ruwan babban ruwa ne kuma me tafiya yasa batasha wahala wajen qara qaimin janye kyakkyawar qafarta daga jikinsa ba, haka kuma duk iya qoqarinta na takalli fuskar mutumin seta samu kanta da kasayin hakan dole tasa ta fara qoqarin barin gurin a matiqar kiÉ—i me.
Tsayawa tayi cak lokacin data É—an fara takawa kaÉ—an zuwa nesa da bakin ruwan zuciyata na wani irin racing, take taji wani irin tausayin mutumin ya samu gurbi a cikin kaso tamanin na zuciyarta wanda hakna yay mata tasiri sosai a duk wata kafar jinin dake gudana a sassan jikinta.
Komawa tayi da sauri gurin tareda zube gwiwoyinta duka biyu a qasa, lokaci guda kuma takai hannunta saitin qirjinsa a ɗan tsorace, ji tayi jikin nasa sanyi qarara kamar tana taɓa jikin qanqara, a ɗan hanzarce ta sake kai hannunta dedai mahaɗar babbar jijiyar dake kai saqo zuwaga qwaqwa, nan da nan kuwa ta fara fleeing ɗin yanda jijiyar ke bugawa kaɗan-kaɗan alamar akwai sauran numfashi a tredashi.
Hular kanta ta zare tareda sanya hannayenta biyu cikin gaggawa ta naɗe gashin kanta sosai ta yanda sam baze takura mata ba, miqewa tayi da hanzari har tana haɗawa da gudu ta koma inda Saleym yay parking motanta ɗazun, gabaɗaya aɗan rikice take musamman yanda taga jikin mutumin duk ciwo alamun seda yasha baqar wahala kafin ya iso inda take, wani qaramin box naga ta ɗauka wanda naga anyiwa alama da jan fenti kaɗan hakanne ya bani tabbacin cewar akwatin bada taimakon gaggawa ce, da sauri take gudanar da komai fiyeda farko,  sannan ta juya don komawa inda tabar mutumin a kwance bisa gabar ruwan inda tabarshi.
Ajiye akwatin tayi da sauri sannan ta buÉ—eta ta fara fito da abubuwan dazatai amfani dasu, wani qaramin kwanon silver ta fara fitowa dashi sannan almakashi audiga da kuma askar feÉ—a dakuma wani blue É—in ruwa a cikin wata qaramar roba me murfi.
BuÉ—e ruwan robar tayi sannan ta zuba a cikin silver wadda ke É—auke da almakashi da kuma askar data fito dasu sannan ta sanyawa hannunta safar hannu irin wadda ma’aikatan lafiya suke amfani da ita, tashin farko gefan hannunsa na dama ta fara yakawa dedai saitin inda harbin bindigar ya sameshi, take jini ya fara fita alamar da sauran rai a taredashi.
Ta jima tana fama sannan ta samu nasarar cire harsashin ta ɗinke gurin ta ɗaure, ajiyar zuciya ta sauke meɗan nauyi sannan tasa hannunta ɗaya a saman goshinsa donta tabbatar da abinda takeson ganowa a taredashi, cire hannun tayi tareda zare safar hannun data saka ɗin ta fara qoqarin kwashe kayan datai amfani dasu ta mayar cikin madedaiciyar akwatin.  Wani siririn tsaki taɗanja a lokacin data kalli haɗaɗɗen agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunta.
A É—an hanzarc ta zaro wayar dake jikin aljihun matsatsen wandon dake jikinta ta fara qoqarin kiran wata lamba, ta É—an jima tana wayan sannan ta katse daga yanayin datake magana a wayar zaka fahimci a cikin ujila takeyinta, nan da nan cikin mintunan da bazasu gaza 10ba sega wata zabgegiyar motar Ambulance 🚑 me É—auke da hatimin Q/B special hospital ta danno kai zuwa gurin gadan-gadan.
Cikin mintunan da bazasu gaza biyar ba wasu malaman Asbiti maza suka fito da wani siririn gado wanda yafi kamada na musamman suka É—orashi bisa kai, a hanzarce suke gudanar da komai sannan suka fara qoqarin shiga motar, har sun tada motar ta dakatar dasu dedai lokacin datake ware gashin kanta ya baje a gadon bayanta har zuwa kan tudun cikakken qirjinta, cikeda qasaita take takawa harta isa inda Malaman Asbitin suke takarda ta É—auka tareda zarar biron gaban rigar É—aya daga cikin malaman Asvitin dake sanye cikin farin uniform ta É—anyi rubutu kaÉ—an wanda baze wuce tsayin layi uku ba ta miqa musu, tareÉ—a faÉ—in” make sure kunyi masa wannan alurar sannan kuma lallai ku tabbatar an saka masa jinin dazeyi dedai da nasa, kuma ku bashi kulawa ta musamman.
Cikeda girmamawa suka Amsa da to ranki ya daɗe. A kwatin ta ɗauka tabar gurin cikin takunta na isa gamida yarda da kanta ta nufin inda ake gudanar da shagalin mazaunanta na wani irin juyawa,  sannan suma suka tashi motar da hanzari suka nufi tsadadden Asbitin dake cikin tsakiyar Unguwar Rimi.
Tana zuwa gurin bata nufi ko inaba se inda Saleym yake zaune tace “pls my car key!
Yana shirin magana kenan ta dakatar dashi ta hanyar faÉ—in “pls Saleym!
Bece mata komai ba ya miqa mata ta juya da sauri tabar gurin kamar walqiya, da ido kawai Saleym kebinta ganin dayay tana shirin É“ace masa ne yasa yay hanzarin bin bayanta, tana qoqarin shiga motar ya riqe mata hannu yace “Noor lfy kuwa naga duk kin sauya? Koda…… “pls Saleym I have an emergency patient in the hospital so pls let me go bani da time É—in É“atawa.
Ajiyar zuciya ya sauke sabida jin abinda tace ko bakomai ai hankalinsa yanzu kam ya kwanta, yana sakinta taja murfin motar ta rufe tareda murza mata key tabar harabar gurin at 360.
******
A hankali yaron ke tafiya duk lips ɗinsa sun bushe sabida tsabar qishin ruwan dake addabarsa, amma sabida baqin naci sam yaqi jefar da qaramar jakar goyon dake hannunsa, kamar daga sama yaji wani abu ya sarqe masa qafafu nan take ya qwalla qara tareda zubewa qasa sumamme!!!!!!
Comment
Nd
Share
​
Name: | [ ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |