Hausa Novels

Muradin Zuci Hausa Novel

Muradin Zuci Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Muradin Zuci Hausa Novel

*MURADIN ZUCI…*💘

“`romantic story“

 

*MRS SADAUKI *

 

 

“`GA MASU BUƘATAR BOOKS ƊINA NA KUƊI ZA SU IYA YI MIN MAGANA TA WHATSAPP +22795045822 AKWAI RAGI GA WANDA YA SAYI BIYU LOKACI GUDA,TOBY ƊAN DAMBE DA BANGO NA BUƊE BONUS GA MAI SO ZAI BIYA 200 A MAIMAKON 300“`

 

Page 1-2

 

 

 

Kwance yake bisa ɗan madaidaicin gadonsa na ƙarfe daidai kwancin mutum ɗaya,hannun shi riƙe da malheci yana fifita domin kore gumin da ke feso mashi.Kwanciya ya gyara ya ɗora hannun shi bisa lafiyayen ƙirjin shi mai yalwatacen gashi, ya na shafa sa har izuwa shafafiyar mararsa yayinda idon shi ke lumshe kamar mai barci.

 

 

Jikin shi ne ya bashi kamar ana kallon shi hakan yasa ya buɗe ido, tsaye take bakin ƙofa ta leƙo ta jikin labule tana ƙare mashi kallo tun daga santala-santalan cinyoyin shi masu ɗauke da gashi baza-baza har izuwa ƙirjin shi mai yalwar gashi kamar wata ciyawa ya kwanta luf.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Rumtse idonta tayi ganin ya miƙe da azama wanda hakan yasa mazantakar shi kaɗawa kasancewar gajeran wando ne kawai jikin shi.

 

 

“Wane irin hauka ne ki shigo min ɗaki babu sallama?ke wai tukunna ma uwar mi kika zo yi ba nace ki shafa min lafiya ba? Fitaaa !!!!”ya faɗa cikin ɗaga murya yana nuna mata hanyar waje da yatsa.

Maimakon ta fita kawai sai ta ida shigowa tana mai fashewa da kuka “FARUK ka bar yin haka please duk lokacin da kake faɗa da fushi guguwar sonka ƙaruwa take a raina”kallon bakida hankali yake mata kafin yace “FARHAT ki shiga hankalin ki ban son iskanci ni sa’an ki ne da har zan maki magana ki ƙi bi?nace ki fita”ya faɗa amman awannan karin ya ɗan sassauta murya,ƙarasowa tayi dab da inda yake tace “toh zan tafi amman dan Allah ka so ni ko da ɗan kaɗan ne kaji?Allah ina maka son so “ta faɗa tana kallon cikin idon shi ba tare da shakkar komi ba kamin ta ajiye wani ɗan ƙaramin nounous(Teddy) mai sarkaye da makulli.

 

 

Bin ta yayi da ido yana mai kallon yadda ƙugunta ke kaɗawa ta jikin doguwar rigar da ta saka wacce ta matseta sosai,ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon inda ta ajiye makulin ko bata gaya mashi ba ya san makulin mashine ne🏍️.Fitowa yayi waje ya tsinkayi h kalar babur sabo fil cikin ledar shi,ƙarasawa yayi murmushi ɗauke da fuskar shi ya haye babur ɗin.

 

 

 

💕💕💕💕💕

 

 

*UNIVERSITÉ ƊAN DUKO DE MARADI* ɗalibai ne ke ta shawagi a ciki wasu na shigowa wasu na fita yayinda wasu ke taɓa hira gungu-gungu.

 

 

 

Ƴan mata huɗu ne kyawawa,tafe suke suna cin abinci a leda tamkar wasu yara in ka fidda ɗaya wacce kanta ke ɗuƙe ledar abincinta ga hannu.

 

Gungun wasu samari suka kawo wanda ke dab da ajin su,muryar da suka tsinkayo yasa duk suka tsaya yayinda fuskar ɗayan ta fafaɗa da murmushi “chérie shine kika fita ba tare da kin nemi izini na ba ko?”wani ɗan farin saurayi ya faɗa yana mai ƙarasowa kusa da ita “BASIRA ki tardo ni classe dan hirar ku ba mai ƙarewa ba ce kamar wasu mata da mijin na gaske”ɗaya daga cikin ƴan matan ta faɗa su kuma sauran suka yi dariya tare da wucewa.

 

 

“Ya zaman sa idon ne har kun fara tun yau?”ta faɗa tana ɗan hararen shi, murmushi yayi yace “matata na gaya maki babu wani sa ido da muke kawai hira ce muke”

“Toh Allah ya sa mu tafi ka rakani aji tunda ka kore min ƙawaye”bag ɗinta da ke sarkaye da kafaɗa ya amsa kafin su doshi aji.

 

 

Ganin shigowar su yasa aka ɗauki ihu ana “mijin hajiya Abdul mijin hajiya”ko ci kanku bai ce masu ba sai ma dariya da yayi tare da zaunawa kusa da ita suka fara cin dambu da ta sawo har suka cinye tare suka sha ruwa…

 

 

 

 

“BASIRA ni fa gani nike kamar dagaske ABDUL son ki yake”JAMILA ta faɗa tana kallon ta, murmushi tayi tace “babu wani so juste nous sommes des amis intimes ne kin fi kowa sani tun collège (,secondry)muke classe guda da shi har muka zo nan kinga doli mu saba da juna”BASIRA ta faɗa tana lalubo kuɗi daga cikin jaka ganin an kusa kawowa gidan su,a bakin ɗan madaidaicin get ɗin su mai adaidaita sahu ya tsaya ta biya shi harda na JAMILA tayi godiya suka yi sallama…

 

 

 

 

💕💕💕💕💕

 

 

 

Sanye yake cikin riga da wando na Indou farare ya ɗora jan ƙyale a wuya (cache cou) fitowa yayi yana mai ɗaura agogo a hannu kamin ya ƙarasa ƙofar ɗakin maman wanda yake ɗan nesa da nashi ,sallama yayi ta amsa hakan yasa ya shiga tun daga nesa take ƙare ma tilon ɗan nata kallo kyakyawar Chocolat coulor ɗin shi sai sheƙi take kayan ba ƙaramin karɓar shi suka yi ba.

 

 

Turo baki yayi gaba yace “Maman gaishe ki fa nike amman kallona kawai kike ko ban yi kyau ba?FARUK faɗa yana mai cire takalmin ƙafarshi ya tako bisa tabarmar da aka shimfiɗa a tsakar falon wadda mamar shi ke zaune.

 

 

“Kayi kyau sosai kamar Amita Bacha na Indiya”Maman ta faɗa tana murmushi kafin ta fara motsa damamar furar da ta sha nonon shanu da ƙanƙara ta turo gaban shi.

 

 

Tanƙwashe ƙafafun shi yayi har yanzu murmushi bai fita daga fuskar shi ba na yabon kyawunsa da maman tayi,sai da ya sha ya ƙoshi sannan ya fiddo moton da FARHAT ta kawo mashi jiya.

 

 

Saurin fitowa Maman tayi jin ƙarar mashine cikin gidan su,tsaye tayi shaye da mamaki ko kafin ta ƙaraso FARUK har ya fita a tsiyace addu’a tayi mashi ta koma ɗaki tana mamakin yaushe ya sayi moto.

 

 

 

*I.S.B* can yayi tsinke yadda ya shigo a tsiyace yasa duk idon kowa ya dawo kan shi,wasu na yaba burgar shi yayinda wasu ke tsine mashi “wlh da ace a farin namiji ya fito da ƴan mata sun shiga uku diba ki ga wani irin shiga da yayi sai kace wanda ya fito daga India mtsw…”wata ta faɗa tana mai kallon shi ta kusa da ita ta karɓe da cewa “ai kam sun mashi kyau kuma a haka coulor ɗin shi tafi ta fararen mazan”,”ni kam sajen shi ke burge ni da gashin da ke kwance a ƙirjin shi,shiyasa nafi so yayi shigar ƙananun kaya ta yadda zan dinga ganin komi”wasu gungun ƴan mata ne ke gulmar shi.

 

 

 

 

Tun daga nesa ta kafe shi da ido duk takun guda da zai yi sai zuciyarta ta buga,ƙamshin turaren shi sai ƙara dosota yake lumshe ido tayi tana mai jin daɗi har ƙasan zuciyarta.Iskan da taji an hura mata a ido yasa ta buɗe su tarau kyakyawar fuskar mai zagaye da saje tayi mata maraba ido cikin ido suke kallon juna kafin ya gota ta ya wuce yana mai cewa “ki rinƙa adana maitarki dan ta fara fitowa fili”wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tare da waigawa tana mai kallon takon shi na ƙasaita,jin an wani fizgota da ƙarfi yasa ta dawo da hankalinta , fuskarsa cike da ɓacin rai kafin ta samu damar magana ya sharara mata mari tare da nunata da yatsa “last warning wlh ko kallon shi naga kin sake yi sai nayi ƙasa-ƙasa da ke na sa a ɓatar da shi “NUR ya faɗa yana huci……

Leave a Comment

error: Content is protected !!