Musayar Zuciya Hausa Novel

Musayar Zuciya Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MUSAYAR ZUCIYA
HADIZA D AUTA

Ƴanmata biyu ne cikin motar, ɗaya tana driving ɗin motar yayin da ɗayar take zaune a gefenta tana nazarin wani littafin husnul Muslim dake hannunta ɗaya, ɗaya riƙe da carbin roba tana lazimi jefi-jefi. Nazira ta kalli Nana da hankalinta ya ɗauku ga littafin tace

“Wai Nana yanzu ma ba zaki bari mu tattauna abun da ya dace ba?”

Nana ta É—ago da kanta tare da É—ora idanuwanta gareta tana murmushi, ba tare da tace da ita komi ba, cikin É“ata fuska Nazira tace

 

Tattalin So Hausa Novel

“Don ALLAH ki ajiye littafin mu yi magana Ni dai”

Nana ta rufe littafin ta mayar a ƙaramar jakar da ke saman cinyarta, sannan ta dawo da kallonta ga Nazira tace

“Hakan ya yi maki ko?”

Nazira ta É—an harareta kaÉ—an tana Æ´ar dariya tace

“Ko kefa!? To yanzu faÉ—a man ina zamu fara zuwa? Wurin Æ™unshin ko wurin saloon É—in? Ko kuwa mu fara zuwa in karÉ“o É—inkuna na?”

Nana ta yi murmushin da ya ƙarawa doguwar fuskarta kyau sannan tace

 

 

 

 

Musayar Zuciya Hausa Novel

“Mu fara zuwa ayi maki Æ™unshin ina ga hakan sai ya fi, idan an gama sai mu je wurin Madam Ngozi ta gyara maki kan, da mun kammala da cen sai mu karÉ“o É—inkin mu yi gida kawai”

Nazira cike da jin daÉ—in wannan tsarin na Nana tace

“Thanks my beautiful sis, Amman ke wai da gaske kike yi ba za ki yi kwalliyar tarbon my Bear ba?”

Nana ta É—an haÉ—e fuska kaÉ—an sannan tace

“Bani a ciki gaskiya”

Nazira tana Æ´ar dariya tace

“Kin ci bashi Hajiya zan rama ne ai!”

Nana tana Æ´ar dariyar itama tace

 

 

 

Musayar Zuciya Hausa Novel

“Oho Ni dai kam ba zan yi ba”

Haka suke ta firarsu cikin raha da annushuwa har suka je gidan Æ™unshin, tsawon awa biyu Æ™unshin ya cenye masu sannan aka kammala, suka biya kuÉ—in suka fito zuwa shagon Madam Ngozi, a cen ma sun ci lokaci kafin a gama saboda sun taradda mutane, bayan sun gama ne suka nufi wurin karÉ“o É—inkin Nazira, cikin sa’a ko da suka je ledar É—inkin kawai ya miÆ™o masu suka fito cike da murna.

Suna kan hanyarsu ta komawa gida ne Nazira tace

“Ban san ya zan yi ba idan na Æ™ure lokaci a shagon kwalliyar nan ba, wai ko dai mu juya mu je in yi wankana a cen a shirya Ni kawai?”

Nana da ke ta kallon gaban titin cikin murmushin da ke fuskarta har lokacin tace

 

 

 

Musayar Zuciya Hausa Novel

“Eh hakan ma ya yi, amman me zai hana mu fara zuwa gida mu ci abinci ki yi wanka?, Saboda na kira Basira zata zo har gida ta yi maki kwalliyar”

Nazira cike da masifar jin daÉ—i tace

“Wowwww! Da kin gama burgeni my sis don na tabbatar da cewa sai na fi fitowa a cikin kwalliyarta, na ji daÉ—i sosai Wallahi ai na manta shaf da ita ne Allah, amman ki Æ™ara kiranta yanzu ta zo da wuri don ALLAH, gudun lokaci ya Ƙure muna har ya zo ba a gama ba”

 

 

Musayar Zuciya Hausa Novel

Ta ƙare maganar cikin damuwar da ta kasa ɓoyuwa a kan fuskarta, Nana ta yi ƴar dariya sannan tace

“Kar ki damar da kanki a kan hakan, wataÆ™ila ma ko da zamu je mu taradda ita gida tana jiranmu”

See also  Hakki Ne Hausa Novel Zahra Surbajo

Nazira ta yi saurin riƙo hannunta tace

“I love you so much my sis, shi yasa a kullum kike Æ™ara matsayi a zuciyata, ALLAH ya nuna muna ranar aurenku ke da yayanmu mu sha rawa”

Ta ƙare maganar tare da sakin sitiyarin motar tana tausaya, Nana ta maka mata harara tana cewa

“Ki bi a hankali Hajiya, kar garin murna ki je ki É“aradda mu ki hana mu ganin lokacin to”

Ta ƙare maganar tare da haɗe fuska alamun ba wasa ɗin nan, Nazira tana dariya ta ɗora hannunta ɗaya a kan sitiyarin tana juyashi cikin ƙwarewa tace

“Haka ne kuma fa, sai dai kin san me?”

Nana tace “A’a sai kin faÉ—a”

Nazira ta shiga natsuwarta sosai sannan tace

 

 

Musayar Zuciya Hausa Novel

“Ina jinki a jikina tamkar Æ´ar’uwata da muka fito ciki É—aya, amman ban san me yasa wata rana Hajiya take yin wasu abubuwan ba, ko ko ita bata gano yanda kike Æ™aunata da zuciya É—aya bane Oho?”

Nana ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

“Har kullum ina cewa da ke ki daina kama irin waÉ—annan abubuwan a zuciyarki, Hajiya uwa ce gareni kamar yanda take a wurinki, duk abinda kika ga ta yi man ba don bata sona ta aika abun ba, saboda haka ki daina kama irin waÉ—annan Æ™ananun abubuwan plss! don ALLAH”

 

 

 

 

Musayar Zuciya

Nazira ta sauke ajiyar zuciyar itama sannan tace

“Na daina amman kema ki ci gaba da haÆ™uri da halinta don ALLAH, don na san wata rana zata gano gaskiya ta daina Æ™in zamanmu da juna”

Nana ta kawar da zancen da murmushin da baya rabo da kan fuskarta tace

” Yau dai wata zata yi kwalli da Angonta, mu dai don ALLAH kada ki bari ya gano kin fishi zumuÉ—in haÉ—uwarku, amman fa ban ce kada ki nuna masa farin cikin ganinsa ba yasin”

 

 

 

Musayar Zuciya Hausa Novel

Nazira ta fashe da dariya tana cewa

“Idan naje ai fuskar shanu zan masa, in yace lafiya in ce da shi Nana ce tace in yi maka hakan…..”

Nana ta zaro fararen idanuwanta masu kama da an É—iga zaiba tace

“Rufani ki saya kar ki janyo in kwana a prison yau, wannan mayen Æ™arfen naki ai zai iya yin gunduwa gunduwa dani in ya ji ina lalace masa hanya”

Nazira banda dariya ba abinda take yi har suka shiga Gate É—in gidansu, tana dariyar ta yi parking tana cewa

“My sis kin cika tsoro da yawa fa, to miye a ciki ai kina da ikon da zaki sakani in yi abu ko?”

Nana ta janyo ledar kayan É—inkin ta fito tana cewa

“Eh kam! amman ban da wannan tsakaninki da Æ™albinki sam! bani a ciki tabbas!”

 

 

 

Musayar Zuciya Hausa Novel

Ta yi gaba tana Æ´ar dariya Nazira ta rufe motar ta biyota a baya tana faÉ—in

“Yasin kika ce kada in yi magana har ya tafi hakan zan yi ALLAH”

Nana cike da bugun zuciya a kan maganganun nata tace

“Allah ya kiyayeni da wannan gangancin to”

Suna dariya suka shiga gidan, sai dai hango Basira da akwatin kayan kwalliyarta a gefenta, yasa Nazira buga wani uban tsalle tare da ihun murna ta yi wurinta da gudu ta rungumeta, Nana ta ƙaraso babban falon ta ajiye ledar ɗinkin dake hannunta, ta zauna kusa da Basirar itama tana murnar ganinta, sai ga Hajiya tana saukowa ƙasa idonta a kansu tana faɗin

“Tun da na jiyo ihunki na san kun dawo gidan, ke kan Nazira yaushe zaki natsu ne ki daina wannan rawar kan naki ne?”

See also  Ali Dan Tsoho Hausa Novel Download

Nazira ta ɓata fuska cikin Muryar shagwaɓa take cewa

“Me na yi kuma yanzu daga dawowata Hajiya?”

Hajiyar ta zauna ranta a haÉ—e Basira ta fara gayar da ita ta amsa ba yabo ba fallasa, Nana ma ta kalleta cikin É—ar É—ar tace da ita

“Mun dawo Hajiya Barka da gida”

Hajiyar cikin haÉ—e fuska tace “Sannunku”

Nazira ta ɗauki akwatin Basira tare da riƙo hannunta tace

“Zo mu je sama ki huta kafin in kammala abunda zan yi mu fara tun kafin lokaci ya Ƙure muna”

Tana janta suna hawa sama take maganar, Nana a bayansu riÆ™e da ledar É—inkin Nazira suka haye, Hajiya ta bisu da kallo zuciyarta cike da takaicin Æ´arta Nazira, saboda ganin kamar bata san ciwon kanta ba kwata-kwata, don ta tsani saka Nana da mutanenta da take yi a jikinta irin hakan, ta kasa gano akwai tazara mai yawa a tsakaninsu tun tuni, ta dawo da kallonta a kan t.v’n dake falon yana aiki ta yi Æ™wafa, a ranta tace

_”Ban san me yasa a kullum na kalli yarinyar nan nake jin faÉ—uwar gaba ba, bana sonki Nana bana Æ™aunar ina buÉ—a idanuwana ina ganin shawaginki cikin gidan nan, ina tsoron ki zamewa Nazira musiba a rayuwa, don wannan shegen kyaun naki Ni kaina tsoro yake bani”_

Ta sauke ajiyar zuciya ta miÆ™e cikin matsananciyar damuwar da ta kasa É“oyuwa a kan fuskarta, har zata haye saman ta dawo ta Æ™wallawa mai aikinsu kira, ta iso jikinta yana rawa ta duÆ™a kanta a a Æ™asa saboda bala’in tsoronta da take yi, Hajiyar tace da ita ta je ta kaiwa su Nazira abincinsu sama, kuma ta tabbatar da sun gama ta je ta fito da kayan.

Landi ta miƙe cike tsoron faɗan Hajiyar ta nufi kitchen, saboda saurin ta bar wajen kamar ta kifa ta shige kitchen, Hajiyar ta buga uban tsaki ta haye sama tana faɗin

“Aikin banza kawai”

Nazira kam suna shiga ta faÉ—a gadonsu cike da farin cikin da ke huda zuciyarta, tana ta ihun murna har da su É—aga kafafuwa sama saboda nishaÉ—in da take ciki,, Nana ta zauna kan gadon ta fito da kayan da ke cikin ledar, ta fara yaba É—inkin cike da jin daÉ—in yanda aka tsarashi komi ya hau dai-dai, Basira ma ta yaba É—inkin sosai har da É—aukar rigar É—aya daga cikin É—inkunan tace da Nazira

“Wannan zai yi pitting É—inki sosai mutuniyar”

Nazira ta tashi daga kwancen da take ta sauko gadon ta karɓi rigar, cike da farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskarta ta ɗorata a saman jikinta tace

“Ai telan ya san aikinshi sosai, shi yasa bana jin haushin biyan kuÉ—i ko nawa ya faÉ—a, don na san ba zai sakani ciwon kai ba…..”

Sallamar Landi da wata mai aiki ne yasa duk suka mayar da hankalinsu kansu, cikin ladabi suka gayar da su suka ajiye kayan abincin zasu fice ÆŠakin, Nana tana Æ´ar dariya tace da su

“Sannunku da Æ™oÆ™ari Æ´anmatan Hajiya”

Su Landi cike da jin daÉ—in kulawar da take basu kullum, suka amsa sannun da ta yi masu sannan suka fice É—akin da sauri, saboda tsoron su daÉ—e su yi laifi wurin Hajiyar.

Nana ta sauko ta fara Saving ɗin Abincin suna ci gaba da zancen ɗinkin yabon mai telar da zagin wasu marasa cika alƙawali, sun baje sosai dukansu uku sun ci Abincin sannan suka yi sallah, Nazira kam sai da ta yi wanka ta yi sallah, Basira ta baje kayan kwalliyarta ta fara aikinta cikin ƙwarewa, Nana ma tashi ta yi ta shige toilet ta yi wankanta sannan ta fito ta shirya, cikin wata doguwar riga haƙa ta ɗaura ɗankwalinta, sai dai ban da mayuka bata saka ko powder ba don haka take yi abunta kullum har ta saba, sannan ta zauna tana kallon yanda ake ta fente fuskar Nazira sai ƙara fitowa take yi Masha ALLAH.

See also  Hausa Novel Wattpad Documents

Bayan an ƙare kwwlliyar ne ta saka ɗaya daga cikin ɗinkunan da suka karɓo, ɗanyen boil ne pink color mai ƙuna da ratsin golden a jiki ga ɗinkin ya hau jikinta sosai ba ƙarya, Basira ta yi mata wani disign ɗin ɗaurin ɗankwalin da ya ƙara fito da ita cas-cas, Nana da Basira sai yaba haɗuwar da ta yi suke yi tana jin daɗi, itama kanta da ta kalli madubi sai da ta ji ta burge kanta matuƙa, saboda yanda ta fito tamkar ba ita ba kai kace wata sabuwar Amarya ce, Nana ta fara fesheta da kalolin turaruka tana santin kwalliyar, sannan ta ɗauko waya ta fara ɗaukarta photuna cike da farin ciki sai jujjuyawa take yi, Naxira ta kalli Nana bakinta a washe tana dariyar jin daɗi tace

“Ke ma ki zauna ayi maki don ALLAH zaki yi kyau da irin wannan kwalliyar fa”

Nana tana saka photunan Naxirar a status tace da ita

“Yasin bana so nafi son ganina haka, don haka barni a yanda kika ganni É—in nan, idan ma kin ga zan yi maki cuss da yawa shi kenan sai in yi zamana É—aki ba sai mun gaisa da shi ba”

Naxira ta haɗe fuska tare da riƙo hannunta tace da ita

“Me yasa a komi kike nuna kin fi son in yi ke ba sai kin yi ba? Yanzu ita kwalliyar miye a ciki da ba zaki bari ayi maki ba?”

Ganin yanda ran Naxirar ya É“aci ne Nana ta zare hannunta cikin nata ta zauna, sannan ta kalli Basira tana Æ´ar dariya tace

“Shafa man powder kawai tun kafin ta yi kuka tasa mu yi asarar kwalliyar”

Basira tana dariya ta fara shafeta da kalolin powder, Nana tace ita sam bata son wata doguwar kwalliya, ayi mata make up sama sama sai Oil lips kawai, Basira tana dariyar halin Nanar tace

“Wallahi Nana ina yi maki addu’ar ALLAH ya haÉ—aki da wanda zai ce kullum sai kin yi masa kwalliya kala goma”

Nana ta ƙwace kanta tare da kai mata duka tana faɗin

“Muguwar banza to yasin ko yana so ba yi masa zan yi ba tunda Ni bana ra’ayi”

Naxira ta zauna tana dariya tace

“Shareta kawai Basira don ta san tana da kyau ko babu kwalliya ne shi yasa take gudunta, amman yanda take É—in nan ace tana kwalliya ai ko mu sai mun lalace gurin kallonta bale…….”

Kiran wayarta da aka fara yi ne ta daina maganar, cikin zumuɗi ta ɗauki wayar sannan ta ja gyalenta tare da saka talkama a ƙafarta tana faɗin

“My Bear Oyoyo! Ok jirani minti biyu..”

Sai da ta kai bakin ƙofa da gudunta sannan ta waigo tace da su

“Idan kun ji Ni shiru ku sameni a cen ku gaisa bye! ”

Ta fice É—akin da sauri suna yi mata dariya.

Hmmmm danƙari wannan book tafe yake da cakwakiya mai wuyar fassara, tare da zazzafar soyayya mai tsayawa a wuya, a gefe ɗaya kuma akwai tausayi mai tsayawa a maƙoshi, don haka ku garzayo ayi da ku kar ku bari a baku labari.

​

 

 

Name: [ZUCIYATA HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


6 thoughts on “Musayar Zuciya Hausa Novel”

  1. Pingback: JIKI NA YAKE SO COMPLETE HAUSA NOVEL | My Novels

  2. Pingback: Muradin Zuci Hausa Novel | My Novels

  3. Pingback: Romance hausa novel Wattpad | My Novels

  4. Pingback: Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta | My Novels

  5. Pingback: Wata Uwace Hausa Novel Document - Hausa Novel

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top