Musayar Zuciya Hausa Novels

Musayar Zuciya Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: MUSAYAR ZUCIYA

~ Na ~

 

🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃

 

Page 1

MUWANSHAT COLLEGE OF HEALTH SCIENCE AND TECHNOLOGY JALINGO shine rubuce baro-baro a kofar gate na school in,zaune take a aji gabaki d’aya Bata cikin natsuwar ta bini bini take daga tsintsiyar hannunta tana Kai dubanta ga agogon dake d’aure a hannun nata,Dan tsaki taja ganin lecture in baida niyar fita ita Kuma gabaki d’aya ta hafi a tashi gudun kada 5:00 yayi.

 

 

Sauke numfashi tayi da karfi ganin lecture in ya fice daga ajin, da mugun Sauri ta Mike tsaye sanye take da farin rigan uniform zuwa gwuwa sai guntun hijab shima fari yayin da wandon ya kasance ruwan toka,a wanke suke a goge tas Kamar Wance Bata wuni a school ba jakar ta ta Saba Baki da Sauri ta fita a ajin ta sauka a floor na hall nasun kafarta sanye da boot fari tass,dogowace sosai, Mai dauke da diri Mai kyau Kuma Mai ban sha’awa karyan lafiyayyen namiji ya karewa tafiyarta kallo baiji d’ar ba.

 

 

Harta Isa gate taji ana kwala Mata Kira daga nesa”beentee beenteei Kee beentee I”…….Dan guntun tsaki taja, taja ta tsaya ba tare data juyo ba jingina tayi da bishiyar flowers dake gefen gate in,karasowa yarinyar tayi a kalla itama zata Kai tsarar ta sanye da uniform na school sai dai ita ta daura abaya akan uniform in jikin nata, ga dukkan alamu ta Saba da hakan,”Wai beentee kina nufin tafiya zakiyi ki barni Koh me kike nufi ne Naga an tashi Baki wani jirani ba kin hau Sauri Zaki bar school in”?

 

Dan yamutsa kyakkyawar fuskar ta tayi cikin yanga tace”kinga sareena Sauri nake wallahi”wani hararan ta budurwar da ta Kira da sareena tayi Mata kafun tace”Kee dai Kika sani wallahi koma saurin me kike ai Zaki jirani mu tafi tare ai,tafiya Suka Soma Suna dan Hira Wanda amsa Mata kawai beenteei keyi Amma ba anan hankalinta yake ba Suna fitowa bakin titi anan Suka tarar da wasu daliban na taran abin hawa wasu Kuma mototin gidan su ke zuwa daukar su Keke sareena ta tare kana ta sanar dashi inda zai kaisu,shiga tayi ta zauna sai Kuma ta juya da mamaki tana kallon beenteei”bazaki shigo bane Koh yauma halin Zaki gwada”murguda Baki tayi kana tace”Ni kawai ki wuce akwai Wace zanje gani a clinic”?

 

 

Zakije ki duba wata Koh Zaki je wajen sa a UMMA CLINIC wallahi beenteei Ina rabaki da lamarin wannan Dan wulakanci Amma Baki ji”Koh kula sareena batayi ba ta tsallake titin ta nufi hanyar clinic in,girgiza Kai kawai sareena tayi Mai keken yaja Suka Lula,tafiya take hankalin ta duk a tashe gudu gudu Sauri Sauri ta shiga cikin clinic in da yake baida wani nisa da school in,tafiya take duk Inda tazo wucewa saita gaida jama’ar wajen daga marasa lafiya harda ma’aikata, office insa ta wuce,don daman an riga an santa Babu Wanda ya dakatar da ita da sallama ta bude kofar tare da leka kanta a ciki Amma Bata shigar da gangan jikinta ba.

 

 

 

Zaune yake akan kujeran office nasa wow Masha Allah kyakkyawan namijine Wanda ya amsa sunan sa namiji farine tass Amma duk hasken sa Bai Kama tata hasken ba don ita hasken nata karshene a d’aukar hankali, duke yake Yana rubuce rubuce duk da yaji karar bude kofar office Amma baisa ya d’ago ya ga kofar ba,lumshe idanunta tayi masu girman gaske tana kara shekan kanshin dake tashi a cikin office in, sai Kuma ta bude idanun nata da Sauri Jin sautin tsakin sa,kallon sa tayi Suka had’a Ido ya tsakar Mata harara Wanda bazai fasssaru ba baza’a ce hararan tsana ba bazakuma a kirashi na soyayya ba,washe Masa hakoran ta tayi masu kyau ras dasu, tana Masa murmushi sauke idanun sa yayi a jikinta, ya mike tsaye Keyn motar sa ya d’auka ya Sabi lapcoat nasa ya nufi kofar Koh motse batayi ba tana tsaye jingine da bangon office in ta waje yayinda daya hannunta ke rike da handle in kofar office in kanta ma na ciki Amma Bata shigar da gangan jikinta ba,dan tsayawa kawai yayi Yana kallon ta cikin haushi Amma Taki matsawa har lokacin idanunta na Kan fuskar sa tsaki taja kana ya bude bakin sa a hankali cikin yanga Yana nuna kofar da yatsa yace”ban waje”

 

Kyafkyafta idanunta tayi kafun ta shugwabe fuska kana tace”baby kayi kyau”hannu kawai yasa ya turata gefe,saura kad’an ta fadi kana ya rabata ya wuce abinsa, da Sauri tabi sa a baya tana dan yamutsa fuska amma Bata damu da Turin da ya Mata ba,tafiya yake cikin hanzari yayinda ita Kuma ke Dan binsa da gudu gudu saboda tazarar daya Bata fitowa sukayi bakin compound na hospital in mutane sai kallon su suke wasu Kam sai dariya suke kasa kasa saboda sanin abinda zai biyo baya,bude motar yayi itama tasa hannu ta bude ta shiga Aiko Nan take ya fito daga motar ya Fara takowa zai zagayo side Inda take da Sauri ta rarrafa ta koma driver seat in, abin ya kuntata Masa rai, Inda ta tashin wajen ya shiga, ya biyota har wajen data koma duk yanda take kokowa da sterin motar Saida ya fizgota waje kana ya rife kofar motar sa ya bar cikin hospital in hawaye ne ya cika Mata Ido har wasu na tsiyaya sai Kuma tasa hannu ta goge idanun nata a hankali ta Soma takawa tana fita daga cikin hospital in yayin da mutanen Suka binta da Ido don su sunfi Mata kallon mahaukaciya Kamar yanda sauran jama’ar da Suka Santa suke Mata kallon Mai matsalar kwakwalwa yayinda ita kuwa tasan lafiyar ta kalau babu abinda take na rashin hankali,wannan Karo babu jaka a hannun ta don ta barshi a cikin motar garin kokuwa shi Kuma Dr ya tafi dashi cikin rashin sani.

 

 

 

Tunda ta fito bakin titin aka Soma yayyafi yaf yaf ga iska Mai karfi da Sauri ta matso tana sa hannu zata tare Keke amma Koh wani Keke ta tare baya tsayuwa saboda halin ruwa da ake ciki kowa so yake ya nemi mafaka,kuka ta Soma a hankali lokacin da ruwan ya barke da karfi gashi kunyan komawa cikin hospital in takeji yanzun haka zalika shagunan wajen duk an rurrufesu saboda ruwa da Kuma mangari ba daya Soma Shiga.

 

 

Takawa ta Soma a kafa ruwa na dukanta gabaki d’aya ta Kara jigilar da kanta ga yunwan school ga dukan ruwan sama ga Kuma wani irin daci daci da takeji a can kasan ranta na wofantar da soyayyar ta da Dr keyi Kuma ta rasa dalili? kyau har kyau tana dashi Amma ta rasa,da kafa ta taka har unguwan gadi zuwa lokacin mangari ba yayi jikinta jakaf da ruwa,tsallako titi tayi ta shiga layin su,babban gate ne na karfe duk da ya tsufa Amma da karfin sa hannu tasa ta tura karamin kofar ta shiga Wanda hakan ya tabbatar da Nan ne gidan su.

 

 

 

Babban gidane Mai sassa daban daban baza’a ce gidan masu kudiba Amma Suna da rufin a sirin su daidai gwargwado don ginin block da block ne a gidan wasu sassan harda tiles da Aminium gidan shuru Kamar babu Jama’a saboda ruwan da ake Kara cusuwa tayi cikin gidan tana Dad’a ratsa sassa kusan biyar kafun ta doshi wani flat Mai D’an kyau step na floor in tayi kofufi biyune akan sa daya babba daya karami a hankali tasa hannu ta tura kofa karamin ta cusa kanta ciki vakinta d’auke da sallama duk da tasan babu Mai amsa mata,ga tarin mamakin ta mama ta gani zaune a bakin katifar ta, ta buga tagumi Jin sallamar ta yasa ta mikewa tsaye fuska ba walwala tace”Amma Kedai benteei bakiji d’adi ba a rayuwar ki wannan wani irin rayuwa ce ace ke baza’a fadamiki magana kiji ba,Ni shikenan bani da kwanciyar hankali a rayuwa ta kinfi son kullum sai kin jazamin magana awajen mahaifinki kafun hankalin ki ya kwanta kenan”?

 

 

 

Sunkuyar da Kai tayi cikin sanyi da muryarta daya dishe tana Dan rawan sanyi tace”Dan Allah mama kiyi hakuri assignment aka bamu shine na tsaya Y……….Bata Bari ta karasa ba tace”rufemun Baki makaryaciyar banza assignment ne kikajeyi a clinic”?

 

 

“Wallahi mama karya ta fadamiki Ni banje clinic ba”wake Miki karyar kenan?duk munafukin da ya gayamiki,bauuu mama ta buge Mata Baki Wanda ya sata sakin ihu kad’an tana dafe bakin”hawaye na Kara taruwa a idanun ta”wallahi kin shiga uku da rashin zuciyar Nan naki wallahi mutum ance ba’a sonsa dole ne Koh ana son dole yarinya sai nacin tsiya Kamar mayya indai har bazaki rabu da yaron Nan ba wallahi kinyi asara”tana gama maganar taja dogon tsaki ta fita a dakin sauke ajiyar zuciya benteei tayi tasan tabbas bata kyautawa mama ba amma Yaya zatayi zuciyar tace duk yanda ta guje Mata kasawa take.

See also  Ba'a Shan Zuma na Benaxir Oumar Complete

 

 

 

Uniform in jikinta ta kwabe anan tsakiyar dakin jikinta sai rawa yake karkar Kar towel ta d’auka ta daura da Sauri Jin ana kokarin bude kofar dakin nata, mama ce ta shigo da flasks a hannun ta ba tare data kalli Inda take ba ta wuce toilet na dakinta bata Jima ba saigata ta fito tare da bawa benteei umurnin shiga ta watsa ruwan data had’a Mata da Sauri kuwa tayi bandakin don batason sake Bata Mata rai.

 

 

Wankan tayi da ruwan dumi sosai data had’a mata,ta fito Zama tayi a bakin katifar Tata kallo mama data dau uniform nata jikekken ta fita dashi kallon kayan data aje Mata tayi, kayan sanyine ta Sanya riga da wando manya manya sai hula duk abin Nan datake gabaki d’aya jikinta a sake yake cikin sanyi take kome nata tana gama sanyawa ta hau katifar Tata ta kwanta tare dajan bargo ta lulluba duk yunwar da takeji kafun a tashi school ta nemesa ta rasa.

 

 

Mikewa tayi da Sauri Jin muryar Bobbon ta Yana nufo dakin nata cikin holo sosai Yana cewa”Ina take Yar kwal uba watoh sai yanzun ta dawo kenan wallahi yau yarinyar Nan zata gamu dani tashi tayi ta zauna cikin bugawar zuciya bankado kofar yayi ya shigo kana cikin bala’i ya Soma zazzage Mata ruwan bala’i ta Inda yake Shiga bata wajen yake fita ba harda cewa”wallahi kikayi tsiya daga yau kin daina zuwa makarantan kenan shegiyar yarinya kinason ki jawomin abin magana ki rasa wa zakina bi sai wannan yaro Aliyu tunda baison ki Dole ne”?

 

 

 

Da Sauri mama ta shigo dakin nasu kana ta kalli bobbo dake ta masifa cikin sanyin rai yace”haba malam baka ga yanda gidan yayi shuru ba ga sanyi duk maganar da kake ana Jinka hakan fa bai Kamata ba,wani malla Mata harara yayi kana yace”eh Dole ai nayi shuru dayake bake Kika haifamin ita ba dole kina fadamin nayi shuru ta lalace,maganar mutane Kuma wannan sai suyi tayi akwai ubanda nake tsoro a gidan Nan ne”?shuru mama tayi sai hawaye daya cika Mata Ido ta rasa meyasa kullum malam baida abin Mata gori irin na haihuwa Kamar ita ta Hana kanta haihuwar.

 

 

Cigaba da masifa yayi dan kansa yayi shuru tare da barin dakin ita dai beenteei har lokacin zaune take tana dai binsa da kallo ne cikin alhinin tsoro amma Sam fuskar ta babu alamun digon bacin Rai Wanda zai matukar bawa Wanda bai santa ba mamaki,aje kulan hannunta mama tayi kana ta fita,mikewa benteei tayi a hankali ta jawo kulan Kan katifar tata budewa tayi,cinkafa ne dafa duka da manja cukalin dake ciki ta d’auka ta Soma cin abinta dan daidai taci ta rufe kulan kana ta d’au pure water dake gefen katifarta laida d’aya tasha ta Miki ta rufe kofarta da sakata ta kwanta tsabar tsananin sanyi da akeyi.

 

 

 

*************

Washe gari da asuba kasa mikewa tayi saboda tsananin ciwon Kai daya rufeta na zazzafar mura daya Kamata idanunta biyu amma sai juye juye take ta rasa meke Mata dadi tanaji har aka shiga sallah Bata iya mikewa ba 6:00am taji ana Bugun kofar Wanda tasan babu Wanda zaiyi sai mama tunda sunsan duk safiya sai ta gaidasu in dai har lafiyarta klau,daker ta iya mikewa ganin sai cigaba da bugun kofar ake,hannu tasa ta ja sakatan baya tare da komawa jikin ginin dakin ta lafe tana maida numfashi daker har kirjinta na amsawa tsabar shakewar da muran ya Mata,zaro Ido mama tayi lokacin da ta karaso cikin dakin da toshinta ta haska taga halin da benteein ke ciki da Sauri tace……………*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08184453785 tare da shaidan biyan ki*

[

*MUSAYAR ZUCIYA*

~ Na ~

 

*Rukayya Ibrahim*

 

 

 

Page 3

 

Hararan ta mama tayi tare da amsawa,karasowa tayi ta zauna akan kujeran da mamar ke zaune akai tare da Dan kwanciya tasa kanta akan cinyar mamar kana tace”mama dan Allah kiyi hakuri nasan ban kyauta Miki ba nasan bobbo zaiga laifi ki kiyi hakuri”haba beentu kullum magana daya dai magana d’aya dai a gidan Nan indai har da gaske kike ai da bazaki Kara Koh kallon yaron Nan, Aliyu sau biyu ba wallahi soyayyar Nan dolece tunda kowa yasan kina sonsa shi Kuma baya sonki ki hakura Mana”?

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Kwab’a fuska beentie tayi kana tace”haba mama wayace Miki baya Sona kunedai kawai kuke ganin hakan amma wallahi Yana Sona”ikon Allah rufemun Baki ShaShaSha Wance batasan Inda yake Mata ciwo ba Kinga mikema kibar min falo kafun kisa Raina ya baci a banxa, yanzun Nan na nad’a Miki na jaki”mikewa tayi a hankali ta fita a falon nasu tsayawa tayi akan dakali tana hangan kofar su Dr, ta tabbatar war haka ya dawo aiki kenan Kuma a ka’idan sa daga ya dawo aiki Zama yake a gida sai weekend yake dan fita, murmushi tayi da Sauri ta shiga dakin nata kulan data gama cin abinci ta d’auka da Sauri tasa hijab nata ta nufi part nasun.

 

 

Tafiya ce Mai dan tsawo kafun ta doshi wani kayatancen part Wanda mutum bazai taba tsammanin akwai irin sa a cikin gidan ba kofar an kewaye sa an Sanya wani gate na karfe yanda duk Yan gidan babu Mai iya hangen abinda ke wakana a bangaren nasu hannu tasa ta bude kofar tare da kusa kanta cikin haraban nasu,babu kowa a haraban gidan sai shuke-shuke da aka kawata wajen dashi kofar su ta nufa kana tasa hannu ta bude kofar vakinta dauke da sallama.

 

 

 

Hajiya dake zaune a falon hannunta dauke da remote tana kokarin canja tashine ta amsa Mata”ah ah waalaikumu Salam Fatima kece a cikin sanyin nan”dan sunkuyar da Kai tayi tace”eh wallahi nice hajiya mun wuni lafiya”?lafiya klau Fatima kwana biyu tun jiya Banga idonki ba nace Koh jikin ne gashi na tambaye yayan su wai.shima Bai sani ba,gashi yau baije aiki ba nama rasa uban me yake damunsa ne oho, sai yashiga ya fita na rasa me yake nema”murmushi beentie tayi kana tace “wallahi Hajiya ban d’an ji Dadi bane shiyasa yanzun ma na kawo kula ne”ikon Allah wannan ba kular dana sama Aliyu abinci bane”eh itace mama shiyasa na kawo Miki dashi”ok toh shigar da ita kitchen”mekewa tayi cikin kwarin jiki ta shige kitchen in tarin wanke wanken data gani ta Fara wankewa,wankesu tayi tas ta share kitchen in tana cikin mopping saiga hajiya ta shigo cikin kitchen in tare da rike baki”haba Fatima mezan gani haka ya ke da Baki da lafiya Zaki buge da aikace aikace?

 

 

 

“Babu kome nama kusa gamawa”ah ah aje aikin Nan maza ki fice a kitchen Nan kinjima ana kiran mangariba saiki shiga dakin su Aisha kiyi sallah don Suma tunda Suka dawo makaranta Basu fito ba”?toh hajiya tace ta aje sandan a hankali tad’au hijab nata dake saman kofa ta Sanya kanta a kasa ta fice a kitchen in da Ido hajya ta bita tare da girgixa Kai don yarinyar tana matukar Bata tausayi wallahi,dakin su Aisha beentie ta shiga dukan su Suna bacci ba tare data tadasu ba tayi alwala tayi sallah kana ta fito Tama hajiya sallama tace zata tafi duk yanda hajiya taso ta saya taci abinci Amma Ina tace itakam a koshe take.

 

 

 

Ta fito daga bangaren nasu sukayi kicibis dashi amma kamar Bai santa ba haka ya ratsata ya wuce abinsa,jikinta a mace haka ta Isa kofarsu ta samu mama a tsaye a bakin kofa tana binta da mugun kallo hartazo ta shige dakin ta ta kwanta,bayan ta canja suturan dake jikinta.

 

 

 

Washe gari da safe tana tashi bayan tayi wanka mama ta kirata Kamar kullum ta dauke abincin karinta na safiya taci, uniform ta Sanya kana tama mama sallahma anan take tambayar ta Ina jakanta? tace ta mantashi a gidan su sareena itadai mama Bata Kara magana ba sai Ido data Rakata dashi,a hankali ta ringa takawa duk juyawar da zatayi sai sun had’a Ido da mama don so take mama ta shiga daki ta,ta samu taje part nasu Dr ta karbi jakanta.

 

 

 

Fitowa kofar gida tayi tana jiran Dr don tasan warhaka Bai fita ba gashi hankalin ta a Tashe yake don sai yanzun ta tuna assignment inda aka basu za’a Yi summit yau Kuma ita Koh assignment in ma batayi ba ta shiga uku,tayi minutes 10 a wajen kafun ta hango sareena da uniform tana tinkaro ta”Kee beentie mekika tsaya kike jira bazaki Isa gidan namu ki jirani ba”mtwss wallahi sareena Dr nake jira”wani mugun tsaki sareena ta sake cikin haushi tace”waike wace irin Mara zuciya ne Wai Dan Allah”?mikewa beentie tayi tace “Kinga Dan Allah ki shafamin lafiya jakata ne a hannun sa tun shekaran jiya”jakarki?karkicemin bakiyi assignment in ba”?

See also  Yayi min illa Hausa Novel Complete

 

 

“Wallahi banyi ba sareena amma ai Zaki tsammin Koh”?uhmmm ke Kinga tafiya ta sai kiyita Zama ki jirasa Kuma wallahi bazan Baki assignment Ina ki copy ba ki sani a matsala “haka sareena ta tafi tabar beentie a zaune a kofar gida,can da dan jimawa saiga Aisha kanwar Aliyu zata tafi makaranta anan beentie taji ashema tun asuba Dr ya fita an Masa Kiran gaggawa xaima wata operation,jiki a sanyaye ta tare Keke ta nufi clinic nasu anan ma Bata samu ganin Saba sai kusan 10:30 Yana fitowa kuwa jakanta ya jefo Mata tare da Mata gargadin kada ta kuskura ta tako clinic innan again in ba haka ba ranta xaiyi mummunan baci”

 

 

 

tana Isa makaranta tayi missing na lecture har an shiga second xama tayi itama tana kallon yanda dalibai ke harhada assignment nasu zasu Kai sunkuyar da kanta tayi tana hawaye tunawa da tayi assignment in shine CA su,aje paper da karfi sareena tayi a gaban ta ba tare da tayi magana ba ta koma ta zauna,bude takardan tayi da Sauri ganin assignment inne da answer sa cikin farin ciki ta bude Jakarta da Sauri tasa hannu zata dauko littattafanta sai Kuma ta tsaya Jin ta taba IPO paper da Sauri ta zaro sa tare da zare Ido ganin tsararrun rubutune masu d’aukar hankali aka xuba akan paper,zare Ido tayi ganin assignment nata aka Mata gashi an cika paper gaba da bawa.

 

 

 

 

Dadine ya kasheta da Sauri ta mike taje tayi summit ba tare data cewa sareena kome ba Wance ta bita da Ido tana mamakin yaushe ta kammala copy Wanda ta Bata,d’aukar na sareenan tayi taje ta sameta kana tace”ba gashi ba innace Yana Sona ku Kama zagina ba gashi Dr yamin assignment nawa ma”wani banzan kallo na makaryaciya sareena ta Mana tare da kwace abinta Bata kulata ba itama beentie zamanta tayi ganin lecturern su ya shigo.

 

 

 

 

 

*********************

London

Zare glass in idon sa yayi a hankali tare da kallon agogon hannun sa ganin 12:50 yayi yasa sa bude kular sa spoon yasa ya Soma iban abincin ba tare da Yama kowa tayi ba ya Suma ci sanin da yayi tayin bashi da wani amfani sai wulakanci,Yana kammala ci ya rife sauran tare da bude Jakarsa ya dauko Goran ruwan sa yasha kana ya kashe computer dake gabansa,ya mike ya fita a hall in nufar waje yayi daidai Inda ya Saba alwala wajen wani pampor dake waje alwala yayi,wani waje daya kebewa Kansa Yana ibadarsa a wajen sallaya ya shimfida ya tada sallarsa a nutse Yana kammala wa yayi adduar sa ya shafa kana ya koma ciki ya cigaba da ayyukan sa.

 

 

 

 

5:00 Suka tashi daga aiki jakar sa ya d’auka bayan kowa dake hall in ya fita ya rage saura shi kad’an sa Kamar kullum shine yake bayan fita a department nasu,Yana rataye da jakansa sai wayarsa da yake daddan nawa gabaki d’aya ya maida hankalin sa ga wayar kawai yaji an bangajesa da karfi Saida yayi tagaltagal xai Fadi sai Kuma yaji an rike hannun sa,kallon Wanda ya bangajesan yayi wani abokin aikin same, dan murmushi yayi sai Kuma ya zare Ido hade da rumtsatsu da Sauri ganin ya sakesa Aiko ya tafi da karfi ya Fadi a kasa ihu ya sake Jin wani irin bugu da bayan sa yayi a kasar wajen sai ga hawaye shaaaa a idanun sa Yana kuka Mara Sauti,”,kad’an ma ka gani”yace Masa kana ya ratsashi ya wuce”Raheel Saida yafi kusan minutes 20 a wajen kafun ya mike a hankali jakansa da kulansa ya d’auka ya Soma tafiya a hankali har lokacin Bai daina hawaye ba.

 

 

 

Bus stop ya nufa da kafa dayake baida wani Nisa da company da yake aiki,xama yayi a Kan bench dake wajen kasancewa babu mutane sosai da yake yammace duk yawanci maaikata da dalibai sun tashi da jimawa,wayarsa ya d’auka Yana dubawa duk ya farfashe kuka ya sake fashewa dashi don ya tsani screen in wayarsa ta fashe gashi kullum lallaba wayar yake baison kome ya samesa gashi yau Rana daya wani ya Masa ragaraga,wani tsohon bature ne tun daga nesa yake ta al’ajabin meke damun wannan katon yake kuka.

 

 

 

Zama yayi a gefen sa Yana tambayar sa meke damun sa ne, kin amsa Masa yayi sai kuka yake daker dai baturen ya samu Raheel ya Masa bayani Wai screen in wayarsa ce ta fashe,Baki baturen ya wangale cikin alajabi Yana kallon wayar in sai Kuma ya kurawa Raheel Ido Yana nazarin Anya wannan ba mahaukaci bane kuwa sai Kuma ya kalli ID card nasa Yana al’ajabin wannan yaro ke aiki a babban company haka, dakir dai ya samu Raheel yayi shuru tare da Masa kwatancen Inda ake gyaran waya a wani babban mall cikin murna ya mike tare da d’aukar jakan sa ya nufi Inda mutumin ya Masa kwatance.

 

 

 

 

 

Babban mall ne Mai kusan dauke da Hawa 10 duka na Saida wayoyi da gyaran system ne ya samu an gyara Masa waya akan idanun sa an cire glass in an Sanya sabo cikin murna ya zare card nasa ya biya kudin gyaran zuwa lokacin 6 na yamma yayi har duhu ya Soma lullube gari don shaguna ma yawanci duk an rurrufesu daker ya samu daman Mai gyaran wayar ya gyara Masa don daman tashi xaiyi, wani super market ya shiga yayi sayayya su ice cream dasu chocolate ya nufi gida………………………………*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08184453785 tare da shaidan biyan ki*

 

 

 

Gaisuwa ta musamman gareki Haleema freebook*

 

MUSAYAR ZUCIYA*

~ Na ~

 

*Rukayya Ibrahim*

 

Page 2

 

Subhanallah beentie lafiya kuwa mexan gani haka,kuka ta Dan fashe dashi amma ta kasa amsa Mata da Sauri ta shigo dakin Kamata tayi ta aje akan shimfida da Sauri ta fita a dakin Jin turirin da jikinta keyi, ba’a Jima ba sai gata ta dawo cikin dan rashin hankali tana cewa”Kinga tashi mu tafi asibiti malam ya koma tun asuban farko don haka ki tashi muje asibiti”dan kallon ta beentie tayi ganin yanda duk Hankalin ta yake a tashe tace”mama ki kwantar da hankalin ki ba wani Abu bane jikin baiyi tsananin ba ki kwantar da hankalin ki dan ciwon Kaine da mura chemist ma Zaki ji ki karbomin maganin mura”

 

 

 

Ah ah ban Isa ba malam kudi ya aje saboda irin wannan Rana in dai xai tafi saiya aje kudin kula da lafiyarki kinsan Kuma Dr yace kar ki Fara ciwo a kaiki chemist,maza taso muje”mikewa tayi ta taimaka Mata ta Sanya hijab akan wando da rigan sanyin,Sanya yakalmin ta tayi mama na rike Mata hannu Suka fito Suka nufi gate na gidan,dayake safiya ce duk matan gidan sun fiffito Koh Wance ta Kama aikin ta sai sannu suke mata.

 

 

Hannu mama tasa zata bude gate in sai Kuma tadan koma baya kad’an Jin ana kokarin budowa ta waje,kanshin sane ya buge hancin beentie da Sauri ta daga macecen idanunta ta zubawa gate in,turo kofar yayi bakin sa dauke da sallama sanye yake da jallabiya fari Kal da gani masjid ya fito dan tsayawa yayi ya zuba musu ido,hade fuska sosai mama tayi kana tace malam ka bamu hanya Mana”?

 

 

Dan rusu nawa yayi Yana gaidata amsawa tayi fuska a hade tace”lafiya nace abamu hanya Koh”? Mama Bata da lafiya ne”ai kafun kowa sani”dan Allah mama kiyi hakuri in babu damuwa muje na dubata Naga Kamar jikin baiyi tsanani sosai ba, Kuma kinsan Bai dace akaita chemist ba”?

 

 

Harta bude Baki zatayi magana sai Kuma da Sauri beentie tace”ayya mama ki Bari ya dubanin mana”tsaki kawai mama tayi ranta a bace ta saketa ta koma cikin gidan ta barsu anan a tsaye,takawa yayi yabi mama a baya itama beentie daker ta iya Kai kanta flat nasu matan gidan Kan da Ido Suka bisu Suna tattabe baki wasu Kam kasa hakuri sukayi har Saida suka tofa.

 

 

 

Ya rigata Isa kofar tasu itakam mama daya kofar ta shiga shi Kuma Yana tsaye a flat nasun ya zuba Mata Ido Yana kallon yanda take tahowa daker,kofar dakin nata ya Kama ya bude tare da shiga ciki ganin ta karaso daker tahau floor in dakin ta visa ciki,Zama tayi a bakin gadon tana maida numfashi tare dasa hannu ta zare hijab nata ta aje a gafe,kauda fuskar sa yayi har lokacin a hade kana yace”Banda mura da zazzabi Ina Kuma ke Miki ciwo”?

 

 

 

Kwanciya tayi ta zame hulan sanyin kanta yalwacecen gashin kanta Mai tsawo da laushi bakikirim Suka zuba har gadon bayan ta,duk da ba ita yake kallo ba hankalin sa nakam wayarsa hakan Bai hanata Masa pointing in kanta ba,a hankali tace da kaina”meyasa Kika shiga ruwa bayan kinsan matsalar ki”hararan sa tayi cikin yamutsa fuska tace”toh ba Kai bane”Bai saurare taba ya mike tsaye ya fita a dakin,baijima ba sai gasa ya dawo hannun sa dauke da first Aid box,kallon ta yayi kana ya ce”yaushe ne rabonki dashan magangunan ki”?

See also  A wani gari hausa novel complete

 

 

Shuru ta Masa sai kallon sa datake tayi tunda ya shigon girgixa Kai yayi cikin takaici ya nufi wajen drower dake gefe ya bude maganguna ya gani birjib da gani ma ba shansu ake ba,daukosu yayi yazo ya babbala Mata kana ya dau ruwan pure water ya Mika Mata Saida yayi magana kafun ta amsa Tasha tana babbata fuska Koh minutes biyu ba’a Yi ba dasha ta mike da gudu tayi cikin toilet tana kwarara amai,cikin haushi ya bita da kallo kana ya gyada Kai laidan ruwa ya zaro kana ya makala a jikin kusan dake kusa da katifar ta Wanda hakan ya nuna an saba da saka Mata kenan,tana fitowa tazo ta kwanta tare da lumshe Ido tana maida numfashi,hannun sa yasa a hankali ya Kama hannun ta Mai bala’in laushi da tsantsi ya rike da Sauri ta zabura tana kallon sa shikam Yi yayi Kamar vaisan da ita ba Yana kiciniyar sa Mata ruwa,Yana kammalawa ya aje Mata sauran maganin kana ya fita a dakin saura kiris suyi Karo da sareena kauda fuska tayi ta ratsashi ta wuce ba tare data Koh gaidashi ba,tsaki kawai yaja ya nufi part nasu.

 

 

 

 

************

LONDON

Bude idanunsa yayi a hankali masu matukar girma da sheki sakamakon kukan Alerm daya ratsa kunnen sa, kyafkyafta gashin idanun nasa yayi masu matukar yawa da daukar hankali,dan rumtsa idon yayi kad’an kana ya budesu gabaki d’aya Yana Mai kallon saman dakin yadan Jima kad’an kafun ya mike zaune yasa hannu ya kashe Alerm in, wow Masha Allah matashin balarabe ne mai jini a jika duk da a zaune yake hakan Bai Hana gane tsawon da Allah ya Masa va,fuskar sa cikin rashin fara’a ya zura fararen kafarsa a kasan tiles in dake shimfide a tsakar dakin a hankali ya mike ya Soma takawa a hankali Kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki,sanye yake da kayan bacci wando da riga, toilet ya Shiga kana ya wuce side in brush ya zaro da maclen,sai Kuma ya kalli madubin dake makale a jikin ginin,sosai ya kurawa farar fuskar sa idanu Yana brushing in Yana kallon fuskar sa.

 

 

Wanka yayi ya fito daure da guntun towel sai karami dake hannun sa Yana goge suman kansa dashi,shiryawa yayi cikin wasu arnan wando da riga na company Gucci yayi stoken sai canvas maikyau ya daura agogo a tsintsiyar hannun sa sai turare daya fashewa jikinsa harya Kama handle na kofa zai bude sai Kuma ya dawo yazo ya dau wayarsa Kiran iphone dake bedside drowern sa da jakansa dake gefe,kana yafito a dakin a hankali take sauka daga Kan step in kansa a kasa Kamar Mai tunani.

 

 

 

 

Mikewa tayi ta tsaye ganin fitowar Raheel harya karaso yazo zai zauna akan 1seater dake cikin kayaceccen falon kawai by mistake kafarsa ta bugu da katakon kujeran ji kake Kau ihu yasa da karfi tare da dukawa Yana kuka Yana kallon yatsar tasa da jini ya Soma bulbula,da gudu yar tsohowar ta Matsu hade da Kama yatsan NASA cikin turanci tana kallon Raheel in sai Kuma da Sauri tabar falon sai gata ta dawo da akwatin gaggawa a hannun ta Kama kafar tasa tayi,da gudu ya mike tare da kwala Kara Jin wani dan zafi a yatsar kafarsa da gudu ya nufi upstairs itama ta Mara Masa baya tare ta rokon sa akan ya tsaya amma Ina yaki saurare ta ba har Saida ya Isa karshen step in kafarsa ta harde sai gashinan ya xubo da gudu Yana gangarowa,ya salam shine abinda tace da Sauri ta tarosa saura kad’an yaci da Baki,kamo hannun sa tayi.yana tirjewa Yana kome ta jasa har falo aje sa tayi tare da zare Masa ido tace”karka kuskura ka Kara tashi”tana karasa maganar ta mike sai gata ta dawo da tiren a hannun sa jawo center table Inda ke falon tayi zuwa gaban sa kana ta aje tiren abinci ne da abinsha aka jera a ciki Mai Rai da lafiya bubbudewa tayi kana ta kalli ubangidan nata har lokacin Bai kalle Koh Inda take ba sai hawaye da yake.

 

 

 

Cikin maganar dolaye yace”nikam bazanci ba”spoon kawai ta d’auka Bata kulasa ba ta ibi breakfast in ta Soma basa da kanta ba musu ya karba ya Soma ci Saida taga ya Fara bawa abincin muhimmanci, kafun ta daina basa ya koma ci da Kansa ita Kuma ta gyara Masa yatsar kafar tasa,Yana gama breakfast in mikewa yayi yadau jakan aikin sa ya nufi kofa ba tare daya saurare maganar da take Masa ba akan ya tsaya,da Dan Sauri tadau lunch box nasa tabi bayansa daker ta samu ya karba.

 

 

 

Yana fita daga gidan rataye da jakansa yayinda hannunsa dauke da da kulan abinci a kallah xaikai shekara 30 Amma hakan bazai Hana daga mutum ya d’aga Ido ya gansa ya kasa gane lalurar dake tattare dashi ba na rashin cikekken lafiya,da yake safiya ce kowa Yana had’a hadan aiki wasu makaranta hakan yasa Koh Wace bus stop take cike da masu jiran abin hawa wasu Kuma da abin hawan su, tsayawa yayi a bus stop Bai wani Jima ba bus dake d’aukar sa zuwa wajen aiki ya tsaya,ayari yabi Shima ya shiga ciki.

 

 

 

8:00am cicip ya Isa company su ID card nasa ya zaro a jaka ya makala a wuyarsa kana ya shige ciki,tunda ya shiga abokan aikin sa turawa Suka Soma tsokanarsa shidai shuru yayi Kansa a kasa har ya Iso Kan table nasa don daman babban hall ne na maaikatan Mai dauke da table kusan talatin saidai an ma kowa tsakani da Dan uwansa duk da hakan Bai Hana suga juna ba jawo kujeran sa yayi zai zauna daya daga cikin makwantansa yasa hannu yaja kujeran baya,shi Kuma a rashin sani ya zauna sai ji akai Tim ya zube a kasa dariya da yawan maaikatan suka fashe dashi daga maza har Mata shikam Kansa na kasa ya kasa Koh dago Kai,tasowa wata baturiya dake gefen baya tayi Wance take kallon duk abinda ke faruwa a hankali tasa hannu ta d’au jakan nasa da kula ta aje Masa akan table in nasa a hankali ta Kama hannun sa ta taimaka Masa ya mike.

 

 

Rai a bace ta Soma magana”Amma dai Baku da Imani menene wannan mutumi ya tsare muku da Zaku sashi a gaba Koh don kun gansa Yana aiki anan matsayin sa na African,Koh saboda lalurar da yake dashi karfa ku manta kaf company nan babu Wanda yake aje Mana bayanan sirri da kular Mana da duk wani information na kammani Kamar sa tunda aka daukesa aiki haryau ba’a taba samun Wanda ya datse Mana na’urorin mu ba Koh hacking,Kuma duk Nan nasan babu Kamar sa,don hakan duk Wanda ya Kara Masa rashin da’a maganar Nan zata tafi wajen shugaban company don Shima mutum ne Kamar kowa”

 

 

 

“No Alena basai yakai ga hakan ba ki Bari kawai na yafe musu banason tashin hankali”tsaki kawai tayi ta juya ta tafi yayin da sauran Suka ringa kananun maganganu,shidai Zama yayi ya Sanya glass fari a idanun sa kana ya natsu ya Soma aikin sa cikin kwanciyar hankali Kamar babu abinda aka Masa.

 

 

 

 

****************

NIGERIA

Cikin bacci taji mutsin mutun kusa da ita kana Kuma Yana taba Mata hannu bude Ido tayi sukayi Ido hudu dashi,murmushi ta Masa da Sauri ya maka Mata harara ya kauda fuskar sa tare da zare Mata ruwan,mikewa tayi ta zauna har lokacin kallon sa take,mikewa yayi ya tsaya tare dasa hannu a aljuhu cikin gadara yace”ki tashi kiyi sallolin da ake binki kana kici abinci Kisha magani Kisha magani kinji dai na gaya Miki yana Gama maganar ya fita a dakin Bai saurare amsar taba,Yana fita ta mike wanka tayi don Bata da tsarki tazo ta zauna tare da bude kulan data gani a kusa da katifarta,firfisun kazane yasha kayan hade Wanda hakan ya tabbatar Mata ba abincin mama bane d’aukar spoon tayi ta Soma Iba tana ci hankalinta a kwance.

 

 

 

Jin jikin nata da sauki ya sata mikewa ta fito a dakin nata kallon tsakiyar gidan nasu tayi da yake yammane kowa na had’a girkin dare musamman masu madafa a waje irin su,kallon kitchen in mama tayi ganin Bata ciki yasata Kama kofar falon nasu ta shiga,zaune mama take akan kujera fuskarta babu walwala sam,karasowa ciki beentie tayi da sallama,d’aga Ido tayi ta kallleta kana ta cigaba da abinda take ba tare data amsa sallamar ba”haba mama babu kyau musulmi Yama Dan uwan sa sallama Amma yaki amsawa fa”…………. ……….*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08184453785 tare da shaidan biyan ki*

 

 

1 thought on “Musayar Zuciya Hausa Novels”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top