My Bestie’s Husband Hausa Novels

My Bestie’s Husband Hausa Novels

 

 

 

 

 

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

[Page 1 to 2
Yanayi ne me sanyi da kwantar da hankalin duk Wanda zuciyarsa ke cikin nutsuwa inda zai kasance matashin hankalin duk wanda nutsuwa tayi qaura cikin rayuwarsa, yaf yaf yaf ruwan yake sauka a saman manyan motoci da suka parkar a harabar Event center din da akayiwa laqabi da.

*Beautiful bridal*
Bude qofofin akayi a tare Kuma lkc daya wasu zafafan kyawawan yammata suka fara fitowa a jere a gefe guda Kuma sautin sassanyar iska da kida me zama a zuciya ya qawata gurin da yasamu qawatuwa da wasu kyawawan manyan flowers abindai sai Wanda yagani.

Salon kidanne ya sauya lkcn da wata arniyar mota ta samu matsuguni aka bude mawa wadanda ke cikin motar suka fito yammatane guda biyu kyawawa cikin shigar da take nuna amare ne sanye suke da farar wadding gown data karbi jikinsu, tare Kuma a lkc daya Suma angwayen suka  fito a tasu motar suka nufosu inda suke tsaye kansu a lullube.

Tahowa angwayen sukeyi inda sukuma amaren suke tsaye qiqam bude musu fuskar akayi inda duk Wanda ke gurin yayi mutuwar tsaye suka zuba musu ido dukkansu kyawawane na kwatance daya farace tas kamar bargonta zai fito inda dayar ta kasance wankan tarwada duk da hasken ya rinjayi baqin da ya sirka fatarta.

Dawowa sukayi a tare suka sauke idanunsu aka cikin na angwayen wankan tarwadar ce ta saki wani murmushi ta Kama hannun farar ta kamo hannun daya cikin angwayen ta saqala a nata ta bude Dan qaramin bakinta tace “Hml Mr Ja’afar Wakil”

Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke tare da qoqarin tattaro nutsuwarsa ya hada guri guda ya kama hannun amaryar tasa ya janyota jikinsa har yanzu idonsa nakan na dayar budurwar ya bude bakinsa cikin sanyin yanayi yace “koda bantaba ganinki ba kamanni da siffa da yanayin sanyin halitta ya bayyanamin waceceke tabbas tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya halicci kyawawa guda biyu Kuma ya sanyasu suka zama aminan juna…”

Dariya wanda yake babban aminin angon yayi yace “Rafi’ah Nasir Darazau kenan aminiyar arziqi wannan itace remote control din matarka aduk lkcn data rikice maka to ka nemo Rafi’ah zata daidaita maka ita cikin sauqi” har yanzu idon Ja’afar akan Rafi’ah yake inda har ta fara qosawa da kallonsa ta juya ta dubi dayan tace.

“Muhseen kodai abokinka yayi ciwon makanta ne Bestie mijinki ya taba samun eyes issues ne” hannu takai zata janyota ta janye da sauri tana murmushi yayi saurin riqota yace “kinga Ni’imah qyaleta zamu rama ne danma ta samu an kalleta shine take wani jin dadi?” Muhseen ne yace “abin mamaki miskilai biyu ku mu qarasa fili nasan mu ake jira a fara program”

Read Inada Hujja Hausa Novels

Takawa sukayi muhseen na gefen Ja’afar ita Kuma na gefen Ni’imah suka Isa cikin Hall din inda gurin ya kaure da tafi da sowar mutane a haka suka qarasa ango da amarya suka zauna MC ya fara aikinsa bayan kowa ya nutsane ya gabatar da Muhseen da Rafi’ah a matsayin wadanda zasu bada tarihin amarya da ango.

Rafi’ah ya fara bawa Abin mgn ta karba cikin qwarewa tayi sallama tare dayiwa kowa godiya da nuna farin cikinta da zuwan wannan rana ta farane da gabatar da kanta a matsayinta na best friend ta amarya sannan tabada tarihin amarya kamar yanda aka buqata sannan  tabada tarihin amintarsu anan ne zuciyarta ta karye hawaye ya fara zuba a idonta inda take cewa.

“Tabbas burin kowacce mace a rayuwa shine samun masoyi na haqiqa amatsayin miji duk da yau itace rana ta farko dana fara ganin Mijin Aminiyata na yaba da zabinta Kuma nayiwa Allah godiya daya kasance a matsayin mijinta Ja’afar Ina cikin wani yanayi na quncin zuciya saboda zan fara rayuwar kadaici ka rabani da bestie na  munsan dama wannan ranar zatazo amma bamu shirya yanda zamu dauketa ba inayi maka fatan nasara da addu’ar riqemin Bestie na amana don Allah bayan matsayin miji da ubangiji ya baka ka maye Mata gurbina a matsayin amini kada kabarta tayi kuka ko kewar rashina duk mace haka ta gada sai haquri haka Allah ya tsara mana mubar iyayenmu mubar yan’uwanmu da qawayenmu mu tafi sabuwar rayuwa da itace zata zamo hanyar samun tsiranmu duniya da gobe kiyama…..”

Muryarta ce ta fara sarqewa da gaske tayi qoqari domin tun a harafin farko kuka yakeson qwace Mata inda gurin ya dauki kabbara da tafi a lkc daya, bawai don ta rasa abin fadaba saidon ganin qawar tata itama tana kuka yasata miqawa MC din abin mgnr  ta nufi step din zata sauka kasancewar duk wata nutsuwarta ta qaura sun dade suna kukan zuwan wannan ranar Amma Basu tabajin dacinta kamar yau datazo ba.

Jitayi an riqo hannunta ta baya ta juya da sauri idonta na shararar da hawaye ga mamakinta sai taga Mijin aminiyar tata ne murmushi ta qaqaro ta janye hannunta ta bude bakinta tace “karka damu Ja’afar bakayi laifiba hakan shine cikar gatan kowacce ya mace munsan da zuwanta rashin hankaline yasa muka kasa shiryawa zuwan nata…”
Fakar idon mutane yayi ya dora hannunsa a bakinta yana me qare Mata kallo yanajin bugun zuciyarsa daya fara tun farkon haduwarsu yana qaruwa yace “Nasani Rafi’ah amma Ina Zaki?” Janyewa ta kumayi tana saita qoqarin bashi space kasancewar qarancin taqin tsakanisu yayi yawa tace “zan zanje na sallami baqinmu ne abokan karatunmu”

Jinjina Kai yayi yace “Ni’imah tace kince idan kika kawota tafiya zakiyi why?” Shiru tayi tanaci gaba da jan zuciya yayi murmushi yana ayyana abubuwa da yawa a ransa yace “kiyi har kada ki tafi ki jira a tashi mu tafi mu tare mu kaiku gda please kada kiqi kinji?”

Daga masa Kai tayi ta juya da sauri saboda tagaji da gwama numfashi dashi binta yayi da kallo shikadai yasan me yake saqawa a ransa ya juya ya koma gurin zamansa ya kamo hannun Ni’imah yace “ta hqr daqyar qawarnan taki akwai wayo” murmushi tayi me hade da kuka tace “danma kaine tana ganin girmanka da bazata tsayaba kafaffiya ce akan ra’ayinta daqyar Dad ya rarrasheta tazo shima don ance ita zatayi history ne”

Numfashi yaja yace “tanada kyau….” Dariya Ni’imah tayi kadan tace “danma bata cikin nutsuwa ne shiyasa duk a hargitse take ko kwalliya taqiyi” da wannan akaci gaba da gabatar da dinner din duk wani motsi da Rafi’ah takeyi idon Ja’afar akanta bayako qiftawa hakanne yasa tasha jinin jikinta ta koma gefe tana caje kanta ko want abune yasa yake kallonta da bazai iya fada mataba

Ta jima tana qarewa kanta kallo a madubin motar kawai saiji tayi ance Mata “sannu” a tsorace ta juya kuma a firgice hakan yasata karo dashi tayi taga taga zata fadi yayi saurin tarota ta daidaita a qirjinsa yaja wata ajiyar zuciya tare da dora kansa saman kanta ya shaqi qamshin gashinta, jin yasa hannu ya qara shigar da ita jikinsa tayi saurin janyewa don ganin waye.
Ja tayi da baya da sauri tare da cewa “lfy?” Duk da baiji dadin tambayar ba haka ya hadiye ya shafa kansa yace “ankirani a waya na taso don amsawa kawai na hangoki so nayi tunanin kukan kikaci gaba dayi shiyasa na qaraso am sorry please na tsorataki ko?” Numfashi taja ta furzar tace “ok ka koma gurin Bestie bani bakai zata shiga damuwa”

Binta yayi da kallo yace “ke Kuma kinason zama a damuwa ko?” Wani kallo tayi masa daya sanya lakar jikinsa tsinkewa tace “ita ce yake wajibi a gurinka kayi qoqarin gusar nata da damuwa nima inada me gusarmin da tawa shi nake Shirin Kira ma yanzu kaje na gde da kulawa..]

KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇👇👇

 

Preview: [DOWNLOAD COMPLETE BOOK 👇]
 

Name: My Bestie’s Husband
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: MYNOVELS.COM.NG
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books
Groups/Writers: Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: July, 2021

 

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.