Hausa Novels

Na fada So! (I fall in love)

: *NA FADA SO💘*

( _fall in love_) 

*Nuceeyluv😘*

1….

A hankali ta yaye labulen window dakin d take bcci tana dan lumshe ido a hankali alamar bccin be saketa ba ganin bata hango Abinda takeson gani yasa ta zuge glass din a hankali saidai dukda haka saida yayi Kara tsii…. Dan cije lips dinta tayi yayinda wata sassanyar iskar safiya ta sirnano ta kofofin ragar dake jikin window, sake lumshe ido tayi kafin ta bude su a nutse tarrr ta sauke su kan kyakkyawar fuskar sa wacce da ita take kwana take tashi a cikin birnin zuciyar ta, tafiya yake Mai daukar hankali da nutsuwa kokarin gyara tie dinsa yake dayan hannun sa rike da rigar coat dinsa yana makale da ita a wutsiyar hannu, fuskar sa gata Nan kadaran kadahan gashin kansa me kama Dana turawa sai walwali yake Kai da gani yasha gyara, har yanzu tana jikin window idonta ko kyaftawa bayayi har ya juya Baya izuwa wajen parking space, cikin jerin motocin dake jere a wajen ya nufi wata hadaddiya daga ciki a nutse ya bude motar ya Shiga ciki still ta jikin window tana kallon sa har yanzu, Sam besan Ana kallon nasa ba har ya gama fiddo da motar daga wajen cikin Wani irin slow kafin ya Karya kan motar a nutse ya nufi bakin gate, tun kafin ya Karasa har gateman ya bude Masa Dan haka yana isa ya fice daga gidan gaba1. Sauke ajiyar zuciya tayi a hankali tana sakin labulen data dage dazu, a nutse ta dawo da zaman ta kan gadon da take kwance zuciyar ta na harbawa da sauri2 bargonta ta jawo tana me lullube kanta da sauri sbd yadda hawaye ya fara cika mata ido tana Jan zuciya a hankali, ba komai yasata kukan ba sai yadda taji hankalin ta ya tashi, idan da sabo ya kamata ace ta saba amma inaa Sam ta kasa daurewa da irin wutar son da take yiwa 

Ya khaleed, ta sani sarai ko mutuwa zatayi bazata samu soyayyar shi ba bare ma akai ga zancen aure toh ita a wa? ‘yar karere ‘yar zaman agolanci? Wacce bata da kowa sai Allah sai Kuma mahaifiyar ta Ammi, ai Kai da gani tasan wutsiyar rak`umi tayi nesa da kasa, musamman idan akayi duba da yadda suke rayuwa a Wannan tafkeken gidan Wanda idan daga waje ka hango koda iya gate din gidan ne zaka san naira tayi kuka bare cikinsa Hakan zaisa mutum yayi tunanin Duk mahalukin dake ciki rayuwar jin dadi yake zallah, amma hausawa sun iya mgn da sukace kallon kitse akewa rogo Dan rayuwar ta da Ammi a gidan abin takura ne da ni ‘yasu. Karar bude kofar dakin da taji ne yasa tayi saurin goge Dan guntun hawayen daya sirnano ta can gefen idanun ta tana Kara shigewa bargo alamar Mai bcci, Ammi ce ta fara dukan gefen da take kwance tana kiran sunan ta, “kamla, kamla..” ta fadi Hakan a nutse, Dan mikar Karya kamla tayi tana yatsina fuska kamar gske Tace, “uhumm…” Ammi Tace, “yanzu kamla ace har bakwai ta taho baki tashi daga Wannan bccin asarar da kike ba?” Cikin yanayi na bccin Karya kamla Tace, “yanzun Nan zan tashi Ammi” Dan karamin tsaki Ammi tayi Tace, “kada ki sake na sake dawowa na ganki a kwance baki fito kin kama aiki ba” tana gama fadar haka ta juya, ture bargon kamla tayi zuciyar ta ba dadi tana dan mika a hankali ba komai yake bata mata rai ba sai Wannan tashin sassafen ace mutum shi ba Dan aiki ba amma kullum yana hanyar kitchen alhalin ga suntuma-suntuman ‘yan mata Nan a gidan kowacce saidai ta Mike kafa tana kwance ko danna waya mtwss.. da Wannan kunkunin ta Ida sauka Akan gadon tana me sanya dogon hijab dinta Akan kayan bccin ta. Koda ta fito ma gidan tsitt yake dake safiya ce mutanen gidan anata bcci sai masu aiki ne kawai ke Kai kawo Dan Karin kumallo, can tsakiyar su mama ladi ta hango Ammi Suna aiki tare, Dan kyabe baki tayi ta Karasa wajen tana gaishe su, bayan sun gaisa ta karbi aikin dankali tana barewa a nutse.

••••

Tun daga bakin gate din Access Bank security suke Sara Masa har yakai ga Shiga ainahin Inda zai sada shi da office dinsa matan dake ciki both muslim and christian suma suka mike Suna Girmama shi da kananun ma’aikata mazan dake kasan sa sun mike Dan Girmama shi, ko kadan be dubi Inda suke ba kamar yadda ya saba iya hannu kawai ya daga masu ya wuce Abinsa. “Hmmm…!” Wata daga ciki ta saki ajiyar zuciya, daga gefen ta wata Tace, “ke lpyrki zee?” Wacce tayi ajiyar zuciyar Tace, “bazaki gane ba salma amma Wlh *Chief Accountant* dinnan  yana tafiya da imani na sallon sa na daban ne Wallahi” Dan tsaki salma taja tana me Dan jin kishi kadan Dan itama ta fada so a Dan kule Tace, “sai kije ki fada masa” “wa ni? Rufamin asiri” tayi mgnr tana zama da sauri salma tadan harareta ta gefe tana tabe baki, daga can bangaren ma christian din sunata kus-kus kasa2 ba komai suke mgn akai ba saita Chief Accountant. 

Kwashe kulolin Kamla tayi tana kaiwa can dining area ita da hansai me aiki, saida suka gama komai suka tsaftace kafin suka baro kitchen din Ammi tun dazu ta wuce daki Dan itace da abinci amma koba ranar girkinta ba dole kamla ta fito ta taya masu aiki abinci Wannan dole ne. tana cikin tafiyar ta a nutse taji an jawo hijabin ta da sauri ta juya a razane tana kallon me Jan hijab din nata, Anty Sara ce rike da qugu tana kallon ta up and down Tace, “Kin manta aikin Dana saki ne tun jiya kike Shirin barin kitchen?”  Dukar da kai kamla tayi Tace, “Kiyi hakuri Anty so nake naje na canja kayan jikina sai nazo nayi maki girkin” “mtwss..” Anty Sara taja tsaki kafin Tace, “ki hanzarta Dan da wuri bakona zai iso daga Abuja Dan jirgi zai biyo” gyada Kai kamla tayi tana tabe baki kasa2 itadai Anty bazata daina karyar samari ba, “wuce ki tafi” Anty Sara ta katse shirun daya gifta Hakan yasa kamla ta juya da sauri tana tafiya yayinda Anty Sara ta bita da Wani matsayin kallon tsana.

*Ghen ghenn… Yess nuceeyluv is back💃🏻 tare da new novel dina NA FADA SO😍 nasan wasu zasu ce Ina cigaban K’ASAITA? K’ASAITA yana Nan Rashin comments dinku yasa na dakatar dashi, so Wannan ma idan naji shiru ba comment zan ja bakina na tsuke🤐😂😂 karku manta comments dinku shine karfin mu😍 yawan comment yawan typing Insha Allah💃🏻💃🏻💃🏻*

[

By 

*Nuceeyluv😘*

2….

Cikin sauri ta Karasa shiryawa tana tsane gashin kanta Dan yunwa takeji sosai tun safe take aiki kamar jaka ita data tashi da wuri ya kamata ace tayi Karin kumallon ta dawuri amma ace yanzu kusan 11:30 bata Karya ba sbd girkin da tayiwa Anty Sara na bakon ta, aje towel din da take matse Kai tayi gefe tana jawo plate din soyayyen dankali da Ammi ta kawo mata cikinta har wata ‘yar Kara yake sbd yunwa, ta debo kenan zata Kai baki aka banko kofar dakin nata a razane ta dago kanta zuciyar ta ce ta tsinke yayinda tayi arba da Mommy, hannun ta sai rawa yake ta kasa kaiwa cikin bakin bare ta aje, cikin fada2 Tace, “tashi yanzun Nan kije ki mikawa khaleed breakfast dinsa tun kafin ranki ya baci” Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci kamla a firgice Tace, “Ya khaleed kuma?” Mgnr ta fito mata batare data shirya ba sbd firgita, kankace ido mummy tayi Tace, “kinfi karfin Kai Masa ne? Ai a gidan Nan ma babu Wanda ya dace ya dinga Kai Masa abinci sama da ke” jikin kamla ne yahau rawa ta kasa furta komai mummy ta karaso wajen da take tana kwashe abincin gabanta Tace, “idan kin Kai Masa kizo ki karba” ta Ida mgnr tana wucewa, Wani siririn hawaye ne ya ziraro mata ta gefen idanu ta goge da sauri daidai lkcn Ammi ta shigo ta ganta a haka, Ammi Tace, “ke kuma meye haka naga lkci guda kin birkice?” Cikin sanyi kamla Ta zayyane wa Ammi Abinda mummy Tace mata, can kasan zuciyar Ammi taji tausayin ‘yar tata sosai kamar tayi kuka amma a Fili Tace, “toh kuma kaiwar shine abin tashin hankali kamla?” Kamla ta girgiza kai Tace, “haba Ammi kema fa shaida ce Duk gidan Nan babu Wanda ya khaleed ya tsana sama da ni ko kallo ban ishe shi ba toh ni kada naje ya wulakanta ni a gaban jama’a” dafa kanta Ammi tayi Tace, “Kiyi hakuri kamla kamar yadda a koda yaushe kike hakuri haka ma yanzu zakiyi banason ki maida karamin Abu babba tunda sunce ke zakije toh kije din ki kuma kiyaye Abinda bayaso ku rabu lafiya Insha Allahu babu Abinda zai maki” ajiyar zuciya kamla tayi tana duban Ammi idonta cike da kwalla Tace, “kuma yunwa nakeji Ammi” tayi mgnr a karye, kadan ya rage Ammi bata zubar da kwallar tausayin ‘yarta ba Dan haka ta mike da sauri tana kawar da kanta can gefe Tace, “tashi ki shirya ki sameni a parlo” ta Karasa mgnr tana ficewa, matse kwallar ta kamla tayi ta mike dakyar ta dauko dogon hijab dinta ta saka kafin ta baro dakin zuwa parlo, tana zuwa Ammi ta miko mata dari biyu, karba tayi Tace, “me zan sayo maki Ammi?” Ammi Tace, “idan kun fita da driver sai kisa ya tsaya a hanya akwai masu tuyar kosan rogo ki siya kafin ku Karasa bank sai kici” washe baki kamla tayi da murna Tace, “Nagode sosai Ammi Allah ya Kara maki budi me Albarka” “Ameen” Ammi ta furta Hakan tana murmushin yake Dan tausayin ‘yar tata ne fal zuciyar ta. Bayan ta karbi basket din da za’a kaiwa Ya khaleed ta wuce wajen Ado driver Dan su tafi yana hango ta kuwa ya mike da sauri kafin ta Karasa Harya bude motar tana isowa ta Shiga kafin ya tada motar suka bar gidan gaba1, kirjin ta sai dukan tara2 yake domin yauce rana ta farko da zata fara zuwa office din nasa toh ko idan taje Ina zata nufa? oho. Shewa suka sa Suna tafawa Lkcn da suka gama leken barin su gidan Anty Sara ce Tace, “Wlh Allah ya taimakeki Mimi badan mummy ba yau da kin bani” Mimi Tace, “shiyasa na lallaba naje nace mummy tasa waccar agolar takai masa abinci yau Ina zan iya? Yadda aka kwashe dashi jiya lalle Duk Wanda ya tunkare shi yau ya bani” Hehehe ‘yar bantan uba nifa ba Abinda nakejin dadi kamar naga Ana musgunawa agolar can” cewar Anty Hanan, Anty Sara Tace, “Ai bansan irin maitar su ba da suka kasa bar Mana gida ita da uwar ta shegu matsiyata sadakar yallah…” “yau kuma dawa ake Zance?” Cewar wata budurwa data shigo dakin ‘yan matan Hanan ce Tace, “wa kika sani Banda wa’ancan kodaddun” dariya tasa Tace, “baki da dama Hanan yanzu sauri nake na fita Dana tsaya anyi dani” Anty Sara Tace, “Ashe bazaki ga sabon catch din nawa ba safara” safara Tace, “haba ai zan dawo before time yanzu dai ku aramin earpiece nawa na Rasa shi” Hanan ce ta miko mata ita kuma tayi masu sallama ta tafi, tana barin wajen Anty Sara Tace, “aikin kenan sai shegen are-are ba daraja” “Wlh fah” cewar Hanan daga Nan suka koma gulmar safara. 

*ASALIN LABARIN*

Gidan Alhaji Muhammad khaleed, Gidane daya tara mata uku babbar matar sa ta farko hajia Rabi wacce ake Kira da mummy sai ta biyun habiba wacce ake Kira da Mami ta cikon ukun itace Aisha wacce suke Kira da Ammi, Hajia Rabi tana da yara hudu, babban yaron ta Khaleed sai Anty saratu amma ya bata tazarar haihuwa sosai sai kuma wacce take binta hannatu, Suna kiranta da Anty Hanan ‘yar autar su mardiyya Ana kiranta da mimi, a bangaren habiba Mami kuwa yaranta uku ne itama tanada babban danta Kamal Baya gari yanzu sai me bi Masa Anty safara kafin ‘yar autar su Rahma, ta cikon ukun kuwa itace Aisha wacce suke Kira da Ammi amaryar Alhaji Muhammad wacce ya aura a matsayin bazawara ya kuma karbi ‘yarta hannu bibbiyu wato Khadeeja wacce ake Kira kamla, ya maida ta tamkar ‘yarsa ta cikin sa farkon zaman ta da Alhaji Muhammad a matsayin miji taji dadi sosai har Wani jaa da haske ta karayi sbd hutu da nutsuwa saidai kashhh yau da gobe sanadiyar kishiyoyin ta yasa Sam batajin dadin zaman gidan saidai ba yadda ta iya dole ta zauna a haka, Tsanar su Akan Ammi ya Samo asali ne sbd ta kasance matar Mai gadin su. *YADDA ABIN YA FARU…* Mlm isuhu da Aisha cikakkun ‘yan Nijar ne cikin dare sukayi kaura suka dawo Nigeria batare da dalili ko makamancin haka ba sun baro kasar tasu cikin kunci tare dajin a zuciyar su sun tsani a Kira masu koda sunan garin ne, dama can asali Aisha marainiya ce Allah ya hadata da isuhu ya aureta ta fita daga cikin kangin bautar da take ciki a gidan da ake rikon ta, isuhu Allah ya rufa Masa Asiri yanada nasa na kanshi har ya samu mahassadda a cikin ‘yan uwan sa Suna kulafacin abin hannun sa, tunda aka fahimci Aisha na dauke da cikin wata daya hankalin masu bakin ciki ya tashi har saida akayi shige da fice aka rabasu da komai nasu ciki harda mahaifar su, shiyasa lkcn da mlm isuhu ya iso Nigeria ya kasance bashida komai dole rayuwa ta fara canja masu a lkcn, dakyar da sudin goshi suka fara neman aikin da zasu samu rufin Asiri uwa uba cikin dake jikin Aisha sai Kara girma yake, Hakan ya sake dagawa mlm isuhu hankali har yana zubar da kwalla cikin dare, da taimakon Allah ya samu aikin gadi a gidan Alhaji Muhammad lkcn da zasu tare a sabon gidansu kenan shi da iyalan sa, Alhaji Muhammad ya karbi mlm isuhu hannu bibbiyu harma yace zai iya kawo iyalin sa tunda a gidan haya suke Nan kuwa ba Abinda zai biya, yaji dadin kwarai dgske haka ya dauko Aisha itama da murnar ta suka tare a bangaren da Alhaji Muhammad ya basu na me gadi, rayuwa ta fara sauya masu a hankali Suna zaune cikin mutunci tare da iyalan gidan saidai Suna kokari wajen kare martabar su na Inda matsayin su ya tsaya basa shishshigi bare roko Albashin da ake biyan mlm isuhu ma ya ishesu suyi rayuwa me inganci. Cikin Aisha yana wata takwas da wasu sati aka farwa gidan Alhaji Muhammad manya-manyan ‘yan fashi ne sukayi masu dirar mikiya Inda suka samu nasarar Alburushe mlm isuhu tashi guda yace ga garin ku, sunyi mummunar barna a gidan Dan dama kudi ne ya kawo su har da gwala-gwalan matan gidan sanda suka kwashe a lkcn Alhaji Muhammad Baya gari yaje dubai yaransa Maza Duk Suna kasashen ketare karatu, washe garin ranar gidan ya tashi a rikice hankali a mugun tashe musamman da sukaji rasuwar mlm isuhu me gadi, hankalin Asha yafi na kowa tashi Harya sa ta fita hayyacin ta kafin Wani lkci harta suma a gurguje aka kaita gadon asibiti domin ceto rayuwar ta Dana Dan cikin ta, ba bata lkci aka sanar da Alhaji Muhammad halin da ake ciki shima a Ranar ya diro Nigeria hankalin sa a mugun tashe, babu Abinda yafi daga Masa hankali sai mutuwar mlm isuhu Wannan Abu ya girgiza shi ta yadda ya kasa nutsuwa da lamarin gaba1, bayan sati da rasuwar mlm isuhu Aisha ta haihu cikin wahala Dan har yanzu mutuwar kamar sabuwa takeji a ranta, ita yanzu Ina zata nufa? Dama can Allah ne gatan ta sai kuma mlm isuhu yanzu kuma ya zatayi? Bayan wata uku da rasuwar mlm isuhu Alhaji Muhammad ya sako da bukatar auren Aisha da fari taki amsar tayin sa musamman da taga narka-narkan matan sa suma kullum cikin fada suke irin na kishiyoyi Sam babu sulhu a Tsakanin su kowacce na nuna itace ‘yar gaban goshi, saidai yayi mata cikakken bayanin cewar taimakon ta yakeson yi musamman yarinyar dake hannun ta tana bukatar kulawa a yanzu, tabbas yanada gsky Dan haka Tace Allah yasa Hakan shi yafi Alkahri, Bommm…, Ne ya fashe a lkcn da matan Alhaji sukaji mgnr auren sa da Aisha habawa daga Nan kowacce ta birkice Duk Wani kishi da suke yiwa junan su ya juye kan Aisha tsananin tsana da kyara ya fara bayyana agaresu Nan suka rufarwa Aisha daga me ce mata mayya sai me ce mata sadakar yallah abubuwa dai gashi Nan barkatai kishi Duk ya rufesu kowacce na gugar zanar mgnr ta, saida Alhaji Muhammad ya tsawatar musu kafin abin yadan lafa kadan a haka dai akayi auren a lkcn ma Ya khaleed yana American toh kishin su Anty Sara ke taya iyayen su kishin Aisha. A kwana a tashi har kawo yau da jaririya Khadeeja ta shekara 17 a duniya Wanda tun bata fahimci matsayin ta a gidan ba har tazo ta gane cewar ita din ba kowa bace face agola wacce bata da Wani matsayi a gidan.

*CIGBAN LABARI…*

•••••

Sunzo Karya kwana kenan Tace wa Ado driver ya dakata zatasai wainar rogo haka kuwa akayi bayan ta sauka tana zuwa yau babu layi sosai Dan haka bata dade ba aka zuba mata a leda ta koma mota, tafiyar 20mins ce ta kaisu bakin gate din na Access Bank, kallon Ado driver da yyi parking tayi Tace, “toh inane Inda yake zama?” Ado driver yace, “haba kamla ni Ina zan sani? Ki kirasa Mana” zaro ido tayi tana rike haba Tace, “tabbb…”

[

KYAUTAR page na farko gareki *SAFIYA NURA* comment dinki na daban ne domin bakya gajiya a koda yaushe kina supporting dina Tnx u😘🤝🏻

*Wattpad*

@nuceeyluv

By

*Nuceeyluv😘*

*Nuceeyluv😘*

3…

Tace, “tabbb ni Ina naga wayar bare na Kira shi? Toh ko Ina da waya ma zan iya samun number sa ne?” Ado driver yace, “toh yanzu ya za’ai?” Shiru tayi tana dafe goshi can Tace, “bari na Shiga kawai” gyada Kai yayi ita kuma ta bude murfin kofar ta fito tare da basket din a hannun ta, sallama tayiwa Ado driver tayi gaba. a hanya ta hadu da securities masu tsaron kofa suka dubeta da kayan basket a hannu Hakan yasa suka tmbyeta Ina zataje da basket haka? Adan tsorace Tace, “dama..dama wajen Yah khaleed nazo” Dayan ne yace, “Who is Yah khaleed?” Rarraba ido Kamla tayi ta Rasa abin cewa can Wani yazo wucewa ya matso wajen kafin yace, “meke faruwa ne?” Da sauri Kamla Tace, “uhumm dama wajen Yah khaleed nazo kuma Suna tmby na waye shi? Ni kuma bansan dame zanyi kwatancen sa ba” Dan jim yayi yana duban basket din hannun ta kafin can yace, “kodai chief Accountant?” Da sauri ta gyada Kai dukda bata da tabbacin meye matsayin sa a wajen Amma dai ta kagu ta Shiga daga ciki idan ma bashi bane sai a sake duba mata, security din mutumin ya kallah yace, “Joseph raka ta wajen chief Accountant” “Okay Sir” yyi mgnr cikin girmamawa, Nan ya dubeta itama yace, “ki bishi” “Okay Sir” itama ta fada tana dukar dakai Hakan ya bashi damar binta da kallo harta juya batare daya Amsa mata ba sanin a waje yake ya wayance da gyara glass din idonsa  yana Kara gyara tie dinsa yabar wajen shima. Saida suka hau bene kafin suka fara dosar office din chief Accountant, tun daga nesa joseph yaja ya tsaya yana mata nuni da hannu kafin yace, “ga office din can Kiyi knocking kafin ki Shiga” girgiza kai Kamla tayi Tace, “Thank you” “Welcome” ya furta Hakan yana juyawa da sauri har Hakan ya bawa kamla mmki ta bishi da kallo, Dan tabe baki tayi kawai taci gaba da tafiyar ta. A nutse ta fara knocking din kamar me ciwon hannu, Yana zaune kan kujerar sa ta Alfarma fuskar sa a hade ga computer a gaban sa yana gani gefe guda wata desktop din ce ke aiki tana nuna Masa Duk Wani mahalukin dake shige da fice a cikin bank din tun daga gate din farko har kawo cikin office dinsa ba Abinda Baya gani, sanin wacece a jikin kofar yasa ko kadan beyi niyyar amsawa ba yana kallon ta tsaye harta gaji da knocking din ta jingina da bango, Dan tsaki yaja a ransa yana ayyana irin punishment din da zaiyiwa Mimi wacce itace take kawo Masa breakfast har office ba Wannan yarinyar ba….tunanin sa ne ya katse lkcn da wayar sa ta fara ringing sunan mummy ya gani tar yana yawo bisa screen dinsa kamar baida laka a jikinsa haka ya manna wayar a kunne hade da sallama, Amsawa tayi daga dayan bangaren kafin Tace, “yauwa khaleed zaka ga na turo yarinyar Nan kamla nayi Hakan ne sbd mimi na aiketa Wani wajen” Dan jim yayi kafin a takaice yace, “sauran kuma aikin me suke mummy?” Mummy Tace, “ina sanar maka ne ba tmby nakeso ba” “yi hakuri” ya furta Hakan a nutse, tabe baki tayi ta kashe wayar batare data ce komai ba, jingina kansa yyi jikin kujerar da yake zaune yana lumshe ido a hankali karar knocking din da kamla ta Kara yi ne ya sashi bude ido yana Jan tsaki kafin yace, “Yes come in” badan kamla ta Kara kunnen ta a jiki bama bazata ji mgnr ba Dan harta fara tunanin koh babu kowa ne a cikin office din? Murda handle din kofar tayi tana tura kofar bakin ta dauke da sallama, idan Dutse yyi mgn toh kuwa Yah khaleed yyi Dan Sam bataji Amsa sallamar sa ba Dan kanta kallon Wani gefen yake ba direction dinsa ba, Hakan yasa bata fahimci iya Labban sa ne kawai ya motsa wajen Amsa sallamar ba, shiru ne ya ratsa Tsakanin su Hakan yasa ta aje basket din hannun ta murya can kasa still batare data kalleshi ba Tace, “gashi Nan” tana gama fadin haka ta juya da nufin komawa, Wannan Abu yana daya daga cikin halayen ta da yake kular dashi yadda take nuna halin ko in KULA a gabansa abin na bata Masa rai Dan shi mutum ne da zaiga Ana rubibin yana fisga kamar Wani jinin sarauta shiyasa ya tsani kamla sosai sbd yadda bata kallon sa kamar yadda sauran ‘yan mata ke yi, a wajen kamla kuwa tanayin hakane Dan controlling kanta a gaban shi, da kuma kama kanta wajen gudun wulakanci Dan a gabanta yasha wulakanta ‘yan matan da suke nuna soyayyar su a gareshi masu aji kenan ma bare ita da ko kusa bazatayi gigin nuna Masa wutar son da take Masa ba Dan tasan ya wuce ajin ta kwarai dgske kawai zuciya ce bata da kashi da zata kamu da soyayyar sa shiyasa ta gwammace kullum tayi ta leken sa ta window idan zai fita…ta rike handle din kofa kenan zata fice taji shi cikin kaushin murya yana fadin, “did i tell you to go?” Wata irin tsinkewar gaba ce ta dirar mata a daburce ta juya tana

Sunkuyar da kanta batare data iya bashi Amsa ba ta hade yatsun ta biyu tana murzawa a hankali. Tsaki yaja a kufule ya maida hankalin sa kan aikin sa yana dubawa. Shiru ne ya sake ratsa wajen Banda karar A/C babu Abinda kkeji a wajen, Hakan yasa Kamla ta juya Baya tana facing din kofa ta zaro ledar kosan rogon dake makale a hijab dinta a hankali ta bude tana tsoron kada yajiyo kamshin ta gutsoro kadan kafin tasa bakinta cikin hijab ta sanya a baki. Duk Abinda take yana kallon ta ta cikin camera mmki ne ya ishe shi yadda yaga tanacin Abu me maiko a leda kamar Almajira Dan tsaki yaja a ransa yana ayyana Rashin wayewar ta she’s not classic atall, ita kuwa batasan yanayi bama saima ci gaba da cin abinta take harta cinye ta makale ledar a gefen skirt dinta idan ta fita saita yar, bude kofar office din akayi da sallama mutumin dazu ne ya shigo yana duban kamla data ja gefe tana dan murmushi Tace, “sannu” “yauwa sannu ‘yan mata har yanzu kina Nan?” Yyi mgnr tana wucewa, gyada Kai tayi batare data ce komai ba, Sam Yah khaleed be dago ya kalli Inda suke ba bare yasan sunayi har Wanda ya shigo din ya zauna yana duban sa yace, “chief Accountant is she your sister?” Yyi mgnr yana zama, kamar Wanda aka yiwa Dutse mgn haka yyi shiru be tanka ba saima sake hade rai da yyi Wani kululun takaici na kama shi wato ya lura Duk duniya babu wanda yarinyar Nan ta Raina sama da shi kowa zatayi Masa kallon arziki shi ko duban fuskar sa batayi bare tasan Allah yyi ruwan sa a wajen Duk yadda ‘yan mata ke rubibin sa da son kallon sa ace Wannan lower class din tana Masa gani2? Anya ma tasan kamannin sa? Lalle zai koya mata hankali mtwss…, Tsakin ne ya fito Fili har Wanda ke zaune gefen nasa yadan buga table din gaban sa yana fadin, “Are Alright?” Yatsina fuska yyi yana mgn dakyar yace, “meka gani?” Na zaunen yace, “tun dazu Ina mgn bakace komai ba karshe ma kaja tsaki, amma dai babyn can kanwar ka ce?” Yyi mgnr kasa2 hade dayi Masa nuni da kamla da ido, Sake Jan Wani tsakin yyi yana duban gefen kamla data tsurawa TV dake manne a bango kallo hannayen ta harde da kirjin ta yace, “Hey you me kikeyi har yanzu anan baki tafi ba? Ko babu kallo a gidan ku ne?” Yyi mgnr yana kafe ta da ido, Ahaf….Kamla ta furta Hakan a zuciyar ta dama ta sani Wannan tsayartar da yyi neman yadda zai wulakanta ta yake kuma gashi Nan yyi a gaban Wani yaji dadi ta ayyana Hakan a ranta batare data kalleshi ba Tace, “Sai anjima” tayi mgnr tana wucewa da sauri Hakan ya Kara bata Masa rai bata bashi hakuri ba sannan bata kalleshi ba kwafa yyi yana duban system zuciyar sa na turiri, duban sa Yaseer yyi yace, “haba Khaleed I didn’t expect dis from u wulakanta Dan Adam Bashi da amfani meye kuma kallo?” “Enough pls Yaseer” yah khaleed ya katse shi da sauri yana me daga hannu yaci gaba da fadin, “Kai baka dubi Rashin kunyar da tayi ba? She can’t even say sorry” “sorry for what?” Yaseer shima ya katse shi yana ci gaba da fadin, “Kai ke da lefi ni banga lefin ta ba da zata bada hakuri” tsaki khaleed yaja yana fadin, “tunda kanwar ka ce saika dawo da ita” yyi mgnr yana tashi daga wajen ya wuce toilet din ciki, girgiza kai Yaseer yyi  yana tausayin kamla Dan ya lura da yadda taji kunyar muzantata da yyi haka yake akwai jin tausayi musamman ga mace.

By

*Nuceeyluv😘*

4……

Ransa a dagule ya kunna tap din dake gaban sa yana tarar ruwa a hannun sa kafin ya watsa bisa fuskar sa mirror dake manne gaban tap din ya zubawa ido yana karewa kansa kallo, sake watsa ruwan yyi Nan yasa hannu ya gyara sumar kansa data yiwo gaba yana matse fuskar sa zuwa habar sa Dan karamin tsaki yaja yana tunanin Anya kamannin sa ba irin na dodanni bane? Da har waccar tatsitsiyar yarinyar take kauda Kai d zarar ta ganshi a waje? Toh amma ai wasu har waigowa suke Suna Kara kallon sa mtwsss yaja tsaki a Fili yana fadin, “toh kuma sai me? Dan bata kalleni ba mtwsss..” ya sake Jan tsakin a karo na biyu yana kokarin fitowa daga toilet din. Kamla na Shiga cikin mota ta dafe kirjin ta take wasu zafafan hawaye suka fara sintiri ta gefen idanun ta da sauri tasa hannu ta goge tana fatan ace kada Ado driver ya fahimci halin da take ciki hijab dinta ta jawo ta rufe fuskar ta tana Dan cije lips dinta kadan sbd yadda taji zuciyar ta na daka tsalle, wata irin zazzafar soyayyar sa ce ta sake taso mata musamman da taji muryar shi dukda ya muzantata amma muryar shi kadai ma ta isa ta Kara rura mata wutar soyayyar da take Masa, komai nasa abin so ne a gareta, mgnr sa, tafiyar sa, salon sa bare akai ga kan kyakkyawar fuskar sa abin ba’ace komai…”mun iso” taji ado driver ya katse ta da sauri ta goge sauran hawayen da basu gama fita ba murya can kasa Tace, “toh” budewa tayi ta fito Nan tayi tozali da wata hadaddiyar mota sai kyalli take a harabar gidan nasu, wucewa tayi batare data sake kallon wajen ba ta nufi sashen su, tazo wucewa kuwa taji an bangaje ta Ashe mimi ce dauke da miya data sha manja zata wuce take ya wanke mata gaban milk hijab dinta ranta a mugun bace ta dago zata wanke ta da mari tunda bata fi sa’ar ta ba sai kuma ta fasa sbd Wani Abu data tuna tahau huci dariyar shakiyan ci mimi tasa tana rike siririn kugun ta Tace, “kike kallo na kinada Abinda zakimin ne?” Kwafa kamla tayi ta juya a zuciye da nufin wucewa taji ana “ke…ke..” aka fada da karfi ko bata juyo ba tasan Anty Hanan ce, juyowa tayi batare data Amsa ba tana dubanta daga nesa, “au so kike nazo na sameki uwata?” Anty Hanan ta fadi Hakan tana jifanta da kallo, girgiza kai tayi tana danne bacin ranta Tace, “Kiyi hakuri” “mtwsss” Anty Hanan tayi tsaki tare da fadin, “biyoni” dafe goshi kamla tayi ta ayyana a ranta babu ko tantama aiki ne, bata da Wani zabi sama da tabi ta lkcn mimi ta koma kitchen Dan sake debo wata miyar tana dariya, a parlo ta tarad da ita tare da Anty Sara, Anty Hanan ta dubi Anty Sara Tace, “yauwa Anty Sara gata Nan” Anty Sara ta dubi yadda gaban hijab dinta yake kaca2 da manja kawai saita kwashe da dariya, Anty Hanan Tace, “meya faru kuma?” Anty Sara Tace, “miko min wayata yanzu nayi wata tsokana” miko mata wayar tayi ita kuma ta karba tana danna kiran wayar tasa a handsfree daga dayan bangaren akace, “honey kin barni inata jira I can’t wait to see your beautiful face dear” Dan murmushin jin dadi Anty Sara tayi Tace, “I’m on my way ka shirya ganin yadda nake” daga dayan bangaren yace, “Duk a yadda kike dukda ban taba sanin fuskar ki ba nasan nayi dace daga yadda muke mgn ma I know big gal ce” sake murmushi tayi Tace, “okay gani Nan” Nan suka katse wayar ta fara dariya, Anty Hanan Tace, “me kike yi haka ne?” Anty Sara Tace, “zan fada miki” kafin ta dubi kamla dake tsaye ta kasa nutsuwa sbd yadda hijab dinta ke dauke d manja kaca2 Tace, “ke zo ki dauki Wannan kayan ki mika shi parlon baki ki Tabbatar kuma kinyi serving bako na Ina Nan zuwa” kamla ta dukar da kanta kasa kafin Tace, “toh bari na canjo hijab dina” “ki canja?” “Ah lalle wuyanki ya isa yanka kamla” girgiza kai Kamla tayi Tace, “manja ne ya baci” “an so what? Ko daga cikin kwata kika fito idan nace kimin Abu haka zakayi baki da zabi agola” cije lips dinta tayi cike dajin zafi batare data sake cewa komai ba ta nufi Inda kayan suke, Haka ta kwashi katon tray din tayi hanyar fita, tana barin wajen Anty Sara Tace wa Hanan, “so nake naga reaction din salim shiyasa nace gani Nan zuwa zo muje mu leka tacan Baya muga yadda zasu kwashe nasan salim da kyankyami kila ya kwashe ta da mari ma idan ya ganta a kazance” shewa suka sa a tare Suna tafawa da sauri suka juya ta Baya Dan ganewa idon su. Ranta a bace tayi knocking mutumin dake rike da waya kirar iphone12 ya sake gyara mazaunin glass dinsa kafin yace, “Yes come in” sannan ya maida idonsa kan Wani picture da yake kallo a twitter, Budewa tayi bakin ta dauke da sallama, daidai lkcn ya dago idanun sa a nutse ya bita da kallo. su Anty Sara Suna makale ta window ita kuma kamla ta Dan daidaita fuskar ta kadan Tace, “ina wuni…” Shiru ne ya ratsa wajen Hakan yasa ta dago kanta zaton ta beji ba sai kuma taga ita yake kallo adan tsorace ta wara manyan idanun ta fuska adan hade Tace, “lpy?” Kawar da kai salim yyi yana Dan sa  yatsan sa bisa lips dinsa batare dayace komai ba, Hakan yasa kamla ta fara serving dinsa itama cikin sauri2 ta jera Masa komai gaban sa kafin tayi nufin tafiya, da mmki ya dago yana duban ta dan dama Duk Abinda take yana ankare da ita cikin cool voice dinsa yace, “Saraa…” Yi tayi kamar bataji me yake fada ba tayi wucewar ta da sauri. su Anty Sara na jikin window suka matsa can gefe Anty Hanan Tace, “tun kafin gayen Nan ya tsallake ya gudu batare da yasan asalin wacece ke ba wlh kije” kirjin Sara ne ya buga Dan tana mugun son salim Tace, “kwarai kuwa” Nan suka koma daki a gurguje ta Karasa shirinta tayo waje, can parlon baki ta nufa sai sauri take kamar zata kifa Dan gani take kafin ta Karasa ya tafi. Ita kuwa kamla rai bace ta Karasa parlon su a parlon ta tarad da Ammi tana kallo, duban ta tayi a nutse bayan ta Amsa sallamar da tayi mata Tace, “meya zaunar dake baki dawo da wuri ba?” Tayi mgnr tana karewa hijab dinta kallo, yamutsa fuska kamla tayi kamar me shirin yin kuka ta zayyane wa Ammi dalilin dadewar tata har aiken da Anty Sara tayi mata da yadda mimi ta bata mata hijab, hmmm…! Ammi ta sauke ajiyar zuciya tana mata alama da tazo karasowa tayi ta fada jikinta bayan ta cire hijab din, shafa sumar kanta tayi Tace, “Kiyi hakuri kamla rayuwa ce ta maida mu haka watarana sai labari kinji koh?” Girgiza kai Kamla tayi kafin Tace, “amma Ammi yaushe zaki kaini wajen dangin ki Dana mahaifina?” Zuciyar Ammi ce ta buga da karfi har saida taji kanta ya Sara da sauri ta rike tana karanta “innalillahi wa’inna ilaihin raji’un” Hakan ya dagawa kamla hankali harta dafe ta itama tana mata Addu’a zancen daya sha ruwa kenan basuyi ba. Batare da tayi knocking ba ta tura kofar da sauri daidai lkcn salim yake kokarin biyowa bayan kamla tunda yaga kamar dgske guduwa tayi zaton sa ko kunyar sa takeji, ja Baya yyi yana karewa Anty Sara kallo, itama dafe kirji tayi tana lumshe miri-mirin idanun ta daya sha eyeshadow da fake eyelashes dinta Tace, “Washhh…” Kafin ta bude tana duban salim daya saki baki yana kallon ta, cikin yanga Tace, “I’m sorry de….” Bata Ida zancen ba ya daga mata hannu yana Dan kakaro murmushi yace, “it’s okay” sannan yaci gaba da fadin “baiwar Allah ko kin hadu da wata da zaki shigo Nan?” Er dariya Anty Sara tayi kafin Tace, “oh wai me aikin mu?” Tayi mgnr da gadara ita a dole suma sunada kudi, “me aiki kuma?” Ya fada yana zaro ido d mugun mmki, Anty Sara Tace, “kwarai kuwa kayi mmki koh?” Girgiza kai yyi yace, “amma Tace min er gidan ce” murmushi tayi kafin Tace, “calm down dear ba itace saran da kke zato ba” kan salim ya kulle harma ya Rasa abin fada zuciyar sa na dukan uku2 a ransa fadi yake badai Wannan nunar ranar bace SARAAA? 

5…..

A ransa fadi yake badai Wannan nunar ranar bace SARAAA? Katse tunanin nasa tayi da fadin, “surprised” tayi mgnr tana dan wara hannu taci gaba da fadin, “nice Nan Saraa habibty” kamar Wanda ruwa ya cinye shi haka salim yyi tsaye yana dubanta da mmki har saida ta danyi tafi tana er dariya Tace, “nasan zakai mmki ai ba waccar kazamar bace” tayi mgnr tana murmushi, tafin da tayi Masa shi ya farkar dashi kokarin danne Abinda ya taso Masa zuwa makogwaro yake yana Dan murmushin da be Kai har ZUCI ba yace, “wai dgske kece Sara?” Yyi mgnr yana Kara kare mata kallo, Anty Sara Tace, “haba Mana dear ka zauna sai muyi mgnr a nutse kaji?” Dan shafa sumar kansa yyi kafin yace, “I’m sorry ni zan wuce ne” yyi mgnr a takaice, kirjin Anty Sara ne ya buga cikin sauri Tace, “dear da wuri haka? Ko abinci bakaci ba fa, zaro wayarsa yyi yana Dan latsawa yace, “sorry nxt time zamu hadu..” yyi mgnr yana kokarin tafiya, da sauri ta dan tare hanyar Tace, “uhumm nace ko sbd kazamar can ne kkejin kyankyamin ci?” Tayi mgnr hankalin ta a tashe, kamar bazai ce komai ba sai kuma can ya maida wayar aljihu yana zube hannayen nasa cikin alijun wandon sa duka biyun yace, “wacce kenan?” Anty Sara Tace, “wacce ta kawo kayan idan sbd itane kayi hakuri ni yanzu sai nasa a sake maka Wani ita kuma zan hukuntata tunda tazo da kazanta wajen ka” Dan murmushi yyi yace, “ita din bata da Suna ne?” Da sauri Anty Sara Tace, “uhumm wai kamfala ne ko kamla ni sunan ne kamar na Aljanu” murmushi sosai salim yyi zuciyar sa na ayyana abubuwa sosai yace, “Thanks you” Dan murmushi jin dadi tayi ganin yana mata mgn d murmushi kafin Tace, “amma me nayi na godiya?” “Sbd kin…Ammm….Ina nufin naji dadin Duk hidimar da kikayi sbd ni thanks you so much” Anty Sara dadi ya kama ta Tace, “toh amma kaki zama bare kaci komai” dage kafadun sa yyi yace, “don’t worry next time zamu hadu yanzu sauri nake akwai Inda zani zamuyi waya kinji?” Ba haka Anty Sara taso ba amma ba yadda ta iya dole ta amince Dan haka ta gyada Kai, Nan suka fito waje Dan rakashi jikin mota, Suna tafe tana Masa hira amma gaba daya rabin hankalin sa na kan masu yawo a gidan sai Dan juyawa yake a kaikaice be hango Abinda yakeson gani ba a haka har suka isa gaban motar ya kwaso Duk shopping din dayazo mata dasu ya bata hade da bugun Abuja dadi ya kama Anty Sara tuni fuskar ta ta washe tana murmushi a haka suka rabu har ya fita daga gidan yana waige kamar Wanda yabar ajiya a ciki.

Yana fitowa bakin layin su ya hango ta tana tafe ba kowa bace face kamla cikin sauri ya taka burki Hakan yasa kamla ta dago kanta da sauri kirjinta na bugawa Dan batayi aune da Hakan ba sbd sauri take ta kaiwa Ammi aiken da tayi mata dazu ta samu ta tafi islmiyya, fitowa yyi da hanzari kamla na ganin shine ta tsuke fuska tana duban sa da mmki, washe baki yyi yace, “yi hakuri fah na tsorata ki ko?” Dan tabe baki tayi Tace, “aa” daga haka tayi gaba da sauri ya sha gabanta Hakan yasa ta dago a razane tana ja Baya Tace, “bawan Allah lpy?” Hannayen sa ya zube cikin Aljihu yana daidaita nutsuwar sa da jifan ta da Wani irin kallon daya Kara tsoratata yace, “lpyr ce ta kawo haka domin har nabar gidan Ina waigen Ina zan ganki? Sai kuma Allah yyi muka hadu anan Kamla…” Yyi mgnr yana dage mata gira cike da annuri a tattare dashi kamar Wanda ya santa tun da can, ita kamla mmki d dariya ma yaso bata Hakan yasa ta danyi murmushin da be wuce kan Labban ta ba kafin Tace…..daidai lkcn Anty Hanan suka wuce da driver tana binsu da kallo batare da sun ankare waye a motar ba daga lkcn da yyi mata murmushin har lkcn da itama tayi Duk Akan idonta Wani irin zillo tayi tana lalumen wayarta Tace, “kan uban can Wannan ba salim bane?” Tayi mgnr tana danna kiran Anty Sara wayar ta Shiga amma bata dauka ba tsaki taja ta sake danna kiran Nan ma bata dauka ba sai yi take tana waigen su har ta daina hango su ga kuma kiran da take ba’a dauka ba tasan shiriritar Anty Sara yanzu haka wayar ta bari a Wani wajen aikuwa taja tsaki yafi dubu a kufule Tace, “dallah Ado kayi sauri inaso naje na dawo yanzun Nan” ado driver yace, “toh.”  Kamla ta dube shi sosai Tace, “da alama makawa kayi mlm ko ka manta wajen Anty Sara kaje? Miye hadina dakai da dole saika ganni???” Tayi mgnr tana dan hade fuska, shafa sumar kansa yyi yace, “yeah wajen ta nazo amma dake na fara tozali a gidan” adan tsorace Tace, “toh kuma sai akayi yaya??” Salim ya gyara tsayuwar sa kafin yace, “Hakan yasa na FADA SO batare da nayi aune ba…” Ja Baya da Baya kamla tayi har tana neman yin tuntube hankalin ta a tashe ta juya cikin hanzari ta fara tafiya salim na ganin haka ya biyo ta da sauri yana fadin, “kamla..kamla… Pls wait..” inaa Sam batasan yanayi ba domin hankalin ta a mugun tashe yake yi yyi kamar ya bita sai kuma ya tuna Sara a gidan dole yasan abin yi Dan Wlh bazai iya hakura da kamla ba badan yaso ba yanaji yana gani ta tafi sai zabga sauri take kamar zata tashi sama, motar sa ya shige ya zauna yana kifa kansa a steering wata irin wutar son kamla ne take tashi a zuciyar sa Hakan har yaso ya bashi mmki daga kallo daya? A haka dai yaja motar yyi gaba. A rikice kamla ta fada gidansu can ta hango Anty Sara a tsaye tare dasu mimi a compound din gidan Hakan yasa hantar cikin ta ya kada especially da taga irin kallon da suke mata, sum..sum tazo wucewa ta gaban su take taji sun kwashe mata da dariya Anty Sara Tace, “Ai nake gaya miki safara anyi bake yasin sbd kyankyamin salim be iya cin komai da yazo daga gareta ba na gaya muku sai sauri yake nasan ba komai bane ya sashi Hakan sai tashin zuciya yoh Duk fah kaca2 taje hijabi jage-jage da miyar manja sai kace asararrun ‘yan yayen Nan” Nan suka sake kwashewa da dariya safara Tace, “kur’ani baku kyauta min ba domin naso naga show dinnan” Anty Sara Tace, “haba ai sai Hanan ta dawo ma zakuji bayani dalla-dallah.” Kamla najin su ta saki ajiyar zuciya kafin ta Kara saurin tafiyar ta a gurguje ta afka parlon su lkcn Ammi bata ciki ta wuce daki cikin hanzari ta canja kayan ta zuwa na islmiyya ta fito ko takan Ammi bata bi ba ta wuce can ta hango Rahma kanwar safara tana fitowa daga sashen su Dan tsayawa tayi ta karaso kafin kamla Tace, “Ashe kun dawo” Rahma da murmushi Tace, “Wlh inata dubaki ban ganki ba ai” kamla Tace, “Ammi ce ta aike ni Ina mami?” Rahma ta danyi yake sbd tasan yadda mamin su ta tsane ta sosai Tace, “yanzu na baro ta tana wanka islmiyya Zaki tafi da wuri haka?” Ta bata Amsa hade da jefo mata wata tmbyr sbd kawar da mgnr farko, kamla tayi murmushi Tace, “eh Wlh inada hadda gara na isa dawuri sai na dinga tunawa kafin lkcn Shiga aji yyi” Rahma Tace, “badan na gaji ba ai sai muje tare” kamla Tace, “ai nasan ba lalle kije yau ba Ina ya kamal?” Rahma Tace, “kin sanshi ya fice ko dadewa beyi ba aka kirashi” Kamla Tace, “likita bokan turai” dariya suka sa Nan suka fara takawa Suna Dan zancen su har ta raka kamla bakin gate daga Nan ta wuce islamiya ita kuma ta koma ciki, tana fitowa bakin gate ta hango motar ado driver sai sauri yake da mmki ta matsa gefe tana kallon Wanda ke ciki toh Wannan saurin na miye suke? Tabe baki tayi ta wuce abin ta, Anty Hanan kamar ta fisge tukun haka takeji har suka iso farfajiyar gidan bata daina bala’i ba Ko gama parking beyi ba ta bude murfin kofar ta fito gyalen ta a hannu tayi gaba lkcn ba kowa a wajen sun koma bangaren mami data dawo, batasan can suke ba ta wuce bangaren su tana zuwa parlo ta dinga raraka sallama shiru ba labari mummy ce ta sakko daga daki tana duban Anty Hanan Tace, “ke lpy irin Wannan Kira?” Anty Hanan Tace, “neman Anty Sara nake” Dan tsaki mummy taja Tace, “toh kuma sai ki dinga Wannan ihun kamar zararriya?” Dafe kanta Anty Hanan tayi mummy ta tabe baki tana shirin komawa daki Tace, “sai ki duba bangaren su safara inajin Suna can” tayi shigewar ta daki, a hanzarce kuwa ta juya d sauri har tana tuntubi tayi bangaren su safara, dukkansu na parlon suna hirar dazu taki karewa mami na jinsu tana dariya Hanan ta fada dakin, Anty Sara Tace, ” ‘yar halak kenan kinki ambato yanzu muke mgnr ki Ina kika dade ne haka?” Memakon ta bata Amsa itama Tace, “wai Ina kika aje wayar ki Anty Sara?” Anty Sara Tace, “oho maybe tana daki” Dan tsaki Anty Hanan tayi ta zauna gefen kujera, hakan yasa suka zuba mata ido Suna kallon ta Anty Sara Tace, “Wani abin ne ya faru?” Cike da takaici Tace, “meye ma be faru ba??” Da mmki Anty Sara Tace, “kamar ya?” Anty Hanan Tace, “billahillazi tun kafin Abu yyi nisa kisan Inda dare ya miki” Kai a mugun daure Anty Sara Tace, “ke ni kin sani duhu dallah ki warware min Kai meye kuma nasan Inda dare yamin?” Anty Hanan Tace, “kina Nan zaune hoto waccar mayyar ta lashe miki zuciyar salim baki sani ba” a razane Anty Sara ta mike tana isowa gaban Anty Hanan ta kama cinyoyin ta Tace, “ban gane ba kinyimin bayani dalla-dallah” Nan Anty Hanan ta zayyane musu ganin da tayi musu a gefen layi dazu ta karkare da fadin, “baku ga yadda suke jifan junan su da kallo suna murmushi ba tamkar Wanda suka dade da juna irin tsofaffun masoyan Nan” Wani irin ihu Anty Sara tasa tana dora hannu akai Anty safara kuwa sai tafa hannu take mimi kam a guje tayi bangaren su dan sanarwa da mummy, mami tana girgiza kai sai fadi take, “zata aikata, tabbas zasuyi indai jinin Aisha ce Abinda yafi haka zatayi” Nan fah waje ya rikice Anty Sara Tace, “wllhi tallahi sai tasan tayi da er halak daga ita har uwar tata shegu mayu matsiyata” tana gama fadin haka tayi waje Nan ta nufi bangaren su kamla, sauran ma du binta sukayi suna zuwa suka ga wajen a rufe alamar basa Nan Ammi ta fita duba wata kawarta da suka hadu a asibiti tun a haihuwar kamla itace suke kawance har yanzu kamla kuwa dama taje islamiya, juyowa sukayi a tunzure sai ga mummy Nan ta fito itama sai bala’i take Nan suka hade a compound din gidan kowanne ransa a bace, Har kusan shida na yamma suna zaune a compound din gidan sai tufka da warwara suke kamar Ammi ta sani bata dawo ba har lkcn ita kuwa kamla sun tashi ta taho gida yanzu kam hankalin ta a kwance yake tunda dazu ta wuce taga babu alamar komai a fuskar su ta saki ranta shikuma salim yaje ya karata tana zaman ta bazai ballo mata ruwa ba bayan haka ma ita me zatayi dashi ma? Mtwsss kayan haushi, suna zaune motar Ya khaleed ta danno ciki Duk suka zuba Masa ido shima daga can cikin motar mmkin zaman su a wajen yake kamar masu jiran Wani Abu yasan dai daddy Baya gari yau tun safe yabar gidan, yana gama parking kuwa sai ga kamla ta shigo kamar hadin baki kirjin ta ne ya buga yyi rasss ganin su jere reras kowa ya zubo mata na mujiya can kuma Anty Sara ta zaburo daga wajen ta nufo ta, kamla batasan meke faruwa ba ta juya da sauri zata gudu ta bangaje kirjin ya khaleed daya gama parking ya fito a gigice tayi Baya daidai lkcn Anty Sara ta nufo da hucin ta, zamewa gefe tayi tana wuki2 d ido Anty Sara Tace, “munafuka algunguma nayi Dana sanin turaki wajen salim wlh” tayi mgnr tana kokarin jawota yah khaleed ya daka mata tsawa yana duban ta yace, “are you out of your senses?” Anty Sara Tace, “yah khaleed bakasan me Wannan yarinyar tayi min bane Wlh daga turata ta kaiwa saurayi na ruwa shikenan sai ta lashe zuciyar sa idan ba maita ba ace har ya bita waje Suna Zance harda murmushi wa junansu?” Kirjin kamla ne ya bada Wani irin damm….. Mummy ce ta karaso wajen tana fadin, “Kai barta taci min ubanta yau dinnan” Motar kamal ce ta shigo gidan Ashe tare suke da Ammi suka fito da sauri ganinsu cirko2 sunyi zaton Wani Abu ne ma ya faru mami na ganin haka ranta ya baci ta tsani taga kamal da Rahma na kula Ammi da erta abin na bata haushi yana karasowa yace, “lpy meke faruwa ne anan?” Mami a kufule Tace, “Idon matambayi” tayi mgnr tana hararar sa, kawar da kai yyi Yana duban kamla da tayi tsumu2 tsakiyar Anty Sara da yah khaleed yace, “kamla zo Nan” da sauri ta kama hanya zata tafi yah khaleed yace, “taku daya kika Kara anan sai ranki ya baci” yyi mgnr yana kallon ta, kasa gaba ko Baya kamla tayi Ammi na ganin haka kawai tayi gaba ta barsu a wajen kamal yace, “meye kkeyi haka khaleed?” Yah khaleed ya daga Masa hannu kafin ya dubi kamla data dukar da kai jikinta sai rawa yake yace, “follow me” yana gama mgnr ya juya Dan wucewa sashen sa, Kamla bata da Wani zabi a yanzu sama da ta bishi Dan haka ta juya akalar ta hanyar daya nufa tabi bayansa kirjinta na dukan uku2.

[

By

*Nuceeyluv😘*

6……

Yah khaleed yana Shiga parlo ya zauna bisa doguwar kujera yana Dan jingina bayan sa hade da lumshe ido a gajiye yake matuka, kamla a darare ta shigo parlon itama tana bin bango kamar wata kadangare can karshen bayan kujera ta samu ta rakube tana me dukar da kanta Dan tunda ta shigo kallo daya tayi Masa ta dauke kan ta da sauri zuciyar ta na harbawa fat-fat, parlon tarr yake kewaye da fitulu masu haske dake Ana daf da Kiran magrib shiyasa wajen yyi haske sosai gwanin ban sha’awa kamar ba bil’adama a ciki fanka ce kawai ke aiki kamla Duk ta kagu data bar parlon Dan tunda tazo idon sa ke lumshe kila ma bcci yake Wannan tunanin nata yasa ta dan dago idon ta kadan taga har yanzu dai a lumshen yake Dan haka ta fara matsawa Baya da Baya zata gudu tana daf da ficewa kuwa taji mgnr sa tamkar daga sama yace, “kina Kara matsawa zaki gane kuren ki” a tsorace ta dago kanta da mmki taga har yanzun idon sa a lumshe yake kamar zatayi kuka ta koma ciki sumi2 tana shirin zama gefen kujera taji yace, “zonan” tashi tayi ta isa gaban sa tayi tsaye kanta a duke, a kufule yace, “kin hadiyi icce ne?” Zama tayi da sauri tana girgiza kai, Dan tsaki yaja yana me turo duka kafafun sa gaban ta cikin yanayi na gajiya yace, “cire min” da mugun mmki ta dago manyan idon ta tana duban sa daidai lkcn da zai bude nasa idon duka tayi sauran saukar da nata, ji tayi yace, “ke kurma ce?” Bata bashi Amsa ba saima kama takalmin da tayi tana kokarin cirewa hannun ta sai rawa yake ta kasa yi, shikuma wayarsa kawai ya zaro yana dubawa a nutse har lkcn bata iya cire Masa ba Dan ji take bugun kirjin ta yana Kara yawaita kaunar sa tana Kara tasiri a ranta especially da suka kasance su biyu yanzu kawai sai ta fada tunanin gasu can sunyi aure matsayin mata da miji kuma…. ringing din wayarsa ce ta karade wajen Hakan yasa ta dawo daga banzan tunanin data tafi shikuma be dauka ba saima Jan tsaki da yyi, kiran ne ya katse aka sake Kira again yana dan karamin tsaki ya daga bakin sa dauke da sallama daga dayan bangaren akace, “My dear” yana yatsina fuska yace, “yes babyluv” kirjin kamla ne ya bada Wani irin rasss daidai lkcn data take kokarin fitar Masa da safar kafar sa taji Wani irin bacin rai ya ziyarce ta da sauri ta fisge har yah khaleed yana dagowa daga kishingiden da yake yana kallon ta kamar ba ita tayi ba kawai saita Wani maze ta kama dayar kafar ta fisge itama da karfi ranta a bace wayar yake amma hankalin sa gaba1 na kan kamla, kamla na gamawa ta mike da sauri tayi hanyar fita, da sauri yah khaleed yace, “Tsaya Nan..” wacce suke wayar Tace, “ina zan tsaya?” Yah khaleed yace, “bada ke nake ba” yana duban bayan kamla da take ta sauri zata tafi yace, “nace tsaya Nan” yyi mgnr dadan karfi ko sauraren sa batayi ba zuciyar ta a sama take har tana Kara saurin tafiyar ta bata saurare shi ba, katse wayar yyi da sauri batare da yyiwa waccar din sallama ba cikin zafin nama yyi taku biyu zuwa uku tana dab da ficewa ya damko hannun ta, a firgice ta juyo tana duban saitin kirjin sa dukda ranta a bace yake amma Hakan be hana Wani irin mugun tsoron sa ya shigeta ba daga hannu yyi zai wanke ta da mari sai kuma ya fasa ya bugi bangon dake gefen su ransa a mugun bace yace, “sbd bakida kunya Ina miki mgn har ki wuce baki saurare ni ba?” Yyi mgnr yana huci Dan gani yake raini ne kawai zaisa tayi Masa haka, kanta a duke ta kasa ce Masa uffan kirjinta na harbawa da sauri, Aikuwa ransa ya sake baci besan lkcn daya dauke ta da mari ba dama yana Nan cike dajin haushin ta a hasale yace, “idan wasu ne can a waje kin iya yashe baki kamar sabuwar kamu kina musu fara’a da murmushi koda basu maki mgn ba amma sbd tsabar kin Raina ni nayi maki mgn ki share ni? Wacece ke? Me kikeji dashi? Banza lower class irin ki…” ya Karasa mgnr yana huci ba Abinda ya Kara kona Masa rai sai rigimar daya zo ya tarar sunayi da Anty Sara kuma Duk a dalilin yashe bakin da take wa mutane ya jawo wancan yace yana son ta tsabar Rashin sanin darajar Kai Mtwsss yaja tsaki, kamla kololuwar bacin rai takai Hakan yasa batasan lkcn data fashe da kuka ba bata da amsar da zata bashi to wacce Amsa ma bayan ya gama ci mata mutunci? Juyawa kawai tayi a guje ta baro Masa bangaren tana kuka bilhakki, can su Anty Sara suka hango ta window ta wuce hawaye jabe2 saman fuskarta sai yanzu ransu yyi fari tass dama sun san Yah khaleed bazaiyi mata ta wasa ba, tana fadawa parlon su Ammi na fitowa a daki direct gabanta taje ta rungume tana kuka me Karya zuciya, zaunar da ita kan kujera tayi Ammi na kokarin danne zuciyar ta Tace, “ya isa haka kukan” sai a lkcn kamla ta bude baki cikin kuka Tace, “wai me muka tare musu a gidan Ammi? Kowa Baya son mu, basu san uzuri ba, basa yiwa mutum uzuri Wallahi na rantse maki Ammi salim shine Nan ya bini bani na bisa ba bayan haka ma ni me zanyi dashi? Su kirashi man ai zai fada musu gsky” Ammi Tace, “ya isa haka Kiyi hakuri Allah zai saka maki” Kamla taja ajiyar zuciya ranta na turiri Tace, “kawai yah khaleed ya sameni ya wanke ni da mari bansan wacce irin tsana yamin ba a gidan Nan” Ammi tayi shiru can Tace, “share hawayen ki kiji” kamla ta share hawayen nata tana Jan zuciya ta dubi Ammi Tace, “inajin ki” Ammi Tace, “nayi nazari Akan matsalar gidan Nan idan munaso ran mu ya daina baci dole ne ke Kiyi aure” a razane kamla Tace, “Ammi aure kuma? Ko university fah banyi ba iyakata secondary yanzu ma hutun namu befi 3weeks ba mu koma a fara shirye-shiryen exam na waec da neco” Ammi Tace, “nasan da haka shiyasa ma na fara maki zancen auren tun yanzu idan kin samu me son ki Tsakani da Allah saiku fahimci junan ku idan kin gama exam din Ayi bikin ki” Wani irin tsinkewar gaba kamla taji batasan lkcn da wasu zafafan hawaye suka fara sintiri bisa kumatun ta ba yanzu ya zatayi da soyayyar Yah khaleed a ranta? Kusan fah tunda tayi wayo da kaunar sa ta ginu a ranta dukda Baya bata fuska tun da can har yanzu amma kuma shi so makaho ne batasan lkcn da wutar soyayyar sa ta fara ruruwa a ranta ba…”kinyi shiru” Ammi ta katse mata tunani, fashewa da kuka tayi na Rashin mafita kafin ta mike kawai ta wuce dakinta. dafe kanta Ammi tayi tana share wasu siraran hawaye daya ziraro ta gefen kumatun ta shakka babu dole tasan abin yi auren kamla shine mafita a garesu da Wannan tashin hankalin da suke fuskanta kullum. Karo na ashirin kenan Anty Sara ta sake gwada wayar salim bata Shiga ba sai yanzu, da sauri kuwa ta danna handsfree su Anty Hanan na kewaye gefen ta Suna jiran ya dauka, tsaki salim yaja yana dafe kan sa yasan dama saita nemeshi shikuma gsky a yanzu babu soyayyar ta a ranta amma dai babu yadda ya iya dole ya fada mata gsky ta daina damun sa, dagawa yyi daga dayan bangaren Anty Sara Tace, “Honey” salim yace, “Sara ya garin” wara ido Sara tayi kafin ta dan rage murya Tace, “yau kuma Sara gatsau haka?” Dan murmushi salim yyi yace, “dama inason muyi wata mgn” damm kirjin Anty Sara ya bada kafin Tace, “toh dear inajin ka” salim yace, “hakuri nakeson na baki Sara gsky bazan iya ci gaba da soyayya dake ba Allah ya jarabceni da soyayyar ‘yar aikin ku” “kut***mr ub**can kayyasa, salim kodai ka fara shaye-shaye ne ban sani ba?” Salim yace, “ke kurma ce baki fahimci Abinda nake fada miki bane?” Saraa Tace, “yanzu salim ni kke cewa baka so sbd wata gaja can Agola?? Billahillazi idan Ina raye baka isa ka samu soyayyar ta ba kaji na rantse maka” salim yace, “toh dama ke haka kalar ki take ban sani ba? Ashe da tuni nayiwa yarana zaben tumun dare sai Allah ya hadani da Kamla kamilar mata” a kufule Anty Sara Tace, “Kai da kamilar na danno na dannan muku a makoshi ‘yan butar uwa asararru sheggu maciya amana yoh waya sani dama can kuna cin amanata toh ni Banda ma toshewar basira me zanyi dakai gaja gajarabul sai tsayi ba jiki kamar Wani jalbe” salim bece mata uffan ba harta gama bala’in ta karshe ya kashe wayar ransa a mugun bace. Tana gamawa Anty Hanan Tace, “wllhi kin biyani Anty Sara yoh me za’ai dashi kamar Wani zare ke farin Nan ma kila Mai ne kinsan Maza Suma sun fara bilicin” Anty Sara Tace, “kwarai kuwa ai daga ji aron kaya ma yyi na Kara ganin keyar sa a unguwar Nan sai ya gwammace kida da karatu” Nan dai sukaci gaba da cin mutuncin salim hade da kamla. Bayan sallar isha Mummy na parlo yah khaleed ya shigo da sallama, amsawa tayi tana duban yanayin sa har yanzu Abinda ya faru Tsakanin sa da kamla be bar ransa ba Dan haka fuskar Nan tasa gata Nan dai, zama yyi kan kujera yace, “Mummy barka da dare” Mummy Tace, “yauwa ya aiki?” “Alhamdulillah” ya bata Amsa, Mummy Tace, “a kawo maka abincin Nan ne?” Dan yatsina fuska yyi yace, “no Mummy na koshi” Mummy ta juyo da hankalin ta kansa tana duban sa Tace, “Kai wato bazaka daina Wannan tsirfar ta kin cin abinci ba koh?” Girgiza kai yyi yace, “aa Mummy banajin yunwar ne kawai” Mummy Tace, “shiyasa naga fuskar ka ta nuna bacin rai meya faru?” Sosa Kai yyi yana kokarin saita nutsuwar sa kafin yace, “Mummy gajiyar aiki ce kawai” ganin ya saki ransa Tace, “toh Allah dai ya bada lpy me amfani” “Ameen Mummy” Nan suka fara hira jifa2 Suna kallo can Mummy ta juyo Tace, “mgnr da muka fara jiya saifu banji kace komai ba” shiru yyi be iya bata Amsa ba mood dinsa yana kokarin canjawa, Mummy Tace, “kaga idan baka da matar auren ne ni saina nema maka ga mata Nan birjik wasu ma har gaisuwa suke kawo min har Nan gida Duk a dalilin ka saifu, idan har baka samu wacce kkeso ba ni saina zaba maka a cikin Wanda suke zuwa ko a yaran ‘yan uwa” yanzu kam fuskar sa a hade take yace, “haba Mummy kamar ni a zaba min mata?” Mummy Tace, “toh naga baka da niyya ne ai daddyn naku kuma be Wani damu ba idan nayi mgnr auren ka yace komai lkci ne toh gsky ni na gaji na kosa na fara ganin ‘yan dagwai-dagwai baka gani ba gwanin sha’awa idan naga kawayena da jikokin su an kawo masu su weekend” yah khaleed yace, “toh Mummy ai komai lkci ne a Kara min lkci da Kaina zan kawo wacce nakeso”

Mummy Tace, “nifa matsalata dakai kenan tun ba yanzu ba da nayi mgnr aure sai kace na Kara maka lkci yau ko jaririya zaka aura yaci ace rainon da kke mata ta girma” dariya ce taso kama shi Hakan yasa murmushi ya subuce Masa yana sosa keya, Mummy ta mako Masa harara Tace, “da alama dai ka maida ni kakar ka koh?” yah khaleed yace, “a’a Mummy” yyi mgnr har yanzu murmushin bebar fuskar sa ba, Mummy ta hade rai tana duban sa sosai Tace, “Wallahi kaji na rance idan baka kawo mata Nan da sati daya ba zan baka mmki” a tsorace yake kallon ta kirjinsa na harbawa da sauri2 Mummy tayi fuska tana juya keya Tace, “idan ka dauki mgnr wasa mu zuba mu gani” ta Karasa mgnr tana mikewa tabar wajen, sororo ta barshi zaune hankalin sa a mugun tashe toh shi wacce matar zai kawo mata? *Halish* itace kadai yarinyar da yake kulawa aduk cikin enmatan da suke bibiyar sa itama kawai Dan yaga ba lefi tanada nutsuwa ne kuma koba komai ya rage lkci da ita toh kodai ita zai fitar a matsayin wacce yakeso? Akace da babu gwara ba dadi. Da Wannan tunanin ya mike yyi sashen su shi da kamal, kowanne parlon sa daban koda yaje ma kamal din Baya Nan yyi wucewar sa parlon sa tunani fal ransa yana tufka da warwara.

[

By

*Nuceeyluv😘*

7……

Kamar bazata tashi ba zuciyar ta takasa hakura da hango abin kaunar ta Yah khaleed, dakyar ta mike daga kwanciyar tana leken window kamar munafuka abin ya zame mata tamkar ibada bata missing Wannan lkcn me tsada a wajen ta da take samun damar karewa Yah khaleed kallo, Shine ke tafe kuwa cikin Shirin sa na zuwa office yana riga kowa fita a gidan sai kamal daddy kuwa be cika zama ba Sam, wayace manne a kunnen sa yana amsawa fuskar sa cike da murmushi haka kawai taji ranta ya biya mata da mace yake waya take taji ranta yyi mugun baci, kamar an sunkule ta tayi saurin mikewa zumbur ta wawuro zumbulelen hijab dinta tasa saman kayan bccin ta tayo waje bata bi takan Ammi ba dake bcci dama ya kamata ace ta fita zuwa kitchen yanzu, kanta ko kallabi babu tayi sashen su yah khaleed yana tsaye gaban rumfar su yana Amsa wayar tunda ta doshi wajen kuma sai ta Rasa kuzarin ta take gabanta yahau bugawa da sauri2 kanta a duke sai tafiyar tata ta koma tamkar mahauniya, yah khaleed yana kallon ta sau daya ya dauke Kai amma a ransa tunani yake meya kawo ta wajen Nan da sassafe haka? Tazo giftawa ta gefen sa murya can kasan makoshi Tace, “barka da Asuba” tana fadin haka tayi niyyar wucewa kamar bazai ce komai ba dai can yace “where are you going?” Yyi mgnr har lkcn wayar na kunne sa, yatsina fuska tayi dama ta shirya karyar da zatayi tana dauke kanta Tace, “yah kamal zan gani jiya kwana nayi banajin dadi” tayi mgnr tana ci gaba da tafiya a hankali “baby Ina zuwa” ya katse wayar yana mayar da ita aljihu take kamla taji Wani kullutu ya makale mata a makoshi toh wai wacece bbyn Nan? Yah khaleed yana duban ta ransa a hade yace, “sbd bakida hankali da Rashin kamun kai a Hakan zakije a duba ki?” Yyi mgnr yana sake hade ransa sosai shi ya Rasa wacce irin Rashin kamun kaine da kamla duban jikin nata tayi taga hijab din nata dai dogo ne Banda shatin kayan bccin ta daya fito dake wandon da kadan ya wuce gwiwa shiyasa ake hango Inda ya tsaya batace Masa komai ba sbd zafin kiranta da yake marar kamun Kai tayi gaba daidai lkcn ma yah kamal ya dawo daga motsa jiki ta bayan su yace, “kamla kece da safiyar Nan” yyi mgnr da murmushi juyowa kamla tayi tana washe fararen hakoran ta Tace, “Barka da Asuba ya kamal” yah kamal yace, “barka namesake” ya fadi Hakan yana dariya Dan cewa yake sunan ta da nashi kusan daya, yah khaleed ne yaja tsaki yace, “wuce muje” da mmki duka biyun suka maida hankali su kansa da sauri kuma ta kawar da idonta gefe taji yace, “ba mgn nake ba?” Sumsum ta juya tana duban yah kamal tace, “saina dawo” yah kamal yaja tsaki kawai yyi gaba Suna barin wajen tayi kokarin wucewa Inda ta fito ya dakatar da ita da sauri, har jikin motar sa ta raka shi kanta a sunkuye ya bude motar sa ya shige kafin ya zuge glass din motar yana kallon yadda take kallon kasa ya Kara Jan tsaki a karo na babu adadi yace, “kinaji na?” Kamla ta gyada Kai, Yah khaleed yace, “gidan Nan gidan mutunci ne idan na sake ganinki da Wannan shigar kin fito haka sai ranki ya baci bamason lalata a cikin gida” karon farko ta dago a razane tana kallon sa take kwayar idanun su ta sarke da juna zuciyar ta na harbawa da sauri2 bakinta na rawa Tace, “Lalata? Ni?” Kawai saita fashe da kuka tana barin wajen da sauri, tsaki yah khaleed yaja yana dukan steering din motar sa take ya fara tmbyr kansa to wai ma Ina ruwan sa? Tayi yawo tsirara man can ta matse mata ya Karasa mgnr yana Jan tsaki da haka yabar gidan. Kamla na komawa daki ta rushe da kuka tana toshewa baki to Abinda yafi haka ma idan ya kirata ita ta jawa kanta Dan haka ta fara lallaba zuciyar ta tana tunanin mgnr Ammi, Dan ta lura soyayyar yah khaleed tamkar iska ce me wahalar dame kayan Kara toilet ta shige ta fara wanke idon ta kafin ta sake fita zuwa kitchen Dan taya masu aiki. Da yammacin ranar babu islamiya Dan haka kamla suka shirya da Rahma zasu je gidan Hajia babba Yayar daddyn su Hajia Khadeeja wacce ake Kira Hajia babba Yayar daddyn su ce uwa daya uba daya su kadai iyayen su suka haifa suka rasu Hajia babba kusan Duk itace ta rike daddy har Allah yasa ya girma shiyasa yake ganin ta da mutunci sosai domin itace koman sa yadda yake bata kulawa da soyayyar ‘yan uwantaka yasa Mummy ta fara kishi da ita tun tana boyewa harta fara nunawa a Fili shiyasa Hajia babba bata bi ta kanta daga ita har marasa kunyar ‘ya’yan ta Mami kuwa da ta fara kamun kafa a wajen ta dake abin bana Allah bane itama bata bi ta kanta sai ya kasance Ammi ce kawai matar daddy dake kyautatawa Hajia babba shiyasa take son ‘yarta kamla especially da sunan su yazo daya wato Khadeeja. Cikin matsakaicin gida suke ta zabga sallama Hajia babba dake can daki ta fito tana duban su Tace, “au dama kune kuke ta cika min kunne da ihu?” Dariya suka sa mata kamla Tace, “ai Hajia gani mukayi da alama kunnen naki ya fara tafiya” Hajia babba Tace, “ungo naki Nan wato ma nice na kurmance koh?” Kamla na dariya Tace, “a’a” Nan suka Karasa parlon Suna hiraa kafin suka fara gaisawa

Sun dade a gidan Suna hira kafin sukayi nufin tafiya gida Hajia babba taji dadin zuwan su kwarai har kofar gida ta raka so Tace su gaida gida.tunda suka fito babban layi wata hadaddiyar mota ke binsu a Baya har abin yaso basu tsoro toh abinka da ‘yan kidnapping sunyi yawa a gari ba wuya Ayi wuff da kai, Dan haka da sauri suka fara tare napep Dan kaisu gida dake magrib ta gabato sosai sai ya kasance garin kanon dabon cike yake da goslow harma abin hawa walaha yake dakyar dai suka sami napep din da zatayi hanyar unguwar su, hamdala sukayi a zuciyar su kafin suka shige saidai abin mmkin har yanzu motar Nan bata daina binsu ba, kallon juna sukayi kamla a tsorace Tace, “Rahma har yanzu motar Nan fa binmu take” Rahma itama a Dan tsorace Tace, “naga alama amma muyi fuska kawai tunda Allah yasa mun samu abin hawa har bakin gate zai aje mu yadda da mun isa muyi wuff mu fada gida” Dan murmushi kamla tayi Tace, “Hakan za’ayi” Suna Wannan hirar har suka isa katafaren gidan su Rahma ta mikowa me napep kudin sa Suna fitowa sukaci karo da Wannan motar tsaye kofar gidansu take hanjin cikinsu ya kada Suna mmkin yaushe ta rigasu isowa? Basu san cewa tun Suna bada kudin napep ta wuce su ba, kallon juna sukayi kamla tace, “abinda ya rage kawai muyi fuska kamar bamu san da Wani abin a wajen ba” Rahma Tace, “okay muje” Dukda kirjin su na bugawa haka suka taho Suna kallon dayan gefen kamar basu san Abinda ke tsaye gefen su ba da sauri na cikin motar ya fito cikin cool voice dinsa yace, “barka da yamma ‘yan mata” yi sukayi kamar basu san yanayi ba suka karawa tafiyar su sauri da sauri yasha gabansu yace, “sorry daku nake” tsayawa sukayi Wanda ke gabansu yace, “sunana habib Dan Allah idan ba damuwa inason nayi mgn dake” ya nuna kamla a dan tsorace Tace, “ni kuma?” Murmushi yyi yace, “eh ke din dai Baby” kallon juna sukayi da Rahma, Rahma ta gyada mata Kai alamar ta saurare shi, kamar ba zata yadda ba sai kuma Tace, “toh” Rahma Tace, “bari na jira ki a can” Kamla ta rike hannun ta Tace, “aa ki tsaya” Rahma tace, “ba nisa zanyi ba kamla Ina can wajen” ta nuna Wani waje dake kofar gidan nasu ba yadda ta iya haka ta barta ta tafi, habib ya gyara tsayuwar sa fuskar sa cike da annuri yace, “idan ba matsala zan iya sanin sunan baby?” Dukar da kanta kamla tayi tana yatsina fuska wai baby? Mtwsss, “baby Ina mgn” ya fadi Hakan yana Kokarin leken fuskar ta da sauri ta dago tana duban sa Tace, “Kamla” “wow nice name Kamla” sannan yaci gaba da fadin, “A gsky kamla tun lkcn da idanuwa na suka sauka Akan kyakkyawar fuskar ki sai naji babu wacce tayimin a duniyar sai ke kamla idan nace haka Ina nufin zuciya ta kamu da son ki” yyi mgnr yana taba saitin kirjin sa hade da lumshe ido, duban sa tayi da fararen idanun ta masu kyau ta danyi guntun murmushi kawai tana kauda Kai, juyawar da tayi kuwa saita hango motar yah khaleed tsaye a bayan su yana tsaye shi be karaso ba shi be juya ba gabanta ne ya fadi rass amma kuma saita maze kawai tana duban habib daya zuba mata ido yace, “da fatan kyakkyawa kamla zata amshi tayin soyayyar bawan Allah habib” Dan Jan numfashi kamla tayi tana juya idanun ta Tace, “sai nayi tunani” habib yace, “Kamla so kike zuciyata ta buga?” Da mmki Tace, “kamar yah?” Habib yace, “Duk Inda kaji ance sai anyi tunani toh da alama ba’ayi marhaban dakai ba idan kuwa hasashe na gskyne toh tabbas Ina ruwa kusa da kada..” ya kare mgnr da alamun tausayi, Wani iri taji a ranta Dan haka Tace, “ba haka nake nufi ba amma tunda nace sai nayi tunani ya kamata ka bani lkci” Habib yace, “shikenan kamla ki bani number ki sai muyi mgn” Dan murmushi tayi Tace, “kayi hakuri bani da waya” da mmki yace, “ke din?” Kamla Tace, “da matsala ne?” Saurin girgiza kansa yyi yace, “Ah no ba matsala zan dawo” kamla Tace, “okay” Nan sukayi sallama Rahma dake jiranta ta taso, Rahma Tace, “Yah khaleed ko tsayuwar me yakeyi tun dazu a can?’ Tabe baki kamla tayi Tace, “au ni ban lura bama” Rahma tasa dariya Tace, “toh kodai har kin rufta da Wannan gayen?” Kamla tayi murmushi tana Kai mata bugu Tace, “banson wulakanci” Rahma na dariyar Tace, “ai gskyne gashi kin fara mance waye a gaban ki” kamla Tace, “Wlh kinci bashi” da haka suka Shiga gidan kamla na zayyane mata yadda sukayi, Rahma Tace, “gsky gayen yyi Ina muku fatan nasara” Kamla ta yatsina fuska Tace, “ke ni beyimin ba” Rahma Tace, “ke yanzu Ina makusa agun habib? Gashi da kamala gaye Dan kwalisa kamla tabe baki tayi Tace, “ke kika ga haka ni banji yamin ba” Rahma Tace, “ki sake tunani” kamla Tace, “naji zanyi” da haka suka rabu kowa ta nufi sashen su. A nutse Yah khaleed ya karaso cikin gidan nasu koda yake cikin motar ma a parking lot ya dade be fito ba saida aka fara kiran magrib ya fito, Direct sashen su ya wuce tun daga parlo ya aje kayan hannun sa ya shige toilet Dan yin alwala, yana fitowa masallaci ya hadu da daddy Ashe ya dawo, gaisawa sukayi daddy yace, “Accountant ka dawo kenan” Yah khaleed yana murmushin yake yace, “eh daddy bansan ka dawo ba” daddy yace, “Nima dazun Nan na shigo” da haka suka Karasa masallaci, bayan sun fito Suna dawowa gida daddy yace, “meke damunka naga kamar ranka a bace?” Sosa keya Yah khaleed yyi yace, “am ba komai daddy” daddy yace, “toh a dinga hakuri dai da rayuwa” Yah khaleed yace, “Insha Allahu daddy aci gaba da tayamu da Addu’a,” daddy yace, “kullum munayi Allah dai ya Amsa Mana” Yah khaleed yace, “Ameen” Suna isa gidan Daddy yyi bangaren shi Yah khaleed yyi tsaye yana tufka da warwara can dai ya nufi sashen Ammi, Ammi na kokarin fitowa suka hadu a kofa, dukar da kai yyi yace, “Ammi barka da yamma” Cikin sakin fuska Tace, “Barka” shiru ne ya ratsa wajen kafin yace, “kamla na ciki kuwa?” Ammi ta Karasa fitowa waje Tace, “Shiga ka duba ta” tana gama fadin haka tayi gaba, wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki kafin ya wuce cikin parlon zama yyi saman kujerar parlon ya hade kafafun sa duka biyun yana girgizawa, Kamla batasan da zuwan sa ba ta fito ba hijab a jikin ta doguwar riga ce me santsi a jikinta ta kama ta sosai shape dinnan ya fito Masha Allah, Dafe kirji tayi a tsorace cikin daburcewa Tace, “am..yah.. khaleed kaine?…Am..” ta Rasa ma Abinda zatace kawai ta juya da sauri zata koma daki taji ya damko hannun ta, dagowa tayi a firgice zata kwace taga fuskar Nan tasa a hade, jikinta ne yahau rawa murya na bari Tace, “yah khaleed Hi…jab zan sako” tayi mgnr a rarrabe, Kamar bazai saketa ba can kuma yace, “kina sawa ki sameni a waje” da mmki Tace, “waje kuma?” Wata irin harara ya mako mata tayi sauri kame bakinta tana girgiza kai Tace, “to..to..toh gani Nan” tana gama fadin haka ta juya daki da sauri Yah khaleed kuma ya fice daga parlo yana shirya hukuncin dazai mata ganin da yyi mata dazu.

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!