Na Jawa Kaina Hausa Novel

Na jawa kaina

Na Jawa Kaina Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Na jawa kaina

NAJA WA KAINA

(Asanadin son abin duniya)

 

 

Story and writing by

Nafeesat m.aliyu

(Feenah)

 

Bisimillahir rahmanirrahim

Ina godiya da Allah subahanahu wata,ala daya bani ikon fara wannan book nawa,sannan ina fatan rabbi ya nunamun karshen sa lafiya da kuma ikon samun isar da sakon dake cikin labarin,sannan ina maraba da masoya gamai kokarin yimun gyara ko wasu shawar wari zai iya tuntubata ta wannan number 07062481557 daga taku nafeesat m.aliyu (feenah).

 

 

Page 1

 

5:15 kano state

 

Cikin nutsuwa nake kallon saman ginin Islamiyar da naga antashi daliban wannan makaranta awannan lokaci *madrasatus* *sabilarrashd* *islamiyya* shine sunan da naga ya bayyana asaman ginin wannan islamiyya,sosai ”yan mata ke tuttud’owa daga cikin wannan makaranta ko wacce na nufar gida tare da ayarin ”yan unguwar su ko abokiyar tafiyar ta harma ga wanda suka kasance ”yan gida daya.

 

Wasu mata san ”yan mata nagani su uku daya daga cikin su ba zata wuce 17 years ba inda sauran ”yan mata biyun basufi 19 years ba,cikin nutsuwa suke tafiya kowacce hannunta dauke da jakar islamiyyar ta,karamar cikin nasu tadan zarta su a tafiyar Yayinda su kuma ”yan mata biyun ke biye da ita abaya,murmushi Hafsat tayi tare da Dan dafa kafadar Jidda cike da fara’a ”qawata banji kince mun komai ba game da alaqar ku da Yasayyadi Khalil bayan naji wani labari”ta karashe maganar tana kallon qawartata wacce ta kira da Jidda,ya tsine fuska Jidda tayi tare da fad’in ”oh ni Hauwa mutane ba,a rabasu da abunda babu ruwan su yanzu kina nufin har kin ji wannan magana wacce shekaran jiya jiyan nan akayita”ta karashe maganar tana kama baki,qawata kenan sai kace bakisan yanda labarin soyayyar ku da malam Khalil ta zagaye unguwa da Islamiyya ba wannan ai ba,abun mamaki bane kinga nidai bani insha ya ake ciki kinga mun kusa rabuwa gashi Zarah sai nisa take miki”Hmmm Hafsat kenan kinsan ai ko baki tambayeni ba zan fadamiki dama magabatan Malam Khalil ne sukazo gurin Abban mu game da maganar sunason kawo kud’in aure harma dasa rana kamar yanda kikaji ana yama d’id’in maganar agari”wata muguwar runguma Hafsat taiwa Jidda har saida tadan tsoratata tana dariya”Allah qawata kice abu dai zai tabbata insha Allah Jidda amaryar malam Khalil naji Dad’in labarin nan sosai qawata ”Hmmm Jidda tafada tare da yin wani quntun murmushi wanda bai karasa har zuciyar taba tana fad’in”kinga ni inkin gama murnar kamar wacce akaiwa wani shahararran albushir ko wani abun azo agani ya faru zan wuce Zarah tamun nisa sai anjima”ta karashe maganar tare da yin gaba batare da tajira abunda Hafsat zata ceba,girgiza kai kawai Hafsat tai tare da nufar kwanar da sata sadata da kofar gidan su.

 

Cikin sauri sauri Jidda ta kamo Jidda tare da fad’in”dan wulaqanci sai wani zabga sauri kike saboda ki rigani zuwa gida Abba yace ina na tsaya?ki jajamun fada agurin Abba ina zaman zaman haka kawai”tom aunty Jidda so kike nima nai laifin bayan kinsan Abba yasan lokacin da ake tashin mu Islamiyya kuma in yaga bamu shigo da wuriba zaiyi fada yace ina muka tsaya””to ‘yar masu da baki sai kimun shuru tunda dai gani na karaso ko.

 

 

 

Kadan kenan daga cikin Sabin labarina mai suna *NAJAWA* *KAINA* mai taken (asanadin son abun duniya) labarina Free book ne saidai comment da addu’o’i danake buqata daga gare ku shine tukuicin da nakeso kuna bani,ga Link d’in group d’in *NAJAWA* *KAINA* *Fans* amma in kinsan baza kina comments ba karma kishiga Dan Allah.

 

Na jawa kaina

 

Download Hausa Novel Reading App

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.