Nadama Hausa Novels Complete
NADAMA 1-2-& 3​
.
Wannan labarin sadaukarwa ne ga yayata margayiya
Fatima (Allah Ya lullube kabarinki Fatima da rahamarSa.
Amin)
.
Shimfida.
.
Birnin Shehu.
.
A bisa wani titi cikin wata mota kirar Ferrari launin toka,
wasu abokai ne zaune suna tafiya sun yi shiru sai ka ce
wadanda ruwa ya cinye. Dayan wanda ke tuka motar da
ka kalli fuskarsa za ka fahimci ya na cikin damuwa,
dayan kuma wanda yake zaune a kujerar mai zaman
banza, fuskarsa ba yabo ba fallasa, akalla sun shafe
sama da mintina goma sha biyar ba wanda ya ce wa
dan uwansa kala. A wannan yanayin suka karya kwanar
wata unguwa ta masu hannu da shuni, daidai wani
kayataccen gida suka gurfanar da motar tasu, dayan
wanda yake janye da motar ya juyo ya kalli abokin nasa
cikin damuwa ya ce “ka tabbata nan ne gidan kuwa
Aliyu?” Wanda ke amsa sunan na Aliyu ya dago kai ya
ce “haka nake zato ba wai na tabbata ba ne, amma me
zai hana mu tambaya?” Suka fito daga motar suka yi
tsaye suna rabon ido ko za su samu wanda za su
tambaya, sun shafe kusan mintina biyar a hakan kafin
su hango wani yaro ya fito daga wani gida makwafcin
gidan da suke tsaye a kofarsa, cike da zumudi wanda
yake cikin damuwar yai kiran sa.
“Don Allah nan ne gidansu Rukayya Abubakar Rabah?”
ya tambayi yaron bayan ya karaso inda suke, yaron ya
amsa da “eh nan ne”.
“Don Allah ka kira mana ita mana” yaron yai jim! Kamar
ba zai je ba kuma dai sai ya kunna kai cikin gidan, cikin
dakikun da ba za su haura sittin ba yaron ya dawo “wai
an ce waye?” “Je ka ce Zayyad ne”. Yaron ya sake
juyawa ya koma cikin gidan.
Cikin mintunan da ba za su haura bakwai ba sai ga
wata matashiyar budurwa ta fito daga cikin gidan. Cikin
sanyin jiki ta karaso inda suke kallo daya za ka yi wa
fuskarta ka fahimci cewar tana cike da alhini.
“Ina wuninku?” ta fada a sanyaye, Suka amsa a kusan
tare da “lafiya kalau ya gida?” Zayyad bai ko jira
amsawar ta ba ya ci gaba da magana a kokarinsa na
son gabatar da dalilin zuwan su wajenta “Rukayya wani
taimako ne na zo ki min please”.
Ya dan tsahirta sannan ya ci gaba “na daina ganin
kawarki Zeenat ne kwana biyu, kuma a zahirin gaskiya
ina son ganin ta saboda in ba ta hakuri a kan abubuwan
da na yi mata a baya”.
Ya dan numfasa domin ba ta dama ko za ta ce wani
abu ganin ta yi shiru sai ya ci gaba “Lambar wayarta
nake so ki ba ni, ko kuma ki kwatanta min gidansu
please”.
Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba can! Kuma sai
ta ja dogon numfashi.
“Ka yi hakuri Zayyad…….”
Maganar ta makale a fatar bakinta ta kasa karasawa.
A dan sanyaye ya matso kusa gare ta “Me ya faru?
Daure fada min mana” ya fada cikin kagauta da son jin
abin da zai fito bakinta.
Cikin murya mai kama da kuka ta ce “Allah Ya yi wa
Zeenat cikawa, yau sati hudu kenan”.
Kamar shigar alburushi a kahon zuciya haka ya ji
zancen nata, bai san lokacin da ya dafe kai ya sunkuya
kasa ba cikin sambatu ya rika fadin “Haba Zeenat kar ki
min haka mana ya za ki tafi ki bar ni? Me yasa ba ki
tashi tafiya ba sai da na fara son ki? Don Allah ki dawo,
Wallahi! In ba ke, ba zan iya rayuwa ba”.
Ya shafe sama da mintina takwas cikin wannan yanayi,
sai da Aliyu ya kama shi ya saka shi mota ya zaunar
da shi a kujerar mai zaman banza shi kuwa ya zauna a
kujerar direba, ya tayar da motar suka bar layin.
Har suka bar layin Zayyad bai daina sambatu ba. Aliyu
ya juyo ya kalle shi cike da tausayi ya ce “Addu’a ya
kamata ka yi mata Zayyad ba kuka ba, kukan nan da
kai har ita ba zai amfane ku da komai ba, ba dai zai sa
ta dawo ba, haka kuma ba zai mata amfani a can ba”.
“Ka bar ni kawai in yi kuka Aliyu ko zan ji sanyi a raina,
meye amfanin rayuwata? Ai ba abin da ya kamace ni a
yanzu sai kuka, tun da na riga na rasa wacce ke so na
fiye da rayuwarta, babban bakin cikina na kasa amsa
mata son da take min in faranta mata rai, ga shi yanzu
damar yin haka ta kubuce min” ya ida fashe wa da kuka
cikin murya mai karfi.
Aliyu ya dafa kafadarsa cikin yanayin rarrashi ya ce “ka
daina kuka abokina ba fa kuka ne mafita gare ka ba,
dama abin da na yi ta nuna maka tun farko ka kasa
fahimta kenan, yarinyar nan ta so ka irin son da ko a
labaran soyayya ban taba jin an yi ma wani irin sa ba,
amma ka watsa mata kasa a ido, duk lokacin da na
fada maka gaskiya a kan ka daina dizga ta, ko da ba za
ka so ta ba, idan ka nuna mata kulawa za ka rage
mata dafin dake zuciyarta sai ka yi biris da maganata
har laifina kake gani.
Ba na raba daya biyu bakin cikinka ne ya yi sanadiyar
mutuwarta, na tabbata alhakinta ma ba zai bar ka ba,
saboda haka addu’a ya kamata ka rika yi mata, ka
kuma ci gaba da Istigifari ko Allah Zai yafe ma”.
Kwarai maganar abokin nasa ta yi tasiri a zuciyarsa,
tabbas ya san ya zalince ta, ga shi lokacin da ya gano
hakan ba ta raye bare ya nemi afuwarta, yanzu ina zai
kai alhakinta da ke bisa kansa? NADAMA mai tarin
yawa ta zo masa, ya ji gabadaya duniyar ta yi masa
kunci. Sannu a hankali zuciyarsa ta fara hasko masa
abubuwan da suka yi ta faruwa a cikin shekaru biyun da
suka gabata.
September 2010.
.
A cikin wani makeken dakin taro (hall), cikin wata
makekiyar otal (hotel), wasu masoya masu shirin zama
ma’aurata ne ke gudanar da bikin murnar aurensu, bikin
sai gudana yake a tsare cikin ban sha’awa, ga alama
bikin ya na nisahadantar da mahalartansa, idan ka yi la’
akari da yadda fuskar kowa take cike da murmushi.
Bayan raye-raye daga wasu mawaka sai mai gabatarwa
ya karbi abin maganar ya fara magana
“Ah! Ba tare da bata lokaci ba yanzu za mu kira babban
abokin ango, domin mu ji takaitaccen tarihin ango daga
bakinsa. Zayyad in ka na kusa muna bukatar ka a nan
domin mu ji waye ango daga bakinka”.
.
Wani kyakkawan saurayi dogo, wankan tarwada sanye
cikin farar shadda mai surfani launin siminti, ya sanya
takalma, su ma launin siminti, hular da ya sanya ma
launin siminti ce, ya adana idanuwansa da wani
madaidaicin gilashi fari, daure a madaidaicin hannunsa
agogon fata ne launin siminti. wankan ya yi mutukar
fitowa da kyawun surarsa. Ya taso cikin tafiyar kasaita
ya karbi abin maganar ya fara jawabinsa.
Hakika ba ‘yan mata ba hatta samarin dake wurin sai
da saurayin ya birge su. ‘Yan mata da yawa ya tafi da
imaninsu yayin da wasu suka ci buri a kansa.
.
Cikin tattausar murya mai cike da dadin sauraro da
kuma gwaninta ya rika kwararo tarihin angon. Da ya
kammala gabadaya wurin ya dau tafi saboda ya gama
birge kowa. Ya mika abin maganar hannun mai
gabatarwar ya sake juyowa cikin tafiyarsa ta kasaita ya
nufi kujerun baya ya kadaice kansa shi kadai ya ci gaba
da kallon tsare-tsaren bikin. Haka yake dama shi bai
cika son shiga jama’a ba, mutane da yawa su kan yi wa
halayyar tasa mummunar fahimta ta hanyar suffanta
shi da mutum mai girman kai da ji-ji da kai, sai dai a
zahirin gaskia ga duk wanda ya fahimce shi zai
tabbatar da duka wadannan halayen ba shi da su,
kawai dai za a iya kiransa da miskilin mutum mara son
hayaniya.
.
Daga nesa ya na iya hango lokacin da wata santaleliyar
budurwa ta mike daga inda ta ke zaune ta nufo wurin
da yake zaune, hakika yarinyar ta birge shi, domin ta
mallaki duk wani abu da yake so a wurin ‘ya mace, baka
ce doguwa, siririya, sai dai bakin nata mai sheki ne,
kirar jikinta kuwa irin wannan ce da samari ke kira da
coca-cola shape, ta na da dara-daran idanuwa, masu
sanya zuciyar duk wanda aka yiwa fari da su suma na
wucin gadi, bakinta kuwa madaidaici ne dauke da
tausasan labba masu kauri, fuskarta doguwa ce,
habarta ma haka. Ji ya yi kamar ya tare ta idan ta
karaso, amma kuma miskilancinsa sai ya motsa ya ji ba
zai iya yin hakan ba, ya dauka za ta zaga ne ta fita a
hall din amma ga mamakinsa ta na karasowa in da yake
sai ya ga ta janyo kujera kusa da shi ta zauna ya
zamana suna fuskantar juna shi da ita, wani murmushi
mai rikatar da kwakwalwar duk saurayin da aka jefa da
shi ta jefa masa sannan ta ce “Sannunka” cikin izza ya
amsa mata
“Yauwa sannunki”
Ta sake cewa “Sunana Zeenat, na ga ka dawo baya ka
zauna kai kadai shi ne na ga bai kamata babban abokin
ango a ce ya zauna baya kuma shi kadai ba don haka
ne na ce bari in zo in taya ka hira, Allah Ya sa dai ban
yi laifi ba?”
.
Haushin ta ne ya kama shi, kamar ya rufe ta da duka.
Dama hangen kitse ne wai ashe ya yi wa rogo? A
tsarinsa ya fi son mace mai aji ko da kuwa ba ta da
kyau, amma wannan ga ta kyakkyawa ajin farko, ta
kasa rike ajinta, mintina kadan da ya hango tahowar ta,
zuciyarsa makare take da muradin mallakarta, amma
yanzu sai ya nemi muradin a zuciyarsa ya rasa. Danne
abin da yake ji a zuciyarsa ya yi ya ce mata “kar ki
damu ba ki yi laifi ba”.
Jin ya ce haka sai ta ci gaba da jan sa da hira “ba ka
fada min sunanka ba ga shi ni na fada maka nawa”
.
“Zayyad” ya fada kai tsaye. Fari ta yi da idanuwanta
sannan ta ce “Wow! Suna mai dadi”
“na gode” ya sake cewa da
.
Usman Auwalu zng:
.
NADAMA… 2
.
Cikin wata irin murya ta jan hankali ta sake cewa
“Turancinka ya birge ni, a ina kake karatu ne?” Cikin
kosawa da tambayoyin nata ya ce “Usman Danfodio
University, ina karantar kimiyar siyasa ne (Political
Science) UG 3”.
Ya fada mata har abinda ba ta tambaya ba ne saboda
ya san za ta tambaya, shi kuwa duk ya kosa ta daga ta
bashi guri.
Ya zata hirar za ta tsaya a nan amma kuma sai ya ji ta
sake cewa “kawo wayarka in saka ma lambata, ina so
mu rika gaisawa”. Hannu ya saka a aljihu ba tare da
gardama ba ya dauko wayarsa kirar BlackBerry Punch
ya mika mata, da hanzarinta ta karba ta saka lambar ta
kira kanta sannan ta mika masa.
Mikewa ya yi daga kujerar fuska a yamutse ya ce mata
“i have something to do outside (Ina da abin da zan yi a
waje)”. ba tare da ya jira me za ta ce ba ya fice daga
hall din.
Murmushi ta yi tare da fadin “Ok till we met again (to
sai mun sake haduwa)”.
.
A gajiye Zayyad ya koma gida saboda haka, da isar sa
katifa kawai ya nema ya kwanta don ya huce gajiyar da
ya debo wajen biki, bai jima a kwancen ba ya ji rurin
wayarsa alamar shigowar sako, ya so ya kyale sakon
har ajima ya duba saboda rubdugun da gajiyar ta yi wa
gabobin jikinsa, sai kuma ya mike ya dauko wayar bisa
tunanin cewar sakon zai iya kasancewa Urgent (na
gaggawa) ya na dubawa ya ga wata bakuwar lamba ce
ta turo sakon, sai ya bude ya fara karantawa kamar
haka:
.
“Assalam Zayyad ya ka ke? Ba sai na tambaye ka ba na
san gajiyar biki baibaye take da kai, saboda haka ne na
ga ya dace sakon ban gajiya ta ya riske ka a daidai
wannan lokacin. Ka huta lafiya.
.
Zeenat.”
.
Har ya gama karanta sakon bai fahimci ko sakon waye
ba, sai a karshe da ya ga sunan Zeenat sannan fa ya
tuna da dazu wurin bikin ya hadu da wata har ya ba ta
lambarsa.
.
“Wai wannan wace irin mace ce haka, sai kokarin cuso
kanta take wurin saurayi ba ta ko jin kunya, ba ta ko
damuwa da zubar da ajin da take” ya ja tsaki ya ajiye
wayar ya koma yai kwanciyarsa.
.
Washe gari ma ko da ya farka daga bacci ya tarar da
sakonta, bayan ya karanta tsaki ya yi ya goge.
Haka sakuna, da kiraye-kirayen wayarta suka ci gaba da
zarya a wayarsa, ta na nuna masa kauna, gogan ko a
jikinsa, ganin ya ki ba ta kulawa sai ta shiga tunanin ko
bai fahimci manufarta ba ne, hakan ya sa ta fitowa
baro-baro ta fada masa ita fa son sa take yi, hakan da
ta fada masa shi ne ya kara cusa jin haushinta cikin
zuciyarsa, kiran ta ya yi a waya tana dagawa ya ce
“yanzu ke don Allah ko kunya ba za ki ji ba ki buda baki
ki ce wai ki na so na? To ya isa haka ki fice min a ido
or else i will humiliate you”. Bai tsaya sauraron amsar
da za fada masa ba ya kashe wayar. Ta sake kiran sa
ya ki dagawa don haka sai ta turo masa sakon kar ta
kwana.
.
“Haba Zayyad me ye aibu a cikin bayyana soyayyata a
gare ka, ka fahimce ni Wallahi ina mutukar son ka shi
ya sa na kasa danne abin a zuciyata”.
.
Duk lokacin da ta turo masa sako ko ta kira shi sai ya
ji kamar ya shake wuyanta ta mutu a huta, ya sha fada
mata maganganu masu zafi da tozarci, idan ta kira shi,
duk don ta daina son sa amma kamar hura wutar son
nasa yake yi a cikin zuciyarta. Kullum sai dai ta yi
murmushi ta ce “meye laifina don na ce ina sonka
Zayyad, hakika babu macen da ba za ta yi alfaharin
mallakarka a matsayin masoyi ba, ka ga kuwa don ni na
fitar da maitata fili bai kamata ka ga laifina ba”.
.
Daga karshe da ya fahimci ba za ta daina damuwarsa
ba ya yanke shawarar sauya layin wayarsa. Hakan
kuwa ya yi. Sauya layin da ya yi ya huta da
damuwarta, har ya fara tunanin cewa ya yada kwalllon
mangwaro yanzu zai huta da kuda Ashe yanzu ma
kudan suka fara bin sa.
.
.
Bayan wata daya da wasu ‘yan kwanaki Zayyad ya na
zaune a kofar gidansu, shi da abokinsa Aliyu suna hira,
wata mota kirar Toyota Yaris launin bula mai duhu, ta
yi fakin kofar gidan nasu, wasu kyawawan ‘yan mata
biyu suka fito daga cikin motar, har za su wuce cikin
gidan, sai ya ga dayar ta nuno su, sai kuma ya ga sun
nufo inda suke, sai da suka kusanto sai ya fahimci
Zeenat ce da wata wacce yake zaton kawarta ce, shi
har ya manta da ita, sai yanzu da ya ganta ya tuna da
ita, da fara’arta ta karaso inda suke, yayin da shi kuwa
ya daure fuska kamar wanda aka aiko wa da sakon
mutuwa. Cikin salon jan hankali ta ce “sannunku! Dama
Zayyad nan ne gidanku? Lallai yau a sa’a na fito”. Cikin
tsananin bacin rai ya daka mata tsawa “wai ke wace
irin ballagaza ce, me kuma kika zo yi gidanmu?”.
Idan har ta ji ciwon tsawar da yai mata da kuma kiran
ta ballagaza da ya yi, to ba ta nuna a fuskarta ba,
murmushi ta yi sannan ta ce “Ballaganzacin me na yi
Zayyad? Laifi ne zuwa gidan naku? Na rako kawata
Rukayya ne, ban ko san nan ne gidan naku ba sai da na
ganka a zaune, na ga bai kamata na wuce ba mu gaisa
ba, meye laifi a cikin yin hakan?” Ta karashe maganarta
da yin tambaya.
A harzuke ya ci gaba da fadin “sai kokarin cusa min
kanki kike ta yi, na yi ta maki hannunki mai sanda kin
ki, ki fahimta, na fahimci ba kya fahimtar yaren kawaici,
dole sai na maki baro-baro sannan za ki fahimta. Ba na
sonki, ko so dole ne? Zai fi kyau ki yi gaggawar taka
wa wawiyar zuciyarki birki tun ba ta kai ki ga yin dana
sani ba”.
.
Aliyu da ke zaune yana saurarar abinda ke faruwa ya
soke kansa kasa cikin jin haushin abokin nasa. Ita kuwa
Zeenat murmusawa ta sake yi sannan ta ce “To meye
aibu don na ce ina sonka Zayyad, ka sani ba ni na saka
wa kaina sonka ba, da ina da hali da na hana sonka
shiga cikin zuciyata, shi so yana Shiga zuciya ne ba tare
da shawartar zuciyar da zai shiga ba, ya kan yi shigar
ba zata ne kamar yanda yai wa tawa zuciyar. Ba zan ga
laifinka ba duk abinda ka yi min, sai dai ka sani ba zan
iya hana zuciyata sonka ba, sai dai duk abinda zaka yi
min ka yi min”. Kawar tata dake tsaye tun zuwan su
wurin ba ta ce uffan ba, ita ce ta ja hannunta suka yi
cikin gidan.
Bayan shigewar su Aliyu ya dago fuska cikin fushi ya ce
“Haba Zayyad! Wannan wace irin rayuwa ce haka, don
ta ce ta na sonka, bai kamata ta fuskanci wannan
tozarci daga gare ka ba, samari nawa ne a garin nan ba
ta ce ta na son kowa ba sai kai, ai ko da wasa mutum
ya ce ya na sonka ya gama maka komai. Sannan da
ganinta ba ka bukatar a tsaya fada maka ka san ba wai
ta rasa masu sonta ba ne, shi yasa ta ce ta na sonka”.
Zayyad shi ma a kufule ya ce da Aliyu “idan har ta na
da masoyan me yasa ba ta tsaya wurinsu ba, kuma
tozarcin ai ita ta ja wa kanta, don na yi ta kokarin zille
mata, ita ce ke dada manne min, in ban da ballagazanci
me zai sa ta biyo ni har gida?”
Cike da takaici Aliyu ya sake cewa “kar fa ka yi amfani
da damar da kake da ita a kan yarinyar nan, ganin ta na
tsananin sonka ka ci gaba da wulakanta ta, ka sani
Allan da Ya saka mata son ka a zuciyarta, ba tare da
shawartar ta ba kai ma Zai iya jarabtar ka da son ta
fiye da yadda take son ka a yanzu………..
.
Zayyad ya tari numfashinsa “God forbid, Aliyu ya
kamata ka daina shiga gonata, yarinyar nan in ma ta
biya ka ne ka yi mata kamfen, ka sani kamfenka bai
samu karbuwa ba, sai in ce Allah raka taki gona”.
.
Aliyu ya yi murmushin takaici sannan ya ce ” in ma dai
biya na ta yi in mata kamfen, ka sani ina yin sa ne a
inda ya kamata, amma dai ka sani ya kamata ka yi
tunani”.
[10:42AM, 12/26/2015] Usman Auwalu zng: NADAMA… 3
.
“Ka ga Aliyu mu bar maganar haka please”. Zayyad ya
fada a kufule
.
“Tun da ba ka son gaskiya you must said so, ai kamata
ma ya yi ka yi wa Allah godiya da har ya cusa son ka a
cikin zuciyar wannan kyakkyawa yarinya”. Shi ma Aliyun
ya mayar masa a kufule.
.
“Ba za ka bar maganar ba kenan” Zayyad ya fada tare
da daga masa hannu.
.
“Eh ba zan daina ba, meye amfanin abotakarmu in dai
har zan ga ka kaucewa hanya ba fada maka gaskiya
ba”.
.
Mikiwa tsaye Zayyad ya yi ya fara tafiya “ba kuwa da ni
za ka ci gaba da yin maganar ba.
.
Sororo Aliyu ya yi ya na mamakin abokin nasa saboda
ya fada masa gaskiya shi ne ya ta shi ya ba shi wuri.
Girgiza kai ya yi kana ya shige motarsa ya nufi gida.
Shi kuwa Zayyad don ma kar ya kara sake haduwa da
ita unguwar ya bari gabadaya sai dare ya dawo gida.
.
BAYAN WASU KWANAKI
.
Cike da annushuwa, da jin dadi yake jan motar, za ka
iya fahimtar haka ne ta la’akari da yanda yake ta faman
murmushi shi kadai tare da kada kansa kamar wani
kadangare.
Daga Unguwar su Aliyu yake bayan sun gama kallon
kwallo shi ne ya nufo gida,
Farin cikin nasa bai rasa nasaba da cinye Real Madrid
din da Bercelona ta yi 3-0, hadi kuma da sautin wakar
Aminu Dumbulum mai suna “Sauda’i” dake ratsa dodon
kunnuwansa, yana cikin saurarar wakar ne aka zo daidai
wani baiti da yake cewa
.
“Wallahi So wani kaya ne
bai daukuwa idan ba a shirya ba”.
.
Ya girgiza kai cikin gamsuwa da abinda mawakin ya ce,
tare da cewa “Haka yake Dumbulum”.
A haka ya karyo kwanar layinsu ya iso kofar gidan nasu
ya yi ham (horn) maigadi ya zo ya bude masa ya shige,
ya tsugunnar da motarsa a inda ya saba tsugunnar da
ita, har zai wuce kuryar gidan sai hankalinsa ya kai kan
wata bakuwar mota dake tsugunne kusa da inda ya
ajiye tasa, tabbas ya san mai motar, sai dai kuma ya
kasa tuna inda ya san mai motar. A haka ya shige
kuryar gidan nasu ya na so ya tuno inda ya san mai
motar amma kuma ya kasa tunawa.
.
Ga mamakinsa ya na isa cikin farfajiyar gidan sai ya
tarar da Zeenat zaune ta dage sai wanke-wanke take yi
cikin gidan nasu. Da fara’arta ta gaishe shi “Sannu da
zuwa yaya Zayyad”. bai amsa ba sai ma harara da ya
bi ta da ita, sannan ya wuce dakin mahaifiyarsa, bayan
ya shiga ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa cikin fara’a,
har zai yi waje sai ya ji ta ce “Surukata kuwa na nan ba
ta tafi ba”.
.
Cikin rashin fahimta Zayyad ya juyo ya ce “wace
surukarki hajiya?”
.
“Zeenat mana ko ba ka ganta ba? Gaskiya ka yi sa’a,
kyakkyawar yarinya da ita, ga ta da kirki, duk ta zo
gidan nan ita ke yin duk aikace-aikacen gidan nan, duk
yanda na yi kokarin hana ta sai ta yi, har wanki take
min, na yi ta nuna mata ta bari tunda ga masu aiki nan
sai su yi, amma ta ki dainawa. Tun ma ba ku yi aure ba
kenan, to ina ga kun yi auren. Yarinyar kirki Allah Ya yi
mata albarka Ya kuma nuna min an daura maku aure
tare”. Mahaifiyar tasa ta fada cikin annushuwa.
.
Shiru kawai ya yi tare da soke kansa kasa “wato dama
ta saba zuwa gidan na su kenan ta na kamun kafa, har
ta siye soyayyar mahaifiyarsa, lallai duk inda ake neman
ballagazar mace yarinyar nan ta wuce nan, tabbas sai
ya yi da gaske sannan zai fincike ta daga jikinsa. Ya
fada a ransa, tare da afkawa kogin tunanin ina zai samu
mafita. Cikin sanyin jiki ya fice daga dakin ya nufi nasa
daki.
.
Sansanyar iskar dake busowa a hankali sakamakon
bishiyoyi dake kada rassansu cikin nutsuwa da
kwanciyar hankali, hade da lumshewar da garin ya yi ba
karamin taimakawa ya yi wurin ba wa jama’a lasisin
yawo cikin garin, tare da cire fargabar dake zukatansu
na barazanar da suke fuskanta daga zafin rana dake
shirin tasafa kwakwalwar duk wanda ya yi yunkurin fita
cikin ranar da nufin magance wasu matsalolinsa.
Daga cikin wadanda wannan yanayin ya ba wa lasisin
fita har da Zayyad da Aliyu, lasisin da suka samu ne ya
basu damar shiga kasuwa don sayen kayan bukatun
rayuwar yau da kullum.
Sun fito cikin wani shagon siyar da agogo kenan sai
suka yi kicibis da Zeenat, yau ma tare suke da kawarta
Rukayya da kuma wata wacce bai san ko wace ce ba.
Zayyad na ganinta ya yi saurin kawar da kansa kamar
bai gan su ba, ita kuma ganin su da ta yi sai farin
cikinta ya karu, cikin nuna kulawa ta karaso inda suke,
ta gaishe su, kawarta Rukayya da dayar ma haka. Aliyu
ya amsa cikin sakin fuska, Zayyad ko kallon arziki bai
mu su ba bare su samu arzikin amsa musu gaisuwar.
Idan ta ji zafin hakan to ba ta nuna A fuskarta ba sai
ma fara’arta da ta karu ta ce masa “Zayyad ina magana
ka kyale ni, ko na yi ma laifi ne?”.
Abinda kawai ya zo ran Zayyad shi ne, yanzu ne
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels PdfÂ
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
lokacin da ya fi dacewa ya yakice ta daga jikinsa, don
haka maimakon ya amsa mata sai kawai ya daga
hannu ya wanke ta da mari, ji kake Tass!! Karar marin
ya yi sanadiyar janyo hankalin mutanen da ke wurin,
kowa ya sako musu na mujiya yana kokarin ya fahimci
me ke faruwa ganin haka sai ya shiga zuba mata rashin
mutunci son ransa, cikin karaji yake cewa “Na ce ba na
son ki, ana so dole ne? kin nace min sai ka ce cingam,
Wallahi idan ba ki kyale ni ba, sai na shuka maki rashin
mutunci, ballagaza kawai mara aji”.
Lokaci daya mamaki ya ziyarci zukatan wasu daga
jama’ar da suka zubo musu na mujiyar, ganin yadda
ake yarfa tsaleliyar budurwa irin Zeenat cikin kasuwa,
wasu kuwa tausayinta ne ya kama su, watakila sun
tausaya mata ne da suka fahimci ta na cikin koshin
wahala ne (son ma so wani) yayin da kuma wasu
haushinta ya kama su tare da jin Zayyad ya birge su.
Zeenat ta dago kai dafe da kunci ta ce “meye laifina
Zayyad, saboda na ce ina sonka ne ka mare ni, haba!
Zayyad ashe so zai iya zama laifi? Ba zan ga laifinka
ba, amma ka sani da ina da ikon tankwara zuciyata ta
daina son ka da tuni na yi hakan, amma zan ci gaba da
rokon Allah akan ya cire min sonka a cikin zuciyata in
hakan shi ya fi zama alkhari.
Zayyad bai ko tsaya saurarar abinda take fada ba ya sa
kai ya wucewarsa, Aliyu kuwa sai ya tsaya yana
rarrashinta. Cikin tausayawa da kuma jin haushin
abokin nasa.
A mota Aliyu ya taradda Zayyad ya na jiransa ya bude
motar ya shiga sannan ya juyo ya kalli Zayyad ransa
bace ya ce masa
“Anya ka na da imani Zayyad?
Shin ka san tarin kunya da kawaicin da mata suke da
shi? Amma duk ta ajiye su gefe ta fada maka ta na son
ka?
Wai kuwa ka san yanda zafin so yake a zuciyar wanda
masoyinsa ya ki amsa tayin soyayyarsa?
Ka kuwa san yanda dafin so yake hana zuciyar masoyi
sukuni?
Kana kuwa da masaniyar yanda gubar so ke cin
zukatan masoya ta hana su runtsawa a darare
barkatai?
Ka na so ka ce da ni ba ka san yanda Zuciyar masoyi
ke kuntatuwa da kewar masoyinta a lokacin da yai
mata nisa ba?
Haba Zayyad ba za ka bar yarinyar nan da duk
wadannan nau’ukan azabtarwa da ciwon sonka ke mata
ba sai ka hada mata da tozarci irin wannan? Wallahi ina
jiye maka tsoron ranar da alhakinta zai kama ka.”
Zayyad ya kalle shi cikin rashin damuwa ya ce
“wadannan nau’ukan azabtarwa kuma ai kai ka san da
su kai da kake yin soyayyar ni da ba na yi ta ya ya zan
sani, ni dai abin da na sani kawai mafita ce na samar
wa kaina. Saboda bacin rai da takaicin abokin nasa
Aliyu shiru ya yi bai kara ce masa uffan ba har suka isa
gida a haka suka rabu ko sallama ba su yi ba
Whatapps
07066055575
​
Name: | [Nadama Hausa Novels Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Allah ya Kara basira
I like it this novel.