Hausa Novels

Nafisat Abdullahi ta bayyana dalilin ficewa daga fim din Labarina

Nafisat Abdullahi ta bayyana dalilin ficewa daga fim din Labarina

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Nafisat Abdullahi

Labarina shiri ne da nake alfahari da shi ah duk inda na shiga.

 

Saira Movies kuma na dauke shi tamkar kamfani na saboda mun Jima Muna aiki tare.

 

 

Ina bakin cikin fada muku cewa bazan ci gaba da Aiki a fim din Labarina ba.

 

 

Dalili shine rashin samun lokaci na yadda yakamataba. Inada nawa kasuwancin da karatu da kuma wasu hidindimu da nake yi a gefe.

 

Nafisat Abdullahi Labarina

Bazan ce ah jira ni sai sanda na samu lokaci ba, dole za’a ci gaba da film din Labarina ko da ni ko ba ni.

 

Tarihin Nafisat Abdullahi

Ina ba dubban masoya hakuri Akan fita ta daga shirin. Alakata da Saira movies Zata ci gaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi, Allah Kuma ya basu sa’a Wajen kammala sauran shirin.

 

Na gode daga Nafisat Abdullahi.

 

9 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!