Hausa Novels

Naga ta kaina Hausa Novel Complete

Naga ta kaina Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: NAGA TA KAINA

A garin na Sabo da ke kusa da Zaria, gidan Babana Mallam Shehu, tsangaya ceta karatun Alkur’ani mai girma, daga wurare daban-daban na nesa da na kusa kai wasu Almajiran ma daga Maradi a kasar Nijar da Yawunde ta kasar Cameroon da Kumasi ta kasar Ghana ake kawo su.

Tangayar Babana katuwa ce kwarai, akwai Almajirai sama da dari biyar a cikinta, don haka ko daga Zaria ka ce kana neman tsangayar Malam Shehu na Soba zaka samu wadanda zasu kawoka.

Mu biyar ne wurin mahaifinmu, babbarmu itace Hajiya Shema’u, mu kuma sai muke kiranta Hajiyar Zaria saboda a garin Zaria take aure gidan wani dan kasuwa Alhaji Umaru. Ita kadai ce matarshi, ‘ya’yansu hudu sai dai gidan nasu gidan yawane kwarai.

Gida ne nagado kuma ko da suka girma suka yi arziki basu fita daga gidan ba sai kawai kowa ya sami hali ya bige sashinshi ya tsantsara ginin zamani irin yanda yake so, don haka shi da ‘yan uwanshi duka a cikin gidan suke ga kuma sauran Iyayensu da suke raye.

Hajiyar Zaria ita kadai mahaifiyarta ta Haifa ta rasu, bayan rasuwarta ne Babana ya auri Innata ita kuma ta rike mishi ita tamkar ita ta haifeta har kuma itama Allah ya albarkace tada nata ‘ya’yan guda hudu maza biyu mata biyu nice kuma ‘yar auta.

Hajiyar Zariya tana matukar hutawa a gidan mijinta, ganinta kawai ita da ‘ya’yanta ya isa ya baiyana maka wane irin zama take yi.

Haka nan kullum a cikin yi wa Iyayenmu hidima suke ita da mijinta, duk lokacin da zata yiwo aike kuwa bata mantawa sai ta ware wani abu na musamman tace wannan na Badi’aotu ne ‘yar autar Inna. Inna tana matukar jin dadin hakan, don a duk lokacin da suka gamu sai tace mata “ke dai Allah ya yi miki albarka, na lura ke kadai kike taya ni son ‘yar autar nan tawa, sauran sai dai suyi ta zungurinta. “Ta yi dariya tace, “ai ke ce Inna kin bar ‘yar autar taki bata komai sai sakarci wai ana karatu a kofar gida amma ita sai a same ta tana wasan ‘Yar bebi’”. Inna kuwa murmushi take yi tana cewa, “in lokacin yin karatun nata yayi zata yi ne”.

Wata ranar Talata da hantsi Innata tana aikin girki a cikin dakin girkinta ni kuma ina zaune na gama jeren ‘yar bebina ina aikin yi mata kwalliya daga cikin gidanmu muna jin yadda muryoyin yara suka gauraye da karatun Alkur’ani mai girma. Inna ta dakatar da talgen da ta ke yi ta juyo tana kallona, tace “Anya Badi’atu yanzu yanda ake karatun nan ba za ki yi sha’awa kema ki je cikinsu ki zauna ko rike allonki ki yi ba? Yarinya kullum aka yi miki rubutu jikin allo sai ya yi dikin – dikin kafin ki wanke shi, na makale kaina jikin kafadata nuna alamar ba zani ba, nace ni sai gobe, bari yayanki ya shigo ya same ki babu rowana.”

Ta juya ta ci gaba da aikinta “Assalamu alaikum”. Muryar da ta yi sallamar tasa na zaabura har na yi jifa da gadon ‘yar bebina, itama ‘yar bebin ta hantsila.

Da gudu naje na rungumeta Hajiyar Zariyace, yarinyar da ke yi mata reno tana biye da ita rungume da yarinyar da take goyo, Zainab, sai kuma Almajirai rungume da kaya niki-niki na tsrabar da ta zo dasu suna shigarwa dakin inna, sannunku da zuwa abinda Inna keta faman fadi kenan cikin hanzari da fara’a ta wuce ta shiga dakinta tana kokarin yi musu shimfida tare da tambayar sauran yara dalilin da ba’a zo dasu ba , Hajiya tace Inna kun manta ne yau ranar Makaranta ne? To har da mai sunan Mallam shima Makarantar yake zuwa? Ta sake tambayar ta tace, “eh ai shima Alhaji ya saka shi. Inna ta rike baki tace kai kudai da fitina ku ke yaro ko shekara uku bai kaiba amma wai an sanya shi wata makaranta don dai kar a kyale shi a gida ace mishi bari? Hajiya ta yi dariya kawai suka shiga gaisawa da suka gama sai ta kawo mata kunun tsamiya da ta dama ta kuma goya Zainab ta nufi dakin dahuwa don ta kamala kwashe tuwo.

Ina zaune cikin farin ciki ina duba dinke-dinken da Hajiyar Zaria ta sa aka yi min, ga kuma turamen atamfofi uku na Innata, Manyan riguna aska biyu guda biyu na Babana, sai ga Babanmu ya shigo yana murmushi sammako yau kuka yi mana ne haka? Cikin ladabi da tamsa “Eh Baba Alhajin ne wai sai dai in koma kafin La’asar, shi yasa na zo da wuri, ai an gode mishi, Allah ya kara mishi albarka in ji Baba. Mallam kaga hidimar da yarinyar nan da mijinta suka yi mana ko? Ta shiga nuna mishi, ya gama gani ya dago kai ya kalleta, Alhajin baya gajiyane ko Shema’u? kullum cikin wannan hidimar yake ba fa mu kadaine da shi ba, ya yi tasa mata albarka ita da mijinta da zuriyarsu ma baki daya.

An zauna ana hira ni kan ina can gefe daya don ban iya saka baki cikin hirar manya ba, hira tayi dadi sosai sai Hajiyar Zaria tace Baba ko za’a bani Badi’atu ne ta danyi min kwana biyu? “Tana maganar tana murmushi, yace “Ke gidan ku cike da yara amma bakya gajiya da rokon Badi’atu taje miki kwana biyu ba kwanannan na ji ance da Balaraba ta yada wanka sati biyu taje tayi a wajenki ba? Ta ce, “Lah, Baba in Balaraba ta je mun bakunta ai daga gidan mijinta taje, Baba ya gyara zama yace mutanen gidan naku ne Shema’u kar mu kure su Kullum a cikin dawainiyar mu suke mu kuma bamu da abin yi musu in ban da addu’a kar su ga kullum kannen ki suna yi musu zarya a gida.

Cikin murmushi tace ba komai Baba shi kam Alhaji ma ai murna zai yi don ya sha tambaya ta in ce ko Inna rowar ‘yar autar take yi ne? In ce mishi a’a ba Inna ce mai hana Badi’atu zuwa ba Baba ne yake cewa kuna fama da mu mu kuma muna dabo kannenmu muna kawo muku ku yi ta dawainiya da su, ya yi ta dariya, yace, “To ai suma kannensu ne, Baba yace “To ai shi kenan, sai ki tafi da ita amma kwana biyu na baku karta wuce haka don ma kece yasa ai kin ga Balaraba kanwarki nan kusa damu take amma ban barin badi’atu zuwa gidanta, iyaka in an sauko daga sallar jumma’a taje gaishe su ta dawo. Saliha ita kadaike wuni a gidan nan in babu badi’atu kewa ma kadai ya isheta. Hajiyar Zaria tace to baba ai kwana biyun ma mun gode, ya tashi ya fita.

 

Ni kam sai murna da zumudi nakeyi a cikin zuciyata dokin zuwa Zaria nake yi don na riga na saba da wasu daga cikin yaran gidan saboda yawan zuwa dasu da Hajiyar Zaria takeyi tun ma ba Wasila ba, wacce muke kai daya da ita kuma tana sona har aiken kyallayan dinki take yi mun in sanyawa ‘yar bebina.

An yi sallar Azahar Baba ya shigo a lokacin nan kuma Inna tana ta aikin tankade kukar miya da busasshiyar kubewa da ta bayar aka dako mata, wanda Hajiyar Zaria za ta tafi dasu, ko dama can kuwa kullum Inna ta samu mai tafiya Zaria zata bashi kudin acaba ta bashi kuka da kubewa da daddawa tace ya kaiwa Hajiyar Zaria don mijinta mai son miyar kuka ne.

Wai ina Salihar ta ke ne? Baba ya tambaya ya kuma nufi cikin inda ya jiwo ta tana fadin gani nan, Yawwa kina ta kokarin shirya musu ba? Ta ce, mishi “Eh daddawar ce kawai basu dawo da ita ba, daga wurin dakan” “Nace, su daka ta tare da citta da kayan yaji, to ai sai ki tura Badi’atu taje ta karbo don kar su bata lokaci, bana so su wuce lokacin da ya ce su koma gida, ga kaji can guda goma sai ki hada musu, Inna tace to Madalla, kiya maza kije gidan su tambai Badi’atu kice wai in an gama dakan daddawar a baki ki zo mun da ita, nace to na yi maza na fita ina sauri, duk inda na hadu da kawayena suka tambaye ni ina za ki kike sauri haka Badi? Sai na tsaya na gaya musu yau zan tafi Zaria ni da Hajiyan Zaria, sai ka ga an zuba min ido ana kallona, wai na naji dadi zanyi tafiya ina shiga gidan Tambai na gaishe ta tare da sauran matan gidan.

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Tambai tace hala dai Hajiyar tazo ne? nace mata “eh, kuma yanzu ma zamu tafi, har dake? Ta tamabaye ni ni kuwa ina zumudi nace mata “Eh” Tace, Allah Sarki Badi, kice zaki zama ‘yar birni, Nace aima kwana biyu zanyi. “Tayi murmushi tace, “ke dai kawai sai an ganki, amma yanda nake ji ana bayar da labarin gidannan nasu Hajiyar Zaria ai zaiyi wuya ka shigeshi ka fito a kwana biyu kawai in basu suka ce bakuntar ta ishesu ba. Sauran matan gidan suka yi dariya, na dauko kwaryar cike da garin daddawa na

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!