Hausa Novels

Nahuce Hausa Novel Complete

Nahuce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Nahuce Hausa Novel Complete

SHIMFIDA

ZAMFARA STATE, NAJERIYA

Y

amma lis, a wata ranar Lahadi, wadda tayi daidai da shida ga watan Yuli, ta shekarar alif dari tara da casa’in da tara da misalin karfe biyar na yamma, majalisarsamarin unguwar Kofar Jange ta hadu, ta cika ta batse cikin birnin ZAMFARAN Najeriya. Opposite wannan majalisa ta samari wani gida ne da za’a iya kira ginin masu kudin da, koko a ce ‘yan bokon da, wanda aka yi wa renovation daidai da zamani, gida ne mai asali da tsohon tarihi a unguwar ta (Kofar Jange) da yayi fice sakamakon kasancewar mamallakin sa tsohon dan boko kuma dan siyasa da aka dama dashi a gwamnatin Zamfara tun daga state har federal.

Ita wannan unguwa KOFAR JANGE unguwa ce mai tsohon tarihi wadda ta samar da jiga-jigan ‘yan boko da masu fada aji a jihar Zamfara. A dalilin maigidan tsohon dan siyasa ne wanda ya kare rayuwar sa cikin hidimar al’umma. Wadanda suka gudanar da siyasar su ta gaskiya da rikon amana tun duniya na kwance, lokacin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar. Duk wani Bazamfare ya kwana ya tashi da sanin tarihin gidan Alhaji Mustapha Bilyamin Nahuche.

Karanta Littafin Farrah Hausa Novel

“GIDAN NAHUCHE!”

Shine lakabin da ake kiran wannan gida a garin Zamfara. A saman gidan ma an rubuta hakan cikin rubutu na ruwan gwal. Gida ne mara tarin iyali domin matar aure daya ce tal tayi rayuwa a cikin sa ba tare da kishiya ba; su biyu ne kadai ‘ya’yan gidan a wajen marigayi mahaifin su Hon. Mustapha Bilyamin da mahaifiyar su Hajiya Kaltume (Hajiyar Nahuche).

Wannan zama da samarin nan suka yi ba na komai bane na jiran isowar sa ne, shi kadai ran sa dan Nahuche jikan Nahuche…. da suke matukar kauna, ya kuma zame musu role-model wato mutum abun koyi a halayya da dabi’a, da kuma yadda yake gudanar da kafatanin tsarin rayuwar sa, bi ma’ana, shi mutum ne da suka yiwa kyakkyawar shaida ta saukin kai da girmama matasa; ga sukuni Allah ya bashi, ga tarin kuruciya da zuzzurfan ilmi amma babu ashararanci ko kankani a tare da shi. Bai gaji mahaifin sa ba ta fuskar siyasa, amma ya gaje shi ta fuskar ilmin boko, shi kawai dan boko ne mai ci da gumin, biron sa.

Tun safe suke zaune, har zuwa yanzu da rana ta tasamma faduwa, suna da labarin ya shigo Zamfara a safiyar yau yana gidan sa na GRA, kuma duk ranar da ya shigo matasa da masu neman aiki na unguwar su sun warke, shi ba dan siyasa bane (business tycoon) ne mai kishin matasan yankin sa, sannan mai connections a birnin Tarayyah, suna da tabbacin dole zai zo ya gaida mahaifiyar sa Hajiya Kaltume komai dare, ba zai kwana cikin Zamfara ba, ba tare da ya zo ya ganta da tilon Dan sa ba.

Karanta Littafin Deen House Novel Complete

Karfe nawa zai zo ne basu sani ba, in kuma zasu kwana dakon zuwan sa bazasu gaji ba, dalilin zaman su kenan a majalisar kofar gidan Hajiya Kaltume Nahuche.

Hira suke irin ta samari masu jini a jika masu burin da babu ranar cika shi; duka burin su dai shine su zama kamar sa a komai; a ilmi, a dabi’a, a halayya, a kasuwanci, a taimakon al’umma, a irin motocin da yake hawa, a irin simplelife-style din sa, a farin jini…..a kyawun sura a komai da komai. A cewar su dai, yana daga cikin masu sa’a a rayuwa in ka dauke gwaurantakar sa da bata dada shi da kasa ba.

Abin kamar hadin baki rediyon hannun daya daga cikin su ta soma kwararo muryar sashen Hausa na BBC (British Broadcasting Corporation) cikin shirin su mai taken: “DOMIN MATASA…..”

Mai gabatarwa yayi sallama sannan ya ambaci sunan bakon mako, wanda ya sanya samarin baki daya sakin ihu cikin hargagi irin na samari harda masu mikewa suna daga juna. Shiri ne da sukeyi duk karshen sati wato ranar Lahadi domin tattaunawa da talentedbusiness tycoons masu jini a jika irin “HABIBU NAHUCHE….”. Domin karfafawa matasa wajen neman na kai da neman ilmi.

Mai gabatarwa, AbdulHadi Taheer, wakilin BBC a jihar Zamfara, ya ce “Assalamu alaykum masu sauraren muryar Hausa ta BBC, a yau muna tafe ne tare da “NAHUCHE”, in nace Nahuche ina nufin HABIB, MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE……. The propriator of NAHUCHE HOTELS & NAHUCHE GROUP OF HOTELS. Barka da zuwa wannan fili Engnr. Nahuche, matasan Zamfara na son sanin takaitaccen tarihin ka?”.

Zuzzurfar muryar sa kasaitacciya ta mazan da suka hantse cikin ilmin addini dana zamani ta kwararo sallama da Bazamfariyar accent din sa, wadda banbancin ta da sakkwatanci kadan ne…..

“Assalamu alaykum, sunana Habibu Mustapha Nahuche, ni Bazamfare ne gaba da baya, nayi karatun firamare da sakandire duka a kauyen Nahuche kafin mahaifi na ya dawo birni a dalilin neman ilmi da neman abinci. Bayan kammala karatuna na sakandire na samu scholarship daga (Petroleum Technology Development Fund) da aka fi sani da PTDF zuwa kasar Germany, na karanci ‘Hotels Administration’ daga jami’ar Cologne, Germany. Nayi digiri na biyu duk a Cologne akan fanni guda. Na dawo gida a shekara ta 2000 na fara aiki da babban hotel din Najeriya na wancan lokacin (Nicon Noga) inda na rike manyan mukamai acan, daga baya na fara ginin hotel dina na farko a garin mu wato Zamfara, daga nan ne abubuwa suka mike har aka samar da NAHUCHE GROUP OF HOTELS a manyan jihohi na wannan kasa tamu mai albarka. Na taba aure, inada yaro”.

Abdulhadi Tahier yayi murmushi yace “masu sauraro zasu so su samu karin haske akan kalmar “na taba aure” domin kalma ce mai harshen damo, har yanzu da auren ko babu?”

Wani kasaitaccen murmushi ya saki, wani abu ya soki zuciyar sa, a lokacin da bafullatanar fuskarta ta gilma masa kamar walkiya, “ta yaya zai mantata da lokutan kwanaki bakwai?” A hankali kuma cikin karayar murya na tasowar wani tsohon miki yace.

“Duk yadda anka fassara ta, daidai ne!”.

 

Abdulhadi Tahier bai ja tambayar da nisa ba don ya fahimci ya gama amsa ta. Sai ya dauko maqasudin tattaunawar, wanda shine abinda suke so matasa su amfana da shi.

“Ko menene sirrin da ke karkashin nasarori da habakar ‘Nahuche Hotels’ akan sauran gidajen saukar baki da muke dasu a kasar Najeriya?”

Bai bata lokaci ba ya amsa.

“Excellent Service Delivery!”

“Shin ina ne NAHUCHE? Domin banda Zamfarawa, ba kowa ya san garin ‘Nahuche’ da ake kiran ka da ita ba, wadda har ta boye asalin sunanka na yanka? A yanzun ana maganar kasarmu Najeriya ne in general da babu babban birnin da baka da Hotel, kana da masu kallon ka as a role-model suke kuma son jin wasu daga boyayyun sirrikan rayuwar ka”.
Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi

Matar Makaho Complete Hausa Novel

Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam

Matar Yaro Hausa Novel

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Gyaran Nono a sari data

Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd

“Nahuche karamin kauye ne a karamar hukumar Bungudu. Ainahin garin Nahuche gari ne dadadde, garin ne da mutanen garin hausawa ne. Mutanen garin bakake ne sid.

A wata shekara garin ya hadu da musibar hare-hare daga wasu garuruwan. An addabi garin da yaqi har suka rasa yadda za suyi. Ana cikin wannan halin ha’ulin, sai wani shahararren mayaqi Ya zo daga Katsina, cikin kabilar Rumawa. Rumawa kuma ka san fulani ne kyawawan gaske.

Wannan shahararren mayakin tafiya ta biyo da shi ta cikin garin Nahuche, sai Kekun Nahuche (sunan ainihin sarautar Nahuche kenan) Ya roki wannan mayakin da ya taimaka masu kan hare-haren da su ke fama da su. Har yayyi mashi alkawarin idan har yacci wannan yaqin to zai bashshi rabin kassar shi da kuma sarautar Uban Dawakin Nahuche.

Aka yi yaqi, kuma aka samu cin nasara, shi kuma Kekun Nahuche bai manta da alkawarin da ya dauka ba, ya ba wannan mutumin sarautar Uban Dawaki (saboda ko da yazo a kan Doki yazo) ya kuma bashi rabin kasar shi Nahuche, shi kuma ya koma Katsina ya zo da iyalin shi suka ci gaba da zaman lafiya da mutanen garin, da Keku da Uban Dawaki sune ainahin sarautun da ke Nahuche kuma kowanne na mulki individually.

Har yanzu akwai rabe-rabe akan sunan wannan Bakatsinen amma mafi yawanci sun ce sunan shi Juli (sunan fulani ne). Juli ya sa ‘ya ‘yan shi sun yi makaranta, ciki har da kakanninmu, my grandfather (Bilyamin Nahuche) yana daga cikin dattijan wannan gari”.

“Madallah da wannan kyakkyawan bayani na tarihi akan garin Nahuche, a karshe wane sako gare ka ga matasa masu burin zama manyan (business figures) irin ka a Najeriya?

Wannan karon da murmushi ya amsa.

“Su duba organizational theory of business, kafin kafa kowanne irin kasuwanci. Gaskiya, rangwame da rikon amana shine sirrin nasarar kasuwanci, kada a raina riba komai kankantarta. A zama kullum cikin tunanin sababbin hanyoyin habaka kasuwanci a zamanance (technological innovation). Abu na karshe shine mai cin muguwar riba, baya taba nasara a kasuwanci kuma dukiyar sa bata albarka”.

Samarin nan banda ihu ba abinda suke yi lokacin da shirin ya kare, muryar shi kadai tsuma samarin Zamfara take yi, kaunar da suke mishi ba ‘yar kadan bace. Da a ce shi mai bin ra’ayin wasu ne ba ra’ayin rikau ba, da ya dade da shiga siyasa “……..Allah ya taimaki Nahuche…….Allah ka bar mana Nahuche…….” kawai suke ambato cikin hargowa. Daidai lokacin da motar baka wuluk kirar PORSCHE ta sulmiyo ta shigo layin kamar yadda suka yi tsammani. Suke kuma dakon jira.

Dan sardidin matashi da shi. Habibu Nahuche. Yau ma kamar kullum ya fito yana takun nan nasa majestically, cikin farin danyen Voyel mara nauyi dan shafal, dinkin jikin sa (very simple) wanda aka yi shi dan siriri da farin zare, sai da ya baiwa kowannen su hannu daya bayan daya babu gazawa cikin far’a da sakin fuska, sannan ya kawo ihsanin da ya saba yi musu a dunkule yayi musu, addu’a iri-iri Habibu ya sha ta, bai tsaya sosai ba ya wuce kai tsaye zuwa cikin gidan iyayen sa.

Mahaifin Habibu Alhaji Mustapha Bilyamin Nahuche tsohon dan siyasa ne wanda ya rike manyan mukaman siyasa a jihar Zamfara a lokacin rayuwar sa, yayi dan majalisar dattijai mai wakiltar Zamfara ta kudu, yayi sanatan Zamfara ta kudu, yayi shugaban karamar hukumar su wato Bungudu wadda garin Nahuche ke karkashin ta. Ya rasu ya bar matar aure daya da ‘ya’ya biyu mace da namiji.

Itace aunty Badiyya Nahuche, wadda ke aure a garin Kaduna, tanada yara hudu, sannan shi Habib, dake binta, daga kansu Allah bai kara baiwa Haj Kaltume haihuwa ba.

Da sallama ya shiga falon Hajiyarsa, tana kishingide akan tumtum, ta kunna rediyo tana sauraron hirar da ake yi da shi. Shigowar sa tayi daidai da karewar shirin. Ta kashe rediyon tana mai shimfida masa karamin center carpet, bakin ta dauke da murmushi, fadi take.

“Habibu bazaka bari ka kwanta ka huta zuwa gobe sannan ka shigo ba? Ka taho tun daga Lagos? Ka san dai tunda samarin nan suka ganka ba bari zasu yi ka huta ba”.

Murmushi yayi yana zama akan shimfidar data yi masa, idanun sa cike da kewar ta, da ganin su zaka san akwai shaquwa da kauna ta musamman bayan ta iyaye da Allah ya riga ya assasa, cikin nutsuwa irin tasa ya sunkuya ya gaisheta, sannan yace “bana taba gajiya dasu Hajiyar mu. They are part of me (su rabin jiki na ne), nima shekarun baya ai kamar su din nake; matashi mai buri. Ina Abdallah?”

Hajiya Kaltume ta nisa, sannan ta ce “Badiyya ta tafi dashi Kaduna hutu, amma gobe insha Allah nace a kawo shi don ku gaisa, kafin ka tafi Makurdi din da ka ce zaka wuce daga nan.

Anya Habibu ina amfanin a dinga yamadidi da kai a kafafen yada labarai ana fadin baka da aure sai kace wani dan siyasa? Shin ita ta kara tuna ka a duka wadannan shekarun nan ko bata san inda kake ba da dan ta? In tana da niyyar cigaba da rayuwa da kai ai da tuni ta nemeka. Tunda na tabbata ta san inda ka ke. Kai ne baka san inda take ba. Kai din a yanzu kuma fitacce ne kuma sananne a kasar Najeriya, bai yuwuwa ace bata san da wanzuwar ka ba koda a kafafen yada labarai ne. Idan har tana da muradin sake rayuwa da kai.

Mata na duniya babu irin wadanda iyayen su basa kawo min, babu ‘yar wanda bazaka aura ba Habibu, ka hakura da yarinyar nan…… ka hakura da ita bisa umarni na!”.

Hajiya Kaltume bata ankara da cewa hawaye ne ke zuba daga idon sa ba…..sai da ta kai karshen maganar ta. A fili ta furta

“Yaa Salamu sallim!”

Domin al’amarin Habib da uwar dan sa yafi karfin tunanin ta.

A duk lokacin da ta takura masa da zancen aure karshenta kenan, yayi mata hawaye. Don bai da abin cewa. Shin wacece wannan uwar Abdallah haka? Kuma me ta taka da har ta mallake zuciyar namijin duniya irin dan ta Habibu Nahuche???

****

 

 

 

 

 

ABUJA, NAJERIYA

(Cikin Gidajen Likitoci na National Hospital

9:30 am).

T

a kashe rediyon a hankali, zuciyar ta na wani irinragaita, tana daga cikin wadanda suka fara aikawa BBC sakon appreciation din su ga wannan shiri na musamman. Abubuwa masu yawa da suka gabata a birnin Cologne din Jamani shekaru GOMA a baya na gilma mata. Wannan ita ce kaddarar su, da har gobe ba wanda ya san ta. Kuma kaddarar data hana ta AURE shekaru goma bayan rabuwar su. Kaddarar data maida rayuwar ta duhu didim; farin ciki bai kara gudana a cikin ta ba; “Kaddarar auren kwana bakwai”.

Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo, hawaye na sauka akan fararen sumul-sumul din kundukukinta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare. Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi. Damuwar ta ba akan kulawar da zai samu bane domin hakika Habib Nahuche zai kula da dan sa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigar aure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafar sa bai kama ba, koda kuwa ya fi shi komai na rayuwa.

Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami’ar Cologne ba’a matsayin sa na yanzun ba (mamallakin Nahuche Hotels) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashin sa na rayuwa daga ranar da ya yi kidnapping Dan su. Dalilin bibiyar ne bata sani ba har yau, tunda ita tace bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai bata ba, kuma burin Dada shine tayi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza da gashi sai dan mutanen Nahuche. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah yayi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwar su.

Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar bazata daina zubar dasu ba har zuwa karshen rayuwar ta. Idan har rayuwa bata koma yadda take a baya ba; with him by her side.

“Auren Wucin Gadi”. “Auren kwanaki bakwai kacal”. Wadanda abubuwan da suka wakana cikin su sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwan sa duniya ne yayi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami’ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar data samu kanta. Plus rashin cikakken gata da ya baibayeta a lokacin.

Shekaru goma a baya, suka soma tariyo kansu a idanun ta, tamkar a majigi.

*****

 

 

 

 

 

 

 

(FARKON LABARIN)

SHEKARU GOMA A BAYA

D

aga cikin bututun maganar cikin jirgin Boeing745 wanda ya tashi zuwa kasar Jamus a yau daga filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Lagos, bututun sadar da sako na gaggawa ya karade kunnen fasinjoji, “jirgi yana cikin hatsari, jirgin mu yana watangaririya, hazo ya lullube sararin samaniya gabadaya, direbobi sun rasa direction din su, a sabili da haka muke shawartar a sanya rigar hatsari, don komai na iya faruwa, sannan ta soma bayanin (how to escape a plane crash) cikin gaggawar magana.

Abinda ya gigita fasinjoji, ya firgita mata da yara, masu kuka na yi, masu salati na yi, bata san sanda ta kankame mutumin dake gefenta ba tana rusar kuka.

“Ina da gyatuma, da Allah da ni kadai ta dogara, dama sai da tace min kada in taho karatun nan, don ba lallai mu sake ganawa ba, don Allah don annabi ka taimaka min kada in mutu, in koma wajen Daada”.

Za’a iya cewa shikadai ne bai razana a cikin jirgin ba, da ganin yarinyar ta gama tsurewa, kokari yake yasa mata rigar hadari amma ta bi ta cukuikuiye shi gabadaya.

Ta kankameshi kamar ta samu uwar ta. Duk da cikin tashin hankali suke sai da yaji wani iri a cikin jikin sa da ruhin sa. Da karfi ya yakice ta,

“Hey! Relax, are you not a Moslem? Kiyi addu’a, ki cika ni insa miki rigar kubuta daga hadarin jirgi”. Ya soma ambaton “innalillahi wainna ilaihi raji’oun……” a fili har itama ta kama eventually.

Cikin ikon Allah ba’a yi minti talatin ba kuma komai ya daidaita. Hazo ya yaye, jirgi ya daidaita akan hanyar shi, ba jimawa suka sauka a birnin Cologne, Germany.

Kunyar abinda ta aikata kuma ta zo ta lullubeta, ta kasa sake hada ido da shi, ta nemi hanya ta sulale abin ta, cikin nasihohin Daada kafin ta taho har da cewa kada ta yarda jikin ta ya rabi na kowanne namiji haramun ne in ba mijin auren ta ba, yau ba raba ba kadai ta kankame namijin da bata san daga inda yake ba, tana tafe tana waige-waigen neman abokan tafiyar ta.

Bafulatanar Adamawa ce kyakkyawar gaske, doguwa sambaleliya, siririya, shekarunta sha tara da haihuwa, tana cikin dalibai masu hazaka da gwamnatin jihar Adamawa ta zaba tayi sponsoring karatun su na likita zuwa kasar Jamus akan likitancin fidar kunne, hanci da wuya (ENT surgeon) wadanda sunyi karanci a Nijeriya, specialization din su shi ake kira (Otorhinolaryngology).

Ta tashi ba tare da iyayen ta ba, sun mutu tun tana kankanuwa, a hannun kakarta Daada wadda ta haifi mahaifin ta ta tashi, don haka duk wani wayo irin na yaran da suka tashi gaban iyaye bata da shi, goyon kaka ce ziryan, mai tarin yarinta, wauta da shagwaba, amma a fannin karatu zaqaqura ce. Daada ita tasa ta a makaranta, hazakarta tun tana karama daban ce data sauran tsararrakin ta. Bata san kowa ba a danginta sai Dada, Dada ce kawar ta, uwar ta uban ta komai nata.

Hazaqarta ce ta sayo mata kauna a gun malamanta, bayan kammala sakandire wadda ta gwamnati ce, tafi kowa cin WAEC da NECO, B2 guda biyar rus, da A1 a biology, physics, chemistry da lissafi, wannan yasa hukumar makarantar ta bada sunanta a gurbin sukolaship na dalibai biyu masu hazaka ‘ya’yan marasa karfi da gwamnatin jiha ta basu.

Komai za’a yi musu, sannan za’a dinga basu alawus na cin abinci, har su gama karatunsu a Jamus wanda zai dauke su tsawon shekaru biyar zuwa bakwai har specialization din da a ka tura su su yi. A karshen kowacce shekara zasu zo gida su yi hutu su koma.

Ba karamin dauki ba dadi aka yi da Daada ba, kafin ta barta tahowa Germany, sai da shugabar makarantar su ta zo har gida da kanta ta same ta, ta roketa ta kuma kwantar mata da hankali, ta gaya mata yara irin jikanyar ta ba’a wasa da talent din su, irin su ake nema don a farfado da harkar kiwon lafiya a Najeriya, sannan karatun da zata yi (Otorhinolaryngology) babu mai irin shi a fadin Najeriya a wancan lokacin, tayi wa jikanyarta addua ta bita da fatan alkhairi ta bar ta taje, ita kuma zata kula da rayuwar ta acan, akwai kanwarta dake aure a kasar.

Sannan ne Daada ta hakura, amma tace abu na halin rai da tsufa, ko a ina ta samu damar yin aure tayi, koda wanene, in dai musulmi ne, babba ko yaro, in dai zai rike maraicin ta, sabida bata da tabbacin zata dawo ta sameta a raye.

Don haka ne da jirgi ya kusa kifar dasu tafi kowa nadamar wannan tahowa, da ta yi hakuri ta yi zamanta bayan Daada, akan gadon bonon ta, da wannan ajali ya dauketa ne a bayan Daada cikin kwanciyar hankali. Don ta san mutum baya tsallake ajalin sa, saidai inda ajalin kowa yake ne daban.

Suna saukowa daga jirgi ta hau raba idanu, abokan tafiyar ta duk sun kama gaban su, taimakon da Allah yayi mata tana da adireshin jami’ar data zo da duk wasu muhimman takardunta a tare da ita.

“RAHINA OMAR! RAHINAH OMAR!! RAHINAH OMAR!!!”

Taji an kira sunan ta daga baya, da sauri ta juya don ganin mai kwala mata kira haka, nan da nan ta gane shi, shine agent wanda aka turo daga Embassy yayi musu jagora a komai har su gama registration dinsu. Kuma tana da hoton sa. Sannan principal tace shi zai kaita wajen kanwarta Dr. Laura wadda lakcara ce anan Cologne take aure. Gara ta zauna gidan ta madadin zaman (students hall of residence).

Murmushi ya subuce mata, data hango abokan tafiyar ta tare da shi, suka rankaya cikin babbar mota suka wuce cikin gari.

 

Sunan ya cigaba da wata irin amsa-kuwwa a kwanyar sa, ba tare da sun ankara da shi ba, sabida a lokacin ya basu baya “…….Raheenah Omar…….”. Ya ji amsa-kuwwar wannan suna har cikin bargon sa. Kamar yadda har zuwa yanzu yake jin ta cukuikuiye a jikin sa. Surar ta bazata taba gushewa daga idanun sa ba, domin bai taba ganin kyakkyawar surar data manne a ruhin sa irin tata ba, sannan innocentlooks dake cikin fararen idanun ta wani sign ne daya makale a zuciyar sa.

****

FIRST ENCOUNTER (HADUWAR FARKO)

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

The Cologne Public Library” babban dakin karatu ne na jami’ar Cologne wanda yake lamushe dubunnan dalibai komai yawan su, yawanci daliban anan suke assignments din su, kuma idan kazo a matsayin sabon dalibi dole ne kayi register da Labirare, a matsayin ta na sabuwar daliba mai yin registration yau ta shigo labirare tunda wuri, bata kai ga tarewa gidan kanwar principal ba ta zauna tare da abokan tafiyarta a (hall of residence) har zuwa sanda zata kammala da registration.

Bayan ta kammala abinda ya kawo ta ta juya zata fita, accidently ta bugi mutum wanda ya juya baya yake jera littatafan Encyclopaedia Britannica a bookshelves na library din. Littafan hannunsa suka fadi kasa. Da sauri ta sunkuya tana tsince masa, ta mika masa cikin cewa “i’m sorry…….” sorry din ta makale a makoshin ta sakamakon ganin makwabcin ta na jirgi. Wanda ta sulalewa. Ga dukkan alamu ma’aikacin library din ne. A very handsome figure din data zauna mata a rai sati biyu da suka wuce, ko na kwana daya bata fasa tuna shi ba.

“You?”

Ya fada yana nuna ta da dan yatsa. “…… matsoraciya mai tsoron mutuwa” ya sake fadi cikin harshen hausa. Murmushi ta yi tayi gaba tana fadin “wa ke son ta? Da jirgin nan ya kifa da ni Dada na ma mutuwa zata yi”. Dariya yayi ya bi bayan ta har kofar labirare. “Daga wane gari kika zo?” Bata san meyasa ta samu kanta da kantara masa karya ba tace “Benue” kallon mamaki yayi mata don ko kusa bata yi kama da kabilu ba, face zallar fulani, bafullatana cikakkiya, ita kuwa ta fadi hakan ne sabida Dada ta ce mata never trust a stranger. Sai yayi tunanin watakila zama ne ko aiki ya kai su zaman Benue din.

Bai cika ta da tambaya ba, suka yi sallama ta wuce ya wuce, amma da ya koma dakin sa na accomodation din dalibai sai ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ta yi masa karan -tsaye a zuciya a kan dalilin da bai sani ba. A kuma yadda ya lura bata da wayau, wayau na fahimtar abubuwa muhimmai irin wanda ya samu kansa akan ta, bai taba tunanin aure nan kusa ba, amma yau ji yayi in bai mallaki yarinyar nan ba bazai iya rayuwa ba. Ya manta da abinda ya kawo shi karatu ne kuma a yanzu ne ya fara masters din sa, ya samu part time job da labirare don ya taimaki kansa, kasancewar kudin da PTDF take basu ko kusa baya isar sa sabida tsadar studentaccomodation.

A yau da ya sake haduwa da Raheeenah, sai ya tuna cewa ashe shima namiji ne, ashe yana da bukatar mahadin rayuwa duka shekarun nan biyar da ya kwashe a Jamus, ashe bai taba haduwa da wadda zuciyar sa zata aminta bane, shiyasa bai taba son aure ba, sai akan Rahinah. Wadda ganin shi da ita bai fi a kirga ba. Gabadaya ya rikice ya birkice ya rasa inda zai sa kan sa. Aure kawai yake so yayi kuma ba da kowa ba sai Rahinah Omar.

Yana da Ubangida limamin masallacin musulmai na jami’ar Colgne wanda ke karatun doctorate, mutumin kasar Maghrib ne, shine ya samar masa aikin da yake yi a library yanzu, duk da albashin ba mai yawa bane amma bai nemi komai ya rasa ba, har ya bar cikin jami’a ya kama private gida karami a wajen makaranta. Rigimar son aure data shige shi a yanzu harda kuruciya domin kuwa abinda bai sani ba infatuation ke damun sa akan Raheenah ba soyayya ba. Kyawun ta ne ya riba ce shi. He just wants to have her as a spouse at the age of 27 a lokacin da ya kamata ace karatun sa ne a gaban sa ba mace ba. Ga Hajiyar sa ta dade da samar masa mata a kauyen su, Nahuche. Wadda take matukar so, don ‘yar kanin baban sa ne. Jira take ya kammala masters ya dawo ayi musu aure.

Amma haduwar sa da Raheenah ta rikita shi ta hargitsa shi, gabadaya ya rasa lissafin sa, bai taba tunanin yin zina a rayuwar shi ba duk da cewa ita tafi komai arha a Cologne, amma ji yake kamar zai iya raping Raheeenah in bata yarda ta aure shi ba, laifin da ya san zai iya kai shi ga hukuncin kisa a kasar turai, ji yake in bai yi aure da Rahinah ba a daidai wannan lokacin zai iya rasa ransa, al’amarin da ya kawo shi gaban ubangidansa at a smart pace (afujajan) yana neman mafita.

Dr. Sayyed ya dube shi sosai bayan ya gama jin damuwar sa, da yake malamin Psychology ne a take ya gama fahimtar halin da Habib yake ciki (infatuation/lust), yace masa “ita yarinyar tana son ka, kuma ta amince zata aure ka? Annabi SAW yayi umarni da ayi wa samari aure a lokacin da suka bukaci hakan, in ba haka ba barna bazata gushe ba a doron kasa. Don haka in ta amince ni zan daura muku aure (ba tareda tunanin abinda zai biyo baya ba)”.

Cikin rauni Habib yace “ni ko dosarta da zancen bazan iya ba, i’m sure ba abinda ya kawo ta kenan ba, she’s very naive and innocent, ni kuma zan iya cutar da ita idan ta ki yarda ta aure ni, i just want to marry her…… or rape her…..in ba haka ba Dr mutuwa zan yi. Na yarda bayan dayan wannan in kare behind bars!”.

Dr. Sayed ya gama gane inda Habib ke fuskanta, infatuation ne mai tsanani ya kama shi ba soyayya ba, yace “ba zaka mutu ba insha Allahu, kuma bazaka aikata zina ba har karshen rayuwar ka, sannan bazaka je kurkuku akan laifin fyade ba, kaje ka gwada sa’ar ka, in har ta amince ni kuma zan yi kasadar daura muku aure, ai karatu baya hana aure”.

Tun daga lokacin yake tunanin ta inda zai bullo mata, sun sha haduwa a wurare daban daban musamman labirare data ke yawan zuwa. Amma kwarjininta ya hana ya tunkare ta. Until that fateful day…..da ya ga an daukota ranga-ranga a sume an yi asibitin jami’ar Cologne da ita a ambulance.

Abokan karatun ta sun tabbatar wa da likita cewa basu san me aka gaya mata a waya ba, ana cikin lecture ta ansa waya sai gani su kayi ta zuba kara ta zube a wurin a sume.

Ya makale a asibitin nan a kofar dakin da aka shiga da ita, ya ki matsawa ko nan da can, lokacin da likitoci suka yi nasarar dawo da numfashin ta shi suka ce ya zauna tare da ita kasancewar duk abokan karatun ta sun koma makaranta. Sun dauka shima coursemate din ta ne.

Tana bude ido da sunan DADA ta bude baki…..tana kuka tana fulatanci, fulatancin da bai san me take fadi ba, a karshe ya tsinci kalmar hausa. … Dada ni da ke shike nan? Dada kema kin tafi kin bar ni ba uwa ba uba a kasar da bani da kowa? Dada kin kyauta min kenan? Meyasa baki ce mutuwar ta dauke mu tare ba? Me yasa baki jira na zama Otorhinolaryngologist ba na saya miki gida mai kyau da mota?”

Ta soma zabura tana fizge karin ruwan ta, da sauri ya rike ta ya kuma danna kararrawar kiran likitoci suka zo suka zurmuqa mata allurar barci.

Kwana uku cif Rahina na cikin wannan halin na tsananin firgita da dimuwar rasa Kakarta. Ko na minti daya Habib bai bar asibitin nan ba, da nasiha da banbaki da janyo ayoyin Al’qurani masu tabbatar da kowanne mai rai mamaci ne “kullu nafsin za’iqatul maut” Habib ya samu ta soma dawowa hayyacin ta. A ranar data kwana biyar a gadon asibiti, cikin dare ta farka yana sallah, ta hada kai da gwiwa tayi kukan ta ta koshi, yana jin ta har ya gama nafilfilin sa ya juyo don ya kara bata baki.

Sai gani yayi ta mike, ta dauki mayafin ta ta yafa, tana shirin barin dakin. Yayi maza ya sha gaban ta “Rahina ina zuwa? Likita bai sallame ki ba tukunna, ya ce sai gobe, kiyi hakuri ki kwanta ki kara nutsuwa zuwa gobe, ni da kaina zan maida ke gidan ku”.

Cikin kuka ta ce “Najeriya zan koma na fasa karatun, passport dina zan je in dauko a gidan aunty Laura, dama sun tsane ni, a dole nake zaune a gidan, bazan iya rayuwa babu Daada ba, don Allah…..don Allah ka fadawa hukumar makaranta na koma gida”.

Wani matsanacin tausayin ta ne ya kama shi, yace “Rahinah in kin bar karatun ki, kuma babu Dada, kin koma gida, menene madafarki a gaba? Gara ki karbi reality na cewa Dada ta rasu, ki tsaya ki gina future din ki, wanda ya riga ya mutu baya dawowa, kiyi hakuri zuwa gobe likita ya sallameki in raka ki gidan Antin ki, in kuma san gidan naku don yanzu ni Yayanki ne wanda bazai bari ki ragaita a rayuwa ba”.

Da haka ya samu ya kalallameta, da tausasan lafuza, har ta yarda ta koma gado ta zauna. Saidai yadda suka ga rana haka suka ga dare. Kowanne abinda yake sakawa a ransa daban ne. Ga Habibu, tunani yake wannan dama ce Allah ya bashi ta auren Rahinah cikin sauki, tunda bata da gatan da zai zame masa cikas, ba sai ya wahalar da kansa wajen neman soyayyar ta ba.

Raheenah kuwa tunanin ta irin zaman data fuskanta ana yi a gidan anty Laura ne; zama na kafirci da rashin tuna dokokin ubangiji, ta tsani zaman gidan don dai bata da yadda zata yi ne, sabida basu da kirki ko kadan, Anty Laura tana da wani Da Yasir fitinanne mai ruwan ‘yan iska, wanda ta gama gane take-takensa na banza da wofi a kanta, don haka tunda ta yi sati a gidan ta fahimci zaman gidan bazai yiwu mata ba domin ‘ya’yan anty Laura ko sallah basa yi. Yanzu tunanin ta shine taje ta kwashe kayanta ta dauki passport din ta ta koma makaranta da zama yadda ta fara tun farko. Tunda Habib ya ce komawar ta gida ba amfani.

Gari na wayewa likita ya sallame su, suka fito tare zuwa bakin titi, ya tare musu taxi suka hau zuwa gidan Dr. Laura wanda ba shi da nisa da makarantar su.

Cikin halin ko’in ‘kula Dr. Laura ke tambayar ta inda ta tafi har kwana biyar, bayan an gaya mata kakarta ta rasu, shi kuma wannan saurayin ina ta samo shi?” Kamala da kwarjinin Habib yasa ta kasa ci masa mutunci yadda tayi niyya, a take ya kara fahimtar cewa dan sauran gatan da yake tunanin tana dashi a kasar ma babu, wannan matar da gani ba jinin ta bace ba.

Nan yayi mata bayanin daga asibiti suke, ya gaya mata duk halin da Rahina ta kasance, ga mamakin sa sai ta kyabe baki, “don tsohuwa ta mutu ne kike neman kashe kanki? Ai kawai yarinya ki zauna kiyi rayuwa mai ‘yanci a Jamus ki tarawa kanki ilmi da dukiya, kin ganni nan tun da na bar Africa na huta da wahala, aure kuwa na yi ya kai goma, yarannan da kike gani duk uban su daban, bana daukar bakin cikin namiji, in kika samu kwalin Cologne kin gama tsallakewa, ki tsaya kiyi karatu ki nemi rayuwar ‘yanci kawai”.

Rahina ta saki baki tana kallon ta, Shikuma Habib tsoron matar ne ya kama shi, ya tabbata barin ta da Rahinah hatsari ne babba, don haka ya yi gaggawar cewa shi yana son auren Rahina, a bashi auren ta.

Aunty Laura tace “ai ba ‘ya ta bace, ba kuma ‘yar uwata bace, student din yayata ce kawai, don haka zan mata magana, in ta amince kuma kanada sana’ar da zaka rike ta ko gobe zan wakilta muji na ya daura muku aure”.

Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, domin principal cewa tayi Dada ta bar mata wasiyyar idan Rahina ta samu miji musulmi, wanda zai rike maraicin ta ayi mata aure shine babban kwanciyar hankalin ta a kabarin ta.

Dr. Laura tace “ai gashi kam ta samu, har da tabon sallah a goshin sa karewa, kuma ga yadda na lura yana son ta sosai, zan gaya wa baban Nihal ya zama waliyyinta ranar jumaa a daura musu aure”.

Baban Nihal mijin Anty Laura da Dr. Sayed suka zaunar da Raheena suna nuna mata amfanin tayi aure shine martaba da kwanciyar hankalin ta, Rahina ta kasa musa musu sai kuka, daga Sayed ya dinga lallashin ta, daga bisani suka daura auren a masallacin Cologne bayan an idar da sallahr jumaah, akan sadakin da Dr. Sayed ya biya masa in Euros. Kudi tsababa masu yawa duk don ya taimaka ta amshi auren domin ta kafe kai da fata bayan daurin auren tace bata so, duk da convincing din ta da Dr. Sayed ya bata lokaci yayi, har mari ta sha a wajen anty Laura tace “ubanki ya ce ki kwaso min shi? Ba tare na gan ku ba? To in baki son shi sai dai ki bar min gida na, ko ki auri Yasir ya sha cocaine dinsa ya lakadaki ba ruwa na”.

Ta debi kudin sadakin ta watsa mata, tace “kije ki hada kayan ki da daddare zasu zo su tafi dake, Allah ya gani ni taimakon ki na yi, don nasan in bakiyi auren bama karshenta ki zama international prostitute. A Jamus kike yarinya ba a Najeriya ba”.

Tana kuka tana komai Anty Laura dasu Nihal suka loda mata kayan ta a bayan taxi din da Habib ya zo a ciki, kamar dama zaman ta tare dasu ya takura musu don dai basu da yadda zasu yi da ita ne.

Tunda suka shigo motar take kuka, kuka tukuru tamkar zata fidda rayuwarta. Wannan wace irin rayuwa ce? Daga ganin mutum bata san komai a kan shi ba, don kawai musulmi ne kuma ya zo daga kasarta sai a aura mata? Kawai don an ga bata da gata? Ita bata ce lallai sai ta zauna da Dr. Laura ba ta so ta koma hostel kawai tunda ko ta koma Najeriya babu Dada wajen wa zata je?

Tunda ta taso bata san kowa nata ba sai Dada, daga dangin uwa har na uba, ta rayu karkashin kulawar tsohuwa Dada a shekarun rayuwarta bakidaya. Yau ga rayuwar da rashin gatan Dada ya jefa ta a ciki; auren mutumin da bata sani ba, bata san asalin sa ba, bata san halayen sa ba, bata san manufar sa a kanta ba. Just haduwar kan hanya wadda bazata iya bada shaidar komai a kan sa ba, wannan taimako nasa ya zame mata masifa, duk yadda aka yi yana da target dinsa a kanta, amma in ba haka ba ta yaya daga ganin ta bai san asalin ta ba zai zabe ta ta zama matar auren sa?

Ko da take goyon kaka, tana da hankalin ta. Bazata taba barin shi ya gurbata mata rayuwa ba.

Ta soma yi mishi kallon mutumin kirki tun daga haduwar su ta farko, amma ashe ba haka bane yana da mission dinsa da yake son cikawa a kanta.

Zata bashi mamaki, zata nuna mishi ka bar raina allura….karfe ce, komai kankantar ta.

Wannan take hakkin dan adam ne, a aure shi babu cikakkiyar yarda da amincewar sa.

Tana da damar da zata kai su ga hukuma daga su har anty Laura, amma bazata yi hakan ba, sabida ko yaya dukkan su sun taimaketa a Jamus. Kuma Dr. Sayed yayi iya kokarin sa wajen convincing din ta.

Amma ta gama kudurta mafita, mafitar da zata nemawa kanta ta kwatarwa kanta ‘yanci…..

 

“Bazata taba bari ya samu access din keta mata haddi ba, in ma kwadayin hakan ne yasa shi auren ta da gaggawa haka. Har sai ya gaji ya bata ‘yancin ta na dalibtaka wanda shine abinda ya kawo ta Jamus ba auren sa ba”.

*****

Kugin karshe da motar tayi, a kofar flat din Habibu ne, wanda ke shiyyar Klettenberg. Shi ya bude mata kofa da kansa ya kuma rungumota barin jikin sa. Ji tayi kamar ya dala mata wuta, amma haka ta daure ta cije ta shiga gidan tana hawaye.

Dr. Sayed ya biyo bayansu har falon gidan, ya zauna yayi musu nasiha sosai, yace su taru su rufawa juna asiri su zauna lafiya, duk wata matsala da suke da ita su sameshi, shi uba ne a garesu, kuma Raheenah ta kwantar da hankalin ta Habib mai son ta ne, bai aureta da wata manufa ba sai bisa son cika sunnar Ma’aiki SAW.

Da wannan yayi musu doguwar addua’a sannan ya tafi, bayan Habib ya taka masa ya rufe gidan ya dawo.

A inda ya barta anan ya sameta, amma ta yaye lullubin fuskarta tana yi masa wani irin kallo, kallo irin na kamar ka ga makiyin ka, koko abunda zai cutar da kai. Da gaske zuciyar ta da dan kankanin tunanin ta basu bashi kowanne matsayi ba, face na mai mugun nufi a kanta.

Ya zauna dab da ita, har tana iya jin kamshin turarensa Carolina Herrera (Men). Da sauri ta matsa ta ja baya, sannan ta nuna shi da dan yatsa ta soma magana cikin hawaye.

“Allah ya fi ka! Duk abinda kake nufi da ni Allah ya fi ka”.

Cikin madaukakin mamaki yake kallon ta, baki sake, ya ce “Rahinah are you alright?””A’a a haukace nake, kawai daga ganin mace akan hanya baka san ko wcece ba sai kasa power ka aureta? Sabida ka fahimci bani da gata ko? Shiyasa ban cancanci ka nemi soyayyata ba, ka nemi dangi na ka aure ni cikin mutunci, ka taimaka min inyi abinda ya kawo ni sai kawai kayi min kutse a rayuwa ka raba ni da burika na?

Ni na ce maka na zo Jamus don in yi aure ne?”

Habib yayi mata wani irin kallo, domin ji yayi ya muzanta a gaban ta, yarinya tamkar mai gani har hanji! Da gaske yasa kaimi ya aureta ne don biyan bukatar ruhin sa da gangar jikin sa, bai taba fadawa a wani abu wai soyayya ba, kallon ta yake da jin ta as waste of time, burin sa da lokutansa na tunanin maida kobo ya koma dari ne, yana da manyan burika da suka zarce soyayya. In fact, bai dauki mace a bakin komai ba banda abar hutawar gangar jikin mijin auren ta.

Amma ita wannan inda bata bullo masa ta haka ba, da bata nuna ta san ba son ta yake ba, bayan target dinsa na auren ta yanada burin tallafar rayuwar ta da maraicin ta, tare da cigaba da zama da ita har karshen rayuwar sa.

Amma tunda ta nan ta bullo, ya san ta yadda zai yi maganin ta.

Daga sanda ya mike ya durfafe ta, da sanda ta soma ja da baya cikin tsoro, cikin abinda bai gaza sakan bane idanuwan su suka hadu, ta hango wani boyayyen al’amari cikin brown kwayan idanun sa, al’amarin da har gobe ta kasa mantawa, shekaru bakwai kenan; Babu soyayya a cikin a cikin kwayar idon Habibu ko kankani face lustfuldesire wanda ya kara darsa mata tsanar sa. Ta kuma kara yarda da cewa manufarsa kenan ta auren ta.

Da farko yayi kokarin lallashin ta, amma sai ya gane zai bata lokacin sa ne kawai, ga rashin kunya da tsiwa kala-kala na fita nau’i-nau’i daga bakin ta, sai ya ce “Raheenah bari in yi maganin ki…..”.

Duk wani kokari na kwatar kai da neman ceto Raheenah Omar ta yi, kafin ta gane all her effort was futile (kokarin ta na banza ne), tamkar Habib Nahuche ya jima yana jiran wannan ranar, ya gama shirya mata. Abubuwanda suka wakana a tsayin daren bakidayan sa ba masu dadin fada bane. Saboda al’amarin baida maraba da rape banda igiyar aure data suturta shi.

Kuma wannan ne abinda ya gina matsanancin tsoro da kiyayyar sa a zuciyar ta. She hates him with passion from their first night. Ta alkawartawa ranta koda jan ciki sai ta bar Jamus, gara ta dawo Adamawa ko bara ce ta yi ta ci da kanta, da dai ta zauna da wannan mugun mutumin mai halin dabbobi.

Tamkar ya san tunanin ta, washegari da zai fita makaranta saida ya kulle ta ta waje.

*****

Ba shi ya dawo ba sai yamma lis, tunda ya san ya bar mata komai da zata bukata. Amma ga mamakin sa a inda ya fita ya barta anan ya dawo ya sameta, a kwance akan marbles kamar kayan wanki, baya tunanin ko sallah ta tashi ta yi, balle akai ga wanka.

“And your name is bride?”

Ya tambayeta cikin zolaya.

Hararar data ke masa tamkar idanunta zasu fado, wadanda suka kada suka yi jajazur kamar an gumbuda musu barkono. Da za’a bata dama zata iya kashe shi ta hanyar rataya, sabida tsanar data yi masa.

Ya tsugunna a gabanta ya ajiye mata ledar abincin McDonalds da lemun power horse mai sanyi, yana wani makalallen murmushi na tura haushi yace “ki ci ki sha, ko kya wartsake kinji amarya ta! We’re going for the second phase.,…. what is the marriage meant for? I don’t believe in what is called love. Ban sani ba ko in kika haifa min ‘ya’ya….. “”ta Allah ba taka ba..kada Allah ya nuna min wannan ranar””ko?” Ya tambaya yana kara hade filin dake tsakanin su…… kuma wannan karon ma kokarin ta da bijirewar ta, bai kwace ta da komai ba.

“You goddam lunatic! I hate you…..kuma insha Allahu sai Allah ya saka mini, ta hanyar da baka taba zato ba. Abinda kayimin sai an wa ‘yar ka, in baka haifa ba kanwar ka, in baka da ita UWARKA!”

Bai san sanda ya daga hannu ya zabga mata mari ba, marin da Raheenah ta tabbatar taga wuta a cikin sa. Kafin ya kama hannun ya rike cikin nadama! Wai shine da dukan mace…..macen ma mai amsa sunan matar sa. Amma abu na karshe da bazai iya dauka ba shine raini, don abinda take gani a matsayin babban laifi daga gare shi shi ko kusa bai kalle shi hakan ba. A tunanin sa ana aure ne for sex only, kamar yadda ake cin abinci kullum. Baya jin a duniya zai so wata mace bayan mahaifiyar sa. Kuma baya comparing din ta da sauran mata. Talkless of Rahinah ta ambace ta ta zaga.

“Duk rainin ki ya tsaya a tsakanin ni da ke, kada ki sake ki hada da uwata”.

Ya fada yana sake rugumota jikin sa ba tareda tausayi ba ya sake maimaita laifinsa, har da cewa “ai sadaki na biya, ki jawomin ayar da tayi umarni da soyayya, aure Ubangiji yayi umarni mu yi ba soyayya ba”.

This man is unbelievable ga tunanin Raheenah bata san a rukunin mutanen da zata sanya shi ba, gashi dan boko mai matakin master, amma jakancin sa akan diya mace ko gardin kauye bazai yi ba. She hates him again and again for his wickedness. Tunanin ta gabadaya ya koma kan how to escape from this abusive marriage.

Amma har kwanaki suka nausa zuwa biyar, bata samu wannan damar ba.

Yayin da Habib ya dukufa ga morar sadakin sa, don bai taba tunanin abinda yake yi din ba daidai bane, ko zata iya tafiya ta barshi tunda bata da kowa.

(Akwai maza da yawa irin Habibu Nahuche, wadanda baza’a ce rashin ilmi ya hana su son matan su ba, ko kasancewa masu nuna soyayya da tarairaya koda fake ce. Suna aure ne for their own pleasure. Ita mace kuwa ‘yar son lallashi ce da soyayya kuma har abada in baka iya tafiyar da ita ba, hankalin ta bazai taba nutsuwa da kai ba. Ita Rahinatu ma kallon Habibu take as rapist don bata yarda miji zai iya yiwa matar sa izayar da yake yi mata ba).

A duka kwanakin nan bata ci bata sha, sai taji hanjin cikin ta na neman tsinkewa ne take shan ruwan bunu ko ta sha madarar kwali, wanka kuwa rabon ta dashi har ta manta, watakila in yaji tana tsami, a yadda yake dan gayun nan mai son wanka da kamshi zai daina rabar ta.

Amma gogan nata ko a jikin sa, wani sabon abu ma ya tsiro da shi; fesa mata turaren sa ‘Carolina Herrera’ a duk sanda zai kusance ta, tana kuka tana tsine masa, amman kaman tana kara zuga shi.

Tsahon kwanaki shida ya tabbatar shi kansa ya samu lafiya daga masifar dake damun shi akan Raheenah, zamu iya cewa kanwa ce ta kar tsami kwannafi ya kwanta. Ya soma jin tausayin ta, kuma ya rage takura mata.

*****

RANAR KWANA BAKWAI

R

anar da auren su ya cika kwana bakwai ne komai ya faru, haduwar da rabuwar masu kama da blink of an eye (kiftawar ido). Gabadaya haduwar sa da saninsa da Raheenah Omar, zuwa auren su da zaman auren watanni uku ne cif har kwanaki bakwai na aure data yi a gidan sa.

A safiyar ranar tun asubah ta faki idon sa ta dauke masa mukullai, neman duniya yayi musu bai gan su ba, kuma baya so ta gane abinda yake nema kenan, don haka yaja bakin sa yayi shiru, kada ta gane bai rufeta ba tayi tunanin guduwa, shi kuma daga ranar ya fara nadama, ya kuma alkawartawa ransa bazai kara kusantar ta ba sai bisa amincewar ta.

Sannan zai yi kokari ya koma yadda duk take son sa, wato namiji dan soyayya, mara gaggawa, loving, caring, romantic. Mai bin komai a sannu. Sex will be his last priority a rayuwar auren su. In ta kama zai je makaranta ya shiga aji ya zauna a koya masa yadda zai koyi zama da mata ne zai yi hakan, sakamakon wani irin pleasant feeling (so na hakika) tamkar maganadisu mai jan zuciya da ruhi da ya ji yana shigarsa a hankali akan RAHINAH OMAR daga daren jiya zuwa wayewar garin yau.

Wayewar garin data cika kwanaki bakwai da auren su.

Bata taba yarda sun kwana gado daya ba, in suka gama damben su yayi galaba akanta anan kasan marbles da ya barta bata canza matsugunni, sai in ya fita ne taji yunwa zata kasheta take yunkurawa ta isa ga firji ta sha madara ta koma ta kwanta. Haka zata wuni kuka idan ta tuno karatun ta, da abokan karatun ta da Dadar ta. Yau ta dauke masa mukullai ne da niyyar zata gudu, kuma zata bar Jamus gabadaya.

Bai nuna mata bai ga mukulli ba, tana daga kwance inda take ya sunkuya ya ajiye mata kofin tea. Sai tiriri yake. Ta runtse ido hawaye na bulbula domin ko fuskarsa bata son gani. Kamshin turarensa duk ya mamaye ta. “Kiyi hakuri sweetie, i promised to become a changed person, if you give me another chance (nayi alkawarin canzawa, in har zaki bani dama). Yanzu dai na makara, inna dawo zamu tattauna sosai”.

“Allah yasa kafin ka dawo ka tadda gawata!”

Ta fada cikin rishin kuka. Tana mai addu’ar Allah ya dauki ranta ta huta kafin Habibu ya dawo

Murmushi Habib yayi, sannan ya sunkuya ya sumbaci bakin ta lightly. Wani abu da bai taba wanzuwa tsakanin su ba (sumba). Ta tattaro miyau ta tofa masa a fuska. Maimakon ta ga ransa ya baci ko ya falleta da mari kamar yadda ya saba, sai taga yasa dan yatsa ya lakato miyan ya kai bakin sa ya lashe.

Ya kuma kasheta da murmushi yace “i know that i offend you, and it’s intentional as you expect, but i promised to become new HABEEB (masoyi) har sai kin koreni sabida soyayya. Ki bani thirty minutes yanzu zan dawo we will discuss everything, in nace EVERYTHING ina nufin har ASALI NA da naki”.

Maimakon maganganun sa su farantawa Raheena, sai ma suka kara shafa masa shuni a idanun ta. Ba abinda zai ce ta yarda yana kaunar ta. Ya baro gini tun ran zane….zuciyar ta ta riga ta mace a tsanar sa.

Abinda kuma zai farfado da matacciyar zuciyar nan ba kankani bane. Ya riga ya raunata zuciyar ya yi mata illah. Tsanar data yi masa ba ‘yar kadan bace. Kuma zata nuna masa ita ba yar tsana bace duk rashin gatanta ta san ‘yancin kanta.

Haka ya fita yana waiwayen ta, ita kam ko ido bata sake dagawa ta dube shi ba. Mintina goma sha biyar ta bayar bayan fitar sa, ta mike tasa jallabiyya, tasa jilbab, sannan ta tattara duk wasu muhimman takardun ta da passport dinta ta fice cikin zafin nama.

*****

 

“Divorce (Scheidung) a kasar Germany: ba karamin abu bane. Domin tunda ke ke son sakin, sai kin dauki lawyer. Sannan zaki biya kusa €3,000 kudin kotu dana daukar lawyer. Ki rubuta application for divorce (divorce petition) in kin tabbatar kina da gamsassun hujjoji. Sannan ne za’a shiga family court a gudanar da sakin under German-law. Tunda dukkkannin ku kuna kasar Jamus.

4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!