Nameer Hausa Novel Complete
*NAMEER*
_(A good dog,deserve a good bone.)_
_By_
_Mom Mus’ab_
Follow me un whatpad
https://www.wattpad.com/user/Saadahjaafar?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
Page:-20
_Wanan page d’in sadaukarwa ne ga NAMEER FANS,sharhinku na kara mani karfin gwiwa,sai naji kamar nayi ta samb’ada muku ruwan pages dake d’unkule da read mores_
_Bazan barku haka ba,sai nace daku one love kawai_
Yana jinta ta fashe da wani matsanancin kuka mai tab’a rai, amma a wancan lokacin sam baiji wani abu mai kama da tausayinta ba,sai yanzu da ya fahimce komai.
Ya dawo da tunaninsa ga Hajiya da har yanzu bata daina kuka tana sharar hawaye ba, da kyar ya iya tsayar da nasa hawayen sanan yace bayan ya kawar da fuskarsa gefe.
“Abinda ka shuka shine zaka girba,shairan ko hairan shiyasa akodawane lokaci ake so ga musulmi yayi iya bakin kokarinsa wajan yak’i da shaid’an.
Kin bani mamaki Hajiya, ban kuma tab’a tunanin haka daga wurinki ba,amma babu komai ina fata hakan ya zamanto izina gareki tare da y’an baya.”
Karanta Littafin Jarababben Namiji Complete
Sai ya tsaya ya share hawayen sa sanan ya cigaba “Na yafe maki tuntuni zan kuma tayaki neman yafeyar Ubangijinki daya dubi tubanki ya yafe maki,amma kafin nan kiyi kokarin tuno duk wata yarinya da kika b’ata ma rayuwa domin muje ki neme yafeyarsu saboda ubangijinmu bai tab’a yafe laifin wani akan wani.”
Ta sunkuyar da kai k’asa tana jinjina maganar da take son fad’i.
“Bazan iya tuna iya adadin wad’anda na lalata ba,suna da yawan da ni kaina bansan su ba.
Sai dai kamar yanda na gaya maka Husna ce kawai na janyo da k’arfe sauran duk su ke kawo kansu gareni.”
Nan ma sai da yayi yak’e da zuciyarsa akan abinda ta fad’a d’in, kafin ya samu yace “Kada ki damu,ki samu ki tuno ko ba duka ba,in sha ALLAH ni zan shige maki gaba.”
“Zanyi,amma dai ina fata zaka fara rok’ar mani Husna, itace wacce nafi shiga alhakinta da yawa,itace nafi zama silar jefeta cikin masifa.
Husna na yawan zuwar mun a mafarki tana kuka tana fad’in na cuceta,na rabata da farincikinta na tabbata idan har bata yafemun ba,na cigaba da ganin masifu kala-kala a rayuwata.”
Rufe idanuwansa yayi yana tuno kyakyawar tarbiyyar Husna,da yanda komai ya canza lokaci d’aya abun bak’inciki kuma wai duk saboda mahaifiyarsa kafin yace “Shikenan Hajiya zan rok’eta.”
Bata iya cewa komai ba, har ya mik’e yana jan k’afa ya fice.
ALLAH ne kawai ya kaisa gida a wanan lokacin,tunani yake shin mey ma ya kamata yayi,kuma daga ina zai fara?
***
Yau cike da matsanancin tashin hankali su Mama suka tashi, sakamakon k’ara rikicewar jikin na Husna,nan da nan suka kira Mahrazu.
Shima dai hankalinsa a tashe ya kira Faruq ya sanar dashi.
Lokacin da suke gaya masa tashinsa a barci kenan, ko shiryawa baiyi ba.
Bai iya yin komai ba,ya zare keys ya fita cike da tashin hankali.
Sai dai kuma mey, yana fita k’ofar gidan yaci karo dashi zaune a mota da alamu ma ya jima a wurin.
Da mamakin abinda ya kawo sa ya taka burki sanan ya fito ya tunkaresa.
Ganin dosuwar Faruq d’in ya sanya Nameer dirowa ya tsaya akan k’afafuwansa har ya iso inda yake.
“Nameer, lafiya dai ko?”
Ya kallesa ido cikin ido,tsananin tashin hankali tare da firgici ya hango a k’wayar idon nasa, ya kuma sauke kallo da nazarinsa akan fuskar tasa, itama dai ta bayyana halin da yake ciki.
“Ban iya runtsawa ba sam,ban iya samun sukuni ba,ban iya samun nutsuwa ba.Na kasa had’iyar koda yawu ne ballantana kuma ruwa a bakina,kai halin da na shiga yayi muni da yawa ta yanda baki ma bazai iya misalta shi ba, komai yanzu ya shiga dawo mani a k’walwata tamkar wani shirin film.”
Da rashin fahimtar inda zancen nasa ya dosa yace “Duk akan mey?”
Bai basa amsar tambayarsa ba sai cewa yayi “Nasani kaine kad’ai zaka fayyace mani gaskiya, shiyasa nazo wurinka,cike da fatan zaka ce k’arya nake, mafarki ne kawai,cike da fatan zaka ce shirin film ne, dan ALLAH abokina kada kace da gaske ne ya faru,ka k’aryata ni,ka k’aryata zancenal”
“Wai menene? Ka hanzarta sanar dani mana ina sauri fa.” Yace wanan karon har da d’aga murya.
Hawaye kawai ya gani suna fita daga idanuwan nasa,abinda yasa shi yaji ya fara tsoron lamarin kenan.
Muryarsa na karkarwa yake fad’in “Wani mummunan mafarki nayi,wanda bana fatan sake kwanciya ma bare na kuma yin irinsa.
Faruq, nayi mafarki wai ina wulak’anta Matata abun sona,na kasa bata kulawar data dace da ita, a lokacin da take buk’ata,na kasa iya d’aga ido na kalleta bare kuma na tausaya mata a halin rashin lafiyar da take ciki, wai kuma dalilin haka har sai da muka samu sab’ani da kai saboda k’ok’arinka na son fad’a mani gaskiya saboda…” Sai ya fashe da kuka wanda yasa shi kasa k’arasa zancen da ya d’auko.
D’if wutar kan Faruq ta d’auke, ya shiga kallonsa da tsantsar mamaki, yana mai bitar abinda ya fad’a d’in.
Shikuma bai daina kukan ba har lokacin cikin kukan yace “Dan ALLAH Faruq kace ba gaskiya bane, dan ALLAH kace mafarki nake,Husnata,sanyin idaniyata abun k’aunata,ai bazan iya yi mata haka ba,kace dan ALLAH ba haka bane.”
Kamar wanda ya farka daga barci haka yayi firgigit ya dubesa yana cewa “Kana nufin kace bakasan kayi duk wad’anan ba?”
Ya tsayar da kukan nasa cak yana kallonsa, can kuma sai yace har yana hard’ewa “Kenan da_da gaske nayi d’in?”
“Biri yayi kama da mutum,kar dai zancen Mubeeena ne yake son tabbata”
“Kayi shiru Faruq, ka gaya mani da gaske na aikata?”
Batare da ya shirya ba ya kad’a masa kai game da cewa “Duk ka aikata Nameer.”
“Innalillahi wainna ilaihi raji’un.Yanzu ina Husnar take?” Tambayar kawai da yayi.
Har yanzu bai daina mamaki da tsoro a ransa ba,dan haka ma bai iya basa amsa da wuri ba, sai da ya kuma nanata masa tambayar sanan yace “Tana gidansu.”
Da azama ya juya zai nufi mota ya damk’osa ya dawo dashi baya yana tambayar “Ina kuma zaka?”
“Zanje na ganta na kuma shaida mata duk abinda ya faru, ba a hankalina nake ba,na rok’eta ta dawo mu cigaba da zamanmu kamar yanda muka saba.”
“Hmmm,bakin alk’alami ya bushe Nameer,ina tabbatar maka da yanzu idan kace zaka gidansu Husna to sai sun karya ka, saboda yanda suke hak’e da kai.
Abinda ya fi kawai kayi hak’uri ka bari mu bi komai a sannu.”
“Wallahi ko kashe ni zasu yi sai naje, na ga Husnata.”
Ganin dai da gaske yake yasa yace “To nutsu,yanzu dama can zanje saboda sun kirani jikin nata yayi tsanani, inaga muje taren”
Ai ko kafin ya rufe baki yayi tsalle ya fad’a motar Faruq yana “Muje na ganta.”
Ya bishi da kallo,kafin ya juya kawai ya kad’a kai ya nufi mazaunin deriba.
Tunda suka d’au hanya babu wanda yayi ma wani magana cikinsu, sai sak’e-sak’e da Faruq ya shiga yi, da son hasaso abinda yake faruwa.
Koda suka isa gidan, sun tarar da ita tana ta aman jini, wanda hakan ya d’aga hankalin Iyalin nata.
A rud’e ya shigo shi da Faruq d’in suka yi kanta,kan kace kwabo tuni ya sunkuce ta yayi mota da ita Faruq yana rufa masa baya.
Su ma su Mama bayan nasu suka bi batare da sun bi ta kan kasancewar Nameer a wurin ba.
*Some hours ago*
Komai ya soma lafawa,ta samu taimako daga likitoci, har ma ta samu barci ya d’auke ta.
Wanan ne ya ba Iyalan nata damar dawowa cikin hayyacinsu,sai dai abinda baza’a rasa ba.
Saifullahi ne ya dube Faruq bayan duk an basu umurnin fitowa daga d’akin da take saboda ta samu hutu sosai yace yana nuna Nameer da yake can gefensu ya had’a kai da bango.
“Mey kuma ya kawo wancan munafukin anan ?”
Faruq ya dubesu yana gyara tsayuwa yace “Ba wanan ya kamata ka tambaya ba Saifullahi,ina ga kamata yayi ka tambaye abinda ke damun y’aruwarka dan ciwon nata na yanzu ba wancan wanda kuka sani bane.”
Mama ta zaro ido cike da tashin hankali tace “Menene yake damunta likita?”
“A bincikenmu da mukayi ya tabbatar mana da ciwon zuciya ne ta kamu dashi,wanda hakan ya faru ne sakamakon damuwa da take ciki idan kuma ba’a gaggauta d’aukar mataki a kai ba, za’a iya rasata bakidaya dan zuciyarta zata iya bugawa farat d’aya.”
“Innalillahi wainna ilaihi raji’un.” Shine salatin da Mama take yi.
Mahrazu yace “Mama dan ALLAH kuyi hak’uri ku ceto rayuwar Husna.”
“Ta yaya mu zamu iya cetonta?”
“Nameer,na tabbata Nameer shine damuwar Husna, kamar yanda ta bayyana mani a baya, dan ALLAH kuyi hak’uri ku manta abinda ya faru.”
Saifullahi yayi caraf ya k’arbe “Wallahi k’arya ne, kawai wasan k’waik’wayo kuke so ku mana, shiyasa kuka zo dashi kuma kuka shirya cewa ta kamu da ciwon zuciya wato duk cin kashin da yayi mana ya tashi a banza ko?”
“Saifullahi, dan ALLAH ka dunga hak’uri a rayuwa,ita fa rayuwar nan bata yiwuwa sai da hak’uri, kada kuma tsananin fushi yasa ka manta d’umbin ribar dake tattare da hak’uri.”
Faruq ya dube Mama da duk jikinta yayi sanyi yace “Mama ni ban kira Nameer ba, duk da akwai niyyar kiran nasa domin yazo ga Husna,kamar yanda take muradi, ko hakan yasa hankalinta ya kwanta, ta amince a fita da ita waje ayi mata aikin da zata rabu da ciwon dake damunta kwata-kwata.
Kwatsam ina cikin tunanin ta inda ya kamata na biyo wajan shawo kansa, ya amince yazo d’in, saboda yanda na lura da sam baisan ganin Husnar, sai gashi yazo da kansa.
Maganar da yazo da ita ta matukar gigita k’wak”walwata, na shiga tsoro da mamaki daga k’arshe dai nayi nasarar tabbatar da abinda nake zargi na an shiga tsakaninsa da ita ne da zummar son a rabasu.
Wallahi Mama, ba wai saboda Nameer yana abokina nake son kare sa ba, sai dan nafi kowa sanin halinsa, kuma yanayin da yazo mani dashi ya k’ara tabbatar mani da duk abinda ya faru baida masaniya a kai.”
Ya kwashe yanda sukayi d’azu ya sanar dasu,hakan ya sanya jikinsu yin sanyi su duka.
Mama tace “Ruwa bai tsami banza,nima na so nayi wanan zargin duba da yanda suke a da.”
“Mama kada dai kice zaki yarda da wanan k’anzon kuregen?
Idan har da gaske hakane waye zai musu asiri, kuma meyasa zaiyi musu,ko su kad’ai ne ma’auratan da suke zaune lafiya da junansu?”
“Saifullahi shi fa tsafi gaskiyar mai shi ne,dan haka sanin waye yayi ko miye dalilinsa bashi da wani amfani tunda dai har hankalin yaron nan ya dawo batare da anyi aika-aikar da bazata gyaru ba, ai sai mu gode ma ALLAH, wanda kuma yayi hakan yaje shi da ALLAH duniya ce ai, tafi bagaruwa iya jima.”
Ya k’uta kad’an yana harare-hararensa.
Ta sake duban Faruq tace “Hakika kai d’in abokin arziki ne,irinka kuma sunyi k’aranci a wanan lokacin. Na jinjina ma k’ok’arinka sosai, na kuma yafe ma abokinka duk abinda ya faru.”
Har ran Faruq yaji sanyi matuka,fuskarsa ta cika da murmushi ainun.
“Mun gode sosai Mama,kuma in sha ALLAH nasan abokina a shirye yake domin ba wa Husna duk wata kulawar data dace.”
“Babu komai, mu ma ku yafe mu a bisa rashin fahimtar ku da mukayi tun farko.”
Yace “Babu komai Mama, akan gaskiyarku kuka yi komai, dan duk wasu iyaye nagari suna kokari wajan ganin sun k’wato ma y’arsu y’ancinta,,dan haka bazan ga laifin ku anan ba.”
Suka girgiza kai.Mahrazu yace “Ka kira Nameer d’in mu sake yafar juna.”
Da murmushi a fuskarsa ya amsa masa sanan ya juya ya nufi wurin nasa.
2 be continued.
Mrs A.I Faska ce.
Leave a Comment