Hausa Novels

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

 

 

 

 

NA MIJI K’UDAN ZUMA

 

 

By maman Islam

 

 

 

 

☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION

 

 

 

 

Page 1

 

 

“Assalamualaikum maman Khalid yaudai gani a kar ki ciny……………d’if maganar ya d’auke sakamakon ido hud’u da sukayi da SAMAD dan haka tayi kicin kicin da rai yayin da taji aranta kamar ta juya ta koma sai dai ta san idan ta koma anty DEENAH bazata tab’a jin dad’i ba tunda sun riga sunyi da ita yau zata zo, sannan kuma tana yawan yi mata korafin rashin zuwan ta wanda hakan yana da nasaba da yadda tayi masifar tsanar Samad d’in.

 

 

“Oyoyo mommy” yaron anty Deenah da fito yanzun wajen daddynsa ya kwala ihun murnan ganinta, saurin durkushe wa tayi ganin yayo kanta da d’an gudun sa ai kuwa yana zuwa ya fad’a jikinta ta rungume shi tsam tsam ajikinta tana mai jin dad’in ganinsa.

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

Itama cikin murnan ganinsa tace “oyoyo my boy ina Momma?”

Bai bata amsa ba yace “mommy ina tweets tin da titace a kawo min ya?”

Ya tambaye ta cikin tsatstsamar hausar da bata gama kama bakin sa ba.

 

 

Murmushi tayi ta d’an ja kumatunsa tace “kai my boy mai yasa baka mantuwa ne?”

Ta fad’a tana d’ebo alwan a cikin Jakarta ta mik’a masa karb’a yayi da murnan sa na gode my mom ya fad’a yana barin wajen da gudu yayin da tashi da kallo har ya haye jikin daddyn sa wanda tun shigowar SUHANA yake binta da wani mugun kallo suna had’a ido itama ta galla masa harara karab sai a idon Deenah wacce ta fito yanzun.

 

 

 

 

“A a SUHANA bana son iskanci meye haka wai Daddy sa’anki ne da kikayi masa irin wannn rainin?”

 

Itama sak’on hararan ta aika mata kafin ta saki wani mugun tsaki ta mik’e da sauri ta juya.

 

“SUHANA SUHANA SUHANA” Deenah ta bita da sauri tana kira harda d’an gudun ta, “SUHANA dan Allah karki tafi” Deenah ta fad’a da da d’an sanyi jiki, cak SUHANA ta tsaya tana goge hawayen da ya zubo mata amma bata juyo ba.

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

 

“Haba SUHANA me yasa kike haka ne duk kin bi kin canja hali sam raina Babba ba halin ki bane me yasa yanzun kika canja haka da yawa?”

 

 

 

Kuka ta fashe dashi tace “to anty me na masa da zai rik’a hantarana yana min kallon tsana da hararana?”

 

 

“Ba hararan ki yake ba SUHANA abinda mutane suke zargin ki dashi shine shima yake tunanin hakan sam baya jin dad’in yadda mutane suke ya mud’id’i dake akan abinda ba haka bane”

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

Kafeta tayi da ido tana kallonta yayin da wasu irin hawaye masu mugun zafi ya zuba mata tace “anty kema ZARGINA KIKE?”

 

girgiza kai Deenah tayi tace “ko kad’an bana zarginki ‘yar uwata tunda nike dake ban tab’a ganin wani abun assha atare da ke ba dan haka ban tab’a zargin ki ba SUHANA’ amma kinsan cewa dole zargi ya hau kanki abisa abubuwan da kike aikatawa”

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

“Ai kema kinsan dole ce tasani hakan bani da yadda zanyi ina samawa kaina nutsuwa ne amma wallahi bana aikata wani mugun abu”

 

 

“Na sani SUHANA amma dan Allah ki rik’a taka tsantsan da rayuwa saboda kinsan yanzu kiwon mutum ake”

 

“Naji kuma zan kiyaye ta fad’a tare da shafar fuskar ta tace”ni zan wuce anty”

 

“Au bazaki shiga ba?”

“Eh”

“Me yasa?”

“Saboda na tsani SAMAD kuma bana son ganin sa”

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

Murmushi Deenah tayi tace “SUHANA kenan kedai wallahi rigiman ki yawa ne dashi”

Itama murmushin tayi ta sumbaci hannun yayar tata tace “good by my ant”

Ita ma hannunta ta d’aga mata jikinta a sanyaye aranta tanaiwa kanwar tata fatan samun sassauci abisa matsalar ta.

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

 

Sanda ta koma d’akin tuni SUHAIL yayi bacci ajikin daddyn sa wanda yai kicin kicin da rai.

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

Yadda ya had’e rannan tasan saboda ganin SUHANA ne dan haka ta d’an saki murmushi ta k’arasa ta shige jikinsa tana kafe shi da kallon ta mai sanya masa nutsuwa da gusar da duk wani fushin sa, a sanyaye yace “ki hanata zuwa gidannan bana son ganin ta”

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

Kallon da tai masa shi da kansa sai da yaga rashin da cewar maganan sa,ko ba komai SUHANA yar uwarta ce kuma JININTA bai kamata ya rik’a nuna mata tsana karara haka a gaban taba.

 

“Wa fa akan wa kake magana?” ne ta tambaye sa fuskar ta d’auke da wani murmushi mai CIWO, rungumeta yayi ya kasa ce mata komi domin tunda wuri ya gano kuskuren shi.

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

“Dan Allah ka sassauta mata ka daina nuna mata baka sonta saboda idan BABU NI ITACE ZATA MAYE MAKA GURBI NA”

 

 

“Allah ya sauwake min” ya fad’a tare da hankad’e ta daga jikinsa tayi wani irin baya zata fad’a kan tsohon cikin dake jikinta, cikin wani irin zafin nama ya fisgota ta dawo jikinsa kafeshi tayi da wani irin kallo kafin ta fusge jikinta ta tashi ta barshi anan.

 

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

Ya k’ure ta Kennan?

Ya ayyana hakan a ranshi take ya durk’ushe anan tareda dafe kansa cikin takaici sam Deenah bata ganewa batasan wacece SUHANA ba, batasan tantirancin SUHANA ba shiyasa har take iya fushi dashi dashi akanta tunda yake bai tab’a ganin mara mutuncin yarinyar sama da SUHANA ba bai tab’a jin tsanar mutum kamar SUHANA ba a rayuwar sa ya jima sosai a wajen yana saka da warwara.

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

Niko ina fitowa daga gidan anty Deenah nasawa raina cewa nida gidanta har abadan saboda bana k’aunar ganin samad ko kad’an a rayuwata, ta fad’a tana hararan gidan kamar gidanne yayi mata laifin.

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

 

 

Kanta tsaye gidan su Sameer ta nufa yana ganinta ya tare ta cikin farin ciki ya rungumeta tsam a jikinsa yana sakin wata ajiyar zuciya “SUHANA jiya kin barni cikin tashin hankali da damuwa dan Allah SUHANA ki taimaka ki AURENI wallahi zanyi miki duk abinda kike so”

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

K’wace jikinta tayi daga nasa tare da galla masa wata katuwar harara tace “amma baka da hankali Sam, sau nawa zan fad’a maka cewa babu aure a tsakanin mu wannan ya zama na farko da k’arahen da zaka kumayi min zancen wani aure idan ba hakaba to wallahi saina yanke duk wata alak’a dake TSAKANINMU kaji na fad’a maka” ta k’arasa tana kuma galla masa wata hararan da tafi ta karko tare da sakin wani mugun tsaki ta zari mayafinta da jakkar ta da ya yasar mata anan gefe ta gaba ta barshi dafe dakai.

 

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

Allah ya sani yana k’aunar yarinyar sai dai yarasa dalilin dayasa koda wasa bata k’aunar yayi mata batun aure baisan dalilin ta nayin hakan ba ko kuma shine bata k’auna?

 

 

 

 

MAMAN ISLAM CE

 

Namiji Kudan Zuma Hausa Novels

 

Yawan comment yawan typing insha Allah

Leave a Comment

error: Content is protected !!