Nasmarh a cell Hausa Novel Complete
Tag: NASMARH A CELL
© Anup Janyau
Page 1
“Dakata D.p.o! ban fahimce ka ba?. Kud’i na fa ya cinye, nairah na gugar nairah har dubu goma sha biyar, amma za ka wani ce in basa hakuri ayi sulhu. Idan na bashi hak’uri Allah tsinen albarka”.
Nasmah da ke zaune kan wani d’an teburi ta fad’a a mugun fusace tana mik’ewa tsaye.
“Ke! ya kamata ki iya bakinki ki san da wa kike magana, ko kin manta nan police station ne muke ba tsakiyar kasuwa ba?”.
Inji wani dan sanda da ke gefenta. Wani kallo Nasmah ta shiga watsa mashi tun daga k’asa har zuwa sama kana tace;
“Madallah! ko ba police station ba?. To da kai da Police da station din da d.p.o, da d.s.p na bi ku da gudu ba wando”.
Karanta Littafin Gidan Uncle Hausa Novel
Idan naji ruwan comments zan cigaba
#Anup: NASMARH A CELL
*Tsokaci: Wannan labarin k’irk’irarre ne kuma gajere. Banyi shi don cin zarafin kowa ba, sai domin in nishad’antar da masoyana tare da masoyan Queen Nasmah a duk inda suke Sannan ban yarda a juyamin labarina ta kowace irin siga ba sai tare da izini na.*
Page 2
Da wani irin sauri D.P.O da sauran jami’an da ke wurin suka bita da kallo mai d’auke da mashahurin mugun mamaki. Yayinda bakunan wasun su ke a hangame, tsabagen dirar mikiya da kalaman nata sukayi musu.
Lokaci d’aya gaban Nasmah ya k’ire ya fad’i ganin irin kallon da suke binta da shi, amma haka ta maze tare da d’auke kanta daga barin kallonsu ta mayar wani gefen tana murgud’a baki.
D’an jinjina kai D.P.O yayi tare da ajiye biron hannunsa akan file d’in gabansa, har lokacin ya kasa cewa komai.
“Yallab’ai! don Allah ku yi hak’uri, ni wallahi sam bansan rashin ta idonta ya kai har haka ba”.
Inji saurayin da ke zaune chan k’arshen teburin da Nasmah ta tashi. Murmushin yak’e D.P.O yayi tare da fad’in,
“Kar ka damu. Ai mun saba ganin irinta ba wannan ne karon farko ba. Saidai munada masu yimuna maganin su cikin ruwan sanyi”.
Nasmah ta had’iye wasu yawu da k’arfi, jin abinda ya fad’a saidai har lokacin bata yarda ta sake kallon b’angaren su ba.
“Kin gama bin mu da gudun ko da saura?”.
Shiru tayi tak’i cewa komai. Ganin hakan ya sanyashi sake fad’in,
“To tunda kin gama sai ki zauna ko?”.
Sai a lokacin Nasmah ta juyo ta kallesa tace;
“Kaga ni ba sai na zauna ba D.P.O. Kawai kuce ya biyani in kama gaba na, don na bar mai adaidaita a waje yanata jirana tun d’azun”.
“Ai maganar barin ki wurin nan be ma taso ba”.
“Kamar ya?”.
Ta tambaya a d’an razane.
“Kamar yanda kika ji”.
Ya bata amsa, tare da kai dubonsa ga d’an sandan da ke tsaye gefen sa yace;
“Je kira min Lami Sangama!”.
Cike da girmamawa yace;
“To Yallab’ai”.
Umurni ya ba sauran jami’an da ke tsaye sunata kallon Nasmah akan su wuce. Suna barin wurin D’an Sandan da ya aika na dawowa tare da wata sangamemiyar mace. Wacce tun a kallon farko idan ka yi mata zaka sha jinin jikinka. Irin manyan matan nan ne masu k’irar k’atti. Fuskarta a murtuk’e tamkar bata tab’a dariya ba.
“Yallab’ai gani, aka ce kana nemana”.
Jin k’atuwar muryar Lami Sangama ta sanya Nasmah da hankalinta ke wani b’angaren saurin kai dubonta zuwa garesu.
Tun daga kan manyan takalmin Lami Nasmah ta shiga bi da kallo har ta kai kan bak’ar fuskarta cikin rashin sa’a suka had’a ido. Wanda yayi sanadiyar hautsinewar yan hanjin cikin Nasmah…….
#Anup NASMARH A CELL
© Anup Janyau
Page 3
Lami ta wani sake had’e fuskarta tamau! alamar ba wasa, ganin yanda Nasmarh ke bin ta da wani irin kallon k’urillah tamkar ta samu Tv, don sai ta faro tun daga k’asa zuwa sama sai kuma ta dawo daga sama zuwa k’asa. Ita kuwa Nasmarh kallon mamaki da ban al’ajabi ne take yimata. Saboda zata iya rantsuwa a kan tunda ta zo duniya bata tab’a ganin sangamemiyar mace mai k’irar samudawa irin ta Lami ba, wanda tun sanda tayi tozali da ita wani mashahurin tsoronta ya mamaye ilahirin zuciyarta, maimakon ta bata dariyar da ta zame mata d’abia, don kuwa duk lokacin da taga abun dariya saita dara ko da za’a kasheta ne ko, amma sai gashi a wannan karon dariyar ma ta nemeta ta rasa, sai fad’uwar da gabanta ke cigaba da yi. Duk yanda ta so danne tsoron da take ciki ta kasa.
Tuni D.P.O ya hango tsoron Lami k’arara a cikin k’wayar idanuwan Nasmarh, hakan ne ya sanyashi yin guntun murmushi tare da kallon Lami da ke k’ame wuri d’aya tamkar an dasata, yace;
“Dama wannan yarinyar ce naga kamar tana buk’atar karb’ar ‘yar marba a wurinki. Shiyasa nace a nemo ki kusa. Amma kafin nan bari mu ji idan har yanzu tana nan akan k’udurinta na k’in bin umurnin da na bata”.
Da sauri Lami ta tari numfashinsa ta hanyar fad’in,
“Yallab’ai! ko dai ka bani ita a yanzu, Allah so daga baya ku k’arasa, don naga a tsaitsaye take ga dukkan alamu notin kanta yana d’an rawa, kaga sai in d’an d’aura mata shi”.
Ga baki d’ayan hankalin Nasmarh yana wurin kallon k’attin takalmin Lami wad’anda girmansu baida misali. Shiyasa bata ma san me suke cewa ba.
“Keeee!”.
Lami ta daka mata wata gigitacciyar tsawar da saida ko ina na d’akin da suke ciki ya amsa. A rud’e Nasmarh ta d’ago ta kalleta, don ba k’aramar shigarta tsawar tayi ba. Saidai lokaci d’aya ta fara kiciniyar b’oye tsoron da take ciki ta k’arfi da yaji, don ta fahimci idan har ta nuna tsoron wannan sangamar matar kashinta ya bushe, dole ta nuna mata itama jan wuya ce. Da wannnan tinanin tayi amfani da shi wurin wurgawa Lami wata mugunyar harara tare da murgud’a mata baki tace;
“Malama! Nasmah sunana ba Ke ba kin gane ko?. Ki bar ganinki wata babbar halitta da ke, ba tsoron ki zan ji ba, don wallahi tsaf zanyi tsallen albarka in chafki wuyanki in wujijjigasa in watsar gefe”.
Ta k’arashe maganar cike da k’arfin hali. Wani irin zaro idanuwa waje Lami tayi, tana k’ok’arin nufar wurin Nasmarh D.P.O yayi saurin dakatar da ita da hannunsa kana ya kalli Nasmarh fuskarsa a d’aure yace;
“Wai ke halama gidan ku babu manya ne?, da kike yiwa mutane rashin kunya”.
Nasmarh tayi masa wani kallo sannan tace;
“Tambaya kake ko neman sani?. Ai duk abinda nayi ku ne kuka janyowa kan kh, In bancin da rashin adalci meyasa ba za’a biyani hak’k’ina ba?, sai a wani fake da in basa hak’uri don na zagesa, gareshi farau zagi ne?, naga ko shugaban k’asa an zaga kuma an zauna lafiya bare shi banza dillalin kashi. Tou billahil azim a kan kud’ina banada mutunci ko na k’wayar zarrah. Bari kaji D.P.O a kan kud’ina na fi son station d’in nan ta kama da wuta!”.
Tana gama fad’a masa haka ta juya a fusace wurin Saurayin da ya ba D.P.O hakuri d’azun tace;
“Na rantse da Allah Kamalu ka bani kud’ina tun muna shaida juna. Idan ba haka ba zan shuka maka rashin mutunci fiye da na baya.!”.
Hahahaha a kafta
Nasmarh tace duk mai yimata dariya zatayi tsallen albarka ta chafki wuyan mutum, to nidai babu ruwana
#Anup
Leave a Comment