Hausa Novels

Nawwal Hausa Novel Documents

Nawwal Hausa Novel Documents

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

NAWWAL

 

STORY AND WRITTEN BY

 

GIMBIYA AYSHU

 

 

ELEGANT ONLINE WRITER’S

 

 

BISMILLAHIN RAHMANIN RAHIM

 

 

PAGE 1

 

__________________________Wata matashiyar budurwa na hango mai kimanin shekara goma sha tara,sanye take da dogon riga na abaya kalan baki,tayi rolling kanta da dankwalin rigar,kafan ta sanye da wani bakin kanvas,kai da gani kasan takalmin ya ci kudi,hannun ta rike da makullin mota da waya kiran iPhone 13 tana daddannawa,bayan kaman second biyu ta kara wayan a kunne,ringing biyu kawai wayan yayi aka dauka daga dayan bangaren,”Sallama wata matashiyar budurwa mai kimanin shekara goma sha tara tayi”,amsa sallaman dayar matashiyar budurwar mai suna Suhailat tayi tana yauki sannan tace”ki fito mu tafi”,da toh dayar matashiyar budurwar mai suna Nawwal ta amsa,”kashe wayan Suhailat tayi bayan ta gama magana”,fita tayi daga parlor ta nufi parking space,wani bakin EOD ta bude ta shiga,bayan ta gama warming  motan ta ja shi ta nufi gate,horn tayi mai gadi dake cikin dakin shi ya fito da sauri ya bude mata gate ta fice daga gidan,bayan kaman minti biyu tayi horn a kofan gidan su Nawwal,fitowa Nawwal tayi jikin ta sanye da dogon hijabi kalan ja,hijabin ya amshe ta sossai,dama gata farar mace,bude wurin mai zaman banza tayi ta shiga ta gaida Suhailat,”amsawa  Suhailat tayi a dakile ta dauke kai”,murmushi kawai Nawwal tayi ta juya tana kallan hanyya,ko tari bai kara hada su ba har suka isa makaranta,Suhailat na gama parking ta kalli Nawwal da har ta bude kofa zata fita tace”kar ki bar ni ina jira idan an tashi,inko hakan ta faru tafiya zanyi na barki”,murmushin ta mai kyau Nawwal tayi tace insha Allahu sis Suhailat,”dalla mata harara Suhailat tayi sannan ta dauke kai,kulle kofan Nawwal tayi ta nufi hanyyan department din su tana murmushi,domin inda sabo ta saba da halin Suhaila,ta rasa inda ta samo wannan halin,girgiza kai kawai tayi ta shige Dpt din su.

 

Sai da Suhailat ta shafe minti goma kafin ta fitar da kafan ta daya daga cikin motar,bayan minti biyu ta fitar da na biyun,gyara zama tayi ta daura kafa daya kan daya,tana lasa waya,daga kai tayi taga wani mota ya doso parking space,”zaro ido Suhailat tayi sakamakon gane mai motan da tayi,da sauri ta dau jakar ta ta kulle motan ta nufi department din su da sauri tana tafiya tana waigen shi,tana shiga hall shima ya shiga ya kulle kofan,ajiyar zuciya Suhailat ta sauke ta naimi kujera ta zauna.

 

 

 

Da misalin karfe Uku da rabi Suhailat ta fito daga hall fuskar ta a murtuke,hannun ta rike da goran ceway water,tana tafiya a hankali kaman bazata taka kasa ba,tsaye ta tadda Nawwal a jikin mota ta nade hannun ta a kirjin ta tana ta kalle-kalle,dannan car key Suhailat tayi tayi unlocking motan,bude driver seat tayi ta shiga,Nawwal ma ta bude bangaren mai zaman banza ta shiga ta zauna bayan ta gaishe da Suhailat,bayan kaman minti uku Suhailat tayi reverse suka bar haraban makarantar…………………………………

 

 

By Gimbiya Ayshu

Nawwal page 2

 

 

STORY AND WRITTEN BY

 

 

 

GIMBIYA AYSHU

 

 

 

 

ELEGANT VERIFIED WRITER’S 📚

 

 

 

 

PAGE 2

 

 

__________________________Basu suka isa ba sai gabda la’asar,Suhailat na ajiye Nawwal aka kira sallah a masallacin dake da dan tazara da gidan su, knocking Nawwal tayi a bakin gate din su,bayan kaman minti biyu mai gadi yazo ya bude mata,gaishe shi tayi fuskan ta da alamun fara’a,da kulawa mai gadi ya amsa mata yana tanbayan ta ya makaranta,”da Alhmd Nawwal ta amsa ta nufi cikin gida”,bude kofar parlor tayi ta shiga bakin ta dauke da sallama, shiru kake ji a parlor babu kowa,direct up stairs Nawwal ta nufa,bata zarce ko ina ba sai dakin Mummy,sallama tayi a bakin kofar, Mummy da fitowan ta kenan daga bayi ta amsa mata tare da bata izinin shiga,”tura kofan Nawwal tayi tana ya mutsa fuska,gaida Mummy tayi ta naimi gefen gado ta zauna tare da jingina bayan ta”murmushi Mummy tayi tace kin gaji kohhh!Habibty,”daga kai Nawwal tayi tana shagwabe fuska”,dan dariya Mummy tayi tace Allah ya shirye ki da san jiki wlh,Ni dai tashi kije kiyi wanka,zakiji karfin jikin ki,kuma kinga an kira sallah,maza kije kiyi sai kizo kici abinci kinji,yau favourite dinki na dafa”tashi Nawwal tayi da sauri kamar wata karamar yarinya tana tsalle tace yeeeeehhhhhhh!Mummy na shiyasa nake sanki kaman kinsan ko shi nake marmarin ci yanzu”,dariya Mummy tayi tace i nasan abinda Habibty na tafiso,kinga ko dole na miki,ke dai je ki shirya lokacin sallah na tafiya,”da toh Mummy Nawwal ta amsa ta nufi dakin ta da sauri”dariya Mummy tayi tace Allah ya shirye ki Nawwal,zanga ranar da zakiyi hankali,ta karasa maganar ta da murmushi a fuskar ta tana girgiza kai.

 

 

 

 

 

 

Horn ta danna da karfi,da sauri mai gadi ya tashi ya bude mata gate,cilla anchin motan tayi ta naimi wuri tayi parking,jakar ta ta dauka sannan wayoyin ta da handout dinta ta fito daga motar ta kulle,har tayi taku uku kafin ta mika hannun ta ta baya ta danna makullin motar inda motar ta shiga key,danna kararrawar kofan parlor tayi,bayan kaman minti biyu mai aikin su ta karasa da sauri har tana tuntube,dan tasan ba mai wannan aikin face Suhailat,dan kaf gidan ita ke irin wannan salon,aiko tana buɗe kofan Suhailat ta rufe ta da masifa,har da zagi,uffan mai aikin bata furta ba,dan idan ta kuskura tayi magana toh ta siya ruwan dafa kanta.

 

 

 

Upstairs Suhailat ta nufa ta shige dakin ta,tana shiga ta ajiye kayan hannun ta a bed side drawer sannan ta yaye gyalen kanta ta linke,drawer ta nufa ta dau sabon towel,kayan jikin ta ta cire sannan ta daura towel,kayan data cire ta kwashe ta zuba su cikin basket din kayan datti,bayi ta shiga ta haɗa ruwan sanyi da ruwan zafi,bayan kaman minti goma ta gama wanka ta dauro alwala sannan ta fito daga bayin,direct dressing mirror ta nufa taja kujera ta zauna, lotion dinta ta dauko ta fara shafawa bayan ta kammala ta dau tulare tabi jikin ta da shi,tashi tayi ta nufi jikin drawer ta,gefen inda take ajiye kananan kaya ta bude ta dau bom-short da wani harmless singlet dukkan su fari kal-kal,kulle bangaren tayi ta bude inda take ajiye dogayan riguna ready maid,wani jan dogon riga ta dauka ta ajiye kan gado saman bom-short din data ajiye,gefen inners ta nufa ta dau jan bra da pent Shima kalan ja,kulle drawer tayi sannan ta shirya cikin kayan,bayan ta gama shiri ta bude bangaren hijabi ta dau wani jan hijabi dogo har kasa,kulle drawer tayi ta dau darduman dake bed side ta shinfida,saka hijabin tayi sannan ta tada sallah,bayan minti biyar ta idar,bayan ta gama Addu’a ta mike ta linke hijabin tare da darduman ta ajiye su kan bed side,dankwalin rigar ta daura ta dau babban wayan ta ta fice daga dakin ta nufi na Mum,bayan tayi knocking aka bata izinin shiga,tura kofan tayi ta shiga,iske Mun tayi akan darduma tana lazimi,gaida ita tayi,daga mata kai kawai Mun tayi ta cigaba da abinda take, Suhailat na ganin haka ta daura kafa daya kan daya ta kunna data ta bude tik tok………………………………….

 

 

 

 

Kuyi hakuri da wannan bani da lokaci ne Amman insha Allahau zan riga squeezing nayi posting.

 

 

 

Ina qaunar ku maso yana tare da muku fatan Alkairi.

 

 

 

By Gimbiya Ayshu

 Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [ Nawwal Hausa Novel Documents]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!