Hausa Novels

Ndaigolam Hausa Novel Complete

Ndaigolam Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Zaune yake akan d’aya daga cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun da ke cikin k’awataccen parlour Wanda ya kawatu kuma ya had’u,mai zaman mutum biyu,

 

 

A zahiri TV yake kallo sai dai a badini kuma ba TV yake kallo ba, zaka lura da hakan ne idàn ka karanceshi domin ko kefta ido bayayi saboda nisan da yayi a wata duniya wacce babu ranar da Allah zai wayi gari ba tare ya Yaje ba,

 

 

Tunani yakeyi na mamaki tsawon shekarun da aka kwashe ana dauke kudinsa ta account duk da irin matakan tsaron daya sawa bank account dinsa amma yasan every Monday sai ancire masa makudan kudade wadanda har ila yau ya rasa daga ina matsalan take, shin daga shine? Ko kuwa na bank dinne?

 

 

Macece wacce a kallah ba za ta haura 45 ba ta shigo palourn bakinta d’auke da guntuwar sallama,ganinsa a haka yasa ta yin wata shegiyar murmushi mai d’auke da tarun ma’anini Wanda ita kadai ta sani.

 

 

Karan ajiye tray d’in data shigo dashi mai d’auke da 2 cups sai just and water ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin d’aya tafi,

 

Kallonsa tayi kana tace “har dai ila yau ka na kan wannan banzan tunanin naka ko? Hmm tukunna ma,kana ta juya ta fita abunta,

 

 

Numfashi ya sauke kana ya d’auki bottle water ya ballen marfin ba tare da ya juye a cup ba kawai ya kafa kai ya hau sha.

 

 

 

Zaune suke parlourn yayin da kowa ke abunda yakeyi,

 

 

Maza biyu ne sai mace d’aya,

 

 

Namiji kuda d’aya Wanda a kallah Shekarunsa zasu kai 30 mai suna fahad, daga ganinsa za ka san lallai tarbiya da mutunci basu samu gurbin zama a wajen shi ba, duba irin askin dake kanshi,

zaune yake a kan 1str shisha ne a hannunsa yana sha kaman Wanda ya samu abunda yake so don har wani lumshe ido yakeyi,

 

 

Sai mai bi Wanda ba zai haura 27 ba mai suna Ameen shima dai kaman na fahad ne duba da kayan jikinsa da kuma askin Dadan dake kanshi,

shi kuma waya ne a hannunsa kiran iPhone 11 pro,yanata aiki akanta Wanda daga motse-motsen da yakeyi zaka San ba abun arziki yake aikatawa a ciki ba,

 

 

Sai kekkyawar budurwar wacce ba za ta wuce 25 ba ita ma dai wayar ce a hannuta tana chart a ciki,a yayin da kekkyawar fuskarta ke dauke da sihirtaccen murmushi.

 

 

 

Shiga tayi cikin parlourn

Kallo ta kare musu d’aya bayan daya,kana ta kada kai ta shiga daki,

Hajiya Khadijah matar Alhaji Abubakar nura kenan,

 

 

 

******

Amina! Amina! Amina! yake kira,

 

Wacce ke zaune akan gado ta jingina da allon gadon, sai dao ko kira daya batajiba sakamakon nisan da tayi a tunanin data fada Wanda ya dauketa tsawon lokaci,

 

Hannunsa yasa ya dan bugi cinyar ta yasata dawowa daga tunanin,

 

 

Kallon ta Yayi kana ya kada kai yace”haba Amina har yaushe ne zaki daina wadannan tunane-tunanen? Bazaki fawwalawa Allah komai naki ba? Shifa haihuwa na Allah ne ko kinason ja da hukunci Allah ne?

 

 

Sauke Numfashi tayi kana tace

 

“Kayi hakuri Alhaji na rasa yaya zanyine ,na kasa sabawa da kalaman da umma ke gaya min kullum idan naje gaisheta duk da ba yau bane ta fara,

 

 

Ni kaina yanzu rashin HAIHUWA ta fara damuna yanzu Auren mu ya kai shekara 20 har da wani abu amma shuru, kaima nasan abun na damunka kawai kana boyewane,

 

ta karasa maganar tana share hawayen dake saukowa akan kunshinta,

 

Zama yayi a gefen ta kana ya jawo hannun ta yasa a cikin nasan kana ya fara mata nasihohin daya saba fada mata.

 

 

 

★★★★★

 

Mikewa yayi sakamakon wani tunani da yazo mishi,

 

Hanyar da zata sadashi da babban parlourn gidan ya nufa inda ya iske su fahad zaune kaman yadda Mommy (Hajiya Khadijah) samesu,

 

 

 

Kallo ya kare musu daya bayan daya sannan ya fara magana cikin daga murya yana cewa,

 

 

Wato duk yadda zanyi sai dai nayi bazaku daina abunda kukeyi ba ko?

 

 

Modern 7yrs ake dauke mak’udan kudade account dina a ko wani sati , wallahi this time around bazan bari ya tafi a banza ba sai na dauki mummunan mataki akanku,

 

Wai kukam wani irin yaya ne wadanda basu da buri sai na ganin durkushewana?

 

 

Nikam meyasa Allah ya azirtani da wadannan yayan?

 

 

Ya Allah meneyi maka? ya karasa maganar cikin rauni sanna muryansa na rawa,

 

 

“`ai nane ma lelwa doggata 6iyum lada“` (Ai dama 6arewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba) inji mommy wacce ta fito daga dakinta zata kitchen ta fada tana mai shigewa cikin kitchen tamkar ba ita tayi maganan ba,

 

 

Daddy kam ka’da kansa kawai yayi ya nufi nufi hanyar waje a yayinda idanunsa ke fidda wassu hawaye masu zafi,don irin wadannan kalaman mommyn sukan tuno masa da abunda ya faru na tsawon shekaru talatin da wani Abu,Wanda bai ta6a dana sani ba ko dan k’ank’ani ne.

 

 

 

Bro nifa Ina ganin gwara mu karasa wanna old man din kowa ya huta , abunda ya fito daga bakin ameer kenan bayan fitan daddy,

 

 

Wani shegen murmushi fahad Yayi kana yace

 

“Yaro yaro ne me kake sauri na baka na zuba kasan ni bana gaggawa a lamari na,domin gaggawan 1mnt kan iya saka kayi asaran tsawon shekaru,don haka ka bari mu gama da *A&N an sons company* sannan jiya naji yana magana zayyi wata tafiya zaije Canada magana wassu motocin dayayi ordern su ,kaga kafin ya dawo zamu gama da companynsa na Saida motocin dake cikin State lowcos,kaga kuma wannan filin dake cikin New GRA dayakeson gina estate mai dauke da school, hospital shoprit D.S shi mun kusa gamawa dashi don saura kirisi mu karasa aiki akansa , daga nan kuma sai mu Karasa wassu abububuwan ina son ganin yadda zayyi idan ya gane abunda muke shirin aikatane masa don sai hawan jninsa ya tashi,ko ya kace ya karasa maganar yana mai dagawa ameen gira iya daya (Irin ya dinnan)

 

 

Ihu ameer yayi yana mai buga kafarsa a kasa , kana yace ”ai ciwon zuciya ce zata kamasa ba hawayn jini ba,kasan bazai rage da komai ba .

 

 

 

Dariya sukay kyalkyale dashi Wanda daga jin sa zakasan na zallan mugunta ne.

 

 

 

 

Ameerah ce ta dago da kanta tace ” ya fahad wallahi kuji tsoron Allah,

 

 

Ke!!!

 

 

Shine abunda ameen ya fada yana mai girgiza kansa irin zaki dakunnan,

 

 

Ameen kuwa kallon behave your self ya mata kana ya kada kansa tare fita daga daga parlourn ya nufi hanyar waje,

 

 

 

Duk abunda sukeyi mommy dake kitchen tana jinsu daidai kala bata tofa ba.

 

 

 

Alhaji nura kuwa jin kansa na neman tsagewa ne saboda ciwo yasa ya dauki wayarsa ya dannawa docco Ahmed (family doctor) kira.

 

 

 

 

*****

A washe garin ranar da musalin 9:30 Hajiya ameenah ce da mijinta alhaji Abdullahi nasir ke tafiya a jere cikin shirinsa na tafiya office,

 

 

Hanyar da zata sadasu da side d’in Hajiya iya (Mahifiyar Alhaji Abdullahi )suka nufa don gaisheta kaman dai yadda suka saba ko wace Safiya kasancewar gidan daya,

 

 

 

Da isarsu parlourn sallama sukayi inda suka tarda wata bakar mata mai Dan jiki wacce tsufa ya gama bayyana a jikinta,a shekare matar zata iya kaiwa 76-78 zaune take akan daya daga cikin kujerun parlourn ta mike kafafun yayinda wata `yar budurwar yarinya da alama yar aikice ke mata danna a kafaffun ,

fara’arta ce ta dauke lokacin da idunta sukayi tozali da Hajiya Amina don babu wacce ta tsana sama da ita,

 

 

Dukkansu tsugunawa sukayi a yayinda Alhaji Abdullahi ya fara gaisheta sannan Hajiya Amina , sai dai bata nuna tasan da wanzuwar wata halitta a gurin illa ma hankalinta data mayar akan TV tana mai cewa Alhaji Abdullahi

 

”anshirya za’a tafi? to Allah ya kiyaye hanya ya kuma bada sa’a,

 

 

Cikin hadiye abunda ya tsaya masa a makoshi ya amsa da ”ameen

 

Kana sukayi Sallama suka fito,

 

 

 

Kallon ta Yayi kana yace ”kici gaba da Hakuri ameena Insha Allah komai zai wuce,

 

 

Murmushi tayi Wanda daga kallon wannan murmushi zaka San lallai ba har zuci bane iya leben baki ne,

 

 

Kana ”tace ba komai ai Iya ma mahaifiyata ce tunda ta haifamin gwarzon miji da baya gajiya da kwantar min da hankali ,Wanna dalilin yasa nake alfahari dakai a kullum ya mijina ta karasa maganar cikin sanyi murya.

 

 

 

*Waye Alh.Abdullahi nasir?*

Sunan mahaifinshi malmnasir, haifeffen garin Bauchi ne a anguwar jaki,shida matarsa Hauwa’u-kulu (Iya) sai dansu daya mai sunan Abdullahi,

 

 

Kulu irin masifaffiyar matce wacce bata barin ta kwana ballen tana tayi tsami,India ka tabo kulu to Wallahi kaga bone domin kwata-kwata bata da hakuri ko na miskala zarrati don zawo ma zaifi Kulu hakuri wannan masifar nata yasa bata shiri da kowa a cikin danginsa don bata ragarwa kowa ba.

 

a yayinda malam Nasir ya kansanceai sanyi sannan maharkuci wonda Allah yaso Abdullahi ya gado halayen mahaifinshi,Anyiwa Abdullahi taribiya daidai gwargwado Yayi makaramta arabi da boko indai a boko har yakai matakin degree inda ya karancin Accounting, bayan yin service ya samu aiki a GT Bank dake cikin garin.

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!