Neehal Hausa Novel Complete
……….Bayan Sadik ya gama cin abinci suka haɗu gaba-ɗaya a Parlour’n Abbansa, shi, Abba, Maamah, Umma, Hajiya, Kawu da mahaifiyar Maamah da ƙannen Abba guda biyu. Abba ne ya fara magana da faɗin. “Alhamdulillah, Alhamdulillah, Masha Allah, muna ƙara godewa Ubangiji buwayi gagara misali, mai mayar da farin ciki zuwa baƙin ciki, da mayar da baƙin ciki zuwa farin ciki. Kwana takwas i war haka zuk’atanmu cikin tsananin farin ciki suke, amma cikin ikon Allah washegari sai ya canza mana zuk’atanmu zuwa baƙin ciki da fargaba da tsoro gami da zullumi. A yau kuma sai ya sauya mana su da tsananin farin ciki, muna fata kuma ya yarje mana mu cigaba da kasancewa cikin farin ciki har ƙarshen rayuwarmu, Ubangiji Allah kar ka ƙara maimaita mana irin wannan tashin hankalin da muka shiga har ƙarshen rayuwarmu.” Suka amsa da Amin gaba-ɗayan su. Kawu ya kalli Sadik ya ce. “Masha Allah Abubukar, mun ji daɗin dawowar ka cikin k’oshin lafiya wanda ba mu taɓa zaton haka ba, babu irin sak’e_sak’en da ba mu yi ba akan ɓatan ka, mu ce kidnappers ne, mu ce ko masu satar mutane ne, mu ce ko kai ka gudu da kanka, mu ce ko asiri akai maka ka bazama duniya, babu abun dai ba mu ayyana ba, sai daga baya muka gane bakin zaren, amma duk da haka muna son jin ƙarin bayanin abun da ya faru daga gare ka wanda shi zai sa mu ƙara tabbatar da abun da muke zargi.” Sadik ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce. “Misalin ƙarfe uku na daren ranar ina cikin yin Sallah na ji kamar motsi a bayan ɗakin da nake, wanda ga dukkan alamu ƙofar BQ ta baya ake bugawa da ƙarfi. Na cigaba da Sallah ta ba tare da tunanin komai ba a raina, amma kafin na sallame Sallar na ji an banko ƙofar falo da ƙarfi, gabana ya faɗi ba shiri na sallame Sallar na tashi na je na lek’a window, bana ganin Parlour’n sosai saboda babu wadataccen haske, amma ina iya hango alamun mutane a Parlour’n, kuma ɗakin da nake ciki suke tunkarowa. Na tsaya ina cigaba da kallon ikon Allah, cikin mintuna ƙalilan na ji ana dukan ƙofar ɗakin da nake, na koma bakin ƙofar da sauri na ƙara locked ɗinta, sannan na koma ƙarshen ɗakin ina ambaton sunan Allah tare da neman ɗaukin sa. Kawai sai gani na yi an banko ƙofar ɗakin ta faɗi ƙasa an ɓalle ta ɓal. Na firgita sosai tsorona ya ƙaru, ban gama zullumun ba na ga ana haske ɗakin da wata fitila mai hasken tsiya, sannan aka dallare mun fuskata da ita, hakan yasa ban tantance adadin mutanen da suka shigo ba, balle naga kammanin su, na fara kare idona saboda hasken fitilar dake ƙoƙarin yi masa illa, ba tare da sun ce mun k’ala ba na ji sun watsa mun wani abu a fuska kamar powder, lokaci ɗaya na ji numfashi na yana ƙoƙarin ɗaukewa, kaina ya fara wata irin juyawa, na ji ƙafafuna sun kasa ɗauka ta, na tafi luuu zan faɗi ƙasa, daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba. Sai farkawa na yi na gan ni a wani ƙaramin ɗaki a kwance akan wani ƙaramin gadon ƙarfe. Na shiga bin ɗakin da kallo kwanyata na tariyo mun last abun da ya faru, na yunƙura da sauri da nufin in tashi amma sai hakan ya gagara, na ji jikina kamar ba nawa ba, kamar an zare mun lakar jikina, kamar an zuk’e mun jinin jikina, na kasa d’aga ko da ɗanyatsana ne duk iya ƙoƙarin yin hakan da na yi kuwa. Idanuna ne kawai suke iya aiki a jikina suma ba kamar da ba, dan sun mun wani irin nauyi. Na shiga ƙarewa ɗakin kallo a tunanina ko zan iya tuno ɗakin da nake, ko na taɓa zuwan sa a rayuwata. Amma babu abun da na gane, na kasa tantance dare ne ko rana lokacin. Na lumshe ido ina tunanin me na yi aka kawo ni nan? Su waye suka zo har gida suka ɗauko ni saura awanni kaɗan d’aurin Aure na? Bayan ku san minti talatin ina ta yiwa kaina tambayoyin da ba ni da amsar su na ji an turo ƙofa a hankali an shigo ɗakin, na buɗe idona da sauri ina kallon mai shigowar, wani ƙaton mutum ne dogo fuskarsa a rufe da bak’ar face maks ta roba, ƙwayar idanunsa kawai ake gani wanda suka kasance jajaye ne. Na buɗe bakina da na ji ya mun nauyi da ƙyar na ce. “Who are you? What do you want to me?” Kamar da dutse na yi magana bai ce mun k’ala ba, ƙarasowa kawai ya yi ya tattab’a jikina, ni kuma ina cigaba da yi masa tambayoyin dalilin da yasa suka kawo ni gurin. Ya fita bayan ya gama tattab’a jikina, jimawa kaɗan ya dawo da abinci da ruwa a hannunsa, ya ajiye a gefen gadon sannan ya tayar da ni zaune, ya buɗe abincin ya turo mun gabana sannan ya tashi ya fita. Na bi shi da kallo har ya fice, ban ko kalli inda abincin yake ba balle na yi tunanin ci. Bayan wasu mintuna ya ƙara dawowa ɗakin, ganin ban ci abincin ba sai ya kalle ni kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya rufe abincin ya kamani na tashi ina jin jikina kamar ba nawa ba saboda rashin k’wari, wata ƙofa dake cikin dakin ya nufa da ni, yasa hannu ya tura ƙofar ta buɗe sannan muka shiga, ashe toilet ne. Ya zaunar da ni akan toilet sannan ya juya ya fita, na gane mai yake nufi in ina jin wani uzurin in yi kenan. Na tashi da ƙyar ina layi na kunna pampon sink na yi alwala, duk da ban san ƙarfe nawa ba, ban kuma san sallar da zan yi ba, amma na san a lokacin baza a rasa sallar da ake bina ba wadda ban yi ba. Bayan na idar da alwalar na fito dak’yar ina jin kamar iska zata ɗauke ni saboda rashin k’warin jiki. Na tarar da darduma a shimfid’e a tsakiyar ɗakin, bangon ɗakin kuma ta inda dardumar take fuskanta alamun nan ne gabas an saka wani ƙaton agogon bango mai 24 hours a jikinsa, na ga a lokacin ya nuna ƙarfe bakwai da mintuna na safe. Sai dai na kasa gane time ɗin na wacce rana ne, safiyar ranar juma’ar d’aurin Aure na ce ko kuma wata ranar ce daban? Na ƙarasa gaban agogon sai na ga ashe har da rubutun days mitsi_mitsi a cikin sa, a yanda ya nuna kuma safiyar ranar juma’a ce. Na sauke ajiyar zuciya sannan na tayar da Sallah, na yi Sallar asubahin dake kaina. Bayan na idar na zauna na rafka tagumi zuciyata cike da tsantsar tashin hankalin sabon al’amarin da ya same ni, wanda ban san dalilin sa ba amma na fawwalawa Allah komai, na shiga roƙon sa akan ya kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri mutum ko na aljan. Sai kuma na fara tunanin gida da mahifina da sauran ƴan’uwa, dan na san zuwa yanzu an farga da rashin gani na a gidan, an fara nema na hankali a tashe. Ina zaune inata tunanen gida da dalilin sato ni da aka yi aka kawo wannan gidan har goma na safe ta yi. Na tashi da sauri kamar wanda aka tsikara na nufi ƙofar ɗakin na fara ƙoƙarin buɗewa amma na jita a kulle gam, ni kuma jikina babu k’wari balle na yi yunƙurin buɗe ta. So nake in yi ihu ko wani zai jiyo ni ya kawo mun ɗauki amma k’warin muryar ihun ma bani da shi. Idan na tuna ranar ne fa d’aurin Aure na sai hankalina ya ƙara dugunzuma ya kai k’olokuwar tashi. Na zube a bakin ƙofar jin jiri na neman yarda ni, babu irin tunanin da ban yi ba akan kawo ni gurin da akai. Na ce ko wani abokin aikina ne yake jin haushina yasa a sato ni? Ko kuma kidnappers ne? Ko kuma wani case ɗin na yi daya ɓata wa wani rai ya k’ullace ni? shine zai saka a zato ni ranar Aure na a matsayin ɗaukar fansa. Ni kaɗai a ɗakin babu alamar wani yana inda nake, ko kukan tsuntsu ban ji ba balle na wasu dabbobin ko na mutum. Ina nan zaune aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo, na d’ago da sauri sai na ga mutumin d’azu ne, hannunsa ɗauke da take away da ruwa da lemo, ya ajiye a gabana ba tare da ya yi magana ba ya juya ya fita. Ni kuma kamar an ɗaure mun baki na kasa yi masa magana, duk da tarin tambayoyin dake raina. Na yi ball da abincin da ƙafa cikin tsananin takaici, na san zuwa lokacin ahalina da abokan arzik’i da amaryata suna can cikin tashin hankalin ɓata na.
Haka na wuni ni kaɗai a ɗakin cikin tunanin mafita, Sallah ce kawai take tayar da ni idan na ga lokacin ta ya yi. Har bayan Magriba ko ruwa ban kurb’a na saka wa cikina ba, yunwar ma da ƙishirwar ko jin su bana yi, ko ma ina ji bata su nake ba. Kafin isha’i mutumin ya ƙara dawowa ya kawo mun wani abincin da ruwan. Na tashi da sauri cikin ƙarfin hali dana zuciya na cakumi mutumin ina tambayar sa dalilin yasa suka kawo ni nan? Me nay musu? Kamar wani kara haka mutumin ya yakice ni daga jikinsa ya dank’wafar da ni a ƙasa ya juya ya fice. Na rarrafa a ƙoƙarina na ganin na riƙe ƙofar kafin ya rufe, amma tuni ya ja ta sai motsin saka mukulli a jikinta na ji. Na kwanta akan carpet ɗin dake malale a ɗakin cikin tsananin damuwa. Sai da takwas ta wuce sannan na miƙe ina layi na shiga toilet na ɗauro alwala na yi Sallar isha’i, na ƙara da nafila a cikin kowacce sujjada ta ina roƙon Allah ya fitar da ni daga cikin wannan riskin da nake ciki. Ina kan sallaya mutumin ya sake shigowa, na zuba masa ido in ga mai kuma ya shigo yi, da yake ɗakin akwai hasken wani farin k’wan wuta guda ɗaya dake sak’ale a bango. Ga mamakina sai na ga ya kama ni ya kai ni kan gado ya kwantar, na bishi da kallon mamaki, ban gama mamakin ba na ji ya juya ni gefe ya d’aga jallabiyar jikina ya tsikara mun allura. Daga nan na fara ganin bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan bacci ya yi gaba da ni. Ban farka ba sai ƙarfe shida saura na safe, na bi ɗakin da kallo, sai na ga fankar sama tana wulwulawa, na juya b’arin damana sai na ga Television ta bango manne a bangon dakin, sai wani abu mai kama da GO TV a ƙasan ta da remotes biyu a kansa. A gefen ta kuma wani ɗan table ne an ɗora Alkur’ani izifi sittin akai. Mamaki fa ya kusa kashe ni, na shiga tambayar kaina abun da mutanen nan suke nufi da ni? Ko duk a cikin salon cutarwar da za su mun ne? Ko kuma wani abu suke nema a guri na? Na yunƙura na tashi sai a lokacin na lura da bargon dake lullub’e a jikina, kaina kuma ashe akan pillow yake. Sai na rasa da yaran da zan fassara wannan al’amarin da na tsinci kaina a ciki. Haka na yunƙura na sakko daga kan gadon, jikina a matuƙar sanyaye kamar jiya na nufi toilet. In tak’aice muku zance haka na kasance a cikin ɗakin nan, kullum za’a kawo mun abinci da ruwa da lemo safe, rana, dare. Da farko bana ci, sai daga baya dana ji yunwa na neman yi mun illa sannan na fara ci ba don daɗi ba. Kuma duk dare sai mutumin nan ya mun allurar nan, wanda na fuskanci ta bacci ce, amma asuba tana yi zan farka. Hakan yasa jikina kodayaushe babu k’wari, ya yi mun wani irin lagwab. Ban taɓa wanka ba sai sau ɗaya da na ji kamar zan mutu saboda k’aik’ayin da jikina yake mun, a toilet ɗin akwai kat’on soap na wanka da toothpaste da brush sabo. Tun ina tambayar mai kawo mun abinci wanda ban taɓa ganin fuskarsa ba dalilin da yasa suka ɗauko ni suka ajiye ni a gurin, har na haqura na daina na zubawa sarautar Allah ido da ganin iya gudun ruwan su, amma har na baro gurin ba su taɓa ƙoƙarin cutar da ni ba, Alkur’ani nan shi ya zamo abokin hira ta, shine nake karantawa wuni guda cur, hakan yasa nake samun nutsuwa a cikin zuciyata. Kwana na huɗu aka kawo mun jallabiya guda biyu da ƙaramin wando, da har na ƙi sakawa sai kuma na ɗauka na saka, da na yi tunanin ina Sallah kar kayan jikina su yi dattin da baza su yi Sallah ba, Tunda ban san ranar fita ta daga gurin ba. Jiya da ya kasance kwana na shida a wannan ɗakin na lek’a waje ta window, sai na fuskanci kamar gida ne inda nake ciki, saboda dana lek’a like bayan gida na gani. Yau na tashi kamar kullum na yi Sallah na ɗan taɓa abincin da aka kawo mun kaɗan, sannan na ɗauki Alkur’ani na fara karatu. Wajen sha biyu lokacin na ajiye Kur’anin inata ta tunane_tunane na, mutumin nan ya shigo ɗakin. Ya ɗauke Alkur’anin gaba na ya ajiye akan table ɗin nan, sannan ya fito da wani baƙin k’yalle ya ɗaure mun idanuna tamau, ina tirje_tirje da yi masa ihun ya rabu da ni amma bai kula ni ba. Na ji an ƙara buɗe ƙofar ɗakin an shigo, daga nan kuma sai ji na yi sun kama ni mun fice daga ɗakin. Inata tambayar su ina zasu kai ni, amma babu wanda ya ce mun kanzil. Har suka saka ni a cikin mota suka ɗaure mun hannuna ta baya muka fara tafiyar da ban san inda za’a kai ni ba. Addu’ar neman tsari kawai nake karantawa a raina. Mun yi tafiya sosai sannan na ji mun tsaya, suka fito dani muka shiga wari guri, sai da muka shiga suka kunce mun daurin fuskata dana hannuna, suka buɗe wata ƙofa suka kaini bakinta, ina shiga na ga toilet ne. Mamakin waɗan nan mutanen nake da basa wasa da Sallah, dan na gane tsayawa suka yi da tafiyar dan na yi Sallah. Na ɗauro alwala na fito na tayar da Sallah akan carpet ɗin dake tsakiyar gurin mai kama da ɗaki, amma babu komai a cikin sa, ko labule babu. Na tayar da Sallar kenan ɗaya daga cikinsu ya taso ya juyar da ni, da alama ban fuskanci alk’ibla dai-dai ba, tunda dama shata kawai na yi. Ina idarwa suka mayar mun da k’yallen fuskata suka kuma ɗauren hannuna, suka kama ni muka fice daga gurin. Muka koma motor aka cigaba da tafiya, wadda har sai ana la’asar muka shigo cikin gari, nan ma sai da suka tsaya suka shigar da ni wani gida da babu kowa a cikinsa na yi Sallah, sannan muka fito, tafiya kaɗan muka yi suka sauke ni tare da kunce mun d’aurin fuskata dana hannuna cikin sauri sannan suka juya suka shiga cikin Mota suka manne ta da mugun gudu. Na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi lokacin dana fuskanci a bayan gidan nan nake. Jikina har rawa yake dan murna da zumud’i na miƙe na nufo gida, ina son na yi gudu dan ƙarasowa da wuri amma rashin k’warin jikina ya hana ni, dole sai a hankali na tako na zo, ina tafe ina tunanin mutanen nan da tambayar kaina menene fa’idar ɗauke ni da sukay? Kuma gashi sun dawo da ni gida ba tare da cutarwar ko ƙwarza ne a jikina ba? Wannan shine abun da ya faru da ni.”
Gaba-ɗaya mutanen Parlour’n suka yi shiru kowa yana jimanta al’amarin a cikin ransa cikin tsananin mamaki. Abban Sadik ne ya fara magana a cikinsu cikin matuƙar mamaki ya ce. “To fa, ka ji kuma wani ikon Allah, amma wannan abun da ɗaure kai yake, to su waye waɗan nan mutanen, mene kuma fa’idar su na yin hakan?” Kawu ya ce. “Shine abun tambayar.” Hajiya ta ce. “Yo wanne abun tambaya kuma ga abu nan a zahiri? An sace Sadik ba dan komai ba ne sai dan kawai akan wannan yarinyar, saboda kar auransu ya yiyu, Allah ya rufa mana asiri shi ba’a kashe shi ba kamar na bayan da aka kashe.” Cikin sauri Sadik ya kalle ta amma bai ce komai ba. Hajja (Mahaifiyar Maamah) ta ce. “Gaskiya ne zargin mu ya zama gaskiya, saboda yarinyar ne.” Kawu ya ce. “Lallai Sadik ka auna arzik’i, Allah ya yi da sauran kwanan ka a gaba kana da rabon shan ruwa, Eh, Alhamdulillah mun godewa Allah, fatan mu Allah ya baka wata matar ta gari, wannan yarinya kam ba matar Aure ba ce.” Abba ya ce. “Nima na tsorata gaskiya, gwara da ba mu yarda an ɗaura Auren ba, wataƙila da waɗan da suka sace shin sun ji labarin an ɗaura Auren da tuni sun kashe shi.” Hajiya ta ce. “Zancen yaushe kuma? Ai Allah ne yay mana gyaɗar doguwa, gobe in Allah ya kai mu sai a karb’o kaya da kuɗin da aka kai gidansu yarinyar, maganar aure kuma ta ruguje, tunda yarinya ta zama annoba.” Abba ya dubi Sadik dake cikin tashin hankali ya ce. “Ka yi haquri Abubukar, tun kafin ka dawo mun gama yanke hukunci baza ka auri yarinyar nan ba, dan alamu sun nuna kota yi auren ma za’a iya bi har gida a kashe mijin.” A ruɗe Sadik kamar zai yi kuka ya ce. “Abba ni na san ba domin Neehal aka sace ni ba, abun da kuke tunani ba haka ba ne Abba, ka manta aikina, ka manta wani zai iya yin komai dan yana jin haushi na, may be mun samu wata matsalar akan wani case daban, ko kuma…..” A zafafe Hajiya ta katse shi da faɗin. “Lallai Sadik na yarda baka da hankali, ka ci akai ka dawanau a duba ƙwaƙwalwarka, yarinyar da kafin kai samarinta biyu an kashe su, kai kuma aka sace ka ana i gobe d’aurin Auren ku shine kake ƙoƙarin kare ta? Saboda Kai ne Majnoon sarkin soyayya, ko kuma in ce sarkin hauka? To yarinyar nan in ma mayya ce ta lashe maka kurwa sai ta sake ka wallahi, kai da ita kuma haihata_haihata kun rabu, rabuwa ta har abada, in ma zaka cire ta daga ranka ka cire ta, na san wannan farar fatar ta_ta da dogon hanci da manyan idanu su suke rud’ar ka a kanta, to indai wannan ne zaka samu wadda ta fita sau dubu a duniyar nan.” Sadik ya dafe kansa dake sara masa kamar zai tsage lokaci ɗaya. Abba ya ce. “Abubakar ka yi tunani da hankalinka mana, idan dan jin haushin ka ko dan ɗaukar fansa aka sace ka baza a barka lami lafiya ba sai an cutar da kai, amma wannan fa dubi yadda aka kula da kai, harda saka maka kayan kallo dan su ɗebe maka kewa. Amma na jinjinawa koma waye ya sace ka, yanda bai bari ka yi wasa da Sallah ba, kuma yake baka abinci akai_akai, tabbas ya san darajar ɗan Adam. Sai dai ba mu san mene a cikin zuciyarsa ba daya aikata hakan.” Ɗaya daga cikin k’annen Abba ya ce. “Abun da mamaki ba kaɗan ba, ita kuwa wannan yarinya wa yake yiwa rayuwarta haka, ni tausayi take ba ni dan na san su ma ba su da masaniya akan mai aikata mata wannan al’amari.” Hajja ta ce. “Abun da tausayi gaskiya.” Umma ta ce. “Wataƙila aljanu gare ta.” Kawu ya ce. “Koma mene ne Allah ya yaye mata, mu dai an yi walk’iya mun gani, ɗanmu ba zai aure ta ba, fak’at.” Sadik zai yi magana Kawu ya katse shi cikin faɗa ya ce. “Karka ce komai, indai mun isa da kai daga yau ba kai ba wannan yarinyar.” Sadik ya kalli Maamah da bata ce k’ala ba tunda ta zauna yana marairaice fuska, a ƙoƙarin na son ta roƙar masa su Kawu akan kar su raba shi da Neehal, amma sai ya ga ta sunkuyar da kanta ƙasa alamun tana bayan su Kawu, ta goyi bayan a raba shi da Neehal kenan ita ma? Ya ɗauke kansa daga kanta cikin ƙarfin halin radad’in da yake ji a zuciyarsa ya ce. “Shikenan Kawu, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi.” Yana gama faɗar haka ya miƙe cikin sanyin jiki kamar zai faɗi ya fice daga falon. Suka bi shi da kallo dukan su. Maamah ta ji tausayin ɗan nata ya cika mata zuciya, sai ta ga kamar su Kawu ba su kyauta masa ba, daga dawowar shi su tarye shi da zancen rabuwa da abar son sa, wanda kowa ya san zai ji ciwon hakan ba kaɗan ba. A ganin ta aida sun bari an kwana biyu ya ƙara hutawa ya dawo cikin nutsuwarsa. Baza ta iya barin ɗanta a cikin halin damuwa ba tare da rarrashe shi ta faɗa masa abun da zai ji sanyi a ransa ba, hakan yasa ta miƙe ba tare data kalli kowa ba ta bi bayan shi. Umma ta tab’e baki. Hajiya ta shiga mita da masifar Neehal ba haka ta bar mata jikan ta ba, asirce shi ta yi, ban da haka mutum yana ganin mutuwa muraran amma yana ƙara kai kansa gare ta.
Yana kwance akan gadon ɗakinsa ruf da ciki Maamah ta shiga ta same shi, idanunsa a lumshe sai faman sassauke numfashi yake. Maamah ta zauna a bakin gadon tare da ɗora hannunta a kansa cikin sanyin murya ta ce. “Ka yi haquri Sadik, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, ka miƙawa Allah komai zaka ga ya warware maka damuwar ka cikin sauƙi, ta hanyar da baka taɓa tsammani ba. Ka saka a ranka idan Neehal matar ka ce duk runtsi duk wuya sai ka aure ta, just pray hard my son everything will be Okay by the grace of God.” Sadik ya gyaɗawa mata kai tare da sauke ajiyar zuciya. Maamah ta ce. “Dan Allah karka damu kanka da tunani, ka kwantar da hankalinka, ka ga yau ka dawo kana murna muma muna murna, karka ɓata Mood ɗinka ka ɓata namu.” Ya gyaɗa mata kai. Maamah ta shafi sumar kansa ta ce. “Allah yay maka Albarka, ya baka ƴaƴa masu biyayya kamar yadda kake mana, ya zaɓa maka abun da yafi Alkhairi a rayuwarka.” Ya buɗe ido cikin daɗin addu’arta ya ce. “Amin Maamah ta, thank you so much.” Maamah ta yi murmushi ta miƙe ta fice. Ya bita da kallo cikin matsananciyar k’aunar ta, uwa uwa ce, mai sanya farinciki a zuciyar ƴaƴanta akodayaushe, dole duk wanda ya rasa uwa ya yi kuka. Ya lumshe ido a ransa yana faɗin, dole ya yiwa iyayensa biyayya ya rabu da Neehal, duk da ya san zai cutu, cutuwa ba kaɗan ba, bai ma san ya zai kwatanta rayuwarsa babu Neehal ba, bai sani ba ko zuciyarsa zata ɗauki rayuwa babu ita ko ba zata ɗauka ba? A fili ya furta. “I’m sorry Neehal, dole zan bar ki ba dan san raina ba.” Ya sauke ajiyar zuciya tare sakawa a ransa ya rabu da Neehal rabuwa ta har abada kamar yadda iyayensa suke zo, zai dage da addu’ar Allah ya rage masa soyayyarta a cikin zuciyarsa ko da rabi ce, dan ya san ba zai taɓa daina son ta ba har abada. Amma Neehal fa? Yaya zata ji idan ta ji ya bar ta akan ƙaddarar da ba ita ta ɗorawa kanta ba? me yasa mutane baza su yi mata uzuri ba? Me yasa za’a ƙyamace ta a hana a aure ta? Mene laifin ta a cikin ƙaddarar ta? Hawaye masu d’umi ne ya ji suna zarya akan kuncinsa, na tausayin kansa da tausayin abar k’aunarsa, masoyiyarsa, muradin ransa, wadda ya saka ran zata zamto matarsa uwar ƴaƴansa amma *ƙaddara* ta raba su, a lokacin da ba su taɓa tsammani ba, lokacin da suke gab da mallakar junan su, su zamto abu ɗaya. Ya share hawayen fuskarsa wanda ya manta rabon da ya gan su akan fuskarsa sai yau, shi musulmi ne ya yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, haɗuwar su da Neehal wani shafi ne a cikin shafin littafin ƙaddarar rayuwarsa da Ubangiji ya rubuta masa, haka ma rabuwa da ita, dan haka He accepted it, Rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa daga Ubangijin sa. Fata kawai Allah yasa mu iya cinye dukkan jarrabawoyin rayuwar mu, wanda muke fatan hakan ya kai mu ga samun dacewa a duniya da lahira baki ɗaya……..✍️
_*Not edit, sorry for the typed errors.*_
*By*
*Zeey Kumurya*
Nice to read the book
Nice to read the book
Thanks