Ni da Ya ya Al’ameen Hausa Novel Complete

Ni da Ya ya Al’ameen Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Ni da Ya ya Al’ameen Hausa Novel Complete

Page 1

 

 

 

 

Tafe suke a mota sai rusan kuka takeyi kamar wanda aka ce mata mahaifiyarta ta mutu, yanda na lura da kukan nata harda na shagwab’a ma, shi ko duk da kasancewar yana jin kukan nata har k’asan ransa bai saka ya daina tuk’in nasa ba ko kuma yayi yunk’urin rarrashinta, dan abinda ya sakata kukan shi nashi b’angaren farin ciki ya saka shi.

 

 

Jin kukan nata bana k’are bane yasa ya taka wani mahaukacin birki wanda sai da *Meenat* wanda take kuka ta hantsila sannan ta dawo ta zauna a mazauninta, take kuma kukan da take ya tsaya cak ta zaro manyan idanunta waje saboda tsananin tsoro.

 

Ganin yanda ta firgita yasa *Al’ameen* fashewa da dariya yace “ya kika bar kukan kuma, ai da kin ci gaba da kukanki tinda Abbie ne ya mutu. ”

 

 

Wani kukan ta fashe dashi tana kai masa bugu, shi ko me zaiyi in ba dariya ba, dariya yakeyi yana fad’in “dukeni *Meenat* indai zai saka kiji sanyi a ranki. ”

 

 

Sai da taji hannunta ya fara zafi sannan tabar dukanshi tare da jingina kanta a kafad’arsa tana sakin ajiyar zuciya, a hankali ta bud’e baki tace “yah *Al’ameen* wai baka tausayi na ne.?”

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Ajiyar zuciya ya sauke ya d’ago da kanta ya kalli cikin idanunta sannan yace ” *Meenat* me yasa zanji tausayinki bayan kina kuka ne akan abinda ya kamata kiyi farin ciki. ”

 

*Meenat* tace “farin ciki?!! Farin ciki fa kake cewa inyi yah *Al’ameen*, ta yaya zanyi farin ciki bayan wanda nake so ya bar ni, wanda nake so ne fa aka rabamu dashi, shine kake cewa nayi farin ciki, shine kake cewa kar nayi kuka.?”

 

Murmushi *Al’ameen* yayi yace “to gani nayi fa mahaifiyarshi ce tace bata sonshi dake, k’iri-k’iri ta nuna miki k’iyayya, to dan yanzu ya kiraki yace an saka masa ranar aure da y’ar uwarsa sai ya zama abin kuka ? Ni zatona kuka ba naki bane, saboda ko aurensa kikayi ba zakiyi farin ciki ba, ni wallahi murna ma nayi miki, gara yaje can ya auri ‘yar uwarsan, uwarsa kuwa taje ta bak’in halinta badai k’anwata ba. ”

 

 

Shagwab’e fuska *Meenat* tayi tace “to amma ai shi yana sona ni ma ina sonsa.”

 

Cike da jin haushi *Al’ameen* ya tayar da motan yana fad’in “to ai sai kije ki auresa, kuma wallahi kika k’ara cika min kunni da kukanki sai na tsayar da motar a ajiyeki sai dai ki nemi taxi ya k’araso dake gida. ”

 

 

Turo baki tayi gaba cike da shagab’a tace “yah *Al’ameen* kai baka san soyayya bane shi yasa. ”

 

 

*Al’ameen* bai san sanda ya k’ara taka wani Burkina ba ya kalleta yace “bansan soyayya ba kika ce *Meenat*,? To kallo ni nan. ”

 

Kamar yanda yace aiko ta d’ago ta zuba masa ido shima d’in kuma ita yake kallo, cikin wata irin murya yace “me kika gani cikin idanuna.?”

 

Kau da kanta gefe tayi saboda irin tasirin da idanunsa yakeyi mata ajiki a duk lokacin da ta kallesa tace “ni ban ga komai ba. ”

 

Murmushi yayi ya tayar da motar yana fad’in “k’arya kike wallahi”

 

Tab’e baki tayi tace “to ai kai idanun naka ko yaushe a haka suke, mutum ba zai iya kallonsu na mintuna biyu ba ma saboda tsaban kwarjininsu. ”

 

 

“Ashe dai ki ce gwarjinin sukayi miki kika kasa ka gano abinda suke cikinsu. ”

 

 

*Meenat* tace “ni dan Allah k’aleni naji da abinda yake damuna. ”

 

 

Murmushi *Al’ameen* yayi ba tare da ya k’ara cewa komai ba ya ci gaba da tuk’insa.

 

Kaitsaye unguwar nasara g.r.a suka nufa, daidai k’ofar wani tamfatsetsen gida naga yayi horn, me gadi ne ya lek’o ganin motar *Al’ameen* ne yasa ya koma ya bud’e masa da sauri shi kuma ya danna hancin motar nasa cikin gidan.

 

 

 

Suna shiga ko parking bai gama yi ba *Meenat* ta bud’e ta fice da gudu tayi cikin gidan ko tsaya ta d’auki kayan siyayyar da suka siyo ba tayi ba, girgiza kai *Al’ameen* yayi ya bita da kallo sannan ya k’arasa gyara parking ya d’auki ledan kayan shima ya fito ya nufi cikin gida.

 

 

Da sallama ya shiga falon gidan, *Ummi* da take zaune a falon ne ta amsa masa sallamar tana fad’in “d’ana har kun dawo. ?”

 

Zama yayi saman kujera yana fad’in “eh mun dawo *Ummi*. ”

 

 

“To sannunku da dawowa, amma me ya sami mutuniyar taka ne naga ta zo ta wuce ranta a b’ace ina mata magana amma ko ta kulani. ?”

 

Murmushi *Al’ameen* yayi yace “hmmm *Ummi* kinsan halin rigimar *Meenat* sarai dai, kawai muna kan hanyar dawowa ne *Salis* ya kirata yake fad’a mata an saka ranar aurensa da ‘yar uwarsa nan da sati biyu shine fa ta d’aga hankalinta take tayi min kuka. ”

 

Tsaki *Ummi* tayi tace “au akan hakan ne take wannan kumburin, ni ai gara hakan ma, dama ni ba sonta dashi nakeyi ba, dan ko ta auresa mahaifiyarsa ba zata barsu suyi farin ciki ba tunda bata sonta. ”

 

*Al’ameen* yace “nima haka na fad’a mata, amma ita so ya rufe mata ido.”

 

“Allah ya kyauta” cewar *Ummi*

 

Ameen *Al’ameen* yace yana mik’ewa, sannan yace ” *Ummi* ga kayan nan ki bata ni zan shiga gida, sai zuwa anjuma zan dawo na k’ara rarrashinta domin nasan yanzu ba zata saurareni ba. ”

 

Murmushi *Ummi* tayi tace “da kanta ma zata biyoka na sani, domin shak’uwarku da juna ya wuce misali, ka gaida min da Ummar taka in ka shiga gidan. ”

 

Murmushi shima yayi ya nufi hanyar fita yana fad’in “zata ji *Ummi*. ”

 

 

*************

 

 

*Al’ameen* yana fitowa gidan dake manne dana su *Meenat* na ga ya shiga, gidan bashi da banbanci dana su *Meenat* hatta da fenti kuwa, tagwayen gida kenan wanda mamallakanta suma suka kasance tagwaye.

 

 

Da sallama ya shiga k’ayatatcen falon wanda bashi da banbanci dana gidansu *Meenat*, komai na falon irin d’aya ne da wancen, in ka shiga wancen gidan ka dawo ka shiga wannan ba zaka banbaceau ba, cewa zakayi gida d’aya ka shiga.

 

*Umma* ce da take fitowa daga kitchen ta amsa masa sallamar tana fad’in “ina ka bar min d’iyar tawa ne. ?”

 

Fad’awa *Al’ameen* yayi saman kujera yana fad’in “d’iyarki ko y’ar rigima, tana can tana kukan an sakawa *Salis* ranar aure. ”

Ajiye abincin hannunta Umma tayi a saman dining sannan tace “ni bansan maitan me *Meenat* takeyi ba akan wannan yaron, inda aka ce ba’a sonka to meye na tusa kai.?”

 

Tab’e baki *Al’ameen* yayi yace “ohon mata.”

 

Cikie da jimami Umma tace “amma saboda Allah tana kuka shine ka tawo ka barta ba ka tsaya ka rarrasheta ba. ?”

 

Mik’ewa yayi tsaye yace “Umma kin sani sarai bana son damuwar *Meenat* bare har naga hawayenta, amma a wannan gab’ar ba zan iya rarrashinta ba, saboda ni banga abin da zai sa ta d’aga hankalinta ba, in ta hak’ura da kanta zata tawo nemana, bari naje nayi wanka na d’an kwanta na huta *Umma*. ”

Yana gama fad’in hakan ya nufi hanyar d’akinsa.

 

 

 

Da kallo Umma ta bishi tana fad’i afili “ni har yanzu na kasa gane wani irin so yaran nan sukeyiwa junansu, in kayi zargin soyayya tsakaninsu sai su zo su kifar da kai ka kasa gane komai kuma. ”

 

Ta dad’e a tsaye tana sak’e-sak’e kafin tace “Allah ya kyauta.”

Ta nufi kitchen tana me ci gaba da aikinta.

 

 

**********

 

 

*Al’ameen* yana shiga d’aki toilet ya fad’a ya shek’o wanka abinsa, yana fitowa gaban dressing mirror ya nufa yayi shafe-shafensa sannan ya nufi closet d’insa ya bud’a ya d’auko wani wando three quarter da wata riga singlet ya sanya, yana kammala ya koma gaban mirror ya fashe jikinsa da turaruka sannan ya d’auki computer d’insa da take saman wani d’an k’aramin tebur ya haye gado.

 

Yana bud’e computer d’in hoton *Meenat* ce ya bayyana saman screen d’in computern tana dariya, shima bai san lokacin daya saki murmushi ba ya kai hannu ya shafi fuskarta yace “I love you so much my *Meenat*” tayi kyau sosai cikin hoton, sanye take da k’ananun kaya riga da wando kanta babu d’ankwali k’ananun kitson kanta sun zubo saman kafad’unta, daga ganin hoton an d’aukesa ne cikin yanayin farin ciki.

 

Ya jima yana kallon hoton kafin ya shiga ya fara abinda zaiyi…

 

 

 

 

 

 

Muje zuwa

 

 

 

 

 

More comment more typing

 

 

 

 

 

*Heenat ce*

06/08/2019 à 10:53 – HASBUNALLAH:

 

*NI DA YAYA AL’AMEEN*

 

 

 

 

*STORY AND WRITING*

 

BY

 

*RAHEENAT M ABBAKAR*

_(Heenat)_

 

 

_WAYYO DAD’I KARKA KASHENI BARNI DA RAINA NA CI GABA DA GANIN COMMENT D’IN MASOYANA, HAK’IK’A NI RAHEENAT YAU NA GA RUWAN COMMENT TARE DA ADDU’OINKU READER’S, KUMA HAKAN BA K’ARAMIN DAD’I YAYI MIN BA WALLAHI, INA SONKU MASOYANA, KU CI GABA DA SAMBAD’O COMMENT NI KUMA NAYI ALK’AWARIN SAMB’A MUKU TYPING AKAI AKAI_

See also  Rayuwar Maraici Hausa Novel Complete

 

 

SADAUKARWA GA

 

*MAMAN LABYB* *(MAMIEN MU)*

*FAUZIYYA MUHAMMAD WAKILI*

*SHAFA’ATU BALA BABA*

*ADAMA TANIMU A BIYE*

*AISHA NICHOI*

 

 

MARUBUCIYAR

 

*1 KOMAI YAYI FARKO….*

*2 HALIN RAYUWA*

*3 RAYUWAR SAUDA*

*4 RAYUWAR HANEEFA*

*5 MAHAK’URCI….*

*6 RUK’AYYATU*

*7 RAINA FANSA NE GARETA*

Loading…. *NI DA YAYAH AL’AMEEN*

 

 

*ZAMAN AMANA WRITER’S*

*(Z.A W)*

“`(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)“`

 

 

 

Page 2

 

 

 

 

 

Yana cikin aikinsa a computer yaji a turo k’ofar d’akin an shiga da sallama, d’ago kai yayi ya zuba mata ido yana kallo, sanye take cikin wasu riga da wando yar kanti, rigar har gwiwa take yayin da wandon ya kasance fencil ne, wandon fari ne k’ar yayin da rigar kuma pink colour ne mai adon fari, wani siririn gyale ne ta rataya akanta fari, tayi kyau sosai cikin katan yayin da fuskarta tayi fayau kasancewar babu komai cikinta, ma’ana ba tayi makeup ba.

 

Takowa ta farayi a hankali gurin gadon tana turo baki gaba alamar shagwab’a, shiko *Al’ameen* har lokacin idanunsa na kanta, zama taje tayi gefensa ba tare da tace dashi komai ba.

 

Ajiyar zuciya ya sauke yace “my *Meena* fushi kikeyi da yayan naki.?”

 

D’ago manyan idonta tayi ta watsa masa su ba tare da tayi magana ba, rufe computern yayi ya juyo sosai ya fuskanceta cikin taushin murya yace ” *Meenat* shirunki na iya tarwatsa zuciyar *Al’ameen*, dan Allah kice wani abu. ”

 

Hawaye ne suka fara zuba mata, cikin wani irin rud’ewa wanda ni raheenat yayi matuk’ar bani mamaki naga *Al’ameen* ya kai hannu yana share mata hawayen yana fad’in “dan Allah kibar zubar min da wad’annan tsadaddun hawayen, kin kuwa san zubar hawayenki kamar zubar ruwan dalma ne a zuciyata, daina kuka my meenat fad’a min damuwarki. ”

 

Cikin muryar kuka tace “kar ka rink’ayi kamar baka san komai ba mana yah *Al’ameen*, me yasa ne kuka kasa fahimtar irin rad’ad’in da na keji a zuciyata ce ? Yah *Al’ameen* ina son *Salis* amma an rabamu da k’arfi da yaji, ku kuma kun kasa fahimtar halin da zuciyata take ciki, dan dama ba sona kukeyi dashi ba, ya kuke so nayi yah *Al’ameen*, me yasa aka kasa samun wanda zai taushi zuciyata cikinku ? Har dakai ma yayah wanda nake ganin in kowa ba zai fahimceni ba kai zaka fahimceni.”

 

 

Hannunta *Al’ameen* ya kamo ya rik’e yana kallon cikin idanta yace “yanzu na fahimceki *Meenat*, ina so ki sakawa zuciyarki hak’uri dan Allah, ki sani komai da kika ga ya faru da sanin Allah, in *Salis* mijinki ne wallahi komai rintsi sai kin aureshi, ko kin manta babu mai auren matar wani ne ?, to da wannan nake son ki ajiye komai gefe ki rungumi k’addara, in Allah yayi da aure tsakaninki da *Salis* kina zaman zamanki zaki ga ya dawo gareki, in kuma babu aure tsakaninki dashi sai kiga ya fito miki da wani zarkad’ed’an saurayin kamar yayanki, ko bakya son miji irina.?”

Ya k’arasa maganar da sigar zolaya.

 

Murmushi ta saki tare da kai masa bugun wasa tace “kai!!! Yayah ai kai mijin manyan mata ne ba irina y’an sakayau ba. ”

Ta k’arasa maganar da dariya.

 

Had’e fuska *Al’ameen* yayi yana hararanta, saurin gintse dariyarta tayi tana fad’in “sorry yayah.”

 

Murd’a kunninta yayi yace “nak’i sorryn.”

 

“Wayyo kunnina, yayah da zafi fa. ”

 

Murmushi yayi yace “ai nasan da zafin nayi miki, ke in kika samu miji kamata ma ai kin more, amma saboda kin rainani sai ki rink’a fad’a min duk abinda yazo bakinki. ”

 

Turo baki tayi gaba cikin shagwab’a tace “wallahi da gaske nakeyi yayah kayi min girma, kalleni fa. ”

Ta mik’e tana juya jikinta a gabansa cikin sangarta da tab’ara, dan bana ce yarinta ba, wai ita a dole ya kalleta ya gani.

 

Shi ko *Al’ameen* gaba d’aya ya shagalta gurin kallonta, zuciyarsa na k’ara narkuwa cikin soyayyarta wanda ita ta kasa gane hakan.

 

Rintse idonsa yayi yana ya mutsa gashin kansa cikin wani irin yanayi, har *Meenat* tazo ta zauna kusa dashi bai sani ba, muryarta yaji kawai tana cewa “yah *Al’ameen* lafiya.?”

 

Bud’e idonsa yayi ya kalleta yace “ina sonki my meenat. ”

 

Murmushi tayi tace “nima ina sonka yayana. ”

 

Wani irin murmushi yayi tare da lumshe idanunsa, ita kuwa *Meenat* ko ajikinta saboda ba yau ne suka saba irin wannan ba, tun tana yarinya take jin kalmar so daga bakin *Al’ameen*, kuma a kullum in ya fad’a mata ba ta d’aukarsa da wani abu face soyayyar jini d’aya.

 

 

_Niko nace kinyi kuskuren fahimta Ameenatu

 

 

 

*Meenat* ce tace “yah *Al’ameen* bani wayarka na buga game d’in nan…”

 

Murmushi yayi yana yi mata nuni da wayar nashi dake kan seat-drower da hannunsa.

 

Mik’ewa tayi ta d’auko ta dawo ta zauna ta fara buga game d’in cike da nishad’i.

 

Shiko Al’ameen kallonta yayi a ransa yace “Meenat kenan, yanzu har ta manta da damuwarta. ”

Girgiza kai yayi yana murmushi ya janyo computer d’insa ya ci gaba da aikinsa yanayi yana kallon Meenat lokaci zuwa lokaci wacce ta mayar da hankalinta kacokan kan game d’in da take bugawa.

 

 

 

Kiran sallar magriba ne yasa *Meenat* ajiye wayar ta mik’e ta kalli *Al’ameen* tace “yayah ga wayarka nan ni zanje nayi sallah. ”

 

Shima mik’ewan yayi ya nufi hanyar toilet yana fad’in “ajiyeshi inda kika d’auka nima alola zanyi na wuce masallaci. ”

 

Ajiyewa tayi kamar yanda yace sannan ta fice daga d’akin.

 

 

Tana fitowa suka ci karo da *Abba* wanda ya fito zaije masallaci, gaisheshi *Meenat* tayi tare dayi masa sannu da zuwa dan tasan bai jima da dawowa ba, amsa mata yayi cikin sakin fuska yana fad’in “maza kije kiyi sallah *Meenat* ni na tafi masallaci gashi can za’a tayar. ”

 

To tace ta nufi d’akin *Umma* shi kuma *Abba* ya fice da d’an saurinsa.

 

Kan sallaya ta taras da *Umma* ta tayar da sallah, dan haka itama sai ta nufi toilet ta d’auro alolan tazo ta saka hijjabin *Umma* ta kabbara nata sallar.

 

 

Sunanan zaune suna lazimi aka kira isha’i, nan suka mik’e suka kawo nasu, sai da sukayi shafa’i da wutiri tare da addu’oi sannan suka mik’e suka fito zuwa dining.

 

Zaune suka samu *Al’ameen* a dining d’in yana danne-dannan wayarsa, ganinsu ne yasa ya ajiye wayar yace “sannu da fitowa *Umma* ”

 

 

Jan kujera tayi ta zauna sannan tace “yauwa sannu *Al’ameen,* ina ka baro Abban naka da sauran ‘yan uwanka.?”

 

Ya bud’e baki zaiyi magana kenan sai suka jiyo sallamar Abban da Usman da Aliyu k’anninsa.

 

Amsa musu sallamar sukayi sannan suka k’araso suka zazzauna suma.

 

Meenat ce ta fara saving d’insu d’aya bayan d’aya tana turawa kowa gabanshi, sai da ta kammala sannan ta zuba nata ta zauna ta fara ci itama.

 

 

*******

 

 

Suna kammala cin abincin *Meenat* ta mik’e tace “Abba Umma ni na tafi saida safenku. ”

 

Kallonta sukayi da murmushi a fuskarsu Umma ce tace “mu kwana lafiya Meenat. ”

 

Abba ma dai cewa yayi “sai da safe yar gidan Abbinta. ”

 

 

Murmushi tayi ta kalli su Usman tace “yah Usman yah Aliyu mu kwana lafiyanku. ”

Tana gama fad’in hakan ta nufi hanyar k’ofa.

 

Had’a baki sukayi gurin cewa “Allah ya tashe mu lafiya Meenat.”

 

Al’ameen ne ya mik’e yabi bayanta yana cewa “wato ni ba za kiyi min sai da safen ba kenan.?”

 

D’an d’aga murya tayi tace “to ai nasan kai d’an rakiya nane. ”

 

Da sauri ya taka ya bita yana cewa “tsaya ki fad’a min waye d’an rakiyar naki. ”

 

Tana jinsa a bayanta ta kwasa a guje ya rufa mata baya, su kuwa su Abba da kallo suka bisu sunayi musu dariya…

 

 

 

 

 

Muje zuwa

 

 

 

 

Ga mai k’orafi ko wani gyara yayi min magana ta wanann layin

 

07033643262

 

A shirye nake da amsar gyaranku ko k’orafinku readers

 

 

 

 

 

 

*Heenat ce*

06/08/2019 à 10:53 – HASBUNALLAH:

 

*NI DA YAYA AL’AMEEN*

 

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

 

 

*STORY AND WRITING*

 

BY

 

*RAHEENAT M ABBAKAR*

_(Heenat)_

 

 

MARUBUCIYAR

 

*1 KOMAI YAYI FARKO….*

*2 HALIN RAYUWA*

*3 RAYUWAR SAUDA*

*4 RAYUWAR HANEEFA*

*5 MAHAK’URCI….*

*6 RUK’AYYATU*

*7 RAINA FANSA NE GARETA*

Loading…. *NI DA YAYAH AL’AMEEN*

 

 

SADAUKARWA GA

 

*MAMAN LABYB (MAMIEN MU)*

*FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI*

*SHAFA’ATU BALA BABA*

*ADAMA TANIMU A BIYE*

*AISHA NICHOI*

 

 

*ZAMAN AMANA WRITER’S*

*(Z.A W)*

“`(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)“`

 

 

 

Page 3

 

 

 

 

 

 

Da gudun tare da sallama a bakinsu suka shiga falon su Meenat, Abby da Ummi da sauran y’an uwan Meenat da suke zaune suna hira ne suka bisu da kallo, domin hakan ba bak’on abu bane a gurin su, Abba ne ya fara magana yace “Al’ameen sai yaushe zaka girma kabar wasan yara da k’anwar naka ne wai.?”

 

 

Murmushi Ummi tayi tace “hmmm ai banga wannan ranar ba kuwa, dan kullum k’ara girma yakeyi amma yana biyewa Meenat suna shirme. ”

 

Murmushi *Al’ameen* yayi yana sosa kansa cikin jin nauyi ya nemi guri ya zauna yace “Ummi ita ce fa ta kirani da d’an rakiya. ”

 

Girgiza kai Ummi tayi tace “shine kai kuma ka biyota a guje ko. ?”

 

Dariya yayi yace “a’a Ummi ita ce dai ta fara gudu.”

 

Abba ya amshe da cewa “kai kuma sai ka biye mata ko.?”

 

 

Dariya k’annin Meenat suka kwashe dashi, shi kuma Al’ameen ya had’e gira irin ba wasa d’in nan yace “ina wasa daku ne.?”

See also  Mu gani a kasa Hausa Novel Complete

 

Aiko nan take suka gintse dariyarsu suna zare idanu, domin sun san yah Al’ameen babu wasa yanzu zai masge yaro, dan shi iya wasansa da shiriritarsa akan Meenat ce kad’ai, sauran k’anninsa kuwa tsoronsa su keji sosai.

 

 

Abba da Ummi ne suka mik’e suka shige ciki, nan suma su Isma’il suka mik’e suka nufi d’akunansu aka bar Meenat da Al’ameen zaune su kad’ai, kusa dashi Meenat ta koma ta zauna suka ci gaba da hirarsu har zuwa k’arfe 10:00pm, Al’ameen ne ya mik’e yana hamma yace “ni zan shiga gida na kwanta. ”

 

Itama Meenat mik’ewar tayi tace “ok, muje na rakaka dan nima baccin nake ji. ”

 

Baice komai ba sai nufar k’ofa da yayi ta mara masa baya, daidai get taja ta tsaya tace “to sai da safenmu yayah. ”

 

Kallonta yayi yace “mu kwana lafiya k’anwata, gobe ki shirya da wuri karki saka nayi latti gurin aiki. ”

 

Meenat tace “to yayah. ”

 

Hannunta ya kamo ya sumbata yace “kiyi mafarkina bye. ”

 

Murmushi tayi ta juya ta fara tafiya, har ta d’anyi nisa taji Al’ameen yace “Meenat!!”

 

Juyowa tayi tana kallonsa ba tare da tayi magana ba, shima kallontan yakeyi yace “dama cewa zanyi karki manta da addu’a. ”

 

Wani murmushi ta sakin masa tace “insha Allah ba zan manta ba yayah. ”

Tana gama fad’in hakan ta juya ta ci gaba da tafiya, sai da Al’ameen ya ga shigarta cikin gidan sannan ya fice daga gidan ya nufi nasu gidan.

 

 

 

*************

 

 

Washe gari misalin k’arfe bakwai da mintuna arba’in na safe Al’ameen ne ya fito cikin shirinshi na tafiya aiki, sallama yayi wa Umma wacce ke zaune a falo tana kallon sunna tv tayi masa addu’ar tsarewa dana dawowa lafiya sannan ya fice daga gidan.

 

Yana fitowa gidansu Meenat ya shige, da sallama ya shiga falon, Meenat ce ta amsa masa wacce take zaune saman dining tana break, k’arasawa yayi dining d’in yana fad’in “ke sai yanzu ne kike naki break d’in. ?”

 

Mik’ewa tayi tare da d’aukar jakarta dake saman dining d’in tace “ai nama gama muje kawai. ”

 

“Ok, ina Ummi take.?”

 

 

“Ummi ba ta dad’e da hawa uptsar ba.”

 

 

Be k’ara magana ba sai hanyar fita da ya nufa tabi bayansa.

 

 

Gurin motarsa da ya ajiye jiya ya nufa ya bud’e ya shiga, itama Meenat bud’ewa tayi ta shiga ta zauna, sai da ya tayar da motar nasa yayi ribas ya nufi get sannan Meeenat tace “good morning yah Al’ameen.”

 

Kallonta yayi yace “morning how are you. ?”

 

“Am verry fine yayana. ”

 

 

Murmushi yayi daidai lokacin da mai gadi ya bud’e mana get yace “k’arfe nawa zaku shiga lecture.?”

 

Meenat tace “k’arfe 9:00 ne. ”

 

 

Agogon hannunsa ya kalla yace “da sauran time ashe. ”

 

 

 

Babu wanda ya k’ara magana cikinsu har motarsu ta daidaita saman kwalta.

 

 

 

 

*************

 

 

Suna tafe Meenat nayi masa hira har suka isa B.U.K, parking Al’ameen yayi gurin ajiye motocin makarantar yana kallon agogon hannunsa, “k’arfe takwas da talatin da biyar. ” Al’ameen ya fad’a a fili, sannan ya kalleta yace “to ni zan wuce asibiti k’arfe nawa zaku tashi na zo na d’aukeki.?”

 

Fari tayi da idanunta sannan tace “sai k’arfe biyu zan bar makaranta, yanzu zamu shiga 9 to 11, sannan 12 to 2. ”

 

“Ok, zuwa k’arfen biyun zan zo. ”

 

D’aukar jakarta tayi ta fice tana fad’in “sai ka zo, Allah ya kiyaye hanya. ”

 

 

Ameen yace yana tayar da motarsa ya nufi inda suka fito, wato ya koma zoo road Inda asibitinsa yake.

 

 

**********

 

 

Duk da tarin aikin da yake dashi a asibitin amma yana ganin k’arfe biyu tayi ya ajiye komai ya rufo office d’in nasa ya shiga motarsa ya fice daga asibitin, kai tsaye b.u.k ya nufa, da zuwansa ya iske Meenat ita da wata k’awarta mai suna Suhailat tsaye bakin get tana jiransa, tana ganinsa tayiwa Suhailat sallama ta shiga suka kama hanya.

 

 

Suna tafe Meenat ta kalli Al’ameen tace “yah Al’ameen banyi tsammanin zaka dawo ba fa, dan nasan kana da aiki sosai a asibiti. ”

 

Murmushi yayi yana ci gaba da tuk’insa yace “ai duk aikin da nake dashi ba zai hanani zuwa na kaiki gida ba, kinsan fa bana son direba yana kaiki ko da unguwa ne. ”

 

Murmushi tayi cike da jin dad’in kulawar da yake bata tace “shi yasa kake da babban matsayi a zuciyata yah Al’ameen. ”

 

Kallonta yayi ta gefen ido sannan yace “har yau Meenat baki bani matsayin da nake son kaiwa ba a zuciyarki. ”

 

Da mamaki ta kallesa tace “wani irin matsayi kake son na baka bayan wanda na baka yayah.?”

 

 

Waigowa yayi ya kalleta sosai sannan yace “bar maganar kawai zan gaya miki nan gaba kad’an. ”

 

 

Turo baki tayi gaba cikin shagwab’a tace “nidai yanzu nake son ka fad’a min. ”

 

 

Wani siririn dariya yayi yace “Meenat rigima. ”

 

 

*Wai shin su waye ma wannan family d’in ne ??*

 

 

 

 

 

 

Muje zuwa

 

 

 

 

 

_Kuyi hak’uri da wannan yau na yini bb chaji ne_

 

 

 

 

 

 

*Heenat ce*

06/08/2019 à 10:53 – HASBUNALLAH:

 

*NI DA YAYA AL’AMEEN*

 

 

 

 

*STORY AND WRITING*

 

BY

 

*RAHEENAT M ABBAKAR*

_(Heenat)_

 

 

Wattpad

@rahinamustapha

 

 

 

*GASKIYA INA JIN DAD’IN COMMENT D’INKU READER’S*

 

 

 

MARUBUCIYAR

 

*1 KOMAI YAYI FARKO….*

*2 HALIN RAYUWA*

*3 RAYUWAR SAUDA*

*4 RAYUWAR HANEEFA*

*5 MAHAK’URCI….*

*6 RUK’AYYATU*

*7 RAINA FANSA NE GARETA*

Loading…. *NI DA YAYAH AL’AMEEN*

 

 

 

SADAUKARWA GA

 

*MAMAN LABYB (MAMIEN MU)*

*FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI*

*SHAFA’ATU BALA BABA*

*ADAMA TANIMU A BIYE*

*AISHA NICHOI*

 

 

*ZAMAN AMANA WRITER’S*

*(Z.A W)*

“`(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)“`

 

 

 

Page 4

 

 

 

 

 

Alhaji Hassan da Alhaji Husaini ‘yay’a ne ga Alhaji Sabi’u da hajiya Suwaiba, Alhaji Sabi’u haifaffan garin maiduri ne iyaye da kakanni kuma shuwa arab ne su, su uku iyayensu suka haifa Sabi’u, Hajara, Halimatu, Sabi’u da Hajara da Halimatu sun taso da matuk’ar k’aunar junansu, lokacin da aka aurar da Halimatu da Hajara lokacin ne Allah yayiwa iyayan nasu rasuwa, Sabi’u ya taso yaro mai k’wazo da neman na kansa, tunda iyayansa suka rasu ya k’ara dagewa gurin karatu da neman na kansa domin inganta rayuwarsa da kuma taimakawa k’anninsa duk da cewa suna gidajen mazajensu, da taimakon ‘yan uwan mahaifinsu ya samu ya kammala digiri d’insa har ya samu aiki a wani kampanin sarrafa abinci dana sha dake garin kano matsayin manager, wannan ne dalilinsa na dawowa kano da zama gaba d’aya, sai dai yana yawan zuwa maiduguri gaida dangi, ana cikin hakane ya had’u da Suwaiba, Suwaiba y’ar nan maiduguri ce itama, wani zuwa da yayi gaida y’an uwa ne Allah ya had’ashi da ita, Suwaiba yarinya ce kyakkyawa kuma mai tarbiyya, kanuriya ce ita, ba a d’auki wani dogon lokaci ba manya suka shiga al’amarin aka d’aura musu aure, bayan auren kano ya kawota ya ajiye, haka suke zamansu zama na lafiya tare da soyayya, saida suka d’auki shekaru bakwai da aure sannan Allah yabawa Suwaiba ciki, zo kaga murna gurinsu, y’an uwa ma sun tayasu murna sosai.

 

Nan suka fara rainon cikin nasu cikin kulawa, watan haihu na tsayawa Suwaiba ta haifo ‘ya biyu duka maza, murnar gurin Sabi’u da ‘yan uwansa kamar anyi musu bishara da gidan aljanna, ranar suna na zagayowa aka sanyawa yara Hassan da Husaini, Hassan da Husaini sun taso cikin tsananin soyayyar iyayansu tare da kulawa, iyayansu suna matuk’ar k’aunarsu, duk soyayyar duniya sun d’auka sun d’aura akansu, wani ikon Allah kuma tun da ga kansu Allah bai kuma bawa Suwaiba wani haihuwa ba.

 

 

Hassan da Husaini sun taso komai tare sukeyinsa, makaranta tare suke tafiya tare suke dawowa, sutura iri d’aya suke sakawa, ko unguwa d’aya zaije tare zasu tafi, sai kayi mugun saninsu zaka iya banbancesu saboda tsananin kamamninsu da juna, lokacin da suka shiga jami’a kuwa mata kamar zasu d’aukesu su kaisu gidajensu saboda so, su kuwa wannan damar suka samu suke gwara kan y’an mata yanda ransu keso, na farko Allah yayi musu arzik’i daidai gwarwado mahaifinsu na dashi, na biyu ga kyawu da Allah ta’ala ya hore musu wanda yake k’ara dulmiya y’an mata cikin kogin soyayyarsu.

 

 

Bayan sun kammala jami’a suka fara aiki akan abinda suka karanta wato business, da farko dai shiga da fitarwa sukeyi daga gida najeria zuwa wasu k’asashen haka ma daga wasu k’ashashen zuwa gida najeria, kuma cikin hakan ne suka had’u da masoyan zuciyoyinsu.

 

Asma’u da Fateema k’awayen juna ne na k’ut da k’ut, a unguwa d’aya suke zaune, zan iya cewa ma tare suka taso kasancewar gidansu na kusa dana juna, iyayensu kuma aminan juna ne, suna da kyansu daidai misali, cikkaku kanawa ne su, kuma babu laifi iyayansu na da kud’i daidai gwargwado, sun had’u dasu Hassan ne a super market sunje siyayya, sun zo fito kenan suka ci karo da Hassan da Asma’u, nan take kayan hannunta ta watse, kasancewar ita ce ta bangajeshi yasa ta bashi hak’uri tana mai duk’awa ta fara tattara kayan, shima duk’awa yayi ya tayata kwashe kayan yana binta da kallo domin yarinyar ta tafi dashi sosai, d’agowa sukayi a tare bayan sun gama kwashe kayan sai suka ga Husaini da Fateema tsaye a kansu, kallon kallo sukayi tsakaninsu sai kuma suka saki murmushi, a wannan rana su Husaini suka bayyana soyayyarsu gasu Asma’u, nan take su kuma suka amsa masu.

See also  Labarina Season 3

 

 

Tun daga wannan rana soyayya me k’arfi ta k’ullu tsakaninsu, ba’a d’auki wani dogon lokaci ba aka sanya ranar aurensu, nan aka fara shirye shiryen biki gadan-gadan, lokaci nayi aka d’aura auren Asma’u da Hassan, da Fateema da Husaini, bikine na y’an gata akayisa a wannan lokacin, sun ajiye matan nasu ne a gida d’aya, wato gidan da Dadynsu ya gina musu a hotoro.

 

Zamana na lafiya da tsantsan soyayya suke gudanarwa a tsakaninsu, yayin da b’angare d’aya arzik’i ke ta k’ara hab’b’aka musu, muje muje har yakai ga sun bud’e wani katafaren companyn da yake sarrafa zannuwa da jakunkuna.

 

 

Shekararsu biyu da aure Asma’u ta haifi Al’ameen, Al’ameen kyakkyawa ne sosai domin babanshi ne sak, kana kallonshi kaga jinin shuwa, ita kuwa Fateema har lokacin bata da ciki, tafi-tafi shekaru nata ja har Asma’u ta k’ara haihuwa biyu Fateema har lokacin bata da ciki, kuma hakan bai sa ta damu ba, tunda mijinta ma bai tab’a nuna mata damuwarsa ba, bayan Al’ameen Umma ta haifi Aisha da Bilkisu, Al’ameen tunda ya fara wayau yana gurin Ummi wato Fateema, yayi matuk’ar shak’uwa ta ita fiye da Ummanshi, itama sosai take son yaron a ranta, hakan ne yasa Umma take ce mashi d’an Ummi.

 

 

Umma na da cikin Aliyu wata hud’u Ummi ta fara laulayin ciki, murna gurinsu ba’a magana, kuma a wannan lokacin ne suka tare a tamfatsa-tamfatsan gidajensu da suka gina nasarawa g.r.a, gini ne na gani a fad’a, gidajen jere suke da juna komai iri d’aya, kowa yaga gidajen nan sai sun burgeshi.

 

Laulayi sosai Fateema takeyi kamar ba zata sha ba, cikin ikon Allah cikin na shiga wata biyar tabar laulayi, lokacin kuwa Umma ta haihu yaronta namiji mai suna Aliyu, haka dai Fateema ta ci gaba da rainon cikinta har watan haihuwa ya kama ranar wata juma’a ta tashi da nuk’uda, haka aka d’auketa akayi asibiti da ita, basu jima da zuwa asibitin ba ta haifi y’arta kyakkyawa mai kama da ubanta, kowa yaga yarinyar babu abinda yake fad’i sai masha Allah, tunda Al’ameen yayi arba da babyn nan yake manne da ita, ya hana kowa d’aukarta.

 

 

Bayan Ummi ta huta aka sallamosu suka dawo gida, tunda suka dawo gida ‘yan uwa da abokanan arzik’i suke zuwa barka, kowa yazo sai ya fad’i kyawun yarinyar.

 

 

Sati na zagayowa yarinya taci suna Ameenatu, Al’ameen shine wanda ya fara kiranta da Meenat nan kowa ya kama, sosai Al’ameen yake son Meenat tun tana jaririyarta, sam baya son kukanta, ko wanka ake mata yaji tana kuka zai fara rok’on Ummi ta k’yaleta, in kuwa kukan rigima takeyi tare sukeyi, dan in ya rarrasheta tak’i shiru shima sai ya fashe da kuka, komai ya samo na Meenat ce, ko makaranta yaje duk abinda yaci sai ya rago mata, itama Meenat ko da ta fara wayo komai yayah Al’ameen, shak’uwarsu har mamaki yake bama iyayansu, babu mai son damuwar d’an uwansa, kuma basa tab’a fushi da juna, kome ya had’asu to basa wuce mintuna sha biyar suna fushi da junansu, duk inda Al’ameen zaije yana manne da Meenat d’in shi, lokacin da Meenat ta fara zuwa makaranta shi yana jss 1 ne, amma haka zai jira a shiryata su tafi tare, sai ya ga shigarta har ajinsu sannan zai dawo ya shiga mota a wuce dashi nasu makarantar, shak’uwace tare da soyayya bana wasa ba a tsakaninsu, suna girma kuma shak’uwarsu na k’ara k’arfi, duk kuma inda suka shiga anga yayah da k’anwarsa saboda kamarsu da juna, Al’ameen bai san ya kamu dumu dumu cikin soyayyar k’anwar nashi ba sai lokacin da yake shekararshi ta k’arshe a jami’a, a lokacin shekarunsa ashirin ne da shida ita kuma Meenat tana shekara sha shida aji biyar a secondary, a lokacin sam bata son yaga wani namiji ya rab’eta ko kad’an, bayan kammala karatunsa na likita Abba ya sama mishi addimition a k’asar India dan yaje ya k’aro karatu akan abinda ya karanta, amma fafur Al’ameen yace ba zaije ba, dan ba zai iya tafiya yabar Meenat ba, dole Abba ya hak’ura ya k’yalesa ya d’aura karatun nasa anan gida najeria yayin da b’angare d’aya kuma ya fara aiki a asibtin malam Aminu kano (A.K.T.H).

 

 

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Al’ameen na b’oyewa Meenat soyayar da yake mata duk da cewa wasu lokutan yana kwatanta kansa a matsayin mijin aurenta cikin wasa, ita kuma tana cewa yayi mata girma, dan gaskiya Al’ameen dogo ne me d’an jiki, ga faffad’ar k’irji, namiji ne me k’iran k’arfi a tsaye yake kana kallonsa ka ga jarumin namiji, ita kuwa Meenat siririya ce amma ba can ba, doguwa ce itama d’in sai dai Allah ya hore mata k’ira da duk mace zatayi fatan samunsa.

 

 

Cikin hakan ne Meenat ta kammala karatunta na secondary, kuma a lokacin ne Abbie wato baban Meenat ya mallakawa Al’ameen katafaren asibiti da ya gina masa mai suna twins Hospital, asibiti ne da ya bashi kyauta halak malak, shigar Meenat university babu dad’ewa Allah ya had’ata da Salis, lokacin da ta zo wa Al’ameen da maganar Salis hankalinsa ya tashi sosai matuk’a da gaske, amma tsaban mazantaka ya dake ya nuna mata farin cikinsa, tare da k’arfin gwiwarsa ta fara soyayya da Salis, sun d’auki watanni hud’u tare Salis ya buk’aci turo magabatansa, nan Meenat tazo ta gayawa Al’ameen, lokacin ma hankalinshi k’ara tashi yayi yana ganin zai rasa Meenat d’inshi, kuma ya kasa fad’a mata sirrin zuciyarsa saboda ta riga ta kashe masa jiki da kalamanta na cewa shi mijin manyan mata ne😄, haka dai Al’ameen yayiwa su Abba maganar Salis, nan su ka bashi damar turowa.

 

Sati d’aya da ba Salis dama amma shiru bai turo ba, hakan yasa Meenat tambayarsa dalili, nan ya fara yi mata y’an kame kame, daga k’arshe dai ya fad’a mata mahaifiyarsa ce tace ba zai auri bare ba sai y’ar uwarsa, hankalin Meenat ya tashi domin kuwa tana son Salis, nan tazo ta fad’awa Al’ameen abinda ke faruwa, shi kuma hakan ba k’aramin dad’i yayi masa a ransa ba, nan ya nuna mata ta hak’ura da Salis kawai tunda Mahaifiyarsa bata son bare, amma Meenat ta dage ita fa tana son Salis, shima b’angaren Salis ya nata fama da mahaifiyarsa amma tak’i yarda masa sam, ana hakane ya d’auki Meenat ya kaita ta gaisheta, habawa ranar sunyi dana sanin zuwa, domin kuwa a fili ta nuna k’iyayyar Meenat sannan ta rok’eta da tabar mata d’anta ta riga tayi masa mata, da taga Salis ya duk’a gabanta yana rok’o da magiya tabarsa ya auri Meenat sai ko ta mik’e ta fara jan Meenat har sai da ta fito da ita bakin get tace tabar musu gida basa buk’atarta matsayin suruka, abin nan yayiwa Meenat ciwo sosai, ko sauraran Salis ba ta tsaya yi ba wanda yake rok’on ta tsaya ya d’auko mota ya kaita gida ta tari taxi ta nufi gida.

 

Da zuwanta d’akin Al’ameen ta nufa tana kuka, cikin rud’ewa ya mik’e ya rik’ota yana tambayarta abinda ke faruwa, nan ta fad’a masa komai, haushin mahaifiyar Salis tare da ita Meenat d’in ne ya kamasa, cikin fushi yace “to ke me ta kaiki gidansu, Meenat wai me yasa bakya jin magna ne, ki rabu da wannan yaron yaje yabi zab’in mahaifiyarsa tace bata sonki to dole ne sai kin tusa kanki inda ba’a sonki. ?”

 

Aiko sai Meenat ta k’ara fashe masa da kuka, wannan rana Al’ameen rufe ido yayi yayi tayi mata fad’a cikin b’acin rai, daga baya kuma ya dawo yana rarrashinta, to tun daga wannan rana Meenat ta fara ja baya da Salis, amma dai soyayyarsa yana nan a ranta, suma su Umma da suka ji batun fad’a sukayi mata sosai akan ta rabu dashi, ana cikin wannan halin ne kuma sun dawo daga shopping ita da Al’ameen Salis ya kirata a waya yake fad’a mata an sanya masa ranar aure da y’ar uwarsa, shine fa ranar ta dinga kuka Al’ameen yayi burus da ita domin kuwa yaji duk abinda Salis ya gaya mata da yake a hand-free ta saka wayar.

 

To ga dai yi nan yanzu kamar Meenat taji maganar Al’ameen, domin bata kara maganar Salis ba, kuma tsakanin jiya da yau ya kira wayarta yafi a k’irga tak’i ta d’aga masa.

 

 

Yanzu haka Al’ameen yana da shekara talatin a duniya ita kuma Meenat tana da shekara ashirin yanzu haka tana shekara ta uku a jami’a tana karantar likitanci domin tace yayanta zata gada.

 

 

 

*Back to story*

 

 

 

 

Daidai k’ofar get d’in gidansu Al’ameen ya faka motarsa har lokacin Meenat na zuba mashi shagwab’a wai sai ya fad’a mata wani irin matsayi yake so ta bashi, shi kuma yak’i fad’a mata yace da akwai lokacin da zai fad’a mata.

 

 

Kallonta yayi yace “to Ameenatuwa sauka ki shiga gida ni zan koma asibiti na bar aiyuka da yawa. ”

 

Turo baki tayi cikin shagwab’a tace “kaima yayah Ameenatuwan zaka ce kamar yanda Mama (kakarsu mahaifiyar su Abby) take fad’a min sai kace wata tsohuwa. ?”

 

 

Rik’e kunninsa yayi yace “sorry meenat d’ina sub’utar baki ne. ”

 

Murmushi tayi tace “na hak’ura sai ka dawo. ”

Tana gama fad’in haka ta bud’e motar ta fice tana d’aga masa hannu, shima hannun yake d’aga mata har ta shige gida sannan yaja motarsa ya koma asibiti zuciyarsa cike da nishad’i, hak’ik’a in yana tare da Meenat yana samun kansa cikin farin ciki mara musultuwa, yana so ya sanar mata soyayyarsa amma ya rasa ta inda zai b’ullo mata, dan shi sam baya son abinda zai b’atawa Meenat rai, yayiwa kansa alk’awari duk randa ya fad’a mata soyayyarsa tace bata sonsa ba zai mata dole ba.

 

 

 

 

Muje zuwa

1 thought on “Ni da Ya ya Al’ameen Hausa Novel Complete”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top