Hausa Novels

Ni da Yaya Marwan Love and romantic story

Ni da Yaya Marwan Love and romantic story

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*NI DA YAYA MARWAN*

 

 

_Love and romantic story_

 

 

_TSARAWA DA RUBUTAWA_

 

 

_HASSY SOJA_ ::

 

 

*ELEGANT ONLINE*

 

 

*Allah ya jikan iyaye na yayi masu rahama*

 

_*Godiya ina mik’a d’inbin godiyata ga Allah subahanahu wata’ala daya bani damar fara wannan sabon book din lafiya”yadda nafara lafiya Allah yasa nagama lafiya Amin ya Allah*_

 

 

 

_*Gargad’i.l, banyarda wani ko wata yajuyamin da labari ba …idan akayi haka to gaskiya sai mun samu matsala da ko wane ne kuwa insha Allah kuma zan d’auki mataki”*_

 

 

 

*Amman fa ba kullum zan riƙa posting ba sai naga ruwan comment da sharhi*

 

 

_*Wannan labarin tunda daga farko har karshin sa na sadaukarwa ga Masoyana ƙasashe dabam dabam ina alfahar da ku sosai*_

 

 

 

_Bismillahir Rahamani Rahim_

 

 

*Free book*

 

 

*Page one__________ 1&2___________*

 

Gidaje ne guda biyu ya cika da yan biki mutane har waje wace kawai ake da abinci Kala kala daban dabam dukk wanda kagani fuskar sa dauke da murmushi Yara sai guje guje suke farfajiyar gidan wasu ƴan mata ne suka fito daga wani bangaren fuskar su ta sha make up masu kiɗin ƙwaraya suna ta kiɗin kwarrya wasu ƴan mata kuma sulfe kawai suke farfajiyar gidan cike take da mata Umma ce tsaye da wata mata suna magana sai ga wata tazo tana cewar “Maryam Karfe nawa za’ayi wankan Amarya ne wai mutane sai tambaya suke”!? Ma yarda duban ta tayi ga matar tace “Sai anjima da la’asar insha Allah Hajiya murja” yauwa shiyasa na tambaya juyawa tayi ta fice gurin sannan ta cigaba da maganar da suke, cikin ɗakin kuma Hajiya Umaima ce tsaye cikin falon mutane dukk sun cika falon wata hamshaƙiyar mata ce tazo tana kallon su tace “Hajiya ya hidimar biki”!? Wlh Alhamdulillah Hajiya sai yanzun “!? Eh wlh kin san yarana basu dade da dawowa ba, acan ɓangaren kuma dakin da ƴan matan Amarya suke zaune saman kujera har saman bed su kuma ƙasa Amarya Nabeela ce zaune gaban merro tana kallon fuskar ta da tasha make up sosai Addan Ayshat sai Addan Ummu Salma sai kawayen su da ke zaune cikin ɗakin surutu kawai ake acikin dakin wayar ta ce tafara ringign ɗauko wayar suna my Sweetheart ne yake yawa ga screen ɗin waya ɗauka tayi tare dukka sallama cikin sanyin murya nace ” Aslm Alkm mySweetheart “acan bangaren Yaya lameer yace”Amin wslm Amarya ta nasan yanzun kina cikin farin ciki sosai ko”Uhmm ai kai ma kasan haka” wow gaskiya ne nima ganin har na gyara saura minti biyar a daura shine nace bari dai na kira ki naji zazzaƙar Muryar ki”lumshe idanuwan ta tayi tace “Allah ko Ango na”!? Sosai ma kuwa farin ciki raina” nima haka Ango na yau fa wlh ina cikin farin ciki, sosai”Wow yanzun dai bari na barki ki huta kafin zuwa anjima”wani irin faɗuwar gaba taji lokacin ɗaya hankalin ta ya tashi muryar ta na rawa tace “to Allah ya kaimu lfy ka kula man da kanka sosai” insha Allah kashe wayar ta tana ajiyar Zuciya gaban ta sai faɗuwa yake kallon ta Addan Ayshat tayi tace “ke lafiya dukk kin wani firgita”!? Kwalla ne suka zubo mata tace “Addan wlh ina jin gabana yana faɗuwa sosai”girgiza kai tayi tace “ki rinka cewar Innalillah wa inna ilaihir raji un kin ko”!? Eh insha Allah.

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Bayan Ya lameer ya ajiye wayar sa marar sa yaji ta ɗaure sai yaji hancin sa da sanyi hannu yasa ya laƙato jini yake zubowa da sauri ya ɗauko toilet pepa goge jinin yayi yana ajiyar Zuciya yace “ya Allah can yaji mararsa ta wani irin juyawa da sauri ya zuɓe ƙasa yana nishi sama sama da sallama captain yashigo cikin ɗakin sanye yake da shada bullur da tasha aiki dakk bullu sai hular sa itama bullu ce tare da takalmin su wow kamar shine Ango fuskar sa yau da ɗan fara’a yana ahankali yake takowa har yazo inda Ya lameer yake zaune saman bed ya dafe kansa kirjinsa da zuciyar sa ciwo suke masa hannun sa ya ɗaura saman kafaɗar sa yace “Haba dai Lameer kai fa kawai ake jira” ahankali ya ɗago fuskar sa wanda jini yake gangaro Zaro ido yayi cikin tashin hankali yace “Subhanallah ciwon menene”!? Ajiyar Zuciya yayi muryar sa na rawa yace”bani da lfy wlh” dafe kansa yayi yace “to meyasa baka kirani mukaje asibiti ba”!? Murmushi yayi yace “Aa basai anje asibiti ba” Himm! To yanzun dai katashi mu lallaɓa muje gurin ɗauren Auren idan angama sai mundawo gida”Har ya buɗe baki sai amai jini hankalin captain yayi mugun tashi amai jini kawai yake Sannu ahankali amai jini ya tsaya sai famar ajiyar Zuciya yake muryar sa na rawa yace “ruwa Captain ruwa”kallon sa yayi cikin tausayawa yace “ruwa zaka sha”ɗaga masa kai yayi shi kuma da sauri yajuya ya ɗauko ruwan ya bashi amsa ruwan yayi jikinsa na rawa ya ɗan kurkure bakin sa sannan ya kurɓa ruwan, cire mallun mallun ɗin yayi ya ɗauko Mopping ya fara goge gurin bayan ya gama gogewa sannan ya ma yarda da Mopping din yadawo, ya feshe dakin da turaruƙa masu shegen kamshi Alhaji Ahmad ne ya shigo cikin ɗakin yana kallon su ya fada yake masu yace”Lameer marwan zaman me kukeyi acikin wannan ɗakin saura fa minti ukku ɗaura Aure fa”Runtse idanuwan sa yayi yace “Zamuje yanzun ina jiran lameer ne mutafi” too ƴan Albarka kusan Aure ba wasa bane ku hanzarta kunji ko”!? Too Abba”har ya juya sai yaji muryar Lameer yace “Abba”!? Juyawa yayi yana kallon sa yace “Naam akwai magana ne”!? Wata katuwar takarda ce ya ɗauko yana miƙa masa yace “ga wannan idan kaje gurin ɗauren Auren sai ku karata tare da Abby da Uncle har da liman”dawowa Abba yayi ya amsa takarda yana dubawa Amman be buɗe ba haka ya juya ya fice daga cikin ɗakin ajiyar Zuciya yayi yana kallon amininsa murmushi yayi masa yace “dan Allah ka kwantar da hankalin ka please captain” shiru yayi yana kallon sa yace “haba dai na fa kwantar da hankalina fa kace Himm!” Haye bed yayi yana dariya kaɗan kaɗan, shaƙuwa ya farayi ahankali ahankali ta fara yawa da sauri Captain ya kalle sa yace “Subhanallah shaƙuwa kuma ko na ɗauko maka ruwa kasha ne”!? Ɗaga masa kai yayi alamar eh hakane “miƙewa yayi yaje buɗe firji ruwan sanyi ya ɗauko ya rufe firji din kamar an ce yajuyo wani irin abu ne yaga Lameer nayi hannu yake miƙa masa alamar yazo kusa da shi da sauri ya tako yazo kusa da shi ya zauna yana masa sannu hankalin sa yayi mugun tashi nuna masa wata ƴar takarda yake sosai shakuwar take damun sa idanuwan sa ya saukar ga takarda hannun sa ya ɗauko tarkadar yana juyawa yana kallon sa jini yake gangaro ta hanci ta baki muryar sa na rawa yace “ka karanta bayan kwana biyu da mutuwa ta”girgiza masa yake hawaye na zubo masa yace “Aa Lameer bazaka mutu ba insha Allah muna tare”murmushi yake masa yace”ka yafe mani sannan kuma kace Nabeela itama ta yafe mani ni dai na yafe maku duniya da lahira” na yafe maka Aminina lameer “murmushi yayi yace “kiran masu Abba”zaro wayar yayi kira su Abba lokacin har sun gama ɗauren Auren kuma sun karata takarda da ya basu Captain ya sanar da su halin da ake ciki sannan ya kashe wayar sa yana Aminina”ko mint biyar ba’ayi ba sai gasu shigo cikin ɗakin da yawa hankalin kowa tashe da sauri suka ƙaraso gurin sa suna masa sannu ko da ya buɗe bakin sa halshen sa ya ƙare ya fara kallon dama da hagu yana cewar” lailai’ilaha illaha Muhammadu rasulillahi sallahu alaihiwasallam” acikin Zuciyar sa Shike nan komai nasa yayi tsaye ciff “gaba kowa ya ɗauko cewar Innalillah wa inna lillahi raji un Innalillah wa inna lillahi raji un ya Allah ya gafar ta maka Al,amin.

 

 

Dai dai wannan lokacin gaban Nabeela yayi mugun faɗuwa tace”innalillah wa inna ilaihir raji un Allahummah ajirni fi’musibati wakalinni khairan minha itace addu’ar ta ke mai maitawa jikinta ne ya ɗauke mazari dumm dummm hawaye ne suka zubo mata rike Addan Ayshat tayi tace “Aunty Ayshat kalle ni please” Ɗago fuskar ta tayi tana kallon kanwata dake rawar jiki tace “lfy ke meyake faruwa da ke”!? Yaya lameer ko Yaya Marwan kamar wani mumuna abu yana faru da ɗayan su” kee wai bana ce kiyi addu’a ba ne dan Allah ki kwantar da hankalin ki please kada mutane su gane…..

 

 

 

 

Wani irin sarawa kan Captain ya yi, Captain dai soja ne, sojan ma baba, wanda ya shiga gwagwarmaya da manyan yan ta.ada, wanda ya kwana cikin rami, wanda ya shiga hatsari kala daban daban na rayuwar yau da kulun, yau gashi gaban ikon mai duka, yana ji yana gani amininsa ya mutu ahannun sa ga gawarsa kusa da shi Ya lameer fuskar sa dauke da murmushi, bakin sa na rawa yace “Innalillah wa inna ilaihir raji un Allahummah ajirni fi’musibati wakalinni khairan minha Ya Rabbi kuka ya fashe da shi kamar ƙaramin yaro Abba shi ma kansa jarumta ya nuna yace “Aa Captain kuka ba naka bane kayi haƙuri Captain “kallon Abby yace “asanar da mutane mutuwa sa ”

 

 

 

Mallamai na zaune cikin masallaci mutane ne cike cikin masallaci Abby ne ya shigo cikin masallaci yace “jama’a to Allah yayiwa Al,amin rasuwa yanzun” salati mutane suka ɗauka, ai kuwa wannan mumuna labarin iske kunnen su Umma hankalin kowa ya tashi Amarya kuwa labarin na isowa kunnen su Wani irin zubur tayi tana jada baya tana girgiza kai muryar ta na rawa tace “Aa ba dai Yaya lameer ɗina ba yanzun fa mu kagama magana da shi yace wai ya mutu aa wani dai ba shi ba”Wata dattijuwar mata, ce tashigo cikin ɗakin tace “Nabeela sai hakuri an riga an ɗaura Aure kuma sai gawata ƙaddara ta gif ta Allah yayi masa rasuwa”Zaro ido tayi tace “Innalillah wa inna ilaihir raji un Allahummah ajirni fi’musibati wakalinni khairan minha Yaya lameerrrrrrrrr ta yanke jiki ta faɗi ƙasa some……….

 

 

*ASALIN LABARIN*

 

Wani katafarin Babban gida ne mai ɗauke da ɗaki goma sai harabar gidan babba gidan abun sha’awa Alhaji Mus’ab ne Babba matan sa biyu wato mahaifin MARWAN sai Matar sa wato mahaifiyar MARWAN Ummu Salma ita ce ta farko yaranta MARWAN shine babba Kuma captain MARWAN kuma doctor ne sai Kanen sa khalid sai Ayshat Hajiya Umaima yaran ta biyu Ummu khairan da Andisha sai Alhaji Habib matan sa biyu shine Mahaifin Nabeela sai mahaifiyar ta wato Maryam yaran ta ukku Ak shine Babba sai Nabeela sai kanenta Ammar gaba yaran gidan goma ne famliyn sai san barka, a wani bangaren kuma Kakan su ne ke zaune A cikin gidan iyayen su mata kan su haɗe yake , Zaune suke cikin falon gaba ɗaya dama dukk ranar juma’a ana taruwa a babban falo Karar machee ne kawai yake tashi sosai cikin gidan Nabeela ce saman machee goya Ammar tayi suna zagaye harabar gidan take Nabeela haɗaɗiyar yarinya ce bazata wuce shekara sha shida ba zaune take saman mashin tana zagaye harabar gidan….

 

 

 

Wani haɗaɗin matashin saurayi ne sanye yake da kakin sojoji miƙewa tsaye yayi yana kallon mejo fuskar sa ɗaure yace “mejo me kuke tunanin ne yanzun ashe har yanzun ba samu wace zata maye gurbin ƴar aiki na ba”!? Kayi haƙuri Captain wlh har dai ba’a samu ba Amman insha Allah za’a samu” cewar mejo kansa a ƙasa mtsss wani dogon tsaki yaja yana kallon sa cikin takaici hanya ya nuna masa yace “……….

 

 

_HASSY SOJA_

 

07063617906





Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022



Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


1 Comment

Leave a Comment