Ni da Yaya Sadeeq Hausa Novel Complete
Tag: Ni da Yaya Sadeeq Hausa Novel
A zaune nike a kan tabarma cikin baranda isaka na kad’a bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gidan mu Ganyen ta na fad’owa ‘kasa gunin burgewa Dambu ne a gabana cikin wata ‘yar samira inaci ina sud’e yatsun hannu na saboda dambun yayi min dad’i banason ya’kare
Kawata Ladiyo. Ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da jini koda na d’aga kaina na kalle ta bance mata komai ba Na maida kaina kasa na cigaba da cin dambu na, Saida na cinye dambun tas Sannan na kora da ruwa, Baki na bud’e iya ‘karfi na Nayi wata katuwar gyatsa tarashin mutunci, Irin wacce idan yaya Sadee’k ya na guri nayi yake buge min baki.
Kallan Ladiyo nayi Na ta’be baki nace “Ladiyo lafiya kika zo ki ka tsaya min a kai ko aiko akayi?”.
Ladiyo. Dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana iya fad’a min na bata kunya tana kuka take fad’a min abinda ya faru.
Tace “Kinsan yaron da jiya muka barar mai da markad’e ai Dazun Umma ta ta aike ni gidan su Zulai anso mata kud’in zubin a dashi,bayan na anso kud’in na had’u da yaron akan hanyata ta dawowa Ni bansani ba a she nan ne layin da yaron yake, shine yayi taimin ruwan duwatsu tako ina har wasu abokan sa suka taya sa Allah ya temake ni Baban
Ramma Yazo wucewa sai yaga abinda ke faruwa, nan take ya tsawatar musu shine suka ‘kyale ni amma wallahi inaga da sai dai a d’auko gawa ta saboda jifan da suka min bana wasa bane Ko gida banje ba nayo nan saboda ya bani sa’ko”. Yace in fad’a miki “wallahi kema saiya fasa miki goshi”.
Karanta Littafin Gidan Uncle Complete
Nace “Kan uban_nan yanzu dama acikin’ kauyen nan a kwai wanda zaija dani har ni zaice zai fasama goshi To wallahi kaf kauyen Dande. Banga mai fasamin goshi ba amma tunda yace haka muzuba ni dashi shege ka fasa kafin ya fasa min ni zan fara zuwa gidan su in fasa na Babar sa inya so kinga yaji dad’in fasa min nawa da hujja”.
Inna da fitowar ta kenan da Buta ri’ke a hannun ta da alama daga ban d’aki ta fito Tace “ke da wa siddi’ka. Ki ke yin wannan ashar d’in kamar bakya zuwa islamiya”? .
Nace “yo Inna bakiga Ladiyo bane?”.sai alokacin Inna ta lura da Ladiyo da ke a tsaye gindin rijiya ta d’ora hannun ta a kai. Inna Tace “na ganta sai akai yaya”?.
Cikin ‘kosawa da tambayar da Inna take min nace “yo wai ke Inna bakiga goshin ta bane a fashe jini yana zuba?”.
Inna tace “na gani mana. tunda ta’ki rabuwa dake ai tana tare da wahala gashi ta zama lusara bata iya ta’buka komi Se tsokana fal cikin ta tsokana kuma tame ‘karfi ce”.
Nace “yo Inna wanda yafasa mata goshin ne nima” yace “zai fa samin duk sanda muka had’u shine abin yabani dariya da takaici Har kika ji nayi wannan ashar d’in Idan duka ‘kauyen nan gatansane wallahi se naci ubansa duk abinda ze faru ya dad’e be faru ba Besan wace ce Siddi’kar Inna ba shiyasa amma ko yaran goye aka amaba ta masa suna na Nan take jikin sa yake fara rawa saboda karo dani babu dad’i”.
Banyi aune ba naji anbige min baki Da masifa na d’ago kaina dan naga wani mara kunyan ne ina magana ze bigen baki.
Amma sai mukayi ido hud’u da yaya Sadeeq Turo d’an ‘karamin baki na nayi. Yayin da shi kuma ya kashemin ido d’aya.
Yace “saidai ke ki ci uban ki, kamin shi yaci nasa, yau ina gida bazani gurin aiki ba Saboda haka kema babu inda zaki fita sakarya da’ki’ki ya kawai ba arabi babu boko se yawan gad’a a dan-dali ke a cikin matan ‘kauyen kin fita zakka saboda kinfisu wauta da tuma sanci.
Inna na daure miki gindi kina yin abinda kika ga dama ko Kina ganin kamar gata take yi miki To kisani inna ta riga da ta gama cin kasuwar ta Ke kuma yanzu kika fara taso wa. Dan baki san komi game da rayuwa ba. kwata kwata ma nawa kike? ko 14 years old baki kaiba amma kin addabi mutanan gari kullum ana cikin kawo min ‘karar ki ina bada ha’kuri”.
Yace “ke yakike da suna ma? Ladiyo yake nunawa da d’an yatsan sa manuni ya
Ladiyo dake a tsaye hannun ta akan goshinta, tace ” “sunana Ladiyo”.
Yaya Sadeeq yace “oho koma dai maye sunan naki maza tashi kibi nan yai mata nuni da hanyar fita gidan.”
Yakuma cewa “ko a ‘kofar gidan nan idan kika bari na kuma ganin ki to kashin ki ya bushe. Bare kuma in ga wa’innan ‘yan ‘kafafuwan naki a cikin gidan nan. Allah sena ‘ba’b-‘ba’bla ‘kafa fuwan. Ina fatan kinji abinda nace miki idan kunne yaji gan-gar jiki ta tsira.
Yace “oya maza zo kibi nan tun muna sheda junan mu”
Ladiyo jiki na ‘bari ta bar gidan mu. A d’ari da hamsin.
Kallo na yayi muka had’a ido da shi ya wurgo min hara-ra Nima na rama ina ‘kun’kuni ciki-ciki nace “nima idan ido ne ba a fini ba bare ayimin bara zana dasu kuma mu zuba ni da kai d’in.
Yah Sadeek yace “ke me kike cewa?”.
Inna tai saurin cemai ba da kai takeyi ba tafi abinka”.
Yah Sadeek yace “Inna kiba ta abinci na takawo min”.
Inna taja dogon numfashi tace waini Garba me yarinyar nan taimaka ne haka? daka tsaneta. banason haka fa tun ba yau ba nasha fad’a maka Amma dake ka rainani bakajin magana ta. Ko kad’an saboda ni kaka ce To alhaji karami na nan zuwa wata ya kusan ‘karewa idan kai ban isa da kai ba shi na isa dashi. Kuma shine mahaifin ka Idan yafad’a maka wata ‘kila kaji nasa tunda ka ‘ki jin nawa ni”.
A sakarce yaya sadeek ya kalli Inna yace “haba hajjaju makkatun mu karrama ranki shidad’e Ki dad’e kiyi ‘kar’ko kiyi shekarun bishiyar dabino Ni na isa in raina ki duk da cewa nike aurenki amma ke ke bada umarnin Kuma yadda Kiki ce haka za ai nadena daga yau babu ruwana da ita.”
washe baki inna tai tace ” ko kaifa Garba shikenan ya wuce amma da kasa ka ‘yar mutane a gaba se ramewa take shiga ciki yanxu zansa ta kawo maka abincin naka
NI DA YAYA SADEEQ
love story 2021 typing free book_
Story & Writer by
Siddiqahtul khair Y Faru
(S beauty ✍️)
بسم الله الرحمن الرحيم
_________Inna tace, “Siddi’ka daure ki tashi ki kaiwa yayan ki abincin sa ya dawo daga aiki ya gaji ga yunwa”. ‘Daure fuska ta nayi ina turo baki nace, “ni dai Inna bazan kai mishi abinci ba duka na zeyi, baki ga yadda yake kallona ba kamar wani tsohon maye, kwana biyu be samu ya dakeni ba, kinsan halin muguntar sa ba se nayi masa laifi ba, yana iya rufo ‘kofa idan na shiga kinsan shi kullum cikin jin haushi na yake”.
Inna tace, “Garba ko kunnan ‘kashi ne dashi baze dake kiba nayi masa magana kuma a gaban ki akai, idan ko ya ta’ba ki sena had’ashi da Alhaji ‘Karami. Tashi maza kije ki kai maisa yar albarka
Nace, ” yo ina abincin nasa yake Inna?”.
Inna tace, “yana kitchen mana inda kika d’auko naki”.
koda na ‘dauko abincin a saman kaina na d’orashi ina d’igir-gire. Inna tace “A’a fa kada tsautsayi yasa ki zubar mai kinga yana cikin fushi babu abinda baze iya miki ba”, nace “haba Inna baze zube ba sedai idan kece kike so ki zubar dashi, amma ai ba yau nikeyi ba kuma be ta’ba zubewa ba”, Inna tace “Allah ya bada sa’a ta shige d’aki abinta” nace “amin hajiya Inna”
Ina tafe ina ‘yan wa’ko’ki na ina tafa hannu, hanyar d’akin yaya sadeeq na nufa saboda yana daga hanyar waje ne. Koda nazo ba’kin d’akin ban tsaya yin sallama ba kuma ban buga kofar ba duk da yasha yimin gargad’i a kan inde nazo d’akin sa kada nashiga se nayi sallama ya bani izinin shiga ko kuma na buga masa kofar. Ina tura ‘kofar na bankad’a labule nakutsa kaina ciki. Yanayin da naga yaya Sadee’k yasa nasaki wata uwar ‘kara, har saida kular abincin kaina ya fad’i murfin kular ya bud’e dambun ciki ya watse.
A fusace yah Sadee’k ya nufo ni kamin in Ankara ya wanka min kyawawan maruka. Haske nagani wal a idona. Har saida gani na ya d’auke na wasu ‘yan da’kiku, babu riga a jikin sa kirjinsa a kwai yalwa taccen gashi baki sid’ik dashi kwance luf-luf banta’ba ganin namiji a haka ba tunda nike a rayuwa ta, ja da baya na fara yi yah Sadee’k kuma yana nufo ni, na furgita dashi matu’ka. Saboda haka na fara ihu iya ‘karfina yadda Inna zata ji tazo ta cece ni. Takaici na ne yakama ya Sadee’k cikin zafin nama ya ‘karaso inda nike belt din jikin wandan sa yaciro se alokacin nai yun’kirin guduwa daga d’akin. Amma caraf yakama hannu na sannan ya maida ‘kofa ya rufe harda samata kye da sakata, Duka na ya fara yi kamar Allah ya aiko shi, kota ina zabga min belt d’in yake yi. Ihu nikeyi da duka murya ta, saboda naga so yake ya kashe ni tun kamin lokaci na yayi.
Inna da dake cikin d’aki tajiyo ihuna da gudu ta fito tazo bakin ‘kofar d’akin sa buga ‘kofar tafara yi tana kiran suna na da’karfin ta. Ganin ba kiran suna nane mafita ba yasa tafara kiran sunan yah Sadee’k, Garba Garba kada ka kashe yarinyar mutane na shiga uku, dan Allah kaya’kuri ka ‘kyaleta haka nan kome tai maka ai tada ku bazata ‘kara ba daga yau insha Allah”.
Tun ina iya jiyo muryar Inna tana magiya har nadena jiyo ta nasan ta tagaji ne saboda bata jure yawan magana yanzu se hawan jinin ta ya tashi. Sadeeq kuwa kunnen uwar shegu yayi kamar bashi Inna kema magiya ba, tuni Inna hawaye sun fara zarya a kan kuncin ta saboda tasan yah sadeeq zeyi d’anyen aiki,
Ni kuwa har muryata ta dashe ko sautin ihun nawa ya dena fita, hawaye ne kawai suke zubar min. Kuma har yanzu be dena duka na ba saida yaiwa jikina rud’u rud’u. Sannan yacemin “shiiiiiiii” yana wani irin huci kamar yayi dambe da ‘kartai.
Murmushin mugunta yayi, Nikuwa a cikin raina nace, “mugu burin ka ya cika kaci zalina” wata doguwar ajiyar zuciya naja kamin na fara sauke numfashi da sauri da sauri”. Yah Sadee’k yace “idan na’kara jin kinja ajiyar zuciyar nan wallahi saina sako miki farkon dukan nan koma nayi miki mafiyin wanda nai miki yanzu”. Ya cigaba da cewa “so nake kiyi shiru kamar bakya gurin nan ko numfashin ki kar inji saukarshi. Hakan ne kawai idan kikayi zaki temaki kanki, kifita daga d’akin nan lafiya da ‘kafa-funki batare da anzo an d’auke kiba”.
Nasan halin yah sadeeq sarai ba ‘karamin mugu bane, saboda haka nayi Kamar yadda yace nayi “haka nayi shuru kamar wacce ruwa yacita” numfashina na neman d’auke wa ina ta ‘ko’karin dawo dashi ba tare da inason yah Sadee’k ya gane ba. jinike kamar ana so a zare min raina saboda azabar dukan dana sha, gaba d’aya jikina rad’a-d’i yake min, ga kaina da nike jinsa kamar ze bar gangar jikina ya fad’i’ kasa.
lura da yanayin yadda nike ciki ne yasa yaya Sadee’k cewa ” kad’an namiki ma wallahi saboda batun yauba nasha fad’a miki kidena shigo min d’aki kamar d’akin arna, bama d’akina kawai ba duk inda zaki shiga kishiga da sallama a matsayin ki na musulma, Amma dayike kunnen ki na ‘kashi ne ina gama fad’a miki kike watsar da maganar anan, to wannan shine na ‘karshe wallahi idan aka’kara ai koki baki sallama ba kika shigo zakiga abinda zan miki”.
Yace, “Tashi kiban guri na gaji da ganin wannan mummunar fuskar taki gashi kin tsura min ido kamar sa’anki ne yake miki magana”.
Tashi tsaye nayi Ina layi ina bin bango har na iso bakin’ kofar na bud’e. Ina fitowa naci karo da inna dake faman sintiri. Kamar wacce tayi ‘karya. Cikin sauri Inna takomo ni. zubewa nai a jikin ta babu numfashi ihu inna tafara tana kiran ya sadeeq da karfinta Garba inalillahi wa innah ilaihi rajiun shikenan ka kashe ta. Garba ka kashe ‘yar mutane, bazaka fito ba mukaita asibiti ina magana kayi shuru. ya sadeeq yana jin Inna amma yai banza da ita kasan cewar yasan halin inna da zuzuta abu shiyasa ya’ki fitowa. Can dayaji ihun nata ya’ki karewa yasanya rigarsa jallabiya me ruwan madara Yafito. A zaune yaga inna dirshan, ni kuma ina kwance a jikin ta kamar matacciya, yayin da Inna keta faman jij-ji-gani tana sun batu kamar wacce tafara ta’buwa.
bece wa Inna komi ba yawu cemu cikin gida yashiga ya bud’e fridge yad’ibo ruwa me sanyi acikin kofi, koda Inna tagan shi da kofi batasan meye aciki ba, ta bud’e baki kenan zatai mai magana
ya antaya min ruwan duka ajikina harda mugunta, wata doguwar ajiyar zuciya na sauke ina ‘kan-‘kame jikina ina ‘kara shigewa jikin Inna, ta kaicin yah sadeeq yahana Inna magana. amma ganin ina motsi yasa tadanji sau’ki aranta. Tace “siddi’ka sannu, haka Inna taita kiran suna na tana min sannu, sedai na kalle ta da ido kawai saboda bazan iya magana ba.
da’kyar na iya d’aga han-nuna na mikawa Inna saboda na gaji da kwan-ciyar so nike in tashi, Inna ta fahimci nufi na saboda haka ta kama hannun nawa. Tana fadin “sannu Siddi’ka sannu kinji, Allah zesaka miki, se a lokacin na iya magana cikin wahalal-liyar murya nace “Inna zan mutu inaji ajiki na karshena yazo” nafad’a ina rushewa da wani irin kuka me ban tausayi, itama Inna kukan tasaka, tana fad’in “bazaki mutu ba ‘yar Inna saidai shi yamutu zaki tashi Insha Allah” hannun Inna na kama na d’ora a ‘kir-jina nace “Inna nan d’ina kusa da zuciya ta zafi yake min”.Inna tace “ciwo yake miki?” nace, “eh Inna, Ji nake yi kamar ba ajiki na yake ba”.
yah sadeeq da yake a tsaye tun sanda ya kwara min ruwa na far fad’o yake jin diramar damukeyi. Bakaramar dariya muka bashi ba amma yasan babu halin yin dariya yanzu se abin yayiwa Inna yawa. Dabara ce ta fad’o masa. Saboda haka yaje d’aki ya dauko wayar sa yazo yake mana video. A cewar “sa idan yashiga d’aki ya kalla abinsa yayi dariyar sa san rashi”.
Cikin muryan kuka Inna tace, “garba ashe rashin inanin ka ya kai haka. Kayi mata dukan mutuwa be isheka ba kazo kana d’aukar ta hoto. Bakomi kana lokacin ka”. Ta kuma fa shewa da kuka tace, “yanxu Garba bazaka zo kafad’a min yadda zanyi da ita ba?. Ko tunda ka illata ta shike nan burin ka ya cika?. to kiramin ubanka awaya nasan duk inda yake yaji ina nemansa zezo yanzu da gau-gawa. Idan kuma baya garin ze turomin Wanda ze share min hawaye”.
‘Dan ta’be baki yah sadeeq yayi, Sannan yamatso inda nike, ya tsugun-na han-nun-sa ya d’ora a kan wuya na, yaji da zafi sosai
Ya cewa Inna “ki d’auko mata hijabi inkaita asibiti naji jikin ta ya d’anyi zafi”. Inna tace “au ya d’anyi ne ko Garba Allah ze saka mata mugu, kaje d’akin ta ka d’auko mata kowani irin hajabi ne”. Yah sadeeq yace “Inna bafa dake zani asbitin ba a gida zan barki”. Inna na salati tana tafa hanna-yenta tace. “Garba me kace? na d’auki yar mutane na baka katafi da ita kai kad’ai kaje kai mata wani abun nasan saboda tsabar ba’kin halinka ko gawarta ma bazamu gani ba. To ban yarda katafi da ga kai se ita ba. Kafata kafar ka maza shiga ciki ka taho min nima da maya fina”.
kallon mamaki sadeeq yabi Inna dashi sannan ya ta’be baki yace, ” bari na fara fidda motar waje senazo na d’auko muku”. Inna tace “da dai yafi maka saboda bazan bari kaje ka kuma cin zalin ta ba, Nima se Allah ya tambayeni”.
Fita daga gidan yaya sadeeq yayi.
Ina kuka nace, “inna wallahi banasan zuwa asbitin nan”. Inna tace “ya zakiyi Siddik’a daurewa zakiyi dama ba a zuwa asbiti se idan ba’ada lafiya. Duk ni naja miki da dakika ce bazaki ba na rabu dake ai da haka bata faru ba”.
Yah sadeeq ne ya dawo yatar da Inna tana shere ‘kwalla. Be ce mana komi ba ya wuce cikin gida se gashi ya dawo da hajabi na da maya fin Inna. Yana zuwa ya mi’kowa Inna yace “dan Allah ni kuna ‘bata min lokaci ina da abin yi kisaka”
Amsa Inna tai bata kula shiba saboda ya gama kaita bango. Saida tayafa maya finta sannan tafara ‘ko’karin d’agani amma ta kasa, saboda shekaru sunja kuma tun ina jari-riya a cikin tsumma na take d’awainiya dani, saboda haka tace ma yaya sadeeq “.
Temaka ka d’aga min ita nasaka mata hijabin. Yi yai kamar beji abinda Inna ta fad’a ba. Kome ya tuna oho. Se gashi yazo ya dagani sama ta yadda fiskata zata kalli Inna. Saka min hajabin tayi, yasan Inna baza ta iya d’auka taba saboda haka ya ajiye ni a ‘kasa amma be sakeni duka ba. Yace “Inna muje ko,’ko’karin fara jana yakeyi, Inna tai saurin daka mai tsawa tace” wai Garba lafiyan ‘kalau kuwa?”
Be ce mata komi ba yasa’ba ni a kan kafad’ar sa, Saboda yayi min mugun ta yazuro kaina ‘kasa sosai. jini na se dawo min kai yakeyi, a haka muka isa bakin motar, a gidan baya ya ajeni sannan yashiga gurin zaman direba. Inna ma baya tashigo tana mita. domin Allah ya mata mita koda yiki yawanci tsofaffi sunada wannan mitar, kaina nadora kan cinyarta ina matso kwalla bawani bab-ban asbiti ya kaini ba illah asbitin dake cikin ‘kauyen mu asbitin shi kadai ne asbiti. kuma babu wasu kwararrun ma aikata acikin sa.
Leave a Comment